Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yini don itama in taje gidansu yini cur takeyi,
Haka badan taso ba ta zauna.

Kiran Abbansu sweety tai tayi a waya tana fad'a mishi Nahnah tazo ya dawo da wuri su gaisa.


Suna zaune a parlour sunata hira wata y'ar aiki ta shigo da kayan fruit yankakku tazo ta ajiye gaban Nahnah ta juya zata fita wata uwar tsawa sweety ta buga mata"keee jaka mahaukaciya, haka ake ajiye abu gaban mutane".

Jiki na rawa ta dawo ta k'ara gyarawa bowel d"in zama kan center table d'in.

Wani kallo Nahnah tabi Sweety dashi na rashin jin dad'in abinda tayi, ta kalli y'ar aikin tace "jeki abinki".

Bayan fitar ta sweety tace"Nahnah ya naga kin canja fuska haka?.

" gaskiya banji dad'in abinda kikai mata ba, ai d'an Adam ba abin wulak'antawa bane, dukda tana aiki k'ark'ashinku kinci zarafinta wlh".

Ta k'arashe maganar cikin yanayin b'acin rai,

"Hhhmmm Nahnah biki san way'annan y'an aikinba,basu da nutsuwa ko kad'an".

"Duk rashin nutsuwarsu basu can canci dizgi irin haka ba, tunda har Allah ya karrama d'an Adam ya dace muma mu karrama kanmu mu girmama junanmu, gaskiya sweety in har kina son mu shirya dake karki k'ara irin haka ba kyau irin hakan kinji".

Jin jina kai tai tare da fad'in "shikenan na daina Nahnah".

Cike da mirmishin farin ciki tace"yawwa my Sweety na gode da fahimtata da kikai".

Daga nan suka shiga wani zancen har Abbah ya dawo suka gaisa da Nahnah yaita sa mata albarka don shima zuciyansa na matuk'ar k'aunar Nahnah.

Da yamma Sweety ta dawo da ita gida a motanta, tare da tarin kayan kwalliya da turaruka Wanda ta had'a mata,sannan Auntynsu ta bata tirmin atamfa da wani less d'an ubansu da mayafi, sannan Abbah ya bata 20k Wanda tak'i amsa Sweety kuwa tasa mata cikin jakanta bata Sani ba, saida tazo gida ta gani. ta d'auka ta
kaiwa Yaya Haroon wai ya mayarwa Abban sweety ita bazata amsa ba, yaya yace " a'a ba haka za'aiba don Alh, baya son yayiwa mutum kyauta yak'i karb'a".

Don haka ya kirashi a waya yamai godiya, sannan ya bawa Aunty Hafsa kud'in yace ta ajiyewa Nahnah in tana buk'atan siyan wani saita bata.

Nahnah tai shiru can tace" yaya ba abinda zan buk'ata dasu,ka d'auki " 15k,ka bawa Aunty 5k".

Mirmishi yaya yai yana jin dad'in hankali da nutsuwa irinta Nahnah khadijah autar Baffah.πŸ˜€

K'irgo 5k Yayi ya mik'awa Aunty Hafsa,sannan ya k'ara k'irgo wata 5k d'in ya mik'awa Nahnah yace "to rik'e wannan a hannunki, karkice komai daga haka".

Badan zatai wani abu dasu ba amsa.








Taku ce
Y'ar mutan ja'oji.πŸ™‹β€β™€
🍑🍑🍑🍑🍑🍑🍑
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
🌸 *YA'N* *ARABIC*🌸


*NA*
*LAYUZA* *KABIR* *ADAM*
​

_DEDICATED_ _TO_ _ALL_
_ARABIC_ / _ISLAMIC_ _STUDENTS_
πŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“š



πŸ’» *ZAMANI WRITERS ASSOCIOTION*

πŸ“ .
​​WΙ› Ι‘Κ€Ι› Ι¦Ι›Κ€Ι› tΡ³ Ι›Ι—ucΙ‘tΙ›, MΡ³tiΡ΅Ι‘tΙ› Ι‘Ι³Ι— Ι›Ι³tΙ›Κ€tΙ‘iΙ³ Ρ³uΚ€ ʀɛɑɗɛʀร​​

