Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kawai nake yi.kasancewar wajan ba maza sai yara kawai yasa muka cashe abun mu,amarya ta fito na balle bandir d'in kud'i inata mata lik'i itama bud'e pos d'in ta tai ta fiddo kud'i ta shiga maida min martani,ganin haka yasa Aunty ummu sulaim itama tazo tanata mana lik'i ai kuwa sai akai rubdugu cikin filin ana mana watsin kud'i, masa kid'an kwarya fa sun ga abun nema sai suka sake dagewa da sakin sabon kid'a.
Zee ji tai kamar zata mutu don takaici,haushi taje ji in taga family d'in su na nan nan dani kowa sona yake wanda na tabbatar kyautatawar da nake musu ce tasa suke k'ara k'aunata,ita kam takaicinta yanda nake ba y'ar boko ba ba wata me bud'ad'd'an ido ba amma na iya zama da mutane da siye zuk'atan su,(bata san ba anan take ba,iya zama da mutane baiwa ce,kuma hankali da nutsuwa ke sa ka fahimci kowa ka iya zama dashi gwargwadon halin sa)

Tai nisa cikin tunani hassada da kyashi taji an dafa bayan ta,juyowa tai taga waye wata cousin sis d'in ta ce wadda halin su yazo kusan iri d'aya, tace"sis ya kike zaune anan duk son ki da rawa ga jama'a nata cashewa ?".

Yatsina fuska tai cikin takaici tace "A'a filin ba irin namu bane,naga kucakai sun cika wajan".

Dariya Khairy tai yace" Hhhhhhhh nasan kuma da wa kike,wlh karki sa damuwar wannan yarinyar ta hanaki walwala wajan bikin da kika ci burin rak'ashewa".

D'an tsaki tai tace "ke ni wlh fa ko son kallon ta bana yi sam yarinyar nan bata min ba,ai Broz ya tafka asara wlh duk ajinsa ya k'are ga wannan yarinyar".

Rashin abun yi yasa suka ita gulmar su,nikam inata rak'ashewata da walwala banma San suna yi ba.

Sai magriba aka tashi daga kamun.



***********duka gidan nawa muka rankayo da su,ni dai bayan na tabbatar nasa su lami sun ajiye musu duk abun buk'ata sama na haye don yin salla.


Wanka na fara yi sannan na d'auro alwala bayan nai sallar na d'an shafa creem tare da perfumes d'ina, riga da sket English wear nasa wanda suka zauna jikina d'as na sanya hula kan kitson da aka yarfa min tamkar na barebari,don tabarakallah gashi a kaina kam ba'a magana, ganin har lokacin UK bai shigo ba yasa na k'ara sakkowa k'asa, nan na same su sun baje a parlour suna cin abunci wasu na hira,wasu na danna waya,tsallakawa nai kusa da Ikee na zauna ina tsokanar ta" manya gatan wasa ke baki cin abincin ne?".

Y'ar dariya tai da fad'in "Auntyn mu wlh banjin yunwa ne kawai a gajiye nake jina".

" Ayya sannu,to ko ruwa za'a had'a miki me d'an d'umi kiyi wanka,maybe gajiyar zaman mota ne".

Lumshe ido tai tace "Eh yanzu zan yi wankan in kwanta,waya nake son in gama".

Dariya nai da fad'in" hhhhhmmm ashe soyewa ake yi nazo na zauna,bari in canja waje to".

Dariya duk akasa,nan muka shiga hira da labarin yanda kamun yau ya kasance.

Da gudu gudu Sweety ta shigo parlourn tana fad'in "Aunty na Aunty na".

Cikin kulawa nace " ya akai Amarya?".

"Zo sirri ne abun taso mu matsa kar way'annan yaran su jimu".

Dariya wasu suka sa yayin da wata cousin sis d'in tace" Eh lalle yarinya nuna mana zakiyi kin girma za'a miki aure shi yasa kike kiran mu yara".

Gwalo tai mata da fad'in "Eh d'in fa ba yaran bane ku,amma banda Shukrah da Aysha da Ummy su sun girma amma duk ku d'in nan yara ne".

Ni kaina dariya nai ina mik'ewa don jin sirrin me zamu yi, caraff cikin kunnena naji yo wani lafiyayyan tsaki Wanda babu tantama nasan daga bakin wa yake don haka ko juyawa banyi ba sai Sweety ce tace " Wai ke Zee meke damun ki yau duk na ganki a wani cunkushe ?".

