Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta kamaki a waje".

Da k'yar ta zauna tana dariya tace"To k'orafi dai ya k'are yau na dau hutu a school sai kuma Allah ya rabamu,don haka nazo in dubaki da babyn mu wannan abun farinci ai ba zama".


Bayan mun gaisa take k'ara taya ni murna ni kam dariya kawai nai, tace "a bani abinci inci" nasa Lami ta kawo mata abincin,munata hira har sallar magriba sannan Salis yazo ya d'auke ta.





**********
Wannan cikin nawa me laulayi ne matuk'a,kullum ina sallar asuba sai nai amai ba kad'an ba,haka nan da zazzab'i nake kwana, ga tsirfa ba komai nake iya ci ba, duk abunda aka dafa to haramiyata ne,sai dai furta nake sha wani sa'in yogurt kawai,ko kunun aya, da dare kuwa kullum Tsire ne abinci na da Malta.

Allah sarki UK yanzu bashi da wani sukuni sai na kula dani,da zazzab'in na ya hauni zai sani jikin sa ni ina bacci shi yana gadi na,duk kuwa abunda nace ina so jikin sa na rawa zai nemo min shi,har mamakin kulawar da ya ke bani nake.

Allah yasa sau biyu kad'ai na ke da lecture a sati don haka school bata takura ni,dana shiga nai musu lecture nake tahowa gida.



********
Cikin ikon Allah Sweety ta sauka y'a mace,murna kamar me waje na lokacin da naje barka na ga Baby kamar little d'ita kasancewar y'ar kamar mamanta tai, kullum muna zaryar gidan me jego har ranar suna aka rad'awa yarinya Rukayya, bisa alk'awarin da Salis yai mata in ta haifi mace sunan Mamanta kuma sunan ta zai sa mata, ai kuwa tace yarinya da little za'a rink'a kiranta, tunda daman sunan guda ne,har raina nayi farin ciki Sweety tai mana Kara.




********
Ban fara samun gamsarshiyar lafiya ba sai da cikina ya shiga wata biyar.
Yanzu kam ba amai ba tsirfar cin abunci sai ma wani tsananin ci dana koya,da na ci anjima zanji an min yasa.

B'angaran UK kam hak'uri ya sawa kansa,sabida Sam yanzu ban yarda dashi,naji ba abunda na tsana irin sex sam ban jin wani feelings tare dani,da ya shiga damuwa amma daya nemi shawarar doctor kan lamarin yace "ai wasu matan haka suke ko wane ciki da salon da zai zo mata,sai yayi hakuri kawai".

Babu yanda ya iya haka ya hak'ura ya zuba min ido, nasan sarai yana damuwa amma ya zan yi? Ko na tursasa kaina banjin wani dad'i Sam,amma dai a haka nake d'an takura kaina wani sa'in in barshi ya rage zafi.




**********
Duk siyayyar haihuwa komai sabo mukai don tunda naga na rufa shekara bayan rasuwar little ban samu ciki ba duk na fidda komai nata na bayar,sannan gashi a wannan karan scanning ya nuna namiji zan haifa,amma dake ba tabbas bane hakan ya kasance yasa ban wani karkata ga iya kayan mazan ba.

Lokacin da cikina ya shiga wata tara duk wani shiri mun gama ranar kawai muke jira, kullum bana rabo da tofa ayoyin Qur'ani cikin ruwa ina sha, sannan addu'oin dake sassauta ciwon nak'uda,don ban tab'a manta uwar wahalar da nasha haihuwar little, haka daga gida ko yaushe Aunty Hafsah itama cikin aiko min y'an dabaru take na neman sassaucin nak'uda.










_Ta ku ce_
~Y'ar mutan Ja'oji~πŸ™‹
🍑🍑🍑🍑🍑🍑
🌸🌸🌸🌸🌸🌸
*'YAN* *ARABIC*
🌸🌸🌸🌸🌸🌸
🍑🍑🍑🍑🍑🍑

*NA*
*LAYUZA* *KABIR* *ADAM*

_DEDICATED_ _TO_ _ALL_
_ARABIC_ / _ISLAMIC_ _STUDENTS_
πŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“š


πŸ‘©πŸ»β€πŸ’»πŸ‘¨πŸ»β€πŸ’»
*ZAMANI* *WRITERS* *ASSOCIATION*
πŸ“
_We_ _are_ _here_ _to_ _educate_ , _motivate_ ,and _entertain_ _our_ _Readers_




