Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ai mata awo ko".

"Eh hakan yayi murja yanzu kije ki fad'a mata ta zama cikin shirin sannan saiki d'an k'ara mata bayanin yanda abun yake ki wayar mata da kai ko".

Mik'eqa Aunty murjah tai cikin farin ciki tana fad'in " ai mu yanzufa ba zama Daddy zai haifo jika ".

Duk dariya sukai ,sweety tabi bayan ta suka fita,shi kuwa Abba bin bayan su yai da kallo yanata fara'a.



Ina kwance d'aki don har nai shirin bacci ina jiran kiran mijina don wayar ma na hannuna,jinai sweety na magana a bakin k'ofa " Aunty na har an tafi tsinkar furen ne ".

Y'ar dariya nai nace 'kema kin sani ai yanzu lokacin me zuciyata ne, ki shigo mana kika tsaya ".

Shigowa d'akin tai tana fad'in " A'a ai naga a irin wannan lokacin bakya buk'atar kowa kusa dake".

Dukan wasa nakai mata ta matsa tana dariya tace " kizo Aunty murjah na parlour tana son magana dake ".

Zaro ido nai nace " don Allah da gaske ,innalillahi,me kika ce mata?kar dai har kin sanar dasu ".

Cikin basarwa sweety tace " Ah to me za'a jira,kedai kawai kizo muje sauri take".

Jikina har rawa yake na lalubo hijab nasa nabi bayan sweety, a zaune na tadda Aunty murjah πŸ˜‚πŸ˜­fuskarta cike taf da fara'a take kallona,k'arasa nai na zauna k'asan cafet ina gaidata ,da fara'ar ta take amsa min tace "Yau munji abun farin ciki munwa Allah godiya,amma kuma bamu samu labari da wuri ba,har k'awar ko abokin na shirin zuwa dukda sweety ta fad'a mana plan d'inki, yanzu ki shirya gobe in Allah ya kaimu zamuje kiga likita ya tabbatar da lafiyarku sannan ki fara zuwa awon ciki kinji".

Kunya kamar k'asa ta bud'e in shige haka na zama kaina k'asa nama kasa amsa mata ,nan taita min bayanin yanda zan kula da cikina da kaina, daga nan taimin sallama ta tafi ,tana fita sweety ta kyalkyale da dariya tace " To kunyar tamene Aunty na tunda an riga an samo mana d'an India ".

Hararanta nai nace " zamu had'u wlh ,ni duk kinsa kunya ta dabaibayeni wlh ni yanzu da wane ido ma zan kalli Abba ".

Cikin dariyar tsokana tace " da wannan idon da kike kallon kowa,ke shifa Abba yana can dad'i ya cikashi sai hamdala yake".


Hararanta kawai nai na tashi na shige d'aki don jiyo Ringing d'in waya na da nake.





Misalin k'arfe takwas na shirya tsaf don kar Aunty tazo tana jirana,ina zaune gaban mirror sanye da hijab d'ina ina fesa turare sweety ta shigo tace in fito Aunty tana parking lot tana jirana, y'ar jakata na d'auka tare da zura takalmina na fice ina rufe d'akin.

Tun daga nesa na gango driver harya saita kan motar yana kallon gate k'arasawa nai na bud'e baya inda Aunty murjah ke zaune na zauna ina gaidata kaina a k'asa amsawa tai tana dariya tace " ya jiki jikin " cikin tsananin kunya nace "Alhamdulillah"

Gaisuwar da driver kemin tasa na d'aga kai ina amsa mai sannan yaja motar muka tafi.





********
Duk iya bincike da dube duben daya kamata likita yayi yamin ya tabbatar da lafiyata data abunda ke cikina sannan ya k'ara bani shawarwarin kula da kaina da abincin daya dace me ciki ta rink'a ci, sannan muka baro asibitin.





