Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Lumshe ido tai tana fad'in "lafiyata qlau Nahna kawai ina kewan habeebina ne".

Y'ar dariya nai nace " kai Aunty nah daga tafiyarsa yau har kin fara kewansa?".


D'an zaro ido tai tace "hhhhmmm khadijah kinsan kuwa me ake nufi da aure? bazaki gane girman so da k'aunba sai kinyi aure,wlh yau ji nake kamar inyi me Nahna nai kuka nai kuka harna gaji,ji nake kamar yai wata guda da tafiya don tsananin kewansa na yini gudan nan".


Cikin mamaki nake kallonta don sai nake ganin kamar Wannan son da Takewa Yaya usman yayi yawa,ban tunanin zan iya son namiji haka a rayuwata,kai ina bazan iyaba gaskiya.


A hankali na dafata cikin sigar rarrashi ganin k'walla ta fara kwanciya a Idonta " kiyi hak'uri Aunty na insha Allah kamar yaune zakiga ya dawo tunda yace sati biyu zaiyi ya dawo,kuma kinga yacema transfer yake nema zuwa kano insha Allah nan kusa zai samu ya dawo gida gaba d'aya aita shan k'auna".

Mirmishi tai tace "na gode Khadijah, amma nasan yau da k'yar zan iya bacci wlh".

Nidai a zahiri rarrashinta naitayi amma a zuciyata ina mamakin mata irin wad'annan masu zazzafan so ga maza.


Da lokacin kwanciya yai tace mu kwanta a bedroom d'inta nace " a'a bari dai in kwanta a Wannan d'akin tunda shima da gado".

"Meyasa bazaki kwanta anaba ?".

Girgiza kai nai ina fad'in " gadon da mijinki yake kwanciya bai dace in kwanta akaiba,bama niba kowa ma bai dace ya kwanta kan gadon da kuke kwanciyaba".

Jin jina kai tayi tace "To muje can d'in mu kwanta,daman bama kwanciya Wannan d'akin".


Mun kwanta muna d'an hira tanata ban labarin Lokacin tana school da rayuwar boarding school d'insu, nikam sai dariya nake ina jin jina rayuwa irinta boarding school, wayanta tai ringing da sauri naga ta tashi zaune tana dafe k'irji tace " wayyo my hubby".

Mirmishi nai kawai nai addu'a na shafa tare da juya baya na lumshe idona ina son bacci ya d'aukeni don jin yanda take magana da yaya kamar wata y'ar Baby.

Amrah irin matan nan ne masu soyayya matuk'a in tana tare da yaya sai tai ta baka kunya don idonta rufewa yake taita mai soyayya.

A hankali naji ta dafoni tana fad'in "Khadijah ga yayanki zakuyi magana".

K'arb'a nai nai sallama muka gaisa nake tambayarshi sun sauna lafiya,ya amsa da eh can yace " Autan Baffah ki kula da Auntynki kinji kirink'a bata hak'uri kinga dik ta tayar da hankalinta kinji".

"To yaya ba damuwa zan rink'a kula da ita sosai insha Allah karka damu".


Bayan ta karb'i wayan taci gaba da shagwab'anta tana sakar mai wasu zafafan kalamai,nikam duk jinai kunya ta rufeni nai tsit ban k'ara ko motsiba.


Da safe tana bacci na tashi na shirya abin breakfast naci na shirya zuwa school, saida zan fita na tasheta " Aunty ki tashi ki rufe gidan ni zan wuce school ".

Da sauri ta tashi tana fad'in " Khadijah bikiyi breakfast ba zaki tafi,wlh bacci ne ya d'aukeni da nauyi,bari in d'ora miki ko ruwan tea ne kisha".

Mirmishi nai nace "Ai na shirya komai ma har naci nasa miki naki a cooler".


" Ayya sannu da k'ok'ari Nahna na gode ".


Har k'ofar gida ta rakoni ta rufe gidan.

