Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

" Allah na gode ma daka azurtani da mace irin Khadeejah, hankali nutsuwa biyayya soyayya duka nata ne,Khadeejah me ajiye farin cikinta ne ta d'auki nawa ko zai k'untata mata,nasan yanzu tana cikin dangi tana nishad'in ta amma sabida farin cikina ta koma gida,Allah kaiwa Khadeejah albarka duniya da lahira".

Ina shiga gidan naga sweety ta fito yiwa saurayin ta rakiya bakin motar sa, bayan ta sallameshi ta k'araso inda nake da tambayar "Aunty nah lfy na ganki kin dawo yau".

Bayanin da naiwa y'an gidan mu shi nai mata, jim tai tana fad'in" Ayya gaskiya broth ya had'aki da aiki,bari in canja kaya in shigo tace min tana wucewa ciki,

Ina shiga d'akina na fad'a na cire kayana tare dasa rigar baccina sai da nasawa k'ofar key sannan na hau gadon ina kiran wayar sa ringing d'in farko ya d'aga " My Deejah"

"Na'am reality nazo gida harnai shirin bacci ma"

"Sannu kinji Allah yai miki albarka, gobe da safe saiki koma kiyiwa su Mama sallama ko".

" eh haka za'ai"

"Kiyi hak'uri kinji wlh na rasa yanda zanyi ne yasa na takura ki,marata ciwo kamar zata fashe".

" sannu kaji Honey da muna tare da tuni ina jikinka ina wasa da ita ko".

"Washh Allah don Allah kizo gareni yanzu".

" ba yanda zanyi ne mijina nima a buk'ace nake da kai duk jikina kewanka yake harma tweens d'in ka duk suna buk'atar ka. . . .".

Kalmomi masu zafi nake fad'a mai Wanda suka k'arasa rikitashi daga nan na shiga fad'a mishi Wanda suka kwantar mai da hankali, har k'arfe biyun dare sannan muka kwanta.


K'arfe bakwai na shirya na koma gida wasuma ko tashi a bacci basu bai sai gani na sukai, nima bayan na karya bacci me nauyi ya d'auke ni, ban farka ba sai sha d'aya, wajan k'arfe biyu motocin da zasu d'aukesu suka zo ba b'ata lokaci mukai sallama dasu suka d'au hanya.









************
Rayuwa ta mik'a na koma school inda muke ta karatu ba kama hannun yaro, b'angaran rayuta da mijina kuwa Masha Allah don sosai yake nuna min kulawa,kullum k'ara k'aunar junan mu muke cike da kulawa.

Wani abu d'aya daya fara shigar min rayuwa shine yanda naga jini namin wasa wani sa'in sai in ganshi kad'an yazo wani sa'in kuma ya d'auke a haka naketa bin sa in yazo in aje ibada inya tafi inyi tsarki, ban jin wani canji a jikina amma kuma ciwon kai ba'a magana kullum dashi nake kwana nake yini,harya zame min jiki tun inashan magani na daina kawai na alak'anta hakan da tsananin karatu don yanzu da mukai nisa karatun yafi zafi, yanzu wata na biyu da sati biyu da dawowa daga India banyi wani cikakken jini ba sai d'is d'is dinnan da nake gani don haka yau kam nace zanje ganin likita bisa takuramin da umar yai kan inje inga likita kar wata cuta ta shigeni,k'arfe wajan Tara ba isa asibitin bayan yin duk abunda ya dace na isa ga likita ina sanar mai matsala turani yai amin tes kusan guda hud'u yace in dawo Washe gari amin scanning a marata,haka na dawo gida ina addu'ar Allah yasa ba wata babbar cuta bace ta kamani, haka na kwana ba dad'i Washe gari kuwa daga makaranta ina fitowa lecture ta farko na tafi asibitin, anyi scanning sukace awa biyu in jirasu, school na koma awa biyun na koma,kai tsaye likita ya tabbatar min ina d'auke da cikin sati goma,amma cikin wasa yakeyi in ba'ai da gaske ba zai b'are ne tunda ina zubar da wannan jinin kad'an lokaci lokaci, bayanin yanda zan kula da kaina da cikin yamin sannan ya rubutamin wasu uban magunguna harda ba k'arin jini.


