Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

bacci ba". D'an hararenta nai ina fad'in "ba wani nan kawai kin manta dani ne cikin gidanku,amma bacci me zamuyi tayi har yanzu around 11" y'ar dariya tai tanamin rad'a a kunne " nasan ko ansha amarci jiya" duka nakai mata ina fad'in "Allah ya shiryeki Ke kam ni ban hanya in wuce". Dariya ta farayi ta ruk'o hannuna " zo in rakaki ciki nasan surukanki kika zo gaidawa" ban kulata ba na fara gaisawa da y'an wajan sannan muka shiga ciki,babu wasu mutane da yawa,y'an uwansu ne na katsina sai tsirarun na nan garin,tsugunnawa nai na fara gaishesu, nan suka shiga ansawa cikin sakin fuska suna tambayata ya bak'unta,kaina a k'asa naji fitowar Aunty Murja daga d'aki tana cewa "a'a amarya kin fito ai na aika muku da abin breakfast akace k'ofar a rufe buku tashi ba". Cikin tsananin kunya nace "Aunty ai nayi mana breakfast d'in ma" haba Khadeejah me yasa kika wahalar da kanki ga gajiyar biki tare dake aida biki yi ba ma kin huta sosai, mirmishi kawai nake kaina a k'asa tace "taso muje ki gaida Abban naku" mik'ewa nai ciki da nutsuwata nabi bayanta zuwa sashin Abban,da sallama muka shiga na tsaya daga bakin parlourn tace " k'araso mana " a zaune muka same shi kan rug yana cin abinci da fara'a kan fuskanshi yace yace "Khadeejah har kin fito" cikin girmamawa sosai na gaisheshi ya amsa yana tambaya ta ya gajiyan taro, d'an mirmishi nai nace "A khan fulfill ah " yace " Murjah Allah yasa dai y'ar taki taci Abinci ko?". "Eh Alh, an aika musu ma k'ofar a rufe basu tashi ba,sai yanzu take cemin ai tayi musu ma ". "Masha Allah, Allah yai muku albarka ya Baku zuri'a d'ayyiba kiyi hak'uri da rayuwar aure kinji Khadijah kisa a ranki jihadi zakiyi aljannarki zaki nema kinji" gyad'a kai kawai nakeyi nan yaci gaba da yimin nasiha sosai , Aunty murjah ce taje ta d'auko key tana mik'o min tace " Khadeejah ga mukullin motarki jiya ban baki ba sabida jama'a Kar ki yar". Karb'a nayi ina fad'in "Na gode Allah ya saka da alkairi Allah ya k'ara girma". Ameen Ameen suketa amsawa, sallamar sace tasa suka kalli k'ofar ni kuwa banko d'ago ba kaina yana ak'asa, nan ya sami waje kusa da Abban ya zauna ko kallon inda nake baiyi ba yace " Abbah barka da safiya, Aunty kin tashi lfy " tare suka amsa da "lafiya qlau ya gajiya " cikin basarwa yace "Normal". Kallon sa sosai Abbah yai yace "d'azu naga fitarka ina kaje da safe haka?" "Ah naje raka friend's d'ina ne airport zasu koma". " ok an gode musu Allah ya saka da alkairi". Inji Abbah mik'ewa yai yana fad'in "Abbah bari in k'arasa in huta " a'a zauna muyi magana ". Komawa yai y zauna badan yaso hakan ba, "Daddy nah ga matarka nan amana ce a gareka Amanar Allah kuma amanata ka rik'e ta da amana ka bata dukkan kulawar data kamata karka sa aranka ni na aura maka ita,ka rink'a ji har cikin zuciyarka cewa kai ka ganta kaji kana so ka aureta,in har kayi hakan ya gama min komai a duniya,kuma zanci gaba da alfahari da kai dukkan wani hak'k'in uba akan d'ansa ka sauke min nawa in har ka kula da Khadeejah, marainiya ce ka zame mata miki ma gurbin miji kuma ka zame mata gurbin uba a sanda buk'atar hakan ta taso kaji Baba nah". " ok Abbah ba damuwa " juyowa yai gareni yace "Khadeejah kiyi biyayya ga umarnin mijinki matuk'ar bai sab'awa umarnin ubangiji ba kinji". " insha Allah Abbah ". " yawwa Allah yai muku albarka ku tashi Kuje ".
Jira nai ya fara mik'ewa ya fita sannan nabi bayan sa, a balcony mukaci karo da sweety nace "To wuce muje ". Dariya tai tace " yanzu mijinki yace wai inzo in had'a mai abin breakfast nace kin shirya mai ai,don haka kije ki had'a mai zan biyoki a baya in na k'arasa abinda nakeyi ".
Kallonta nai cikin had'e rai nace " ba komai na gode tun yanzu kin fara guduna don kin ganni a cikin gidanku".
Rik'oni tai da sauri tana fad'in "Sorry Aunty nah wlh yunwa nakeji ban karya ba ".
" yawwa Daidai kenan Kinga saimu karya tare ai nima banci komai ba".
Badan taso ba ta bini muka tafi, muna shiga na taddashi kan dining harya had'a abinda zaici ya fara kwasar gara, kallon sweety nai nace "jeki zubo mana muci anan kinji" wata dariyar rainin hankali tai tace "ashe kuwa bazamuci ba,karki bada kanki don Allah muje kawai dining d'in muyi fuska muci kayanmu" ruk'oni tai muka k'arasa kan dining table d'in ta zauna tana fad'in "Aunty nah had'a mana don Har k'amshi ya cikamin hanci".

