Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tare da cije lips d'in sa,komawa yai kan kujerar ya zauna yana jin wani nishad'i na ratsashi yau ya shirya sosai da sahibar sa dukda bai kai ga gaci ba amma yau kam akwai alamun nasara sosai da ganin mirmishin dake sauka kan fuskar ta.

Da azama ya fara cin abincin duk ya zak'u.😜


Ni kuwa ina shiga d'aki na cirewa little kayan jikin ya na samata na bacci,sannan nima na shige toilet nai brush sabida ban dad'e dayin wanka ba, fitowa nai nasa night gown na feshe jikina da turare na goga ko ina, har bayan kunne na zuwa wayana dasu tsakanin boobs d'ina, amma ban shafa a jikin suba sabida nasan duk jikin su babu inda UK baya tsotsaπŸ™ˆ,gashi nima tun daga salon farko daya min duk jikina ya amshi sak'onnin shi.

Bayan na gama na k'ara saka air freshener a d'akin ya d'au kamshi kashe hasken dakin nai na haye gado ina tofa addu'a adukkan sassan jikina da jikin little sannan na tattofe gabas da yamma na jawota jikina ina sakin wani miskilin mirmishin nai don nasan yana jin shiru zai biyo ni .

Shi kuwa UK yana gama cin abincin ya mik'e cike da d'oki ya wuce d'akin sa wanka yai a gaggauce ya fito ya zauna gaban mudubi yana gyara jikinsa kamar wani mace ya goggoga turaruka a duk jikinsa sannan ya d'auko d'an boxer yasa zama yai bakin gado yana tunanin shigowar ta,har zuwa yai bakin gadon daya sawa little a d'akin sabida inya d'auko ta wani lokacin in tai bacci ciki yake zurata.
K'ara gyara mata gadon yai yana fad'a a ransa "my daughter yau a cikin gadon ki zaki kwana Abban ki zai more yau".
Sai kuma ya saki mirmishi, yana kallon agogo k'ara minti goma yai tabbas in bata shigo ba binta zaiyi.


Ina kwance tunani kala kala a raina naji an turo k'ofan an shigo tare da mayarwa a rufe,k'ara lumshe idona nai irin na masu baccin nan, kusan minti guda yana tsaye yasa hannu ya kunna glop tare da takowa a hankali zuwa bakin gadon ya zuba mana ido na d'an seconds sannan a hankali yasa hannu ya zare ta a jikina yana rungume ta a k'irjin sa tare da kissing d'in duk jikinta ya k'arasa zuwa bakin gadon ta yana jawoshi jikin gadon mu ,sanyata yai a ciki yana tofa mata addu'a, zuwa yai kashe glop d'in ya hayo gadon a hankali yasa hannunshi ya kunna lamp ya jawoni jikin sa yana sauke wata ajiyar zuciya,duk bidirin da yake idona na rufe ni ban yarda ba me bacci, a hankali naji yana shafa gashi na dana sake shi ban samai ribbon ba, sanya bakin sa yai cikin kunne na yanamin rad'a " my heartbeat nasan fa idon ki biyu kina jina kawai jamin aji akeyi,nidai kaina bisa wuyana a karb'i tubana".

