Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tashi a gunmu da wuri su Hafsa busu tashi ba nakan shiga gunsu in zauna anan ma na d'an koyi kwalliya irin wadda ake yayi, tare da gyaran gashi.


Cikin nasara muka gama entrepreneurship d'inmu , aka bamu shaidar kammalawa "certificate".


Duk wani abu daya dace muyi a school d'inmu munyi mun had'a duk Slip's d'inmu dasu semester form zuwa duk wasu takardu da ake buk'ata munyi bucking result.


Sati shida dayin bucking d'inmu result d'ina ya fito tare da tarin nasarori ,ranar Dana amshin result d'ina na shaidar N.C.E ina zuwa gida na zube nai sujudishshikur ga ubangijina na gode mai tare da naiman agajinsa a karatuna na gaba da zan d'ora.

Aunty cike da farin ciki ta d'auki Waya ta kira Yaya, ai kuwa ba'afi 30 minutes ba sai gashi a gidan fuskarshi d'auke da fara'a yazo yakarb'i result d'in yana dubawa ,ai kuwa hak'oransa tar a waje ya dube ni yana fad'in " Alhamdulillah, Allah kaine abin godiya Autar Baffah ta fito da kyakyawan sakamako ,Allah ya sanya alkairi, yayi miki jagoranci a karatun da zaki d'ora"

"Ameen ameen yaya" abinda kawai naketa maimaitawa kenan zuciyata da fuskata cike da tsantsan farin ciki.



Da dare ina kwance d'aki ina charts saiga kiran sweety ya shigomin, saida nai d'an mirmishi sannan na d'auka, bako sallama ta faramin k'orafi,

"Lalle Nahna kin kyauta kin nuna min ni d'in ba komai bace a gunki biki d'aukeni yanda na d'aukekiba ,wai Nahna har ki karb'i result d'inki amma ki Kasa fad'amin sai a status d'inki naga kinsa, ba komai na gode".


K'it naji ta kashe wayan, mirmishi na kuma sannan na bita ,harta kusa katsewa sannan ta d'auka,

" haba tawan kinsan ke d'in ta dabance a guna, Abubuwa ne kawai sukai min yawa shiyasa ban samu kiranki ba kiyi hak'uri kinji my sweety ".


Sai sannan naji ta d'anyi dariya sannan ta faramin murna tana min fatan alkairi, nan muka d'an tab'a hira sannan mukai sallama.


Tun a washe gari Yaya yaje ya siyamin form d'in degree, yana kawomin naje cafe na cike tare da tura musu, ba'a d'au lokaciba muka gama komai na fara lecture inda suka bani level 2.


Yanzu banda wani ishashshen lokacin zama a gida kullum in na fita tun safe sai yamma lis, don haka na manta da duk wani Abu sai karatuna kawai nasa agaba.



Fannin addu'a kuwa ban gaza ba kullum nai sallah saina rok'i ubangiji ya tabbatarmin da alkairi cikin wannan had'in.


Addu'ar da nake yasa naji hankalina yana k'ara kwanciya, yanzu banjin tashin hankalinnan da nakeji inna tuna batun auran.



Kwanaki sukaita wucewa bikin Yaya usman ya matso don yanzu saura wata guda cif, munata shirin biki harda sweety don tunda na fad'a mata zancen bikin tace ai tafiyar da ita za'ayita itama zata garinmu,don haka duk ankon bikin da aka turo mana sakkwato tare yaya ya siya mana, ashe itama acan tasa Abbansu yai mana sabbin d'inkuna har kala hud'u hud'u Kaya masu tsada, tare da takalma da jaka harda mayafai.



Naso ace tun saura Sati d'aya bikinnan zan tafi amma school bazai bari ba, gashin kwana biyar za'ai Ana programs na bikin inata tunanin ya zan b'ullowa tafiyar, haka dai ina gani zan tauye wasu lectures d'in nawa don ba k'aramin shiri dangi sukaiwa bikin nan ba , bikin mutum uku ba wasa ba , don haka ma yanda aka tsara duka gidanmu za 'ayi komai , suma su Aunty juwaira gida zasu taho da gidansu yaya Babbah don hankali ya tsaya waje guda.