Cikin nutsuwata wadda ta had'u da sanyin da jikina yai na bud'e baki ina fad'in " Barka da safiya" yi yai kamar ba dashi nakeba saida na k'ara maimaitawa sannan yace "yawwa" kawai fara had'a wa sweety nai sannan na D'an d'ibi chiefs da ruwan tea rabin cup , shuru wajan sai k'aran cokula kawai kakeji, sweety jin shurun yai yawa tace "Aunty nah wlh kunna na fa ya fara motsi,wannan girkin ai sai kisa mutum ya fad'o akan kujera".
Cikin hararan wasa nace " hhhhmmmm tsokana ko".

"Da gaske ba tsokana ba girkin yazo da wani salo fa ". Mirmishi kawai nai don Duk a takure nake, zata k'ara yin magana yace " kai sis mana kin cikawa mutane kunne,kinsan dai ban son ina cin abinci ana surutu ko,son a tofe abinci da yawu kawai ". Dariya tai tace " na manta amin afuwa big broth ".
Daga nan bata k'ara magana ba,ni na fara tashi na komai parlour na zauna ,bayan y'an mintuna ta biyo bayana, shi kuwa k'arawa ma yai yaci gaba daci, araina nake mamakin wane Irin cine dashi haka tun kafin mu faraci yake ci har min gama yana aikawa".
Kamar sweety tasan tunanin da nake cikin raina naji ta matso kusa dani tana min rad'a " Aunty na saifa kinyi da gaske don wlh mijinki babban container ne dashi a cikinsa mugun ci gareshi baya wasa da nik'a".

Mirmishi nai a hankali nace " hhhmmm ba ruwana in yajiki"

Dariya tai tace "to shike nan tunda bakya so na rink'a baki sirrin. . .".
K'arar wayarta ce ta katse abinda zatace ta d'aga tana fad'in " ok gani nan zuwa".
Mik'ewa tai tace " Aunty na bari inje ana nemana Kinga muna da sauran bak'i amma in duk suka tafi zan dawo anjima".
Kai kawai na d'aga mata,
Tana fita na tashi na shige d'aki na cire hijab d'in jikina ina kwanciya kan gado, wayata na d'auka na kira number din Aunty Hafsa bugu biyu ta d'auka tana fad'in "Amarya yanzu nake zacenki ai "
Cikin muryan kamar zanyi kuka nace "Um um Aunty kin manta dani dai".
Dariya tace " Haba wa zai manta da y'ar sa,koda biki kirani ba anjima zan kiraki, ya gidan ya bakunta".
Nan muka gaisa ina tambayarta yaya tace yana waje , nace su umma fa tace duk gasu nan,Basu wayar tai muka rink'a gaisawa dasu nace ta bawa su Aunty juwairiyyya, tana karb'a nace "Aunty wai bazakuzo ba har yanzu " dariya tai tace mu kan Bazamuzo ba amma da ga y'an matan nan suna shiryawa duk zasuzo"
"Yawwa Aunty don Allah kice suzo yanzu fa".
Nan mukai sallama na kashe wayan ina murna yanzu zan rabu da zaman kad'aici.









