Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ARABIC /ISLAMIC STUDENTS
πŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“š

πŸ‘¨πŸ»β€πŸ’»πŸ‘©πŸ»β€πŸ’»
*ZAMANI WRITERS ASSOCIOTION*

πŸ“
​​WΙ› Ι‘Κ€Ι› Ι¦Ι›Κ€Ι› tΡ³ Ι›Ι—ucΙ‘tΙ›, MΡ³tiΡ΅Ι‘tΙ› Ι‘Ι³Ι— Ι›Ι³tΙ›Κ€tΙ‘iΙ³ Ρ³uΚ€ ʀɛɑɗɛʀร​​



0⃣2⃣2⃣


Tunani ne ya cika zuciyar Sweety, shin wai dama akwai sanayya tsakanin Nahna da broth d'inta, amma kuma ai Nahna bata tab'a nuna mata tasan shi ba,koda ta ganshi a photo ai bata nuna sanayya tsakaninsu ba,amma dai Gobe Duk yanda ake ciki zata nemi Nahna taji komai, tana wannan tunanin har bacci ya d'auketa.


A gidansu Nahna kuwa koda yaushe mik'a lamarinta ga Allah take, bata dogon bacci kullum tashi take cikin dare tana kai kukanta gun me share mata hawaye, don haka koda yaushe take jin zuciyarta na mata sanyi,kamar ba wani abu gabanta, Sam take jin tsanar UK da tsanar auransa na fita cikin ranta,Duk da baza tace ta fara son abin aranta ba amma baza tace tana k'insa kamar farko ba.



Da yamma lik'is Sweety tazo gidansu Nahna bayan sun gaisa da Aunty suka shige d'aki,cikin fara'a sa tsokana ta dubi Nahna " Aunty nah zance ko amarya zance?".

Mirmishi Nahna tayi tace "ko d'aya karki fad'a,in bazaki kice Nahna ba kice Khadijah".

" a'a ni yanzu wannan sunan yamin nauyi a baki ai sai mutane suga rashin kyautawa ta ina fad'ar sunan matar yayana".

Dukanta tai a baya tana fad'in "ai kuwa Duk abinda zakice in dai ba Nahna ba ko Khadijah bazan amsa ba ".

Dariya sweety tai kana ta gyara zama kan gadon tana fad'in " kai gaskiya Nahna kina da zurfin ciki na bala'i wlh,yanzu Duk tsawon zamanmu dake ace biki tab'a nuna min kin san Broth ba koda wasa,ashe akwai sanayya tsakaninku,to shi ya fad'amin kun Dan juna a college ba kad'anba don zumunc kukai sosai ".

Zaro ido Nahna tayi ba tare data tuna ba ta fara fad'in " kai sweety UK d'in ne yace miki munyi zumunci?to wlh tsawon sani na dashi a college ba wani Abu na arzik'i daya tab'a had'a mu in banda tsantsar tsanar juna da tsangwama da yakemin,Duk inda nake UK sai ya bibiyeni yaje ya tozar tani ya wulak'anta ni gaban tarin jama'a,har randa na daina ganinsa a skul d'in".

Ruk'o hannunta sweety tai ganin yanda yanayinta ya sauya lokaci guda tace "kiyi hak'uri Nahna amma don Allah ina son ki fad'amin tsakani da Allah komai dake tsakaninki da Broth tin farkon saninki dashi".

Nahna bata b'oyewa Sweety komai ba ta sanar da ita tun farkon had'uwarsu,idonta yana tara k'walla ta k'arasa zancen , hannu sweety tasa tana sharewa Nahna ido " kiyi hak'uri Nahna don Allah karki k'ullaci Broth a zuciyarki,karki k'ulla ceshi hakan zai hanaku jin dad'in zaman aure,matuk'ar kina tuna Irin haka bazaki tab'a ganin farinsa ba zaki rink'a jin tsanarsa a ranki, nasani Nahna Ke me ilimi ce sanin addininki yana miki amfani,don haka nasan auranku zaiyi albarka Duk abunda yaya zaiyi gareki don Allah ki daure Nahna komai lokaci ne wata rana ba zaiyi ba kinji Nahna, hak'ika Duk wanda yaji wannan labarin yasan akwai wani abu da Allah ya b'oye gareku shiyasa harya had'aku a baya cikin rashin fahimta yanzu kuma ya had'a Ku matsayin ma'aurata,tabbas akwai wani Abu da Allah ya b'oye tsakaninku kiyi hak'uri kinji don Allah ".