Tun daga wannan ranar yau sati guda kenan ban bari mun had'u da Abba ba don ko sashin su nak'i shiga tsananin kunyar had'uwa da Abba nake,shikuwa Abba kullum cikin yimin siye siye yake na kayan k'walama in ya kawo zai bawa sweety kosu Kamis su kawo min,ina son zuwa inyi godiya amma na kasa, innace sweety tace mai na gode sai taita min dariya wai inje da kaina, haka in taje wajan Abba zata ita bashi labarin kunyarsa da nakeji ban son had'uwa dashi, shima dariyan yake kawai yace Khadeejah kenan.




Yau sweety taje gidan ummu sulaim ta sanar da ita zancan cikin itama murna tai tayi wayar ta ta d'auka tana fad'in "bari inyiwa broth murna an kusa zama Abba".

Da sauri sweety ta rik'o hannun ta tana fad'in " Rufamin asiri ".

Kallon tuhuma take mata ,nan sweety ta warware mata komai kan matsalar k'in haihuwa da UK keyi da kuma rashin sanin da zaman cikin, da b'oyewa su Abban su gaskiyar zanzan da sukai , hawaye ummu sulaim take tace " Ashe muna murna broth ya shiryu ashe da sauran sa,yanzu meye abun k'i cikin haihuwa don Allah wasu nacan nata nemanta ido rufe shi ambashi yana gudu, wlh Allah sweety kullum a gidan nan rok'on ubangiji muke ya ban cikin kullum burinmu in yiwa fu'ad k'ani ko k'anwa Abban fu'ad Allah ya jarrabeshi da son yara gashi ni bame yawan haihuwa ba,amma shi broth baima tab'a haifa ba amma har yake neman tsari da ita saboda ak'idar boko ak'idar banza".

Jinjina kai sweety tai tace " dukda haka broth ya shiryu matuk'a ya gyara d'abi'unsa zamansa da Nahna ,wannan muguwar ak'idar tasa ce kawai ta rage kuma insha Allah ina kyautata zaton in ya dawo yaga cikin zai hak'ura ".


Haka sukaita tattauna matsalolin Uk suna mai addu'ar k'ara shiryuwa.


Tsawon sati biyu naga b'oye b'oye bazai kaini ba don haka na shirya na tafi gaida Abba da magriba kayan sallar isha'i sanne in sanar dashi ranar nayi graduation a ranar dukda ya sani don har kud'i sosai ya aikomin inyi hidimar graduation d'in dashi,

Da sallama na shiga parlourn nasa ya amsa min cikin sakin fuska yana fad'in " k'araso mana Khadeejah shigo"

A nutse na k'arasa k'asan rug na zauna kaina a k'asa nace "Abba barka da dare ".

" yawwa barka dai Khadeejah,ya exams yau dai an gama ko".

Gyad'a kai nai ina d'an mirmishi, yace "To Allah ya fito da kyakykyawan sakamako,dukda nasan yarinyar tawa akwai himma da k'ok'ari Allah ya dafa miki".

Cikin jin dad'in addu'ar tasa nake amsawa da " Ameen Abba na gode,Allah yaja da rai ya k'ara lfy ".

" Ameen Khadeejah, ya kuma jikin naki,ina fatan babu wata matsala a tare dake".

To anzo wajan fa nan na k'ara k'asa da kai kamar zan nutse, y'ar dariya Yai yace "ki daina damun kanki fa Khadeejah koda yaushe ina fad'a miki ki d'aumeni mahaifi ba suruki ba ki daina jin kunya ta, duk damuwarki ki rink'a sanar min kinji".

Gyad'a kai kawai nake kamar k'adangaruwa,haka yaita jana da hira nikam sai dai inyi mirmishi kawai,dayaga dai na takura sai yace " Tashi kije ki kwanta ki huta don nasan yau kunsha hidima, kamar jira nake tsam na tashi inai mai sallama na fita.