Kwatsam labarin tafiya yajin aiki ya taso daga makarantun gaba Da secondary a k'asa baki d'aya, Wanda babu ranar komawa har sai Baba ta gani, duk son karatuna naji dad'in wannan yajin aikin don ko ba komai zanyi shagalin biki hankali kwance.


Nan na fara tunanin tafiya a washegarin ranar,don lokacin ya kama bikin saura kwana biyar a fara, amma matsalata guda Sweety inna tafi nace sa taho dasu Aunty Hafsa baza taji dad'iba, kuma in nace mu tafi tare inaga kamar Abbanta bazai bartaba taje tai kusan sati biyu, ina zaune ina neman mafita saiga kiranta a wayana, ina d'auka ta fara magana
" Nahna kinji wai yau an tafi straight ko"

"Eh wlh yanzu nakeji a radio, ai naji dad'i kinga zamuyi sabgoginmu hankali kwance, badan ma Abba bazai barki ba ai da tun gobe zamuyi gaba"

" Haba dai me yasa bazai barniba ai ba wani matsala, in dai goben kike so mu wuce saimu tafi"

"OK to Allah ya kaimu mu tafi bari in shirya trolley back d'ina"


"A'a karki had'a bari in kira Abba yanzu in fad'a mai gobe zamu tafi sai inzo gidan naku yanzu mu had'a kayan waje d'aya don Akwai wasu kayanki anan da Abbah ya d'inka mana".


" OK to ina jiranki"


Bayan na kashe wayan nai shiru ina tunani araina wai shin haka rayuwar Y'ay'an masu kud'i take sakaka ba tsaro ba tsangwama? Daga jin magana sai tafiyaπŸ€”,

Koni da garinmu zani yanzu fargabar sanar da Yaya tafiyar nan tun gobe nakeyi, duk da nasan bazai hanani ba, amma ita daga fad'a mata har tace to.


Fitowa nai parlour ina kiran sunan Aunty , ta amsa daga d'akinta tana fad'in "Nahna gani cikin d'aki"

"Aunty kinji wai an tafi straight duka k'asa yau"

"Haba da gaske"

"Wlh da gaske Aunty yanzu nakejin a radio kuma saiga sweety ta kirani yanzu tana k'ara fad'amin , shinema nake cemata da Abbanta zai barta da mun wuce gobe wai tace eh zai barta"

Dariya Aunty tai tana fad'in" was yaga areni muje biki"

Mirmishi nai ina cewa " ai Aunty rayuwar gidansu sweety ba tsaro wlh, yanzufa da yamman nan zatazo mu had'a Kaya,nida ko fad'a a'a Yaya banyiba"


"Ai ba matsala kinsan bazai hanaki ba ,kawai dai ki kirashi awaya ki sanar dashi kafin ya dawo ma"


Wayana na d'auka na kira number Yaya duka biyu ya d'auka
"Nahna ya dai "?

" um yaya barka da yamma ya aiki"

"Barka dai Nahna aiki gashi munata fama"

"Yaya daman yanzu ne nakejin an tafi yajin aiki k'asa baki d'aya shine nakeson gobe in tafi sakkwato inyi gaba"


"Hhhhmmm Nahna naga dai bikin nan kina d'okinsa, amma kuma Sweety ta rigaki fad'i don muna tare da Abbansu yanzu ta kirashi take fad'in zaku tafi goben"


Dariya nai ina fad'in "um sweety zumud'i"

Shima y'ay'an dariya ya d'anyi yace "To shikenan sai a had'a Kaya Allah ya kaimu goben"

"Ameen yaya sai ka dawo "


Ba'a jima ba saiga sweety da jakunkuna da Kaya nik'i nik'i kallonta na tsaya yi ina dariya " Sweety wannan uban kayanfa kamar zamuyi tafiyar wata biyu, duka fa sati biyu zamuyi "


"Oh Nahna biki tareni ba kin tsaya min tsiya"


" To sannu da zuwa sweety nah, Kawo kayan in tayaki"

D'akina muka wuce nan take firfitomin da kayan da Abbansu ya siyamana, nai shiru ina wani tunani can nace "mun gode Allah ya saka da alkairi, amma Sweety Allah yasa ba takurashi kikai dole ya siya mana ba."

