Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ko ya raya mana".

Ban kalleshi ba na mik'e tsaye da fad'in "Bari na sauka nabar jama'a".

Bina yai da ido harna fice abuna

Girgiza kansa ya shigayi yana mamakin wannan shiru shirun dana koya a gareshi, shi wlh yanzu bashida matsala face ita, haihuwar ce daman bai so kuma yanzu yaji yana k'auna k'arshen ransa to menene kuma matsalar tunda daman akan ta suka sami sab'ani yanzu ai komai sai ya daidaita su had'u suyi rainan y'ar su cikin so da k'auna. Ya dad'e yana sak'awa da kwancewa daga baya ya zame ya kwanta yana kwantar da Babyn a k'irjin sa,a haka bacci ya d'auke shi.



Tunda na sakko k'asa mukaci gaba da hira da jama'ata amma rabin hankali na duk yanaga y'ata,musamman danaga lokaci yayi tsayi har awa guda da saukowa ta, nan duk idona ya koma ga stair's d'in ina jiran sakkowar sa amma har awa biyu lokacin na kalli agogo sha d'aya dai dai tun k'arfe tara kuma nakai mai ita, tabbas kunya da kawaici au kad'ai ne sukai min Katanga da tashi zuwa d'auko abata, sabida ko dai dai da minti guda banso in wulga idona ban ganta ba kusa dani.duk da bazan nuna hakan a zahiri wani ya fahimta ba amma zuciyata zata kasa sukuni kuwa.

Sha biyu dai dai kowa ya tashi daga hira don kwanciya,amma nikam ko baccin ma banji,Goggo ce tace " To yau dai da alama jinjira wajan Baban ta zata kwana tunda gashi har yanzu bai sakko da ita ba".

Yaya jummai tace "hhhhhhhh komai dare zaki ga ya kawo ta wuyar ta ta buk'aci nono ai, k'ilama bacci ne ya d'auke su amma data farka zata nemi uwar ta ai".


Daga haka naga kowa na k'ok'arin kwanciya, tashi nima nai zuwa d'akin jegon mu zuciyata ba dad'i, toilet na wuce na gyara jikina nai brush na fito sannan nai shirin bacci cikin doguwar rigar bacci me laushi wadda ta sauka har k'asa ,batada hannu sai d'an siriri,gabanta duk botir ne ajere har zuwa wajan ciki, d'an turare na goga na haye gadon da addu'a kan bakina.



Tunda na kwanta ko sau d'aya bacci baizo idona ba,yayin danaga sauran jama'ar d'akin sun bud'e baki sunata bacci harda minshari abinsu.

Duk motsin agogo na kan idona har wajan k'arfe biyu saura ji nake kamar in tashi inje in d'auko abata.
Can nakejin kamar sautin kukan ta na k'ara kasa kunne sosai kafin in tabbatar naji an bud'e k'ofar fatima ta shigo idonta cike da bacci take fad'in" Aunty kinga kizo Baby ta tashi gata can hannun Abban ta,muna kwance a parlour kukan ta ya tadani yace in kiraki".

Tashi nai nabi bayan ta muka fita,ina fita parlourn naji yanda take tsanyara kuka har cikin raina,da d'an sauri na na k'arasa ya mik'o min ita yana fad'in "yanzu ta farka kuma da kuka,bacci ne ya d'aukemu tun bayan fitar ki".

Ban tsaya sauraran surutun da yake ba na juya zuwa d'aki don kukan da take har tsakiyar raina nakeji.


Da sauri na d'auko ruwan zamzam d'in ta nai bisimilla ina samata fidar a baki ta fara shan ruwan da sauri saurin ta, daga nan na b'alle botir d'in Rigar na fara bata nonon cafka tai ta fara sha na lumshe idona ina k'ara rungume ta a jikina,wani sanyi na ratsa zuciya ta,ji nake kamar tai shekara bata wajena,ta dad'e tana shan nonon na canja mata wani shima saida na Tabbar ta k'oshi sannan nasata a kafad'a ina shafa bayan ta can naji tai gyatsa ,sauko ta nai na cire mata rigar jikin ta har pampas d'in na canja mata wasu, zuwa lokacin harta koma baccin, bayan na kwanta na sata jikina inajin wata nutsuwa na ratsani daga nan bacci me nauyi ya d'auke ni.