Sai ya zama na tun daga ranar na rage kunyar had'uwa da Abba na koma kamar kullum duk kwana biyu zanje in gaidashi mu danyi hira.






***************
Wata rana da dare ina kwance muna waya da Ruhina yace "my wife kwana biyu fa biki turomin pic d'in kiba,ko rowar jikin akemin ".

Dariya nai me cike da k'issa da jan hankali nace" ka tab'a ganin anwa me abu rowar abunsa, nida Ruhina da jikina duka naka ne kayi yanda kaso".

Cikin jin dad'i da kalamaina yace "yawwa wify to aturomin yanzu in gani kuma tun daga sama har k'asa ".

Ba tare da damuwa ba na fara d'aukan pic d'ina cikin kayan baccin dake jikina yar ficici dasu na tura mai,

Yana kalla mirmishi yake tayi can ya kirani " Ke me kike ci kikai k'iba haka, ko inafa yai b'ulb'ul dashi".

Sai a sannan ma na tuna da yanayin jikina daya sauya don cikina har yanzu bai wani fito sosai yanda za'a gane kai tsayeba,amma nai k'iba ta jikina don Boob's d'ina sun cika matuk'a su K'ara girma,haka ma hip's d'ina ya k'ara bud'ewa yai girma,jikina ma duk ya murje yai k'iba madaidaiciya,
Cikin basarwa nace "Hhhmmmm hutu ne kawai ba zuwa school ba karatu brain d'ita tayi fresh banda wata matsala".

Dariya yai yace " lalle kuwa kina hutawa don gashi nan ko ina ya nuna har an tsokane min ido da tws d'ina".

Dariya kawai nai ina janye hankalin sa daga maganar k'ibar muka fad'a duniyar k'auna.





*********
Rayuwa na tafiya yanzu cikina ya shiga wata bakwai kenan, kuma a yanzu ne ya fito sosai ya zauna a jikina, zuwa yanzu ba k'aramin shiri Abba kewa cikin ba sabida yace baya buk'atar Daddy ya dawo yasai komai na taran Babyn,don haka ya bawa Aunty murjah A.T.M card d'insa yace muje nida ita da sweety mu siyo duk wani abu da ake buk'ata na tarar Baby,ca nai bazan bisu ba suje su biyu ni kunya nakeji wlh, sukai sukai nak'i don haka Aunty murjah ta kira Aunty ummu sulaim tace ta shirya zasu siyayyar haihuwa suka had'u su uku suka tafi.

Kaya suka jido bana wasa ba fa kamar bada kud'i ake siyaba ,duk wani abu na buk'atar baby sun siyo kayan wanka kayan shafa,kayan sawa komai fa basu bari ba,haka suka lodesu gaban Abba yaita dariya dajin dad'i bayan dukya gama gani yasa aka kawosu pat d'ina d'aki guda a gefe aka zuba kayan aciki,nidai binsu kawai nake da kallo irin dukiyar da aka kashe, sai bayan sun koma pat d'in su na shiga d'akin ina duba kayan fuskata d'auke da fara'a ina yaba k'aunar da wannan family sukemin, zuwa nai na d'auko akwatin kayan babyn da nazo dasu daga India na had'a a d'akin, sannan na rufo k'ofar ina addu'a a raina Allah ya rabani da cikin nan lfy.






*Taku* *ce*
*y'ar* *mutan ja'oji*πŸ™‹
🍑🍑🍑🍑🍑🍑
🌸🌸🌸🌸🌸🌸
*'YAN* *ARABIC*
🌸🌸🌸🌸🌸🌸
🍑🍑🍑🍑🍑🍑

*NA*
*LAYUZA* *KABIR* *ADAM*


_DEDICATED_ _TO_ _ALL_
_ARABIC_ / _ISLAMIC_
πŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“š

πŸ‘¨πŸ»β€πŸ’»πŸ‘©πŸ»β€πŸ’»
*ZAMANI* *WRITER'S* *ASSOCIATION*

πŸ“
_We_ _are_ _here_ _to_ _educate_ , _motivate_ _and_ _entertain_ _our_ _Reader's_



