Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

hankali matata wlh har zuciyata ta fara bugawa bai tunanin ko wani abune ya sameki naga inata kiran wayarki baki d'aga ba ,gashi bikizo d'auka na ba harna fara tunanin in hau motan friend d'ina ya saukeni sai kuma gaki".


Danne fishina nai na k'ak'alo mirmishin k'arfin hali nace " Sorry dear aikine ya rik'eni ina kitchen banga kiran ba saida na fito kuma kafin in shirya lokaci ya tafi ".

Ajiyar zuciya ya sauke yana rungumeni yace " Har hankalina ya kwanta,amma da kam zuciyata ta fara shiga rud'u".

Dakewa nai nace "oh Reality d'an cikani mu k'arasa gida tukun".


Janyewa yai yana mirmishi yace " amma kodm d'an kiss bikiyimin ba"

D'an kissing d'inshi nai na tada motar muka fita a skl d'in hannunsa na jikina ".





Koda mukaje gida danne zuciyata nai tayi don nafison inyi kishi me aji na Wanda tasan me takeyi,don haka kamar yanda na saba mai komai haka na taimaka mai yai wanka mukai salla koda mukazo cin abunci yanda muka saba haka nai mai,amma me wai duk wannan daurewar da nake ina sawa zuciyata k'warin gwiwa ya fuskanci akwai wani abu a k'ark'ashin raina don haka ya kamoni jikinsa tare dayin k'asa da murya yace " My khadeey wai meke faruwa ko bakida lfy ne naga kamar yanayinki ya d'an canja".

K'ak'alo mirmishi nai nace "a'a ba komai lfy ta qlau kawai dai ajizancine irin na D'an Adam".

Shafa kaina yai yana fad'in " indai bakyajin dad'i dai ki sanar dani muje kiga doctor ".


Bance komai ba sai d'an mirmishi na kamo gemun sa ina d'an wasa dashi.




Da yamma yace muje mu d'an zaga gari ko zan dawo normal, kallon sa nai nace " Bafa komai dear ba abunda ke damuna".


Dagewa yai shidai mu fita inga k'ara ganin gari,ban soba don zuciyata banjin dad'inta haka na daure na shirya muka fice, shike driving d'in muna tafe muna d'an hiranmu, wajan shan iska ya kaimu muka samu gefe guda kusa da wani ruwa muka zauna, wajan yamin dad'i yanda k'amshin furannin ke tashi a wajan ga wata iska me sanyi dake ratsa mutum ga ruwa nata gudu ta cikin duwatsu,hakan yasa naji duk wani bak'in cikina ya yaye nishad'i ya mamaye zuciyata, hiranmu muke irinta Masoya cike da shauk'i muna shan ice cream, kujera d'aya muke zaune don haka ne muke manne da juna, yana tsokanata yakai ice cream d'in bakin sa ashe cokalin bai saitu ba ya b'ata mai suk gashin bakinsa har gemu,dariya nake sosai ina tafaโ€น hannu,cikin wasa yasha mur yana fad'in "kin sa na b'ata bakina kuma kina min dariya ko zan kamaki".


Cikin dariya na kamo camera d'in wayata na shiga buga mana selfie ina dariya, ganin dariyar tawa tak'i k'arewa yasa ya kamoni ya matseni cikin jikin sa, cikin tun tsira da'riya nake fad'in " tsaya tsaya in goge maka kaji na daina ".

Sassauta rik'on da yai min yai a hankali nasa harshena na shiga lashe suk inda ice cream d'in ya tab'a,lumshe ido ya shigayi yana wani k'ara rik'eni,d'an janyewa nai ganin ya fara tafiya wata nahiyar don nasan ya manta ba a gida muke ba.



