Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Ihu da tafin daya cika wajan ne ya dawo dashi tunanin daya shiga ai kuwa yaji wata bala'in kunya ta kamashi amma duniyanci Irin nasa da nuna shi wayayyene yasa kawai ya bud'e babbar rigarsa ya sakani a ciki tare da hugging d'ina yana dariya, nan duk friends d'insa na gida Dana k'etare sukayo kanmu da sabon lik'i suna b'arin manyan kud'i don nuna kara ga abokin nasu, ganin yanda mazan suka kewaye mu naji wani sabon fargaba da ta k'ara lullub'eni ai kuwa ban san sanda na kifa kaina bisa k'irjinsa ba tare da kewaye hannuwana jikinsa,wani k'ara rungumeni yai yana shafa bayana tare da kashe wa abokansa ido cikin shak'iyanci ai kuwa waje ya k'ara rud'ewa da ihu m.c ya samu abinyi fad'a yake yana k'ara fad'a"gaskiya wad'annan ma'aurata sun dace da juna Allah ya kawo zuri'a ta gari Allah yasa wata Tara masu zuwa muzo shagalin suna". Masu video fa hotuna suka shiga aikinsu na d'auke d'auke.

Mun d'au tsawon lokaci sannan m.c ya bamu damar zuwa mu zauna nan ya ruk'o hannu na muka tafi gun zamanmu muka zauna a high table,anan na k'are mai kallo shima kayansa kalan nawa ne light blue shadda d'inkin babbar riga da y'ar ciki babbar rigar irinta samarin Zamani y'ar k'arama dai dai jikinsa, idonsa sanye da farin glass kamar yanda ala'adarsa take,sai wata hula zanna me tsadar gaske da akewa lak'abi da minister kalan kayan nashi, hannunsa sanye da agogon vansar chairman world, sai k'afarsa sanye da bak'in takalmi south, duk a cikin abunda bai kai minti d'aya ba nai mai wannan kallon.

Nan akaci gaba da gudanar da event d'in cikin aji da nishad'i,zuwa d'an lokaci aka fara raba abinci ganin duk hankalin jama'a ya bar Kansu yasa ya sunkoyo sosai yana min magana cikin kune "Hhhhmmmm yarinya taga faffad'an k'irji shine harda wani lafewa a ciki to k'walelanki wannan k'irjin na matar zab'in raina ce ba matar tushe ba ".

Ganin masu Neman abinyi sun fara d'aukanmu a hoto yasa ya janye jikinsa yana wani mirmishi, Wanda nima mirmishin ne d'auke a fuskata wanda ban san name ne ba.

Sai misalin k'arfe sha d'aya aka tashi, yanzuma motar Abdushshakur muka hau Hafsah a gaba kamar yanda muka zo,
Bayan sun ajiye mu k'ofar gida ina shirin fita a motar ya rik'o hannuna yana magana k'asa k'asa " yau kin fidda kanki kunya sai kuma Sunday shima kiyi k'ok'ari kinji ko".

Ganin Abdushshakur na kallonmu yasa na gyd'a mai cike da gajiya wanda zakai tunanin shagwab'a ce.


Koda na shiga cikin gida tsokana ta akai tayi wai mun kasa hak'ura zuwa jibi gaban jama'a muke rungume juna, mirmishi kawai nakeyi ba tare dana tankawa kowa ba.

Washe gari asabar akai culture day tun k'arfe biyu ake gudanar da wasannin gargajiya da al'adu a filin wasa na Ahmad Musa sannan zuwa k'arfe hud'u aka wuce lunch sai bayan sallar magriba aka dawo.