Taku ce
y'ar mutan ja'oji๐Ÿ™‹โ€โ™€
https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation?


๐Ÿก๐Ÿก๐Ÿก ๐ŸŒธ๐ŸŒธ๐ŸŒธ๐ŸŒธ
๐ŸŒธ *Y'AN ARABIC* ๐ŸŒธ


NA

LAYUZA KABIR ADAM

DEDECATED TO ALL
ARABIC /ISLAMIC STUDENTS
๐Ÿ“š๐Ÿ“š๐Ÿ“š๐Ÿ“š๐Ÿ“š๐Ÿ“š๐Ÿ“š๐Ÿ“š

๐Ÿ‘จ๐Ÿปโ€๐Ÿ’ป๐Ÿ‘ฉ๐Ÿปโ€๐Ÿ’ป
*ZAMANI WRITERS ASSOCIOTION*

๐Ÿ“
โ€‹โ€‹Wษ› ษ‘ส€ษ› ษฆษ›ส€ษ› tัณ ษ›ษ—ucษ‘tษ›, Mัณtiัตษ‘tษ› ษ‘ษณษ— ษ›ษณtษ›ส€tษ‘iษณ ัณuส€ ส€ษ›ษ‘ษ—ษ›ส€เธฃโ€‹



ุฃุนูˆุฐ ุจุงุงู„ู„ู‡ ุงู„ุณู…ูŠุน ุงู„ุนู„ูŠู…ุŒ ู…ู† ุงู„ุดูŠุทุงู† ุงู„ุฑุฌูŠู….



0โƒฃ2โƒฃ8โƒฃ

K'arfe d'aya ina kan prayer mat na idar da sallar ina addu'a naji ana knocking door mik'ewa nai naje don bud'ewa hayaniyar da naji na tabbatar y'an gidanmu ne,da sauri na bud'e ina murna,cikin farin ciki na rungumesu muka k'araso cikin parlourn, bayan mun gaisa bajewa mukai muka shiga hira ana shafta Azeeza tace " Ke ina fatan kin d'ora mana watu don bamuci na rana ba muka taho"
Dariya nai nace "he lalle ma ni zan muku girki wlh tashi Ku shiga kitchen d'in da kanku Ku girka abinda kuke so don a gajiye nake matuk'a" Zainab ce ta kalleni wai "lalle ansha amarci dole a kasa girki amma ai kinwa mijinki yaci" "ah donme bazanwaciki ina ba yaci kune dai bazan muku ba".

Mik'ewa sukai zuwa kitchen suna nemawa Kansu abinda zasu girka, nida Asma'u da Zainab suka barmu zaune,muna hira Asma'u tace " wlh Nahna bikiga yanda kikayi kyau ba, kin dace da gidan sosai ".
Mirmishi kawai nai Zainab ta d'ora " To mamana ta shigo sahun mu y'arki ta rigaki sanin dad'in aure".
Dungureta nai nace " Y'ar duniya Ke kikasan wani dad'in aure ni ba ruwana ". Hira muke sosai suna k'ara fad'a min yanayin zaman aure kasancewar su sunyi sun san yanda zaman yake, sosai na bud'e kunne ina k'ara kwasar dabarun zama da miji, kusan awa da rabi suka gama girkin shinkafa da miyar kaji sukai da couslow, bayan sun gama naje na d'auki wasu sabbin cooler na zuba mai abincin, ina fitowa daga kitchen d'in shi kuma yana fitowa daga d'akinsa,kallo d'aya nai mai nasan bacci yasha,don da alama ma alwala yayo zaiyi sallah gaisheshi sukai ya amsa ba yabo ba fallasa, ya fice , d'aya palourn naje na shirya mai abincin sannan na dawo muka fara cin abincin, bayan mun gama muka gyara gidan tare da kitchen din, nan muka k'ara bud'e shafin hira tunda daman suma sunyi sallar azahar d'in su, sai da akayi la'asar sannan muka tashi don gabatar da sallah daga nan kuma suka fara shirin komawa gida number d'in sweety na kira nace tazo suyi sallama dasu azeeza mutuniyarta,nan tazo suka gaisa tace bari taiwa driver magana ya fito da mota ya maidasu, tana fita na bud'e musu duk akwatinan lefe na nace su zab'i Duk abinda suke so,ganin sun tsaya filako,yasa na shiga fitar musu da kaina kayan kwalliya ko wacce na cika mata Leda dasu underwears,saida sukace ya isa , sweety ce ta shigo tana cewa su fito driver ya fitar da mota, haka na rakasu suka tafi duk jikina ba dad'i don Gobe zasu wuce nasan ni damu k'ara had'u wa kuma wata hidimar ta taso a sakkwaton, bayan na koma k'ara gyara gidan nai nasa mai turare,sannan na shiga wanka ,bayan na fito na shirya cikin wata doguwar riga kalar popul me jikin roba duk jikinta stones ne nasa d'an k'aramin mayafi kalanta nai rolling,lokacin k'arfe biyar da rabi ina fitowa na ganshi ya fito daga k'aramin parlourn kaina a k'asa nace "sannu da zuwa" bai kalli inda nake ba yace " wa kika ajiyewa wancan abincin sauran mutane,ko ance miki ina cin abincin da mutane da yawa sukayi shi,niba k'azami bane don haka kije ki fiddashi cikin parlourn ".