Inajin sa amma banko motsa ba,shima shiru yana yawo da hannun sa a sassn jiki na, inda kullum hangen sa yake yakai hannu yana shafosu cikin wani irin salo tare da d'an matsasu,ban San sanda na runtse ido ba ina d'an bank'arewa, a hankali ya zare rigan dake jiki na,had'uwar k'irjin mu waje guda ya haifar mana da balaeen shock a tare muka sauke ajiyan zuciya,ya k'ara matseni a jikin sa, nima na kwantar da kaina akan fuskar sa hancin mu na gogar na juna,harshen sa yasa yana lasan lips d'ina,bud'e bakina nai nima ina jawo harshen sa da nawa muka shiga tsotsan bakin juna,hannayen sa biyu yasa yana wani irin wasa da k'irjina tare da kada kansu, Tabbas har cikin kwanyata nake karb'ar sakonnin sa,wani numfashi na sauke a galabaice ina k'ara sarrafa harshena cikin bakin sa, duk mun gigice mun gigita kanmu,mun lula can wata nahiya, wato mijina yai masifar sanin lagona don in har zai gogamin gemun sa a fuskata zuwa wuyana yai wasa da k'irjina to nikam ya gama kunna min wuta,ban aune ba naji kan abuna cikin bakin sa yana wani irin tsotsan su, tare da lailaya d'ayan da wata siririyar k'ara na saki ina zare mai boxers d'in dake jikin sa,cikin wani irin gigitaccan shauk'i ya juyani k'asan sa muka can duniyar sama.


Tsawon watannin da muka d'auka bamu had'u da juna ba muke k'ok'arin fanshewa a wannan daran,don damunyi Rleax muke k'ara tsokano juna da sabbin wasanni, mun raba dare har muna k'ok'arin cinye daran wajan rayashi da aikin kashe arnaπŸ™Š.

Bayan mun tabbatar wa kanmu mun gamsu ,ya jawoni jikinsa yana shafa bayana ni kuwa na wani saki jiki inata mai shagwab'a da k'orafin ya hanani bacci,wata shu'umar dariya ya saki cikin kunne na yana fad'in, " um um Baby kece fa kika hanamu rintsawa ni tun a second round naso hak'ura amma kika rik'e min abuna tsam a jikin ki, ina janyewa kina k'ara matseni,ai dajin kukan dad'in da kike nasan kin fini ma buk'atuwa kawai halin mata ne yasa ake wani basarwa amma aini yau naga k'wa. . .
Kafin ya k'arasa nai saurin toshe bakin sa da tafin hannuna ina bubbuga mai k'afafuwa na dake sak'ale cikin nashi tare da kukan shagwab'a "um um Allah Allah nidai bana so ni ka bari, Allah kaine ka hanani sakat ".

Hannunn nawa ya zare daga bakin sa yana dariya sosai,bugun sa na shigayi a k'irji tare da tuttureshi daga jikina, amma ya rik'e k'am yana dariya tare da mak'ale kafafuna da nake bubbuga masa a nasa, ganin yanda yake dariya gashi yak'i bari na in bar jikin sa yasa na sakin kukan sakal ci harda wangale baki kamar k'aramar yarinya, saurin rufemin bakin yai yana d'an zaro ido yace" Rufamin asiri don Allah, tsakiyar dare ne fa,kar jama'a su juyoki, yi hak'uri ni duk wasa nake miki kawai tsokana ne,amma nasan ke bikiyi kewana ba ko kad'an tunda dai ni me lefi ne gareki, nine kawai nai missing d'inki kuma na cika da sha'awarki har yasa naketa rounds ban gaji ba,amma ke kam kawai taimakona kike badan ma na tab'o shocking point d'in kiba nasan da bakida lokaci na".

Ya k'arshe yana had'iye dariyar datake cinsa, ina k'ok'arin magana little ta fara k'ishin k'ishin d'in kuka,da sauri ya lalubo boxers d'in sa yasa ya d'auko ta, yana mik'o min,mak'ale kafad'a nai na tashi na lalubo zanin da nake salla a gefan drawer na d'aura na wuce toilet, saida nai tsarki na d'aura Alwala don bazan shayar da ita da najasa a jikina ba,gudun sharrin shed'anu, sannan na fito na karb'eta tanata cilla kuka,haske na kunna na bata ruwa kafin nono don da ruwa nake fara rarrashin ta in tana kuka sabida zuciyan ta tai sanyi kafin in shayar da ita

d'an kallon sa nai ta gefen ido bayan na zauna kan kujerar dake gefan gadon nace " d'an janye mana wannan bedsheet d'in kabar plen d'in ".
Cikin tsokana yace " sabida me za'a canja shi yanzu".

