Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

na d'auro alwala sallar ma a daddafe nayi ta don yanda jikina ke rawar d'arin zazzab'i.

Auntyn hafsa ce ta farka itama taje tai alwalar sannan ta fito ta tashi sweety, ganina kwance kan abun sallar ya tabbatar mata nayi tawa tuni tai zaton ma bacci na koma don haka ta shimfid'a wata sallayar ta tada salla.


Duk yanda naso daurewa abun ya gagara don haka na sanar wa sweety ta kira family doctor d'in su ya rubutomin maganin da zai rage min zugin, ba b'ata lokaci ta kirashi kuwa Yace zai kira UK yazo ya amsa a asibitin.

A rikice ya shigo d'akin yana fad'in "meya faru yanzu doctor ya kirani in zo in amsa miki magani".

Ban iya bashi amsa ba,sai Aunty Hafsah ce tace mai " Ciwon nono ne kasan dama dole zai yi ciwo,amma insha Allah tana samun magani zai dai na".

Cikin tausayawa ya k'araso bakin gadon yana fad'in " muje asibitin tare kawai ya duba ki sosai zaifi".


Ba musu na mik'e da taimakon sweety naje toilet na kintsa,sannan muka wuce asibitin.



********
Allura doctor d'in yamin tare da bani magunguna,muka dawo gida.duk yanda nake daurewa sai da ya kaini ga kwanciya ruf har ranar da akai sadakar uku ne naji dama dama,amma daka ganni zaka tabbatar da ina jin jiki, jiki ba dad'i zuciya ba dad'i.



********
Duk wata walwala ta kau daga cikin rayuwar mu musamman UK ya hana kansa sukuni kullum cikin zancan little yake da kewar rashin ta,kayan ta yake sawa a gaba yai ta kuka,hakan yasa na tattara duk wani abu nata na kai su d'akin kayan ta dake k'asa na rufe.
Nikam kullum dake ina yawaita addu'a da neman sassauci a zuciyata sai Allah yasa min dangana,ya zama na ma nike bashi hak'uri ina nusar dashi, amma duk da haka zuciyar sa ta kasa dangana,babu wata rana da zata fito ta fad'i bai yi zancan little ba,sai a yanzu yake k'ara jin wani tsananin son ta a zuciyarsa,yana rayawa a ranshi daman haka yaya suke a zuk'atan iyayen su,ashe a duniya zai so d'a har haka cikin ransa, tabbas Allah ya jarrabeshi da tsananin soyayyat little gashi ta rasu ma abun ba sauk'i.






********
Wata guda da rasuwar little ne muka sami labarin sati na sama mu fita camp daga hukumar N.Y.S.C sabida tsaikon da muka samu na strike d'in dukkan universities d'in mu yasa tun wata biyu baya bamu shiga camp ba.


Tunda na sanar mai ya shiga damuwa kan wadda yake ciki,amma naita rarrashin sa har Allah ya kawo ranar tafiyar muka wuce jigawa dake daman nan aka turamu.


Ko yaushe na sami sukuni zamuyi waya ina k'ara kwantar mai da hankali don ni yanzu ma bala'in tausayi yake ban dukkan lamuran sa cikin sanyi yake yi,bashi da wai kuzari.




*********
A haka cikin ikon Allah mukai wata biyu muka yo gida,daga nan kuma akai posting d'in ko wannan mu inda zai yi hidimar k'asar sa,Allah yasa daman ni ina da catipicat na aure UK ya kai musu anyi duk yanda akai aka barni a garina, cikin ikon Allah muka fara hidimar k'asar mu.