*TAKU* *CE* *Y'AR* *MUTAN* *JA'OJI*✍
🍑🍑🍑🍑🍑🍑
🌸🌸🌸🌸🌸🌸
*'YAN* *ARABIC*
🌸🌸🌸🌸🌸🌸
🍑🍑🍑🍑🍑🍑

*NA*
*LAYUZA* *KABIR* *ADAM*

_DEDICATED_ _TO_ _ALL_
_ARABIC_ / _ISLAMIC_ _STUDENTS_
πŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“š


πŸ‘©πŸ»β€πŸ’»πŸ‘¨πŸ»β€πŸ’»
*ZAMANI* *WRITERS* *ASSOCIATION*
πŸ“
_We_ _are_ _here_ _to_ _educate_ , _motivate_ ,and _lentertain_ _our_ _Readers_




0⃣5⃣2⃣





Tun sassafe gida ya fara kacamewa da hayaniya, hidima kowa keyi, nikam ina d'aki cikin adona me sauk'i na atamfa super riga da zani,sai babyn da akaiwa wanka itama cikin kayan sanyi don da sanyin safiya garin.
Sweety ce ta shigo da gud'a tana fad'in "Broth ya biyani,ya gama min komai wlh,yayiwa sweet mom d'ina takwara kuma nima yayi min,shiyasa tunda akai haihuwan nake tambayar sa me sunan Babyn yak'i fad'a min nace zan bada ai mata calander ne yace ya bada ayi komai duk don yana son surprise d'ina,tnx tnx my broth".

D'aukan Babyn tai ta rungume ta tsam" Allah ya raya mana ke namecy yayi miki Albarka".

Kowa dariya kawai ke mata, ta jiyu tana kallona da kashe ido cikin tsokana tace"Em Aunty na naga wannan gidan naku baku bani d'aki ba sabida ba'a buk'ata ta,amma yanzu kam dole zanya kaina d'aki don inyi rainon sweet daughter ".

Dariya nai ina fad'in" hakan shi zaifi min dad'i wlh,ki kwaso kayan ki kawai".

Y'ar dariya tai tace tom "Tom yanzu me zamu rink'a kiran ta".

Kafin nai magana Aunty Amrah tace " Ai zab'i na gareki maman Baby ".

Farrr tai da ido cikin tsananin farin ciki da nishad'i tace " em mu rink'a kiran ta little ko Aunty na ".

Mirmishi nai ina fad'in" banida zab'i fa sweety duk yanda kukai".

Sauran y'an d'akin suka amsa mata da yayi, don haka ta juya cike da farin ciki ta fice.



Taro yai taro zuwa azahar gidan nan namu babu wajan aje k'afa aji dad'i, jama'a damk'am ,kowa barka barka,anyi hidima anyi yanke yanke ,anci ansha an raban kayayyaki ,sosai ga calendar, stickers memo,key holder abubuwa sosai aka raba, Duk hidiman da ake Abba shima yana can parlourn sa da mutanan sa suna waleema,haka uban gayyar,abokan sa kamar mata haka aka rink'a taron nan dasu,masu hotuna da video tako ina d'auka suke,abun yayi,ni kuwa sabida d'inki na ban wani zirga zirga,ina zaune main parlour yanda kowa yazo zai ganni sai dai in zan canja kaya nake tashi, pic's ma da k'yar naje aka yiyyi dani, na sake da UK anata mana hotuna ina fara'a ta kamar ba komai tsakanin mu,Babyn sa kuwa yana manne da ita, har sai da wani abokin sa ya tsokaneshi "Oh abokina nan kaita kukan an had'a ka da y'ar Arabic an gama dakai,to sai gashi daga aure kai bilulun da ita harda ciki da haihuwa".