Fadhal wacce take zaune can nesa damu tana kallon duk abunda mukeyi zuciyar ta ta gama kumbura,don tun fitarmu daga gida akan idon ta ta fito zata unguwa taga tashin motar mu haka kawai taji ziciyarta ta raya mata tabi sahunmu don haka a hankali taita binmu har gun,koda mukaje tai nesa inda bazamu gantaba amma ita tana kallon duk motsinmu, abunda muke yasa take ganin ma kamar ma da gayya muke don haka zuciyarta ta rink'a k'issima mata taje ta shak'oni kawai wata zuciyar kuma tace zuwa zaki ki wargatsa wannan farin cikin da suke ciki ki haddasa fitina a tsakanin su,da wannan shawarar tai amfani ta mik'e kai tsaye tayo gurinmu.

Nuna mai pic's d'in nake shima yanata dariya kawai mukaga mace tazo ta zauna a kujerar dake daura da tamu ta d'ora k'afa d'aya kan d'aya tana kad'asu cikin wata lank'washashahiyar murya tace " my hubbey ashe kana nan kana shan iska,yanzu na k'araso wajan kawai naji k'amshin turarenka,nan zuciyata ta tabbatar min kana gun ina wara idanuwa kuwa na hangoka".

Tamke fuska yai matuk'a yace "Ke fadlah wai wace irin mace ce me zuciyar tunkiyoyi,me ya kawoki nan eh".

Kad'a ido tai cikin iya duniya tace " Ah kasan mun saba zuwa wajan nan dakai ko wace yammaci,to kwana biyun ma da k'arfen k'afa tazo maka in kewarka ta dameni sai inzo in d'ansha iska d'azu da safe ma naje gida Neman ka don idona yana tsananin son kallonka a lokacin amma waccan tace min wai kana bacci ta hanani ganin ka , yau kuma sai gashi mun had'u,gaskiya my heart nayi missing d'inka sosai fa,ka gane kawai ta fad'a tana kashe mai ido ".


Mik'ewa yai cikin zafin nama zai kwasheta da mari yana fad'in" ke ni zaki rainawa hankali,yaushe muka tab'a zuwa nan dake don uwarki,banza mayya na fad'a miki bazan aurekiba bazan iya auranki ba,inada mata ta data fiki komai kuma dukkan zuciyata tata ce,babu wani sauran wajan wata mace a cikin ta".

Kamoshi nai ganin yanda yake balbala masifa na kashe murya cikin salona "haba Reality me yasa kake tada jijiyoyin ka akan d'an wannan maganar,don Allah karka wahalarmin da kanka kasa b'acin rai aranka,kan abunda bai kai ya kawo ba, cool down my man, muje gida kawai don ina buk'atar hutawa a jikin ka kaji shimfid'ata mayafina farin cikina".

Na k'arasa ina manna mishi kiss a leb'ansa naja hannunsa mukai parking lot don d'aukan motar mu, muna tafiya ina jiyo muryan ta tanata bala'i tana fad'in " Banza munafikin mata,sau nawa kake fad'awa duniya babu abunda zakai da mace kalar wannan kai mijin wayayyiyar mace ne,kullum fad'a kake auran dole akaima amma don munafirci shine yanzu a gabanta kake fad'in itace zab'inka".


Fizge hannunsa yai zai koma nai saurin rik'oshi fuskata a d'aure nace "kome tace kai kaja tunda kana mu'amala da ita don haka bakada bakin cewa komai yanzu, ni ka maidani gida in zaka dawo sai ka dawo".


Ina fad'a na bud'e mirfin motar na shige, jiki a sanyaye ya bud'e shima ya shigo, bayan yayi wa motar key mun d'au hanya sosai ya sako hannun shi zai kama nawa na janye ina kauda idona zuwa kallon titi, kallona yai yaga yanda na k'ara tsare gida nan jikinsa ya k'ara yin sanyi cikin sanyayyar murya yace " kar kiyi fishi dani zuciyata karki yarda da maganar wannan mahaukaciyar yarinyar".

Katseshi nai da sauri ta hanyar d'aga hannun nace "ka bar wannan maganar don Allah bana buk'atar jinta ko kad'an don na riga na gama jin komai daga bakinta kuma".

Jan bakinsa yai yai shiru yana tunanin irin hukunci da zai d'auka akan fadlah data had'a mai wannan gwaramar.











