Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Tafiya ya farayi zuwa hanyar toilet d'in yana fad'in" ki gyara mana".
Ya shige toilet d'in, yana shiga na fara gyara d'akin na canja bedsheets d'in nasa sabo na share d'akin na kunna turaren wuta a lokacin ya fito daga wankan yana tsayawa gaban dressing mirror na fad'a toilet d'in na had'a inner wears d'in sa na wanke sannan na wanke toilet d'in na fesa freshener na fito, harya sa kayansa ya gama shiryawa yana tsaye yana d'aura agogo na wuce shi saida naje bakin k'ofa sannan nace mai "food is ready " "OK" yace kawai ,

D'akina na koma na k'ara goga Humrah na kalli kaina a madubi naga komai dai dai, ina fitowa shima yana fitowa son haka a tare muka k'arasa dining table d'in, na had'a mai break d'in kunun gyad'a ne da awaran kwai sai ferfesun kifi wanda yasha kayan k'amshin miya, cup k'arami na d'auka nima na zuba kunun na fara sha sab'anin da da kullum sai ya gama ya tashi nake cin nawa, nayi mamakin yanda naga yana shan kunun gyad'an haka don saida na k'ara mai sau biyu cup uku yasha sauran abubuwan nema bai wani tab'a ba, bayan ya gama yana goge baki da tishu na kalleshi kad'an tare da rage muryata sosai nace "Am don Allah ina son komawa school gobe ".
Kamar bazai magana ya mik'e saida yai taku biyu zuwa uku sannan ya amsa " ba matsala"

Daga haka ya fice daga gidan,
Ni kuwa nan da nan na tashi na had'a wanke wanke nayi,na tsaftace kitchen d'in sannan na tafi wajan su sweety duk da bata nan tana school muka gaisa da Aunty murjah na zauna muka d'anyi hira a nan take fad'a min Abbah yace za'a bani y'ar aiki guda d'aya ta dinga taimakamin ,mirmishi nai nace " Aunty wane aiki ne dani da har za'a kawo min y'ar aiki,wlh ba komai duk zan iya,kicewa Abbah ya barta kawai".
"A'a ko wanke wanke ai ta rink'a miki da moping".
Nace " To Aunty mu bari zuwa gaba in Aikin ya fara min yawa zanyi magana ".

Nan nake shaida mata ma gobe zan fara koma school, taimin fatan alkairi mun D'an jima muna hira sannan na koma part d'ina,

Yau da wuri na fara Aikin girkin dare don Danbun cous cous nake sonyi kuma da yawa nake sonyi sabida har Abbah nake son kaiwa don nasan mutuminsa sannan ina son inyi lemon kwakwa.

Aikina nake cikin nishad'i na kunna wak'ar mu ta graduation Na N.C.E d'in mu wak'ar larabci ce ta bugu sosai ina son wak'ar duk lokacin da nake cikin nishad'i ta kan tayani ko in ina cikin kad'aici sai in kunta,yanzunma dagani sai d'an wando 3qurter da riga y'ar figigi mara hannu kasancewar zafi ta busa, ina aikina ina bin kasidar nan da nan na gama aikin kafin sallar magriba harna kammala na zuba a Warmer's sannan na zubawa Abbah a wani kalan cooler d'in na d'auko juk babba na zuba mai lemon kwakwa d'in na d'auko kwandon sa abinci nasa aciki na d'auko wani farin bowel me ruwan garai na zuba mai had'in coleslow d'in da nayi Duk na jera sannan nashiga d'aki don yin wanka.

