Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

shekara bai cika ba za'a mai k'ani ko k'anwa,shiru nai tare da zabga uban tagumi duk na rasa ma wane tunanin zanyi.



****Da dare da UK ya dawo bayan yaci abunci yake tambaya ta me da naje asibiti me suka ce min,result d'in na mik'a mai kawai,kalla yai sosai yace "ban fahimta ba, yi min bayani."

K'walla cike da idona nace "ka duba sosai wai fa haka suka ce ciki gareni har wata uku."

Da sauri ya kalleni yana fad'in "Wai da gaske ko wasa?."

Hawaye na yaci gaba da zuba nace "wane wasa wlh da gaske,kaga kenan tun Raees na da wata biyu ka jibga min aiki."

Wata irin dariya naga yana yi har da nunani yama kasa magana k'arshe kawai sai ji nai ya rungumoni tsamtsan jikin sa yana fad'in "Alhamdulillah, Allah kai ne abun godiya,cikin shekara guda zaka min kyauta Yaya biyu,Na gode My Khady na gode kinji,daman ni tunda na ga kin gyare a son abun nan nasan kin k'aro k'ok'ari da fasaha baza kiyi sanya wajan cafewa ba."

Tureshi na shiga yi tare da kukan shagwab'a, shi kam dariyar sa kawai yake kwasa yana ta tsokanata,harda cewa"kin San me?Wlh rannan danaga Hafeez wani abokina da mukai school tare da yaran sa maza guda uku duk Kansu d'aya nake tambayar sa y'an uku ne yace min a'a kawai babu tazara ne tsakanin haihuwar su,wlh sun birgeni kinga nima in Allah ya taimake ni haka zaki rink'a min."

K'ok'arin mik'ewa na farayi daga jikin sa ya rik'e kam da cewa"Fad'a min meye matsalar ki don Allah, wai haihuwan ne baki so kome?."

"A'a ni bance ban son haihuwa ba,wa zai ce bai son haihuwa kawai ni tausayin yarona nake ji."

Serious ya koma ya gyaramin zama sosai yace "Kullum ke kike fad'a min Allah baya d'aurawa bawa abunda bazai iya ba,kuma kin sani yanda muka rink'a rok'on Allah kafin haihuwar Raees sai da little ta shekara uku da rasuwa muka sami Raees yanzu bakya ganin babbar baiwa ce ya mana ya share hawayen mu ya bamu ya k'ara mana da wuri, sannan dukkan wasu dalilai da suke sa ayi tsarin iyali a musulunci ko a likitance babu dalilin da zai sa mu muyi shi, ke kika fad'a min musulunci ya yarda ayi tsarin iyali ne don tsira da lafiyar uwa ko yaro, ko gudun lalacewar tarbiyar yara ta rashin samun uwa ta gari ko uba na gari, rashin abun kula da cin sauran yaran da aka haifa balle a sake haifo wani,tsoro firgici na rashin tsaron rayuka duka way'annan dalilan sharia ta bada damar a jinkirta haihuwa har sai zuk'ata sun nutsu,kuma a hakan ma in Allah ya kawo a k'arb'a ayi mishi godiya,to mu gashi Allah ya mana arzikin da zamu iya kula da Yaya sama da d'ari in ya bamu,sannan muna da nagartar da zamu tarbiyantar dasu al'umma ta amfana, muna cikin nutsuwar tsaro da kwanciyar hankali,uwa uba ke da Allah ya bawa kina da isashshiyar lafiya, sannan Raees Allah ya bashi wadatacciyar lafiya wannan cikin bazai shafi lafiyar sa ba,ki kwantar da hankalin ki kinji. "

Share hawayena nai nace "Na gode Mijina da wannan tunatarwar,dama ajizanci ne na d'an Adam yasa na damu, na gode Allah da ya bani miji me tunasar dani."

"A'a madam wannan duk cikin koyarwar ki gare ni ne,dama kuma ai tunasarwa mumini kawai take amfanarwa ,Allah ya bamu zuri'a D'ayyiba."


********
Haka naci gaba da rainan cikina cikin sassaucin ubangiji, b'angaran Raees banda matsala don yanzu ya fara cin abunci kuma muna bashi magungunan sa kuzari duk da kasancewar sa me kuzarin dama.


Ba kowa ya lura da cikin ba sai da ya fara fitowa, masu min dariya nayi masu barka na yi.