Mirmishi Nahna ta k'ak'alo tana Gobe k'wallan idonta tace " karki damu sweety Duk wannan na san yana cikin k'addarata, auren UK babbar k'addara ce gareni wanda sanin tsakanina dashi yasa hankalina ya tashi amma dana kai kukana game sharemin hawaye sai naji Duk hankali na ya kwanta, ni yanzu banda wata matsala da wannan auren domin na rok'i ubangiji zab'i kuma da alkairi don haka karki damu,insha Allah ni dai daga gareni babu wata matsala kan auren nan matsalar tana ga d'an uwanki".

"Insha Allah shima ba wata matsala zaku zauna kuyi rayuwarku cikin kwanciyar hankali harku Tara mana baby's ma ".
Ta k'arshe tana dariya,girgiza kai kawai Nahna tai tana mirmushi don bata da abin fad'a, sun dad'e suna hira har aka fara kiran sallah nan sukai sallah sannan sweety ta wuce gida.




************
Kwanaki ba jira suke ba,don gashi yau an cinye wata Guda dasa ranar Nahna da UK wanda yanzu ya rage wata biyu, sweety ta matsawa Nahna su fitar da anko amma fir tak'i tace ita bata da sha'awar yin anko a bikinta, ganin ta kafe yasa sweety yiwa Aunty Hafsah maganar, nan tace karta damu zata mata magana ta shirya suje Gobe su fitar.

Da dare Nahna na zaune parlour tana koyawa su Ashraf Assignments kasancewar yaya usman na gari bazata kwana gidansa ba, Aunty tazo ta zauna gefenta tana fad'in "wannan assignment d'in bai k'areba ne har yanzu?".

" a'a mun gama yanzu Aunty bayani nake musu dai , wani abin za'a miki ".

" a'a magana nakeso muyi,Kai Ashraf had'a books d'in na kai d'aki".

Bayan yaran sun shiga d'aki Aunty ta dubi Nahna sosai tace "Nahna ki shirya Gobe kuje kasuwa da Sweety zaku fitar da anko,sabida Kinga rannan ma Su Aunty sukayo waya suna tambayar bamu fitar da anko ba har yanzu, Kinga saiku fitar harda namu na yini ko".

Kallon Aunty tai kamar zatai kuka tace "Aunty wlh ban sha'awar anko gun bikin nan kawai a barshi ".

" Nahna kina so ki nunawa duniya baki son auran nan kenan,kullum sai kice mana bakida matsala da aurannan amma yanzu kuma zaki fara tsiro da zancen kin yin anko tun a matakin farko,don haka ki shirya gobe kuje ".

" Tom Aunty Allah ya kaimu " bazata iya yiwa Aunty gaddama ba don haka tace haka taja bakinta tai shiru".



*****
A gidansu sweety tana zaune gaban Abbansu tana fad'a mai zancen siyo ankon da zasuyi " Abbah ka bamu kud'i mu fitar da anko kasan miji Ke bada kud'in anko".

Cikin jin dad'i da nishad'i Abban yace "karki damu ga ATM kuje dashi Duk abunda kuka siya ba matsala Ku ciri kud'i".

D'auka tai tana fad'in " yawwa Abbana, don hidima fa nakeso muyi da bikin nan bikin babban yaya ba wasa ba ".

Aunty murjah ce tace " in kunje Nahna sai Ku fitar mana da less me kyau na yinin bikin na manya anunawa dangi".