Da k'yar na k'ara sa ga mota ta ina shiga na dafe kaina duk ilahirin jikina rawa yake gabana na fad'uwa ban San halin da nake ciki ba, tunani nake ya zanyi in wannan labarin yaje ga kunnan umar me zai biyo baya yaya rayuwar Abunda zan aura zata kasance tunda uban bai so bai marmarin samun d'a yanzu,to shinma cikin zai zaunane tunda likita yace min rawa yake bai zama lalle yai k'wari ba,innalillahi wa inna ilaihi ra'jiun ina mafita ga rayuwata ni Khadeejah shafa fatar cikin cikina nai ina jin wata nutsuwa na saukar min in har Allah ya bani d'a ko y'a a wannan rayuwar ya gama min komai kawai sai dai in nemi lahira.






_Shin_ _ya_ _zata_ _kaya_ _ne_ _da_ _wannan_ _cikin_ ?πŸ€”





Y'an uwa mu had'u bayan salla insha Allah, ibadar da zamu shiga ibada ce wadda me rabo ke riskarta,muna rok'on uban giji ya datar damu ya samu cikin y'antattun bayin saπŸ™










Taku ce
Layuza kabir AdamπŸ™‹β€β™€
https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation?


🍑🍑🍑 🌸🌸🌸🌸
🌸 *'YAN ARABIC* 🌸


NA

LAYUZA KABIR ADAM

DEDECATED TO ALL
ARABIC /ISLAMIC STUDENTS
πŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“š

πŸ‘¨πŸ»β€πŸ’»πŸ‘©πŸ»β€πŸ’»
*ZAMANI WRITERS ASSOCIOTION*

πŸ“
​​WΙ› Ι‘Κ€Ι› Ι¦Ι›Κ€Ι› tΡ³ Ι›Ι—ucΙ‘tΙ›, MΡ³tiΡ΅Ι‘tΙ› Ι‘Ι³Ι— Ι›Ι³tΙ›Κ€tΙ‘iΙ³ Ρ³uΚ€ ʀɛɑɗɛʀร​


Masha Allah fan's ina fatan munyi salla lafiya,Allah ya karb'i ibadun mu ya maimaita manaπŸ‘



0⃣4⃣6⃣




Da k'yar na kai kaina gida don banma bi ta kan wata skl ba, key nasa na bud'e pat d'ina na shiga duk kayan hannuna na watsar na fad'a kujera na kwanta dafe da kaina,zuciyata ta cushe nama rasa wane tunani ne zanyi, Meye mafita meye madafa gareni,me zanyi dariya ko kuka, tabbas ya dace inyi dariyar rabauta da samun ciki don baiwa ce me girma gareni,kuma tabbas ya dace inyi kukan makoma a wajan mijina sa'ilin da yai karo da wannan zancan, tunda bai so bai marmari, sama da awa guda ina kokawa da zuciyata wajan samowa kaina mafita amma hakan bai yuyu ba,daga bisani Allah ya taimakeni bacci me nauyi yai gaba dani Wanda ya d'aukeni har tsawon awa uku,sanda na farka k'arfe biyu a kasalance na tashi na daddafa zuwa toilet wanka nai tare da d'auro Alwala, Sallar azahar nai nan na zauna ina godiya ga Allah bisa kyautar dayamin sannan nakai kukana gun sa don ya share min hawayena ya dasawa mijina k'aunar haihuwa ya samai farin ciki a lokacin da wannan labarin zai riskeshi.