Wani bak'in ciki naji ya turnik'eni amma saina hadiye na wuce, fito da cooler d'in nayi na fara k'ok'arin d'ora mai wani abin,Abu mai sauk'i nake son girka mai amma ina tunanin maganar sweety ta d'azu da take cewa cine dashi sosai baya wasa da cikinsa,don haka na duba cikin kayan abincin namu naga akwai garin doya don haka nan da nan na d'ora ruwan zafi kafin meye ya tafasa nan da nan na tuka sakwara na kira sweety a waya nace don Allah ina zan sami farar Leda zan kwashe sakwara tace bari ta kawomin, D'an lokaci Sai gata da ita tace," na fad'awa Aunty ma yanzu babu Leda a part d'inku gashi can ta bawa driver ya siyo muku".
Karb'a nai na fara bud'e ta ina cewa "don Allah ya za'ayi da abincin nan Kinga baici ba Kar abarshi ya lalace"

" OK kawo in kaiwa ma'aikatan nan zasu ci "

Tana fita na kwashe sakwaran a Leda na jera cikin wasu warmares d'in masu d'aukan hankali don ba k'arya an zubamin foodflast da yawa kuma masu matuk'ar kyau, miyan agushi na shirya lafiyayyiya da taji naman kan rago,naso in had'a lemo amma lokaci ya tafi don har an fara salla a masallatai, Nima da azama na juye miyan na had'a zuwa dining area, da sauri sauri na shige toilet na d'auro alwala, na tada sallah, ina idarwa naji shigowansa don haka ban tsaya doguwar addu'a ba na shafa na fita,amma saina tadda baya parlor d'in don haka na koma na k'ara gyara wa na feshe jikina da turare na k'ara shafa powder da lipstick, na fito yanzuma baya nan kitchen na wuce na wanke tukwanan da y'an kwanikan dana b'ata, ina goge hannuna da kitchen towel naji maganarsa a bayana "Ke haka ake ajiyewa mutum abinci ba serving spon koda hannunki zan d'ibi miyan"
Dafe kai nayi don gaba d'aya sauri saurin da nake yasa na sha'afa bansa serving spoon d'in ba, amma saina nace "kayi hak'uri don Allah wlh na sha'afa ne" tsaki kawai yaja ya fita a kitchen d'in a ransa yana k'unk'uni shi rabon ma daya shiga kitchen harya manta don komai yimai ake,amma daga yin aure jiya shine har yau ya fara shiga wai kuma a haka ake cemai komai nashi zai canja tunda yai aure wai zai sami kulawar dabai tab'a samu ba mutttsss yaja dogon tsaki yana zama kan kujerun da sukai wa dining d'in k'awanya".

A hankali na k'araso inda yake na fara zuba mai abincin Wanda k'amshi ya gama cika gidan tako ina, wani yawu ya had'iya nan da nan yaji yunwar da yakeji ta k'aru, don haka ina gama ziba mai yaja flat d'in ya fara ci,mik'ewa nai zan bar wajan yace "Ke dawo ki zauna,

Ba musu na dawo na zauna kaina a k'asa ina jinsa yanata loma abinsa, wayata dake aje gefen kujera ce taketa k'ara amma banko yi alamar tashi in d'auko ba saida yace "Ke wai bake ake kiraba kika barwa mutane abu na cika musu kune"