Wanka na shiga nayi tare da d'auro alwalan magriba sannan na fara kwalliya sosai yau nai kwalliyar na saka dogon wandon jeans wanda yake pencil sosai nasa wata body hug me roba k'aramin hannu gareta iya cinyar hannu ta kamani sosai k'irjina yayi d'am a ciki kasancewar dukda nake siririya Allah ya wadatani da dukiyar fulani da hips wanda suke da jan hankali don haka ko wane irin kaya suke karbar jikina, doguwar riga after dress na d'auko nasa tare da hijab nai sallar magriba ina idarwa bayan nai addi'oi na fito na d'auki abincin Abbah zan kai mai a k'ofar parlour mukai karo da sauri na matsa ina fad'in "sannu ban kula bane" cikin tsare gida yace " ina zaki?" " Abbah zan kaiwa abinci".
"Haka yace miki baici abinci ba". " a'a danbun cous cous nayi ne naga yana sonshi shine na dibar mishi". "Ki sauri ni dawo malama ina buk'atar abinci yanzu". " To " nace na wuce ina k'ara saurin tafiya ta, koda naje part d'in nasu sweety na bawa abincin nace don Allah ta k'arasawa da Abba shi".
Tana ta min tsiya banko saurareta ba na juya na fice,
Sanda naje na sameshi dagashi sai gajeran wando da singlet na maza yana zaune a dining area d'in hijabin jikina na cire tare da After dress d'in na k'arasa gareshi yana d'agowa yaji wani Abu ya cakeshi a k'irji duk dashi bai zama me yawon sha'awa ba sannan yana iya kallon mace ako wace Irin shiga bata rikitashi ba kasancewar yana rayuwa cikin indai wa da turawa wanda basu damu da sitirce al'aurarsu ba amma yanzu kallon da yai mata sai yaji wani abu ya tsirga mai dukda abinda ya gani d'in ba bak'onsa bane a garin data baro, ya fad'a duniyar tunani harna kammala zuba abincin naga ya lula tunani,bance komai ba na koma na zauna saida naga abincin na shan iska baici ba nai k'asa da murya sosai nace "Abincin fa yana hucewa ". Da sauri ya kauda kansa yana basarwa yaja abincin ya fara ci,daga yanda naga yanaci yana kurb'ar lemon tare da lumshe ido na gane yaji dadinsa sosai, satar kallon juna muke kusan sau biyar muna had'a ido hakan yasa duk ma naji kunya ta kamani don na kula idon nasa akan k'irjina yake yawo,cikin wata murya daban san sanda nayi ta ba na marairaice fuska" Don Allah inje d'aki "
Yi yai kamar baiji abinda nace ba yaci gaba dacin abincinsa, k'ara maimaitawa nai badan yaso hakan ba yace "jeki " yana fad'a nai sauri na tashi don duk na takura, gado na fad'a ina wani tunani araina mirmishi ya sub'ucemin na jijjiga kai ina k'ara yarda da shawaran da zuciyata take bani.

B'angaran uban gayyar kuwa da kyar ya k'arasa cin abincin ya tashi ya shiga d'akinsa tunani fal ransa anya kuwa bai fara jawa kansa raini ya bari yarinyar nan ta kamashi yana kallon ta haka,lalle ya kamata ya k'ara tsare gida sosai yasan makircin mata iri iri in suna son ka fad'a tarkonsu amma ita kam bata isa ya fad'a nata tarkon ba,wai meye ma abin birgewa ga wannan k'aramar yarinyar kuma y'ar Arabic me k'arancin wayewa mutttssss yaja tsaki yana dayawa kawai k'ara ya fara shirin komawa India nan da sati biyu don baiga amfanin zaman sa a nan ba tunda dai an tilastashi yayi auran to ai shima sai abashi damar shi kuma don haka gobe zaijewa da Abbah maganar nan gaskiya.





Taku ce
Y'ar mutan ja'ojiπŸ™‹β€β™€
https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation?


🍑🍑🍑 🌸🌸🌸🌸
🌸 *Y'AN ARABIC* 🌸


NA

LAYUZA KABIR ADAM

DEDECATED TO ALL
ARABIC /ISLAMIC STUDENTS
πŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“š

πŸ‘¨πŸ»β€πŸ’»πŸ‘©πŸ»β€πŸ’»
*ZAMANI WRITERS ASSOCIOTION*

πŸ“
​​WΙ› Ι‘Κ€Ι› Ι¦Ι›Κ€Ι› tΡ³ Ι›Ι—ucΙ‘tΙ›, MΡ³tiΡ΅Ι‘tΙ› Ι‘Ι³Ι— Ι›Ι³tΙ›Κ€tΙ‘iΙ³ Ρ³uΚ€ ʀɛɑɗɛʀร​