_*Alhamdulillah komai yai farko zai yi k'arshe,yau dai na huta da k'orafin Fan's dana Hussain 80k sarkin posting kan rashin typing,wannan sadaukarwar taka ce kai da dukkan fan's*_❀❀❀❀

_Mu had'u cikin sabbin novels d'ina masu fitowa insha Allah_



πŸ‘‰πŸ”šπŸ”šπŸ”šπŸ”šπŸ”šπŸ”šπŸ”š

5⃣8⃣ ➑ 6⃣0⃣





Ranar da d'alibai suka gama exam zasu tafi hutun sati shida na second semester nai aikin exam na gaji matuk'a, don duk exams d'in d'alibai dake hannu da sai da nai mark na kai su ga Exams officer, a gajiye tik'is na tuk'o mota ta zuwa gida,lokacin har an fara kiran sallar magriba, wanka nai tare da d'auro alwala nai sallah kiran wayar kitchen ne nace su lami su shirya min dining ban jin zan iya wani aiki yau don baya na a rik'e yake,don haka na zauna k'asan cafet tare da mimmik'e k'afafu na,idona lumshe suke ina jin jikin nawa sam ba dad'i, sautin muryar sa na jiyo kamar yanda ya saba in dai ya dawo bai same ni falon k'asa ba to tun daga step d'in farko zai fara kirana har sai na fito na tare shi,yau kam ban jin zan iya tashi don haka mirmishi kawai nake na zubawa k'ofa ido, da saurin sa ya turo k'ofar yana fad'in "wai ina my angle d'in ta mak'ale ne."

Tsayawa yayi yana kallona fuskar shi cike da tausayi don da ganin zaman da nai ya san bana dad'i bane,jiki sanyaye ya k'araso ya zauna dirshen gabana,y'ar dariya bai da fad'in "oga Wannan zaman y'an borin fa?."

Yak'e kawai yayi da fad'in " ya dai na ganki zaune haka ko jikin ne?."

Rik'o hannun sa nai da fad'in "gajiya ce kawai wlh yau nai aiki over matse kaina nai na kammala duk aikin dake gabana".

A hankali ya shiga matsa min k'afa da fad'in" Ayya sannu kinji Baby na,kinga shi yasa nace miki da na iya Islamic duk ni zan rink'a miki makin exams wlh ki huta,to ko na karb'a ban San me zan maka ba."

"Hhhhhmmm ina godiya da kulawa,amma yunwa nake ji na kasa sauka ki dining d'in na shirya."

Da sauri ya mik'e yana rage kayan jikin sa,sannan ya sauka k'asa, kayan abunci ya hayo dasu suka saman har d'aki, da sauri sauri ya sakamin tuwon da miyar danyan kub'ewa,ai kuwa ba sauraro na fara zubawa cikina,sai da na cinye malmala biyu sannan na sha kunun aya nai hamdala.
Sai a lokacin ya fito daga wanka tare da alwalar sallar isha'i, kayan ya had'a ya matsar gefe, da nufin in ya dawo salla shima ya ci anan.

Bayan fitar sa masallaci na yunk'ura da k'yar nai toilet don d'aura alwala nima,amma sai naga bakon yanayi tare dani,gabana ne ya fad'i don alamun nak'uda na kusa kenan, tsarki kawai nai na fito ruwan zamzam d'ina na d'auka na k'ara tofa wasu addu'o'in na sha, duk sai naji jikina ya mutu har hawaye ya fara zubomin don na san ciwon nak'uda bai min da wasa ba.

Ina nan zaune cike da tunani kala kala ya dawo,ganin yanayi duk sai ya damu yace"Ko dai baki da lafiya ne muje asibiti?. "

Girgiza kaina nai ina k'ok'arin b'oye damuwa ta nace"A'a nace ma fa gajiya ne kawai,kaci abincin sai ka min tausa zan ji dad'i. "

Cikin hanzari ya jawo kulan abincin ya zuba ya fara ci,sama sama ya ci ya tashi, dawowa yai ya d'aga ni zuwa gadon ya kwantar dani kamar yanda ya saba matsamin jiki haka yai ta min massaging d'in, ai kuwa naji dad'i har wani lumshe ido nake, a haka bacci me dad'i yai gaba dani,bai bar yi ba sai da ya tabbatar nai nisa cikin baccin sannan ya tashi ya gyara d'akin ya sauka da duk kwanikan, sannan ya had'o min kayan shayin da yasan duk dare ina farkawa sha.


