Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Sai a sannan naji d'an sanyi ya ratsani na saki raina mukaci gaba da hiranmu cikin nishad'i.









Taku ce
Layuza kabir AdamπŸ™‹β€β™€
https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation?

🍑🍑🍑 🍑🍑🍑
🌸🌸 🌸🌸🌸🌸
*Y'AN ARABIC*
🌸🌸🌸🌸🌸🌸
🍑🍑🍑🍑🍑🍑

*NA*

*LAYUZA* *KABIR* *ADAM*


DEDECATED TO ALL
ARABIC /ISLAMIC STUDENTS
πŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“š

πŸ‘¨πŸ»β€πŸ’»πŸ‘©πŸ»β€πŸ’»
*ZAMANI WRITERS ASSOCIOTION*

πŸ“
​​WΙ› Ι‘Κ€Ι› Ι¦Ι›Κ€Ι› tΡ³ Ι›Ι—ucΙ‘tΙ›, MΡ³tiΡ΅Ι‘tΙ› Ι‘Ι³Ι— Ι›Ι³tΙ›Κ€tΙ‘iΙ³ Ρ³uΚ€ ʀɛɑɗɛʀร​



0⃣3⃣8⃣


Haka akaci gaba da gudanar da ibadar azumin Ramada cikin kwanciyar hankali , har yau ankai goma, Abba yayi matuk'ar k'ok'ari don kayan Abinci ya had'a bana wasa ba ya aika dasu can gidan mu sakkwato yace inji mijina, haka akaita rabawa y'an uwa na kusa da nesa tare da abokan arzik'i, sannan yasa turaman atamfaofi da yawa yace nasu umma da mama sauran na y'an uwa, Haka ma anan kano Ya aikawa yaya haroon kayan abinci bana wasa ba haka ma yaya Usman sannan yasa turaman atamfofi na Aunty Hafsa da Aunty Amrah suma su Yayan harda shaddodi, gaskiya Abba yayi k'ok'ari, waya tako ina aka rink'a kirana anamin godiya wai sunga kaya inji mijina sun gode, nikam sai dai inyi mirmishi kawai.


A daran ranar Abban ya kiramu nida sweety bayan munyi sallar Asham ya bamu kud'i wai na kayan sallar mu ne in zamu k'aro, ga Atamfofi da shaddodi yace mu d'auki iya yanda muke so, godiya nikam nai tayi yace "ba komai ai hakki nane"

Bayan kwana biyu ma saiga transfer kud'i daga Uk 100k wai inyi hidimar salla nace Abba ya mana komai, amma yace babu ruwan sa da kud'in Abba wannan kyautar shi ce tsakaninmu wannan kuma hakkin sane ya dole yayi min, nikam godiya nai tayi ina mai addu'a, a ranar nake tambayarsa zanje in yiwa su yaya na barka da shan ruwa, yace to ba matsala, washe gari da safe kuwa na tafi gida bayan na tsaya na saiwa su Ashraf wasu tsada tsadan kaya riga da wando wando masu masifar kyau da tsada kowanne kala biyu, sanda naje gidan kuwa murna kamar sayi me, bayan mun gaggaisa na sami nutsuwa nan na fito da kayan na basu sukaita murna, a gida nasha ruwa naje nawa su yaya usman ma barka da shan ruwa sai bayan sallar Asham sannan na koma gida a mota ta dake da ita na tafi.



Kwanaki nata gudu azumi nayin nisa yayinda muka k'ara k'aimi wajan bautar Allah da addu'oi,kullum in zanyi addu'a ta saina rok'i ubangiji shiriyar sa ga mijina da kuma k'ara neman alkairi cikin zamanmu, wanda kullum kuwa ina ganin canji na k'aruwa a zamantakewar mu.