"Ah haba wannan y'an kayan zakice na takurashi kedai kawai tashi mu shiryasu"

Komai mun had'a da muke buk'ata manyan trolley back biyu da k'arama d'aya don Kaya muka dija kamar me.

Sai Bayan magriba sweety ta tafi gida da shirin gobe da wuri zamu wuce don kar muyi dare.

Bayan yaya ya dawo yakirani parlour na zauna ya fara magana kamar haka "Nahna gobe insha Allah zaku wuce ko,Abban sweety yawa driver d'insa na office magana zaizo k'arfe Tara ya d'aukeku shi zai kaiku, sannan sweety inaso ki kula sosai in kunje kinga bake kad'aibace zaki tafi da bak'uwa, kuma yanzu kinga duk zuri'ar gidan Alh Usman sun zama surukai garemu, don haka ki kula da ita mu fita kunya kar tana ta murna zataje garinmu kuma ta gano wani abin da zai b'ata ranta, dukda ba alfahari ba nasan zuri'ar gidanmu ba baya bane wajan karrama bak'o amma duk da haka ita a k'ara mata akan Wanda akewa, naiwa su umma Waya na fad'a musu da ita zakuzo don haka a tanadeta."


"Tom yaya Allah ya kaimu goben, kuma insha Allah za'a kula sosai"

"Yawwa Nahna daman nasan baki da matsala, Jeki ki kwanta Allah ya kaimu goben".








K'arfe Tara driver d'insu sweety yai parking k'ofar gidanmu tare da ita a tsaitsaye ta shigo suka gaisa da Aunty Hafsah muka fita da kayanmu mukai musu sallama, nan driver ya cilla mota muka d'au hanya.






Taku ce
Y'ar mutan Ja'oji πŸ™‹β€β™€
🍑🍑🍑🍑🍑🍑🍑
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
🌸 *YA'N* *ARABIC*🌸


*NA*
*LAYUZA* *KABIR* *ADAM*
​

_DEDICATED_ _TO_ _ALL_
_ARABIC_ / _ISLAMIC_ _STUDENTS_
πŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“š



πŸ’» *ZAMANI WRITERS ASSOCIOTION*

πŸ“ .
​​WΙ› Ι‘Κ€Ι› Ι¦Ι›Κ€Ι› tΡ³ Ι›Ι—ucΙ‘tΙ›, MΡ³tiΡ΅Ι‘tΙ› Ι‘Ι³Ι— Ι›Ι³tΙ›Κ€tΙ‘iΙ³ Ρ³uΚ€ ʀɛɑɗɛʀร​​

β€‹πŸ“š ​​Zaku iya samun littafan mu a Facebook​​ πŸ‘‡πŸ½
Fb.me/ZAMANIWRITERSASSCIATION


πŸ“© ​​Zaku iya aika mana sako ko korafi, Ta email namu​​ πŸ‘‡πŸ½
Zamaniwriterassociation.@gmail.com




0⃣1⃣6⃣


Sanda muka shiga gidanmu da murna aka taremu tare da d'ibar mana Kayanmu zuwa masauki kowa na mana sannu da zuwa.

Kai tsaye alwala mukai muka maida sallan dake kanmu, bayan mun idar na tashi na fito parlour nan na tarar an shirya mana kayan abinci iri da kala na koma d'akin na cewa Sweety " taso mu ci abinci don ji nake cikina ba komai"

Bayan mun fito parlour nan muka gaisa da umma da Mama suka k'arai mana sannu da hanya, nan na had'a mana abincin muka fara ci, kasancewar Sweety batada bak'unta yasa ta saki jiki take kwasar loma😜.


D'aya daga cikin jikokin gidanmu Wanda suke zaune a gidanmu ne ya shigo yana fad'in " Aunty Nahna wai direban daya Kawo Ku ya gama cin abincin zai wuce"

"To jekace ya shigo su gaisa dasu Mama ko"


Jim kad'an ya shigo suka gaisa yai mana sallama zai wuce nan mukaita mai Allah ya kikaye hanya, yana amsawa da Amin ya fice.