Ya dad'e zaune yana kallon yanda nake bacci tabbas duk wanda ya kalleni ya san ba wai jin dad'in baccin nake ba,duk tausayi ne ya k'ara kamashi, yana k'yamar halin daya aikata da a baya, ina cikin irin wannan halin amma ya rink'a wulak'antani da hantara ta,duk irin wannan wahalar nasha a baya amma babu mai taimaka min,wani hawayen tarin nadama ne suka gangaro mai ya goge tare da fad'in "Allah ka yafe min, ka amsa tubana,Allah ka raba wannan baiwa taka da cikin nan lafiya."




*************
Misalin k'arfe sha biyu na farka don jin wani azababban fitsari da k'yar na k'arasa toilet nayi, ina dawowa ko minti biyar banyi ba naji wani,Cikin k'osawa na k'ara zuwa nai,amma ina dawowa zan kwanta naji bayana ya rik'e k'am,duk dabarar da zanyi in kwanta kwanciya ta gagara,ga bacci sosai a idona,na rasa ya zanyi kawai sai nasa kuka,cikin shagwab'a na fara bubbuga bayan sa ina kiran sa, da saurin ya tashi yana kunna hasken d'akin yace"Subhanallah, meya faru Nahna?."

Kuka sosai na sanya mai kuma nak'i magana,gaba d'aya rikicewa yayi ya rik'oni yana fad'in "pls fad'a min mene ne don Allah? Ko baki da lafiya?."

Gyad'a mai kai nai da sauri ya sauka a kan gadon ya sami jallabiya yasaka,nima kaya ya d'auko ya samin inata kuka don sosai naji bayana da mara sun rik'e min, kuma ma dai harda shagwab'a naga yanda jikinsa ke rawa duk gigice( k'ara kiyi k'ara'i Khadeejah ai a fari biki haka ba😜)
Bai wani tsaya d'aukan wani abuba ya sauko dani k'asa, da sauri ya fita yaje ya fito da mota yai parking d'in ta kusa kusa,ciccib'oni yai cikin azama ya sani a motar,muka fice.



**********
Doctor na dubani tace haihuwa ce amma dai da saura,nan suka bamu gado,kad'an kad'an ciwon ke lafawa amma in ya motsa ba labari,nace UK ya kira Abba ko Aunty murja amma yace Aa bai buk'atar kowa ya kula dani bayan shi.


Awa uku da zuwan mu asibitin nak'uda ta kankama dole likitoci suka koreshi daga labour room d'in, fitar sa da minti biyar Allah ya rabani da cikin, kukan jinjiri ne kawai ya ankarar dashi na sauka,da sauri ya k'araso bakin k'ofar yana kasa kunne,ai kuwa cikin kunnan sa yaji doctor tace"Alhamdulillah ta sauka."

Da sauri ya juya yana d'aga hannayensa sama yace "Alhamdulillah Alhamdulillah Alhamdulillah"

Nurse ta bud'e k'ofa ta fito tana mai albishir d'in samin Baby boy,cikin tsananin farin ciki yace "Kina da babbar kyauta na wannan albishir d'in, kuyi amfani da komai naku, a samin a bill don bamu zo da komai ba".

Juyawa tai ciki tana dariyar ganin irin rikicewar da yayi.



Ni kam ina haihuwa naji kamar an zare min wani katon dutse sakayau naji na koma sai dai rashin k'arfin jiki.


Bayan sun Shiryamu ni da Baby aka kaimu d'akin hutu, zuwa lokacin har an kira asuba, a masallaci asibitin yai salla ya dad'e a sujjada yana nuna godiyar sa ga Allah.

Har lokacin bai kira kowa ya fad'a mai ba, yana son yin surprise d'in su.


K'arfe bakwai likitocin suka sallamemu bayan an gama tabbatar da bamu da wata matsala ni da Baby boy d'in, duk bill d'in da aka cajeshi transfer yai musu haka itama nurse d'in da tai mai albishir ya tura mata kyautar 20k


Yana d'auke da Babyn muka k'arasa mota ya bud'e min na shiga sannan ya dora min babyn a cinyata ya zagaya ya shiga,bakin nan nashi kamar gonar audiga haka muka tafi gida yana ta samin albarka tare da min sannu,nikam mirmishi kawai nake ina rungume yarona a jikina wani sukuni na ratsani.



Sai da muka kusa k'arasa wa gida ya dau waya ya kira Aunty murjah Tana d'auka yace "Aunty don Allah shigi gidan mu."

