Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

a cikin wajen domin bata taba zuwa wajen da ta ji cewa ita ma kamar kowa bace irin yau , ta yi farinciki kuma ta manta duk wasu damuwoyinta.

Suna rabuwa da Su Abiel yanayinta ya canja hankalin ta ya fara tashi domin ta fara hasaso tashin hankalin da zata fuskanta inta je gida.
Sambatu ta fara tana tafiya kawai ba tare da ta ankare ba.

Tana zuwa get din gidansu ta fara labe laɓe da leke leƙen yadda za ayi ta shige.
Juyawan da zata yi kawai ji tayi Zayd ya damketa.
Tana kallonsa tsabar tsoro take jijiyoyin wuyanta suka tattashi ta yi wata ajiyar zuciya.
Ko kulata bai ba ya rike hannunta kawai ya jata cikin gidan.

Suna shiga ya ce, "Ga mu nan mun dawo ashe wai da nace ta fara gaba ina zuwa bata gane gidan bane mai taxi din ya batar da ita."

Momynta ta kalleta ta na, "Wato ke yanzu komai saidai ki fadawa Uncle dinki saboda ya shagwabar da ke,shiyasa da sassafe kika wuce biki gidan kawarki ba sanarwa ko?"

Kallon Zayd tayi da mamaki tana tunanin ta ya za ayi ace ya shirya karya don kawai ya kareta, anya kuwa shine? Inma kuwa shine din to babu shakka akwai wani abu na musamman da yake shirin haɗawa.

Murmushi ya yi yana, "ai ni nace kar ta tadaku kuna barci ba matsala amman ayi hakuri Little Princess ba zata kara ba."
Ya fada yana rungumeta tare da fadin, "Ko?

Kau da kai tayi, aiko ya danna mata mintsini a jiki, cikin sauri ta yi murmushin dole tana girgiza kai alamar eh.

Zayd ya ce, "Yawwa My Little Princess yanzu ki tashi kije kiyi wanka sai kizo in baki food ko?"

Tuni ta tashi domin daman jinta take kamar tana zaune kan ƙaya.
Ta shige dakinta.
Tana shiga ta daura hannu tana danne kanta don gabadaya juya mata yake,dakin ma juya mata yake yi addu'a ta fara , " Rabbie Inniy Lima Anzalta ilayya min khairin Faqir."
Haka ta dunga maimaitawa har saida ta ji ta fara dawowa daidai kafin ta dakata.
(Wanda daman wannan addua ce mai tasiri sosai tare da kubutar da bawa cikin yanayi mara kyau da kuma biyan bukatu na Alkairi ga duk wanda ya jibanci yinta)

Kwanta ta yi ta dan huta na mintuna sannan ta ta shi zumbur kamar an tsikareta tayi toilet wanke hannu ta yi kamar yadda ta saba, har sai tazo ta zauna kan gadon ta sai ta kara komawa a karshe ma ta je ta yi wanka gabadaya ta canja kaya, tana gama sa kaya taji an kira sallah ta koma ta dauro alwala ta yi da ta idar ma ta kara karanta Rabbie Inniy Lima Anzalta ilayya min khairin Faqir sannan ta tashi ta fara gyaran dakin duk da cewa a gyara yake babu wani datti amman ita gabadaya a tsarge take tana jin kamar tana zaune cikin datti shara tayi ba adadi haka ma gadonta ta kade ta kara gyarawa yafi a irga.
Daga karshe kuma kawai ta tsaya tana irga tiles din dakinta.
Zayd ne ya hankada kofar yana, "Kina ina Little Princess? Azo aci abinci don na sanki da kin son abinci yanzu sai ki kama barcin karya."
Ya rike mata hannu yana janta suka fita.

Ji take kamar ta fisge hannunta ta koma dakinta amman ba dama haka ta bisa yana janta.

Dadynta ya ce, "ta bata rai wai bazata ci ba ko?"

Zayd ya yi dariya yana, "eh fa wai ita ta koshi bata jin yunwa,bata so ta kara girma ta kamoni ne, don haka ni bazan yarda ba da kaina zan bata abincin ma."