~Bayan wata takwas~ ~A gurguje pls~πŸ™
************

Zuwa lokacin UK ya k'ara ficewa hankalinsa, ba iya rashin little ba kawai yanzu burinsa dare da rana ya bud'e ido ya ganni da ciki,amma Allah bai kawo ba,gashi kuma ya jarrabi zuciyar sa da tsananin son haihuwa a lokacin dalilin da yasa dukkan nutsuwar sa da kuzarin sa suka kau,daman shi mutum ne mesa abu a ransa, a hakan ma ina iya bakin k'ok'arina wajan kwantar mai da hankali,tun bansa damuwa a raina har nima Abun ya far damuna, nan na shiga addu'ar Allah ya dubemu ya azurtamu ya bani ciki kodan kwanciyar hankalin mijina.
Da naga abun nasa ya ci tura sai na fad'awa Abba halin da muke ciki na damuwar sa na rashin little da son samun wani gudan jinin, sosai Abbah ya mai nasiha tare da nuna mai cewa shi Allah ba'a mai tilas yanda yaso haka zai aiwatar.
Nasihar Abba tasa kwana biyu ya d'an rage damuwa,nima sai naji dad'i don rashin walwalarsa na damuna matuk'a da gaske.



********
Yau kam tunda na dawo gida na shige kitchen don da kwad'ayin danbun shinkafa na tashi,aiki sosai nake a kitchen dagani sai d'an gajeran wando iya kacinsa cinyata sai y'ar riga mara nauyi,na juya baya ina wanke cabej naji numfashin mutum a bayana,da d'an sauri na juyo don tabbatarwa kawai sai naji yasa hannu ya rungumeni a jikinsa, ajiyar zuciya na sauke tare da lumshe ido,cikin sansanyar murya nace "Heartbeat kaso tsoratani fa".

Kansa ya sanya kan wuyana yana goga min k'asumbarsa a dukkan wuyana da kafad'una, muryansa can k'asa yace" masha Allah tunda dai ban tsorata ruhuni ba, kusa dai tsoratata nai ko?".

Hannu nasa ina shafo gefan fuskar shi tare da mirmishi nace" Ka dawo da wuri Honey Allah yasa lafiya dai".

Kusan minti guda bai ce min k'ala ba,sai aikin shinshina wuyana da yake kamar magen data samu wajan laushi,duka hannayensa na zagaye dani yana k'ara sani cikin jikinsa, ganin yai shiru nima sai nai shiru ina wasa da yatsuna kan hannunsa dake zagaye dani,can ya sauke min wata malalaciyar ajiyar zuciya a cikin kunne wadda tasa har tsikan jikina duka ta tashi wani yarrrrrrr tun daga k'wak'walwa ta har k'asan k'afata,na k'ara lumshe ido ina cije baki, can k'asa k'asa da murya yace "my life!".

Ban iya bud'e baki na amsa ba illa cewa kawai da nai" ummmmm"

"Yau duka banyi wani abun kirki ba a office, tunda na fita nake jin wani tsananin feelings tare dani,duk yanda nake ta daurewa zuwa lokacin tashi na yayi na kasa,dauriyata ta k'are zuwa yanzu shiyasa na taho gida ga halalina gudun karna fad'a ga halaka".

Jiyo dani yai gabansa muna fuskantar juna,idanuwanmu sarke cikin na juna muna sakarwa junan mu wani lafiyayyan kallo me narka zuciya, kwantar da kaina nai bisa k'irjinsa ina cusa duka hannayena cikin gashinsa nace " mijina baka da wani wajan hutawa bayan jikina,bakada gonar yin shuka bayan ni,nice shimfid'arka wajan sauke gajiyarka,kuma mayafinka me tare maka dukkan sanyi da k'ura,ka kawo buk'atar ka inda za'a sauke maka sannan ka samu tarin lada,ina maraba da kai ako wane lokaci domin a shirye nake kuma a buk'ace nake da kai mijina".

Zame jikina nai a hankali na k'arasa ga gas na kashe sannan na rufe cabej d'in da nake wankewa,na wanke hannuwana tass sannan na jiyo gareshi.

Yana sak'ale da hannayensa a k'irji yana kallona fuskar sa d'auke da dukkan annuri,mirmishi na sakar masa tare da d'age gira nace "Bisimillah yallab'ai mu k'arasa ga turaka".