Yau kam haka na yini sukuku ba wani kuzari y'an class d'in mu suka kirani jin shiru ban dawoba nace musu banjin dad'i na wuce gida, lokacin da sweety ma ta shigo ta taddani zaune na rafka tagumi tace yadai D'an sakin fuska nai nace mata ba komai kawai kaina ke damuna da ciwo tace to insha magani nace mata nasha kawai, haka nakai har dare ba sukuni,ko UK daya kirani ina yin sallama ya fuskanci da damuwa tambaya ta ya shigayi meye damuwata ,shima cemai nai gajiyan skl ce ta samin ciwon kai kuma nasha magani bacci ma nakeji, sallama yamin yace in bacci na kawai da safe ma had'u,daman hakan nafi buk'ata don haka na kashe wayan na kwanta zuciyata cike da tunani.


Da safe dana tashi na d'anji sassaucin zuciyata don haka na lallab'a na tafi skl, ban wani sakeba haka dai ganinan har k'awayena na fadin in koma gida tunda banjin dad'i nace musu kawai ba komai zan iya, ana tashi kuwa daga skl d'in na biya pharmacy nasai magungunan da likitan ya rubutamin sannan nayo gida.


Tunda na fara shan magungunan sai naji jikina yamin dad'i na Sami k'arfi sannan ciwon kanma na dainaji, tunfa daga nan kuma sai lafiya ta wadaceni sosai don haka na tabbatar magungunan sun karb'eni k'ara dagewa nai da shansu ban wasa ko kad'an, zancan damuwa kuwa na yakicewa zuciyata na fidda abun a raina, na k'udurtawa kaina bazan tab'a fad'awa mijina inada ciki ba,kowa ma bazan fad'a mai ba, sai randa ya fito kowa ya gani, a lokacin kuma zan shirya karb'ar duk wani hukunci daga me cikin wato uk.


Maida kai nai sosai a karatuna don semester d'in mu ta k'arshe ce, kuma babu sauk'i a exam's na tabbata, b'angare d'aya ina k'ara godewa Allah daya wadatani da lfy duk irin wannan laulayin na masu ciki banayi ciwon kanma tunda na fara shan magungunan nan ya kama gabansa,har wani kuzari nakeji a jikina koda yaushe, hakan yasa na k'ara sakewa da mijina koda yaushe d'inke muke muna k'ara narkewa cikin k'aunar juna, shirin da yake na zuwa kawo mana ziyara ya rushe dalilin matsesu da akai skl ana turasu camfanoni da yawa yanzu basa zama ma cikin skl d'in don haka koda ya nemi excuse ma basu bashi ba,lokacin da yake fad'amin kamar zai kuka cike da b'acin rai yake, dukda nima naji ba dad'i don ina buk'atar mijina amma sai na riski kaina da farin ciki don koba komai hakan zai k'ara b'oyar min da cikina,duk da yanzu ya haura wata uku amma ko kad'an bai wani fara fitowa ba,amma amma inajin motsinsa kad'an kad'an kuma Ina yawon zuwa ganin likita yana tabbatar min da lafiyarsa, maida kai nai naita bashi hak'uri da nuna mai damuwa ta don karya fahimci wani abu har kuka nai wai na gama shrin taransa,daga baya shi ya juya da rarrashina haka muka gama nunawa juna damuwar mu muka hak'ura,nace mai ba komai ai saura k'iris ma ya dawo duka bai wuce wata biyar ba su dawo gaba d'aya.