*Allah* *kasan* *damuwar* *dake* *k'asan* *rai* *Allah* *kai* *mana* *maganin* *ta* πŸ‘πŸ‘πŸ‘




0⃣4⃣8⃣



Yanzu kuma duka hankali na ya koma ga tarar dawowar mijina wanda nake k'arfin hali kawai don zuciyata taf take da fargabar abunda ka iya zuwa ya dawo,sati hud'u ci ya rage zai dawo Wanda lokacin ciki na yana wata takwas cif, yanzu bama samun wani sukuni dashi sabida course d'in nasu ya k'are sai project suke had'awa da shirin tahowa gida, anan Nigeria kuwa company d'in su an gama komai an bud'e jiran dawowarsu kawai ake su fara aiki,don haka yanzu koda yaushe yana busy,sai muyi kwana biyu bamuyi waya ba sabida lokacin da zai gama uzurinsa ya dawo gida ni tuni nai nisa a bacci ma.



B'angaran Abba kuwa yasa an tada ginin katafaran gidan mu,dake kusa danasu don filin dake jikin gidan k'aton gaske yasa ake mana gini na d'aukan zance, tunda yai alk'awarin daman inya dawo a gidan mu zamu tare, nikam bana murna ma da sabon gidan da za'a karb'i ra'ayina abarni cikin gidan nafi son haka balle yanzu ga ciki zanfi son zama cikin mutane.



**********
Kwanaki sunyi gudu sosai harya rage yanzu kwana goma cif UK ya dawo gida Nigeria,kowa murna yake amma nikam yak'e kawai nake,dalilin yawon fad'uwar gaba ma yasa duk na rame na fige sai hanci zirit da idanuwa,ga cikina ya fito sosai yai girma, gidan mu kuwa an gama komai har furniture's duk an saka zuwa kitchen material komai an kammala,sai batun y'an aiki Abba ya tuntub'eni kan za'a samomin masu aiki ko inadasu ta b'angarena, har zance a'a bana buk'atar masu aiki mata,sai kuma nai tunanin yanzu haihuwa zanyi ina buk'atar mataimaki, ga gidan ni kad'ai zan samu mutane kusa dani amma dai ni ba wani son me aiki nakeba ,sai kuma nace eh zan duba gudawa nawa za'a samo,Abba yace a samo mata guda uku biyu masu aiki d'aya me rainon Babyn da za'a haifa, sannan a samo maza guda uku suma me gadi dame kula da gida filawowi da sauran su ,sannan me wanki da guda da zuwa d'an aike haka, cikin gamsuwa nace tom Abba za'a samo.


Bayan ba dawo part d'ina na kira yaya na bayan mun gaisa nake tambayarsa ko za'a samu masu buk'atar aiki a can gida sakkwato, yace min zai kira au yaji,aikuwa bayan kamar awa guda ya kirani ya sanar dani akwai masu so da yawa daga maza har mata a irin mutanan unguwar mu masu k'ara min k'arfi.

Da safe na sanar da Abba an samu acan sakkwato,yace tom ba matsala zai aika driver yaje ya taho dasu,naji dad'in hakan sabida nasan duk ma'aikatan dake aiki k'arkashin Abba ba k'ara min alheri suke samu ba ga albashi me tsoka,koba komai nima y'an garinmu sa samu daga gareni.




**********
Kayan gyaran jiki sosai Aunty ta aikomin sannan ta aiko me gyaran tamin gyaran fata,bana wani d'okin don cikin jikina ma ya isheni ga fargaba,don haka ban wani bada had'in kai a gyaran ba fatana kawai Allah ya daidaita mu idan ya dawo.