Taku ce
Layuza kabir Adam๐Ÿ™‹โ€โ™€
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*โ€‹

_*Wษ› ษ‘ส€ษ› ษฆษ›ส€ษ› tัณ ษ›ษ—ucษ‘tษ›, Mัณtiัตษ‘tษ› ษ‘ษณษ— ษ›ษณtษ›ส€tษ‘iษณ ัณuส€ ส€ษ›ษ‘ษ—ษ›ส€เธฃ*_

https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation?





๐Ÿก๐Ÿก๐Ÿก ๐Ÿก๐Ÿก๐Ÿก
๐ŸŒธ๐ŸŒธ ๐ŸŒธ๐ŸŒธ๐ŸŒธ๐ŸŒธ
*'YAN ARABIC*
๐ŸŒธ๐ŸŒธ๐ŸŒธ๐ŸŒธ๐ŸŒธ๐ŸŒธ
๐Ÿก๐Ÿก๐Ÿก๐Ÿก๐Ÿก๐Ÿก

*NA*

*LAYUZA* *KABIR* *ADAM*


DEDECATED TO ALL
ARABIC /ISLAMIC STUDENTS
๐Ÿ“š๐Ÿ“š๐Ÿ“š๐Ÿ“š๐Ÿ“š๐Ÿ“š๐Ÿ“š๐Ÿ“š

๐Ÿ‘จ๐Ÿปโ€๐Ÿ’ป๐Ÿ‘ฉ๐Ÿปโ€๐Ÿ’ป
*ZAMANI WRITERS ASSOCIOTION*

๐Ÿ“
โ€‹โ€‹Wษ› ษ‘ส€ษ› ษฆษ›ส€ษ› tัณ ษ›ษ—ucษ‘tษ›, Mัณtiัตษ‘tษ› ษ‘ษณษ— ษ›ษณtษ›ส€tษ‘iษณ ัณuส€ ส€ษ›ษ‘ษ—ษ›ส€เธฃโ€‹



0โƒฃ4โƒฃ4โƒฃ



A haka muka k'arasa gida kowa zuciya ba dad'i, Allah yasa muna shigama ana kiran magriba don haka hankalinmu ya koma gayin salla,yana fita masallaci na tada tawa a cikin sallar nake kaiwa Allah kuka kan ya tsare kuma ya kare min mijina ya tsareshi daga sharrin masharratan mata,harya dawo ina zaune kan prayer mat d'in ina y'an addu'o'i na,ganin yazo ya Sani a gaba yasa na shafa na tashi, fuska ba walwala,cire kayan sallar nai na d'auko wata figigiyar riga nasa,kai tsaye na wuce kitchen na had'a mana abuncin dana girka kafin mu fita, bayan na gama jera komai na shigo d'akin taddashi nai kwance ya dafe kansa yana tunanin, a d'an dake nace " na shirya abinci".

Shiru bai ce komai ba,ganin ina tsaye shiru kawai na juya zan fita, cikin sanyin murya yace "Deejahhh ".

Ban amsa ba kuma ban juyoba,sai dai tsayawa danai cak, a hankali naji ya taso yana taho wa, had'a ni yai da jikinsa yana k'ok'arin juyo dani,a hankali na lumshe idona don ban sonma k'wayar idona ta shiga cikin tashi, zubawa fuskata ido yai yana nazarin canjawa ta lokaci guda,

" my Deejahhh don Allah ki tsaya ki saurreni,ki tsaya na fad'a miki tsakanina da yarinyar nan kinji".

D'an zamewa nai ina kauda idona nace "ka bar wannan maganar fa ta riga ta wuce,muje muci abinci kawai".
Ina fad'a na rik'o hannunsa zuwa parlourn.