A haka muka kammala azumi mukayi sallar idi cikin kwanciyar hankali da farin ciki, bisa umarnin da Abba ya bashi yace inje sakkwato inyi kwana hud'u don in gaida iyaye da y'an uwa,hakan yamin dad'i matuk'a ranar da na sanar da yaya nah Haroon yace ai suma sunyi shirin tafiya harda yaya usman da matarsa don haka muka rankaya ranar biyu ga salla mukai gida sakkwato, nayi tsaraba sosai kasancewar shine zuwa na farko tun bayan aurena,gashi Abba ya cikani da kud'i haka shima Uk ya turomin 50k yace inyi tsaraba, na zaga dangi sosai cikin kwana hud'un nan kuma Duk inda naje zan musu alkairi, badan naso ba na dawo son su yaya acan na barsu tunda mu muna tsakiyar semester don hutun sati d'aya kawai aka bamu, randa na dawo washe gari aka koma school amma banje ba sabida gajiya ga gyare gyare Dana d'anyi.




*************
Haka rayuwa taci gaba da gudana yai da dad'i gobe babu,amma nikam a fanni na sai dai nace masha Allah don yanzu anzo matakin ma da na daina kiran uk a waya sai dai shi ya kirani wata irin kulawa nake samu daga gareshi,abunda na tabbatar addu'ar da nakeyi dare da rana Allah yana amsamin tunda gashi kullum gari ya waye da sabon salon k'aunar da zan samu daga gareshi,yanzu bama sai iya dare ba koda rana yaso jin muryata zai kirani sai dai bama wani dad'ewa da dare ne dai sai mun manta ma a waya muke sannan muke hak'ura mu rabu da juna.




**************
Yana kwance saman d'an madaidaicin Royal bed d'insa bayan gama wayar su,tunanin yake cikin ransa shin wai meke damun sa ne kan wannan yarinyar, shikam abun har mamaki yake bashi yana rasa yaushe kuma ta ina ya fad'a tarkon k'aunar ta,shida yasan wayar gari kawai yayi ya ganshi tsamo tsamo cikin tafkin k'auna wanda har yake shiga damuwa in baiji muryar taba, yanzu Nazo matakin da yake kasa rintsawa sabida tunani da begenta,duk dare in sukai waya tafiya take ta barshi da begenta, gashi shi bamai yawon sha'awa bane amma dayaji muryan ta sai yaji hankalin sa ya fara gushewa nan da nan za'a sakar mai da notinan sa yaita mata sambatu yana fad'in abunda bai san ma yana fad'a ba, wani sa'in in suka gama waya ma sai yai wanka don jinsa yake sharkaf ya jik'e, amma fa dake d'an duniya ne har yanzu yak'i barin hanyar da wani zai gane tsananin su,cikin abokansa tunda sun san ba son auran yake ba shiyasa yanzu ma bai bari su fahimci ya fad'a tarkon k'auna ba, yanzu Fadlah ma Sama Sama yake da ita, ko gidanshi yanzu bai bari tana shigowa sosai inma ta shigo bai wani sakar mata fuska, ta tambayeshi ta tambayeshi kan ya fad'a mata lefinta amma amsar d'aya ce yace ba komai,


Yau ina kwance banjin dad'i kwata kwata ko school banje ba, kiran wayar sa ya shigo wayata na d'aga muryata can k'asa me cike da alamar rashin lafiya tattare dani, "Mata ta "

"Na'am miji na,barka da dare "
Na amsa mai,
"Ya naji muryanki wani iri ko gajiya ne"

"Um um wlh banjin dad'i ne tun safe"

"Oh my God meke damun ki"

D'an jan numfashi nai nace " mura da ciwon kai ne kawai"

Da sauri yace " Wane Irin kawai mura da ciwon kai ba kawai bane ai, kinsha magani amma"

Shagwab'e murya nai nace " um um ni banson magani "

Marairecewa yai kamar zai kuka yace " ki taimaka min kisha magani kinji Baby nah, Kar zazzab'i kuma ya kamaki daga mura".
"Bubbuga k'afa na farayi ina D'an kukan shagwab'a nake fad'in" nidai ban so ban son magani da akwai d'aci fa".