Bud'e hannayen yai na shige jikins a haka muke tafiya har zuwa upstairs sannan ya d'aukeni muka haura saman ina sak'ale jikinsa kamar y'ar Baby.πŸ€ͺ






Taku ce
Y'ar mutan Ja'ojiπŸ™‹
🍑🍑🍑🍑🍑🍑
🌸🌸🌸🌸🌸🌸
*'YAN* *ARABIC*
🌸🌸🌸🌸🌸🌸
🍑🍑🍑🍑🍑🍑

*NA*
*LAYUZA* *KABIR* *ADAM*

_DEDICATED_ _TO_ _ALL_
_ARABIC_ / _ISLAMIC_ _STUDENTS_
πŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“š


πŸ‘©πŸ»β€πŸ’»πŸ‘¨πŸ»β€πŸ’»
*ZAMANI* *WRITERS* *ASSOCIATION*
πŸ“
_We_ _are_ _here_ _to_ _educate_ , _motivate_ ,and _entertain_ _our_ _Readers_




πŸ’”πŸ’”πŸ’”πŸ’”πŸ’”
*_wannan shafin sadaukarwa ne gareka Abu khatheer my Honey,my Heartbeat, my soulmate, my hubby,my Reality, my my my my ,kuma Baby na d'an lelenaπŸ™ˆ,cikin bacci da ido biyu tunanin ka nake, dukkan motsina da kai a ciki,Allah ya baka lfy yasa kaffara neπŸ™,Allah ya tabbatar da dukkan alkairan sa garemu, ya . . . . . .πŸ™ˆ kudai kawai kuce Ameen_*
πŸ˜…πŸ˜…πŸ’ƒπŸ’ƒ




0⃣5⃣6⃣



Dukkan wata gajiya sai da na kauda mai ita a wannan lokacin, kulawa sosai na bashi tare da soyayya mai shiga cikin rai, bayan nutsuwa ta kama zuk'atan mu ya kwantar dani bisa k'irjin sa yana shafa bayana, a hankali cikin gajiyayyiyar murya yace "Heartbeat! Yanayin dana tsinci kaina yau a ciki Allah yasa rabo ne ya keta,Allah yasa kin samu ciki a wannan yammacin, wlh Allah my khady haihuwa nake so, so nake na bud'e ido na ganki d'auke da wani cikina, ina ma ki zama daga cikin mata masu haihuwa duk shekara,kafin shekara biyar inga yara hud'u na yawo cikin gidan nan matsayin nawa halal d'ina masu amsa sunan su da nawa".


Cikin salon kwantar da hankali na shafo sangalalin hannayensa har zuwa yatsunsa,ina k'ara tura fuskata cikin k'irjin sa,tare da sauke wasu tagwayen numfashi masu tafe da tsantsar k'issa da jan hankali na fara magana" karka damu Reality insha Allah very soon zamu samu,Allah shike kyauta ya k'ara ya kuma k'arawa,yana sane damu zai bamu ne,na farko ma ai bamuyi tsammani ba ya bamu wannan ma baya mantuwa yana sane tsaf damu".



Shafo gashina yai idonsa rufe ya sauke ajiyar zuciya tare da fad'in "Khadeejah! Allah ya min baiwa a lokacin da yasan ya dace yayi min amma sai na butulce mai, na nuna cewa nifa kawai an min kutse ne a lokacin, sam ban yi murna ba da nai arba da kyautar da yayi mini,k'arshe ma sai na b'ige da muzguna miki tare da d'ora miki alhakin abun, ranar da little tazo duniya naji bak'on yanayi tare dani,lokaci guda Allah ya sanya min soyayyar ta cikin k'irjina, har nake mamaki da tambayar kaina dama haka muma iyayen mu suke k'aunar mu? haka daman dukkan iyaye kejin son yayan su a zuk'atan su?watanni uku da satika da little tai aduniya sun zomin da nishad'i da farin ciki, lokacin da zuciyata ta shagala ga k'aunar sanyin idaniya ta a lokacin kuma Allah ya nuna ikonsa garemu, tabbas nasan Allah ya hukuntani ne gwargwadon butulcin da nai mai,domin shi Allah baya zaluntar bawansa sai dai bawa ya zalunci kansa,Khadeejah nai tunanin kwanaki kad'an da rasuwar little zaki k'ara samun wani cikin amma sai gashi har an tafi shekara, Allah dai yasa ba rabon mu kenan a duniya ba".