Abincina nakeci hankali kwance shi kuwa sai juya cokalin yake yana d'iba sama sama,fuskarsa cike taf da damuwa


Nasan shi sarai bai wasa da cikinsa ko kad'an don haka yau yanda naga yana cin abuncin sai yaso ya karyamin zuciya,amma wani tunanin danai saina dake,tashi kawai nai naje na wanke bakina na dawo har lokacin bai wani ci abun kirki ba, zama nai na jawo abincin gabana nasa spoon d'in na fara bashi da kaina, kamar wani lusarin yaro haka yake k'arb'ar abincin yanaci,saida na tabbatar yaje gejin dayake k'oshi sannan na ajiye na bashi lemon yasha.

Kayan na had'a nakai kitchen, ya san saina wankesu tas zan fito don haka yabiyo bayana, kamar yanda muka saba ina wankewa yana kifemin su, harna gama na gyara wajan, lokacin sallar isha'i yayi don muna fitowa na wuce toilet na d'aura alwala, shi kam kuskure bakinsa yai don yanada alwalar sa yayi masallaci ni kuma na tada tawa.







Ranar haka muka kwana kowa da tunanin dake ransa,amma duk da haka bamu nisanci junaba a gado,duk da ba wai yanda muka saba nanike juna mukai ba,amma kawunanmu na jere kan pillow d'aya muna shak'ar numfashin juna.



******

Duk fa yanda UK yaso tada zancan nan nak'i bashi dama,koya d'auko maganar sai ince ya wuce yabar zancen,duk hankalinsa yak'i kwanciya ko school ya daina shiga in nace mai school sai yace bazaijeba, nikuwa in shareshi abuna, amma duk abunda yake na hak'k'insa zan mai ko a gado ya nemeni zan bashi had'in kai sosai musha k'aunar mu,ammafa da safe ba fara'a, wato shiruma amsa ce, hukuncin shiru yafi komai hukuntawa, shi anashi b'angaran yafiso in tsaya muyi maganar baki da baki ya fad'a min ko wace Fadlah don yasan maganganun datai a gabana zai samin zargin ko nemanta yake Wanda shi yafi d'aga hankalinsa.

Kwana biyar muka d'auka cikin wannan yanayin, Wanda harya fad'a sabida rashin nutsuwa rashin ganin fara'a ta walwalata kad'ai yasa shi rama,yama rasa ya zaiyi da ransa, ban tab'a tunanin a zahiri haka mijina ke sona ba sai yanzu na tabbatar kuma na gasgata don haka yau kam na d'au aniyar kwantar mai da hankali duk da tsananin kishin fadlah na zuciyata.



Bayan sallar isha ya shigo jiki a sab'ule hannayena d'auke da ledoji,ya zubesu tsakiyar parlour, ina zaune kan kujera two seater hankalina nakan T.V ,jikina sanye da riga da wando kalan peak da fari na roba sun kama jikina tsam rabin albarkatun k'irjina a waje suke ga mazaunaina sun matse cikin wandon wanda yake iya gwiwata rigar ma hannunta iya dantsena yake, kaina babu hula sai gashina dana fakeshi nasa masa ribbon fari.

D'an d'ago da kaina nai na kalleshi fuskata ba yabo ba fallasa,nace mai "welcome dear".

K'arasowa yai kusa dani ya duk'o tare da kissing d'in lips d'ina yana shafa gefan fuskata yace" sannu da hutawa my Deejah sarauniyar mata".

D'an mirmishi kawai nai na mik'e ina fad'in "bari in baka lemo".

Ina tafiya ina kad'a mazaunaina don nasan idonsa na kaina,
Wata ajiyar zuciya ya sauke yana lasar lips d'in shi, tare da tunanin kalar baiwar jiki da Allah yai min,

Dawowa nai d'auke da Ruwa da lemo tare da glass cup akan flat zama nai kan hannun kujerar da yake kai na tsiya yamai lemon ina mik'a mai, idonsa akan k'irjina ya amsa cup d'in yanawa albarkatun k'irjina wani mayen kallo ganin yana neman zuba min lemon ajiki yasa cikin muryan shagwab'a nace " Wai kallon na mene haka Reality ?".