"K'ara k'asa yai da muryanshi yace" Khadeeeeejahhh"

Wani shockkkkk naji ya kamani jin yanda yaja sunan nawa nace "um mijinahhhh"

"Kina son farin cikina?"
" farin cikin ka shine nawa ai "

"Tom in dai haka ne ki daure don Allah kisha maganin kinji zakifi jin k'warin jikin ki Kinga saimu fi jin dad'in yin wayar ko".

" Tom amma fa kad'an zan sha kaji"

D'an mirmishi yai yace "eh na yarda kisha kad'an d'in ma"

"Tom ka jirani minti biyu zanje insha". Bayan na fad'a na kashe wayan na tashi zuwa parlour don samo maganin, a nan na tadda sweety tana kallo tace " yadai Aunty na me kike buk'ata"

Zama nai gefen ta ina fad'in "wlh Yayan ki ne ya takurani sai nasha magani shiyasa na fito insha D'an kad'an"

Dariya tasa tana fad'in "ai daman nasan shi zai saki kisha amma tun d'azu nake miki magiya kisha don Allah kink'i yanzu kyasha don dole ai"

Tashi nai zuwa fridge na d'auko ruwa ina cewa "baki da amsa yanzu don cikin lokacin mijina nake amma ki bari anjima zamu had'u"

Tanata tsokana ta ban kulata ba nasha maganin da k'yar na koma d'akin,

Duk yanda nakejin kaina kamar zai fashe haka na daure nake k'arfafa kaina mukaci gaba da wayan,bamu dad'e ba mukai sallama.



***********
Tafiya sosai lokaci yayi wanda yanzu ya rage saura sati guda mu kammala exams d'in mu da muka fara sati biyu daya wuce, duka yanzu hankalina naga shirye shiryen tafiya India ga mijina, shiri sosai nakeyi , gyaran jiki kusan kwana goma aka fara min wata k'wararriyar mata Maman boy ta had'a ni da ita take min gyaran jiki kasancewar da wuri muke gama exam son kullum d'aya mukeyi don haka ana tashi gidan matar nake wucewa, iya kwana goman da aka fara gyaran na canja matuk'a nayi wani haske amma ba Irin d'au d'in nan ba,kasancewata bak'a yasa sai fatata tai wani brown color taita shek'i da d'aukan ido,ga wani k'amshi na musamman wanda Duk inda na motsa sai kaji k'anshin,ko fitsari nai maimakon zarnin fitsarin sai dai k'amshin miski da wani asirtaccen k'amshi Ke tashi, batun tsimi kuwa ya riga ya zama ruwan sha na, shiri nakewa can jikina matuk'a don nasan yanda muka afka k'aunar junan mu yanzu babu abunda zai hana mu cure mu zama abu guda yanzu, don haka nake mai tanadin kaina na musamman, gashi me gyaran jikin nawa ma tanata tsumani da nata tanadin, bayan wanda nakeyi da kaina,kamar yanda duk wani wanda yasan matan sakkwato ya sansu da gyara da tsimi.


Tunda Abba yace mai mun kusa zuwa mai ziyara ya k'ara rikid'ewa da rigima, ranar muna waya yake tambayata wai ranar yaushe zamu taho na k'ank'ance murya cikin tsokana nace "kai dai daga nan zuwa sati guda kaita tsammanin mu don nima ban san ranar da zamu taho ba amma dai an gama komai na shirin tafiyar".

" wlh ko precious duk na matsu kizo don na gaji da zaman gauran cin nan da matata da komai ina kwana cikin yunwa"
Y'ar dariya nai "Meyasa kake kwana da yunwa baka samun abinci ne?"

Na fad'a kamar ban san inda ya nufa ba,
Cikin muryan shauk'i yace "Bana yunwar Abinci bana yunwar ruwa yunwarki kawai nakeyi"

"Ummmm daman ana yunwar mutum ne"

"Hhhmmm ko ba'ayi nidai ina yunwar ki dare da rana kullum burina inga ranar da zan kauda wannan yunwar tare dani".