Dukan su suka yi dariya.
Dauke abincin ya yi daga kan Dining ya kai kasa ya zauna ita ma ya zaunar da ita.
Ya diba yaji ya cika acikin abincin har saida ya canja kala,kuma yasan kwatakwata bata cin yaji arayuwarta saboda ita ne ma basa sa yaji a abinci sai dai a aje duk mai so yasa.

Zai bata a baki ta kau da kai, ya zare mata ido daidai kunnenta yana fadin, "in baki ci abincin nan ba sai kin jawa kanki bala'in da bakya zato ba ke Yar gantali ba? Har kin iya tafiya gantali ko?"
Sannan ya bude muryarsa yana matsar da kansa daga kunnen ta ya ce, "Haba My Little Princess My Beautiful Daughter, Oya take."

Bude bakin ta yi don dole tana jin abincin ya sauka akan harshen ta rufe idanu tsabar azabar yaji.
Zungureta ya yi ta wuya saida ta kara bude bakin, haka ya dunga tura mata zata dau ruwa ya bige hannunta.
Tana ci tana hawaye ya ji ta ko ina harshen ta har yana sidewa.

Da ya ga ta fara shesshekar kuka sai ya kalli su Momynta yana, "Yau fa abun ya girmama kyakkyawar 'Yata harda kuka akan cin abinci."

"Kai ne ka damu sai ta ci ai, da ka barta kawai cikinta ne ai zata yi bayani." Dadynta ya fada yana kai abinci bakinsa.

Zayd ya rungumeta yana shafa mata baya, "Aa nikam Babyna bazata zauna da yunwa ba,yi hakuri ki cinye kinji zan siya miki chocolate da ice cream."

Momynta ta juya tana kallon su , "eheen daman kai kake bata ta da batun su chocolate ai su zata zauna ta cinye tas amman ban da abinci."

Zayd ya yi dariya, "to don wa nake neman kudi? Ni fa don Little Princess nake neman kudi bana so ta nemi wani abu ta rasa don haka zanyi mata duk abun da takeso muddin bai fi karfina ba."

Abincin ya shaƙeta ga yaji da ya rike mata kirji da tayi wani nishi tuni ta fara aman abincin da ta ci a jikinsa har fuskarsa..
[11/20, 1:03 PM] Xayyeesherthul-humaerath🥀: *°°°VIXEEN°°°*

*NOBLE WRITERS ASSOCIATION✍🏼*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.```
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
*https://www.facebook.com/106494781436168/*

_#5Stars/Zeeyter/Yel/Freeya/Vixen._

©️ *XAYYEESHERTHUL-HUMAERATH*

PAGE-14

Kan ya rufe baki aman ya shige masa.
Wani irin zare idanu ya yi,yana kallon Deejerh,ya daga hannu zai finciketa kenan ya ji Muryan Dadynta na fadin, "Subhannallah Daughter lafiyanki kuwa? Ya zaki mai amai a jiki?"

Kau tar da kai ya yi ya zubda aman da ya shigan masa baki, sannan ya rungumeta yana shafa wuyanta, "ina tunanin zazzabi take fa shiyasa ma ta kasa cin abincin, Sorry Little Princess da na sani ban miki dole ba duk laifina ne."

Momynta ta ce, "Ayyah Sorry Daughter bara in dauke box din magani sai abata ko?"

"Oh No bari dai in kaita dakin in wanke mata jikin sai in bata ta sha ta kwanta ta yi barci."
Zayd ya fada.

Momyn ta karaso garesu tana, "aa ka ga ta bata ka,kawai ka je dai ka wanke jikinka,ni zan riƙeta muje dakin sai in wanke mata jikin.

Deejerh kam tunda ta rufe idanunta bata kara budewa ba,ta saki baki kawai iska na shiga ita kadai tasan azabar da take ji.

Zayd ya ce, "Kar ki damu dani kam in ban wa Daughter ba,wai wa zanwa ne? Kuje ku huta kawai na san kun gaji wunin yau i will take care of her please."

Ya fada yana rike hannun Deejerh tare da dafe mata Ka fada ya nufa dakinta.

Dadynta ne ya bisu da kallo yana dariya, "Ke kam kin san ba a shiga tsakanin Daughter da Uncle dinta, kawai ki barsu."