"Tom ba matsala Aunty kuma zamu zab'o muku cancad'ed'e "


*******
Washe gari misalin k'arfe goma sweety tazo gidansu Nahna ba b'ata lokaci suka tafi,suna zaune a gidan baya yayin da Driver Ke driving nasu, Sweety keta hira ita kam Nahna sai dai tai mirmishi kota d'an tanka kad'an don batajin hira ko kad'an yau d'in Duk da kasancewarta daman bamai yawon hira ba, a k'ofar Mudatex sukayi parking tacewa driver ya jirasu zuwa awa d'aya.

Kai tsaye suka shiga wajan kasancewar daman sweety batada wajan siyayya a kantin kwari inba Mudassir and brothers ba, nan taita gaggaisawa da y'an shagon Duk sun Santa sunata fad'in hjy Ruk'ayya sannu da zuwa,nan ta sami waje ta zauna ta nunawa Nahna wajan zama itama, yaron wajan ya iso suka gaisa sweety tace " Allah yasa an kawo kaya,don ban son gama gari ".

Dariya yai yace" hjy Ruk'ayya mu wuce Sama akwai kaya ko fito dasu ma daga sito ba'ayiba,muje ki zab'a son ranki".


Sosai ta baje take zab'ar kala yayinda yaron gun Ke taya zab'ar kala,ita kuwa Nahna ta zama y'ar kallo sai mirmishi kawai takeyi wanda daman shine d'abi'arta koda yaushe zaka riski fuskarta da mirmishi,koda bazatayi magana ba,


Wani had'ad'd'an less suka zab'a me kyau matsayin ba dinner,sannan suk'a k'ara zab'i wani less kuma na dangin su sweety na mother's day, ta kalli Nahna tace " Nahna naku fa na yinin wane kala zaku zab'a ?"

Jim Nahna tayi tana tunanin gaskiya bazata d'orawa danginta wahala ba don wannan less d'in tanaji suna cewa Duk 1 yard 2500, tayaya zata fitar dashi matsayin ankon yini don dai dai ruwa dai dai tsaki,su danginsu zasu iya siya ko na nawa ne amma ita danginta masu k'aramin k'arfi ne don haka bari ta nemi me sauk'i,

Jin sweety ta k'ara magana yasa ta D'an d"aga ido tana kallon kayan gun kana tace " gaskiya bari mu zab'i atamfa mu don nasan zasufi sonta,tunda Kinga muna da tsofaffi da yawa a danginmu kuma su sunfi ganewa atamfa".

Ta fad'a cikin dariya, itama sweety dariyan tayi,tace "To mu zab'i wadda kike ganin zata yiwa Kowa kyau,

Nan suka fitar da wata me kyau kud'inta 3500 tirmi d'aya, tun a shagon sweety uwar azarb'ab'i ta d'auki hotunan ankon ta d'ora a dp da status d'inta.


Koda suka dawo gida Sweety ta fito da kayan tana nunawa Aunty Hafsah ta jin jina musu sun zab'o anko me kyau,nan itama ta d'auki hoton less d'in dinner d'in da atamfar yini ta turawa mutanan sakkwato.


Da dare Aunty Amrah tazo gidan don ganin ankon tunda Yaya usman yana gari Nahna ba zuwa gidan zatayi ba, nan Yaya Haroon ya cewa Aunty Amrah ta shirya cikin satin zasu shiga kasuwa ayo Duk siyayyan kayan d'aki dana kitchen.



Yayyena maza da mata da iyayenmu mata Duk sun turo da gudun mawarsu ta account d'in yaya,Kud'i ne ba na wasa ba aka Tara don yayyena suna ji dani matuk'a kasancewata auta cikinsu, ga rashin mahaifi don sun san babu me yimin saisu, kuma uwa uba ance musu gidan masu abin hannu zan shiga dole su k'ara k'aimi wajan k'awata min gidan don gudun raini da wulak'ancin dangin miji da jama'ar gari.