Bayan kwana biyu Abba ya tura driver sakkwato yaje ya debo ma'aikatan,don daman sun zama cikin shiri,

Ina son garina da mutanan cikinsa shiyasa lokacin da aka kawosu naita musu barka na rasa inda zan ajesu,babu k'yama ko wani Abu na sake cikin matan munata hira su kuwa mazan bayan sun shigo mun gaisa aka kaisu sukaci abunci sukai salla, can gidan aka kaisu aka nuna musu d'akin su,k'aton d'akine daka shiga gate me d'auke da k'ananun katifu uku, kowa da tasa daga ciki harda toilet d'in su, biyu manya ne don duk da iyalansu ma sai d'aya ne saurayi don haka shine me wanki da guda da zuwa aike,d'aya me gadi d'aya me kula da filowa da sharan gida.



Bayan y'an tambayoyi danaiwa matan na fuskanci suna cikin talauci, d'aya dattijuwa ce da yar autar yarta budurwa tacemin shekararta goma 16 sai d'ayar bazawara ce da bazata wuce shekaru talatinba, b'angaran ma'aikatan gidan su aka kaisu son sai ana gobe zai dawo zamu tare a gidan.




*********
Rana bata k'arya inji y'an Hausa,yau kam gamu cikin gidanmu mun tare Wanda gobe kuma me gidan zai sauka gida Nigeria, kwana nai kan sallaya ina kaiwa Allah kukana kan ya daidaita tsakanina da mijina idan ya dawo har asuba sannan nai sallar asuba na kwanta, bacci sosai ne ya d'auke ni Wanda ya kaini har k'arfe goma da addu'a na tashi a baking,l ganin time yasa nai saurin tashi nai toilet wanka nai na fito ban wani tsaya shafe shafe ba na zura doguwar riga nai parlour, samun su karima nai har sun gyara gidan tsaf sun koma b'angaransu dake can farkon gidan.


Kitchen na shiga don samawa cikina abun tab'awa kasancewar jiya munyi kayayaki sosai na tarar me gidan yasa na d'iba ciki naci, sannan na fito zuwa part d'in masu aikin, sumun su nai har sunyi wanka sun k'ara gyara part d'in nasu batun abunci daman da kitchen d'insu a ciki ansa musu duk kayan girki zasu rink'a yin nasu da masu aikin maza, cikin sauri suka shiga gaida ni na samu waje na zauna muka gaisa, nan nace karima da Binta suzo muje su tayani aiki su bar Baba ta huta ita.




Munata aikin abinci amma hankali na bai tare dasu ko sweety data shigo ta amsa ragamar aikin tanata min tsiya da tsokana nako kasa amsa mata sai dai yak'e nake,ji nake kamar zuciyata zata faso k'irjina ta fito don fargaba, a haka wajan sallar azahar aka gama komai aka shirya su a wasu k'ayatattun warmas masu d'aukan ido,tsaf muka shirya dining table d'in duk girmansa saida muka cikashi da kala kalan abinci da kayan mak'ulashe, k'arfe hud'u zai shigo gida don haka bayan mun gama komai sun k'ara gyaramin gidan suka koma part d'in su.


Wanka nai nazo na zauna bakin gado gabana na k'ara tsananta fad'awa jikina harya fara rawa, ambaton Allah nai tayi sannan nutsuwa ta saukar min, cikin rashin kuzari na kimtsa tsaf cikin wata doguwar riga y'ar k'asar dubai pink color ce an mata adon stone silver, kyau iya kyau rigan nadashi, jikina na wanke tsaf da turare masu d'aukan hankali, bansa d'an kwali akaina ba gashi na da yasha gyara na k'ara tajewa na shafeshi damai sannan na sake shi ya zuba baya, na d'auko plate d'in takalmi kalan kayan nasa a kafata don ban yawo ko cikin d'akina ne ba takalmi sabida sanyin tile's, kasancewar cikin sanyi nake yin komai yasa na d'au lokaci don Dana duba agogo ya muna min uku da kwata, na tabbata zuwa 30 minutes zai iya shigowa gida, don su sweety ita da Abba dasu yaran tuni suka k'arasa Airport don tararsa,