Da yamma dana taso na wuce gida, sai dare na k'ara komawa gidan Yaya Usman.


Ya zama kullum haka nake da magriba in tafi gidan yaya Usman da safe in wuce school in na tashi kuma in wuce gida,har tsawon sati uku Yaya dawo ya kwana Biyar ya k'ara komawa,


*****************
Haka rayuwa taci gaba da garawa komai yana wucewa, kwanaki sunja sosai Wanda ya rage kwana uku UK ya dawo daga karatunsa, tunda labarin nan ya ziyarceni naji hankalina ya tashi matuk'a na rasa inda zan tsoma raina,sabida nasan lokacin aurena yazo kenan da Babban mak'iyina.


Kowa dake tare dani ya lura da canjin dana shiga duk walwalata ta kau,don haka Aunty Hafsah ta Sani a gaba da nasiha da maganganu masu dad'i taita ban shawara kan in k'ara dagewa da addu'a, anan na d'anji nutsuwa tazomin.


Ana jibi zai dawo Sweaty tazo gidanmu ganin irin yanda yanayina ya canja yasa ta fara min magana cikin sanyi " Nahna Duk kin canja damuwa ta bayyana tare dake kuma nasan don dawowar Broth ne,amma don Allah ina Neman alfarmarki daki kwantar da hankalinki waje guda kamar yanda kikai a baya,ni inaji a jikina tarayyarki da Broth d'ina alkairi ne garemu gaba d'aya,don Allah karkiyi abinda za'a gane hankalinki bai tare da yayana har ai k'ok'arin fasa auran nan naku,kinji my sweet Nahna".


Matse k'wallar idona nai nace "sweety bana fatan a samu matsala ta b'angarena domin zanzama y'ar halak ga Yaya na, kawai dai ina tunanin irin rayuwar da zanyi tare da d'an uwanki ne bisa dolan da za'ai mishi akaina,nasan bazan tsinci komai cikin auransa ba sai tsana da tsangwama".

" a'a ki daina fad'in haka My Nahna insha Allah zakiyi alfahari da auran Broth d'ina zaki sameshi me adalci a gareki kiyi hak'uri ki kwantar da hankalinki kiyita addu'a kinji".

Share idona nai nace "To ba komai insha Allah zan kwantar da hankalina ki tayani da addu'a Allah ya daidaita tsakaninmu".


Haka dai taita k'ara kwantar min da hankali,har wajan magriba ta tafi.

Da dare ina kwance d'aki a gidan Yaya Usman ba bacci nakeba kawai tunani nakeyi, Aunty Amrah na toilet tana wanka,bayan ta gama duk abinda zatai ta rufo Wancan d'akin ta kashe duk kayan wuta ta shigo d'akin da sallama,a hankali na amsa mata tazo ta zauna bakin gadon tare dafani tace " Khadijah wai don Allah make faruwa dake ne? Kullum damuwarki k'aruea take Amma inna tambayeki sai kice Norma ne,Khadijah yanzu bankai matsayin da zan San damuwarki ba kenan,koda ban kasance matar yayanki ba ni yanzu na d'aukeki matsayin k'awata kuma y'ar uwa ta, bazan b'oye miki damuwata ba,don haka Khadijah ki fad'amin meke damunki in na shawara ne in baki shawara in na addu'a ne in tayaki da addu'a ".

Tashi nai na zauna ina share hawayena nace " Aunty Amrah aure za'amin da mijin daya tsaneni bai ko son kallona, akan lefin da bansan nai mai ba haka nan tun fara ganina dashi ya kafawa rayuwata ido ya tsangwameni gashi yanzu aure zai shiga tsakaninmu".

"Nahna kina nufin auran dole za'ai miki? Duk gatanki duk yanda yayyanki suke sonki suke ji dake?".

" a'a Aunty Amrah ni a b'angarena ba auran dole za'aiminba,shine dai za'a mai dole a gidansu don mahaifinsa ne ke son had'amu.. ."