Dariya yai yana kallon sauran abokan nasa yace " Wato guys wlh ina baku shawara kuyi azama kuje ku nemo *y'an* *Arabic* d'in nan wlh sunfi ribar aure,duk wata ni'ima an tattarata garesu,nutsuwa da kwanciya hankali tana ga mijin daya auri ma'abociyar addini ga sanin sirrin so da iya sarrafa soyayya nan da nan ake kwancewa mutum k'ulli. . . . 😍

K'arashewa yai da dariya yana tafa hannu.

Suma duk dariyan suka sa wani cikin obakan yace "d'an iska yanzu ai saika daina yimusu gani gani tunda ka latsa kaji bauwar dake tare dasu,ni daman shiyasa nafi son auran mace maabociyar addini wlh,ba ruwana da wani kyanta ko wayewa,don haka don Allah ka fad'awa Khadeejah ta lalubomin cikin k'awayen ta nima inbi sahun mijin *'YAN ARABIC*πŸ˜‚".


Duk Kansu dariya suke wasu na mama kin yanda duk d'abi'un UK ya canja tun bayan auransa .



Bamu muka sami kanmu ba sai bayan sallar magriba gidan ya sarara sai masu k'ara kwana Wanda suma sunfi jiya yawa.


Ruwa me zafi sosai na samu nai wanka na gasa jikina,sannan na had'a tea me kauri nasha,daga nan naji dama dama, Babyn ma wanka aka mata da ruwan zafin don sabida yawan d'auka jikin ta zai mata ciwo,amma da aka gasata da ruwan zafi zataji dad'i.


Da wuri bacci ya d'aukeni ban tsaya sauraran su da hira ba.


*********
Washe gari tashi ba sai wajan Tara,bayan nai wanka Goggo tasa aka shigomin da kayan abunci naci nai nak Alhamdulillah, sai a sannan aka shigomin da Little Ruky an shirya ta tun tuni cikin jan kaya masha Allah tai kyau tsaf da ita sai tsotson yatsa take,a hankali na janye yatsan a bakin ta nasa mata nono ,idona akanta ina k'ara jin son ta na shiga zuciyata, naji an turo k'ofan an shigo, d'ago kai nai don ganin waye,ganin sa tsaye ya harde Hannaye yasa na maida kaina k'asa, k'arasowa yai bakin gadon ya tsugunna tare da rik'o hannu na cikin nasa d'aya hannun kuma yana shafa kan Babyn,tsawon mintina muna a haka daga bisani ya nisa kana yace"my deejah barka da safiya". Tunda ni ban samu matsayin a gaidani ba.

Kunya kuma naji ta kamani amma saina basar ciki ciki nace "ina kwana".
Bai amsa ba illa kafeni da yayi da idanuwa,sannan yasa hannu ya d'auki little ya zauna bakin gadon yana mata wasa.

Minti biyar ya waiwayoni tare da tattara dukkan hankalin sa ya fara magana" Khadeejah tafiya ce ta taso min da asuba aka kirani, wai ana neman mu a Lagos kan company d'in mu,ina tunanin one week zamuyi mu dawo insha Allah, yanzu haka ana jirana k'arfe 11 jirgin mu zai tashi,ki kulamin da mama na da kanki, kiyi hak'uri dani ki yafemin laifukana".

Shiru yai na d'an lokaci sannan ya d'ora " akwai kud'i a d'aki na,duk abunda zakiyi kije ki d'auka, sannan idan bak'in mu zasu tafi ki sallame su.

Mik'ewa yai da Babyn a hannunsa yana yin hanyar waje,tunanin shi zan biyo shi yaga ba niyya,saiya tausasa murya yace "zo muje ki dawo da ita".

