Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

a hankali, shima ajiyar zuciya yake saukewa a hankali muna nan zaune aka fara kiran fasinja da sauri na fad'a jikinsa ina sakin wani marayan kuka, bubbuga bayana yake a hankali yana fad'in "kiyi hak'uri kinji insha Allah very soon ina nan tafe nima".

Ganin fasinjoji nata shiga jirgi yasa ya kama hannayena zuwa gaba dai dai inda ya dace ya tsaya anan ya tsaya yana janyeni daga jikin sa, hannu yake d'aga min yana wani mirmishin yak'e kawai sai naga hawaye na tsiyaya daga idonsa a haka muka rabu idanuwan mu na zubda hawaye.










Taku ce
Layuza kabir AdamπŸ™‹β€β™€
🍑🍑🍑🍑🍑🍑🍑🍑
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
🌸' *YAN* *ARABIC*🌸


*NA*
*LAYUZA* *KABIR* *ADAM*


_DEDICATED_ _TO_ _ALL_
_ARABIC_ / _ISLAMIC_ _STUDENTS_
πŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“š

πŸ‘¨πŸ»β€πŸ’»πŸ‘©πŸ»β€πŸ’»
*ZAMANI* *WRITERS* *ASSOCIATION*
πŸ“
_We_ _are_ _here_ _to_ _educate_ , _motivate_ _and_ _entertain_ _our_ _Reader's_





0⃣4⃣5⃣


Ko acikin jirgin idona bai bar zubda hawaye ba,zuciya cinkushe da rashin sukuni,wata dattijuwar balarabiya da take zaune gefena ganin datai idanuwa sun kasa tsaida hawayan ta kamo hannuna cikin hard'ad'd'an larabcinta na gargaliyya take bani hak'uri wai inyi shiru, jan hanci nai tare da share hawaye na ina gyad'a mata kai alamar na bari.


Tsawon awannin da mukai cikin jirgin ina duniyar tunanin da kewa.


Ina fitowa cikin jirgin na hango sweety tanata mirmishi tare da d'ago min hannu, cikin tsananin farin ciki na k'ara sa muka rungume juna, kallona ta tsaya yi tana dariya tace "Aunty na kece kuwa anya banyi b'atan kaiba".

Dungure mata kai nai nima cikin dariya nace " a'a bani bace sai ki duba cikin jama'ar wajan ko zaki ganni".


Dariya mukasa baki d'aya ta kamo min kayana drivern daya zo da ita ya k'araso ya d'ibar mana kayan yasa a mota, bayan mun shiga ta zuba min ido cikin tsokana "wlh Allah bikiga yanda kikai wani masifar kyau ba Aunty nah,Allah Wanda bai miki farin sani ba bazai ganeki da wuriba".

" kai don Allah ki daina ni banga wani canjawa danai ba".

Mirmishi tai tana fad'in "zakiji maganganun mutane zaki tabbatar da magana ta".


Nidai dariya kawai nake,a haka muka k'arasa gida Aunty murjah muka samu tsaye ta taremu cikin farin ciki, don haka kai tsaye sashin su na wuce,muka gaisa cikin farin ciki Aunty murjah take min sannu da zuwa,ruwa da lemo sweety ta kawo min nasha, nan Abba ya fito shima cikin fara'a yakemin sannu da zuwa,cikin jin kunya na sauka kan kujerar nake gaidashi zama yai yana amsa min da dariya kan fuskar sa ca yake " Sannu da hanya mutanan India ,ya kika barosu".

"Lfy qlau Abbah na sameku lfy".

" lfy qlau Khadeejah ga sweety nan tai kewarki kullum maganar ki".

Dariya nai ina kallon ta ta d'age min gira,
Mun d'an tab'a hira Abba yace "jeki ki huta Khadeejah anjima kyazo muyi hirar jeki huta kiyi salla kici abinci".

Mik'ewa nai sweety ta biyo bayana tana cewa y'an aikin gidan su kwaso min kayana, ina shiga na tadda sashin a gyare tsaf sai k'amshi ke tashi, jiyowa nai inaiwa sweety alamar jinjina nace " sannu da aiki sweetyn mu"

Dariya tai tace "bari a kawo miki abinci kafin ki fito a wankan".