Nan dai na kwashe komai na fad'a mata tun farkon had'uwarmu a school har alak'ar dake tsakanin mahaifinsa da yaya usman da k'awancan dake tsakanina da k'anwarsa, da k'ullin da mahaifinsa yake son k'ullawa a tsakaninmu.

Jim tayi zuwa can tace "Nahna gaskiya dole ki shiga damuwa amma Wannan matsala ce mai saurin warwarewa indai zaki bada had'in kai wlh a sannu Zai soki so ma irin na mutuwa,amma sai kinyi hak'uri kin sawa ranki cewa bautar Allah zakiyi a cikin gidan auranki, Nahna shi namiji agun mace ba komai bane matuk'ar ta iya zama dashi tasan yanda zatayi mu'amala dashi tasan lagonsa da hanyoyin kyautata masa wlh a sannu zai zama a tafin hannunta,sai yanda tai dashi, Khadijah ki kwantar da hankalinki ki k'ara addu'a tunda har da bakinki kince kinyi ta istahara kuma duk sanda kikai kina jin yana Jin tsanarsa ta ragu a ranki to kinga gashi har yakai yanzu kinajin zaki iya zama dashi kuma bakya k'yamarsa kamar da kinga ai addu'a tai tasiri kenan,don haka yanzu ma bacci bai kama kiba tashi zakiyi kiyi alwala kiyita kai kukanki ga Allah, nima bari inyi alwala in tayaki rok'on uban gijinmu".

A zahiri maganganun Aunty Amrah sunmin dad'i don haka na tashi muka d'auro Al'wala mukai sallah raka'a hud'u mukaita addu'a har bacci ya fara fizgar Aunty Amrah taje ta kwanta,ni kuwa saida dare ya raba naje na kwanta inajin zuciyata wasai,( tunasarwa garemu y'an uwa aduk sanda matsala ko damuwa tai mana yawa to Addu'a kad'ai itace mafita)


" da asuba ma wasai na tashi nai sallah ban koma ba na d'auko k'ur'ani naita karatu bayan nayi azkar ban kwanta ba sai wajan shida da rabi kasancewar ranar bamu da Lecture sai k'arfe goma.


****************
Ranar Laraba k'arfe hud'u na yamma UK ya sauka a filin jirgin malam Aminu kano inda ya sami tarar Abbansa da K'annansa,cike da murna suka tareshi kowa na nuna farin cikin sa na ganin sa, nan suka d'unguma zuwa gida, nanma ya tarar an shirya gidan Ka flowers masu tsananin kyau anyi decorations tin daga bakin gate har zuwa cikin harabar gidan, zahirin farin cikin sa bai b'oyuwa don ganin yanda aka k'awata gidansu don tararshi kamar wani ango.

Kai tsaye Sweaty tai mai iso zuwa d'akinsa da aka k'awata maishi nanma da flowers ga kamshin turare air freshener tako Ina, ruwan wankama sweety ce ta had'amai yaje yai wanka,tsawon awa guda ya d'auka yana kimtsawa kafin ya fito harabar gidan inda duka family d'in gidan suka had'u suna jiransa, yana fitowa suka shiga gabatar mai da kayan abinci Abubuwan motsa baki kala kala harma ya rasa me zaici aciki sai dai ya cakuli Wannan ya fincini wancan, yanaci sunata mai hira kowa na nuna kulawansa akansa,har akai sallar magriba suka wuce masque shida Dad.

Ranar dai har k'arfe sha d'ayan dare Daddy (UK) yana tsakiyan danginsa suna hira yana basu lbrn karatunsa.

Da safe k'arfe bakwai saiga kiran waya daga sweaty ina gani naji gabana ya fad'i cikin kasala na d'aga wayan, "Hello Aunty nah kin tashi koni na tasheki?".

" hhhhmmm Sweaty na tashi tun d'azu harma nai shirin school ".

" OK kin tashi lfy ya gida?".