Ba musu na tashi nabi bayan sa,a parlour ya tsaya yaiwa jamaar da sukai saura basu tafiba sallama,suka bishi da addu'ar Allah ya kiyaye hanya.

Ni kuwa a kunyace na ratsasu na wuce.

Driver na hangomu ya tada mota, baya ya shiga ya zauna sannan ya rungume ta jikinsa tare da kissing d'in ta,miko min ita yai idonsa k'ir cikin nawa,yana jira yaga me zance. K'asa nai da kaina a hankali na furta " Allah ya kiyaye hanya ya bada abunda akaje nema".

Cike dajin dad'i ya amsa"ameen ameen dear,ki kulamin da kanki da mamana ".

Gyad'a kai kawai nai na juya shima driver ya tashi motar suka tafi.


Dana koma cikin y'an uwana hira muka bud'e yayin da masu aiki keta faman aikin naman hakika.


*******
Washe gari kowa ya koma inda ya fito ya rage gidan dagani sai goggona da Aslamiyya y'ar Auntyn mu da zatai hutu anan.duk sai naji gidan yamin wayam,donma Goggo me hira ce tana bamu labaran dariya dana mutanan da.



****
Bayan kwana biyar da suna UK ya kirani a waya sama sama muka gaisa ya tambayi y'ar sa nace mai tanan qlau daga haka na kashe wayan.


Munci gaba da wanka tsawon sati hud'u na murje nai kyau dani Little Ruky ma tai b'ulb'ul Masha Allah da ita,ga wayo tayi don yarinyar akwai wayo kullum idonta k'yar tana kallon kowa. Zuwa lokacin ya zama UK bashida wani aikin in yana gida sai na kula da ita,don yanzu inya dawo sai intai kuka kawai nake ganin ta ya kawomin ita inbata nono ya koma da ita,ganin irin kulawar da yake bata yasa zuciyata yin sanyi don dama akan ta ne gabar,amma dukda haka fa ban sakar mai kamar farko,sai dai yanzu zamuyi hira kad'an kad'an fuskata ba walwala sosai .shi kam hakan ma yamai dad'i yasan a sannu zamu dawo normal kamar da.

D'inki na ya warke ras jikina ya had'e yanda ake buk'ata,gashi daman banyi dogon jini ba duka sati biyu ya d'auke min don haka na dage na fara gyara kaina da kayayyakin da aka had'omin daga sakkwato, Goggo ma batai sanya ba wajan bani wasu sirrika daya kamata me jego ta kiyaye bayan d'aukewar jinin bik'i,Masha Allah ni akan kaina inaji na zam zam duk da daman bawai na bud'e bane tunda bada kaina na haihu ba.


Watan mu biyu cif Goggo ta fara shirin tafiya gida,don daman mun dagene ta zauna mana har zuwa yanzu,amma tun muna ar'bain taso tafiya. Siyayya sosai UK yai mata na tsaraba hakama Abban su ya bada kud'i akai Mata siyayyan tsaraba,duk na shiga damuwa sabida ba k'aramin shakuwa da sabo bane ya k'ara shiga tsakanin mu, gashi d'aki guda muke kwana a k'asa ko yaushe muna tare, naso nabita ma muyi yawon ar'bain yayyena maza da basu gantaba in kai musu ita amma danaiwa UK maganar yace gaskiya bazan tafimai da yarinya har sakkwato ba tana wata biyu in bari inta k'ara k'wari da kansa ma zai kaimu, banso ba haka na hak'ura.


Daran da Goggo zata tafi mun raba dare muna hira har bayan sha biyu muka kwanta .

Kiran sallar farko naji ana mana knocking door, da mamaki nace " waye?".

Cikin muryar bacci naji yace "Khadeejah bud'e nine".

Tashi nai ina mutstsika ido na bud'e don nai tunanin ca zai in mik'o mai little don haka na d'auke ta nasa a kafad'a na fita,tsaye na ganshi yanata safa da marwa tsayawa nai a bayansa ina fad'in" lfy?".

