Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kwana a cen ba,shine take fushi."

Officern ya kalli Deejerh ya ce, "Madam, dago ki kalleni, ki fadamun gaskiya don ban gama yarda da mutumin nan ba, sato ya yi ya miki dole ko kuwa da gaske mijinkine?"

Deejerh ta kalli Zayd ya yi gulu-gulu da idanu na alamar tsoro officer ya ce, "ki bar kallon shi fa,ki fada mun gaskiya bai isa ya miki komai ba, mijin kine?"

Deejerh ta ce, "Aa......
Gaban Zayd ne ya fara dukan tara-tara zufa na kara yanko masa, ya rasa ina ma zai sa kansa.

"Ba satoni ya yi ba." Ta fada kanta na kasa.

Ajiyar zuciyan tsira ya yi yana dogon numfashi.
Officer ya kalle ta, "Kenan dai da gaske mijin kine?"

Ta girgiza kai ba tare da ta dago ba.
Ya kara fadin, "ya bata miki ran kenan kike fushi?"
Ta kara girgiza kan.

Officern ya yi murmushi kafin ya ce, "Oyaaa to maza ka durkusa ka bata hakuri,indai har bata yi dariya ta sake fuska ba sai ni nayi Punishing dinka da kaina, taya zaka batawa kyakkyawar yarinya kamar wannan rai? Kasan irinmu da muke neman irinsu bamu samu ba kuwa? Oya durkusa gaban ta ka bata hakuri."

Zayd ya durkusa yana binta da kallo, tayi saurin kawar da kai.
Hannunta ya rike ya ce, "I'm So Sorry Little Princess, ban yi hakan don ranki ya baci ba,ba zan kara ba kinji ko."

Ko dagowa ba ta yi,bare ta kalleshi.

"Wannan lamarin naka fa bai faranta ran Madam ba,oya ka goyeta yanzu ku zaga filin nan har sai tayi dariya,kuma kana yi kana gudu."

Ba yadda Zayd ya iya haka ya durkusa Deejerh ta hau bayansa, yana gudu da ita suna zaga fili tun bai gaji ba har ya gaji taki murmushi bare dariya,ba abun ya mata masifa ba,ya kara jawa kansa wata masifar da bai shirya karbanta ba.

Dakyar yake tafiya ya ma gagara gudun, Suka ce ya tsaya ta sauka.
Officer ya kalli Deejerh ya ce, "Madam ina ga dai kinfi so sai ransa ya bacine kamar yadda naki ya baci, Don haka yanzu ki tsaya kiyi kallo."

Suka sa Zayd ya cire wandonsa daga shi sai gajeren wando, sannan suka sa shi ya kwanta a kasa.
Wata zabgegiyar bulala irin tasu ta yan sanda mai kama da sanda.

Ana buga masa ɗaya a duwawu sai da wandon ya tsage.
Shi ko da ya yi wata irin kara baisan lokacin da ya tashi ya zura aguje yana ihu, "Wayyo Allahna Duwawuna,ya fita shikenan ya fita a jikina ,na shiga ukuna wayyo Allahna."

Da Deejerh ta fara wata irin dariya mai sauti har tana rike ciki.
Nan Officer ma ya kyalkyale da dariya.
"Yawwa haka takeso ku kamo shi a kara masa yadda zata yi dariya son ranta."

Rikeshi suka kara yi yana kokarin kwacewa tuni suka kwantar da shi, suka danne shi, aka kara buga masa gabadaya wandon ya dagargaje.
Fatar duwawun ma ban da jini babu abun da ke fita.

"Shikenan sun gama cire mun duwawun ya fita a jikina,wayyo,wayyo duwawuna, shikenan,duwawuna, ya fita,ya fita,,,ku barni Don Allah ku sake ni ku barni na tuba."

Deejerh tsabar dariya har ma ta manta da inda take.
Officer ya ce, "ku barshi haka,ko ba komai an sata nishadi kuma gaba ba zai kara tunanin batawa kyakkyawa irin wannan rai ba, maza tashi ka shiga mota ku tafi kuma ko kallon banza ka kara yi mata a daren nan zaka sha mamaki."