0⃣2⃣9⃣

Yau Monday tunda nai sallar asuba ban koma bacci ba na shiga kitchen na had'a kayan breakfast,shayin zobo na had'a wanda yaji na'a,lemon grass,da kayan k'amshi danginsu citta da kanumfari,sannan na soya gurasan larabawa,nai D'an yam balls kad'an, bayan na gama nai wanke wanke a gurguje na gyara gidan tsaf, wanka ma a gurguje nai nayo kwalliya ta me sauk'i kasancewar yanzu nasan hakkin dake kaina dole in canja salona ta kowace fuska dukda daman bawai ina shigar banza bane ko yin wani Abu na shashanci amma dai dole in k'ara takatsantsan matuk'a yanzu,na shirya cikin atamfa ta blue me yarfen ganye milk nasa hijab dina me hannu milk wanda yazo min har kusa da idon sahu akwatinan lefe na na bud'e na d'auko takalmi da jaka Duk milk, nasa kallo d'aya zakai min ka gano sabuwar amaryace, lokacin dana fito daga d'akin bakwai da minti ishirin nasan bai tashi a bacci ba amma sabida kare hakki saina tura k'ofan a hankali na shiga, kwance yake kan gadon yana bacci hannayensa rungumu a k'irjinsa tsayawa nai na y'an seconds ina tunanin abinyi naga ya fara motsawa da sauri na juya zan fita cikin muryar bacci naji yana cewa " Ke Mene?"
Ban jiyo ba na amsa mai "em daman nai tunanin ka tashi ne zan gyara d'akin kafin na wuce school".

"Kije kawai in kin dawo kya gyara"
Yana fad'a ya juya yaci gaba da baccinsa.
Ni kuwa dining na nufa na d'anyi break Sama Sama don bana iya cin Abu da yawa da sassafe haka, kud'i nasa a jakata masu nauyi don yin transport da sauran buk'atun school.

Nayi nisa da gidan ina tafiyata a nutse saura k'iris in k'asara titi naji horn d'in mota a bayana ban juya ba illa k'ara matsawa da nai gefe sosai don nai tunanin ko hanya motar Ke nema amma sainaga ma ta matso kusa dani sosai ta tsaya cak nima na tsaya ina mamakin waye wannan, muryar Abbah ce tasa na d'ago kaina ina kallon motar "zo ki shiga mu tafi Khadeejah" naji yace ba musu na bud'e murfin motar na shiga tare da gaishe da Abban da drivern dake jansa, cikin b'acin rai Abbah Ke magana "Khadeejah ya akai kika fito school Ke kad'ai ina Mijin naki ya barki fitowa a k'afa".
Cikin ladabi na k'ara sunkuyar da kaina nace " Abbah bacci yake ne be tashi ba".
"Shashancin banza kenan wannan bacci yafi iyalinshi mahimmanci kenan,ni jiya Murjah Ke fad'a min yau zaki koma school abinda yasa ban miki maganar ba nai tunanin kun shirya komai da mijinki,amma dake shi shashasha ne ya barki zakije ki hau motar haya duk motocin dake cikin gidan sun zama ba amfani kenan,ko yanzu ma driver Ke cemin gaki nan a gabanmu don yaga fitarki a k'afa yana goge mota lokacin, amma zan had'u da Daddyn zai gamu da fishi na matuk'a da gaske, kema daga yau karki k'ara yunk'urin fita ba mota ko ina zakije don haka ma dole ya fara koya miki mota kwanan nan kema ki fara hawa motar ki".

Nidai tunda ya fara magana ban ce komai ba sai wasa da nake da yatsun hannuna,haka muka kai har school d'in Abbah nata fad'a sai driver daketa bashi hak'uri, motar na tsayawa nace " Abbah na gode a dawo lfy".

Kud'i ya miko min wai nasai wani abu nace a'a amma dole yasa na amsa .

Ina shiga aji na tadda hall ya cika taf amma lecturer bai zoba, nan fa K'awaye na sukaita shewan ga Amarya ga Amarya nikam mirmishi kawai nake ina mik'a musu hannu muna gaisawa nan akaita k'ara min Allah ya sanya alkairi way'anda ma basu sami damar zuwa ba sukaita ban hak'uri suna fad'a min uzurinsu nikam ca nake ba komai wlh addu'ar suma ta wadatar, a haka lecturer ya shigo shima saida yamin Allah ya sanya alkairi dake ba wani yawa ne damu ba yasa duk malamanmu sun sanmu kuma an basu I.V din d'aurin aure,
Wajan k'arfe d'aya muna masallaci zamuyi salla Naji kira a wayata da bak'uwar number bayan na d'aga sai naji muryar Abbah nan yake tambaya ta karfe nawa zan tashi nace mai sai wajan 5 yace to driver zaizo d'auka na in na fito bakin gate in duba zan ganshi, godiya sosai nai mishi.