K'arasowa kusa dani yai yana fad'in "lfy qlau ina Goggo?".

Nace " bacci take".

Yace "ki tasheta ki had'a kayanki kema yaya yai min waya yanzu wai an mai waya daga gida umma batada lfy zakuje ku dubata gobe zaku dawo".

Zaro ido nai ina fad'in "innalillahi wa innailaihi ra'jiun,meya sameta kodai rasuwa tai kuka b'oyemin ?".

Rik'o hannu na yai ganin jikina nata rawa ya karb'i little tare da zaunar dani kan kujerar dake gefe na," ki kwantar da hankalin ki Nahna,umma tana nan da ranta wlh kawai ciwon ciki ne yaya yace min to har an kwantar da ita ma a asibitin tun jiya da yamma cikin dare aka mai waya,to suna son zuwa yau don haka yace zasu biyo su dau Goggo tunda daman yau d'in zata wuce,yace inba damuwa kema in barki Ku tafi tare,ki kwantar da hankalin ki yanzu kije ki shirya ana fitowa masallaci zasu biyo ku tafi".

Share hawayen daya gangaro min nai ina mik'ewa zuwa d'aki .

Tashin Goggo nake cikin kuka ta farka da salati take take tambaya ta meye ina matse ido nake sanar mata meke faruwa, salati ta d'auka da mik'ewa tana gyara d'aurin zani tace "Allah ubangiji ya jishshemu alkairi, wannan ciwon ciki kwana biyu ya matsawa Yaya,yi maza ki had'a kayanki bari inyo wanka da alwala".

K'aramin akwati na d'auko na had'a kayana set uku dana little a ciki duk abunda zamu buk'ata na had'a, idona yak'i yabar zibda hawaye don gabana ya tsananta fad'uwa kawai ji nake kamar b'oyemin ake kodai ummata ta rasu ne.


Goggo na fitowa aka kira asubahi da sauri nima naje nai wanka tare da d'auro alwala,a lokacin UK ya kwankwasa k'ofa naje ya mik'o min little zai wuce masallaci, Goggo na mik'awa ita na tada salla,ita kuma ta had'a ruwan wanka ta mata.



Wajan k'arfe shida su yaya sukazo shida yaya usman ne, nida Goggo muka shiga bayan motar UK yanata d'aga mana hannu ya koma, ganin yanda naga jikin su yaya amace lis yasa ni k'ara firgita, cikin share hawaye nace " yaya wai meya sami umman ne".


"Cikin sanyin murya yaya usman ya amsa min " wlh ciwon ciki ne ,wai harya tab'a Mata hanji yauma za'a mata aiki".

"Ya Allah ya bata lfy yasa ayi a sa'a" Goggo ta amsa da "Ameen".



*******
Lokacin da muka shiga sakkwato kai tsaye asibitin muka nufa.yanda muka tatar da y'an uwan mu cirko cirko yasa jikin mu k'ara mutuwa, da sauri na k'arasa ina tambayar su jikin nata sukace an shiga da ita aikin tun tuni,zaman awa guda mukai kafin aka fito da ita,duk kanta mukayo amma aka dakatar damu da cewa ko d'akin kar Wanda ya shiga don tana buk'atar hutu.

Har dare muna zaune muna zaman jiran farfad'owar umma amma shiru,sai cikin dare ta farka amma kuma ba cikin hankalin ta ba,k'arshe ma sai ta fara suma hankali tace muka kira doctor yazo kanta, allurai yai mata nan bacci ya k'ara d'aukan ta, mukam duk hankalin mu a tashe har gari ya waye.


Tsawon yinin ranar nan haka mukayishi cike da tashin hankali don jikin umma fa ba sauk'i saina Allah, kuka nayi shi harna gaji,kawai tunani nake in umma ta rasu shike nan banda uwa banda uba,sai gatan y'an uwa.
wajan yamma Allah ya taimaka jikin yai sauk'i harta fara dawowa hankalin ta,cikin yanayin tsananin rashin lfy ta mik'omin hannu na k'arasa jikin gadon ina share hawaye nace "sannu umma,Allah ga baki lfy ".