Kai tsaye na shige toilet d'in nai wanka na d'auro alwala, bayan na fito nasa simple doguwar riga nai salla sannan na dawo parlourn na tarar an shirya min abinci kala kala zama nai nad'an tsakuri kad'an naci don baccin da nakeji ya kama idona,sabida kwana bana samun wani bacci,ina hawa gadon kuwa bacci yai gaba dani.


Cikin bacci narink'a jin ringing d'in wayata da k'yar na bud'e ido na jawo wayar ganin sunan Wanda ke kan wayar yasa da sauri nai picking d'in kiran,
" Baby nah"

Shagwab'e murya nai kamar zan kuka nace "ummmmm Reality nah'

" ina kika shiga nake ta nemanki baki d'aga ba".

"Bacci nake fa,ya kk ya kewana".

" gani nan ba yanda nake Khadeejah kin tafi da sukuni da walwalata tunda na dawo daga rakaki ina kwance zazzab'i ya rufeni sai yanzu na samu ya sauka na tashi nai salla, kin samesu lfy yasu Abba ".

" duk lfynsu qlau,amma honey kaci abunci kasha magani".

"Khadeejah ban San Abincin ko kad'an maganin wannan zazzab'in kuma bani da maganinsa yana gareki kin tafi dashi".


" kayi hak'uri kaji don Allah kaci abunci ko kad'an ne kaji inba haka ba ciwo zaima yawa ga damuwa,wlh nima jina nake wata iri ban jin dad'in jikina da zuciyata,kewarka duk ta dabaibayeni".


"Hhhhmmmm baby ke ki nama iya fad'a wlh ni yanzu banma San halin da nake ciki ba Sam babu walwala tare dani cikin yini guda na fice hayyacina balle tsayin watanni ya zanyi".

Rarrashin sa na shigayi ina mai kalamai masu dad'i har ya sake mukayi hira sosai cikin so da k'auna ".




************
Washe gari sai ga Aunty Hafsa da yara murna kamar nace me, na rungumota ina fad'in" Oyo yo my Aunty itama cikin farin ciki ta ruk'oni muka zauna tana rik'e da baki tace "a'a Nanah wannan kyau haka har ina,lalle India ta amsheki".

Dariya nai nace " kai Aunty kema haka zakice ni kan banga wani canji ba".

"Ai ke bazaki gani ba,amma masha Allah".

Gaisawa mukai cikin farin ciki,su Ashraf ma suka gaisheni na kamo su jikina ina fad'in" wayyo yarana sun girma fa,Aunty me kike basu haka ".

Dariya tai tace " hhhhmmmm tsayi ne irin naku suka d'ebo gashi nan sunata yi".

Dariya nai nasa su a jikina "ai mun muki wayo Aunty yara sunyo family d'in su,Aunty ina Aunty Amrah".

" hhhmmm Khadeejah Amrah ai tai nauyi ta daina fita don yanzu kwana biyu ma nak'uda take a tsatstsaye wancan satin ma sai da mukaje Asibiti".

"Ayya kice ta kusa sauka,Allah ya raba lfy".


Ameen ya Allah, ai badan wancan cikinma ya lalace ba ai da tuni yaro ya fara zama,wlh tana shan wahalar cikin nan sosai, gashi Usman sam ya hana ta tafi gida shi ba a gari yake ba amma yace bazata wankan jego ba wai k'auyanci ne,shine yasa aka kawo innar ta take zaune da ita".


" wayyo harta ban tausayi wlh".


"Hhhmmm kema haka zaki kawo mana Baby soon".

Zaro ido nai ina cewa " Aunty rufamin asiri don Allah ".

"Hhhmmm kyama fad'a".



Tashi nai na kawo musu lemo da ruwa, duk inda nai Aunty bina take da ido tana fad'in " masha Allah Nahna kin canja sosai wlh ".

Nidai sai dai inyi dariya kawai,hira sosai muke da Aunty Tace bari ta shiga su gaisa da Aunty murjah, hijab d'ina nasa na rakata , tarb'a ta kirki ta mata kamar yanda suka saba,bayan sun gaisa suka d'an tab'a hira sannan muka taso,Aunty murjah tace " Khadeejah karfa ki wahalar da kanki ga girki nan an had'a daku anan ".

"Tom Aunty mun gode Allah ya saka da alkairi".


Da muka dawo shashi na na fitowa da Aunty tarin tsarabar dana zo da ita nace ta tayani fitarwa kowa, kallona tai tace " kamar wadda kikaje saudiya wannan tsaraba haka".