Cikin dakewa nace "sabida ka b'atashi ".

Mik'ewa yai yana mirmishi ya janye shi yana fad'in" mun b'atashi dai a tare ".


Ban tanka mai ba nidai na kwanta ina bawa little nono ,shi kuma ya shige toilet da wancan bedsheet d'in a hannun sa.

Lumshe ido nai ina tunanin tsananin jarumtar dana nuna yau d'in nan,dukda nima nasan na azabtu da rashin mijina tsawon lokaci, gashi bayan na gama jinin haihuwa nai amfani da kayan gyara sosai,kuma daman ran suna inajin wasu y'an class d'in mu matan aure suna hiran wai in mace tai haihuwan fari karan ta na farko da miji yafi komai dad'i, don ita kanta mace a sannan ne take gane cikakkan d'and'anon mijin ta, cike da gamsuwa da zancen nan nasu na lumshe ido,tabbas koba haka bane nikam haka yake gareni, don zan iya cewa duk rayuwar da mukai a India muka gurje juna ban tab'a gamsuwa irin na yau ba,duk da naji a jikina amma dad'in ya lullub'e wahalarπŸ™ˆ.

Fitowa yai d'aure da towel jikin sa na d'igar ruwa alaman wanka yayi, ya zauna bakin gadon yana goga min ruwa a kafafu na,janye su nai cikin muryar baccin daya fara fizgata nace " ban so ka bari fa".

Hayowa gadon yai yana fad'in "karki bacci ki tashi kiyi wanka,kece fa a India kike cemin ba'a son mutum yai bacci da janaba a jikin sa".

D'an bud'e idona nai ina fad'in" ai nayi tsarki kuma na d'aura alwala, na sami kariya daga shaid'an, abunda ba'a so mutum ya kwanta bai baiko yi tsarki ba".

"Hhhmmmm kedai kawai kice bacci ya kamaki bazaki iya tashi ba, kuma mafa uku tayi kina fara baccin asuba zatayi".

juya mai baya nai nace" um zan sami kona awa guda ne".

Shima ya matso muka kwanta.



******
Washe gari cike da nishad'i mu duka muka tashi, sai wani shishshige min yake ya hanani sakat ko motsi nai yana bayana, a wajan break ma sani yai a cinya yana bani a baki, Allah sarki little ko tasan Abban ta na angwancewa yau sai baccin ta takeyi, ba rigima, wajan sha d'aya bayan mun gama break ya d'auke ni tsam muka haye sama, d'akin sa ya wuce dani ya shiga jagwalgwala ni,wannan karon kam nok'ewa nai ina d'an tuttureshi ya danneni a gadon yana cafke bakina ,sosai muke tsotse bakin juna,can ya sararamin na sauke ajiyan zuciya da cewa "ka d'aga ni inje wajan yarinya ta karta farka tai kuka".

Kashe min ido d'aya yai yana magana can k'asan bakin sa" wannan yarinyar kin b'aci da rashin kunya y'ar fari amma bakya kauda ido akanta".

D'an turo baki nai nace "k'ara ni agaban mutane bana nunawa wani fa".

Hannu na dake cikin nasa ya matse yana fad'in" waye wanin to dawa kike?".

Dariya nai na mik'e tsaye ina zare hannu na cikin nasa,saida naje bakin k'ofa nace "kai ne me nunawa gaban mutane baka kunyar y'ar fari".
Nai mai gwalo na fice da gudu.


Dariya kawai yai yana girgiza kai ya maida bayan sa ya kwantar akan gadon.