Ita ma dariyan ta yi tana dafa shi, "wai ni naga ta bata shine amman ai shikenan na bar shiga, mu tafi daki ko?"

Da murmushin shi ya ce, "Yessss Yar Kyakkyawa Yar sukuta." Ya karasa maganar yana mata cakulkulu.
Ita ma fara yi mi shi tayi , ya shige daki da gudu ta bi bayansa.
★★suna zuwa ya hankadata dakin ya kulle kofar.

Mari ya fara kakkafa mata ta kowanni bangare sai dai kawai taji saukar mari.
Sai da ta kai kasa.
Ya durkusa ya na fige gashin kanta kamar yadda ya saba yana, "Wato tsabar mugunta da mugun hali ni zaki yiwa amai a jiki? A jikinma bai isheki ba har sai kinyi mun abaki? Wato ke bakya jin magana ko? Kin san salon mugunta da kazanta yau zanyi maganinki, sai nayi maganinki."
Ya hankadata cikin toilet.

Suna shiga ya hankadata kasan toilet din ta yi flat.
Shi ma ya durkusa yana kara damko gashin kanta.
"Yau harshen ki ne zaiyi mopping din Toilet dinnan da harshen ki zakiyi ba ke kazama ba? Ga karshen kazantarki nan ai."

Haka ya dunga dungura mata kai kan tiles din Toilet din , ganin ta kankame bakinta ya bige shi da hannu ya matsewa saida ta bude, ya kai Harshen nata ƙasa sai da ya tabbatar ta fara kwasan kazantar toilet din a bakinta kafin ya ci gaba da jan gashinta yana zagayar da ita tamkar moper.

Sai da ya tabbatar ta yi laushi sosai kafin ya sake mata gashin yana, "Wannan Kadan ne, babu shakka sai kin fadamun inda kike gantali yau,ki jira dawowata."

Ya fice a toilet din ya barta.
Yana fita ya kulle dakin nata ya yi gaba abin sa.

Jikinta na rawa ba karfi gabadaya hankalinta ya tashi yadda yasa ta goge toilet din da bakinta duk ta gama tsarguwa haka ta ja jikinta ta dauko rubar zumanta ta diba ta dunga wanke bakinta, wanke bakin ta dunga yi wanda ita kanta bata san adadi ba,kuma ta gagara hana kanta gogewan.

Ruwan toilet din duk kayanta ya na ɗe,haka ta cire kayan ta canja tasa wani,har lokacin ta garara rufe bakinta domin ya farfashe ban da radadi babu abun da yake yi mata.

Tunda Zayd ya yi wanka bar gidan bai dawo ba sai 10:00pm
Ya tafi gun yan matan shi kasancewar handsome guy iya daukan wanka yasa mata har bibiyarsa suke suna yi masa tururuwa, amman duk da hakan aranshi bai jin dadin wata 'Ya mace fiye da Deejerh wanda hakan yasa har sai ya zaɓe macen da yake son hulɗa da ita, wasu ma sukan biya shi kafin yake amincewa da su.

Yana taba kofarta gabanta ya fadi tayi wata irin zubura.
Rai ɓace kamar kashin shanu ya shiga yana fadin, "ki biyoni nan yanzu maza ki fito."

Bin bayan sa ta yi domin tasan ko da taki fita sai da ta karawa kanta azaba badai ta rage ba.

Suna zuwa wajen mota ya kalleta,da kanshi ya gyara mata gashinta kanta da rigar jikinta ya fesa mata turare kafin ya ce mata ta bude gaban mota ta shiga.
Har lokacin jikinta rawa yake musamman da ta ga yasata gaban mota tasan lallai da wani abu gangarimi da yake shiryawa.

Driving yake yana lure da yanayinta cikin bacin rai ya yi mata tsawa ta razana tana rungume kujerar motan.
"In baki daina munafurcin rawar jikin nan sai na take ki da motar nan na tarwatsa namanki ki sake jiki ki zauna kuma ki sake fuska don ki tabbatar da cewa in na rasa deal din yau silar shashancinki sai na miki shashancin da yafi naki."