Ko wandonsa bai dauka ba haka ya shige motar,ya gagara zama ma sai ta gefe ya rakaba cinyar Ko kallon Deejerh baiyi ba ya ja motar da gudu suka bar wajen, ban da hawayen azaba babu abun da yake,don har lokacin ji yake tamkar an cire masa duwawun daga jikinsa gabadaya.

Suna isa gida bai iya tsayawa ya yi parking dinma da kyau ba kawai wancakalar da motar ya yi ya fice, Deejerh ta kallesa tana dariya, da ya bita da wani kallo tuni ta hadiye dariyar tana shigewa ciki.

Washegari
Weekend
Babu School kowa ya fito breakfast amman ban da Zayd.

Cike da mamaki Momyn Deejerh take fadin, "Deejerh ina Uncle dinki ne? Yau fa ban ji motsinsa a gidan nan ba kwatakwata lafiya kuwa?"

Deejerh ta ce, "I don't know Mom, kila ko dan yau weekend ne yana hutawa."

Dadynta ya ce, "aiko Weekend ne in lokacin breakfast ya yi dole yana fitowa adai je adubashi aga ko lafiya."

Momynta ce ta tashi ta nufi dakin na shi,tana tura kofa ta sake baki tana binsa da kallo.
Kwance yake ya yi gohu yana ta sambatu ga duwawu duk ciwo.

Karasawa ta yi gabansa tana , "Subhannallah me ya faru? Me ya sameka?"

Zayd ya ce, "Accident na yi jiya da dare dana fita."
Mika masa towel tayi ya daura sannan ta ce, "Shine bazaka je asibiti ko ka fada a rakaka ba? Tashi muje palour ka ci abinci sai in raka ka hospital."

Haka ya daura ta rike masa hannu suka fita.
Deejerh na kallonsa ta sa hannu tana toshe bakinta don dariya.
Shi kuwa da wani kallon mugunta yake binta yana girgiza kai.

Momynta ta fito tana fadin , "Ashe Accident ya yi jiya haba ni nayi mamaki shirun Zayd."

Dadyn Deejerh ya tashi yana rikosa ya ce , "Subhannallah sannu zayd."

Sai a kasa a ka sa masa filo ya zauna a karkace aka ba shi abinci da kyar ya iya ci kafin suka rakashi a hospital.

Da Deejerh na murna yau tana da yanci babu mai takura mata amman kuma tunani ya hanata samun nutsuwa bare tayi walwala.

Gabadaya ta gagara samun sukuni.
Kitchen ta je ta dauki Apple zata ci, ta dau wuka zata yanka kenan sai kuma zuciyarta ke raya mata ai zata cutar da Apple din inta yanka.
Haka ta maida fridge ta fice daga kitchen din.

Ta shiga toilet ta wanke hannunta,ta kara komawa ta wanke sai da ta wanke sau uku kafin ta zauna.
Tana zama ta tashi kamar an tsikareta.
Ta kara komawa kuma ta zauna tana irga hannunta,ta irga ta kara irgawa haka ta dunga yi duk da cikin ranta tana kokarin dakatar da kanta amman sam ta gagara.

Sai da suka je asibiti aka yi treating dinsa tukun ya samu dan sauki radadin ya ragu masa suka dawo gida.

★★★yana jin ya fara dawowa daidai babbar damuwarsa kawai ya samu hanyar zai hukunta Deejerh ita ma ta ji a jikinta kamar yadda sanadinta tasa aka jibgarsa a mazauninsa.

Hakan yasa sai da ya bari kowa ya yi barci cikin dare ya shiga dakinta,tana cikin barci sai jin saukar ruwan sanyi tayi ta ko ina a jikinta.
A firgice ta tashi duk ta rude ga ruwan ya shige mata kunne,baki,da hanci.
Numfashinta na shirin daukewa dakyar take iya yi sama sama.
Haka ya damke gashin kanta yana ci gaba da zuba mata ruwan a fuska.
"Wato ke kinsan salon mugunta ko? Har ni zakina wa dariya kuma kisa adakeni a mun illa saboda ke matsiyaciyar yarinya ce ko? Sai na kashe ki, na fada miki ai in baki bini a sannu ba sai na kashe ki."