β€‹πŸ“š ​​Zaku iya samun littafan mu a Facebook​​ πŸ‘‡πŸ½
Fb.me/ZAMANIWRITERSASSCIATION


πŸ“© ​​Zaku iya aika mana sako ko korafi, Ta email namu​​ πŸ‘‡πŸ½
Zamaniwriterassociation@gmail.com



0⃣8⃣



Haka rayuwa taci gaba da garawa, lokaci yai nisa, Nahnah sun cinye semester sunyi exam har sunje tak'aitaccen hutu sun wuce T.P, nan wata secondary skul ta maza dake bayan gidansu taje, duk da taso zuwa ta bawa makarantarsu ta bada gudummawa, amma yaya ya bata shawaran taje wannan d'in,tunda itama Arabic skl ce, bata ja kan maganar yaya don haka kai tsaye ta zab'i wannan d'in, duk da tarin tsoron koyar da mazan da takeyi.

Ga duk Wanda yasan yanayin koyar da d'alibai maza zataga yasha bamban dana mata, duk iya shegen d'aliba mace tanayiwa malami ne bayan idonshi kama daga sawa malami suna yimai izgila, gwada irin tafiyarshi ko yanayin koyarwarshi, kaikwayen maganarsa da duk irin wannan iskanci d'aliba mace tanaiwa malami ne bayan idonsa, amma d'alibi namiji inka bari ta had'oka dashi zaka ga tijara mabanbanta.

Kashi ne da wulak'anta babba ga malami yaje koyarwa bai san me zai koyar da d'alibi bai San ina ya nufa ba, ma'ana dai ya zama garmaho yaita Kame kame gaban d'alibai, wannan ba k'aramin kaskanci take jawa malami gaban d'alibi ba.

Duk irin wannan matsalolin malamansu sun nusar dasu kafin tafiyarsu, don haka Nahna tun kan tafiyarta (T.P) ta shiryawa kanta rayuwar da zatai don kaucewa duk wata matsala.

S.S 1 aka bata da J.S 2 zata rink'a musu Qur'an da tajweed, sannan tai musu Hadith da musd'alahul Hadith,
Sukuma J.S 2 tai musu Qur'an da fiqihu,

Duka course ne masu zafi wajen koyarwa, don haka ta dage wajen bincike (Ψ¨Ψ­Ψ«) don harkar koyarwa tana buk'atar malami ya Zama kullum cikin bincike, musamman data lura da wani abu tun ranar da sukaje za'a k'addamar dasu gaban d'alibai, malami na farko yaje zai gabatar da kansa ya farayi da Hausa taga wani gani gani da sukeyi mai suna dariya, To na biyu da yake malamin English ne sai yai da turanci, haka akaitayi wani yai da Hausa wani da turanci, don haka tasa aranta da Arabic d'inta zatayi duk kuwa da taga d'aya namijin d'an Department d'insu ne na Arabic amma yai da turanci don a tunaninsa zaifi birgewa, ita kam ana zuwa kanta, bayan tai sallama tai gaisuwa ga malamai ta fara gabatar da kanta cikin harshen larabci, Wanda yaja hankalin d'alibai da malaman, kai tsaye kowa ya gane wace ita da kuma girmama harshen da take koya kuma zata koyar, tun anan ta gane abubuwa da dama don haka ta dage wajan karrama larabci.

Tana jin dad'in koyarwar sosai,don bata fuskantar wata matsala bangaren karatu tsakaninta da d'aliban, sai dai abinda ba'a rasa ba.


D'alibai zama dasu saida taka tsantsan musamman maza, wani sa'in tana musu karatu tana ji zasu rink'a gulmar wasu malaman suna zaginsu, ita kanta tasan bata tsira ba dukda girmamata da sukeyi, amma wani lokacin tana kula da d'an iskancin da sukeyi tasan da ita suke.