A sannu na tashi na d'auko wayar na dawo mazaunina, zuwa lokacin ma har wayar ta katse number d'in Aminyata Hafsah ne da sauri nabi kiran tana shiga ta d'auka da sallama muka gaisa kamar yanda yake mafi yawan lokaci in nida ita ne ko a zahiri ko waya bamu fiye yin magana da Hausa ba don haka yanzuma cikin harshen larabci muke magana tanata tsokanata, mun kai minti hud'u sannan mukai sallama, ina kashe wayan naji ya saki wani mugun tsaki,da sauri na d'ago na kalleshi naga ya k'ara tsare gira don haka na maida kaina ga wayata na nemo number d'in sweety tana d'auka nace "kizo muci abinci mana "
Dariya tai tana fad'in "wane ni nazo cin abinci da daddare oga na kusa kedai kuci kawai ki kulamin da cikin d'an uwana".
Kwafa nai nace " wato ni ba y'ar uwakki bace ko na gode"
"A'a wlh ba haka nake nufi ba Aunty nah ki gane kawai ai yanzu banda sama dake sorry kinji".
" To indai kina son in hak'ura kizo muci abinci tunda ai nasan yanda kike son sakwara ".
" hhhmmmm kin san me na gaji sosai ban son tashi Amma zan turo yanzu a karb'amin".
Lokaci kad'an d'aya daga cikin y'an Aikin gidan tazo ta amsa Mata abincin, a lokacin ne shima ya gama ci na kwashe kwanikan zuwa kitchen don ni kam bazanci ba sai nayi sallar isha'i,ina fitowa zan wuce d'aki naji kiransa a bayana,"Ke zo nan"
Dawo wa nai Nazo na zauna k'asan kafet dake malale tsakiyan kujerun wanda shi yake zaune saman kujeran, nakai wani lokaci a zaune kafin ya d'ago kansa ya kalleni lokaci d'aya ya kauda kan nasa sannan ya fara magana "ina son in sanar dake duk wasu dokoki na, da farko ki sani niba k'azami bane banson k'azanta ko kad'an, sannan ba abincin kowa nakeci ba ni karma kiyi bak'i suyi girki kice zaki ajiyemin bana buk'ata in kuwa kikai hakan zan gane kuma zan d'au mataki,Abu ba gaba indai kika kawo min abinci bazaki tashi ba saina gama ci tsaf na tashi sabida bazai yuyu ki ajiyemin abinci ki tafi ba kuma nazo buk'atar k'arawa ko wani Abu kuma saina kiraki ba,d'akina ina buk'ar a rink'a gyaramin shi sau biyu a rana da safe da yamma, duka k'anan kayan da nake amfani dasu Ke zaki rink'a wankewa sabida kowa na fad'a min nai aure zan huta don haka dole in huta Duk da banga wani abin hutawa cikin auran ba, nayi niyar gasa miki aya a hannun na shishahigin da kikaiwa rayuwata da rashin kunyar da kika dad'e kinamin a school yanzu anzo inda zan rama kin kawo kanki da kanki,amma sakamakon diddani kunya da kikai gun friend d'ina a events duka zan miki sassauci akan abinda na tsara a kanki,karki Bari na kamaki da wani kuskure cikin umarni na"

Cikin sanyin miryata nace "Insha Allah zan kiyaye "
" Jeki " kawai ya fad'a yana kauda kansa gefe ,
Mik'ewa nai na wuce ina fad'in "Saida safe "
Bai amsa ba sai juyowa da yai yabi bayana da kallo har nashige d'aki,
Ajiyar zuciya ya sauke bayan wucewata yana sak'e sak'e a ransa" To wai meyasa ma nake son sassautawa yarinyar nan inda naci burin azabtar da ita amma me yasa zuciyata Ke tankwasani kan na kyaleta? Tsaki yaja ya tashi ya shige d'akinsa ina sak'awa da warwarewa.

Ni kuwa ina shiga d'aki salla na fara k'ok'arin yi
wadda naji har an fara kira a masallatai.