"Lfy qlau yasu Abbah da Aunty murjah?".

" kowa lafiya qlau yake amma biki tambayi Broth d'ina ba kuma dai kinsan ya dawo".

Jim nai inajin fad'uwar gaba nace " hhhhmmm ni ban San ya dawo ba tunda biki fad'aminba".

"OK ya dawo to tun jiyama nata kiranki wayanki a kashe in sanar dake ".

" hhhmm To ya dawo lfy?".

"Um lafiya qlau ya dawo yaushe zakizo mai sannu da zuwa?".

" hmm bari zamuyi maganar yanzu zan wuce school ne".
Nai saurin yanke zancan don ban San me zance mataba

"OK to a dawo lafiya Aunty Nah".

Muna kashe wayan na sauke wata nannauyar ajiyar zuciya, tare da d'aukan jakata naiwa Aunty Amrah sallama.



******
Bayan kwana biyu da dawowar UK da dare yana zaune parlour shida Sweety sunata hira tana nuna mai hotuna a wayanta,a hankali yazo kan folder d'in hotunansu na bikinsu yaya usman a sakkwato,yana kalla a hankali yace " sweety a ina kukai wannan pictures d'in ?".

"Lab Broth a sakkwato ne fa".

" meya kaiki sakkwato ke kuma?".

"Broth bikin yayan friend d'ina nefa mukaje".

" yanzu Abbah ya barki tafiya biki har sakkwato,don sangarta".

"A'a broth akwai alak'a sosai tsakaninmu da ita,kuma yayanta da take gunsa mutumin Dad ne suna harkar kasuwanci sosai".

" um hmm" kad'ai ya fad'a yaci gaba da kallon pictures d'in,

Yazo kan pic d'in amarya Zainab da angonta a gun dinner ya saki mirmishi yana fad'in " wannan ne angon ya wani dankama hula kamar bawa, ni ran aurena ma k'ananan kaya zansa, nasan zagi kawai zansha gun jama'a nikuma maganar kowa baya damuna ".

Cikin zumud'i sweaty tace " oh my Broth don Allah ka kusa yin aure? Ai k'ara kasa hankali wlh kayi,na matsu naga auranka".

Kallon ta yai dalala cike da mamaki yace " sabida me kuka matsu nayi aure, nawa nake da za'a matsu inyi aure 30 years kawai shine za'a sa idona akan inyi aure, haka fa Dad ya matsamin tun kafin in dawo kullum sai yamin maganar aure aure Ku kamar wasu y'an k'yauye kawai ayi aure ayi aure shine burinku lalle kuwa zaku dad'e Baku ga auran ba ".

Rik'o hannunsa tai cikin sigar rarrashi take cewa" cool down my Broth mana meye na d'aukan zafi haka daga maganar aure,shine nan tunda baka so anbar maganar daga yau".

Komawa yai ya jin Gina da kujerar yana fesar da iska me zafi,

" Sisy kinaji ko wato ban San in matse rayuwa inyi aure tun yanzu daga aure kuma shikenan sai a fara haihuwa a gidanka shikenan kuma an shiga wani zance na daban, Haba ina impossible ace guy kamar ni a fara kirana baba kuma Abba Haba baxai yuyu ba,gaskiya ba yanzu ba zuwa nan dai da 5 years haka".

Kallon sa k'ir sweety keyi can tace " yanzu Broth duk tarin baby's d'in da nake gani tare dakai daman duk ba sonsu kakeyiba?".

" hhhhmmm gaskiya ke yarinya ce kawai don kina ganina da emmmata kuma duk saisu zama ina sonsu? Lalle da sauranki, To duk yaran da kike gani girls friends d'ina ne kawai,guda d'aya ce kawai cikin su Fadlah y'ar k'asar nan ce da muka had'u da ita a can take nacemin sai munyi aure,to itama bawai auran nata zanyiba amma duk dai tsarinta yaimin don ta had'u babbar girl ce ko ina tayi gata educated gata so beautiful, gata gentle babyn tayi kawai don ba aure zanyiba da ita zan aura".