Bai tsaya jin me zata ce ba ya katse wayar, ita kuwa kallon Abba tai da take had'awa break fast tace"To Khadeejah ina ga haihuwa tazo don Daddy ne kirana wai inje".


Da sauri Abba yace "Maza jeki ina jin nak'uda take".


Mayafi kawai ta d'auko a d'aki ta fito tana shiga muma motar mu na shigowa, da sauri ta juyo ganin mun shigo a mota,

Sam bata gane me ke faruwa ba don haka ta k'araso bakin motar dai dai lokacin ya bud'e ya fito cikin dariya yake fad'in "Aunty kinyi sabon ango fa".

Bata gama dawowa daga mamakin furucin sa ba taga na bud'e mirfin motar ina mik'a Mata jinjirin, da sauri ta karb'eshi cikin mamaki tace " ya akai haka Daddy?."

Dariya sosai yake yace "muje daga ciki Aunty kisha labari."

Ba musu ta juya muka wuce ciki.

A falo muka zauna Aunty nata jero tambayoyi,cikin tsananin murna ya sanar da ita komai,ai kuwa Aunty me zatai in ba hamdala ba,ta zubawa yaron ido tana dariya tace "masha Allah wannan karon dai Daddy Khadeejah tama wayo,don sak wannan fuskar ta ta ce".

Turo baki yai kamar wani k'aramin yaro yace" Eh wlh Aunty nima haka na gani, amma ai dai fatata ya d'auko ".

Dariya mukai gaba d'aya Aunty ta tashi da sauri ta mik'a mai yaron tace" Bari maza a had'a ruwa me zafi ki gasa jikin ki,sannan a samar miki abunci ki ci".

Kai tsaye ta wuce Babban kitchen inda ta tadda su lami nata k'ok'arin gyarawa da shirya min duk kayan da zan yi girkin break fast suma basu san wainar da ake toya ba,sai da ta fad'a musu,gud'a Lami ta saki da fad'in "masha Allah kaga haihuwa me dad'i, to bari maza a dafa mata abu me nauyi ta ci".

D'aki na guda dake k'asa wanda nai jegon Little anan ma wannan karon muka had'a duk kayan mu na haihuwa don haka muka yada zango anan.
Ruwa me zafi Aunty ta had'a min na gasa jikina na zauna a ciki kasancewar an min d'inki, na fito na shirya tsaf dani cikin riga da zani na atamfa,kafin nan Aunty ta sanar da duk Wanda ya dace ta sanarwa.

Shayi me kauri ta had'a min nasha kafin abunci ya kammala, shi kuwa Baby boy an canja mai kaya zuwa na sanyi masu kyau.



*********
Zuwa wani lokaci gida ya cika da y'an uwa da abokan arzik'i y'an barka.

Ni kam bacci ne sosai ya d'auke ni don haka suka dawo falo da Jinjirin suka barni.


Wannan haihuwar ma Goggo ce tazo min daga Gida sakkwato take kula damu,Aunty Hafsah da Aunty Amrah kullum sai dai suzo su yini su tafi.

Bayan haihuwa da kwana uk UK ya sameni kan maganar sunan da nake son a sawa yaro,nace " zab'i ai na gareka Ogah".

Cikin jin dad'i yace"Za muyiwa Baffa takwara hakan yayi?."

Jim nai cike da farin ciki bace"Um yayi amma ni a son raina kafin nayiwa Baffana takwara sai na fara yiwa Yaya Haroon."

Dariya yayi tare da fad'in "Yanzu dai kin fi son ayiwa yaya kenan?."

Daga mai kai nai cike da farin ciki, ai kuwa take ya d'auki yaron yamai hud'uba da Haroon.

Har k'arshen zuciyata naji wannan dad'in don fatana kullum kenan.

Nan da nan dangi kowa ya san sunan yaro Haroon,yaya ma yai murna sosai da samun takwara,ranar da mukai kwana biyar yayo nana akwati cike da kaya na takwaran sa.



Ana gobe suna kuwa gida ya cika mak'il da y'an suna,mutanan katsina dana sakkwato.

Wannan karon ma Abba yayi hidima matuk'a da gaske, ranar suna an yi komai cikin tsari da wadata, yaro Haroon zamu rink'a kiran sa da Raees.


Bayan kwana biyu da suna gida yai dif kowa ya koma in da ya fito daga ni sai Goggo dake ka damu.

wannan karon sati biyu biki ya d'auke min don haka ba sauk'i na shiga gyara kaina don ni kaina na san nai kewar mijina, yanzu ni da kaina nake ji a jikina ina buk'atar sa.