Ya tsaida motar yana ja mata riga duk kirjinta ya fito waje.
Zata maida ya bita da mummunan kallo.
Ba yadda ta iya haka ta zauna suna ci gaba da tafiya ba yabo ba fallasa.

Kamar daga sama aka zagaye motar ta shi, cikin firgici ya taka birki ganinsu da bindigogi zuciyarsa na bugawa ya ce, "Na shiga uku kar yan sanda ne, shikenan ,shi....

Kan ya karasa an bude kofar ana tura ƙyeyarsa da bindiga.
Rawa jikinsa ya fara kamar mazari.
Wasu irin samudawan maza ne da bindigogi da sanadina kayan jikinsu gabadaya bakake.

Da wani ya buga masa bindigar aka, Zayd ya gama sadakarwa an harba masa ya mutu fitsari ya fara a wando tsabar razana.

Deejerh kuwa mantawa tayi da halin da take ciki, wata irin dariya ta fara ba kakkautawa ganin yadda lokaci guda Zayd ya birkice kamar ba shi ba.

Idanunsa a rufe ya ce, "Don Allah karku kasheni, wallahi babu abun da zan mata, Babu inda zan kaita yarinyar yayatace bazan mata komai ba, na tuba zan fada maku gaskiya."

Wani wanda yake babba cikinsu ne ya fito daga mota,ya kalli Deejerh dake gefe wasu biyu sun tsaya da ita suna gadinta ya sake mata murmushi kafin ya karasa gaban Zayd.

Kafarsa ya daura akan tsakiyan kan Zayd kafin ya fara wata irin dariyar mugunta, "Kai karamin dan duniya ka bude idonka nine nan, ashe kai har yanzu ba ka gama kwarewa ba har kake jin cewa zaka iya zalintata ka cuceni? Ka ci amanata? Wai kana ganin ka tsira ko? Lallai to gani na fito daman na fada ma ai in kere na yawo to zabo ma na yawo dole akwai ranar da za a gamu."

Tunda Zayd ya bude ido ya kasa magana binsa kawai yake da kallo.

Yana karasowa ya rike kunnen Zayd yana ja.
Cikin muryar ruɗu da tsoro Zayd ya ce, "Oga Nawar Don Allah ka yi hakuri ka fahimci ni wallahi ban da.... Ban da niyar ha'intarka...kuma da ka turo saƙo kan na je belinka na je, kin bani dama in shshishi....
Kafin ya karasa maganar Nawar ya buga masa wata sanda a baya.
Zayd ya saki kara.
Nawar ya ce, "ni zaka yiwa karya? Na ce ni zaka yiwa karya? Baka je gidan yari neman yin belina ba,kuma baka taba tunanin tuntubata ba, saboda a tunaninka bazan taba fitowa ba,ka ci gaba da shagali da dukiyata,ka ci gaba da safarar kayayyakina,kana rayuwa yadda kake so?"

Ya matse masa baki yana kara buga masa Sandar.
Wata karar ya kara yi yana rike bayansa.

Deejerh na tsaye Tana rufe hannunta da baki tana dariya ta ciki,don ita a yanzu babu abun da ke bata nishadi fiye da ganin Zayd cikin wani hali.

Dukansa suka ci gaba da yi, har saida ya yi flat a kasa.
"Aa aa ka yi hakuri zan fada gaskiya zan fada gaskiya ka ce su daina Dukana, zan fada,kuma zan baka duk sauran abubuwan ka da ke gurina zan baka,na yi alkawari a yafe mun."

Nawar ya dago kansa yana, "Eheen fada ina ji."

"Ban je ba,ban je ba da gaske wallahi duk sakon da ka turo babu wanda nayi,ban yi komai ba, kuma banyi zaton kinyi hakan zai sa aki sakinka ba,ka yi hakuri ka mun rai,kar ka kasheni."

Nawar ya kalli Deejerh yana wani irin Murmushii kafin ya maida kallonsa ga Zayd, "to ita kuma waccer cikar fa? Daga ina? Er hannuce? Na ganta akwai kaya fa."

Zayd ya ce, "Yarinyar Sister na ce amman wallahi Allah in kana sonta zan bar maka ita kada ka kasheni."