Harara ta watsa mata da fad'in "ba case d'in Ki bane wannan".

Tab'e baki Sweety tai ta rik'o hannu na muka haye sama.

Cikin damuwa ta kalleni bayan mun zauna tace " Aunty nah Allah wannan abun da kika bani nasha yana bani matsala fa".

Cikin dariya nace "Matsalan me ?".
Marairaicewa tai da fad'in" Ni gaskiya bazan k'ara shan komai ba Allah, kinji yanda nake jik'ewa kamar me period, gashi sai injini in feelings ko yaushe, har ji nake kamar ana tsankwalina wlh".


Dariya nai sosai nace "To ai shine gyaran mana Sweety, ko yaushe an fi son mace a jita da danshin ni'ima ba abushe k'amas ba,kin ga kayan nan tun daga gun Sis Nasmat y'ar mutan ark'illa sokkoto nasa aka aikoshi,don ko yaushe ina jin yanda y'an group ke zuzuta kyan kayanta,koni danai amfani dasu na tabbatar da ingancin su, don haka karki damu kiyi ta amfani dasu,Allah zaki zama sarauniyar mata a zuciyar Angonki,domin gyara shine mace,ke Sister in low ce dana bud'e miki zancan kin gane".
Na k'arashe maganar da dariya, turo baki tai da fad'in" A'a ni kam basai an bud'e min ba,Wanda ma ake min bita kullum sun isheni,kin kaini group d'in matan aure ma kullum sai lecture suke kin suna karar min da ruwan kai na".

Tare mukasa dariya dai dai lokacin UK ya shigo yana fad'in "Gulma dai ta kusa k'arewa daga ran lahadi, kullum sai Ku k'ule d'aki kuyi ta gulma".

Dariya mukai ita da Sweety ta mik'e tai downstairs,k'arasowa yai ya zauna kusa dani yana matsa cinyata yace" kun bar bak'in Ku a k'asa kunzo kunata gulma,wai me kike fad'a mata ne kullum yanzu na ganku tare kuskus kukeyi".

Kashe mai ido nai nace "Abun sirri ne tsakanin mu oga".

Matse min hannu yai har nai y'ar k'ara yace" Akwai wani sirrin da za'ai da wani bayan wanda akeyi dani,ni dai Allah yasa ba bata labarin ihun da nake cikin dare ake ba,don Ku mata in za'ai wa yarinya aure sai kuyi ta fad'a mata sirrin ku wai don itama ta rink'a yin haka a gidan mijinta".
Serious na koma ina kallon shi nace "kana tunanin ina cikin mata masu bayyanar da sirrin Auransu? Duk duniya babu wani mutum da zan iya shearing sirrinka dashi duk kuwa yanda muke dashi,rashin ilimi kesa mace bayyanar da sirrin kwanciyar auranta ga wata, ban ce ma mata in sun had'u basa wannan hiran ba amma gaskiya yawanci bita ne mu keyi tare da k'ara wayarwar da junan mu kai kan rayuwar aure da matsalolin cikinta".

Numfashi ya saukr yana fad'in" Yawwa hakan ai yafi, amma ka gama shagali cikin dare da safe a bawa k'awa labari ai an tsiraita ka".

Dariya nai kawai ina kauda zancan ta hanyar fad'in "In had'a maka abunci?".

" A'a bari nai wanka tukun".

D'aki muka wuce don na had'a mai ruwan wankan.




______________Washe gari jumma'a da yamma akai fulani show da dare akai dinner, Ranar asabar kuma akai yini wanda shima a gida akai filin Abba, da dare muna zaune tare da amare UK ya shigo parlourn daga bakin kofa ya tsaya yana kira na,yaron Aysha ne a hannu na,ina zuwa ya amsheshi tare da fad'in "Ki kawo min jakan ban dana baki ajiya me ita yazo".

Nace " OK " tare da juyawa zuwa sama.

Gefen kujerar da ba kowa ya samu ya zauna yana wa yaron wasa yace "Aysha Naeem sa'an little ne ko?".

Amsa mai Aysha tai da fad'in" Eh little ma ta bashi sati biyu".

Gyad'a kai yai da fad'in "Da tana raye da tuni itama fa taba tafiya,yanzu shekara guda da wata uku kenan da rasuwar ta".