Dammm gaban sweaty ya buga don tasan za'a sha wahla matuk'a kafin a daidaita dashi akan Khadijah, jitai duk zaman ta gun ya isheta don haka ta mik'e tsam tana fad'in "broth bari in kwanta na gaji".

" OK good night " kawai yace bai d'ago ya kalleta ba.

Tana shiga d'aki ta fad'a gado zuciyanta fal tunani.

Shikuwa Nan ya zauna yana tunanin me yasa akeso yai aurene,to yama gano dabara daman so yake ya juya inda ya fito don shi bai tunanin zuwa yanzu zai iya zama a Nigeria zaman waje yafi komai dad'i a gunsa kayi rayyuwarka bamai sama ido, don haka bari gari ya waye ma yajewa Abbansu da wannan maganar.


❀❀❀

Readers mu masoyanku ne tunda munayi don ku, amma Ku duk yanda kuka rik'emu babu damuwa,Masoya da mak'iya duk muna alfahari dakuπŸ˜…
❀❀❀



Taku ce
Y'ar mutan j'aoji.πŸ™‹β€β™€
https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation?

🍑🍑🍑🍑🍑🍑🍑🍑
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
🌸 *Y'AN ARABIC* 🌸


NA

LAYUZA KABIR ADAM

DEDECATED TO ALL
ARABIC /ISLAMIC STUDENTS
πŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“š

πŸ‘¨πŸ»β€πŸ’»πŸ‘©πŸ»β€πŸ’»
*ZAMANI WRITERS ASSOCIOTION*

πŸ“
​​WΙ› Ι‘Κ€Ι› Ι¦Ι›Κ€Ι› tΡ³ Ι›Ι—ucΙ‘tΙ›, MΡ³tiΡ΅Ι‘tΙ› Ι‘Ι³Ι— Ι›Ι³tΙ›Κ€tΙ‘iΙ³ Ρ³uΚ€ ʀɛɑɗɛʀร​​

β€‹πŸ“š β€‹β€‹πŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“š


πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡
JINJINA GAREKI MY NASMAT INA TAYAKI MURNAN KAMMALA NOVEL D'INKI (Y'AR GWAGWARMAYA) HAK'IK'A MUN ILIMANTU MUN FAD'AKANTU KANA MUN NISHAD'ANTU DASHI,ALLAH YA K'ARA BASIRA SIS NASMAT
UP
UP
UP
ZAMANAWA KUNAYI MUNA JIN DAD'I πŸ’ƒ
πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡

0⃣1⃣8⃣


Da sanyin safiya Daddy(UK) ya tadda mahaifinsa a turakarsa zaune yana kallon labarai a BBC, waje ya samu ya zauna cikin girmamawa ya gaisheshi,cike da fara'a ya amsa mai yana k'ara tambayarshi ya sauran gajiya,ya amsa da babu tare da k'ara tank'washe k'afa ya fara magana cikin nutsuwa da lankwasa kai " Abbah daman wata magana na k'ara zuwa da ita,amma ina fatan samun had'in kanka kamar yanda ka saba bamu had'in kai a dukkan wasu lamuranmu".
Gaba d'aya Alhj Usman ya tattaro hankalinsa ga d'an nasa yana cewa "OK ina jinka Babana fad'i abinda ke tafe dakai".