Kwana uku a jere suna shiga kasuwa an siyo min furniture Irin wanda ake yayi gado 7by7 Mbf guda d'aya sannan normal set d"aya , kujeru ma set biyu akai min da k'atuwar TV d'ina da firji ga kayan kitchen komai yaji. Haka aka had'asu Duk aka rufe yaya ya kai gidan abokinsa jikin gidanmu ajiya sabida akwai k'aton gareji a gidan basa amfani dashi nan aka had'a Duk aka k'ulle.

A nan na k'ara tabbatarwa kaina ni y'ar gata ce gaba da baya ganin Irin uban siyayyan da akai min.


A can gidansu sweety ma shiri sukeyi sosai don Aunty murjah da ummu sulaim kasuwa suke shiga koda yaushe had'a lefe na ajin k'arshe Abbah ya bud'e bakin aljihu so yake ayi abin harkar girma, b'angaren ma da zasu zauna Duk da daman ba kowa a part d'in k'alau yake amma Abbah ya kawo ma'aikata suna k'ara tsara gun an k'ara fito dashi yanda baka zato.



*******
Biki ya rage sati hud'u aka kawo lefe,subhanallah zo kuga kayan arzik'i abin ba'a cewa komai fa don Abbah basuyi la'akari da cewa Nahna ba y'ar kowa bace balle ayi mata kaya kad'an,a'a sakin jiki akai aka sa mata suttura masu matuk'ar tsada da kyau, English wear's akwati biyu aka cika dashi had'ad'd'u na gaske, lokacin da Yaya Haroon yaga kayan ya kira Alh Usman a waya yake cemai wannan uban kaya ina Nahna zata kaisu,mirmishi kawai yai yace duk abunda akaiwa Nahna na aure ta kai amata nutsuwarta kamun kanta tarbiyarta da iliminta Duk sun kai a kashe mata ko nawa ne, nan Yaya ya k'ara godiya ya kashe wayan.

K'awaye da y'an unguwa tako ina suka rink'a tururuwar zuwa kallon lefe kowa yazo yace alasan barka,

A b'angaran UK kuwa mamaki yake yanda yaga Duk danginsa rawar k'afa suke da auran nan wanda shi shirin sa ma kawai yakeyi na tafiyarsa, bai damu da wani shiri ba, don baya tunanin zayyi wani event ko d'aya don bai san me zai cewa abokansa ba in sukaji zai aure kuma ma abin bak'in cikin ace wai y'ar Arabic Mara wayewa zai aura masu yawo da hijabi kullum.


Ita kuwa sweety ta dage events sosai takeso ayi yayin da ta rasa had'in kan Amarya da ango ita Nahna tace Sam bata sha'awar wasu bidio'i a bikinta,tafi so ayi walima kawai aka d'aura aure, yayin dashi angon ya kafe babu wanda zai gayyata balls azo aga Irin matar tasa, don haka babu wani event ko d'aya da za'a yi, jin hakane yasa tai k'wafa tana nazarin hanyar da zata b'ullo musu.


Da dare sweety ta shiga d'akin UK baya nan sai wayarsa ajiye kan kago,mirmishi tai ta d'auki wayan kai tsaye ta shiga contacts d'insa ta fara tura I.V d'in bikin tai marking baki d'aya cikin sauri ta ajiye wayan ta fice,

Bayan kusan 20 minutes ta jishi yanata k'wala mata kira,lokacin tana gaban Abbah suna hira a dake ta amsa harya shigo parloun kome ya tuna saiya juya ya tsaya bakin k'ofa yana cewa tazo, cikin basarwa taje tace "gani broth"
Cike da masifa da b'acin rai yace " Sweety waye ya d'aukarmin waya ta d'azu"

Nunawa tai Sam bata san zancen ba nan ya hau masifa yana fad'in "ni za'a rainawa hankali a d'auki wayata kawai a turomin abinda banda niyar turawa don q wulak'anta ni".

Daga bayanshi ya muryan Abbah yana fad'in " kaida waye ne Baba na,waya tab'amin kai?"