Sakkowata ne ya dakatar dashi ya k'arb'i jakan tare da mikomi yaron ya fita.

Ban san hiran da sukai ba ni dai bayan na zauna dai naji zee ta kalli Ikee tana tab'e baki da fad'in" Wato sis in baki labari wata ce a group chart d'in mu tai aure tsawon lokaci bata haihuwa ba,bayan wasu shekaru ta haihu sai d'an nata ya rasu kuma gashi mijin nata yanzu bala'in son haihuwa yake, kuma ita ta zama juya don haka mijin harya fara tunanin k'arin aure amma dalilin an shanye shi ya kasa furtawa,wai shine take neman shawara ya zatai,don tasan duk randa aikin da ta ke yi a kansa ya karye tana cikin tasku".

Dariya Ikee tai tace "yo shi aikin asiri duk yanda ta kai ga sabun tashi wata rana zai karye k'ara ma ta barshi yai auran sa tun da wuri ".

Dariya Zee tai tare da mik'a mata hannu suka tafa tace" ai kuwa bari in bata shawarar nan taki".
Kamar gaske ta kunna waya ta shiga dannawa kamar tana typing wani abu.

Ni dai ko yarinya ce nasan dani Zee take,amma ko a fuska ban nuna na fuskanci zancen ta ba,sai Aysha tai k'ok'arin sa musu baki a zanjan nasu da fad'in "To banda abunku ai haihuwa Allah ne ke bada ita,kuma wlh yanzu ma ba kowane namiji ke son haihuwa a kufe a kufe ba".

Tanka musu da Aysha tai ya basu damar jan zancan sukaita yada magana, nikam tunda suke kallo basu ishe ni ba,k'arshe ma tashi nai na bar wajan, d'aki na shiga zuciyata cike da b'acin rai har hawaye suka fara zubomin,sunan Allah nai ta ambata sannan na sami nutsuwa, ina zaune a haka UK ya shigo kallo d'aya yamin ya gane da damuwa a raina bayan ya gama shirin baccin sa tsaf ya hayo gadon yana fad'in" Naga yau sarauta ake ji ko shiryani ma ba'aiba sai ni na shirya kaina".

Cikin k'ok'arin kauda komai daga raina nace"Gajiya ce kawai tare dani ba sarauta ba".

"Wlh kin ga nima cikin gajiyar nake sosai, ai gobe dai da an d'aura aure biki ya k'are".

Zan yi magana wayar sa ta fara Ringing jim yai bayan yaga me kiran naga ya tamke fuska ya d'aga" Hello ina jin ki ".

Ban san me aka ce ba daga d'aya b'angaran naji yace " ke ina taki?".

"OK ina zuwa".

Tsaki ya ja bayan ya gama wayan,ban kalleshi ba nace" ya da tsaki kuma?".

"Wannan yarinyar ce Zee wai in bata aran charger tasa tata yanzu ta k'iyi".

Dummm nai can nace " OK bari in. Bata tawa".

Ina fad'a na mik'e tare da d'ora hijab kan night gown d'in dake jikina.


Tun daga step na biyu na hango idon ta kan hanyar tai tunanin shine,muna had'a ido ta wani d'aure fuska nikam mirmishi na wadata fuskata dashi nace "wace ke neman charger cikin Ku gashi".
Ina fad'a na mik'awa Sweety na juya".







*_Taku ce_*
*_y'ar mutan Ja'oji_*πŸ™‹
🍑🍑🍑🍑🍑🍑
🌸🌸🌸🌸🌸🌸
*'YAN* *ARABIC*
🌸🌸🌸🌸🌸🌸
🍑🍑🍑🍑🍑🍑

*NA*
*LAYUZA* *KABIR* *ADAM*

_DEDICATED_ _TO_ _ALL_
_ARABIC_ / _ISLAMIC_ _STUDENTS_
πŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“š


πŸ‘©πŸ»β€πŸ’»πŸ‘¨πŸ»β€πŸ’»
*ZAMANI* *WRITERS* *ASSOCIATION*
πŸ“
_We_ _are_ _here_ _to_ _educate_ , _motivate_ ,and _entertain_ _our_ _Readers_




*Allah ka dafa mana cikin lamuranmu ka share hawayen mu,ka amsa addu'o'in mu ka tsare mu sharrin mak'iya da mahassadan mu*πŸ™πŸ™πŸ™