Wayata na d'auko na kira number d'in Zainab amarya bugu d'aya ta d'auka tana fad'in "k'aramar uwa yanzu nake shirin kiranki ancemin kunzo"

"Waya fad'a miki munzo"

"Allah da gaske yanzu khairat tacemin kunzo wai taga me motar daya kawoku ma"

"Eh kuwa gamu har mun huta munci abinci"

"To me yasa buku sauka gidanmu ba don Allah Nahna?"

"Lalle ma ga gidan tsohona kawai sai in sauka gidanku, kawai dai zuwa safe in mun huta zamu shigo".


" Allah k'aramar uwa ban yardaba nidai yanzu ma zanzo in tafi daku ai dai biki kukazo ba wajan tsofaffin nan ba ".


" hhhmmm ai kuwa bazamu gidanku ba,kuma tsofaffin sune kanku idawa,da bazarsu kuke rawa".


Dariya Zainab tai kawai ta kashe wayan.

Dake tsakanin Zainab da Nahna ba wani nisa don haka ma suka taso kamar k'awaye, basa b'oyewa juna sirrinsu, amma dukda hakan Zainab tana bawa Nahna girmanta na matsayin k'anwar mahaifiyarta.


Sweety kuwa ta samu su mama sunata hira suna bata labarin garin sakkwato da tarihin kafuwarsa, dake ita d'in gwanar son labari ce ta mik'e k'afa tana kwasan zance.




Sai wajan k'arfe sha d'ayan dare suka kwanta, sweety tana fad'awa Nahna itafa gari na wayewa zata fita taga gari,Nahna dai sai mirmishi.


Washe gari muna sallar asuba muka koma bacci ,wajan k'arfe Takwas muna tsaka da bacci don ko niyar tashi bamuyiba najiyo muryar Zainab a kaina tana fad'in "k'aramar uwa wai ko tashi bukuyiba har zuwa yanzu,gaskiya Ku tashi haka".

Juyi mukai a tare don karad'in Zainab ba kad'an bane,cikin bacci nace " haba Zee tun yanzu har kin bar gidanku kinzo ki damemu ko"


"Haba Aunty nah don Allah ki tashi,wlh ina son ganinki matuk'a nai kewarki"


Badan nasoba na tashi zaune ina mita,

Sweety ma tashi tai tana mitstsika ido don dukanmu da bacci tare damu,

Zainab ta kalli sweety tana mirmishi tace "sorry bak'uwarmu na tasheki da karad'ina ko"


Itama mirmishin tai tana mik'ewa tsaye tace " karki damu amarya ai lokacin tashi a bacci ma yayi".

Kai tsaye sweety ta shige toilet tai wanka tare dayin brush, tana fitowa nima na shiga, hira sosai Zainab kewa sweety dake itama uwar magana ce nan sukaita zuba, bayan na fito ban wani tsaya doguwar kwalliyaba kawai mai na shafa na d'an goga powder tare da lips stick, nasa doguwan rigan atamfa, na dubi sweety da Take kallon wani pic d'inmu tun muna yara a wayar Zainab, nace "Taso maje muyi breakfast in kika biyewa wannan amaryar bazata barki ki huta ba da magana".

Dariya tai tana fad'in " gaskiya Nahna wannan pic d'in yayi kyau zan turashi wayana in ajiyewa y'ay'anki,suka mamansu sanda tana y'ar shekara shida jibi y'ar lukuta dake ".


Mirmishi kawai nai araina ina cewa Zainab ta kwafsamin data bar Sweety ganin wannan tsohon hoton.

A zahiri kuwa rik'o hannunta nai ina fad'in " don Allah ki taso muje mu karya"



Lafiyayyan abinci na samu y'an tsofaffin sun shirya mana, duk da yanzu an kawo musu masu aiki sabida yanayin girma gashi y'ay'ansu sun kawo k'arfin da zasu iya d'aukar musu ma'aikata koda sunfi goma , amma hakan bai hanasu shiga kitchen ba da Kansu suka shirya mana komai, kunun alkamane da had'ad'd'an shayin zob'o a d'aya flask d'in,sannan ga lafiyayyan k'osai, gefe kuma ga soyayyr doya da kwai, d'aya kwanan dana bud'e farfesun kayan cikin ragone yaji kayan K'amshi, nan muka zauna muka b'arji dad'i mukai k'at, bayan mun gama Zainab ta jamu muka fice zuwa inda akemata gyaran jiki,nan muma samu rabonmu aka D'an mitstsika mana dilka.