"Hhhhmmmm Aunty wlh nai nai ya barta yak'i haka yaita min siyayya kamar me".

D'an mirmishi tai tace " zama yai dad'i kenan ".

Dariya kawai nai na shiga fiffitar da kayan, Yaya na na fitarwa tsaraba sama data kowa sannan Aunty Hafsa don akoda yaushe su nake kallo gurbin iyayena, sannan na d'aukarwa Abba riga da wando na Pakistan tunda naga yana sosu, Aunty murjah ma doguwar riga guda biyu sai turaruka ,su khamees ma Riga da wando su biyun,mutinyata sweety kuwa siyayya bata wasa ba daman muka mata, sai Aunty Amrah ma na ware mata nata,kowa dai na ware mai abunda ya dace dashi , wata jaka na zuge na zazzage kayan ciki Aunty tabini da ido ganin uban yawan kayan yasa ta kalleni tace " Nahna har an fara siyan kayan Baby hhhhmmmm mun kusa samun Baby kenan".

Kunya ce ta rufeni nace "a'a wlh Aunty kanti muka shiga naga kayan sun min kyau shine na siyo in anyi haihuwa sai in rink'a barka dasu,kuma kinga ga Aunty Amrah ma akan hanya ".

Mirmishi kawai tai tabar zancan can k'asan ranta kuma tana fad'in" Ai daman da ganin wannan kyan ai nasan An samu".



Bayan munyi sallar azahar sweety ta shigo me aiki na binta d'auke da kulolin abinci, D'an hararanta nai nace " ko lek'oni bikiyi ba tun safe da kika fita ".

Dafe kai tai tana dan mirmishi" wlh Auntyna yai d'in ne sai a slow ina jin wani iri ne,da dare ai muna tare sorry ".

" OK sannu ".

Juyawa tai ta fita na d'auko mana babban tray na had'a mana abincin harsu Ashraf, muna ci na kalli Aunty nace " Aunty harna tuno gida wlh yanzu kuwa mutum yaita cin abinci shi kad'ai ".

Dariya tai kawai taci gaba dacin abincinta.




Bayan sallar la'asar Aunty na shirin tafiya yaya ya kirata a waya wai tai sauri ta wuce asibiti Amrah nacan ".

Da sauri ta lalibo mayafinta tana cewa " Nahna bari in wuce asibiti su Amrah sun koma,bari nabar yaran nan driver zaizo ya d'auke su ".


Ganin yanda Aunty ta rikice nima duk sai hankalinsa ya tashi, fitowa mukai tare naga direbobin gidan duk zaune guda d'aya na kira nace yakai Aunty Private hospital sabon gari.




Tunda ta tafi minti kad'an nake kiran Aunty a waya tace to inta addu'a dai,duk jikina ya k'ara sanyi.

Bayan magriba akazo aka d'auki su Ashraf, har sallar isha'i shiru,ina zaune a d'aki bayan idar da sallata ina azkar naji ringing wayata da sauri nakai ido kan wayar sunan yaya na dana gani yasa na d'auka da gudu gudu gabana na fad'uwa ina d'aga wa nace " yaya ta haihu?.

"Alhamdulillah Nahna Amrah ta haihu an sami Namiji".


"Alhamdulillah masha Allah, yaya amma duk suna lafiya ko".
" eh lafiyar su qlau ana gyarasu tukun".



Muna kashe wayar na kira Yaya Usman ina fad'in "Yaya congrat Allah ya raya mana Baby boy yai mai albarka".

Cikin tsananin farin ciki yake cewa " Ameen Ameen sweet sis yanzu yaya Haroon yake fad'a min ta sauka an samu Baffa ".

" wayyo Allah Baffana kasa yaya Allah ya raya mana yasa yai halin me sunan".

"Ameen Nahna insha Allah gobe ina hanya ma".

" To Allah ya kawoka lfy ".

Bayan na kashe na kira Honey nah bugu d'aya ya d'aga "my beauty one".


" na'am honey Aunty Amrah ta haihu ta Haifa mana d'a namiji sunan sa Yusuf sunan Baffan mu ".

" Alhamdulillah Allah ya raya Baby daman ke yake jira ya fito ko".

Dariya nai "eh mana Ashe tun wancan satin take labor Allah yayi ina gida zata haihu, Honey kamar in tafi yanzu wlh".

" A'a kiyi hak'uri da safe sai kije kinji ".