Ta gagara magana domin koda taso yi ma baza ma ta iya ba don ruwan duk ya gama shige mata a birkice take.
Sai da ya tabbatar ya zuba mata yadda zai iya mata illa kafin ya saketa.
Ya fita yaje ya ɗibo gaushin wuta a irin wutar da suke hadawa a cikin gida.

Ya ajiye adakin cikin tsawa yana fadin, "ni bazan miki yadda zakiji sauki da wuri ba sai na yi maganinki yadda zaki ji a jikin ki, abun da yasa ma bazan ce ki zauna akai ba don kawai kada kije ki janyo mun matsala a business dina ki kore mun costumers ne, amman yanzu ma fa baki tsira ba." Ya fada yana kara janyo gashin kanta.
Ya sa cikin wutar,gashi tana ci sosai tururin har fatar kanta ya fara narkarwa ga gashin duk ya harharde ya ƙone.

Kuma yasa tsimma ya daure mata baki yadda bazata samu damar yin kuka ko ihu ba.
Ban da dariya babu abun da take yi.

Sai da ya tabbatar ta gama galabaita sannan ya hankadata gefe ya fice adakin.

Dakyar ta iya bude bakinta da ya daure tana maida numfashi.
Azaba ta ko ina ta rasa ma da wacce zata fara ji.
Yadda ta ga rana haka ta ga daren domin ko runtsawa bata iya yi ba a wannan daren.
Tamkar mahaukaciya haka ta dunga sambatu adakin ita kaɗai.
Ta kasa samun nutsuwa.
Sai bayan sallar asuba ta samu barci ya dauke ta, tana cikin barcin kuwa sai kara jinta tayi tamkar a rafi, ta farka a razane.
"Wato ke har kin samu damar barci ko? To ki tashi kije ki saida mun kayana School,ban damuwa in kinje kiyi karatu ba ko akasinsa ke ko gawarkice ni zan iya saidawa indai zan samu kudi don haka tun kafin in kara gana miki wata azabar ki tashi ki wuce ki tafi ki sai da mun kaya." Ya karasa maganar yana wurga mata jakar ya fice a dakin.

Haka ta tashi ta yi wanka ta shirya,ko abinci bata samu damar ci ba ta yi School din.
Tana tafiya tana sambatu har ta isa.

Maimaki ne ya kama su Maira ganin yadda tun daga nesa take sambatu har ta shiga cikin School din.
Kuma sambatun ba kowa zai gane me take nufi ba.
Maira ta ce......
[11/20, 1:03 PM] Xayyeesherthul-humaerath🥀: *°°°VIXEEN°°°*

*NOBLE WRITERS ASSOCIATION✍🏼*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.```
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
*https://www.facebook.com/106494781436168/*

_#5Stars/Zeeyter/Yel/Freeya/Vixen._

©️ *XAYYEESHERTHUL-HUMAERATH*

PAGE-10

"Lafiyan ki kuwa Deejerh? Yanzu ku san kullum sai kina sambatu ke kadai." Ta fada tana rike mata hannu.

Noha ta ce, "sai kace wacce sanyi ya taba ba, gashi a miki magana ki tsaya kallon mutane."

Deejerh ta ce, "ni babu abun da ya sameni."
Maira ta jata su ka ci gaba da tafiya tana, "koma mene ne dai muje za a fara Class yanzu kuma su Daeej na cen."

Suna shiga Class Maira na sake mata hannu ta yi toilet ta wanke hannu.
Ta dawo har zata zauna kafin ta zauna ta kara komawa ta wanke.
Ta kara dawowa ta zauna Kamar an tsikareta ta tashi ta koma ta kara wanke hannun nata.

Ta kara tashi zata tafi kenan Noha ta riƙeta , "Wai mene ne kiketa faman wanke hannu ne? Ko kyamar mu kika fara ji kuma?"

Deejerh ta ce, "aa kawai ban so wata cuta ta taba mun hannu ne ya kamani ya cutar dani,Noha Please ki sake ni inje in wanke hannuna nikam."

Ta fada ta na fisge hannunta tayi toilet.
Daeej da Abiel ne suka taso kusa da su Abiel ya ce, "ita kuma wannan ciwon wanke hannune ya kamata?" Ya fada daidai lokacin da Deejerh ta zauna a sit dinta.