Bamu muka dawo gidanba sai yamma lis don ba k'aramin yawo mukai ba daga gidan gyaran jiki muka wuce kasuwa kuma.


Bayan munyi sallar magriba ne muka had'a kayanmu muka wuce gidansu Zainab sai randa za'a sata a lalle kuma zamu dawo gidan tunda anan za'ai taron bikin.



Kwananmu Hud'u yau a sakkwato duk mun zagaya gidajan y'an uwa dake kusa min gaisa Wanda suke nesa kuma nace ma had'u in sunzo biki.

Ana gobe za'a fara bikin mukaje gidan k'unshi aka tsantsara mana ja da bak'i sannan muka wuce saloon akai mana gyaran kai, Sweety ta had'u da k'awayen Zainab sun d'inke kamar sunsan juna dake Zainab ma akwai harkar girma dason fafa, don't haka k'awayenta suka zama wayayyu irin sweety nan suka d'inke abinsu ni kuwa bamai son hayaniya bace don haka ko hira suka b'arke da ita sai dai inyi mirmishi kawai ina binsu da ido.


Gidan Yaya Sani anan aka ware amarya da k'awayenta zasu zauna, dake cikin layinmu gidan,nan muka had'a kayanmu muka kai can,dana k'awayenta da zasu rink'a kwana.


Yau kam za'asa amarya a lalle,gidanmu ya cika yai dam k'am dangi na kusa dana nesa duk sun hallara bikin mutum uku ai ba wasa ba, bayan La'asar su Yaya suma suka dira nan mukaita murnar ganin juna,Aunty Hafsah tanata tsokanata wai Nazi Sakkwato na manta dasu,nikam sai mirmishi kawai nakeyi.



K'arfe biyar jama'a sun cika damk'am a filin da za'ai kamun amarya da ango, nan muma muka fito cikin ado, kowa ya ganmu yace masha Allah,
Yanayin Al'adun garinmu ya birge Sweety nan fa ta bawa wani yaro jikan gidanmu camera d'in data taho da ita yai tai mata video d'in abubuwa.

Sai magriba aka tashi,abin gwanin birgewa.

Washe gari akayi dinner,ni kaina na jinjinawa kaina irin kyan danayi,sosai akamin makeup, gashi ankon bikin ya amsheni nasha gwargwaron ashobe, hakama Sweety tai kyau matuk'a,musamman dake gwanar makeup ce a fuska itama.


Bayan an dawo daga dinner d'in muna zaune anata hira kundan y'am matan amarya da raba dare suna hira, hira muke kamar ba gobe naji sweety ta dafoni tana mirmishi tace "Nahna kinga na d'aura pic d'inmu a status wani ya ganki ya zuzuce".

Mirmishi nai ina fad'in " Sweety ke ko bakida dama".


"Da gaske fa nake, amma nace mishi an miki miji,lokaci kad'an za'ayi bikinki".


Caraf wata k'awar Zainab tace " da gaske an mata miji don Allah?".

"Wlh da gaske an Mata miji , yayana zata aura insha Allah".


Ihu y'an d'akin suka d'auka Iklima na fad'in " Ah lalle sweety Ashe shiyasa agun dinner d'in nan kiketa tareta kar wani ya saceta,Ashe yayanki kikewa gadi,amma gaskiya yayanki ya dace wlh da samun one in towns "

Sunata shak'iyancinsu nidai mirmishi kawai nakeyi,don nasan ko nace zan tanka bansan me zanceba, a haka sukai suka gaji sukai shiru.

Tsawon kwana uku ana gabatar da programs d'in bikin,ana hud'un aka d'aura aure,washe gari lahadi dandazon maza sukayo kano inda aka d'aura Auran Yaya usman da amaryarsa Amrah.


A yanda aka tsara ranar Litinin mata goma zasu taho kano domin d'aukar Amaryar Yaya usman akaita gidanta,kamar yanda yake a al'adance dangin miji ke zuwa karb'ar Amarya.


Don Haka tun aranar Lahdin da yamma aka kai Zainab gidanta,daga nan muka fara shirin had'a kayanmu.