Parlour na dawo na zauna ina tunani kala kala cikin raina, can naji tsayuwar motoci a harabar gidan da sauri naje jikin window d'in da zai sadani da kallon duk abunda ke wakana a k'asan harabar, shine ya fito daga motar sanye da k'ananun kaya jikinsa kalan brown Wanda suka amsheshi sosai k'afansa sanye da brown takalmi sau ciki,haka ma fatan agogon hannunsa take brown, kallo d'aya zaka mai ko daga nesa ne ka tabbatar da tsantsar kyawun da yayi hakama fatar jikinsa tai frees alamun ana hutawa. Gaisawa yake da ma'aikatan da suka taso suna gaida shi,yayin dasu Abba da duk y'an rakiyar tashi sukai mai sallama suka juya zuwa gida Abba yace abarshi ya huta zuwa jimawa sa k'ara gaisawa.


Yanda yake taka k'afafunsa yana tunkaro cikin gidan haka k'arin bugun zuciyata ke tsananta, gumi ya gama lullib'e ilahirin jikina,k'afafuna da hannayena wani bala'in karkarwa suke, na jingina kaina jikin window d'in ina ambaton Allah da neman d'aukinsa.


A babban parlourn k'asa ya dakatar da ma'aikatan da suka biyo shi da jakunkunansa, tsayawa yai yana k'arewa parlourn kallo fuskar sa d'auke da mirmishi kallo yake yaga ta inda zan bayyana jin shiru yasashi sakin wani k'ayataccan mirmishi ina k'iyasto dad'in da zai kwasa yanzu ba anjima ba,juyawa yai ya rufe k'ofan parlourn ya fara taka k'afafunsa zuwa matakal da zata sa dashi da saman benan, cikin wani cool voice yake fad'in "my pretty! my angle! my heart! my sweetness! My heartbeat fito mana in ganki idanuwa da ruhina duka sun matsu su ganki don Allah yi sauri ki fito ina marmarin jinki a cikin k'irjina, zo inji d'uminki, fad'a yake yana lallek'a d'akunan harya k'araso d'akin da nake ganina tsaye na juya baya yasa shi k'arasowa da sassarfa yana fad'in" badai fishi kuma ake dani ba don na dad'e ban hayo saman ba, wata wawuyar runguma yamin ta bayan yana kwantar da fuskar sa akan wuyana tare da sakin wata nauyayyar ajiyar zuciya, matseni ya k'arayi a jikinsa yana jin wani nishad'i na saukar mai, a hankali ya juyo dani idonsa a lumshe yana k'ok'arin sanyani cikin k'irjinsa jin abu ya tokare shi yasa bud'e idonsa yana kai kallon sa ga cikina, k'ara bud'e idonsa yai sosai don yaji kamar gizo abunda ya gani idonsa kemai d'an janye ni baya yai yana kai hannunsa kan cikin ya danna jin tauri yasa shi d'agowa da sauri yana kallona Wanda zuwa lokacin har hawaye ya gama jik'a fuskata jikina kuwa kamar mazari haka yake rawa idonsa ya zuba sosai cikin nawa yana son tunano meyema wannan a jikina, don shi duk tunanin sa ya tsaya,tsawon lokaci muna tsaye a haka,a hankali kuma ya zame jikinsa a jikina ya zauna bakin gadon dafe da kansa, ni kuwa banma sami sukunin zaman ba ina dai tsaye jikina nata mazari kamar nayi sata an kamani, can sama da mintina goma ya d'ago da idonsa da suka kad'a ya saukesu a kaina, cikin k'arfin hali ya fizgo maganar dake son fitowa daga bakinsa, "Khadeejah meye wannan a jikin ki"?.