Lumshe idonsa yai yana D'an kurb'ar lemon, kad'an yasha ya mik'omin nasa hannu zan amsa ya damk'e hannun nawa cikin nashi yana busamin wata iska kan k'irjina,wata gwauruwar ajiyar zuciya na sauke ina fad'in "Yah ".

Hannunsa d'aya yasa ya fara shafo saman k'rjin nawa, yarr yarrr tsikan jikina ta tashi cup d'in dake hannunmu ban San ya akaiba kawai naji lemon ya zube a jikina y'ar k'ara nasa ina duba yanda lemon ya b'atamin kaya " wayyo Allah, Reality ji ka b'atamin kwalliya na ,Allah Allah ni bazan yaddaba ni ka biyani kayana".

Had'e hannayan sa yai alamar ban hak'uri yana marairaice fuska "pls pls my Deejah kece fa kika rikitani nama rasa me zanyi har cup d'in ya fad'i a jikin ki, pls kiyi hak'uri kinji my heart๐Ÿ‘ ".

Turo bakina gaba nai cikin salon shagwab'a nace " To to nidai na ciremin kayan kayi min wanka,sannan ka wanke min kayana".

Jiki na rawa yaji banza ta fad'i ya fara fad'in "To indai wannan ne karki damu duka zanyi kinji beauty nah".

Mik'ar dani tsaye yai ya fara k'ok'arin ciremin rigar, ni kuwa na wani saki jiki kamar yarinya, bayan ya cire rigar ya zagaya ya b'alle min bra d'in wowww nan fa kayan kallo suka bayyana,mai makon yaci gaba da aikinsa sai kawai naga yasa hannayensa biyu kan tweens d'ina yana musu shafar y'ay'an kyanwa,๐Ÿฏ


Bank'arewa nai na fara bubbuga k'afa Wanda hakan ya baya Boob's d'ina damar yin tsalle suma๐Ÿ™Š, luuu ya shagala da kallon su yana wani had'iyar yawu,ina sane naci gaba da tsallena ina yarfe hannu,
Ya ilahi ya furta lokacin da duk wani na'ura ta jikinsa ke had'a shock, idanuwana dake rufe na bud'e jin ya fizgoni jikinsa ya shiga shafa ni tako ina jikinsa na rawa, Kai namiji ma dai in ya shiga wannan level d'in zama mara hankali yake sam๐Ÿ˜ƒ,
Tuttureshi nake ina fad'in "nidai kaje kamin wanka na, ba haka nace kayi ba ".

Bai saurareniba yaci gaba da bidirinsa musamman a kan Na shanuna,jin dayai bakina yak'i mutuwa sai rigima nake mai,ya cafke harshena yai mai kyakyawon ladabtarwa,ai kuwa nai lif ina amsar hukunci ๐Ÿ™Š๐Ÿ˜‚.

To nidai ban San ya akaiba kawai na ganmu kwance kan 3 seater muna ta bitar karatu, hannayensa yasa ya zame 3 quarter wandon dake jikina, sai a sannan na tuna ashefa yau in up ne,don haka na rik'e hannayensa daga k'ok'arin da suke na zame D'an pant d'in, cikin muryar data ladaftu da zafafan darusa nace " Pls banida tsarki fa".

Bai yarda ba saida yasa hannu ya tab'o sannan ya maida hankalinsa ga sauran sassan jikina, had'in kan da bai zato ba ya samu don saida na tsotseshi tass na fitar mai da . . . . . .๐Ÿ˜œ , sannan muka saki juna muna maida numfashi me d'auke da dad'i da gajiya.