Dummmm yaji gabansa ya fad'i,toshi yanzu zai cewa Abbah katin auransa aka turawa abokansa ne kome,kawai Sai yw basar yace "wlh Abbah ban san wanda ya d'auki wayata yamin shirme a ciki ba,kuma tabbas nasan bazai wuce wannan yarinyarba amma gashi tana min musu wai ba ita bace".

Hak'uri Abbah ya shiga bashi yana fad'in koma waye yayi hak'uri yabar zancen, cikin fishi ya koma d'akinsa,ya zauna bakin gado dafe da kanshi, tsaki kawai yake ta ja, don yanda wayanshi taketa ringing yasan abokansa ne suke fama kira don tabbatar da sak'on daya shigo musu,da bak'in ciki ma ya ishe shi saiya kashe wayan baki d'aya ya koma ya kwanta kansa na sarawa kamar zai fashe.


Da safe bayan ya kunna wayansa, tarin sak'on ni ne suketa shigo wa abokai nata masa k'orafi kan zaiyyi aure amma bai sanar dasu da wuriba ciki harda manyan abokansa aminansa, baiyi mamaki ba saida ya bud'e Datan shi ya chiga net nan yaga inda aketa cacca karsa tako ina,rasa abinda zai fad'a musu yayi don haka kawai ya shiga bada hak'uri kan cewa auran ne yazo mai ba zata shima bai shirya wa hakan ba,a haka ya samu ya rufe bakinsu, amma tarin takaicinsa dayaji kowanne na cewa zaizo,dana k'asar da way'anda ba y'an k'asar ba,ya tabbatar kashinsa ya bushe, asirinsa ya tonu kenan,kamar yace musu basai sunzo ba amma yasan hakanma wani watsa kansa zai k'arayi,don haka yanzu kuma dole ya nemi mafita ta gaba kuma, don haka ya kira number d'in abokin sa mashkur yace da yamma su had'u zasuyi magana.


*****
Da yamma suna zaune a balcony kan kujerun roba shida mashkur bayan sun d'an tab'a hiran abokai ,ya gyara zama yana cewa" Wato kanaji ko Mashkur wannan auran da kukemin k'orafin buku sani ba sai yanzu daya rage 2 weeks wlh banda shirin yinsa nan kusa, Abbah ne lik'amin shi kai kasan banda wani tsarin yin aure shekaru kusa,to babban abin takaicin ma abokina zaka iya tuna lokacin da muke SA'ADATU RIMI Lavel 4 wata yarinya y'ar Arabic dana matsawa na tsaneta wata yarinya nan kamar wayayyi ya amma lokal ce ka tunata?"

Jim Mashkur yayi can yace "ohhhh wlh na tunata tabbas na tunata wata y'ar black beauty ko y'ar Arabic na tunata meya faru?"

Yawun takaici UK ya had'iye kana yace "Mashkur wai wannan yarinyar fa Abbah zai aura min".

Da sauri ya k'ara kallon shi " haba dai UK meya had'a ka kuma da wannan yarinyar?"

Yak'e yai wanda yafi kuka ciwo nan ya fayyace mai komai, shuru Mashkur yayi kamar ruwa ya cinyeshi can ya nisa yace "Yanzu dai me faruwa ta faru sai asan yanda za'a gyara gaba domin duk abunda za'a yi a kare mutunci shi za'a yi inba haka ba abokai su rainaka".

" eh nima hakan nake nufi don kasanni ban san harkar k'aranta, ko abunda za'a rainani,don haka ka bani shawarar yanda zanyi".

"Ai mafita gudace yanzu a k'awata bikin sosai a shirya programs zafafa ita kuma amaryar taka tunda ustaziya ce kaja mata kunne ka gargad'eta kan ta fidda ka kunya Kar aje gaban abokai za'ai harkar wayewa tazo tana sissinne Kai".

Jin jina kai UK ya shiga yi nuna gamsuwa da shwarar Mashkur nan sukaita shawarwari sannan Mashkur yai mai sallama ya wuce gida.