Lokacin da muka tashi ina fita bakin gate naga motar Abbah data kawoni na jira nan na shiga drivern yaja muka tafi,sanda mukaje gida biyar da rabi a gaggauce na cire kayana na shiga kitchen faran shinkafa na d'ora na nik'a kayan miya a blender nan da nan na d'ora miya ma sannan na d'auko fruits na wanke na fara gyarawa don had'a fruits lasad, ban koma d'aki ba saida naga na kammala aikina duka na kwashe a flasks na saka fruits d'ina a fridge don yayi sanyi, lokacin k'arfe bakwai don har an shiga salla da sauri nai wanka nai salla nasa wata riga iya gwiwa me d'an k'aramin hannu nasa hula akaina tare da goga humra a duk jikina, zuwa lokacin nasan Me gidan ya shigo ai kuwa ina fita na ganshi kan kujera a kwance, ina k'ara sawa kusa dashi ya d'ago ya kalleni nace "sannu da zuwa ".

Kamar yanda ya saba ba yabo ba fallasa ya amsa min, dining dining d'in naje na shirya mai abincin sannan na d'an tako ina cemai" na had'a abincin "
Cikin isa Irin tashi ya taso ya zauna ya faraci ina zaune gefenshi ina karanta hand out d'ina, harya gama na kwashe kwanukan na gyara wajan,bayan nai sallar isha'i naci abinci ban zauna parlourn ba na koma d'aki nai shirin kwanciya don karatu nake sonyi sosai wanda akayi bana nan.

B'angaren Uk kuwa bayan yayi sallar isha'i a d'akinsa don ba ko yaushe yake bin jam'i kasancewar addini ba waje ya samu sosai a zuciyarsa ba,sallolinsa dai gaba d'aya ba wadda take wuceshi ko baije masallaci ba zaiyi a gida amma bayan kamsa salawat d'in nan fa bai k'ara nafila ko raka'a d'aya,balle azimin tad'auwa'i, addu'oi duk ba nashi bane, yana kwance kiran Abbah ya shigo wayarsa yana nemansa, tashi yai yasa rigarsa ya fice.
Daga yanda yaga fuskar Abbah yasan da matsala don haka jiki a sanyaye ya k'arasa ya zauna yana mai barka da dare, a ciki ciki ya amsa ya maida hankalinsa ga abinda yake a computer d'in dake gabansa saida ya kusan minti uku sannan ya kashe ya juyo gareshi, ya k'ara had'e rai sosai sannan ya fara magana " Daddy ka kyauta matuk'a da tozarcin da kai min yau kaji ".
Da sauri ya d'ago ya kallin Abban yana fad'in " Abbah me nayi ?"
" ni kake tambaya ma me kayi ko yayi kyau".
"Don Allah Abbah kayi hak'uri ka fad'a min Abinda ya faru wlh ban san me nayi ba"
K'wafa Abban yai yace "Ka tozarta ni duk motocin dake cikin gidan nan ace wai Khadeejah bak'uwa a cikin gidan nan yau duka kwananta takwas a gidan nan amma ta fuskanci wulakanci daga gareka, y'ar mutane ka Bari ta tafi makaranta a mortar haya, tsakaninka da Allah Daddy tsawan rayuwar ka zaka iya tuna lokacin daka hau motar haya? Amma sai matarka mutuncinka data cancanci Suturtawa daga gareka itace zaka barta fita titi ta hau mota ga tarin motoci a gida,ko Dan ka nunamin ka isa kayi yanda kaso".

Girgiza kai ya shigayi yana fad'in "Abbah lokacin data fita bacci fa nakeyi,kuma maimakon ta sami driver ya kaita shine ta tafi da kanta".
" OK bacci yafi uzirin matarka kenan yafi karatunta mutunci ko? To umarni nake baka ba shawara ba daga yau karka kuskura in k'ara ganin matarka a wata mota inba taka ba kuma fita ko wace irice Kaine me kaita,sannan daga nan zuwa kwana biyu ina son ka fara koya mata mota koda ka koma indai in uziri ya taso mata ta tafi a motar ta kaji na fad'a maka tashi kaban waje ".