Yau lahadi kuma akeyin Mothers day yau kam mu ba fita zamuyi ba a gida muke yinin mu inda muka yini masu kid'an k'warya suna cashewa, tunda naga anyi sallar la'asar fa jikina ya fara mutuwa naji zuciyata ta narke duk y'ar walwalar dake tare dani ta kau na koma jugum,

Ina jin kiran sweety a waya kuwa tana fad'awa Aziza ta fad'a a cikin gida ana sallar magriba fa za'azo d'aukan amarya nan jikina ya k'ara sanyi hawaye suka fara bin kuncina duk k'awayena ma sai jikin su ya mutu da sauran y'an matan, kayan takaici da rawar kai Irin na abokan UK wai tun kafin akira magriba suka fara zuwa d'aukan amarya ance sunzo da wuri wai sai ca sukai eh duk nuk'u nuk'u da fad'an da za'a yiwa amarya ayi mata kafin suyi salla su fito don ana idar da sallah zasu d'au amarya.
Nan fa na rikice da kuka wiwi na k'udundune cikin d'akin Aunty Hafsah ina matsanancin kuka me shiga rai, Iyayena suna zaune tare dani suna k'ara min nasiha kan hak'uri hak'uri dai nikam kuka kawai nake Aunty Hafsah ta shigo d'akin tana fad'in "Nahna tashi kiyi wanka kiyi salla Kinga an fara kiranvsallar".
Mik'ewa nai cikin jan hanci na shiga toilet wanda daman an gama had'amin ruwan wankan,ina wankan ina kuka saida naji ana min magana in fito haka na hak'ura na fito tare da d'auro alwala, ina sallar ma ina kuka haka naita addu'a a sujjadata ta k'arshe ina rok'on Allah yasa min albarka a cikin rayuwar aurena,
Ban wani sa komai ba humra kawai na goga a jikina nasa kaya aka fito dani ina fitowa Yaya Haroon na shigowa ya koro yara da suke bin motocin da suka d'auki y'an kai amaryar, fad'awa nai jikinsa ina kuka ya rungumoni yana bubbuga bayana shima duk zuciyarsa ta karye, cikin sanyin jiki yace " Kiyi shuru Autah kinji ki daina kuka haka Allah yai miki albarka Allah ya baki zuri'a me albarka Allah yasa farin ciki cikin rayuwar ki ".

Muryarsa ce ta fara rawa don haka yai shuru tare da jawoni zuwa waje da kansa ya sakani cikin motar yana shirin juyawa na ruk'o hannunsa ina fad'in " Yaya na ka yafemin ja yafemin don Allah ".
Janye hannunsa yai cikin nawa yana shafa kaina tare da d'an mirmishin yak'e ya juya da sauri jin idonsa ya ciko da k'walla".

Duk wanda ke wajan saida ransa ya sosu haka umma maman su yaya Haroon ta shigo ta zauna gefena yayin da k'anwar mama ba na ta zauna d'aya b'angaren Hafsa Aminiyata kuma ta shiga gaban motar aka cilla damu,shike nan na bar gidanmu wayyo Allah na.

Muna sauka a mota na shak'i k'amshin iskar gidansu sweety naji wani fad'uwar gaba,yanzu shikenan nan ne fa gidanmu, cikin kunnena Umma tace " maza yita addu'a kinji Khadijah Ke malama ce yi addu'a ki shiga da bisimillah kinji".

Cikin raina naita addu'oi ina neman tsari da dukkan fitinar da take gidan tare da neman Alkairan gidan tare dani, bisa al'ada cikin gidan aka shigar dani wajan iyayensa, parlourn cike yake da manyan mata masu aji da izza kallo d'aya zaka musu kasan ko wanne yana ji da kansa a nera, bayan gaisuwa ga juna umna ta fara mik'a amanata garesu " To Y'an uwa ga Nahna Khadijah nan mun kawo muku ita ta zama y'ar ku,Khadijah dai duk wanda yasanta yarinya ce bame fitina bace ko cikin y'an uwanta halayyarta daban take,amma yanayin rayuwa koda zaku ga wani abin k'i daga gareta Ku mata fad'a Ku nusar da ita tunda yarinya ce k'arama, mun baku Khadijah bisa amana kamar yanda muke kyautata zaton zata sami Duk wani kula daga gareku kamar tana tare damu".