Washe gari k'arfe goma na safe motoci biyu na abokan yaya suka d'auko mu zuwa kano .

Kai tsaye gidanmu suka wuce damu,bayan mun sauka munyi salla tare dacin abincin da yaya yai mana odanshin daga hotel dake shi tun jiya da suka taho d'aurin aure bai sake biyosu ba ya zauna, bayan mun huta masu wanka sun k'arayi, k'arfe biyar duka muka tafi d'aukan amarya Amrah, inda muka samu kyakkyawan tarb'a daga danginta,kunsan kano garin karrama bak'o ce, 😜 bayan y'an nasihohi da aka k'ara yiwa marya kamar yanda yake a al'adance aka bamu ita tare da sauran danginta muka wuce da ita zuwa gidanta dake unguwarmu,nesa da layinmu kad'an don anan yaya ya samo mai gida ya siya.

Tunda muka sada Amarya da d'akinta bamu dad'eba muka dawo gidanmu,muka barta da danginta.


Da darema yaya bai bari anyi girki ba don yasan kowa a gajiye yake, take away ya k'ara yimana,inda y'an tsofaffin ciki sukaita k'orafin sudai basucin wani Abu daddare inba tuwo ba,kumam dariya kawai mukaita musu.


Duk yanda sweety taso wucewa gida aranar hanata nai,nace ta bari sai da safe zan rakata har gida,jin haka yasa ta zauna.



Gari na wayewa muka shirya breakfast muka sallami bak'inmu, bayan duk sunci abinci sukai wanka, ba'a jimaba Yaya usman ya k'araso gidan namu , nan aka gaggaisa ya k'arai musu godiya,sannan yace " driver da zai maidasu sakkwato yazo".


Babbar mota ce yaya ya d'auka musu don karsu takura,nan suka wuce munata d'agawa juna hannu cike da kewan juna.



Bacci duka muka koma sai wajan sha d'aya muka farka nan mukai wanka muka shirya, na had'awa sweety duka kayanta da tarin tsarabar da iyayenmu suka had'a mata da kayan gyaran biki, nan muka fito Aunty nata mata godiya,yaya ne ya d'aukemu don yace "tuwan girma miyarsa nama,yanda Mahaifinta ya bamu ita har zuwa sakkwato dole ya mik'ata da hannunsa tare da mai godiya".


Munyi sa'a kuwa da mukaje Abban na gida bai fitaba wai mura ce ke damunsa,nan ya taremu da murnarsa,sweety y'ar shagwab'a da murnarta ta fad'a kan Abbanta tana fad'in " Miss you my Sweet Dad".

Dariya yai yana shafa kanta yace "ya gajiyan hanya data biki,sweetyn Abbah?".

Cikin murnar ganinsa take fad'in " ai Abbah gajiya akwaita, don mun war-wasa".

Dariya yai yana dawo da hankalinsa kanmu, cike da jin kunya da girmamawa na gaisheshi,ya amsamin cikin sakin fuska da fara'a,yana tambayana gajiyan biki, nidai duk sai najini a takure,don haka kawai mirmishi nai na sunkuyar da kaina, nan Auntynsu ta shigo muka gaisa itama tana mana bangajiya,

Hira Yaya suka shigayi da Abbah don haka muka wuce d'akinta,muma hira muka Fara Wanda duk ta bikice, kusan awa guda Yaya yace in fito mu wuce,nan naitai mata godiya da irin karar da tai mana, ta rakoni bakin motar mukai sallama yayama yanata k'ara mata godiya da Allah ya huce gajiya.







Taku ce
Y'ar mutan Ja'oji πŸ™‹β€β™€
🍑🍑🍑🍑🍑🍑🍑🍑
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
🌸 *Y'AN ARABIC* 🌸


NA

LAYUZA KABIR ADAM

DEDECATED TO ALL
ARABIC /ISLAMIC STUDENTS
πŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“š

πŸ‘¨πŸ»β€πŸ’»πŸ‘©πŸ»β€πŸ’»
*ZAMANI WRITERS ASSOCIOTION*

πŸ“
​​WΙ› Ι‘Κ€Ι› Ι¦Ι›Κ€Ι› tΡ³ Ι›Ι—ucΙ‘tΙ›, MΡ³tiΡ΅Ι‘tΙ› Ι‘Ι³Ι— Ι›Ι³tΙ›Κ€tΙ‘iΙ³ Ρ³uΚ€ ʀɛɑɗɛʀร​​