Tashi yai ya fita ransa a mugu mugun b'ace da wannan hukuncin na Abbah, yana shiga d'akinsa yai cilli da rigarsa ya fad'a gado yana huci da firzar da wata iska me zafi,wai nufin Abbah shine driver na wannan yarinyar wai auran Dolan ma akai mai bai isa ba kuma sai an bishi da dokoki masu zafi haka,gaskiya an takura shi wlh shi wannan yarinyar ta zama masifa a cikin rayuwar shi ,anya bazai nemi hanyar korar yarinyar nan daga gidansu ba ko zai samu ya wataya,saida ya gama kuncinsa da b'acin rai ya shige toilet ya watsa ruwa don yaji sauk'in zafin da ransa Ke masa.
Yana kwance ya kasa bacci yana nazari kan wane Irin k'auna Abbanshi kewa Nahna haka har yake fifita lamuranta akan na kowa,dame ta siye zuciyar mahaifinsa haka,in yai tunanin sai dai kawai yaja mugun tsaki ya juya,a hankali kuma zuciyar shi kuma ta fara mai lissafin Irin k'ok'arin yarinyar wajan yin duk abinda ya umarceta da wanda ma bai umarceta ba,kamar dai yau ko sau d'aya baiyi zaton a wannan safiyar zata iya yimai girki ba kafin ta fita amma daya tashi yana tunanin inda zai sami abinda zaici yana fitowa parlour yaga ta shirya mai komai a table gashi ta gyara ko ina har tana k'ok'arin gyara mai d'akinsa badan yace ta tafi ba amma gashi ma a dawowar da tayi da yamman nan hartai girki ta gyara mai d'aki ta wanke mai toilet, gaskiya in haka ne fa tana k'ok'ari, mutttssss kuma yakuma jan tsaki wani sashin na zuciyarsa na fad'a mai to meye amfaninta daman in batai wad'an nan ayyukanba tunda daman ta saba da wahala tun agidansu.
Haka yaita sak'awa da kuncewa har bacci yai gaba dashi ransa ba dad'i.








Taku ce
Y'ar mutan Ja'ojiπŸ™‹β€β™€
https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation?


🍑🍑🍑 🌸🌸🌸🌸
🌸 *Y'AN ARABIC* 🌸


NA

LAYUZA KABIR ADAM

DEDECATED TO ALL
ARABIC /ISLAMIC STUDENTS
πŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“š

πŸ‘¨πŸ»β€πŸ’»πŸ‘©πŸ»β€??
*ZAMANI WRITERS ASSOCIOTION*

πŸ“
​​WΙ› Ι‘Κ€Ι› Ι¦Ι›Κ€Ι› tΡ³ Ι›Ι—ucΙ‘tΙ›, MΡ³tiΡ΅Ι‘tΙ› Ι‘Ι³Ι— Ι›Ι³tΙ›Κ€tΙ‘iΙ³ Ρ³uΚ€ ʀɛɑɗɛʀร​


*Allah* *ka* *zab'a* *mana* *shugabanni* *na* *gari* , *Allah* *karka* *barmu* *da* *zab'in* *kanmu* .πŸ‘


0⃣3⃣0⃣



Yauma daga sallar asuba ban koma ba na shiga kitchen na fara ayyukana bayan na gyara gidan ko ina na shirya cikin doguwar riga y'ar k'asar Sudan bak'a mai yalwataccen k'asa nai rolling da yalwataccen mayafinta wasu sabbin takalmi da jaka na fiddo cikin kayana orange color kasancewar aikin jikin rigar shima orange ne,dole in kula wajan canja shiga don duk lokacin da mace tai aure idon kowa akanta yake don aga yanda kamannin ta zasu canja da yanayin sutturarta,musamman y'an makaranta(duk da ba yabon kaiba y'an department d'in Arabic sa ido bai damesu ba abinda Ke gaban su kawai sukeyi)

Nazo k'ofar d'akin nasa naji motsin alamar ya tashi don haka na tsaya nai knocking,ya bada izinin shiga,da sallama na shiga ya amsa fuska d'aure tamau cikin sanyin muryata na gaisheshi bai d'ago ba ya amsa,nace "Em daman zan gyara d'akin ne".
Tashi yai ya shige toilet daman dagashi sai towel d'in wanka, tsaf na gyara d'akin nasa turare sannan na wuce nai break, ina mik'ewa yana fitowa cikin shiri 'kauda kai yai gefe yana fad'in" In kin shirya wuce mu tafi".
Cikin D'an dibirbircewa nace "Tom bari in d'auko jakata"
bai tanka ba ya juya ya fice nima da hanzari na shiga na d'auko jakan na fito tare da kulle k'ofar, harya tada motar na bud'e na shiga, cikin fishi naga yaja motar da gudun gaske ya fice nidai kaina naga takardar dake hannuna ina karantawa, kafin me sai ganinmu nai a gate d'in school d'in don bala'in gudun da yake yi har ciki ya shiga dani yaja burki da k'arfi ya tsaya,cikin mutuwar jiki nace "Na gode" na bud'e mirfin motar zan fita yai magana da izzarshi "Ke k'arfe nawa zaki tashi" 4:00 insha Allah "
Waya ya mikomin "sa number d'in ki anan" karb'a nai nasa mai ina mik'a mai zan fita ya k'ara tsaida ni "tsaya" naja na k'ara zama, kira naji cikin wayana ina d'aukowa yace "kiyi saving in kin tashi ki kirani da ita".