Can k'asan bakinta tace " Ameen Auta, ina miki wasiyya da yiwa y'an uwanki biyayya, musamman Haroon ki kula dashi da rayuwar sa,baki da sama dashi duk duniya, sannan kibi mijinki, kibishi iya iyawarki,sannan ki kula da tarbiyar abunda kika haifa kinji ".

Gyad'a kai kawai nake ina share hawayan daya keta gudu a idona. Haka sauran y'an uwan mu ke zuwa bakin gadon suna mata sannu duk da ka taketa amsa musu don maganar ta rik'e ,daga haka kuma sai bacci ya k'ara d'aukan ta, duk sai muka d'an sami nutsuwa, har mukaje mukayi sallar magriba da aketa kira.


Gab da sallar isha'i ta k'ara farkawa da shak'uwa me k'arfi tanayi k'irjin ta har sama sama yakeyi duk likitocin nan suna kanta, sun koramu waje, bayan mintinan da basu wace sha biyar ba rai yai halin sa,Aunty salma dake jingine jikin window d'in taga sunja zani sun rufe mata jiki har fuska bayan duk sun cire injinan dake aiki ajikinta,wata k'ara data saki ya samu ankara da gudu mukai jikin window Wanda dai dai nan likitocin suka fito suna bamu hak'uri.





*Taku ce*
*Y'ar mutan ja'oji*πŸ™‹
🍑🍑🍑🍑🍑🍑
🌸🌸🌸🌸🌸🌸
*'YAN* *ARABIC*
🌸🌸🌸🌸🌸🌸
🍑🍑🍑🍑🍑🍑

*NA*
*LAYUZA* *KABIR* *ADAM*

_DEDICATED_ _TO_ _ALL_
_ARABIC_ / _ISLAMIC_ _STUDENTS_
πŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“š


πŸ‘©πŸ»β€πŸ’»πŸ‘¨πŸ»β€πŸ’»
*ZAMANI* *WRITERS* *ASSOCIATION*
πŸ“
_We_ _are_ _here_ _to_ _educate_ , _motivate_ ,and _entertain_ _our_ _Readers_




0⃣5⃣3⃣



Jina da ganina ne ya d'auke na wasu mintina zuwa can ya dawo min tare da hargitsi da firgici,ganin duk wata halitta data jib'anci ahalin mu zubar hawaye take,nan take na k'ara tabbatar da mahaifiyar mu ta rasu kenan.kuka Wanda ya amsa sunan kuka shine ya kawomin ziyara, na kifa kaina jikin bango ina kuka me cike da ban tausayi da maraici, wato rashin iyaye babu babba ba yaro ba mace ba namiji duk wanda aka tab'a sai ya koka. Ganin yanda muka cika asibitin da koke koken mu yasa aka hanzarta bamu gawar zuwa gida, daga nan aka shiga sanar da y'an uwa jana'izar da safe in Allah ya kaimu.

Nikam ban ma cikin nutsuwar da zan sanar da wani don duka a firgici nake ,ina zaune gaban gawar addu'o'i naketa mata idona na zubda hawaye,Allah sarki Mama abokiyar zama ta gari maman su yaya Haroon ta fice hayyacin ta don suma ma tai da taji labarin rasuwar,sabida shakuwar dake tsakanin su ta wuce misaltuwa busiyi zaman kishi da juna ba tun farkon zaman su har tsufan su.



Haka muka kwana tsam a zaune muna ta yi mata addu'a da karatun Qur'ani,tare da rok'a mata gafarar ubangiji.