Gaba d'aya weekend d'in nan cike da soyayya muka yi shi, soyayya ma kuwa me tsayawa cikin rai, haka yau Monday daya tafi office bini bini ya kirani awaya yana tambayata ya nake ya yarinyar sa yanzu ma ina idar da sallar azahar ya kirani yana tambaya ta ya muke.
Nikam mirmishi nai nace " gamu duka cikin kewan ka ga little ma tanata rigima ".
"Sorry dear anayin sallar la'asar zan taho gida kinji ki shafa min ita ki mata kiss matsayin nawa in na dawo zan maida miki ".

Cikin salon jan hankali nai yar dariya ,nace " ok ba damuwa muna jiran ka,Allah ya dawo mana dakai lfy,ya kiyaye ka".

Cikin jin dad'in addu'ar ya amsa da "Ameen ameen ".

*****
Da dare yace mu shirya muje shopping, ai kuwa ba k'aramar siyayya yai mana ba,musamman little yai mata siyayyan kayan wasa sosai harda kayan wasan ma da sai takai shekara uku bata fara wasa dashi ba, keke mota mashin na yara komai rankacaf,muka ciko mota dasu.

Da mukazo gida d'akin k'asa da duk sauran kayan wasanta yake ciki,muka zuba ya zauna ya k'ara gyara mata d'akin ni kuwa,sama na haye na barshi don yin shirin bacci.



*****
Sosai muka k'ara shiryawa da mijina duk wata damuwa dake tsakanin mu ta kau,mun k'ara d'inke kanmu.







*Taku ce*
*Y'ar mutan ja'oji*πŸ™‹
🍑🍑🍑🍑🍑🍑
🌸🌸🌸🌸🌸🌸
*'YAN* *ARABIC*
🌸🌸🌸🌸🌸🌸
🍑🍑🍑🍑🍑🍑

*NA*
*LAYUZA* *KABIR* *ADAM*

_DEDICATED_ _TO_ _ALL_
_ARABIC_ / _ISLAMIC_ _STUDENTS_
πŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“š


πŸ‘©πŸ»β€πŸ’»πŸ‘¨πŸ»β€πŸ’»
*ZAMANI* *WRITERS* *ASSOCIATION*
πŸ“
_We_ _are_ _here_ _to_ _educate_ , _motivate_ ,and _entertain_ _our_ _Readers_



~Fan's ayi hak'uri da jinkirin da *Y'AN ARABIC YAI INSHA ALLAH YA DAWO BA WASA HAR IZUWA K'ARSHENSA*~πŸ™‹


_*Wannan page na sadaukar dashi ga dukkan y'an uwa Marubuta,musamman y'an k'ungiyata ta* *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*_

_*Tare da dukkan Marubuta na groups d'in*_
_*MARUBUTA*_
*_TASKAR MARUBUTA_*
*LAYUZA KABIR NOVELS GROUP*
*UMMUN YUSRAH FANS*
*ZAMANI WRITERS FANS*
*YAK'I DA RASHIN GASKIYA GROUP*
*Y'AR MUTAN ARKILLA NOVEL*
*AUNTY MAIMUNA O'G NOVELLAS*
*TASKAR LITTATFAN HAUSA NA BILLYN ABDUL*
*Y'AR MUTAN J'AOJI NOVEL GROUP*


_*Marubutan dake cikin dukkan way'an nan groups d'in dana lissafo ina gaisheku kyauta, yawanku yayi yawa dana lissafoku d'aya da d'ayaπŸ˜…Har abada ana kyawun tare🀝 Allah ya tsareku ya kareku da dukkan sharrin masharranta,Allah ya k'ara bud'e k'wak'walanku ya k'ara muku hazaka da basira*_




0⃣5⃣5⃣



___________________________Rayuwa me cike da walwala muke gudanarwa, cikin satittikan da suka biyo baya, hankulan mu sun kwanta,fahimtar juna ta k'ara shiga tsakanin mu,musamman yanda UK ke nuna matuk'ar kulawa ga little sai nutsuwa ta k'ara kamani na tabbatar yayi nadamar abunda yai akan cikinta.