" hhhhmmmm karka damu saura k'iris mu had'u duk yunwa da k'ishin ruwar ka zan kauda ma dasu kaji miji na gari".

"Yawwwa my precious kinyi alk'awari ko?"

"Hhhmmm karka damu kaji"

"Tom wlh ki shirya banda raki banda ragwanta "

Mirmishi kawai nai ban k'ara cewa komai ba, haka yaci gaba da jifana da kalamai masu sanyi da dad'i har sama da awa biyu,muka rabu.




Rana bata k'arya inji masu iya magana gashi yau ya rage kwana d'aya tal jirginmu ya tashi zuwa India, ina zaune gaban akwatina wanda na gama cikashi tsaf da kayan da zan buk'ata na tsawon sati shida, d'ayan akawatin kuwa kayan shafa ne da turaruka dangin su Humra kwalakca dasu lobelia, Duk wani abun k'amshi wanda ya amsa sunanshi me k'amshi da mata ke amfani dashi na tanadeshi, banyi gigin d'aukan wasu kayan maganin mata ba,nasan iya abunda nai amfani dashi yanzu ajikina ya isa min aiki har tsawon watanni, duk da bawai wani tarkacen shirme nasha ba wanda nasan zai tafi da tsarina dai dai nai amfani dasu, kayan fruit kuwa daman mutane nane namusu shan kaca suma, tunani nake meye ban had'a ba na tabbatar komai ya zama ready, kaina yasha kitson gana wanda aka mai d'iba na iyawa kasancewar inada cikar gashi sosai yasa kitson ya zauna akaina kamar an dasa hula jelar gashin kuwa tana zube a kafad'una yar yar da ita, sai hannuwana da k'afafu sun sha k'unshi ha da bak'i koda nake bak'ar fata hakan bai hana bak'in kunshi yimin matuk'ar kyau don bak'ina me kyaune kuma ba can sosai bane bak'in.

Sweety ce ta shigo tana fad'amin kiran Abba, nasa hijab d'ina nabi bayanta, a saman cafet na sameshi zaune bayan na gaisheshi ya amsa cikin fara'a "Khadeejah ya shirye shiryen"

Cikin d'an jin kunya nace " Alhamdulillah "

"Tom daman na kiraki ne in shaida miki yanzu agent d'in jirgin da zamu bi yake sanar dani an samu sauyin yanayin tashin jirgin daga karfe hud'u na yamma zuwa tara na safe don haka saiki zama cikin shiri suk inda takwas tai ace kina ready kinji"

Kaina a k'asa cikin jin nauyi nace "To Abba Allah ya kaimu "

Ya amsa da "Amin"
Sannan yace Inje inci gaba da shiri da nake.



Bayan na gama Duk abunda nake nazo kwanciya na d'auki waya ta tarin Miss call d'inshi na tarar ban san ya akaiba wayan ta shiga silent ga Miss call nan kusan goma, nabishi yak'i d'agawa inata kira amma fir yak'i d'agawa na tabbata fishi yai mirmishi nai araina ina tunanin daya san gobe zamu dirar mai dabai k'irk'iri fishi ba don Abba yak'i sanar mai takamai mai ranar da zamu zo kawai dai yace ya zama cikin shirin ganin mu cikin satin, don so yake yai surprise d'insa,ganin yak'i d'agawa yasa na kashe wayan na sata a charge kawai dana duba ogogo k'arfe sha biyu saura don haka na d'aura alwala na fara nafilfili har zuwa d'aya saura sannan na kwanta.







*Munyi* *zab'e* *mun* *zab'i* *zab'inmu* , *Amma* *Allah* *zab'inka* *muke* *nema* *Allah* *kai* *mana* *zab'i* *na* *gari* *karka* *barmu* *da* *zab'in* *ranmu* *Allah* *ka* *bamu* *shugabanni* *na* *gari.*πŸ‘πŸ‘πŸ‘






Taku ce
Layuza kabir AdamπŸ™‹β€β™€
https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation?