Sai bayan mintina goma sannan ya mik'e ya kamani mukai toilet, wanka yamin tass shima yayi sannan ya mik'omin pad d'ita nasa,muka fito, duk a gajiye muke nasa y'ar yaloluwar night gown na haye gado,shi kuwa fita yai parlour ya kashe duk kayan wuta,sannan ya dawo ya kashe na d'akin ya fad'o kan gadon yana fad'in "kai wannan yarinyar ta galabaitar dani fa,mirmishi nai ina juya bayana ya kamoni jikinsa yana dariya,a hankali yake shafa bayana zuwa gashina, ajiyar zuciya me cike fom da tsantsar son juna muke saukewa, a cikin wata cool voice yake fad'in " Nahna Khadeejah ki yafemin kinji,wlh Allah duk maganganun da fadlah ta fad'a kawai sharri tai min,ban tab'a koda rik'e hannun tab'a da sunan in kusanceta , nasan dai Best friend d'ina ce kafin muyi aure dake,amma tunda mukai aure babu jituwa tsakanina da ita,na fad'a mata bazan aure ta ba amma ita ta kafe, nan dai ya kwashe komai tsakaninsa da Fadlah ya zayyane su cikin kunnuwana, D'an mirmishi nai nace " karka damu my heart komai ya wuce kaji".

Albarka yaita samin har bacci ya d'aukemu.
Tun daga ranar kuma sai komai ya koma normal, muka ci gaba da shimfid'a soyayyarmu me tsayawa a rai, a haka kwana kin hutuna suka taho k'arewa nan kuma damuwa ta fara damun mu na rabuwa da juna,don tabbas zuciyoyinmu da jukkunan mu zasu d'an d'ana rashi, duk kwanakin nan haka muke yinsu cikin rashin sukuni, ganin damuwar da muke ciki nace mai zan k'ara sati guda ya zama sati bakwai kenan, murna kamar zaiyi me nan ya kira Abban sa ya fad'a masa zan k'ara sati d'aya Abban fad'a ya hau yana fad'in "karatunta fa ya zaka rik'e yarinya bayan ta koma school"

Marairece murya yai yace "Abba itace fa tace zata k'ara satin kuma tace kota koma school a satin farko lecture bata kankama ba".

Jin haka yasa Abban yace to ba komai.




***********
Siyayya sosai Yakemin ta tsaraba har ca nake tayi ya bari ya bari amma yak'i.


To duk da k'arin satin da muka samu gashi dai yau ya rage kwana biyu cal in tafi,da safe muna kwance kan gado ya hanani motsawa ko nan da can ya rukunkumeni a jikinsa yanata lallatsani, a hankali nace " mijina zanyi kewarka wadda ban san adadinta ba,zan shiga wani hali na rashin ka tare dani".

Shafo fuskata yai yana magana Wanda sai kai da gaskema zaka ji me yake fad'i " My Deejah duk yanda zakiyi kewana bai kai yanda zanyi nakiba,tun yanzu zuciyata ta gama raunana,wlh Allah ina ji araina zan hak'ura da wannan course d'in in biki mu koma gida muci gaba da rayuwar mu tare".

Girgiza kaina nai idona na zubda hawaye nace "a'a karka fad'i haka Reality, kaga kaci rabi fa muyi hak'uri kamar yaune zaka k'arasa wata bakwai d'in nan ka dawo gida".

" ina jin wannan wata bakwai d'in kamar shekara bakwai a zuciyata,tabbas nan da wata uku zanzo gida insha Allah ".

"Tom my ina sauraranka ina maraba da zuwanka kaji".

Haka mukaita musayar kalmomin da zamu kwantarwa da junan mu hankali, a ranar dai haka muka yini service har saida naji na gaji bazan iya k'arawa ba,don haka naita binsa da wasanni.

Da dare ma fita muka k'arayi yai min wasu siyayyar muna zagaye cikin mall d'in ne sai gamu gaban kayan baby haka kawai naji zuciyata ta kwad'aita da d'iban kayan don haka na shiga jidarsu kamar kamar me,yana can yana d'aukarwa sweety kaya ya zagayo ya ganni na cika kwando da kayan yara zuba min ido yai cikin mamaki ya jawoni jikinsa yana D'an mirmishi ya d'ora hab'ansa a saman kafad'ata " Deejah me zakiyi da kayan Baby haka".

D'an farrr nai da idona nace "Kasani ko kaina nake d'ibarwa".

Nan da nan naga yanayin fuskarsa ya canja ya shiga girgiza kai " a'a mukam baby ba yanzu ba wlh sai mun huta sosai,ko na dawo Nigeria sai mun sami kamar one year sannan zamu fara k'ok'arin samun Baby ko".