Maira ta ce, "ni fa ina da tantama a yanayin Deejerh tana wasu abubuwa shigen wanda Cousin dina Miema take yi, amman ita Ocd ne ya kamata wato , Obsessive Compulsive Disorder, tana yawan sambatu da yawaita wanke hannu ita ko fruit ne ko wani abu aka bata ta yanka sai ta ce baza ta yanka ba, haka kuma tana zaune kawai sai tayi kitchen ta fara dube-dube wai ko ta bar gas a kunne, abubuwa dai haka,amman kuma ita sanadin tsoro ne ya janyo mata kafin su dawo nan Mexico suna America aka samu dan hatsaniya ta bangarensu aka yi fada wanda ya kai ga har iyayenta sun rasa ransu sai ita kadai ta tsira aka daukota, daga nan tsoro da firgici tare da maraici da ya haifar mata yawan tunani sai ya sa mata hakan Dad dina ya kaita hospital ake sanar masa abun da ke damunta kenan, to amman kuma na Deejerh ba na ce hakan bane kai tsaye nidai kawai naga wasu dabi'un nasu duk kusan ɗaya ne."

Noha ta dafa Maira na fadin, "To me zaisa ba za muyi Googling asalin cutar ba da ma symptoms dinsu daga nan zamu fahimci ainihin inma ita ma shine yake damunta."

Abiel ya ce, "Yess Yar dagawas kwalwalarki na ja, ayi Googling din kawai."
Daeej ne ya ciro wayarsa ya shiga Google ya fara rubuta Meaning of OCD.

Ya ce , "Yawwa ku saurara bara in karanta maku kuji, Obsessive-compulsive disorder (OCD) is a long-lasting disorder in which a person experiences uncontrollable and recurring thoughts (obsessions), engages in repetitive behaviors (compulsions), or both. People with OCD have time-consuming symptoms that can cause significant distress or interfere with daily life." (OCD wata dadaddiyar Cuta ce da kan jawowa mutum rashin nutsuwa da kamuwa tare da wani ra'ayi mara tushe, zai dinga yawan maimaita wasu halaye ko tilasta kansa akan wasu abubuwa ko duka biyun. Mutanen da suke da wannan cuta ta OCD suna da yanayi na nawa (nuku-nuku), wanda shine yake basu matukar wuya wajen gudanar da rayuwar su ta yau da kullum)

Maira ta ce, "Tabbas hakane, Yanzu duba mana symptoms dinsa mu ga."
Ta fada tana kallon Deejerh.

Ya rubutawa kuwa suka fito a jera Daeej ya ce, "gasu nan ,
cleaning and hand washing.
checking – such as checking doors are locked or that the gas is off.
counting.
ordering and arranging.
hoarding.
asking for reassurance.
repeating words in their head.
thinking "neutralising" thoughts to counter the obsessive thoughts.
(Tsaftacewa da kuma wanke hannaye.
Bincikawa - kamar tabbatar da rufe kofa da kuma kashe gas.
Lissafawa.
Tsarawa da shiryawa.
Hording (kamar yanayin ajiye tarkace marasa amfani)
Yawan Tambaya domin tabbatarwa.
Yawaita maganganu acikin kansu(maganar zuci).
Tunani "saisaitawa" yawaita tunanin da ke jawo kamuwa da wani ra ayi)

Amman wannan abun fa ina karantawa sai nake gani kamar halayen Deejerh suke karantowa.
Deejerh na jinsu amman bata ce komai ba ta kau da kai kawai.

Abiel ya ce, "Amman kun manta baku duba mana causes din ba,ina ga akwai bukatar saninsu suma ai kafin mu kai ga mataki na ga ba."

Noha ta ce, "Kwarai kuwa a duba mana."

Daeej ya duba causes din yana ci gaba da karanto masu.
"What causes OCD? Experts aren't sure of the exact cause of OCD. Genetics, brain abnormalities, and the environment are thought to play a role.
(Me yake haifar da cutar OCD? Kwararru har yanzu basu tabbatar da abin da ke haifar da wannan cuta ba.
Sai dai kamar yanayin halittar mutum, rashin lafiyar kwakwalwa da kuma yanayin wajen da mutum ke rayuwa yana taka gagarumar gudunmawar wajen faruwar cutar)
to kunji dai, I think bamu da abun da zamu iya a nan abu na farko kawai shine akwai bukukuwa mu sanar da maestro Ramon ba zai rasa solution kan hakan ba amman dai abun akwai daure kai."