🍑🍑🍑 🍑🍑🍑
🌸🌸 🌸🌸🌸🌸
*Y'AN ARABIC*
🌸🌸🌸🌸🌸🌸
🍑🍑🍑🍑🍑🍑

*NA*

*LAYUZA* *KABIR* *ADAM*


DEDECATED TO ALL
ARABIC /ISLAMIC STUDENTS
πŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“š

πŸ‘¨πŸ»β€πŸ’»πŸ‘©πŸ»β€πŸ’»
*ZAMANI WRITERS ASSOCIOTION*

πŸ“
​​WΙ› Ι‘Κ€Ι› Ι¦Ι›Κ€Ι› tΡ³ Ι›Ι—ucΙ‘tΙ›, MΡ³tiΡ΅Ι‘tΙ› Ι‘Ι³Ι— Ι›Ι³tΙ›Κ€tΙ‘iΙ³ Ρ³uΚ€ ʀɛɑɗɛʀร​



0⃣3⃣9⃣



*ALLAH* *KA* *IYA* *MANA* *DA* *IYAWAR* *KA* , *ALLAH* *KAGA* *HALIN* *DA* *JIHATA* *TAKE* *CIKI* , *ALLAH* *KARKA* *BAR* *AZZALUMAI* *SUYI* *TASIRI* *AKANMU* .
πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘





Tunda nai sallar asuba na shiga kitchen don samin abunda zanyi break kafin mu wuce, na d'ora kenan sweety ta shigo kitchen tace" Aunty na jeki fara shiri bari inyi girkin"

Wucewa nai bedroom na cire kaya na shige toilet, wanka na silla iya wanka kamar wanda na kwana goma banyi ba, bayan na fito nazo na jik'a jikina da turaruka masu d'aukan magana, a nutse nake shirina, ba wata doguwar Kwalliya nai ba powder na shafawa fuskata wadda tai wani fayau tai kyau sabida gyaran jikin Dana sha,sannan na shafa Lipstick fari na k'ara gyara gashin idona da maskara sannan nasa brush na gyara cikakkiyar girata na saita kamar naja gira, wata y'ar bala'in doguwar riga nasa bak'a kirar Dubai me tarin duwatsu a gaban k'irjin wanda yake daidai jikina Sai k'asanta da yake a bud'e sosai nasa hills takalmi shima bak'i nai rolling kaina da mayafin rigar, y'ar jaka bak'a na d'auka a hannuna na fito parlour lokacin bakwai harta wuce, samun sweety nai tanata gyaran gidan harta gama had'a mana break fast d'in, da fara'a kan fuskata nace " wayyo y'ar uwa ns barki da aiki ko"

Mirmishi tai duk jikinta a sanyaye tace "Har kin shirya ga break d'in can na jiranki bari inyi sauri inyi wanka kafin ki gama".

D'aki ta shige da gudugudu ni kuma na k'arasa dining na fara had'a abunda zanci.


********
K'arfe takwas da rabi muna filin tashi da saukar jiragen Mlm Aminu kano, Yan rakiyarmu Aunty murjah,sweety, salis da Autansu Hisham, naso yaya na yazo amma yace tunda nazo dai munyi sallama shikenan basai sunmin rakiya ba, duk muna zazzaune muna jiran a fara kiran fasinjoji, nida sweety muna d'an hira tana fad'a min zatayi kewana tsawon kwanakin da zanyi ,nima nace mata zanyi kewarta,y'ar dariya tai tace " kina tare da mijinki yaushe zakiyi wani kewana" duka nakai mata a kafad'a ina dan dariya nace "Ke ko hhhmmm"

A lokacin aka fara kiran fasinjojin nan muka mik'e Abba yai musu sallama nima sallama nakewa Aunty murjah sannan na rik'o hannun sweety nace "Sis sai na dawo?"