" Tom Allah ya kaimu ruhina,daga nan muka shiga hira ".


*************
Washe gari kuwa k'arfe goma na gama komai na shiga na gaida Abba nake sanar mai haihuwar Barka yai yace in naje inyi musu barka,Aunty murjah ma tace in yiwa su Aunty barka kafin tazo, ita kuwa sweety daman ta tafi school.


A mota ta na tafi cike da d'oki ina addu'ar Allah yasa in samu yaya na a gida duk da munyi waya yace bai fita ba.


Ina tsayawa k'ofar gidan mu naga yaya na fitowa da motarshi,da sauri nai parking na fito shima ya ganni don haka ya fito cike da farin ciki k'arasawa nai fara'a kan fuskata ina fad'in "yaya da ban k'araso yanzuba kenan tafiya zakayi bamu had'u ba.

Dariya yai yana rik'o hannuna yace " To Allah yayi zamu had'u yanzu ko mu k'ara sa gidan.

Sosai yaya na ya nuna farin cikin ganina bayan mun gaisa yake k'ara tambayata hanya da India na amsa mai da duk Alhamdulillah, sama sama muka tab'a hira sabida zai fita ana jiran sa,yai min godiyar tsaraba ya tafi, mota ta naje na k'ara gyarawa parking sannan na d'auko jakar kayan Babyn da nazo dashi, nunawa Aunty nai kaya set goma dana zab'owa Baby boy d'in masu masifaffan kyau ,Aunty taita min godiya,nan na tayata k'arasa aikin gidan tai wanka muka fito zuwa gidan mejegon dake tun jiya da daran aka sallamesu.



Da d'an ihuna na shiga gidan ina fad'in "Ina Baffa na ayi sauri a mik'omin shi".

Dariya duk akasa don gidan cike yake da dangin Aunty Amrah,

Masha Allah na fad'i lokacin dana d'auki yaron,sak kamannin sa na y'an gidanmu ne har bak'ar fatar manyan ido da cikar gashi kana ganinsa kaga tsatson Alk'adi Yusuf na rungumeshi jikina ina fad'in" Yaro yayo kaman Danginsa yayo takwaran sa sak, Dariya Aunty Hafsa tai tace "wlh ana haifar sa nace kamar Ashraf yana jinjiri babu abunda ya rabasu".

Wata mata dake gefe tace " Ai gaskiya Khadeejah kunada k'arfin jini Ku duk danginku kaman ninku d'aya ".

Dariya nai " Aimu y'an baiwa ne"
Duk aka d'au dariya nan muka gaggaisa da y'an d'akin mukai wa juna barka, matsawa nai jikin Aunty Amrah ina tsokanan ta cikin raha "Aunty na yadai akwai wahala ne abar naga duk kinyi wani kala".

D'an gyad'a kai tai irin zaki Sani d'innnan tana mirmishi, k'asa tai sosai da murya yanda bamai jin me muke fad'a tace " Tace Wlh zaki d'and'ana yarinya in za'a samu akwai dad'i amma wajan haifowa sai kin kusa mutuwa kima shirya ".

Zaro ido nai nace "kice ba sauk'i?".

Cikin dariyar mugunta tace " wlh ba sauk'i I ciwon arne,balle kinje in had'u da miji kinsha dad'i Allah yasa kin d'auko ciki ".

Da sauri na rufe bakinta mukasa dariya gaba d'aya, kallon mu duk sukai don basu San me mukewa dariyar ba, sai na fuske ina jawo jakar kayan dana kawo na mik'awa Auntyn ta , ana bud'e wa aka shiga yaba kyan kayan guda goma zafafa dasu,nan aka shiga godiya sai kuma hira ta b'arke,ita kam Aunty Hafsa tashi tai ta shiga kitchen don yin aiki da d'ora girki tunda gidan bak'i nata zuwa, janye Aunty Amrah tai tace zatai bacci ta shige d'aki binta nai muka zauna muna hira tana k'ara ban labari kan ciki da wahalarsa uwa uba ciwon nak'uda,jin haka duk sai jikina ya mutu ta kalleni tana dariya tace " kin shiga yana yi ko,kinsha dad'i a India zaki gane kuranki a Nigeria in haihuwa tazo".