Tunda ta fara zuwa da hijab take zuwa, yau kam tai sha'awar saka mayafi, tai kwalliyanta tasa mayafinta na kirki, Tana shiga skul d'in daga bakin gate taga yanda d'aliban ke kallonta,amma bata damu ba ta wuce staff room d'insu, lokacin shigarta aji yanayi ta tashi zuwa ajin, amma tana shiga sai taga d'aliban sun juya suna kallon wani d'alibi tare damai dariya, suna magana k'asa k'asa, kasancewar bamai shiga sabgar d'alibi bace damusu shishshigi cikin lamuransu yasa bata tsaya tambayarsu meke faruwa ba ta shiga yin abinda taje yi.

Tun daga ranar ta fuskanci data shiga ajin zataga suna kallon Hasheem suna dariya da k'us k'us, don haka ta gano wani abu,amma saita basa.

Wata rana an tashi tana tsaye bakin gate tana jiran wata malama dasuke T.P d'in tare yar layinsu ce, daga bayanta taji hiran da suke Wanda su Sam basu ma lura da ita ba, don gun a cakud'e yake d'alibai,

"Kai Yusuf wlh Allah da gaske Hasheem son malama khadeejah yake, don gashi yace yanzu har kasa bacci yake sabida tunaninta".

"He heeeeee jimin d'an iska kai yanzu malamar taka kake so"?

"To bazai sota ba akwai haramci aciki ne"

"Hheee heeee, ba haramci amma akwai iskanci, d'alibi yace yana son malamarsa"

"Wlh ba wani iskanci, ko a girme dai nasan Hasheem ya girmeta kawai don dai karatu yamai gardama ne,amma ko yanzu yaje k'ofar gidansu zance fitowa zatai"

"Hhhmmm wlh ni ko abinda ke birgeni da malamar dad'in muryarta, kanaji fa in tana mana karatu Qur'ani kamar balarabiya, kawai sai inji wani shauk'i ya kamani,ga idanuwanta kalan love shiyasa nake surutu in tana karatu data d'ago tamin kallon nan na kai shiru sai inga kamar kallon k'auna ne".

Ihu sosai sukasa suna k'yalk"gala dariya,

"Kai dallah kuzo mu wuce wannan gayan bazai fito ba".

Haka suka wuce suna ci gaba da hiram ba tare da sun San da ita a gunba.


Kunya, fargaba, b'acin rai suka bai baye Nahna taji inama bata tsaya gunba, wane b'acin raine wannan ace d'alibinka yace yana sonka,πŸ€” inama batazo wannan makarantar ba inama inama.

Tanata wannan nazarin Malama ummi ta taho suka tafi, Sam bata malama ummi bata lura da yanayin da take ciki ba,don haka taketa janta da hira, ita kam sai dai tace um da um um, a haka har suka k'arasa layin nasu kowa ya shige gida.


Tun daga ranar tsakanin Nahnah da d'alibanta sai d'aure fuska yanda take sakar musu tayi musu karatu cikin raha duk ta rage, don haka sukasha Jinin jikinsu suka kama Kansu, ahaka har suka cinye watannin da zasuyi a T.P suka fara shirye shiryen komawa skl su k'arasa semester guda data rage musu.




****************
B'an garan dangantakarsu da sweaty sai abinda yai gaba don yanzu sun k'ara k'ullewa sun zama Aminan juna, sweety tana cin ribar zama da Nahnah sosai don Nahnah bata barin sweety tayi wani abu ba dai dai ba saita nuna mata rashin dacewar hakan, zamanta da ita gashi tana k'ara fahimtar da ita kan abinda ya shafi addini musamman b'angaran fiqihu, don haka sweety take k'ara ganin girman Nahna da k'imarta.




*************
B'angaran samari kuwa Nahna bamai ra'ayinsu bace, bata bawa ko wane saurayi dama akanta don haka duk layinsu suke mata kallon me girman kan tsiya, har wasu na fad'in kwad'ayi da son abin duniya ke sata wulak'antasu ,shiyasa ma ko k'awaye bata dasu sai y'ay'an masu kud'i irinsu sweety take kulawa.


Duka zantuttukansu basa damunta, ita dai bata shiga sabgarsu, don tasan ita bamai kwad'ayi bace kamar yanda suke fad'a yayanta ya tsare mata komai na rayuwa, dukda bai zama me kud'i ba amma me tarin rufin asiri ne.