Rungume ni tai tana min rad'a a kunne"kiyi k'ok'ari ki dawo mana da baby "

Janyewa nai da sauri ina hararanta Abba yace " muje Khadeejah".

Jawo jakata nai nabi bayansa ina d'aga musu hannu.


Muna shiga Abban ya gamu da abokinsa da yayansa bayan mun gaisa yace in zauna kusa dasu shi kuma ya zauna tare da abokin Nasa, bayan jirgi ya lulu bakina d'auke da addu'a karon farko dana fara shiga jirgi a rayuwata,amma ban nuna komai tare dani ba,muka shiga hira da Yayan nasa masu D'an karen surutu nidai harna gaji naja bakina nai shiru.



******
Dai dai k'ofar wani d'an k'aramin gida motar data d'auko mu daga filin jirgi bayan driver yayi parking muka fito muna fitar da jakunkunanmu.


Sau biyu Abba yana k'wank'wasa k'ofar akazo aka bud'e, tsayawa kawai yai cikin wani matsanancin farin ciki ya kama baki yana fad'in "Abba nah"

Dariya Abban yai yace "na'am Daddy nah "

Jakan hannun Abban ya amsa yana wucewa gaba muka bishi duk farin ciki ya cikashi Abba ya zauna kan kujera ni kuwa k'asa kan kafet na samu na zauna da sauri Abba yace "A'a tashi ki zauna Sama mana Khadeejah nace ki daina irin haka "

Girgiza kai nai cike dajin kunya nace "a'a Abba nan ma yayi "

Dawowa yai d'auke da lemo da ruwa kan plat ya ajiye yana zaunawa yace "Abba Kunyi surprise d'ina wlh, Sannun Ku da zuwa ya hanya"

Cikin fara'a da murna suka gaisa da Abban, ni kuwa cikin kunya na gaidashi ya amsa yana tsareni da idanuwan sa yace " Sannunki da hanya,ki tashi ki hau kujera mana kika zauna k'asa"

Girgiza kai nai kawai bance komai ba, sai Abba daya ajiye cup d'in d'aya sha lemo ne yace"Ai bazata zauna ba,kullum haka muke fama da ita tak'i sakin jikinta".

Kad'a kai kawai yai yana D'an mirmishi, idon sa k'yar akaina, duba agogo yai yace "Abba bari inyi muku order na abinci "

"Mirmishi Abban yai yace ai naga ma lokacin sallar azahar yayi ko?"

Duba ogogon nai naga k'arfe biyu na ranar su,

Abba yace "Muje masallaci muyi salla sai muci abincin ko?"

Mik'ewa yai ya shiga d'akin yai alwala sannan ya sako doguwar riga kan tree quarter d'in wandon dake jikinsa,Abba ma shiga d'akin yai kasancewar d'aki d'aya ne kawai a gidan kuma a ciki toilet d'in yake,sai palour da D'an k'aramin kitchen, bayan fitarsu masallaci na tashi na shiga d'akin nima don Yin sallar, ina zaune kan prayer mat ina addu'a ya shigo d'akin jingina yai da jikin k'ofa ya hard'e hannayensa yana kallona, sarai ina kallon shi ta gefan idona,nai kamar ban ganshiba naci gaba da addu'a ta,a hankali ya tako zuwa gabana ya tsugunna tana lek'a idona, shafawa a hankali na kalleshi da sauri nai k'asa da idona sabida wani kwarjini daya min,rik'o hannuna yai yana D'an mirmishi yace "Ki taso ga abinci can na jiranki, " To nace idona na kallon gefe.

Sanda muka fito parlourn har Abba ya fara cin abincin da aka kawo daga gidan abinci da sukai order,
Cikin jin kunya na samu gefe na zauna,da kansa ya d'auki plat ya zuba min tare da turowa gabana, jan abinci nai gabana ina D'an tsakura don duk kunya ta rufeni, ba jimawa Abba ya mik'e yace "Daddy bari in tafi masaukina inaga sai zuwa gobe kuma zan dawo kuma insha Allah jibi zan juya".