~second to the last~




0⃣5⃣7⃣

Bayan na shiga d'akin ban ce mai komai ba na cire hijab d'in tare da hayewa gado,ina hawa wayar sa na k'ara yin ringing ban kalli me yake bama balle in san halin da yake ciki,sai lumshe ido na kawai da nai, ina jin sa yana ta sakin tsaki har wayar ta tsinke,kashe ta yai gaba d'aya ya ajiye kan bed site,tare da matsowa jikina yana juyo dani,"Gimbiya ya dai? ko duk gajiyan ne,bari in miki massaging ".

D'an mirmishi kawai nai ban dai ce mai komai ba,ya shiga mammatsamin jiki yana min tausa, tsawon minti biyar naji yana magana" Wify!".
D'an bud'e idona nai na sauke a kansa ina jiran jin me zai ce" Allah yarinyar nan bata da hankali ko kad'an ".

Cikin nuna alamun ban san da waya yake ba nace" wa fa?".

K'ara jawoni jikinsa yai sosai yana fad'in " Zee mana,wlh bata da nutsuwa, ya za'ayi mutum na tare da matarsa a rink'a ta kiran wayarsa haka? Ba'a san halin da mutum ke ciki ba ayi ta damun sa da kira ana yanke mai hanzari"


Tab'e baki nai cikin halin irin ban damu ba nace"Ita kasan uzirin da yasa ta kira ka ne?".

Wani tsakin ya ja tare da fad'in "Babu wani uziri sai shirme, in da can tana haukan ta ai yanzu tasan ina da aure,tun daga lokacin da nai aure ya dace ta rabu dani,nasha fad'a mata ban da ra'ayin ajiye mace sama da d'aya a rayuwa ta,tunma ban san dad'in auran ba,balle yanzu da nasan sugar d'in da ke cikin sa".

Ya kar'asa da sakar min wani sweet kiss.

Bud'e idona nai sosai cikin nasa tare da fara magana" Ashe daman son ka take? na dad'e da son gano hakan ban gasgata ba sai yanzu daka furta da kanka, amma me yasa bazaka amincewa buk'atar ta ba, tunda jininka ce ita,kaga sai kuyi auren zumunci".

Kafin in rufe baki ya buge min shi, ai kuwa na shagwab'e fuska zan yi kuka, shiru yayi ba tsawon mintina biyu sannan ya ce " karki k'ara had'ani da wata mace da sunan soyayya bayan ke,ban so kinji na fad'a miki".

Ajiyar zuciya na sauke kawai tare da shigewa jikin sa har bacci ya d'auke mu.



********
Washe gari akai d'aurin Aure k'arfe biyar na yamma aka kai amarya gidan mijinta.


Ranar litinin dukkan jama'a kowa ya koma gidan sa.



_A gurguje plsss_
___________________
Bayan wata goma a lokacin ne na samu lecturing a makarantar Koyon shari'a da harshen larabci a nan kano wato legal, abokin Abba ne ya samu Provost a makarantar shine Abba ya nema mana lecturing ni da Sweety a nan,ai kuwa dake yana da ido nan da nan muka sami gurbi,ita sweety English take d'auka ni kuma b'angaran Islamic.

Zuwa lokacin Sweety na d'auke da tsohon cikinta haihuwa yau ko gobe, ni kam harna hak'ura na mik'awa Allah lamarin sa,don na fidda ran ma zan k'ara samun haihuwa.

A tsakanin ne kuma lafiya tak'i wadata gare ni,kullum cikin zazzab'i nake da ciwon kai dare da rana,UK yayi yayi in je asibiti nak'i har wajan sati biyu.

Yau juma'a ko tashi na kasa yi don tsananin zazzab'i, don haka har yayi shirin fita office ya hak'ura ya taimaka min na shirya muka wuce asibiti.
Bincike sosai doctors su kai min nan suka gano ina d'auke da k'aramin cikin wata biyu,kasancewar ni an samin drip ina bacci result d'in ya fito ya sa ban san wainar da ake soyawa ba.

UK ya kasa gasgata me doctor ya ce mai don unexpected yaji zancan, k'ara sa kunne yai yana cewa doctor d'in "doctor me kace ne k'ara maimata min pls"

Cikin dariya doctor ya ce " congratulation Umar Usman Katsina,madam tana d'auke da Unborn Baby na sati takwas,Allah ta raba su lafiya".