*TAB* ' *D'I* *JAN* πŸ€”.
Rana ta farko da Nahna ta gane UK yayan sweety ne taji ba dad'i matuk'a don bata so wani abu ya k'ara had'ata da UK koda kuwa hanya ce, tasa aranta tunda yabar skl d'insu tsawon shekara biyu to bazasu k'ara had'uwa ba, amma me yau taji abunda ya kawar mata da farin cikinta kai tsaye.


Tun had'uwar Nahna da sweety takejin labarin Broth Dady a bakin ta, kullum hiranta saita saka da broth d'inta don shak'uwace me tsanani a tsakanin Sweety da D'an uwanta ko Auntynta ummu sulaim da take mace basu shak'u da itaba kamar broth Dady,Don haka tasanshi sosai a bakin sweety, kasancewar yana k'asar waje yaje yin course na shekara biyu yasa basu tab'a had'uwa na, ko a photo bata tab'a ganinsa ba don ita bamai bincike bace a wayar mutane dukda yanda suke da sweety bata tab'a d'aukan wayanta ta kalli pic's ba musamman data lura komai na wayanta akwai cord akai, sannan tasha cemata zata had'a had'ata dashi a waya su gaisa amma saita nok'e don bata son tura kai inda Allah bai kaita ba, sannan bata tab'a shiga main parlour d'insu ba, kullum ta k'aramin parlour take shiga ta wuce d'akin sweety, hakan yasa bata tab'a cin karo da pic d'insa ba.

Yau kam tana zuwa gidan don dubata batada da lafiya su haris sukace mata sweety na babban parlour, don haka ta tsaya ta kirata a waya tace tana k'aramin parlour tana jiranta, kai tsaye ta fito tana fad'in

"daman zakizo da gaske, ke kamar bak'uwa sai ki rink'a wani abu"

Murmishi Nahna tai batace komai ba suka shiga parlourn, inda Nahna taga abinda ya girmi rayuwarta wato kansa girmansa abin Jan hankali ne balle tsaruwarsa,

Basarwa Nanha tai ta samu waje ta zauna tana gaida Aunty murja da Abbansu suka amsa, tace yamai jiki suka amsa da sauk'i, Abbah yace" kinga tun d'azu ake fama taci abinci tak'i don haka ma na dawo daga office amma tak'ici"

Kallonta Nahna tai tad'an harareta tace "ke sai kace wata yarinya aita fama dake kici abinci kik'i bari in tafi gidama tun kafin ki b'ata min rai".

Da sauri ta rik'e hannunta tana marai recewa "kai my Nahna don Allah karki tafi ni abincin ne banso ko zakimin wannan abin da kikai min agidanku rannan".

"Um zan miki taso muje kitchen d'in naku".

Dariya tasa tana fad'in " yawwa dear na gode, Abbah bari yanzu zakaga naci abincin da yawa".

Suna zuwa kitchen d'in tacewa sweety "d'auko eggs guda biyar ki d'ebo dankalin Hausa guda biyu madai daita ki kawo taruhu guda biyu manya da albasa babba guda d'aya da magi".

Kafin minti ashirin harta gama, palourn suka dawo ta zauna ta cinye tsaf tasha magani,nan Abbah yai tasawa Nahna albarka yana ta mata godiya, itakam Nahna har kunya ta kamata tacewa sweety "mu koma d'akinki"

Tashin datai zasu fita idonta ya fad'a kan k'aton pic d'in dake mak'ale a saman k'ofar fita, dam taji gabanta ya fad'i don bazata tab'a manta wannan fuskarba har abada kuwa.

Jitai kanta na juyawa da k'yar ta k'arasa d'akin, zuciyarta cike da tunanin me had'in UK da gidan nan harda akasa pic d'insa a gidan.

Sweety ta kula da canjawar Nahna don haka tace " yadai dear naga kinyi wani iri?"

Basarwa tai tace "a'a ba wani abu kaina naji yad'an Sara min amma normal ne".