D'igar hawayen sa danaji akan hannayena dake gefan fuskarsa shi yasani d'ago kaina naga yanda hawaye ke bin kuncinsa da gudu gudu, yatsuna biyu nasa ina share mai hawayen tare da k'ara sanyaya muryata nace"haba my heart, ya zaka min haka kana son in shiga cikin damuwa kenan,kana son nima in k'i kwantar da hankali na, don Allah ka daina zubda hawayen ka Allah yana sane damu insha Allah zai bamu wani rabon,gaggawa muke shi kuma Ubangiji bai son aikin gaggawa".

Harshe nasa a hankali na fara lashe hawayen nasa, a sannu na d'ora lips d'ina kan nasa ina gogawa tare da zira harshena cikin bakinsa ina wasa dashi.

Cikin sanyin jikinsa ya shiga karb'ar sak'onnina tare da k'ara sakani cikin jikinsa sosai, tsawon lokaci ina rarrashin sa tako wace siga tare damai kalaman kwantar da hankali, har naga ya fara dariya, sannan na tashi daga jikinsa ina d'aura towel hannu na mik'a mai shima ya mik'e, ina mik'a mishi wani towel d'in amma sai yak'i k'arb'a, kawai jinai ya kunce min nawa tare da shigewa ciki, marairaice fuska nai ina d'an biga k'afa tare dasa hannu ina tuttureshi nace" nidai ka barni inje in wanka kagafa har hud'u tayi tun biyu fa".

Kashe min ido yai yana dariyar tsokana yace" to muje mana muyi wankan,ai bance zan k'ara komai ba yanzu sai Zuwa dare kuma".

Ja nai da baya na fizge towel d'in da gudu na shige toilet. Bina yai da kallo yana dariya tare da d'aukan dayan towel d'in ya d'aura ya biyo bayana.
Ko juyowa banyi ba naci gaba da had'a ruwan wankan tare dasa turarukan wanka sannan na cire towel d'in sak'ale nai tsalle d'aya na shige cikin Bathtub d'in, yanda nai shima haka yai ya shigo ciki tare da mak'alewa jikina yana fad'in ayi min wankan duk na gaji bazan iya yiba".

Ban tanka mai ba sai cud'ashi dana shiga yi yanata wani shagwab'emin da narkewa ,nima wankan nai sannan muka canja ruwa don yin wankan tsarki.


Bayan fitowarmu a gaggauce muka sanya kaya don lokacin har hud'u ra rabi ta kusa,salla ya jamu mukai,bayan mun idar nasa riga mara nauyi iya k'aurina,shima 3quarter yasa da singlet,jansa nai zuwa kitchen ya tayani mukaci gaba aikin tare, munayi muna soyewarmu,har muka gama, shi yaje ya shirya dining table ni kuma na gyara kitchen d'in.


Sai bayan sallar magriba mukai dinner, yace in shirya muje gidan abokinsa da yai aure,cikin murna nai d'aki da gudu na shirya cikin riga da siket na wani had'ad'an boyel less milk da filawa ja,nai amfani da jan Vail da takalmin duk kalan ja ,sosai nai kyau, ina tsaye gaban mudubi ina k'ara gyara d'an kwalina ya turo k'ofan sanye da k'ananan kaya ta cikin mirror na kalleshi muka sakarwa juna mirmishi, yana tsaye jikin k'ofar hard'e da hannayensa yace "Babyna kinyi kyau sosai fa".