*******
Yau kam tun safe da muka tashi jikin little ba dad'i, zazzabi take sosai don na bata magani amma yak'i sauka,don haka yana office na kirashi a waya ina shaida masa yanayin jikin nata,cikin tashin hankali yace" maza ki shirya gani nan zuwa mu kaita asibiti".

Daga haka ya katse wayar da sauri ya mik'e yana had'a takardun gaban sa,masinjansa ya kira ya mai bayanin zai je gida daughter d'insa ba lfy.
Ya mai fatan samun lafiya yana rufo k'ofan office d'in.



**********
Cikin hanzari na canja kayan jikina tare dasa Hijab, parlour na fito na d'auki waya ta,k'ok'arin kiran sweety na fara yi a waya don in shaida mata, ringing d'in farko ta d'aga tana fad'in "Aunty nah yanzu nake k'ok'arin zagayowa ai".

Cikin sanyi muryata data karye nace " Kinga zazzabin little yayi zafi wlh yanzu zamu kai ta asibiti ma".

"Subhanallah, bari inzo muje tare".

Sweety ta fad'a a rikice.


Ina zaune na zuba tagumi idona a kan yarinyar da numfashin ta ke fita a wahalce saboda tsananin zazzabin dake jikin ta, addu'o'i ne d'auke a bakina ina rok'on ubangiji ta bata lafiya.

Aunty murja da sweety sukai sallama tare da shigowa, cikin raunin murya na amsa musu.

Hannu Aunty tasa ta amshe ta tare da tab'a wuyan ta,da sauri ta kalleni jin tsananin zafin dake jikin yarinyar tace " Khadeejah garin ya ya kika zauna da ita haka? ai zafin jikin yai yawa,ba'a son a bar yaro da zazzabi tsawon awanni".

Ji nai wani hawaye ya gangaro min nasa hannu ina sharewa nace "Ai ganin na bata magani ne yasa nake tunanin zai sauka a d'an lokaci kad'an,amma kinga sai k'ara hawanta ma yake yi".

Zatai magana UK ya turo k'ofar parlourn da sauri ya shigo, k'arasowa yai yana cewa " Ai kawai taso mu wuce asibitin don ban ma rufe motar ba".


Tare da sweety muka tafi Aunty ta koma gida tana mana fatan samun sauk'i.


Sai da muka hau titi sosai sannan ya sa hannunsa a jikinta, girgiza kai yai tare da cewa " Gaskiya ya kamata da yawa zazzab'in nan, kinyi sakaci wlh,zazzabi jikin yarinya tun k'arfe takwas har k'arfe d'aya bai sauka ba,amma ki kasa kirana ki fad'a min ".

Nidai ban ce komai ba inata matsar ido,don zuciyata ta gama karyewa,duk dakiyar da nake ta k'are".


**********
Cikin hanzari likitan da muka samu ya fara dubata, tsawon minti ashirin ya bamu gado don yace zazzabin yai zafi in akai sake sai ta fara jijjjiga, nan da nan ya bani umarnin in cire mata duk kayan jikin ta na barta da pampas kawai, umarnin sa nabi duk da ina tunanin sanyin dake ciki d'akin.

Wata Norse ce tazo ta d'an bowl da ruwa a ciki da farin towel ta goge mata jikin,cikin ikon Allah kuwa sai zafin ya d'an ragu,allura akai mata sannan aka jona mata drip don likitan ta tabbatar mana tana buk'atar ruwa a jikinta.


*******
Zuwa dare sai gashi numfashin ya dawo ya dai daita, kuma zazzabin ya sauka sai kad'an,su Aunty Hafsa da Aunty Amrah sunzo tun yamma sai bayan magriba suka tafi,Aunty murja da Abbah ma sunzo sun dad'e bayan sallar isha'i suka tafi.