Ban yaye Raees ba sai dai cikina yayi wata bakwai lokacin shi yana da wata Tara,kuma bai wani sami matsala ba ko kad'an, don yana samun kulawa sosai,ko yaushe daga safiya zuwa yamma duk wajan su Aunty Murja yake yini sai Abbansa ya dawo ya ke shiga ya karb'o shi.





________________
Watan cikina tara da y'an kwanaki Allah ya sauke ni lafiya,Wannan karon ma namiji Allah ya bani,an kuma don shi d'in ma kamannina sak ya d'auko har bak'ar fatata.

Murna wajan UK kamar wannan karon aka tab'a mai haihuwar, hidima sosai ya shiga yi damu,haka ma Abba yai rawar gani daga gidan mu ma kamar ko yaushe y'an uwana sun yi min iya k'arfin su,yaro yaci Sunan Abba wato Usman ana kiran sa da Nurain, an yi taron suna an watse cikin murna da farin ciki.

Haka naci gaba da rainan yarana cikin kulawa da k'aunar su,sun taso gwanin sha'awa musamman dake Nurain me jikin girma ne irin na Abbansa sai nan da nan watan sa uku ya fara zama wanda a lokacin kuma Raees ya ke gudun sa ko ina, masha Allah.


**********
Haka rayuwa taci gaba da gudana mana cikin Wadata da annushuwa,ban nemi komai na rasa ba na rayuwa,mijina ya na matuk'ar sona da yayana kullum burin sa ya faranta ranmu,in ya dawo duka lokacin sa yake bawa yaransa har sai ya shiryasu sunyi bacci sannan ya dawo gareni kuma.




**********
Watan Nurain Goma cif na yaye shi sabida tafiyar aikin hajji da ta yaso mana,ni da UK da Abba da Aunty Murjah, nima na tattara kud'ad'ena na biyawa yayana abin alfaharu na,don banda wani abu da zan sakawa yaya Haroon dashi a duniya yayi min komai na rayuwa,lokacin dana sanar dashi har dashi tafiyar nan farin ciki yasa har k'walla yayi,nan ya kira y'an uwa ya shiga sanar dasu,kowa addu'a yai tamin da sa albarka,ni kam a raina nake fad'in "To in ban yiwa yaya ba wa zanwa? Kud'in da suke account d'ina sunyi yawa matuk'a, ga Wanda UK ke samin ga kud'in albashina,ban siyan ko abun k'wandala a ciki kullum mijina cikin yimin hidima yake."





Zulk'ida na kamawa mune jirgi na uku zuwa k'asar Saudi,kuka rurus nake lokacin da na ganni cikin masallacin manzan Allah, nai godiya gare shi da ni'imar da yayi min.


Munyi aikin hajjinmu cikin kula da shauki,sosai na dage da yiwa iyayena addu'ar samun rahmar Allah a wannan waje me girman daraja da nake.


Bayan salla babba da kwana goma muka dawo gida Nigeria cike da kewar k'asa me tsarki.




*************
Dawowar mu da ga saudiya da wata biyu wani cikin ya bayyana gareni, godiya nai ga Allah daya bani wannan n'iima,lokacin Nurain yana da shekara da wata biyu,tafiyar sa ko ina,UK ma murna ya sha ya gode Allah.





~Bayan shekara biyar~👇🏼
___________________
Lokacin muna da Yaya Biyar Raees,Nurain,Yusuf (Baffa) Umar(junior) sai k'aramar su Little(Ruk'ayya)

Lokacin Raees na da shekara bakwai,Nurain shida,Baffa,Hud'u junior biyu sai Auta me wata takwas.


Yarana Masha Allah Gwanin sha'awa kowa ya kallesu sai ya k'ara kuma ya tanka,don haka kullum cikin tofesu da addu'a na ke,ba dare ba rana,sun taso cikin Tarbiya da girmama junan su,haka jama'ar gari kowa Aunty kowa uncle, ko basu San mutum ba in sunsan ya girmesu basa fad'ar sunan shi, haka tsakanin su suke b'oyewa junan su suna.

Yare uku dam su ke ji,larabci English Hausa, duk Wanda suke yi baza kace suna jin wani yaran bayan sa ba,don makarantar ma da suke boko da Arabic ce, ban yarda sun karkata da iya boko ba,don haka Qur'an ma hadda sukeyi duk da karancin shekarun su,don haka suka zamo taurari ko cikin yaran family.kuma kula da yarana Sam bai shafi aikin koyarwa ta ba,komai ina bashi lokacin sa da yin komai cikin tsari.