Kara kallon Deejerh Nawar ya yi sama da ƙasa,kallon da ya yi mata sai da taji canji a jikinta, walwalarta ta dauke.

Ya ce, "Da kuwa ka ceci kanka domin kasan ba karamin aikina bane yanzu in rabaka da ranka kamar kiyashi, kuma ka sani yanzu za a dawo harka kuma ya zame ma dole ka ci gaba da rayuwa karkashina."

Zayd ya ce , "Na yarda,na yarda indai bazaka kasheni ba."

Nawar ya sake shi yana fadin, "Amman fa bani ita zaka yi gabadaya dukanta ta zama tawa ni kadai kasan bana hadi da kowa in kuma hakan ya kasance wata babbar matsala ce daban a gareka."

Da sauri Zayd ya ce, "na amince amman dole sai mun shiryawa yadda hakan zai kasance."

Dariya mai sauti Nawar ya fara,yana kallon Deejerh yana shan giya tare da yin wata gyatsa mai wari da ƙara.

Tashi ya yi ya nufi Gun Deejerhn yana zuwa warinsa ya daki hancinta,ya kai hannunsa jikinta kenan tayi sauri matsawa ya dago a fusace yana kallonta ya jata da karfi......
[11/20, 1:03 PM] Xayyeesherthul-humaerath🥀: *°°°VIXEEN°°°*

*NOBLE WRITERS ASSOCIATION✍🏼*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.```
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
*https://www.facebook.com/106494781436168/*

_#5Stars/Zeeyter/Yel/Freeya/Vixen._

©️ *XAYYEESHERTHUL-HUMAERATH*

PAGE-15

Bakinsa yake kokarin hadawa da nata,har ya kai zai hada kenan sai kuma ya saketa yana murmushi.
"Ina ganin wannan inna fara taɓata zan iya ficewa a hayyacina yanzu ba shiri Don haka dole in takaita kwadayina ashiryawa lamarin." ya saketa ya kalli Zayd yana, "Yanzu ya? Kasan bana son fara abu da takura zuwa yaushe zaka kawo mun ita?"

Zayd ya ce, "Ko zuwa gobe ma amman bazai yiwu ta zauna Gabadaya ba a gobenma sai dai a shiryawa kan."

Nawar ya kara bin Deejerh da kallo, "Ok zamu daidaita duk da dai na ga alamun tana da ɗan taurin kai,kuma fa irinsu ma sun fi dadin sha'ani." Ya karasa maganar yana shafa tankwal din kansa da ya sha malu.

Zayd ya ce, "Yanzu zamu iya tafiya kenan?"

Nawar ya ce, "Eh zaku iya tafiya amman karka manta duk inda zaka shiga cikin garin nan,kasar nan ko ina ma, zan iya kamoka, a yanzu rayuwarka tamkar a tafin hannuna take, Kodayake ka fi kowa sanin halina, wannan dai Yar tunatarwa ce nake yi maka ko da gaba zaka yi tunanin bata rawan ka da tsalle."

Murya ciki-ciki Zayd ya ce, "Ba ma zanyi wannan katobarar ba In Sha Allah da dinma a kasi aka samu kuma yanzu baza a kara samu ba na yi maka alƙawari."

Dariya Nawar ya fara har yana durkusawa wacce shi kadai yasan ma'anar hakan.

Zayd kuwa yaja Deejerh ya tura ta cikin mota.
Jiki na rawa ya fara driving a guje ya bar wajen.
Ita kuwa har cikin ranta hamdala da jin dadi take ganin cewa zasu koma gida ba tare da an kaita wani gun da Allah ne kadai yasan me za a mata ba.
Sai da kuma babbar damuwarta da ta ji ana batun badata hakan ya kara jefata cikin duniyar tunani da wasu-wasi.

★Tun da sassafe Zayd ya tafi Gun Nawar, hakan yasa da ta tabbatar baya nan su momynta kuma suma barci hakan yasa ta lallaba ta fice gidan ta nufi HOPEFUL ENDEAVORS ORGANIZATION

Tana zuwa kuwa har an fara yiwa kowanni team Therapy.