Abunda kuma ya k'ara hargitsa shi budurwarshi fadlah ta kirashi a waya tana rizgar kuka ta sami labarin auransa, rarrashinta ya shiga yi yana nuna Mata ba lefinshi bane Abbansa zai mai amma Sam tak'i yarda tana fad'in Ya cuceta Ya yaudareta kullum tana cewa suyi aure amma yana fad'a mata shi bai shirya aure ba shekaru kusa amma gashi don yaga sun rabu zaiyi aure, ganin zata b'ata mai rai yasa ya kashe wayan.




Takuce
y'ar mutan ja'oji πŸ™‹β€β™€
🍑🍑🍑🍑🍑🍑🍑🍑
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
🌸 *Y'AN ARABIC* 🌸


NA

LAYUZA KABIR ADAM

DEDECATED TO ALL
ARABIC /ISLAMIC STUDENTS
πŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“š

πŸ‘¨πŸ»β€πŸ’»πŸ‘©πŸ»β€πŸ’»
*ZAMANI WRITERS ASSOCIOTION*

πŸ“
​​WΙ› Ι‘Κ€Ι› Ι¦Ι›Κ€Ι› tΡ³ Ι›Ι—ucΙ‘tΙ›, MΡ³tiΡ΅Ι‘tΙ› Ι‘Ι³Ι— Ι›Ι³tΙ›Κ€tΙ‘iΙ³ Ρ³uΚ€ ʀɛɑɗɛʀร​​



0⃣2⃣3⃣



Duk yanda UK yaso ya kaucewa kula Sweety yaga bazai yiyu ba,tunda indai yana fishi da ita ta yaya zai samu yanda za'a fitar dashi kunya, haka badan yaso ba ya kirata yana fad'a mata taje ta shirya duk wasu programs wanda zasu nuna girmansa gun abokansa,don bai san harkar raini,
Wani bala'in dad'i ne ya rufe sweety harma ta kasa b'oyewa,cike da farin ciki ta mik'e tana fad'in Tom yawwa my broth haka nake sonka,
Wani kallo ya watsa mata sannan ya tsaidata" naga kin fara wani rawar kai Kar kiyi tunanin ko na fara son auran ne wlh ko d'aya balle kije ki sami abin fad'a, kawai haukan da kikayi min ne na turawa friends d'ina invitation yasa ba yanda zanyi Kar suzo su rainani ko suyi tunanin banda kud'in da zan shirya wasu events ne,don haka zan kankarowa kaina k'ima, kuma gobe ki shirya ki rakani gun yarinyar don zan gargad'eta matuk'a wlh ta kunyatani gaban mutane ta k'arawa kanta lefi saina maidata tamkar baiwa a gidana, fice kiban waje".

Jiki ba k'wari Sweety ta fice tana tausayin Nahna har cikin ranta, dole a lokacin ta shirya ta wuce gidansu Nahna.



Tana zuwa ta sami bata nan tana gidan yaya usman Aunty Amrah tayi kiranta, zama tayi suka gaisa da Aunty Hafsah suna d'an tab'a hira tace "Aunty daman Broth ne yace gobe zaizo gun Nahna suyi magana kan sheduls na bikin sabida abokansa da yawa zasu zo dana India dana sauran k'asashe da sukayi karatu tare,to so yake a k'awata abin sosai,to shine kafin yazo nazo in rarrasheta kar yazo tace bata so ayi,Kinga yanda nake fama da ita kan ko dinner ta bari ayi tak'i,to yanzu tunda shi ya amince don Allah Aunty ki k'ara rarrashinta,ta amince".

Gyara zama Aunty tayi kana tace " ba komai zan k'ara tank'wasarta,insha Allah bazata bada matsala ba,yanzu kije can gidan Amran Ku had'u saiki fara mata maganar".