Noha ta ce, "Yes Nice idea."
Tashi suka yi suka nufi office din Maestro Ramon ita kuwa Deejerh na zauna ko motsawa bata yi ba,bare alamar binsu.

Excuse suka taking kafin suka shiga office din.
Maestro Ramon ya ce, "Espero que todo vaya bien (ina fatan komai na tafiya daidai dai)." Ya fada yana kallonsu.

Daeej ya ce, "Ehto kusan hakan Amman muna bukatar taimakon ka Sir, domin babu wani da zamu iya kai wa matsalarmu bayan kai cikin Makarantar nan."
Ya girgiza kai sannan ya ce, "Ba matsala ina saurarenku."

Maira ta ce, "Daman akan Deejerh ne,mun yi observing wasu dabi'u da halayarta tare da yanayin da take ciki a yanzu wanda hasashenmu da kuma binciken mu ya lakantu kan cewa akwai yiwuwar tana dauke da OCD ba mu san me za mu yi domin nema mafita ba tunda ba mu da masaniyar mene ne ainihin abun da ya janyo mata cutar in hakan ya tabbata and Bama jin dadin kasancewar ta cikin yanayi irin hakan."

Abiel ya ce, "mu bamu ma san ta ina zamu fara ba,amman dai gaskiya Deejerh na bukatar taimako domin yanzu kusan rayuwarta gabadaya bata tafiya daidai."

Maestro Ramon ya numfasa kafin ya gyara zama ya ce, "No wonder! Sai da kuka fada nima na fahimci hakan lallai Deejerh na dauke da wannan cutar babu tantama domin dabi'unta kaf a yanzu irin na masu ɗauke da cutar ne, amman ku sani fa nima ba zan iya komai a yanzu ba, har sai naje gidan su na bincika shin koda akwai abun da ke damunta? Dole dai asan dalilin faruwar hakan a tattare da ita kafin komai, Don haka yau zan bita gida In Sha Allah inji duk abun da ke faruwa kafin sai muyi tunanin daukan mataki na gaba, sannan kuma na ji dadin hadin kanku da nuna damuwa da matsalar junanku wannan shine asalin aminta da zaman tare duk da cewa dai bakwa jin magana."

Dariya suka yi duka Noha ta ce, "mun daina rashin jin ai."

"To Allah yasa, hakan mukeso ai daman."
Maestro Ramon ya fada.

Cikin wasa da dariya suka bar office din suka koma Class.

Deejerh kuwa suna fita ta dauki drawing book dinta ta fara Designing kaya kamar yadda ta saba a duk lokacin da ta dan samu nutsuwa a class abun da take yi kenan.
Aranta ko ya ta yi Designing kaya ta kan ji dadi da farinciki mara dalili sun mamayeta kasancewar babu abun da take jin dadin yi fiye da hakan.

Riga da wando ta zana sun zanu sosai kuma sun fita sunyi kyau,ta daga tana kallo tana murmushi ji tayi kawai an fisge ana yagawa.


Ahlam ce tana yagawa tana tsaki ta ce, "Munafuka wai ke dole kin dage sai kin zama ta musamman cikin makarantar nan? To wallahi baki isa ba,inko kinga faruwar hakan to saidai in har numfashi ya bar jikina, banza,wawiya kawai."

Hawaye ne kawai ya fara kwarara daga idanun Deejerh ta durkusa kasa ta kwaso takardar tana kokarin haɗawa.
Tana kwashewa kwakwalwarta na kara dawo mata da lokacin da Ahlam take yagawa.

Kara fisge takardun da ta kwashe tayi ta zubar a kasa tana takawa.
Deejerh ta durkusa tana kautar da kafarta zata dauka sai jin saukar mari tayi a fuskarta.
Daidai lokacin da Su Abiel suka dawo cikin Class din abun da suka fara cin karo da shi kenan.