*******
Tashin hankalin rashi be k'ara gigita wanda yai rashi irin idan an d'aga gawa za'a fita da ita,duk dakiya da k'arfin imanin mutum in aka d'aga gawa sai ya girgiza, k'arfe bakwai dai dai aka d'aga gawar umma cikin makara zuwa k'ofar gida,don sallatar ta,gidan ya hargitse da koke koken jama'a yayin da nikam idona ya kafe k'am ba hawaye don zuciya ta ta wani bushe idona ya k'afe sai wani k'una da nakeji kamar ana suya cikin k'irji na yanda nake a jingine jikin bango ina bin kowa da kallo duk da fahimtar komai nake ba amma kunnuwa na naga k'ofar gida inda nake jiyo saurin muryar liman yanata kabbara, a haka kuma hayaniyar tashin ababan hawa ya karad'e tabbacin an idar za'a tafi kaita makwancin ta.runtse idanuwa na nai ina taune lips d'ina tare da dafe kai cikin raina nake wa Allah tasbihi don neman sassauci a wannan yanayin da k'unci yai wa zuciya k'awanya.




Misalin k'arfe tara ina kwance kan gadon umma na kuka nake mara sauti me cike da k'una, a bayana naji muryar sweety da Aunty murjah suna gaisawa da mutanan d'akin tare dayi musu gaisuwa,juyowa nai da kumburarrun idanuwa na na bud'e su da k'yar a Kansu.
K'arasowa sweety tai bakin gadon tana dafani tace "Sannu Aunty nah,sannu Allah ya jikan umma ya gafar ta Mata zunuban ta".

Mik'ewa nai da k'yar na zauna idona na zubda hawaye , gaisawa mukai da Aunty tana k'ara min gaisuwa, sweety ma tamin gaisuwa tare da zama kusa dani,a hankali tace " tare muke dasu Aunty Amrah harda Abba da broth,tun daren yaya Haroon ya sanar da Abba mun nemi tickets wanda zamu sami jana'izar amma bamu samu ba,saina yanzu ".

Jijjiga kai nai ina share hawaye nace " Wlh ni nama manta ban sanar da kowa ba,wayar tawa ma ban san inda take ba".

"Eh ai munata kira ba'a d'aga ba".


Su Aunty Hafsa ne suka shigo d'akin itada Aunty Amrah idanuwan su taf da hawaye suka zauna muka gaisa tare da yiwa juna gaisuwa.

Wajan k'arfe goma Abba da UK suka shigo gidan don yin gaisuwa wa mata,da k'yar na mik'e na fita zuwa parlourn mama inda suke mata gaisuwa, k'arasawa nai na tsugunna ina gaida Abba " cikin tausayawa yake amsamin tare da min gaisuwa, shi kuwa UK idanuwan sa akaina ya kasa furta min ko kala sai kallon tausayi da yake bina dashi kawai, ni kuwa kaina yana k'asa banma san me yake ba,mik'ewa Abba yai shima yabi bayan sa suka koma k'ofar gida.


*****
Bayan sallar la'asar Abba ya aiko inzo,a bakin gate na same shi dasu yaya haroon a tsaye k'asawa nai ina k'ok'arin taugunnawa yace "A'a yashi tashi Khadeejah, daman sallama zan miki zamu wuce don jirgi zamu k'ara bi kuma biyar zai tashi,amma nida murja ne zamu wuce Rukayya da Daddy na suna nan zuwa jibi sai su taho, kiyi hak'uri kinji Khadeejah ki rage kukan haka addu'a take buk'ata yanzu,ita tata tai kyau tunda ta rasu ta sanadiyar ciwon ciki kinga tayi shahada,fatan mu Allah ya karb'i shahadar ta".

D'aga kai kawai nakeyi kamar k'adangaruwa don ba baki da nayi niyar yin magana kuka ke k'wace min.

Bayan munyi sallama yace in turo Aunty murjah su wuce.

Dana isa na sanar da ita taje taiwa mama da y'an uwa na sallama, sweety ta rakata

Please Login or Register in order to submit comment