" To Abbah daman kan karatuna ne,a school d'inmu sun bamu scholarship mu goma a matsayin way'anda mukafi kowa k'ok'ari a wannan shekarar cikin duk school d'in, kan cewar mu zauna dasu mu k'ara wata goma sha biyar mu k'ara wani course, duka kan business don zasu bud'e company a nan gida Nigeria k'ark'ashin school d'in to suna son mu kasance ma'aikata na farko da zamu fara aiki companyn kuma y"an Nigeria d'in suke so, daga bisani in mun gama course d'in sai ai bikin yayemu sannan mu taho tare dasu a bud'e company mu kasance wakilansu anan Nigeria".
Shiru yai yana tsimayin abinda Abban nasa zaice,
Tsawon lokaci bai magana ba daga bisani ya nisa yana fad'in "Daddy nah naji dukkan batunka kuma nayi matuk'ar murna daka kasance cikin zakarun shekara a school d'inku, wannan babban abin farin ciki ne a garemu baki d'aya, sannan naji dad'in course d'in da zaka k'arayi kan business don karatu ko wane iri ne baya yawa, amma wani hanzari ba gudu ba Daddy nah akwai abu me matuk'ar mahimmanci a gabanka kafin wannan, Wanda shine zai shiga tsakaninka da wannan k'udirin naka".

Da sauri UK ya d'ago ido cikin fargaba yana duban mahaifin nasa bakinsa har rawa yake yana furta " Abbah Abbah meye abinda zai shiga tsaka nina da wannan babban cigaban da zan k'ara samu?".

Cikin rashin damuwa Abban nasa yace " Aure, Aure nake so kayi Daddy nah, auran nan shi kad'aine cikar mutuncinka shine Zaisa ka k'ara nutsuwa kayi cikakken hankali Abbah nah".

A kid'ime yake fad'in " Aure Abbah? Aure fa kake cewa,haba Abbah har nawa nake da aure zai min shigar sauri haka Abbah, wlh Abbah babu aure a tsarina nan kusa,don Allah kamin afuwa ka bar maganar nan ka barni in koma in k'ara samo ci gabana. . . "

Ganin duk yanda ya kid'ime yasa Abban nasa sassauta murya cikin sanyin rai ya fara magana " Daddy nah meya kid'ima ka haka? Maganar auran kawai shine ka tada hankali, haba mana Baba na shin ka manta aure shine cikar mutuncin ko wane d'an Adam ka manta aure sunnar manzon Allah ne, mu ba auran mukai muka haifeku ba? to haka nakeso kaima kayi auran ka haifamin jikoki,ina son ganin iri daga gareka Abbah nah,ina so ace nima yau ga Baba nah ya zama babban mutum, ka kwantar da hankalinki kaji indai don rik'on company ne zan baka guda cikin company nah ka rik'e shi kyauta ma in kana so,nidai burina kayi auran kaji Daddy nah".

Girgiza kai ya shigayi yana had'a hannaye alamar neman agaji yana fad'in "help me my hero help me,kamin rai wlh ban shirya ba ni yaro ne Abbah ban kaiba wlh,ina zan kai mace ni yanzu da k'uriciyata".

Cikin takaici Abban yace " kai d'inne yaro ko ? Shekara talatin harda d'aya kake kiran kanka yaro saiba iya shege, duk y'an matan da kake kulawa daman ba auransu ka shirya ba yaudararsu kawai kakeyi ko, to yau anzo k'arshen shirmanka, don haka kasa aranka Aure ba fashi matuk'ar ina numfashi".

"Wlh Allah Abbah duk y'an matan nan wlh duk friends d'ina ne ni ban tab'a cewa ko waccansu zan aureta ba, kawai su suke haukansu,Abbah ka taimakeni ".

Gyaran murya yai kana ya daidaita zamansa yana cewa " Abbana kwantar da hankalinka ka fahimceni,ni na riga da na zab'a maka matar da zaka aura domin na yaba hankalinta da tunaninta,yarinyar tanada nutsuwa da kamun kai irin matar da kowane namiji ma'abocin hankali yake fatan samu to irinta na sama maka babana, gata na gaba da zanmaka a rayuwa kenan tunda na baka ishashshen ilimi Wanda duk inda ka shiga dashi ka wuce raini,to gashi na zab'a maka mace ta gari abokiyar rufin asirinka,ina Neman had'in kanka Babana akan auran kaji".