Hira suke d'an tab'awa Nanah ta soko zancan "Sweety naga pic d'in wani a k'ofan fita a parlour d'inku wane ne"

" wai bikisan waye ba? Broth Dady nefa, bari in nuna miki a wayana ki gani, daman tun zamanmu biki tab'a ganin pic d'insa cikin wayana ba? ai broth d'ina babban yaro ne hands some guy"

Mik'o mata wayan tai tana fad'in "kalli kiga duka wannan folder d'in pic d'insa ne, ina zuwa bari in d'an watsa ruwa ko jikin ya k'aramin k'arfi".

Ina! Ai Nahnah batama jin me sweety ke fad'i don hankalinta duka ya koma kan photon.. . . .










Takuce
Y'ar mutan Ja'ojiπŸ™‹β€β™€
🍑🍑🍑🍑🍑🍑🍑
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
🌸 *YA'N* *ARABIC*🌸


*NA*
*LAYUZA* *KABIR* *ADAM*
​

_DEDICATED_ _TO_ _ALL_
_ARABIC_ / _ISLAMIC_ _STUDENTS_
πŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“š



πŸ’» *ZAMANI WRITERS ASSOCIOTION*

πŸ“ .
​​WΙ› Ι‘Κ€Ι› Ι¦Ι›Κ€Ι› tΡ³ Ι›Ι—ucΙ‘tΙ›, MΡ³tiΡ΅Ι‘tΙ› Ι‘Ι³Ι— Ι›Ι³tΙ›Κ€tΙ‘iΙ³ Ρ³uΚ€ ʀɛɑɗɛʀร​​

β€‹πŸ“š ​​Zaku iya samun littafan mu a Facebook​​ ??🏽
Fb.me/ZAMANIWRITERSASSCIATION


πŸ“© ​​Zaku iya aika mana sako ko korafi, Ta email namu​​ πŸ‘‡πŸ½
Zamaniwriterassociation@gmail.com





0⃣9⃣



Nahna sosai hankalinta ya tashi, taji lokaci guda ranta ya b'aci tai danasanin mu'amala da Sweety, domin da tasan k'anwar UK ce da batai gangancin k'awance da ita ba, pic's d'inshi sun kai 70 cikin folder d'in, wani shi d'aya wani shida ita wani da duk y'an gidan nasu, wani da friend d'insa, gasu nan dai tari guda bata iya ko kallan goma ciki ba ta runtse idonta tana karanta "Innalillahi wa'inna ilaihi ra'jiun"

A hankali nutsuwa tazo mata ta daidaita tunaninta jin sweety na k'ok'arin fiowa a toilet d'in,
" My Nahna kinga broth d'ina ko,had'ad'd'an gaye ne fa, babban yaro Wanda duniya ke yayi, baya harka da tsamaye komai nashi a tsari yake, classes guy ne fa".

Saida takai aya Nahna cikin basarwa irin tata tace" ya Allah! dear wannan irin yabo haka kin dage kinata wasa D'an uwanki haka ".

Sosai sweety ta kalli Nahna sannan ta zauna bisa stool tana pacing d'inta tace" Khadeejah ! Ina son broth d'ina, ina ji dashi matuk'a,kamar yanda yake matuk'ar sona, broth d'ina ya girmemin sosai amma hakan baisa ya nuna son girmanshi akaina, bashida abokin hira kamarni, dukkan abinda nake so yana sonshi, don haka nakeyinsa matuk'a, b'angaran had'uwa yaya na k'arshe ne, aji ne shi, tun ina k'arama yake koya min yanda yakeso inyi rayuwa ta gayu ,yana son inyi mu'amala da gayu don bai son k'aramar harka, hhhhhmmm bari kawai Nahna ina ji da broth".

" hhhhmmm Sweety me broth".

Juyawa tai taci gaba da shirya kanta gaban mudubin tana fad'in " Khadeejah dama dama dama zaki amincewa buk'atata ki yarda da soyayyar d'an uwana, tun tuni nake sha'awar had'aki da shi matsayin masoya, Nahna ina sonki ina son ki auri broth d'ina don Allah".

Cikin wani tashin hankali Nahna ta dubi Sweety idanuwanta duka a waje tace " a'a bari sweety banson wannan maganar, don Allah karma ki soma wlh, babu wata alak'a tsakanina dashi ta arzik'i balle har aure, gaskiya ban son irin haka karki k'ara min irin wannan maganar".