Cikin marairecewa yace " Ah haba Abba wai da gaske kwana biyun zakai?"

D'an dariya yai yace "To ai dama nace ma rakiya nayowa Khadeejah insha Allah kuwa jibi zan juya kasan dai tarin sabgogin dake gabana".

Shima mik'ewa yai yace " To Abba bari in rakaka".

Saurin dakatar dashi yai yana fad'in "a'a zauna abunka ma had'u gobe".

Dagewa yai sai ya raka Abban, don ce mai yau shima zai D'an tsaya yayi siyayya don haka ya barshi,suka tafi tare yana cemin " To Khadeejah sai gobe ko".

Kaina a k'asa nace "To Abba Allah ya kaimu".



Fita sukai suka sami motan haya suka hau zuwa hotel d'in da Abba zai sauka, saida suka gama komai ya shigar mai da y'ar jakarsa d'akin sannan yamai sallama ya taho,kasuwa ya wuce kai tsaye don yin siyayyar abubuwan ciye ciye dana buk'ata.




Ni kuwa bayan fitar su na saki jiki naci abincin sannan na gyara gun naje kitchen na wanke plats din na ajiyesu inda naga sauran, dawowa nai ina tunanin wanka zanyi ko in jira ya dawo tukun, wani tunani nai don haka da sauri na tashi na shige toilet d'in da sauri sauri nai wankan, na fito cikin sauri na bud'e jakata na Ciro kaya nasa bayan na goge jikina da turaruka, Sama Sama nai Kwalliya na dawo parlourn na zauna ina kunna T.V....

K'aran k'ararrawa naji alamun son shigowa, k'ara dannawa akai ,a hankali na tashi naje na bud'e k'ofan,yana tsaye hannunsa d'auke da ledoji, hannu na mik'a zan amsa ina mai sannu da zuwa,girgiza kai yai yana dariya yace " a'a bazan baki kayaba daga zuwanki rufo k'ofar dai , rufo k'ofan nai na biyo bayansa, a tsakiyan parlourn ya ajiye kayan a sanda na k'araso a hankali ya bud'e hannayensa alaman in shiga ciki,rufe idona nai da hannayena da suka sha rantsatstsan k'unshi, taku uku yai ya k'araso gareni gaba d'aya naji ya sanyani cikin jikinsa . . . . .





Ayi hak'uri da wannan zamu had'u gobe da yardar Allah.








Taku ce
Layuza kabir AdamπŸ™‹β€β™€
https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation?

🍑🍑🍑 🍑🍑🍑
🌸🌸 🌸🌸🌸🌸
*Y'AN ARABIC*
🌸🌸🌸🌸🌸🌸
🍑🍑🍑🍑🍑🍑

*NA*

*LAYUZA* *KABIR* *ADAM*


DEDECATED TO ALL
ARABIC /ISLAMIC STUDENTS
πŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“š

πŸ‘¨πŸ»β€πŸ’»πŸ‘©πŸ»β€πŸ’»
*ZAMANI WRITERS ASSOCIOTION*

πŸ“
​​WΙ› Ι‘Κ€Ι› Ι¦Ι›Κ€Ι› tΡ³ Ι›Ι—ucΙ‘tΙ›, MΡ³tiΡ΅Ι‘tΙ› Ι‘Ι³Ι— Ι›Ι³tΙ›Κ€tΙ‘iΙ³ Ρ³uΚ€ ʀɛɑɗɛʀร​



0⃣4⃣0⃣




Mirmishi nai kawai kaina a k'asa, rik'o hannayena yai cikin miryan rad'a yake fad'in " nayi farin ciki da zuwanki my Khadeejah, Abba nah ya faranta min rai matuk'a, amma ke gashi kin kasa nuna min farin cikin ki".

D'ago idanuwa nai na

Please Login or Register in order to submit comment