Wata mata ce cikin isa da nuna ita wata ce ta fara magana" OK duk munji baya nanki kuma muna fatan Allah ya bamu ikon rik'onta ,amma dai Ku cigaba da yiimata fad'a don kun san rayuwar ta data Daddy ba d'aya bane ,maybe zai iya yin wani Abu taga kamar yai mata ba dai daiba so dole tayi hak'uri dashi tunda tsarin rayuwar sa duk cikin manya yayi ta,to Allah ya tsara madai itace matar sa amma mun so k'warya tabi k'warya. .
Da sauri wata matar ta katseta da fad'in "Haba Aunty iyami wannan ba girmanki bane meya kawo kad'an nan maganganun haba bai dace ba wlh,gaskiya biki kyauta ba ai yanzu Duk mun zama d'aya tsakaninmu dasu Khadijah tunda aure ya shiga tsakani".
Kafin itama ta k'arasa abinda zata ce Aunty murjah ta fito tana fad'in " Ku shigo da ita Abbansu yace a k'araso mai da ita su gaisa".
Son jin gulma dame za'a fad'a yasa Aunty iyami mik'ewa ita da wata magulmarciyar irinta suka bi bayanmu zuwa b'angaran Abbah wanda zuwa lokacin Duk raina ya gama b'aci matuk'a da maganar Aunty iyami ta k'arshe don haka na rik'e sunanta tsam cikin raina don nasan zaman da zanyi da ita.

A gun Abbah kuwa tarb'a muka samu sosai don da fara'arsa ya taremu yana cewa kowa ya zauna akan kujera ganin su umma na zama a k'asa,nikam a k'asan na zauna ina k'ara duk'un k'une kaina, "zo matso kusa dani Khadijah karki zauna a can "

A hankali na tashi na k'arasa gabansa na zube ina gaisheshi cikin muryar kuka,dafa kaina yayi yana cewa "Yi shuru bar kunan haka y'ata y'ar albarka ban son ganin hawayenki".

Gaisawa sukai dasu Umma yanata tambayarsu ya taro ya hidima , su kuwa cikin jin dadin irin karbar daya musu suke amsawa, nan ya shiga musu godiya sosai ya k'aramin nasiha sosai " Khadijah kiyi hak'uri da dabiun Daddy kinji Nasan Ke yarinya ce kamilalliya me ilimi don haka naita addu'a ina kwadayin Allah yasa ki zama abokiyar zamansa don nasan zanyi alfaharin auranki da Daddy,dukkan y'an matan dake rubibin sonsa nasan suk shirme ne ba wacce take sonsa domin Allah, amma ke kuwa nasan zaki zauna dashi cikin ta ilimi zaki rink'a nusar dashi abubuwa da yawa kiyi hak'uri kinji Khadijah ".

Wani bak'in ciki ne ya turnuk'e su Aunty iyami da jin kalamansa don sun san gugar zana yake musu suda y'ay'ansu da suke kwad'ayin auran UK,

Mun jima zaune Abbah nata Nasiha daga bisani ya zaro key d'in mota ya mik'awa Aunty Murjah yace " murjah ga kyautar y'arki nan dana tanadar mata duk randa aka kawo ta gidan sabida zuwa school ".

Cikin fara'a Aunty murjah tace to Abbansu Khadijah ta gode kuma muma mun tayata godiya Allah ya k'ara bud'i".

Su Umma ma Godiya sukaita yi suna jinjina k'aunar da nasan Allah nan kemin tare da karamcinsa gareni".