Mik'ewa tsaye tai fuskanta babu alaman rahma don ranta a b'ace yake ta d'auki jakanta tace " zan wuce gida Allah ya k'ara miki lafiya me d'orewa".

Mamaki ne k'arara akan fuskan sweety don ita bataga abunda ya d'agawa Nahna hankali haka ba,

Rik'eta tai da k'arfi tana fad'in " haba khadeejah me yai zafi haka cikin zance na harda ya d'aga miki hankali haka,cool down Nahna mana. . ."

Tattaro nutsuwarta tai ta d'an sassauta fuskanta tare da fad'in" ba wani abu sweety kawai banson wani maganan soyayya ne yanzu cikin rayuwa ta".

Ajiyan zuciya me k'arfi sweety ta saki " To don Allah kiyi hak'uri ban son ranki zai b'aci ba amma insha Allah bazan k'ara miki maganan nan ba kinji".

"OK ba damuwa, zan wuce gida ".

Bata jira me zata k'ara cewa ba tasa kai ta fice, ba tare data jirata ba don tai mata rakiya.




*********
Zuciya a cushe Nahna taje gida, don tsohon tsimin da UK ya dasa mata a zuciya yau kam ya tashi, duk duniya babu mutumin daya wulak'antata ya tozartata sama da UK , ya cusgunawa rayuwarta matuk'a ya b'ata mata rai ganin UK bai tab'a zama alkairi a gareta, duk sa'in da zasu had'u saiya wulak'antata ganan mutane, shin yaushe ne zuciyarta zata daina ganin bak'in UK, amma wai har Sweety take k'ok'arin had'ata dashi, to ko maza sun k'are me zatai dashi mutumin dabai San darajar d'an Adam ba.

Haka ta yini ranar zuciyarta a damule har Aunty Hafsa ta ganota, amma data tambayeta meya faru sai tace kanta ne ke ciwo daga haka ta wuce d'akinta ta kwanta.


*********
Can gidansu sweety kuwa ta cika da mamaki matuk'a don bata tab'a ganin Nahna cikin makamancin yanayin ba, ta San Nahna Me sanyi ce da taushin hali ba abu k'arami kesa kaga fishinta ba,amma daga cewa zata had'ata da broth d'inta sai ta b'ata rai haka.



************
Bangaran Abbah kuwa bayan fitar Sweety da Nahna daga parlour ya dubi Aunty Murjah yace " murjah wani abu ne yake min yawo arai dangane da yarinyar nan Khadeejah, tun randa na fara ganinta a asibiti naji yarinyar ta burgeni matuk'a nutsuwarta, kamun kanta, yarinyar tanada hankali sosai, don haka murjah nake ganin da zan samu yanda nake so da na had'ata da Daddy na, ko me kike gani".

Dogon numfashi Taja tana tunanin felek'e irin na Dady,donshi d'an k'yale k'yale ne komai bai son inba Wanda mutane zasuce yes ba, don haka tana tunanin bazai amince da tayin Abbansa ba. .. . . .

Katseta yai da fad'in "ya kikai shiru murjah ko da Matsala ne"?

"A'a Alh. daman ina tunanin Dady ne, baka tunanin zaik'i amincewa? Kuma itama yarinyar baka tunanin ko tanada Wanda take so?"

Shafa kansa yai a hankali yana wani d'an tunani zuwa jimawa yace" duka wannan matsalar baza'a rasa ba amma babbar matsalar ace yarinyar nada Wanda zata aura, amma donta Dady ko baiso sai ya aureta hak'ik'a amma zanyi dogon nazari tukun,don matuk'a ina k'aunar yarinyar nan wlh zanso ta zama cikin zuri'ata da yardar Allah".


Ajiyan zuciya tai tace "To Allah ya tabbatar da abinda yake alkairi".