Tare da sweety muka kwana,duk yanda UK ya rikice yace asibitin zai kwana shima, Abbah hanashi yai,yace "inka zauna lafiya zaka bata? kaje gida kai ta mata addu'ar samun lafiya shine mafita".

A haka muka samu ya tafi bayan ya kawo mana duk abunda zamu buk'ata".






*********
Kwanan mu biyu a asibitin tana samun kulawa matuk'a, a kwana na uku kuma sai ta fara jijjiga tana suma,abunda ya matuk'ar k'ara d'aga gankulan mu, UK da sweety kuka kariris, nikam zuciyata ta k'ek'ashe sai k'unar zuci don ma inata yawon ambaton Allah ne nake jin sauk'i sauk'i.


Babban likitan yara dake asibitin ne yazo da kansa ya duba ta,ganin yanda take jijjiga yasa aka canja mana d'aki, don k'ara samun kulawa ta musamman, tsawon yini da daran nan a tsaye mukayi shi, a ranar har Aunty murjah bata tafi gida ba,tare damu ta kwana, k'arfe shida na safe ran little yabar jikin ta.

Ina zaune kan prayer mat ina lazimi da kaiwa Allah kuka na kan ya bata lfy, naji sweety ta saki wata k'ara tana rik'e Norse d'in da take sanar mata ta rasu,don shi likitan tunda yaga numfashin na ta ya fita gaba d'aya ya juya ya fita bai ce komai ba.


Runtse idanuwa na nai ina jin zuciyata tana wani mugun buguwa da tsananin k'arfi,cikin sark'ewar murya nace "Innalillahi wa'inna ilaihi ra'jiun,Allah kasa cikin mafarki nake,Allah karka tabbatar min da abunda kunnawana suke . . . . . ." ban k'arasa ba naji UK da Aunty da suke reception sunje karb'o sun shigo da gudu suna salati.

Jikin gadon Aunty ta k'arasa tana d'ago gawar little Wanda ta tabbatar da ta rasu, salati kawai take da fad'in "Allahu Akhabar,Allah kasata cikin yaran cikin aljanna, kasa me taryar muce".

Wannan lafazi na Aunty ya tabbatar min da babu little ta tafi kenan.

Siririn kuka na saki bakina d'auke da " innalillahi wa'inna ilaihi ra'jiun".


UK kuwa tamkar k'aramin yaro haka ya tsugunna yana rusar kuka da gunji.

Sweety ce tai k'arfin halin tsaida kukan ta ta kira Abbah ta sanar mai,sannan ta kira Yaya Haroon shima ta sanar mai.

Kafin k'arfe bakwai suka bamu gawar tun zuwan Abba muka wuce gida,dukkan mu babu wanda ke cikin nutsuwar sa.



******
A gida muka tarar da su yaya Haroon duk sun zo, zuwa lokacin kuwa sabida ambaton Allah da nake tayi zuciyata ta rage rud'un da take ciki.

Cikin tausayawa yaya ya ruk'o Hannuna yana fad'in "Sannu Nahna kiyi hak'uri kinji, Allah daya baki Rukayya kuma ya amshi abarsa ya fiki son ta,shi zai k'ara miki wasu ".

D'aga mai kai nai kawai na wuce na zauna kan kujera don idona dishi dishi yake min.


Cikin d'an lokaci Aunty murja tai mata wanka,Yaya Usman ya shirya ta cikin likkafanin ta, Auntyn ummu sulaim ce ta mik'omin ita lokacin da aka gama shirya ta aka nannad'e ta cikin bargo,tace " Yi mata addu'a ".

Girgiza kai nai ina share hawayen daketa zubomin na kasa magana, ganin haka yasa Abbah dake tsaye yasa hannu ya karb'eta su yaya suka rufa mai baya suka fita.

Kowa matsar ido yake inka d'auke sweety dake rizgar kuka iya k'arfin ta.