Haka muka baro gun Abbah zuwa part d'ina muka bar masu bak'in ciki natayin k'us ,

Zuwa minti talatin duk manya y'an kawo amarya sun watse sai y'an mata kawai da za'a fita friends night dasu, sweety ce ta shigo parlourn tana zuwa tazo kusa dani tare da rank'afawa ta lek'o fuskana tana d'an mirmishi tace "Shike nan Aunty nah ta dawo gidanmu ta zama y'ar gidanmu har abada".
Hararanta nai ina kauda kaina gefe,
Matar dake bayan ta ce ta ajiye d'an akwatin kit d'in dake hannunta tana cewa" Ruk'ayya a fara kwalliyar nan yanzu don lokaci na tafiya".

Sweety tace "Aunty nah game kwalliya tazo zata miki Kinga 9 za'a tafi gashi 7:30 yanzu".

D'aki muka shiga na na sake d'auro alwala don nafiso ana gama min na nai sallah kafin mu tafi,araina inata bak'in cikin ace wai sabida boko da wayewa dataiwa mutane yawa daren da aka kawo amarya d'akin ta kuma ace wai a k'ara fita wani fatin na daban,

Yau d'in ma kwalliya sosai akai min bayan an gama kafin nasa kaya nai sallar isha'i don zuwa lokacin an dad'e ma da yin sallar duk y'an Matan ma sun k'ara shiryawa, yau farin gown d'in nasa asalin bride gown na y'an k'asar India itama ta amsheni sosai kaina ba gwaggaro bane yau mayafin rigar aka samin saman kai yayin da akamin gyaran gashi Irin ba y'an India sai wani ribbon da aka samin a gaban gashi kamar Irin na sarauta,yau fuskata a waje take,hannayena duka cike da awarwaraye Irin dai yanda y'an India keyi kallo d'aya zaka min kasan tsaf kwalliyar amaren India akaimin don har wannan d'an abin da suke sawa a goshinsu kamar d'an kunne aka samin,

Ihu parlourn ya d'auka lokacin da na fito daga d'akin kowa fad'i yake har nafi ranar dinner kyau.




Taku ce
Y'ar mutan ja'oji πŸ™‹β€β™€
https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation?


🍑🍑🍑🍑🍑🍑🍑🍑
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
🌸 *Y'AN ARABIC* 🌸


NA

LAYUZA KABIR ADAM

DEDECATED TO ALL
ARABIC /ISLAMIC STUDENTS
πŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“š

πŸ‘¨πŸ»β€πŸ’»πŸ‘©πŸ»β€πŸ’»
*ZAMANI WRITERS ASSOCIOTION*

πŸ“
​​WΙ› Ι‘Κ€Ι› Ι¦Ι›Κ€Ι› tΡ³ Ι›Ι—ucΙ‘tΙ›, MΡ³tiΡ΅Ι‘tΙ› Ι‘Ι³Ι— Ι›Ι³tΙ›Κ€tΙ‘iΙ³ Ρ³uΚ€ ʀɛɑɗɛʀร​​


ALLAH KAI MANA MAGANIN ABINDA YAKE DAMUN MU ALLAH KA SHIGA CIKIN LAMARINMUπŸ‘



0⃣2⃣7⃣




Ina tsaye duk kunya ma ta baibayeni na rasa me zance musu da shakiyancin da suke tamin, sweety ta shigo cikin shirinta tsaf tana fad'in " yawwa to duk kowa ya fito ya motoci na jiranmu mu wuce".

Fita suka farayi d'aya bayan d'aya ina tsaye ta k'ara so gareni tana rik'e hannuna tace "amarya Kyan da kikai yau ya zarce na kullum,ki jira angonki yanzu da kansa zai shigo Ku tafi".

Ta k'arashe maganar tana mirmishin tsokana, jin takun takalmansa mukai yana shigowa parlourn a tsakiya yaja ya tsaya hard'e da hannayensa a k'irji cikin shigar suite farare k'al har takalman dake k'afansa farare ne haka ma fatan tsadaddan ogogon dake hannunsa, sai gashin kansa bak'ik'irin kwance luf luf kana kallon sa zaka gano tsantsan kyan da yayi, cike da nuna isa yacewa sweety" jeki ku jiramu gamu nan fitowa ".