Sunkuyar da kaina k'asa nai don banda amsar bashi,muryarsa naji tsakiyar kaina yana k'ara tambaya ta Karo na biyu, nanma ba amsa shiru nai,wata razananniyar tsawa naji ya sakar min karo na uku yana tambaya ta meye wannan a jikina, jinai cikina ya murd'a abunda ke cikina ya dunk'ule ya tare waje guda sanadiyar haka naji fitsari ya fara bin k'afafuna, cikin sark'ak'k'iyar murya na fara fad'in" Kayi hak'uri don Allah ka yafemin wlh ban san ya zaka d'au lamarin ba shiyasa ban sanar dakai ba tun tuni".

Hannu ya d'aga min yana mik'ewa tsaye cikin tsananin b'acin rai yace "ba wannan na tambayeki ba ca nai ki fad'a min meye wannan a jikin ki".

Cikin tsananin kuka nace " Ciki ne".

"Ciki ? wa yai miki shi".

Cikin firgici na d'ago idona a kansa ina kallon sa, kafin daga bisani naji zuciyata ta soye kukan ma ya d'auke k'af nace " Me kake nufi ne umar me kake nufi? Kana tambaya ta wayamin ciki akwai Wanda zaimin ciki ne bayan kai,to kai kamin shi cikinka ne dana taho dashi daga India Wanda na same shi satin da zan baro India, inka so ka yarda".

Zuba min ido yai cikin tsananin b'acin rai yana gyad'a kai yace" naji naji amma meye dalilin da kika b'oyemin tun sanda kika san da zamansa a jikin ki,Khadeejah tun yaushe nake fad'a miki ban shirya fara tara y'ay'a ba sau nawa na sanar dake haihuwa bata cikin tsarina a shekara uku ma nan gaba, na sanar dake ban so ban so, ban shirya tsufa yanzu ba,banso ban marmari,amma don ha'inci irin naki sai kika b'oyemin tun sanda za'a iya zubar dashi,yanzu a lissafe nasan yafi wata takwas yanzu duk dabarata nasan sai kin haife wannan cikin, tom kinyi kuskure na farko a cikin rayuwar ki ,saida kika bari na aminta dake sannan zaki haince ni,to kije ki haifeshi ki raini abunki".



Daga haka yasa kai ya fice yabar d'akin.







Taku ce
Y'ar mutan ja'ojiπŸ™‹βœ
🍑🍑🍑🍑🍑🍑
🌸🌸🌸🌸🌸🌸
*'YAN* *ARABIC*
🌸🌸🌸🌸🌸🌸
🍑🍑🍑🍑🍑🍑

*NA*
*LAYUZA* *KABIR* *ADAM*

_DEDICATED_ _TO_ _ALL_
_ARABIC_ / _ISLAMIC_ _STUDENTS_
πŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“š


πŸ‘©πŸ»β€πŸ’»πŸ‘¨πŸ»β€πŸ’»
*ZAMANI* *WRITERS* *ASSOCIATION*
πŸ“
_We_ _are_ _here_ _to_ _educate_ , _motivate_ ,and _entertain_ _our_ _Readers_



0⃣4⃣9⃣


Da kyar yakai kansa d'akin dake daura da nata dafe da kansa ya fad'a bisa faffad'an gadon yana runtse ido tare da furzar da iska me zafi,cije lips d'in sa yai yana fad'in "why why? Khadeejah zaki min haka,me yasa zaki yaudareni,me yasa zaki b'oyemin? Kin san yanda na dawo da k'ishin ruwan ki kuwa,kinsa yanda zuciyata kemin rad'ad'i kuwa,na tara buk'ata ta watanni takwas ina zumud'i da marmarin k'arasowa gareki ki biya min buk'ata ta amma gashi daga dawo wata naci karo da bak'in ciki da b'acin rai, naci karo da abunda ya canja tunani, kin yaudare ni Khadeejah, kin

Please Login or Register in order to submit comment