Cikin zafin rai Daeej ya karasa ya kai wa Ahlam din ita ma Mari.
Abiel ma na zuwa ya kai mata wani marin.
Noha ta rungume Deejerh tana rarrashinta.
Su kuwa su uku, Abiel, Daeej da Maira suka hadu kan Ahlam suka dinga jibga har sai da suka fasa mata baki da goshi.
Kin saketa suka yi har saida aka turo displine Master na School ya kwaceta kuma aka tattara su duka zuwa Displine office.

Ko da suka je da kyar Deejerh ta iya fadan abun da ya faruwa domin babu abun da kwakwalwarta ke kara maimaita mata illa yadda Ahlam ta yaga mata drawing dinta.

Daeej da Abiel ne suka iya bada cikakkiyar amsa kan cewa Kusan kullum Daman Ahlam na yiwa Deejerh kallon banza kuma ita Deejerh bata shiga harkar kowa bare ya kai ga ta yi fada.

Ita kuwa Ahlam ta dage kan ita babu abun da ta yiwa Deejerh hasali ma Ita ce ta mareta zata rama ne kawai su Daeej suka kama dukanta kasancewar babu kowa a class din sai su kadai.

Ganin cewa kowa da abun da yake fada daban aka ce za a yanke masu hukunci dukansu kowa a hukunta shi.

Dukan su aka sasu tuge ciyayi marasa kyau a garden din School din, suka boye Deejerh bata yi ba su hudun suka yi, suna yi suna kara shirya yadda zasu yiwa Ahlam wani dukan in an tashi.

Aikuwa ana tashi suka fara fita ko jiran Deejerh basu yi ba.

Binta suka yi,suka kara kamata suka mata wani dukan da sai da goshinta ya yi ƙulu bakinta ma ya kumbura suna dariyar mugunta kafin suka barta tana kuka.

Tare da kashedin inta kara shiga harkar Deejerh ko ta kara yi mata wani kallon banza sai sun babbalata.
★★
Deejerh ta fito zata tafi kenan maestro Ramon ya ce ta tsaya yana so zai je gidansu.

Yana fadan hakan gabanta ya yi mummunan faduwa amman ba yadda ta iya haka ta shiga motarsa ta bishi suka tafi tare.

Suna zuwa kuwa sunci sa'a Momynta da Dadynta na gida har ma da Zayd.

Da fara'a duka suka karbeshi kasancewar duk sun san shi.
Deejerh ta shige dakinta.
Shi kuma ya fara yi masu bayanin dalilin zuwansa gidan.

"Ku yi hakuri kila nazo babu sanarwa ganin mahimmancin lamarin yasa na ga ba zan iya hakuri ba, wata yar tambaya ce na san dole ku kadai ke dai amsarta, shin shekarun nan na yanzu da Deejerh ke kara girma bakwa ganin wasu canji tattare da ita kuwa?"

Karaf kafin kowa ya yi magana Zayd ya ce, "Canji kamar ya kuma? Babu wata matsala lafiyarta kalau ai."

Maestro Ramon ya ce, "Nop ba wai ina nufin bata da lafiya bane, amman dai akwai wani canji a tattare da ita da ya kamata ace kun fuskanta kamar yadda muka fahimta, kuma babu wani abu dake damunta haka? Babu wata cutarwa da take fuskanta ko danne hakki?"

Nan ma karaf Zayd ya ce, "wai me kake nufine na maganar cutarwa,damuwa, danne hakki, wai wani abun taje ta fada ma ne?"

Murmushi ya yi ya ce, "Aa atakaice ma ita batasan dalilin zuwana gidan nan ba amman dai....

"Amman dai me? Amman dai me? Dukaninmu nan fa danginta ne kuma munfi kowa sonta a duniyar nan so ba yadda za ayi mu bar wani abu yana cutar da ita, girma ne kawai ya fara kamata da canjin yanayi." Zayd ya faɗa.

Sai a lokacin Dadyn Deejerh ya yi magana, "wannan ai ba wani abun tashin hankali bane, hakan na nufin suna lura da dalibansu da kyau kenan, a yanzu dai gaskiya ba mu fahimci wani takamaiman canji daga gareta ba,amman ta yiwu rashin maida hankalinmu kanta ne da rashin samun lokaci tare Don haka In Sha Allah daga yanzu zamu maida hankali wajen lura da yanayinta duk abun da muka ga ni zamu sanar da ku amman dai ina fatan lafiya ba wani abu ta aikata ba daidai ba ko?"