**********BAYAN WATA BUYU

Biki ne ya taso mana a gida Sakkwato na y'ar yayan mune, na shiryawa bikin nan don na dad'e banje sakkwato ba,don haka naketa d'oki dukda kwana uku kawai zanyi in dawo sabida Satin zamu fara final exam's, Su sweety kuwa tuni ma sukai graduation Tafiya service kawai ya rage musu,don haka muka shirya tafiyan har ita, nai rawar gani sosai a bikin nan sabida duk gidan mu daman Aunty ce mijinta baida wani k'arfi kuma ga girma ya kamashi don tsoho ne ,don haka lokacin da muke waya da Mamana take fad'amin zancan take sanar dani yayyan mune mazama sukaiwa Amaryar kayan d'aki don Babanta bai dashi,tausayin sune ya kamani nacewa Mamana zan kira Auntyn A waya inji me suke buk'ata, ai kuwa na kirata bayan mun gaisa nake tambayarta ya shirin biki tace Alhamdulillah anatayi,na rasa ma me zan tambayeta suke buk'ata Auntyn mu tanada y'ay'a manya duk mata Wanda duk suke gidan miji k'ananan ne maza, don haka y'ar ta ta uku itace ma sa'ata shiyasa muka d'auketa tamkar uwa,jin nauyin tambayarta halin da suke ciki nake don haka nace ta bawa Amaryar wayar muyi magana,Bayan mun gaisa nace "Ummy ya shirin biki ina fatan an gama da komai ko".

Jim tai sannan tace " Eh Aunty Nahna wlh su Yaya Babba duk sun min kayan d'aki komai na d'aki sunmin ".

" OK to b'angaran kitchen fa?"

Shiru tai na d'an lokaci sannan tace "suma d'in su Aunty juwairiyya sunata k'ok'ari wlh yanzu gas ne ya rage da sauran d'an abunda ba'a rasaba".

" ok ba damuwa ki turomin account number d'inki zan miki transfer kud'i sai asai abunda ba'a k'arasa ba".


Godiya tai tamin nidai na kashe wayan ina tunanin nawa ya dace in tura musu,k'arar shigowan account number d'in ne yasa na d'auki wayan tunanin in tura musu 100k nai don haka nai musu transfer d'in dubu d'arin ai kuwa yana shiga ta kirani da murna tana godiya sannan ta bawa Auntyn itama taitamin godiya.


******
Ranar Alhamis muka d'au hanya ni sweety Aunty Hafsa da yara Sai Aunty Amrah, mota Babba Abban su sweety ya bayar akaimu,don haka tafiya mukai cikin nutsuwa kuma cikin d'an lokaci muka isa, kamar yanda muka saba a gidan mu muka sauka, tara me kyau muka samu daga y'an tsofaffin iyayen mu da sauran jikoki da masu aikin gidan bayan mun huta munci abunci tare da salla muka wuce gidan bikin tunda ranar aka fara bikin, tofa tunda muka shiga cikin dangi kowa ke tofa albarkacin bakinsa akaina,wai na canja nai k'iba nai wani asirtaccan kyau tabbas ba makawa ciki gareni, haka suketa fad'i nidai mirmishi kawai nake ina kauda zancan

Haka akai kamu ranar akasa amarya a lalle,da dare gida mukayo duka anan muka kwana,washe gari kuma Amarya tai yinita da k'awayenta Wanda shima ya k'ayatar dukda ba wata k'arya akaiba dai dai gwargwado akai komai,washe gari kuwa ranar Asabar aka d'aura Aure akai yini tare da kai Amarya,to Aranar Asabar d'in ne kuma har naji gidan bikin ya isheni yanda naji zancan inada ciki ya karad'e danginmu kaf kowa ca yake zaizo kano suna in Allah ya saukeni lfy,abun ya wuce inyi musu tunda harda iyayena cikin masu zancan, gashi sunata tambayar Aunty Hafsah amma itama sai tace tana kyautata zaton hakan dukda ban sanar mataba,wata mata dake gun take fadin "Toku banda abinku ai da ganin Khadeejah babu tambaya kunsan ciki gareta gashinan dukta d'anyace alamu k'arara sun nuna, kila irin cikin y'an gidanku zatayo b'oyayye tunda duk kanku sai cikinku yakai kusan watannin bakwai cikin na takwas yake fitowa".
kunyace matuk'a ta rufeni da kalaman ta don haka na tashi tsam na bar gun,ina tskaicin mutane masu surutu haka.