Maestro Ramon na ganinta ya nuna mata inda nasu masu Ocd yake ta shiga.
Zama tayi gefe guda Ajeef ne da kan shi zaune yake yi masu jawabi.

Ya ce, "kafin mu yi nisa ina so da farko mu san shi kan shi ma'anar zamanmu anan wato Therapy , wasunku sun sani kila kuma wasu basu sani ba, atakaice Therapy shine the treatment of mental conditions by verbal communication and interaction.
"the therapy helps the patient to deal with difficult relationships" so dukanmu anan daya muke babu bambanci zamu yi wasa muyi dariya kuma duk mu fadi damuwarmu ga juna domin samu mafitar magancewa cikin sauki, dukkanin mu yan uwan juna ne,muna kaunar juna sannan zamu zamewa juna kariya ko ba haka?"

Hada baki suka yi duka wajen furta"eh."

Ajeef ya ce , "Alright yanzu lokacine da zamu bawa juna labarin abun da ke damunmu da har ya jawo mana wannan cutar."
Kafin Ajeef ya gama rufe baki har wata yarinya ta daga hannu Sopy.

Ta tashi tana fadin, "Komai ya farune dalilin Mahaifina,shine sila kuma shine ya jefani cikin wannan halin yana sex dani tun ina karama ban san komai ba har na fara girma kasancewar sun rabu da mahaifiyata, gashi ni ɗaya ce 'Ya agun shi, kuma kullum yana sani fita waje kan lallai sai na nemo mana abin da zamu ci,in ban samo ba ya mun duka,domin a buge yake bai da aiki sai shaye-shaye da kwanciya dani, wanda a karshe har ya kai ga ya mun ciki,na haifi Ɗa wanda na gagara gane cewa shi Ɗana ne ko kanina ne." Kuka ne ya tirniketa ta gagara karasa maganar.
Da sauri sauran matan suka rungumeta suna rarrashinta.
Ajeef ya ce, "ki yi hakuri kinji, komai zai wuce kuma hakan ba shi ke nufin rayuwar ki bata da amfani ba,sannan baki san wacce baiwa wannan yarinyar take dauke da shi ba."

Bayan sun gama Rarrashinta ta samu nutsuwa.
Amaan ma ya tashi yana bada na shi labarin.

"Nikam ban da iyaye,agun Uncle dina na taso, amman babu wahalar duniyar nan da ban sani ba,domin kullum cikin bauta nake da duka, sannan yana kaini gun maza jinsina suna amfani dani ana bashi kudi,rayuwata gabadaya tunda na taso ban san yancin kaina ba, sai dai inga wasu suna rayuwar jin dadi a waje zuwana nan gurin ne kawai na fahimci cewa ashe nima mutum ne kamar kowa kuma zan iya rayuwar farinciki." Ya karasa maganar yana saurin share hawayen da suka zubo masa.

Kowa na kokarin bada labarinsa amman ban da Deejerh kawai binsu da kallo take kunnenta na saurara.

Ajeef ya kalleta ya ce, "Ke baza kiyi magana ba?"
Ta kalleshi kawai ta kauda kai.
Dafa mata kafada ya yi yana murmushi ya ce, "Komai zai wuce kinji."


Bayan sun fito daga Team Therapy dinne suka wuce babban filin.

Ajeef ya gabatar masu da abokinsa Black Belt kwararre a bangaren Mixed martial arts (MMA).
Yadda zasu iya bawa kansu kariya aduk lokacin da wani ya kawo masu harin da zai iya cutar da su, ne yana da kwarewa sosai a bangaren MMA hakan yasa suka gayyace shi na musamman domin yi masu training.

Tana zuwa Ajeef ya bata kayan training din kamar yadda kowa yasa ita ma tasa nata ta shiga sahu.

Ana yi suna gumi suna zufa amman gabadayansu wani dadi da nishadi ne ya mamaye masu rai tamkar kar adaina.

Bayan sun yi Arif ya dakatar da su kan cewa sai next week zasu ci gaba amman kafin nan zai kara yi masu jawabi da mahimmanci samun horo da goge a ɓangare MMA.