*********
A can gidanmu kuwa washe gari duk yan garinmu suka tafi,amma banda mama na da umma da yayyyena mata guda biyu,sabida basuzo sunga d'akina ba,don haka da dare yaya Haroon ya kawosu ai kuwa murna kamar zan tashi Sama bayan na cika musu gabansu da lemuka nazo na zauna tsakiyansu inata fara'a da murna , nan yaya Ya k'aramin nasiha haka ma su mama suka k'aramin nasiha da hak'uri akan zaman aure, nidai sauraransu nake ina mamakin kowa dai nasiha da ban hak'uri basu son yanzu ni banjin wata damuwa ko d'aya kan wannan auran ba don addu'ar da nakeyi da rok'on Allah ya ansamin ya samin sassauci sa nutsuwa sosai a cikin zuciya ta,

Yaya ne yace inwa su umma rakiya gun Aunty murjah da Abbah su gaisa, d'aki naje na d'auko hijab d'ina muka tafi.

Sosai suka sami tara daga Aunty murjah da Abbah cikin mutunci da girmamawa suka gaisa jin yaya Haroon na waje yasa aka kirashi ya shigo ciki shima suka gaisa Abbah ba ruwanshi a waye yake abinsa don haka baya surukuta ya saki jiki yaketa hira yana k'ara yi musu godiya,kallona yai yace "Khadeejah sun gaisa da Mijin naki kuwa ?".
Cikin jin kunya nace " a'a Abbah da suka zo ya fita amma yanzu ban sani ba koya shigo".

"To maza jeki duba inya dawo ki kirashi su gaisa ai ba dad'i suzo basu gaisa ba kuma".

Mik'ewa nai zuwa part d'in namu ai kuwa ina shiga na ganshi tsaye yana kunna T.V matsowa nai kusa dashi nai k'asa da murya " Abbah yace kazo parlourn sa zaku gaisa dasu maman mu ".
" OK " kawai yace na juya kafin na fita part d'in harya biyo bayana kusan atare muka shiga,Abinda ba halinsa ba wai jin kunyar wani mutum amma yau sai ya tsinci kansa da kunyar su Umma don haka ya sunkuyar da kai k'asa yana gaishesu amsawa sukai cikin girma,wanda hakan ya faranta ran Abbah matuk'a. Nan dinma dai had'a mu akai aka k'ara mana fad'a kan rayuwar aure,sannan sukai musu sallama Abbah ya bawa Aunty murjah kud'i masu yawan gaske ta basu,sukak'i k'arb'a Sam saida taita musu magiya sannan suka karb'a tare da godiya na rakosu bakin motarsu muna sallama nan wani hawaye ya b'allemin harda shashshek'an kuka sweety ce ta rik'oni tana ban hak'uri suka tafi.

Haka ta rakoni part d'in tanata rarrashina a haka ya shigo ya samemu ta gefen ido ya kalleni ya kauda kai gefe har zai shige d'akinsa sai ya tsaya yana cewa"kukan fa ?".
Sweety ce tace "Wai don su maman su sun tafi gobe zasu wuce sakkwato".
" shine abin kuka, jeki zamu rufe k'ofar"

Mik'ewa tai tana cemin "saida safe Aunty na".
Tana fita ya bita ya rufe k'ofar sannan ya kashe kayan kallon ya wucewarsa d'akinsa bai k'ara tanka min ba, ganin zaman bazaiminba yasa na kashe Haske na shige Nima d'akina na sa kayan bacci na kwanta.



*******
Haka rayuwar tamu ta kasance zaman kadaran kada han har tsawon kwana bakwai kullum zan gyara mai d'akinsa safe da yamma sannan koda yaushe innai girki in zaici saina zauna ya gama ci zan bar wajan, yau ya kama lahadi kuma ina son gobe Monday in koma school don lectures da yawa sun wuceni,don haka bayan na gama had'a abin breakfast na gyara ko ina nai wanka na shirya cikin wasu riga da siket y'an kanti masu laushi wanda suka kama jikina matuk'a na gyara gashina nasa mai ribbon kalan kayan ja sannan na d'auko flat takalmi shima ja nasa bansa dogon d'an kunneba sai barima dana mak'alawa kunnan bak'a, na feshe jikina da turare me sanyin k'amshi, fitowa nai zuwa d'akinsa nai knocking saida yaban izinin shiga,na tura k'ofan na shiga tsaye yake dagashi sai d'an k'aramin towel d'aure a kugunsa, da sauri na kauda idona daga kallon sa ina fad'in "Ina kwana"
" lafiya qlau"
Bayan haka duka mukai shuru can nace "um daman zan gyara d'akin ne nai tunanin ko ka shirya ne".


Please Login or Register in order to submit comment