Nikam mik'ewa nai na dafe bango tare da yaye labulen ina kallo sahu biyu da suke sallatar gawar, idona nakan UK dake sahun gaba yanafa kuka idon sa rufe.

Lokacin dana ga Abba ya rungume gawar a k'irjin sa sun nufi mota,na saki wani rikitaccen kuka da fad'in " wayyo little d'ina!!!! Wayyo Allah na ka bani hak'urin rashin ta"

Babu wanda ya dakatar dani daga kukan da nake don duk zuciyoyin su cike suke da tausayi na".




********
Har azahar UK na kuka riris, tun kowa bai rarrashin sa har suka shiga bashi hak'uri damai nasiha, suna nuna mai Allah daya bashi kuma ya karb'e ya fishi buk'atar ta.
Da haka dai ya samu yai shiru,amma zuciyar sa cike take taf da k'unci.



*******
Sai bayan sallar isha'i ya sami gani na,ina zaune cikin d'aki nai salla ya shigo, idonsa k'yar a kaina,ni kuwa kallo d'aya nai mai nai k'asa da kaina don wasu hawaye da suka taho min.

Tsawon mintina biyu yana tsaye idonsa a kan gadon ta dake gefen namu,duk yanda ya so jurewa kasawa yai, hawayen da yake rik'e wa ne suka shiga zarya kan fuskarsa, tun yana yi a zuci har ya fito fili,ya tako a sannu ya dafa kafad'ata,ban yi k'ok'arin d'ago kaina ba don nima kukan nake ban son ya gano halin da nake ciki ya k'ara karaya.

Cikin sark'ewar muryar shi data gaji da kuka ya ke fad'in " Nahna kin ga yanda rayuwa ta mana ko,sai da muka shak'u da yarinyarmu tai wayo ta saba damu sannan mutuwa ta raba mu da ita, yau duka watan Little uku da sati uku Allah ya karb'e ta ba . . . . ".

Da sauri na toshe mai baki jin zai yi sab'o,girgiza kai ba shiga yi ina rik'e kuka na nace" kayi shiru kar kai sab'o,mu zama masu tawakkali sannan mun sani komai dad'ewa daman Allah zai karb'e ta koda kuwa zata shekara dubu ne a duniya, kullu nafseen za'ik'atul maut, dukkan me rai zai d'an d'ani mutuwa,tabbas Allah ne ya bamu ita kuma ya fimu son ta,muyi hak'uri dukkan mu muna hanyar mutuwa m. . . . ."
Kuka yaci k'arfina don haka na datse maganar da ina tsoshe bakina.


Hannuna yake ta murzawa alamar rarrashi shima yana had'iye kukan sa.

A haka Ummu sulaim ta shigo d'akin ta same mu,nasiha ta k'ara mana sannan ta kama hannun UK tana fad'in " Broth kaje waje mak'ota sun zo maka gaisuwa".

Sai da taga ya fita sannan ta juyo gareni tace"ki dawo parlour kibar zaman kad'aici shike sa kike yawon kuka".

Ba musu na tashi na biyo bayan ta zuwa Parlourn.

*******
Wajan k'arfe tara su Aunty Amrah sukai mana sallama zasu tafi,amma yaya haroon yace Aunty Hafsah ta zauna wajena don ta d'an ragemin kewa,zuwa kwana uku kar abarni ni kad'ai.


Tare muka kwana da Aunty Hafsah da sweety a d'akina,ina kallo suna ta bacci amma nikam ko kyas na gagara yi,don zazzab'i ne yamin ruf sabida Nonuwa na da suka cika taf suke min tsiko, na sha paracetamol ma amma dake sun kumbura sun cicciko sosai sai azabar ciwo suke min,ga kewar little da ta addabeni da nayi juyi sai inga kamar tana gefe na,kunnuwa na har jiyo min sautin kukan ta suke, a haka ina wannan halin har aka kira asuba,da k'yar na dafa naje toilet

Please Login or Register in order to submit comment