Wani dammmmm naji gabana ya fad'i, innalillahi wa inna ilaihi ra'jiun, wai daman wannan ak'idar UK ke da ita,lalle akwai gagarumar matsala a gabana,don gaskiya ni Allah ya halicci zuciyata da tsananin son yara,ina son haihuwa fisabilillah,don ko yanzu akace inada ciki zanyi farin ciki in godewa Allah, kai gaskiya duk randa Allah ya dawo da UK Nigeria saina yak'eshi akan wannan mummunar ak'idar".

Juyo dani yai ina kallon sa yace " ya naga kinyi shiru Baby nah".

Jarumta da dakiya na k'ak'alowa kaina na D'an saki mirmishi ina fad'in "Ah ba komai fatanmu dai Allah ya bamu masu albarka".

" yawwa mata ta,kinga yanda muke soyayyar nan muke farantawa juna rai da kin samu ciki komai zai tsaya shike nan sai kiga kin waniyi kalan tsufa duk haka mata suke yanzu".
D'an mirmishi nai ina basarwa nace"wannan fa siyayyar ta Aunty Amrah ce ita taban sautu in siyo mata kayan Baby ".

" cikin jin dad'i da gamsuwa yake girgiza kai yana fad'in "OK OK Bari ma a k'ara mata".

Nan ya shiga jibga wasu akan Wanda na d'iba.


Ni kuwa jikina k'ara mutuwa yai don ban tab'a zaton haka daga UK ba,dukda bai tab'a nuna min daman yana sha'awar Baby ba amma baitab'a cemin bai soba,gaskiya wlh banji dad'in wannan Maganar ba.







************
Daren da zan bar k'asar nan dare ne me cike da Abubuwan masu yawa,dare ne me tarihi a rayuwarmu, dare ne Wanda muka ko kasa rintsawa a cikinsa, yanda mu kaga rana haka mukaga daran nan,mun gurji juna mun mun kashe arna rundina rundina,wani abu daya tafi da tunanina ya tsayamin a rai yanda a kusan karo na biyar sanda zamuyi releasing abunda ban tab'a jiba nadaga dad'i shi naji haka ma UK wani kuka yakeyi yana wani gurnanin dad'i Wanda ya rink'a dukan gadon da hannayensa biyu yana wani salati cikin shauk'i da gigita, lalle wannan abu bazai fita a rainaba naji dad'in da ban tab'a zaton akwai shi a cikin sex ba, haka muka kwana hawaye na fita a idanuwansa Wanda na rasa name ne.


Bayan munyi sallar asuba yau ko karatun bamuyiba ya jawoni muka hau gado duk da yanzu ba wani abun mukaiba muna dai manne da juna har kusan k'arfe bakwai da rabi sannan muka tashi mukai wanka,daga nan na d'an samar mana abunda zamuci Sam bamu wanici abun arzik'i ba don ziciyoyinmu ba dad'i, k'arfe goma jirginmu zai tashi don haka a gaggauce muka k'ara sa abunda zamuyi,ya fito min da tarin jakunkunana yasa a mota, tunda muka shiga motar naga ya tadata na fara kuka,jiyowa yai ya d'an kalleni bai ce komai ba ya maida hankalinsa ga tuk'in da yake rannan nasa a jagule,muna shiga filin jirgi na k'ara tsananta kukana, bayan ya samu yayi parking ya kamo hannuwana yana d'an matsawa tare da cije lips d'in shi girgiza min kai yake alamar rarrashi amma bakin sa ya kasa furta komai,ganin da yai kukan nawa yak'i tsayawa yasa ya bud'e motar ya rik'oni muka fito a hankali yace " Cool down mana pls dear".

A hankali nake tsagaita kukan nawa inda matafiya suke zama ya zaunar dani,sannan ya fito min da jakun kunan kayana, muna zaune hannuwana sark'e cikin nasa yana d'an matsawa

Please Login or Register in order to submit comment