Tana fita ya k'ara taku biyu zuwa uku yaja ya tsaya yana fad'in "ki kula sosai yauma karkiyi abinda zaki bani kunya kinji ko".

Kai kawai na gyad'a mai ba tare dana d'ago ba, shima kauda kai yai daga kallo na ya juya zuwa k'ofa yana fad'in "zo mu tafi"

A hankali na taka nabi bayan sa har zuwa k'ofar fita daga part d'in sannan ya dakata ya tsaya har ba k'ara so kusa dashi yasa hannunshi ya ruk'o nawa k'am a haka muka k'arasa fita inda muka tarar da motar da zamu tafi a cikin ta sauran motocin kuwa duk sunyi layi daga cikin gate d'in har zuwa waje,da sauri d'aya cikin abokansa ya bud'e mana k'ofar muka shiga sannan yaja muka shiga cikin rukunan moticin ,
Tunda muka shiga bai tanka minba saima d'auko wayansa da yayi yana danne dannansa a ciki, ni kuwa kaina yana k'asa ina wasa da yatsun hannu wana,a haka muka k'arasa gun motocin duk suka tsaya saida aka sanar sa m.c zuwanmu sannan muka fito yasa hannunsa ya rab'oni jikinsa yayin sa sauran abokansa kowanne ya tsaya tare da mace d'aya muka jera a haka har zuwa cikin Hall d'in yayin da wani kid'a me taushi yake tashi haka sukai mana rakiya har zuwa mazaunin mu, bayan y'an matan sun gama cashewa a fili aka basu damar komawa mazauninsu, nan aka cigaba da gudanar da program d'in cikin wayewa irinta rik'akkun y'an boko, dama m.c din ya bawa ango da amarya su fito filin rawa su nuna farin cikin su, a nutse muka sakko filin yayin daya nanuk'eni gefen kafad'arsa,wak'a me tsuma rai aka sakar mana ta turanci me d'auke da dadad'an kalaman soyayya ga kid'inta me taushi, duk yanda m.c d'in ya dage kan na rausaya na kasa shi kuwa gogan rausayarwa sa yake cike da iya wa, ganin ina neman kwafsa mai nak'iyin rawar yasa ya rik'o kuguna da hannayensa biyu yana juyi dani kamar y'ar baby, tafi abokansa Ke masa ganin yanda ya wani basar yana jujjuyani a jikinsa, sosai kunya ta lullub'eni k'asa nai da kaina inajin wani fad'awar gaba, lik'i ne ta ko ina ya b'arke a wajan jinai an farke min rafar kud'i akaina kamar ba'a sonsu,a hankali na d'ago ido don gani wace wannan wadda batayiwa angon sai ni kad'ai shima dai dai lokacin yakai kallonsa gareta yanda naga suk sunyi shock a lokaci guda yasa na k'ara kallonsu sosai a hankali naji yace "tnx fadlah " mirmishi kawai tai ta basar tare da juyawa ta bar wajan, binta yai da kallo yana mamakin yanda tazo wajan don bayyi zato ba ko kad'an wai fadlah zata zo kano bikinsa,ganin kallon da yake mata yasa na juya zan koma mazaunina da sauri ya ruk'oni muka jera zuwa mazaunin namu,bayan anyi ciye ciye akaci gaba da cashiya inda abokansa suke ta rawa suna ihu irin na wayayyun samari y'an boko, gab da za'a tashi aka buk'aci mu fito mu yanka cake, k'awataccen cake ne me d'auke da sunayanmu nida shi, hannuna da nasa ya had'a bayan sun kirga 3 muka yanka nan akaita yi mana tafi m.c yace amarya ta yanka ta bawa angon ta a baki,tab d'in babbar magana kenan nanfa k'irjina ya fara lugude ina jin kamar bazan iyaba,amma dana tuna warning d'insa akaina na kada in kuskura in bashi kunya sai na tattaro nutsuwa na daidaita kaina,a hankali na yanko cake d'in nakai bakinsa ai kuwa caraf ya had'a tare da hannun nawa yasa abakinsa yana tsotsa nan da nan hannun nawa ya fara rawa, saida ya had'iye cake d'in sannan shima aka bashi damar ya yanko ya bani,kai rashin kunya tanaga namiji wai daya yanko cake d'in sai yasa a bakinsa ya rik'e da hak'orinsa sannan ya kamo fuskata zuwa tashi fuskar yana kai bakinsa ga nawa da ido yaimin alama dana bud'e bakina,runtse idona nai ina d'an bud'e bakin nawa turamin cake d'in yai cikin bakina yana hade baku nan namu waje guda, innalillahi kawai nake furtawa cikin raina jikina yana rawa, da k'yar na hadiye cake d'in kwalla tana taruwa a idona ta b'acin ran rashin kunyar da yake tsulawa a gun yana sani jin kamar k'asa ta tsage in shige,
Zuwa lokacin ihu ya gama karad'e Hall d'in gaba d'aya tafi kawai Ke tashi da ihun mutane,su anasu ganin ya gama wayewa k'arshe wannan abin da yakeyi, wanda ni kuwa anawa sashin nake ganin zunzurutun rashin kunya ne da wayewa irinta nasara, abinda yayi da wasa ko don nuna wayewarshi ga abokansa sai ya juye mai ya koma sabon yanayii tare dashi don har ya fara manta inda yake tsaye k'ok'ari yake ya wuce makad'i da rawa Allah ya taimakeni Mus'ab ya gane halin da abokin nasa ya fara shiga don haka yai m.c magana kan ya bawa angon da amarya damar komawa mazauninsu, jiki a sanyaye ya ruk'o hannuna zuwa mazaunin namu,Duk kansa yai mai nauyi, yama rasa tunanin da zaiyi,kawai sai ya lumshe ido, dake hankalin kowa naga filin rawa sai ba'a lura da yanda yanayinsa ya canja ba, a sannu tunanin sa ya fara dawowa wani mugun tsaki yaja tare da furzar da iska tunawa da yayi wai bakinsa ne cikin na wannan y'ar Arabic d'in, har yake neman watsa kansa a gabanta, mutttssssss ya k'ara Jan tsaki tunawa da yayi da matsayinsa da nawa matsayin,ni kuwa zuwa lokacin duk jikina ya K'ara yin sanyi jin tsakin da yaketa ja ,daman gashi dik a takure nake.