Sallama taiwa Aunty ta wuce gidan yaya usman d'in,

*****
A gidan yaya usman d'inma samu tai sunata fafatawa da Aunty Amrah me gyaran jiki tazo tana cewa bata so, ganin idon sweety yasa tai shuru me gyaran jikin ta fara dirjeta,dake matar y'ar Sudan ce A unguwar su Amrah take ita tai mata na bikinta,don haka gudunmawarta ta d'auko matar ta biyata tayiwa Nahna,

Sun d'au tsawon lokaci a d'aki tana dirje mata jiki tare da turarata da wasu asirtattun turarika, yayin da Sweety da Aunty Amrah suke parlour suna tattaunawa kan yanda za'a tsara bikin, nan suka k'ara tsara sabon IV ,
Ranar Alhamis za'ayi kamu ayi lecturer, ranar Friday za'a d'aura aure k'arfe biyu bayan sallar jumma'a ,da dare za'a fita dinner, ranar asabar za'ayi culture day,karfe biyu zuwa h'udu sannan a fita lunching hud'u zuwa bakwai, ranar lahadi ayi mother's day,wanda su Sweety zasuyi nasu a Annour event su kuma su Nahna suyi Nasu a gida sai k'arfe bakwai akai amarya bayan an kaita kuma k'arfe tara a k'ara fita friends night wanda iya abokan angone kawai da k'awayen amarya zallah,zasuje nan Sweety ta k'ara typing d'insa cikin wayanta tayi mai editing sosai ta watsashi a yanar gizo,sannan ta wuce ta kai printing press su fitar Mata shi,ranar dai basu zauna da Nahna ba don harta wuce gida ba'a k'arasa gyaran jikin ba, Aunty Amrah tace ta bar komai gunta zata sanar da ita sak'on duka,

Yau kam Nahna taga abinda ya girmeta,aranta take tunanin wane Irin gyaran jiki ne wannan ace ko ina na jikinka sai an dirje,tun tana jin kunya harta daure amma wani gun ca take ta barta ta goga da kanta.

Sai yamma lis aka gama,tana fitowa kamshi na binta,Ta zauna parlour tanata yiwa Amrah k'orafin Duk an wahalar da ita,dariya Amrah tayi tace "kuma daga yau har ranar da za'a kaiki gidan Umar ana miki wannan gyaran jikin, me gyaran jikin ce ta fito,ta bud'e jakarta ta fiddo wasu kullin ledoji ta bud'esu tana kallon Nahna tace " wannan ki rink'a sha da madara wannan kisha da Zuma wannan kiyi turaren tsugunno,cikin rashin fahimta tace "na meye wannan din kuma?"

Dariya Aunty Amrah tayi tacewa me gyaran jikin " Barta zan mata bayani a d'aki naga kamar kunya takeji".

Mirmishi kawai Nahna tayi ta mik'e tsaye tana fad'in "bari in wuce gida maman biyu".

" he lalle ma Nahna bakinki ya bud'e,kema kwana nawa ne zaki zama maman biyun ".

Da sauri Nahna ta rufe ido tana Neman mayafinta ta gudu,ruk'o hannunta tai tace "zauna zamuyi magana kafin ki wuce"

Wuce wa tai ta raka me gyaran jiki k'ofar gida sannan ta dawo, ta zauna tana fuskantar Nahna sosai ta fara " Nahna sweety tazo da magana zakuyi amma Baku sami zama ba taban sak'o ki shirya in Allah ya kaimu gobe Umar zaizo Ku gaisa, sannan yace a shirya events sabida abokansa zasu zo,don haka mun tsara nida sweety, kamar yanda kika ce ran Alhamis kinaso ayi lecture da kamu to hakan za'ayi,amma batun walima da zakiyi bayan d'aurin aure da yamma ta tashi dinner za'ayi da dare,asabar ayi culture show da yamma ayi lunch dangin amarya Dana ango duka waje d'aya sai Lahadi ayi mother's day akai amarya,bayan an kaiki kuma zaku fita friend night sabida abokansa da zasu zo,ina fatan baza ki bamu kunya ba Nahna don in kika Bijire zai fara ganin kin fara mai gaddama tin kafin kuyi aure,ki nuna mai Ke me biyayya ce bisa umarninsa".



Please Login or Register in order to submit comment