Ranar da nai sati uku da haihuwa Ranar Alhamis da yamma Goggo taje gidan yaya Usaman dubashi bai jin dad'i sai ni kad'ai a gidan ina zaune a falo d'auke da Raees ina bashi nono UK ya shigo, muna had'a ido muka sakarwa juna mirmishi ya k'araso kusa dani ya zauna jikin mu na had'uwa hannu yasa yanawa Raees wasa.

A hankali nace "Sannu da zuwa."

Dagowa yai yana lumshe ido yace" yawwa sannu princess, wannan shigar fa? Ana tsokano mutum fa wlh, kuma dana matso ace jego ake".

Wata y'ar dariya nai me cike da k'issa nace"Ai jego ya k'are oga kawai muna jira mu k'ara murmurewa ne".

D'an zaro ido yai da fad'in "don Allah da gaske?."

Dage mai gira nai ina y'ar dariya, jawoni jikin sa yai yana k'asa da murya yace "Plsss princess a taimaka min wlh marata ciwo take, daurewa kawai nake yi fa."

Komawa serious nai nace"Sati uku fa da haihuwa Honey bamu koma normal ba kuma kasan an min d'inki ."


"Eyya my wife kefa kika fad'a min tun rannan d'inkin ya warke rass, Don Allah ko kad'an ne a taimaka min."

Ban aune ba naji bakin sa cikin nawa,nai k'ok'arin janyewa ko don kasancewar a falo muke amma ya k'i bani wannan damar,kusan minti biyar naji abun nasa na son mik'awa cikin hikima na janye ina fad'in "Falo fa muke don Allah in wani ya zo fa."

Idonsa da suka fara yin ja ya lumshe ya na sauke ajiyar zuciya,hannu yasa ya d'aga Raees a kan cinyata ya wuce gaba dashi yana fad'in "Zoki had'a min ruwan wanka."

Jimmm nai can dai na mik'e nabi bayan sa zuwa saman.

Ina shiga na tadda har ya kwantar da yaron ya fara k'ok'arin cire kayan sa, ban tankashi ba na wuce toilet d'in,ruwan wankan na had'a mai sannan na d'auko towel na fito lokacin ya rage daga shi sai boxer mik'a mishi towel d'in nai ina alaman ya karb'a ya d'aura, hannun ya mik'o kamar zai amsa kawai naji ya jawoni jikin sa,a tare muka sauke wata ajiyar zuciya a lokacin da k'irjinmu suka had'e waje guda,wasu salo masu rikita jiki da zuciya ya shiga aika min wanda sukai sanadiyar tsumar dani na shiga maida martani cikin zak'uwa da d'oki, Sam na manta condition d'in da nake don bukace nake da mijina,mun manta mun shagala mun lula can wata duniya bamu gane komai sai kanmu kawai,bamu dawo hankalin mu sai da komai ya lafa nutsuwa ta zo mana,asan nan na tuna cewa fa jego nake duka satina uku da haihuwa,wani takaici ne ya kamani sai ji nai hawaye na zubo min,kaina da ke hannun sa ya bada damar zubar hawayen a tsintsiyar hannun nasa, d'ago guskata yai yana fad'in "kuka? Kuka kikeyi Nahna?."
Wannan maganar tasa na saki sautin kukana,kamar wadda akaiwa wani laifin.
Da sauri ya tashi zaune yana rarrashina damin kalamai masu dad'i da nunamin illar da kin amincewa dashi zata jawo mana,da haka dai na samu na hadiye kukan na tashi zuwa toilet nai wanka,b'angaran kayana dake d'akin naje na d'auko wata doguwar rigar atamfa na saka,duk yana kwance yana kallona, ni kam fuskata d'aure tamau na k'araso gaban gadon na d'auki Raees dake bacci, ban ce mai kala ba na juya na fice.

Wani mirmishi ya saki yana fad'in "Oh! Mata masu duniya,jimin yarinyar nan yanda ta zak'e lokacin da take neman dad'i sai yanzu kuma ta gamsu take ta wani tsare gira."

Mik'ewa yai fuskar sa cike da annuri ya shige toilet shima yai wankan tare da d'auro alwala don lokacin salla ya kusa."


Ni kam jiki sanyaye na sauko k'asa, ina shiga d'aki na samu Goggo har ta dawo tana tsaye ta d'auro alwala, duk duburburcewa nai na fara fad'in "Goggo kin dawo? Sannu da zuwa ya jikin yaya Usman d'in."