Maestro Ramon ya ce, "aa gaskiya ba komai kawai dai akwai bukatar lura da yanayinta ne sosai a yanzu."

"In sha Allah za a lura kuma za a kiyaye da duk wani abu da ya shafeta." Momyn Deejerh ta fada.

Gabadaya yanayin Zayd ya sauya ransa ya baci ya shiru ya ma rasa abun cewa kawai sai bin Maestro Ramon da wani mummunan kallo yake.

Sallama suka yi suna masa godiya tare da rakashi ya fita.
Zayd ya bisa kan cewa zai rakashi gun motarsa.
Ya bude mota kenan zai shige ya rike hannunsa.
Cike da mamaki Maestro Ramon ya kallesa suna kallon juna ido cikin ido.
Ya ce.....
[11/20, 1:03 PM] Xayyeesherthul-humaerath🥀: *°°°VIXEEN°°°*

*NOBLE WRITERS ASSOCIATION✍🏼*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.```
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
*https://www.facebook.com/106494781436168/*

_#5Stars/Zeeyter/Yel/Freeya/Vixen._

©️ *XAYYEESHERTHUL-HUMAERATH*

PAGE-11

"Shawara zan baka, wacce in kabi zata iya zamtoma silar tsira,in kuwa ka kuskure mata tamkar kana wasa da rayuwar ka ne, wannan ne na farko kuma ina fatan ya kasance na karshe, daga yau, rana mai kama da ta yau,kuma irin yau, ka da ka kuskure ka kara tunanin zuwa wannan gidan,bare kuma bincikar wani abu da ya shafemu, mu zaune cikin zaman lafiya da kaunar juna ka rike wannan kuma kasa aranka, sabanin faruwar hakan kuwa hmmmm."

fisge hannu Maestro Ramon ya yi daga hannun Zayd.
Ya bisa da kallo sama da kasa kafin ya ce, "ka sani cewa zan iya yin komai Don tabbatar da lafiya da samun nutsuwar dalibaina, And kuma in kana ji da wani abu na taurin kaine ka ajesa a gefe domin nasan duk abun da ka yi baka kamo kafata ba."

Nuna masa yatsa ya yi,ya shige motar cikin fushi yaja ta ya bar gidan.

Tsawa Zayd ya yi yana mamakin kwarin gwiwa irinta Roman da lokaci guda ya iya dakatar da shi.
A zuciyarsa yake rayawa, "tabbas in ban nemo mafitar kawar da wannan mutumin ba tsaf zai iya bani matsala."
Ya fada yana shigewa ciki.

Ransa ya riga ya gama ɓaci zuciyarsa har zafi take hakan yasa ya tafi dakinsa kawai ya kulle kofa.
Sai Sallah magrib ya fito tunda ya fita Masallaci kuwa bai dawo gidan ba sai can karfe 11 na dare lokacin duk sunyi barci.

Kofar Deejerh ya taba ya ji a kulle.
Ya kula yana wani tsakin takaici sannan ya fita.
Bayan gidan ya zagaye ya haye dakin ta windo.
Tana jin shigarsa ta firgita domin ba barci take ba daman Designing din kaya take ta yi a jikin bangon dakin kamar yadda ta saba don ta ko ina adakin ban da fashion design babu abun da mutum zai gani.

Gabanta ya yi mummunan faduwa tana rike jikinta tare da matsawa jikin bango.

Dankalin ta yasa mu ya daure mata baki da shi.

Sai jin belt tayi a jikinta.
Take ta shiɗe azaba tasa tuni ta fice a hayyacinta bata ma san fitsarin wahala na fita daga jikinta ba.

Domin irin belt dinnan masu kauri ne.
Bude kofar dakin ya yi,yana janta har saidai ya fiddata waje ya bude wani karamin daki wanda yake aje karnukansa ya turata ciki.
Ita kuma Deejerh daman babu abun da take tsoro sama da karnuka a rayuwarta yana turata kuwa ta kara birkicewa tana shidewa.
Tubeta ya yi zigidir su kuwa karnukan suna ganin haka suka yi kanta wajen

Please Login or Register in order to submit comment