Daran Asabar d'in muna kwance d'akin da muka sauka su Aunty Hafsah da Aunty Amrah duk sunyi bacci saini da sweety ni ina waya da mijina ita kuma tana chatting, bayan na kashe wayan sweety ta zubamin ido tana kallon na,ganin tak'i kauda kai nace " emmata yada kallo haka".


D'an mirmishi tai ta tashi zaune tana fadin "Aunty nah ashe yardar dake tsakanin mu bai kai insan kinada ciki ba har sai a sakkwato zanji".

D'an zaro ido nai cikin basarwa nace" Au wai ke yarda kikai da wannan maganar? Lalle sun ruftaki yasin taya zan samu ciki mijina na India ni ina Nigeria kawau surutun sune fa".

"A'a don mijinki na India ai kinje wajan sa munsan a can aka samu ai".

Dariya sosai nai sannan nace " yanzu watana nawa da dawowa daga India sweety ,ki lissafa inda na sami cikin tun a can aida tuni yanzu ya fito kowa ya ganshi zuwa yanzu au yaci ace ya girma ko".

Tsam tai da ranta tana tunanin can tace "gaskiya kam nima saida nai wannan tunanin kuma gashi ni banga kina laulayin da masu ciki keyiba,kinga babu yanda za'ai ai ciki ba laulayi".

Dunk'ule hannu na nai alaman jinjina nace " yawwa y'ar uwa kema kin gano Ashe,kawai wai da anga mutum yai kyau yayi k'iba sai a jawomai ciki,surutu ne bai ishesu ba sai suje suyitayi au".
Da haka na bagarar Da ita muka shiga wani zancan,

Washe gari da sassafe driver daya kawomu yazo d'aukan mu,muka d'auko hanya.


*****
Tun daga nan zancan cikina ya dasu a danginmu kowa ya sani, ita kuwa sweety tun acan tabar zancan don ta yarda da abunda na fad'a mata.



Kwanan mu uku da dawowa na dawo daga skl a gajiye ina zaune kan kujerar ina hutawa sweety ta shiga kitchen kawo min abunci, wayata ce tai ringing ina d'agawa naga sunan Aunty Hafsa,d'agawa nai da sallama ina fad'in "Aunty nah ya gidan".

" lfy qlau Nahna ya exam d'in ?".

"Alhamdulillah Aunty yanzuma na dawo gidan wlh".

" To Allah ya bada sa'a, daman wata magana nake son muyi ".

" Tom Aunty ina sauraranki".

"Cikin ki wata nawa ne Nahna ".

Dammm naji gabana ya fad'i ina k'ok'arin mata musu ta dakatar dani " ban son musu Nahna fad'a min kawai wata nawa ne banga abun b'oye b'oye bafa".

Cikin tsananin jin kunya nace "Aunty wata biyar ne ".

" yawwa daman nima hakan nake tunani zan sanar da yayan ki ne daman ".

" wayyo Allah Aunty don Allah karki fad'a mai wlh Allah kunya nakeji kibar maganar kawai iya mu".

Dariya tai kawai tace "To na barta kinji, amma ki rink'a kula da kanki ki rink'a cin abunci masu kyau sosai".

Dabarun kula da kaina taita bani da nai maita godiya muka kashe wayan.


Ina d'agowa idona caraf cikin na Sweety tana tsaye rik'e da flat d'in abinci kallo take min me cike da tuhuma hakan ya tabbatar min taji hiran mu da Aunty tunda a free nasata, cikin yanayin damuwa tace "Ban kai nasan kina da ciki ba Nahna matsayi na bai kai mu raba farin ciki dake ba".