Farrrr nai da idanuwa ina takowa zuwa gareshi cikin rausaya da rangwad'a,gaban sa na tsaya ina k'ara gyara mai wuyan rigar nace" Kayan nan suna maka kyau matuk'a, amma nai zaton manyan kaya zaka sa fa".

Mirmishi d'auke kan fuskar sa yace" Su kike so in saka?".

Gyad'a Kaine tare da rausayar dashi.
Rik'o hannuna yai yana fad'in "To muje d'aki ki zab'o min wanda kike so in saka".


Wajan closet d'in sa na nufa na zab'o mai wata narkakkiyar shadda
Milk color wadda aka yiwa aiki da bak'in zare,d'in ki boda ne, sannan na zab'o mai bak'in takalmi da hula bak'a, bayan na gama shirya shi wani bayyanan nan kyau naga yayi min,kasancewar sa bamai yawon saka manyan kaya ba yasa duk sanda ya saka sai kaga kamar bashi ba,cikar kamala da haiba duk sai su bayyana a gareshi, lumshe ido nai bayan na sakar mai wani hot kiss nace"kayi kyau har ba'a magana Zaujee,manyan kaya sun fi kowane kaya maka kyau".

Shafo fuskata yai da fad'in "Sabida ke nake d'inka wa Baby na,amma nikam da basu wani birgeni, saka sun da nake yanzu sai nima nake jin dad'in su a jikina".

Waya ta na d'auka na fara buga mana slf ta ko ina.



*********
Kyakykyawar tarb'a muka samu daga wajan Muktar da matar sa laila, mun dad'e gidan muna hira muktar nata tsokanar UK wai duk ya zama kalan ustazai yanzu,har maganar sa ma ta canja,shi dai dariya yai yace " zama da ustazai ne maida ni haka".
Sai k'arfe goma muka baro gidan.

Muna shigowa shirin bacci kawai mukai ina jin sa yanata tsokana ta nai mai shiru don bacci ya kama idona.





~A gurguce plsss~πŸ‘‡πŸΌ

Cikin hukuncin Allah muka gama hidimar k'asar mu cikin nasara,daga nan na samu nutsuwa ban zuwa ko ina ko yaushe cikin hidiman mijina nake.

A wannan tsakanin ne bikin sweety ya taso in da akasa rana wata biyu kawai bisa rok'on da mijin yai tayi kan ayi a wata biyun.

Tun daga lokacin bama samun zama mune kasuwa mune manyan Mall mall.


______________ Rana bata k'arya yau ya rage kwanaki goma bikin sweety Kuma yaune aka k'arb'i lefe kaya na alfarma tun safe bamu zauna ba munata hidimar jama'a,y'an uwa da suka zo karb'ar lefen,sai dare gidan ya sarara kowa ya tafi,y'an aiki duk sun gyara ko ina,
Aunty murjah ma tana b'angaran Abba yasa muka k'ara baje kaya ni da sweety tana ganin kayan, nikam inata tsokanar ta ita dai duk jikin ta a mace yake,sallamar UK parlour d'in yasa muka kalli k'ofan a tare, muna had'a ido ya sakar min harara y'ar dariya nai ina mik'ewa gareshi tare da mai sannu da zuwa,"A'a ni kam ba ruwana dake yau gaba d'aya kin manta dani ina ta kiran wayar ki ma bikiyi picking ba".

Marairaicewa nai ina fadin "hubby nah wake mantawa da zuciyar sa,dukkan abunda nakeyi ruhina na tare da kai gangar jikin ce kawai anan ".

Lakuce min hanci yai yana fad'in" um dad'in baki dai da wayo za'a min kawai".

Kad'a ido nai tare da rik'o hannun sa nace "zoka zauna ka kalli kaya kafin in had'ama abunda zaka ci".