β€‹πŸ“š ​​Zaku iya samun littafan mu a Facebook​​ πŸ‘‡πŸ½
Fb.me/ZAMANIWRITERSASSCIATION


πŸ“© ​​Zaku iya aika mana sako ko korafi, Ta email namu​​ πŸ‘‡πŸ½
Zamaniwriterassociation.@gmail.com



KYAN TAFIYA DAWOWA,YAU DAI ALLAH YA NUFA NA DAWO πŸ’ƒπŸ˜€
GROUP D'IN Y'AN ARABIC FAN'S KULLUM K'ORAFI SUKE DA TSIMAYI,TO YAU GANI NA DAWO,MUNA TARE A KODA YAUSHE🀝



0⃣1⃣7⃣



Tsawon kwana biyu muna matse gajiyan biki, ban koma gidan ya Usman ba saida yaita k'orafi ranar da yamma yazo har gidan yace in shirya muje, nan na shirya na shirya su Ashraf muka tafi tare.


Muna shiga gidan yaya Usman ya fara k'walawa Amaryarsa kira, " precious fito ga Auta nan naje na d'auko miki ita".

Daga kitchen ta fito tana mirmishi tace " ai da har nayi fishi da ita, nan nan kusa amma ta kasa zuwa".

Y'ar dariya mai nace "Haba my Aunty kar kiyi fishi da k'anwarki mana, gajiyan biki ne ya hanani fitowa,amma gashi nazo yanzu".

" OK OK to nayi miki uziri amma yau bazaki fita gidan nan ba sai k'arfe goma na dare".

Nidai mirmishi kawai nai na zauna,nan muka gaisa ta kawo mana kayan motsa baki,munata hira harda yaya,ana sallar magriba ya tafi masallaci muma mukai sallah, bayan min idar nace Aunty Bari mu wuce gida yaya bai son muna magriba a waje".

Daga bayana naji muryan yaya usman yana cewa "ba inda zaku sai munci abinci kunyi sallar isha'i saimu rakaku".

Komawa nai na zauna ina fad'in "to Yaya".


Abinci ta had'o mana mukaci harda yayan sannan yace ta shirya inya dawo sallar isha'i su rakamu gida, ai kuwa taita murna zata fita waje, ni dariya ma ta bani nace
"kwana uku kawai da kawoki shine kike son fita".

" hhhhmmm Nahna ji nake kamar nai wata a gidan nan".

Bayan munyi sallar isha'i yaya ya shigo muka fito, a k'afa yace muje ma motsa k'afa yai parking motarsa,muna tafe muna d'an hira har muka k'araso gida, a k'ofar gida muka had'u da yaya ya dawo daga masallaci cikin fara'a yace "a'a amarya harda ke akai rakiyar, to sannu da zuwa".

A cikin gidama Aunty Hafsa da fara'arta ta tari amarya suka gaisa cikin girmama juna ta gaida yaya ma tanata jin kunya wai ita ga wan miji.

Nanma hira akaitayi basu bar gidanba sai tara da rabi.



Bayan mako biyu ne aka sasanta da gomnati da ASSU dan haka aka janye strike,nan muka fara shirin komawa school on Monday.


Tunda muka koma school karatunmu ya k'ara d'aukan zafi,na k'ara maida hankali sosai ga karatuna.


Lokacin da yaya Usman ya gama cin angwancinsa zai koma bakin aiki yazo ya samu yaya na yana Neman alfarmar inje gidansa in rink'a kwana da Amrah don tace tsoro takeji bazata iya kwana ita kad'aiba, nan yaya ya amince,yace ai ba damuwa.

Ranar daya koma bayan sallar magriba na d'auki kayana da zanyi amfani dashi da safe in zani school da kayan baccina,na wuce gidan yaya usman.


A yanda na sameta kamar Mara ladies tana kwance kan kujera,na k'arasa da Sauri ina fad'in " Aunty Amrah bakida lafiya ne?".



Please Login or Register in order to submit comment