Tana kaiwa nan ta shige d'aki,ni kuwa zama nai jigum ina nazarin maganar ta,ita sweety bata San me yasa nake b'oye zancan cikin nan ba,amma dukda haka nasan baza taji dad'i ba, mik'ewa nai na bita d'akin turus nai ganin tana ta had'a kayanta waje guda,da sauri na k'arasa gareta tare da dafa bayan ta,bata jiyo ta kalleni ba illa k'ara tsuke fuska datai, cikin sigar rarrashi na fara magana" haba sis me yasa zakiyi fishi dani me yasa kike had'a kayanki? Kina nufin barin b'angaran nan zakiyi ki kome".

Muryanta na rawa tace "me yasa bazan koma part d'in muba me yasa zanci gaba da zama inda ba'a nemana, tun tuni na gane ni kad'ai ce nake son zama dake Nake iya raba damuwa ta da farin cikina tare dake, sirrina duka ina sanar miki amma ke akasin haka ne,koda yaushe b'oyemin sirrinki kikeyi me yasa? Yanzu ina tunanin ina cikin sahun mutane na farko da zansan kinada ciki amma lokacin danaji hakan ma daga bakin family d'in ki sai kika musa min kika b'oye min, me nai miki Nahna?".

Rasa abunda zance mata nai don haka na k'ara k'ank'ame hannun ta cikin nawa a hankali nake matsa hannun nata alaman rarrashi,a sannu na fara magana yanda zata fahimceni tsaf na kwashe dalilin b'oye cikin na fad'a mata,na sanar da ita ra'ayin yayan nata akan ciki da haihuwa, idon ta cikin nawa cike da tausayi tace " na fahimceki Aunty nah kuma na gamsu da hujjarki,amma kuma randa ya sani ya zakiyi kuma kina sane yaya zai dawo k'asar nan kafin wata hud'u zaizo ya riski ciki jikin ki,kuma yanzu zakita zama ne da ciki Abban bai sani ba,tabbas bazaiji dad'i ba randa duk yaji kin b'oye mai duk da kema da taki hujjar".

"Sweety ban san yanda zanyi ba wlh,ina son mijina ina son zama da mijina,sannan ina tsananin son cikina Allah ya jarrabeni da son haihuwa bazan iya yiwa Umar biyayya kan gujewa haihuwa ba,kuma tabbas zuwa yanzu zuciya ta taf take da k'aunar mijina da son zama dashi, damuwa ta ban san ya zaman mu zai kasance ba duk randa yasan wannan maganar".

Dafa kafada ta tai tace " ki kwantar da hankalinki Aunty nah insha Allah duk randa broth ya samu labarin cikin nan ko ya ganshi da idonsa zai kasance cikin farin ciki zaiyi murna, yanzu abunda nakeso dake zan sanar da Abba kinada ciki don inyaji bazaiji dad'i ba,amma zan fad'a masa karya sanar da Broth sabida biki fad'a mai ba har yanzu sabida kina son surprise d'insa ne duk randa ya dawo k'asar nan, nasan indai na fad'a mishi haka bazai tab'a mai maganar ba,duk dai dabaran da zanyi zanyi in sanar da Abban kinji "

Gyad'a kai nai cikin rashin gamsuwa don nidai tabbas nasan indai Maganar nan ta shiga cikin gidan su sweety to kamar yaji ne.

Haka dai na tashi zuwa d'aki jiki ba dad'i zuciyata cike da wasi wasi.





Taku ce
'Yar mutan Ja'ojiπŸ™‹
https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation?

🍑🍑🍑 🍑🍑🍑
🌸🌸 🌸🌸🌸🌸
*'YAN ARABIC*
🌸🌸🌸🌸🌸🌸
🍑🍑🍑🍑🍑🍑

*NA*

*LAYUZA* *KABIR* *ADAM*


DEDECATED TO ALL
ARABIC /ISLAMIC STUDENTS
πŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“š