Haka aka tashi a taron dukka ni dashi da abinda muke sak'awa cikin zukatanmu, bayan mun fito yacewa abokansa suyi k'ok'ari su maida dukkan y'an matan nan gidajansu, sannan ya amsa key d'in motarsa yace zai ja mu koma ba wanda zai shigar masa mota yanzu,dariya suke ta masa nan wani abokansa ya matso yana rad'a mai gulma kan zuwan fadla da kukan da tayi sanda taga bakinsa cikin nawa, da kyar suka rarrasheta ta tafi, d'age kafad'a yayi yana jan tsaki yace " damuwanta ne wannan ai ban gayyaceta ba" nan motan yayi yana d'agawa sauran hannu muka wuce gida.


Muna zuwa part d'in mu muka wuce ba wanda ya tankawa wani shi yai d'akinsa nima na shiga wanda aka fara kaini cikinsa matsayin nawa, kai tsaye kayan jikina na cire tare da shigewa toilet nai wanka na d'auro alwala nazo naita jero salloli ina rok'on ubangiji ya samin juriya da hak'uri kan Duk yanayin da zan tsinci kaina ciki a zaman aurena, sannan na rok'i Allah ya sanya dukkan alkairai cikin rayuwar auranmu,na dad'e bisa prayer mat ina kaiwa Allah kukana, har tsakiyan dare sannan bacci ya fara fuzgata,banko cire rigar danai sallarba na haye gado da addu'a bakina ba jimawa bacci me nauyi yai gaba dani.