Kasancewar babu kunya tsananin da Aunty Amrah ba kamar Aunty Hafsa ba don ita gurbin uwata na d'auketa tunda ta rik'e ni tun daga yarinta,ita kuwa Aunty Amrah kusan sa'a muke da ita shi yasa ban damuwa hirarmu muke kwasa irinta mata,
D'an janye ido nai ina fad'in "Allah Aunty Amrah ba komai fa cikin satin da zan taho nai wanka ".

Dariya tai tace " Tunda kikai wankan baku k'ara had'uwa ba kenan?"
Kallonta nai ina d'an mirmishi nace "um um ,ai satin duka muna manne ma ".

Dariyar mugunta tai tace " Allah yasa kin samu cikin satin ma".

Gabana ne ya fad'i, sai kawai na murmusa, Cikin raina kuwa ina tunanin yanzu ace inada ciki ya zamu kaya da umar mutumin daya nuna min kai tsaye bai son haihuwa yanzu,shida yake tunanin shekara biyu nan gaba sannan in samu ciki, lalle in ciki ya samu a yanzu zaman mu ya shiga garari ban San makomata a gunsa ba .

D'an tab'oni tai tace "ke har kin fara tunanin nak'udar ne".

Dariyar yak'e kawai nai na bar hirar.



Sai yamma lis muka bar gidan nida Aunty Hafsa gida muka koma bayan nai sallar magriba naci abinci sannan na wuce gida.




******
Shirye shiryen suna aka shiga ba zama,dake Baban boy ma ya dawo sai farin ciki yake da samun Babyn sa,yanda naga yana rawar k'afa da farin cikin wannan haihuwar sai abun ya birgeni, nace jibi yanda yaya Usman ke murna Allah ya bashi d'a amma mijina yana neman tsari da ita yana rok'on Allah ya nesanta mai rabo a kusa, duk sai naji damuwa ta lullub'eni, na fara nemawa kaina mafita tunda wuri don wlh Allah inya dawo yacemin zai min abunda zai hanani haihuwa sai dai in ya daina kusanta ta.





********
Ana i gobe suna y'an garinmu suka zo da yawan su,kowa da alkairin sa don a dangin mu in dai akaiwa Baffa takwara to yaron zai sha hidima matuk'a haka Ashraf yasha wannan gatan, duk da da wuya kaga wani d'an gidanmu me aure mace ko na miji in dai mutum nada y'aya maza sai ka samu me sunan Baffan mu, haka sauran gidajan dangi suke wa Baffanmu takwara tun yana raye har zuwa yanzu.


βž–βž–βž–βž–
D'inkuna nai mana nida Aunty Hafsa da Aunty Amrah kala biyu biyu wani tsadaddan less ne na mana da Atamfa supar duk iri d'aya na bayar akai mana d'inki don kowa nasan measurements d'inta, sannan nasai mana mayafin da zai hau da less d'in.

Yaya na da yaya Usman ma,duniyar yadi ba shiga na sai musu yadi goma goma kala d'aya na bayar awajan a musu d'inkin babbar riga da y'ar ciki ,haka na siyawa su Ashraf suma na bada a d'inka musu,
Banda matsalar kud'i yanzu kudin da suke account d'ina sun shallake tunanina don kullum mijina da Abban sa cikin samin kud'i suke,don haka naga banda wata matsala sai dai inta yiwa y'an uwana hidima dasu.



Bayan zuwan y'an Sakkwato da dare muna zaune gidan mu anata hidima nan aka shiga fiffito da kayan barkar da za'a kai gidan su Amrah kamar yanda al'ada take kowa ya bada abunda yazo dashi wasu rigunan baby wasu turmin atamfa wasu Shadda, ni kuwa Pampas ma me d'ari na siya na sai set d'in kayan wanka na k'ara rigunan baby guda biyar na saka turmin atamfa da shadda yadi goma, don wancan kayan dana kai bai cikin kayan danginmu nawane daban danai niya, wannan kuwa daman nasan dole kowa a cikin dangi zai bada abunda Allah ya hore mai, akwatina aka cika da kayan barkar da safe iyayen mu da yayyan mu zasu kai, kowa yaga hidimar danai sai yamin godiya dasa albarka,nikam mirmishi kawai nake don banga amfanin samun da bazakayiwa danginka ba.