Cikin nuna bata San me nake ba tace "Eh na dawo tun d'azu ai,jikin nasa da sauk'i."

"Ina sama ina gyara sif ai ban ji shigowar ki ba ai."

Ita dai Goggo bata tanka min ba ta tada sallarta don ta ga alamun rashin gaskiya kiri kiri tare dani.

Nima zama nai na bawa Raees nono don yana ta motsin nema, sai da na tabbatar ya koshi sannan na ajiye shi naje nai sallar nima.



*********
Satin mu biyar cif Goggo ta tafi, don taga rawar k'afar UK tai yawa,ni ni kam tun ranar nan ban k'ara yarda mun keb'e ba,don sai na k'ara gyara sosai gashi ina jin tsoron d'inkin da akamin ance in bai gama warkewa ba aka matsa da Abu yana bada matsala duk da ni nawa ya warke rass amma dai sai na k'ara takatsantsan.


Yau kam tunda Ya dawo da rawar jiki ya dawo Ina kallon na basar, duk kayan buk'atar mu ya maidasu sama ina jinsa yana ta fad'in zaman k'asa ya k'are ai tunda Goggo ta tafi,ko tanka mishi banba don yau sarauta nake ji,ko wanka ma shi yaiwa Raees ya mai shirin bacci ya sashi cikin gadon sa,duk ina zaune ina kallon TV, shima sai dai ya gama shiryawa sannan ya zo gare ni"Madam yau mulkin ne ya motsa ne? Basarwa nai kamar banji shi ba sai da ya k'ara maimaitawa sannan na yatsine fuska da fad'in "me ka gani fa?."

Mirmishi yai kawai ya kashe kayan kallon tare da d'auka na cak bai dire ni sai cikin Bathtub daya cika da ruwa, y'ar k'ara na saki da fad'in " ni ban son wankan ka cire ni."

Bai saurareni ba ya raba ni da duk kayan jikina, tass ya wanke ni yana yi ya jagwagwalani,tun daga toilet zancan ya fara canjawa duk yanda naso basarwa abun yaci tura haka na mik'a wuya kawai.



**********
Tun daka lokacin kuma sai muka zama mannau d'in junan mu ko yaushe aikin mu faranta ran junan mu,ni yanzu har mamakin kaina nake yanda wani sa'in har nake fin UK zumudi da d'oki kan harka,don shi wani lokacin in yai wasannin sama dani sai ya gamsu amma ni sai anje magaryar tuk'ewa nake tsaida birki,shi kansa yanzu tsokana ta yake wai na zama inji ban gajiya da aiki,daya fad'i haka sai dai in murgud'e baki in ce "kai ka koya min ba fika iyawa"."


Watana hud'u da haihuwa hutun dana d'auka ya k'are, na koma Lecture, duk sanda nake da lecture gida nake barin Raees wajan Aunty murja don ya saba da ita sosai,tunda ko yaushe yana gidan dama.

Wani irin so da UK ke nunawa yaron har tsoro yake ban araina nake addu'ar Allah yasa shima ba rasuwa zai ba, har fad'a nake mai kan ya rage nuna Wannan soyayyar da yake mai yayan yanzu ba'a nuna musu irin wannan son a zahiru sai su tab'are.
duk sanda na fad'i haka kicin kicin yake da fuska yace" Haihuwar da sai da yaita zubda hawaye yana magiya ga Allah sannan ya k'ara bashi kuma shine bazai so abunsa ba."

Shiru nake mai in naji ya fara wannan mitar.

Shi kanshi yaron yanzu bai yarda da kowa in Ubansa na gida yata mik'a mai hannu kenan yana tsalle,yai ta gwarancin sa wai ya san Babansa.


********
Watan Raees biyar cif na fara jin canji tare dani don wata kasala da yawon kwad'ayi ke damuna, ban kawo komai cikin raina ba,sai da zazzab'i ya sakoni gaba sannan naje ganin likita, gwajin farko aka tabbatar ciki gareni har na wata uku,a tsorace na kalli doctor d'in don ta tabbatar min da abunda kunne na yaji,mik'omin result d'in tai tana min congratulation, jiki ba k'arfi na k'arb'a na taho gida tuk'in ma a sanyaye na ke yinsa.

lokacin da aka kawomin Raees daga gun Aunty murja tausayin sa ne ya kamani ganin duka yaron watansa biyar gani da cikin wata uku kenan ko

Please Login or Register in order to submit comment