_______________
Duk ran jumma'a Abban su sha biyu yake tashi aiki,suma kuma sha biyun suke dawowa daga makaranta don haka suna dawowa kowa yake shiryawa su tafi masallaci, kafin su dawo na shirya abunci don tare muke cin abinci da yaranmu in har suna gida.


Yau ma na shirya tsaf cikin riga da zani na atamfa wanda sukai min das a jiki suka amsheni, Little ma na shiryata cikin kwalliyar ta gwanin sha'awa na saka ta cikin keken ta don ta barni nai komai a nutse.

Ina tsugunne ina jera cups dintda zamuyi amfani dasu na fara jiyo hayaniya,mirmishi nai na san sun dawo,sallamar Baffa ce ta katseni ya shigo cikin nutsuwa "Assalamu Alaiki ya ummy"

Kafin na amsa sauran ma suka shigo duk da sallama kamar yanda yayi,amsa musu nake fuskata d'auke da mirmishi ina binsu da kallon sha'awa don dukkansu sanye suke da shadda fara tas babbar riga da y'ar ciki,ga hulunan su zanna akawunan su,duk k'ok'arin cire rigunan suke nace "Wai ina Abban na ganku ku kad'ai?."

Junior ne yace"Yana tsaye da Baba me gadi."

Kafin nace wani abu ya shigo shima cikin irin shigar yaran tsaf da babbar riga, "Ga Abba ya shigo madam ni ake jira ko?".

Fakar idon yaran nai na kashe mai ido guda tare da k'yasa mai alamar yayi kyau,dariya yayi kawai yana amsawa a sirrance.


Bajewa mukai muna kwasar garar girki baka jin komai sa k'arar k'ashi😜, bayan mun gama kowa yai hamdala sannan Raees ya taimaka min na gyara wajan,shi kuwa oga ya d'auki little sai wasa suke mata shi da junior, Baffa da Nurain kuma suna harhada kayan su da suka cire suna ninkewa.


Bayan duk mun dawo mun zauna hira muke da yaran mu wanda a haka ne muke gane damuwar moka da kuma burin da kowa ke dashi,Baffa ne yai gyaran murya da fad'in" Abba ni inna girma fa lauya nake son zama."

Da sauri Nurain yace"A'a wallahi na riga ka ko yaya."

Ya k'arasa da kallon Raees,shi kam dariya yayi da d'aga musu kai,nima dariyar nai nace"Kullum dai sai anyi wannan muhawarar fatana kullum Allah ya baku ilimi me amfani wanda Alumma zasu amfana dashi musulunci yayi alfahari da Ku."

Amsawa sukai da amin, UK ya juya ga Junior yana fad'in "Namesake fa mema kace kana son zama inka girma?."

Cikin murna da zak'uwa yace"Abba ni Sarki zan zama."

Dariya mukasa gaba d'ayan mu don daman mun San k'arshen zancan nashi.






_*Alhamdulillahil lazi bi ni'imatihi tatummassalihin*_


_*Anan na kawo k'arshen wannan littafi nawa me suna 'YAN ARABIC abunda nai dai dai a ciki Allah ya bani ladan sa,abunda na kuskure ina rok'on ubangiji ya yafe min*_




_*Dukkan abunda kuka ga nai dai dai wannan daga Allah ne,Abunda kuka ga kuskure wannan daga gareni ne,kumin afuwa Ajizanci ne irin na d'an Adam*_🙏🙏



_*Na gode da jimirin bina da kukayi tsawon lokaci cikin wannan rubutu na gode muku ba adadi kuma masoyana ina musu fatan Alkairi a duk inda suke a duniya,nima ina sonku sama da yanda kuke sona,ana tare har abada*_🤝🤝🤝



~Ku kasance dani cikin littattafaina masu fitowa~

*MAKOMAR KOWA*
*'YA'YANA MATA SUNE SANYIN IDANIYATA*


~Domin k'orafi,gyara ko shawara ga number ta~👇🏼
*07067270055*



*25/9/2019*
An dauko wannan littafi daga shafin www.dlhausanovels.com.ng ku ziyarci shafin na www.dlhausanovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya

Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,

Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490

A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,

Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu

Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC

Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from www.dlhausanovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services

Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us

Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it

Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
__
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Please Login or Register in order to submit comment