Ranar suna kamar yanda yaro yaci Suna Yusuf za'a rink'a kiransa Baffah munso mu samai lak'ani na y'an gayu me ma'ana amma Yaya Usman k'emagadai yace Baffah yakeso a rink'a kiran yaron don zaifiji aransa cewa sunan Baffan namu yaci da gaske, haka kuwa kowa ya d'auka Baffah Baffah, anyi sha'ani anyi bidiri sosai suna yai armashi mun cakare mun d'au wanka anga munsha anko da matan yayyane na sai kuma matan yayyanmu na can Sakkwato suka hau k'ananun maganganu da nuna facalanci mu kuwa ko kulawa bamuyi ba don mun tara jama'a hidimar su ce a gaban mu,ga dangin mijina Aunty ummu sulaim da Aunty murjah ga sweety, sannan ga friends d'ina duk na gayyata, haka akasha bikin suna aka watse, duk a gajiye nake nai wanka na fito a d'akin Aunty Hafsah wayata nata ringing Aunty ta mik'omin tana fad'in "Tun d'azu mijin ki ke kira kin zamanki a toilet".

Karb'a nai ina mirmishi na kara wayan a kunnena " Jin kalmar farko daya fad'a yasa na fara bubbuga k'afa zanyi kuka, "Don Allah son Allah honey kai nefa kace kwana biyu zanyi yaufa akai sunan,gashi duk dangi na nan ana tare kace in tafi gida yanzu,kuma fa dare ma yayi k'arfe tara fa my heart".

K'ara cije Lip's d'insa yai daga can b'angaran yace " Deejah nah tunda akai haihuwar nan kin rage bani kulawa kullum kina gida da rana bama samun waya da dare kuma kiyi saurin bacci wai kin gaji, kin dan halin da nake ciki kuwa?"
Zama nai gefan gadon jin yanda muryan sa ta canja, Allah yasa na kowa a d'akin na k'ara k'asa da murya "Kayi hak'uri kaji mijina zuciya ta nasan kana daurewa ka k'ara insha Allah wata rana muna tare babu abunda zai rabamu kullum kullum ina cikin jikin ka ina wasa da abuna ko?"

Numfashi yaja yana matse k'afarsa yace "Deejah nah! Ina cikin halin da nake neman d'aukin ki kinsan dai halin da nake ciki kin San me nake buk'ata a irin wannan yana yin, gashi kina cikin mutane babu damar ki kwantar min da hankali yanda nake buk'ata shi yasa nace ki koma gida ki kula dani".

Rik'e kaina nai ina tunani shin ina zan kwanta ni kad'ai in kula da mijina muyi waya wadda yake so muyi in fad'a mishi duk kalan kalmomin da yake so in fad'a mai da zasu rage mai tsananin sha'awar dake tare dashi,k'ara d'aga ido nai na kalli agogo lokacin tara da minti hud'u a hankali nace " Ina zuwa ka ban y'an mintina kad'an kaji ".

Kashe wayan nai na tashi na bud'e jakata doguwar riga nasa na yafa mayafinta ko mai ban tsaya shafawa ba na d'auki key d'in mota ta da wayoyina na fito parlour Wanda yake damk'am da jama'a , kowa bina yai da kallo na k'ok'aro mirmishi ina zama gefan kujera yayin da Aunty Hafsa ta cillo min tambaya " ina zaki naga kin d'auko key?"

Dafe kai ne irin da matsala d'innan nace "gida zanje yanzu Umar ya kirani wai akwai wata takar da a d'akin sa in dubata akwai cord ajiki in tura mai zaiyi amfani dashi a skl d'in su kuma yanzu ake so ya tura,shine zanje in duba in tura mai in dawo".

Caraf Aunty juwairiyya tace " a'a auta in kin tafi bazaki biyo dare ki dawo ba kiyi kwanciyar ki da safe sai ki dawo muyi sallama in zamu wuce,yaushe zaki tafi yanzu kuma ki zauna duba takarda har ki tura mai ki dawo ai sai bayan goma".

Kowa ya d'auka eh eh in kwanciyata kawai innaje".

Mik'ewa nai ina musu sallama na fice.


Na d'au hanya sosai naji kiran ya k'ara shigowa hannu nasa na d'aga wayan tare da sata hand free "hello shimfid'ata me kike ne har yanzu ".

" kayi hak'uri gani akan hanyar komawa gida ne ina driven ".

Cikin mamaki da zumud'i yace "da gaske kike don Allah ko tsokanata ?".

",Allah da gaske bari in k'ara sa tukun".

Kashe wayan yai yana juyi kan gadon nasa a fili ya furta

Please Login or Register in order to submit comment