Nan na barshi tare da sweety na wuce kitchen da azama na fara shirya mai plate daman na riga na ajiye mai abincin daran da naiwa Abba, tuwon semo da miyar d'anyan kub'ewa da taji tantakwashi.

Center table na jawo mai gaban sa na shirya mai abincin akai,bayan ya fara ci na shiga d'ad'd'aga mai kayan yana kalla,jinjina kai kawai yake yana yabawa tare da addu'ar fatan zaman lafiya ga ango da amarya.



Sai wajan sha d'aya muka zagayo gidan mu,kai tsaye toilet muka wuce mukai wanka tare da alwalan kwanciya don neman kariya daga shed'anin mutum da aljan.

Muna kwance hira muke tab'awa kad'an kad'an yana matsa min jikina dake min ciwo sabida gajiyan yau,cikin tsokana yace" wato ko ki tambayeni ma yau ina na tsaya sai taran dare kika ganni".

Cikin rashin damuwa da batun nace"Ai nasan don kasan muna hidimar mutane ne baka shigo da wuri ba,don koda ka dawo ma a hidimce zaka ganni,lokacin daka shigo ma ban dad'e da gamawa Abba abinci ba".

"Hhhmmmm yarinya shi yasa nima nai tafiya ta tad'i don nasan in na shigo ma gidan da wuri bakya nan".

Da sauri na tashi daga jikin sa cikin fargaba nace " me kace?".

Cikin dakewa da basarwa yace"Naje gun k'anwar ki ne tace ma in gaida ki sosai".

Jinai wani mashi ya soki zuciya ta da k'arfi,amma cikin y'an seconds nai tunanin wace ce ni,mace me aji nake,don haka na d'an murmusa tare da fad'in "hhhhhmmm ina amswa sosai nima ina gaishe ta sosai".

Kaina na maida jikin sa na kwantar, zuciyata na wani irin bugu.

Mamaki ne ya kamashi ganin yanda na dake duk da yasan tsananin kishin da nake dashi,a zahiri yaga firgici tare dani amma kuma sai furucina ya nuna ban damu ba, cikin son k'ara jan zancan yace" biki tambayeni wace ba kuma ya sunan ta sannan a ina take ba".

K'ok'ari nai na fizgo kalmomi daga bakina nace" hhhmmmm ai wannan duk ba hurumina bane,in ma kuma ina da hurimi dasu nasan in lokaci yai zanji ai".

Daga yanda nake furta maganar yasan nazo wuya kawai b'oyewa nake k'ok'arin yi. Amma kuma sai yaji ba dad'i da ban nuna zafin kishi kansa ba,

D'ago ni yai zaune shima ya zauna tare da fad'in "Da wasa nake miki my life karki d'auka da gaske fa".

Kallon k'yar namai tare da fad'in" Ko da gaske kake ba abun damuwa bane ko b'oye b'oye, na dad'e ina fad'a maka ban marmarin rayuwa da kishiya a rayuwa ta,amma in har akwai zama da kishiya cikin rayuwar aure na to zan zauna da ita tsakani da Allah kuma in amsa kaddara ta hannu biyu, kuma ai zuwa yanzu daman ya dace ka fara neman aure ko don samun Baby kaga sai damuwar ka ta tafi akan son haihu. . .".

Da sauri ya rufe min baki yana jawoni jikin sa sosai, tsawon minti guda sannan yace " Wlh Allah da wasa nake miki Khadeejah, kin sani nasha fad'a miki ban ra'ayin tara mata matsayin nawa,sam sam banda wannan ra'ayin balle har kike cewa wai kodan in sami Baby, kina nufin har anzo matakin da zan miki kishiya don biki k'ara haihuwa ba? to kima cire wannan daga ranki wlh duk abunda nake nema nadaga yaya fata na su zamo daga gareki, kodan samar musu da kyakykyawar rayuwa me cike da nutsuwa da tarbiya, ni da wasa nake mu bar wannan maganar ma don Allah ".