Tunda Alhj Usman ya fara Wannan maganar UK ya shiga comma ta d'an lokaci duk sai yaji kansa baya aiki brain d'insa ta tsaya cak,

"Ko baka jinane inata magana kai shiru".
Maganar Abban nasa ya katseshi,

Da sauri ya d'ago idonshi cike da hawayan tashin hankali ya rarrafa ya rik'o k'afafun sa ya fara magana," kaimin rai mahaifina ka taimaki rayuwata ka ceci farin cikina don Allah nine fa Daddynka Abbah nah baka tab'a yimin abinda bana soba baka tab'a yimin dole ba a rayuwa,komai da nakeso shi kakemin amma gashi yau zakamin auran dole, auran dole fa mata akeyiwa Abbah, matan ma marasa gata amma Abbah ni namiji D'an gata za'a yiwa auran dole,kamin rai Abbah na".

Cikin tarin takaici yace "tashi kaje d'akinka Daddy naga kanka ba dad'i naga tunaninka ya tsaya cak, jeka inka samu nutsuwa ka dawo muyi magana amma tabbas ba fashi indai ina Raye da izinin Allahu sai anyi Wannan auran".

Cikin layi da tangad'i ya wuce d'akinsa,kwanciya yai kan fadonsa idanuwansa na nuna mai komai biyu biyu, a haka bai san iya adadin tsawon lokacin daya d'auka ba a kwance anan".


*******
Tsawon kwana biyu gidan ba dad'i don Sam Alhj Usman ya d'aure fuskarshi yak'i barin kowa yazo mai da wata magana akan wannan lamarin,don Aunty murjah tana ta zuwa da zancan amma sai ya d'aure fuska yace tabar mai wajan bai son wata magana data shafi Daddy.

Shikuwa b'angaran UK yana ta fishi ko abinci bai fitowa yaci sai dai Sweety ta kai mai d'aki,duk ya rame yayi fici fici dashi, shi tunaninsa yanda Abbansu yake bala'in son su yasan in yaga ya shiga damuwa zai janye k'udirinsa,amma abin mamaki sai yaga har tsawon kwana takwas Abban bai nemeshi ba,kuma basu had'uba ko sau d'aya don tun daga ranar da akai case d'in bai fito daga d'akinsaba ko salla ma sai dai ya had'ata yayi don dama ba wani damuwa yayi yayita akan lokaci ba balle har yashiga jam'i.


Sweety kuwa duk k'aunar da takewa d'an uwanta bata damu da halin daya shigaba tasan in yayi fishinsa na d'an lokaci zai bari, don kuwa wlh a zahiri da bad'ininta take son wannan auran.

Abbah fa abin ya fara damunsa don rashin ganin d'an nasa yana damunsa,har sama da sati yana k'ulle a d'aki, gashi Aunty murjah tana fad'a mai kullum Daddy fa ramar tashi tayi yawa sai ya nuna mata bai damu ba amma cikin ransa yana jin babu dad'i amma dai dole ya daure a wannan karon ya fiddaa damuwar Daddy daga ransa.


****
Yau ummu sulaim tazo gida tana zuwa taci karo da halin da D'an uwanta yake ciki hankalinta ya tashi matuk'a nan taita kwantar mai da hankali " Haba Broth sai kace mace zaka zauna cikin damuwa haka, kaga yanda duk kamanninka suka canja,don Allah ka kwantar da hankalinka ka gane gatan da Abbah keson yi maka, kasan dai mahaifinmu bazai tab'a cutar damuba, don haka kasa a ranka zakayi mai biyayya sai Allah ya sanyaya zuciyarka".


Cikin kalan tausayi yace "kin San kuwa illar da Abbah yake son yimin, yanzu fa zab'armu akai mu goma za'a k'ara mana wani course akan business sannan a bud'e mana company a nan Nigeria, don Allah duk ba d'aukakarmu bace,amma sabida wannan auran daya k'udura a ransa yace bazan koma ba,wlh tun

Please Login or Register in order to submit comment