Ya ce, "Ba wai kawai don nishadi ko gasa ba, ba wai kawai don samun galaba akan wani ko cutar da shi ba, aa wannan din wata babbar damace kuma babban darasi ne da zai iya taimakon kowa, ya yin da ake kokarin kawo maka hari, illataka,ko cutarwa ta wani bangare kai tsaye ka san hanyar da zaka bi domin kwatar kanka, atakaice dai kenan zaku koyi hakan ne domin kariya ga rayuwarku gabadaya, duk wani mai tambaya zai iya yi."

Abiel ne ya daga hannu da sauri.
Arif ya ce, "Oya ina saurarenka."

Abiel ya ce , "Can a female Martial artist beat a man?"

Arif ya ce , "tambaya mai kyau, Why Not? Whether you're male or female you don't need an extraordinary amount of strength or power to strike and defeat your opponent, instead, you need proper technique, agility, and speed. A female fighter who dominates proper technique remains calm and in control of herself, can overpower a larger and stronger male, Don haka babu wani bambamci mace ko namiji kowa zai iya yin kokarin bin hanyar kare kai ga duk wanda yaso illata shi."

Daeej ya daga hannu shi ma.
Bayan an bashi dama ya ce, "Sir Will MMA help in a street fight?

Arif ya gyara zama kafin ya ce, "Sosai ma, Striking Techniques: MMA fighters are trained in various striking techniques, including punches, kicks, elbows, and knees. These skills can be effective in a street fight to create distance, defend against an attacker, or escape a dangerous situation"

Ana gamawa Deejerh tai gida da sauri kasancewar ranar basu wani dade ba, har ta shige dakinta ba wanda ya ganta kuma bata tunanin ma an nemata.
Tana shiga ta sake yin wanka.
Ta zauna kenan zata huta training da aka masu ya fara dawo mata arai.
Tashi tayi ta dunga bi tana kara maimaitawa.

Ji tayi kawai an hankado kofa tana durkushe.
Dagowan da zata yi ta ga Zayd ne tsaye yana kallonta.

"Wannan kuma wani irin iskancine kike?"
Kallon shi tayi ta kawar da kai gefe.
Ya yi tsaki har zai fita ya koma ya ce, "kiyi wanka ki tsaftace jikin ki nan zuwa anjima da dare zamu fita." Yana fada ya fita.
Yana fita,Ci gaba da MMA dinta tayi ta ma manta da wani batunsa.

Ta riga ta ci ta ƙoshi gun training dinsu hakan yasa ko tunanin fita palourn ma bata yi ba.
Bayan ta gama zuciyarta ta raya mata kan cewa ta dauki Qur'ani ta karanta.
Haka kuwa ya kasance da ta karanta ta kara jin wani sanyi aranta hankalinta ya kwanta kuma ta samu nutsuwa har barci ya dauketa ba tare da ta ankare ba.

Har wajen karfe hudu tana barci bata farka ba, shiganshi dakin ya ganta tana barci cikin nutsuwa wani takaici ne ya turnukesa a zuciya, cikin fushi ya ja kafafunta daga kan gadon ya dire ƙasa.

Ta farka arazane tana waige-waige.
"Sannu ko! Wato har ni zance ki shirya ki jirani ina zuwa zamu fita ki kwanta kina wani barcin banza ko? Kina son wasa dani cikin kwanakin nan fa."
Ya wurga mata wasu kaya yana, gashi nan ki tashi ki je ki wanke fuska kisa kuma ki gyara jikinki minti Uku na baki.

Deejerh ta tashi ta shiga toilet tana zuwa alwala ta fara, bayan ta idar ta fito yana tsaye ta dauki hijabi zata shinfida sallaya tai sallah kenan ya daka mata tsawa.

"Ke! Me zakiyi wai? Me kike nufi?"

Deejerh ta ce, "Sallah zanyi sai insa kayan mu tafi."

Bugawa zuciyarsa ta fara tsabar takaici ya fisge sallayar, hijabinma ya janye mata saida ya kusan sheƙeta kafin ya kara wurga mata kayan da yazo mata dasu.
"In baki sa kayan nan yanzu mun fita kafin iyayenki su dawo daga anguwar da suka

Please Login or Register in order to submit comment