πŸ‘¨πŸ»β€πŸ’»πŸ‘©πŸ»β€πŸ’»
*ZAMANI WRITERS ASSOCIOTION*

πŸ“
​​WΙ› Ι‘Κ€Ι› Ι¦Ι›Κ€Ι› tΡ³ Ι›Ι—ucΙ‘tΙ›, MΡ³tiΡ΅Ι‘tΙ› Ι‘Ι³Ι— Ι›Ι³tΙ›Κ€tΙ‘iΙ³ Ρ³uΚ€ ʀɛɑɗɛʀร​



*Ina* *barar* *addu'arku* *y'an* *uwa*



0⃣4⃣7⃣




Bayan sallar isha'i Abba na zaune a parlourn sa news yake dubawa sweety tai sallama ta shiga fuskarta d'auke da fara'a,amsa mata yai shima cikin fara'ar yace "sweety nah duk yanda akai akwai labari me dad'i "

Kusa dashi taje ta zauna yana dariya tace "Abba nazo da labari me dad'i kam,amma sai ka bani goron albishir".

Kamo hannun ta yai yana gyara zama yace" Tom na amince maza fad'a min albishir d'in zan baki goro me tsoka ".


" Tom amma Abba ina son kamin wani alk'awari kafin in sanar dakai".

"Kai Sweety nah wai wannan wane irin labari ne me dad'i haka da aketa jan sa".

Dariya tayi tace " Abba kamin alk'awarin in dai na fad'a maka bazaka fad'awa Broth ba".

Da sauri ya kalleta yace "wane abun farin ciki da zaki sanar min kuma kice bakya son d'an uwanki ya Sani,me yasa".


" Abba akwai lokacin da aka tsara zai sani din amma ba yanzu ba ".

" ok to fad'a min ina sauraranki maza".


Gyara zama ta k'ara yi sannan tace "Abba zaka samu jika ta b'angaran broth da Aunty Khadeejah soon".

Da sauri ya kalleta yace " yimin bayani sosai in fahimta mana"

"Abba Ina nufin Aunty Khadeejah tanada ciki na 5 months tun dawowar ta daga India".

Cikin tsananin farin ciki yace " Alhamdulillah, Allah abun godiya ,amma ya akai ban sani ba tuntuni sai yanzu".


"Yawwa Abba anzo inda nakeson azo d'in,kaga nima ban sani ba sai yau Aunty Khadeejah tayi surprise d'in mune, mu duka shiyasa ta b'oye mana bama muba har family nata duk yanzu ne suka San da wannan zancan ,amma ta rok'eni kar mu bari don Allah broth ya sani sabida tana son ranar dawowar sa ya zama shine abunda zata tareshi dashi na gitf,tana son sai a ranar daya dawo zai sani kaima tace inna fad'a maka don Allah ince ma karka fad'a mishi haka tace in fad'awa Aunty murjah".

Dariya Abba yake cike da farin ciki yana godiya ga Allah, Abunka da d'an boko sai ya d'au zancan yiwa UK surprise shima a abun burgewa da k'ayatarwa a duk sa'ar da UK d'in ya shigo k'asar, suna cikin haka Aunty murja ta shigo ganin farin ciki k'arara shimfid'e kan fuskar Abba yasa itama fad'ad'a fara'arta tana zama gefansa take cewa " Alhaji na meya samu ne irin wannan bayyanannan farin ciki haka".


Rik'o hannun ta yai yana fad'in "Abun murna da farin ciki ne suka riskemu murjah ashe Khadeejah ciki gareta tun dawowar ta daga India yanzu cikin watansa biyar ".

Fad'ad'a fara'arta itama tayi tace " kai an gode Allah masha Allah, amma shine sweety keda ita buku tab'a fad'awa kowa ba har zuwa wannan lokacin".

"A'a Aunty nima yau na samu zancan akwai dalilin dayasa ta b'oye".

Nan ta fad'a mata dalilin itama tace
" to ai shike nan indai duk suna cikin k'oshin lfy itada cikin,amma Alhj in Allah ya kaimu gobe sai muje asibiti likita ya dubata sosai sannan

Please Login or Register in order to submit comment