Yana gama fad'a ya koma ya kwanta tare dani a jikin sa, nidai lumshe ido kawai nai zuciyata ba dad'i duk da kalaman da yai yanzu sun Dan samun nutsuwa da kwanciyar hankali amma sai nake jin zuciyata cikin kishi sosai".


A haka bacci yai gaba damu,Wanda bamu farka ba sai asuba, bayan mun idar da salla munyi azkar wanda shi ya ke karantawa da fassaran hausa don bai haddace su duka ba,shiyasa na bashi littafin yake amfani dashi.

Tsawon 30 minutes muka shafa na jiyo ina gaisheshi kamar kullum ya amsa min cike da kulawa sannan ya k'ara k'asa da murya sosai yace" my life kiyi hak'uri da maganar da nai miki jiya Allah wasa ne kawai nake miki".


Mirmishi bayyane kan fuskata nace "lah nifa har nama manta da wannan issue karka damu nasan raha ne kawai ka ke yi".

Shafa kaina yai cikin nutsuwa yace" masha Allah, Allah yai miki albarka mata ta".

Cikin jin dad'in Addu'arsa na amsa"ameen ameen my zaujee,Allah ya kare min kai daga dukkan abun k'i ya faranta rayuwar ka duniya da lahira".





********************
Abun fa yazo, don yau ne Alhamis za'a saka Sweety a lalle, tun safe ban gida duk da gidan nawa cike yake taf da k'awaye da y'an uwan su,duka d'akunan k'asa da parlour sun baje suna bidirin su, shigowa ta daga wajan saloon kenan na zauna tsakiyar su muke gaisawa da d'an hira,wasu da yawan su na san su,wasu kam yau na fara ganin su,dukkannin su y'an mata ne sai mutum biyu da na gani da yara hannun su,da kuma wata shukra ita bazawara ce, raha sosai muke dasu ana hira, na kira lami nace su kasance a part d'in sabida kula da hidiman bak'i da gyara waje, cike da girmamawa ta amsa da fad'in "To uwar d'akina an gama insha Allah".

Daga bayana naji an saki wani siririn tsaki,juyawa nai idona ya fad'a kan Zee yarinyar Aunty uwani,wanda tun shigowa ta ma ban kula da ita a wajan ba,d'auke kai nai daga gareta ina cewa Lami " shi kenan jeki".

Ta mik'e ta tafi,nima tashi nai ina ce musu barin
in d'an watsa ruwa.



******Tunda na shiga d'aki nake tunanin wannan karon zan koyawa zee hankali,sabida duk sanda muka had'u wajan wani taro nasu ko a kano ko a katsina sai taita min tsaki tana hararana ta gefan ido, tun ban gane me nai mata ba,har na fara fuskantar tsakanin ta da UK don da ta ganshi zata fara wani rausaya da rangwad'a tai ta shige mai,babu Wanda ya sanar dani da kaina na fahimci hakan,don haka nasa a raina zan daina koda kulata bare ta rink'a min kallon banza.





************k'arfe biyar aka fara gudanar da kamu a wani babban fili na Abba dake cikin layin namu can k'asa.

An shirya wajan da kayan al'adar hausawa komai yayi gwanin birgewa, yayin da aka d'auko makad'an k'warya na gidan sarki suke cashewa.
shigata nai cikin wani sari riga da siket da mayafin sa, har da sark'a da D'an kunne kalan sa don akwati guda UK yai min na kayan fitar biki kamar yanda yai wa kansa ma,kuma duk yawanci kayan namu kalansu d'aya ne, nai kyau badan san kai ba sai dan sanin cewar nayi kyau d'in. duk in da na ratsa za'a ce kai kinyi kyau, mirmishi kawai nake nace "na gode".

Ina lura da Zee da hararar da take wurga min tunda na shigo wajan,kallon arziki bata isheni ba,don haka sabgar gabana

Please Login or Register in order to submit comment