Kiran sallar asuba ya farkar dani da kyar na iya bud'e idona don baccin dake cikin sa,ga tarin gajiyar biki, haka na daure nayo alwala nai salla azkar ma inayi bacci na jana haka nai na koma gado,wanda ban farkaba sai takwas, ina farkawa naji yana bud'e gidan zai fita bud'e labulen window d'in nayi ina kallonshi haryaje parking space ya shiga mota ina tsaye naga ya tada motar ya fice, toilet na shiga na had'a ruwa me zafi na gasa jikina sannan nayo wanka, wasai na jini yanzu duk gajiyan ta bar jikina,banyi wani dogon kwalliya ba powder da lipstick kawai nasa Sai turaran Humra dana jik'a jikina dashi, na d'auko riga da siket na atamfa na saka tare da kama kaina da ribbon na d'aure,ban d'aura d'an kwali ba sai mayafi dana yafa na fito parlor, kewaye gidan na farayi ina kallon yanda tsarin part d'in yake kasancewar nasan ni kad'ai ce a gun baya nan,

parlour biyu duk ansa kujeru, set d'aya orange and copy, set d'aya pink and purple, sai d'akuna biyu suma Duk ansa kaya,a babban parlourn ansa min dank'akemiyar Plasma t.v a gefe guda ansa show glass ta turaren wuta wanda aka cika ta taf da designed na kwalabe aji iya aji sai standard flowers a jere a gefen show glass d'in yayin da akasa wani had'ad'd'an santer table me matuk'ar a tsakiyar jerin kujerun, cen gefe dining area ne wanda aka saka had'ad'd'an dining table me zagaye da kujeru guda shida,daga gefe kuma fridge ne tsaye ash colour, gefen dining area d'in wata show glass ce ta kwance me hawa biyu duk an jera wasu zafafan glasses cups kalan fari tas Dame kalan ruwan garai sai masu flowers duk ajiki, a gefe guda kuma jikin dining area d'in duka k'ofar shiga kitchen ne,wanda yake k'aton gaske me d'auke da d'an madaidaicin stor a ciki,wanda aka cika su taf da kayan abinci, cikin kitchen d'in a kewaye yake da loga sama da k'asa duk anyi min jeren kayan kitchen sai cooker gas me had'e da oven da electronic ajiki, can jikin stor d'in ansa de freezer bud'e ta nayi naga kayan miya da nama acikinta na maida na rufe tare da jingina jikinta ina tunanin meya kamata in shirya na breakfast, Dukda nasan bai zama dole yaci abinda zan girkaba amma dai hak'k'insa ne in dafa mai,wannan tunanin ya bani k'warin gwiwar fara had'a mana breakfast me kafiya, kasancewar akwai dukkan kayan amfani fa na'urorin girki kala kala a gun yasa nan da nan na gama had'a komai na zuba a cikin wasu zafafan Warmer's lafiyayyu, nazo na jerasu jan dining table sannan na koma na gyara kitchen d'in duk abinda nai amfani dashi saida na gyara na goge ya zama kamar ba'ai komai ba a kitchen d'in, turare gidan na k'ara yi da turaren wuta sannan na koma d'aki na k'ara gyara kaina,hijabi na d'auko cikin kayana wanda ya shiga da atamfar jikina,na fito zuwa cikin gidan,a bakin parlour na had'u da sweety da sauran y'an biki da basu tafi ba suna bawa ma'aikatan gidan umarnin inda zasu gyara, tsalle tai ta rungumeni tana fad'in "oyoyo Aunty Nah wlh tun d'azu nake tunanin inje in duboki amma ina tunanin ko buku tashi a

Please Login or Register in order to submit comment