********

Da gasken gaske Abbah kejin wannan had'in da yakesonyi cikin zuciyarsa duk da yasan waye d'anshi, yasan Dady da abinda yake so, yasan Nahna bazata zamo daga cikin zab'insa ba tunda ita ba babbar yarinya bace me yafa mayafi iya wuya, ita ba y'ar shahararran me kud'i bace yar masu rufin asiri ce kuma masu wadatar zuci, amma bazai karaya ba yanzu dagewa zaiyi da k'ulla alak'a fiye da da tsakaninsa da Yaya Haroon har yakai ga gaci, don yana hango alkairi matuk'a tsakanin d'ansa da Nahna tunda yasan d'ansa ba wani nutsuwa ce dashi ba amma yasan da yardar Allah Nahna zata zamo fitila gareshi.




******
Bayan kwana biyu Sweety tanata kiran wayar Nahna amma duk sai tajita a kashe tana son ta k'ara bata hak'uri duk da tana ganin rashin takamaiman abinda yasa Nahna fishi amma dai itace sila don haka ya dace ta nemeta, gashi wayanta bata shiga don haka ta shirya zuwa gidansu ta k'ara bata hak'uri.







Taku ce
Yar mutan ja'ojiπŸ™‹β€β™€πŸ˜œ
🍑🍑🍑🍑🍑🍑🍑
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
🌸 *YA'N* *ARABIC*🌸


*NA*
*LAYUZA* *KABIR* *ADAM*
​

_DEDICATED_ _TO_ _ALL_
_ARABIC_ / _ISLAMIC_ _STUDENTS_
πŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“š



πŸ’» *ZAMANI WRITERS ASSOCIOTION*

πŸ“ .
​​WΙ› Ι‘Κ€Ι› Ι¦Ι›Κ€Ι› tΡ³ Ι›Ι—ucΙ‘tΙ›, MΡ³tiΡ΅Ι‘tΙ› Ι‘Ι³Ι— Ι›Ι³tΙ›Κ€tΙ‘iΙ³ Ρ³uΚ€ ʀɛɑɗɛʀร​​

β€‹πŸ“š ​​Zaku iya samun littafan mu a Facebook​​ πŸ‘‡πŸ½
Fb.me/ZAMANIWRITERSASSCIATION


πŸ“© ​​Zaku iya aika mana sako ko korafi, Ta email namu​​ πŸ‘‡πŸ½
Zamaniwriterassociation@gmail.com



AYIMIN AFUWA READERS πŸ™,WLH TYPING NE BA DAD'I INA SON YIN POSTING KULLUM AMMA BA DAMA SABIDA YANAYIN ABUBUWAπŸ˜€
KUDAI GANE KAWAI READERS.

INA GODIYA DA K'WARIN GWIWARKU GARENI Y'AN GROUP D'IN Y'AN ARABIC ,KARKU DAMU ZAKURINKA JINA AKA-AKAI INSHA ALLAH.






0⃣1⃣0⃣



A yanda Sweety taga Nahna ta tareta ba wani damuwa akan fuskanta, cikin fara'a da murna kamar yanda ta saba kullum,bayan sun gaisa da Aunty Hafsa suka shige d'akin ta.

"Nahna manya, kin tafi da fishi kuma kin kashe wayanki don karma in kira ko".

"Hhhhmmm ban kashe waya don keba, kawai ina son in huta 2 day's shine na ajiyeta".

Kallonta tai sosai tana d'an mirmishi tace "To nidai zuwa nai in k'ara bada hak'uri don Allah, ban San maganata zata b'ata ranki ba".

"Karki damu ya wuce, daman ni batun soyayya ne kawai banso".


" hhhhhmmm Nikam sai nake ganin kamar da matsala akan wannan ra'ayin naki, don kuwa farin cikin rayuwa baya cika saida soyayya".


Cikin basar da zancen tace " kin tsareni da surutu ko ya jiki ban k'ara miki ba, ina fatan dai kin warke sosai".


"Tunda kika ga na fito ai na warke".

Cikin tsokana Nahna tace " a'a kefa k'afar yawo ce ko biki warke ba in ya motsa miki sai kin fito".


Dukan wasa ta kaimata tana cewa "ji sharri nice k'afar yawon, wlh in ba skl ba da nan gidan

Please Login or Register in order to submit comment