1k ya mik'omin rannan nashi kamar yaji sak'on mutuwa, nidai kaina na kawar ina cewa " ka barshi akwai kud'i a hannuna ".
" wannan ba damuwata bace in zaki amsa ki amsa karki b'ata min lokaci ".
Karb'a nai ina godiya na fice a raina ina mamakin bak'in hali Irin nashi mutum koda yaushe k'unci kuma a haka y'ar uwarsa Ke fad'in dad'in zama gareshi ,ina wannan tunanin na k'arasa Hall d'in da zamuyi lecture a ciki.

B'angaren sa kuwa cikin bacin rai ya koma gida lokacin ya duba agogo ko takwas har sa'ilin batayi ba aka tasheshi a bacci sabida wannan yarinyar tsaki yaja ya wuce dining ya cika cikinsa sannan ya koma d'aki yama rasa abinyi ga bacci Sam ya bar idon nashi daya d'an k'ara matsewa,gashi ba wajan zuwa gareshi ba duk abin dai ba dad'i,haka dai ya d'au wayansa ya shiga net don rage kad'aici.

Ni kuwa lecture ta nai a nutse saida muka shiga period d'in k'arshe ne ya rage saura minti goma mu fito na kirashi nace mun tashi don bansan Sai mun fito in tsaya jiran sa.
Ai kuwa ko bayan fitowarmu saida nai kusan wata minti goman sannan ya kirani yace min yana gate,Allah yasa daman kusa da gate d'in mukai lecture din don haka ba b'ata lokaci na k'arasa da sallama na bud'e na shiga ciki ciki ya amsa nace mai " Barka da yamma ".

" yawwa " kawai yace ya tada motar.



************
Haka rayuwar mu taci gaba da gudana kadaran kadahan ranakun da nake zuwa school hud'u don bama lecture Friday duka rana kun nan shi yake kaini ya dawo dani,sannan weak end da yamma mu fita ya koya min mota duka wannan lokacin ba abinda ya canja daga zamanmu yanda muke dai haka muke Sai dai ni bana wasa wajan yin duk abinda nasan hakkinsa ne dake kaina,sai dai b'angaren Abbah yana k'ok'ari matuk'a wajan son faranta raina don haka nima duk sanda nake da lokaci banje school ba ina zama in shirya mai abinda nasan yana sonci kamar su danbu,dashishin alkama,zob'o,kwad'an zogale kona rama duk ire iren abinciccikanmu na gargajiya don haka kullum cikin kyautatamin shima yakeyi.

A haka muka kai wata guda cif da auranmu,lokacin UK ya fara damun Abbah da maganar tafiyar sa don a cewarsa duka abokansu da aka zab'e su tare zasuyi course d'in wai Duk sun fara don haka Abbah badan yaso ba yace yaje ya fara shiri sati biyu masu zuwa sai Ya tafi,Ba haka yaso Abbaan yace ba,yaso ace kwana biyu kawai ya bashi amma har sati biyu, haka ya hak'ura yabi umarnin Abban,

Ranar da Dare Abbah ya Kira ni a waya inzo yana kirana, ba b'ata lokaci naje anan yake shaida min miji na zai koma indai nan da sati biyu kamar yanda na shaida da tafiyar don haka ya k'ara ban baki yana nunamin mahimmancin Abinda zaije yi badan hakanba yace bazai barshi ya koma d'in ba, Nikam mirmishi kawai nai nace "Ai ba komai Abbah, Allah ya kaimu lokacin kamar yaune zai dawo fatanmu Allah ya bada sa'a ".

Sosai Abbah yaji dad'in maganar

Please Login or Register in order to submit comment