Ji yai wani shock ya kamashi k'wak'walwar sa ta tsaya da aiki na d'an sekonni zuwa can ta dawo aiki,cike da tsananin farin ciki ya cire takalman sa yana tsugunnawa tare da yin sujjada ga Allah don nuna tsantsan farin cikin sa (Sujudushshukur) tsawon mintina yana durk'ufe yana godewa Allah gaba d'aya hawaye ya k'i tsaiwa a idon sa.

Ganin shiru shiru bai d'ago ba yasa doctor d'ago shi ya na bubbuga bayan sa Tare da fad'in " ba kuka za kai ba Umar, wannan abun farin ciki ne dariya ya dace kowa ya gani a kan fuskar ka".

Mirmishi ne ya yawaita kan fuskar tashi yace"Wannan kukan farin ciki ne Doctor yau ban san me zan yi in nuna godiya ta ga Allah ba,amma tabbas a yau nasan na fi kowa farin ciki da walwala ".

Wayar sa ya ciro a aljihu ya fara danna number d'in Abba, kira d'aya Abba ya d'auka da fad'in" Daddy ya dai?".

Cikin zumud'i yace "Abba gamu a hospital Nahna ba lfy,Doctor ya dubata ya tabbatar da ciki gare ta na wata biyu".

" Alhamdulillah Alhamdulillah, Allah kai ka cancanta mu godewa, Allah ya Kara mata lafiya kuma ya raba su lafiya,bari na na fad'awa murja maza tazo wajan Ku yanzu, ina fatan dai jikin nata bai tsanani ba?".

Yanda Abba ke magana cikin farin ciki haka ma UK d'in.

"Eh Abba jikin nata da sauk'i gashi an sa mata ruwa bacci ma take yi".


" To ka kula sosai ga murja nan zuwa ".

Yana yanke kiran ya kira Sweety ta sanar mata,itama ihun murna tasa tana fad'in da ta gama lecture da yamma zata shigo".

Bayan ya yanke kiran ya kira Ummu Sumail itama ya fad'a mata Nahna na da ciki,itama murna tai sosai tai fatan Allah ya raba lafiya.

Lokacin da ya danna kiran Yaya Haroon sai da ta fara Ringing sannan kunya ta kama shi,yana jin Yaya yai sallama ya rage murya tare da gaisheshi sai kuma yai shiru, Yaya Haroon ya ce" Daddy ya gida ya iyalin".

Cikin jin kunya yace "Alhamdulillah Khadeejan ce ma bata jin dad'i yanzu ma muna asibiti".

Cikin damuwa yace " Subhanallah me ya sameta?".

"Um um Zazzab'i ne da ciwon kai".

" To bari in kira Hafsah tazo taga jikin nata,amma dai da sauk'i ko?".

"Eh da sauk'i Yaya gata tana bacci dai yanzu".

" To Allah ya k'ara sauk'i da dare zan shigo in dubata insha Allah ".

Ba jimawa sai ga driver ya kawo Aunty murjah, itama bata jima ba Aunty Hafsa tazo,har lokacin ban farka ba.



Sai bayan sallar azahar na farka,na d'an ji dama dama,su Aunty nata min sannu ni dai amsawa musu nake amma ina mamakin yanda naga fara'a sosai kan fuskar su, taimaka min Aunty Hafsah tai na wanke bakina na d'an sha kunun Gyad'ar da aka kawo,a lokacin doctor yazo ya k'ara dubani sannan yace zamu iya komawa gida bayan ya rubuta mana magungun da zan iya amfani dasu.


Ya juya zai fita UK ya shigo nan ya ke sanar dashi ya ya sallame mu,suka k'ara musabaha,ya k'araso d'akin " kallon farko da naiwa fuskar sa naga yanayin da banyi tunanin gani a tare da shi ba,don na san ko ciwon kai kawai na keyi ya shiga damuwa kenan duk ya rikici amma yanzu gani kwance kan a gadon asibiti na ga fuskar sa d'auke da fara'ar da na dad'e banga irinta tare dashi ba.

Katsemin tunanin yayi ta hanyar min magana "Ya jikin naki?ban San kin tashi ba ai,ina masallaci".

D'an yamutsa fuska nai da fad'in" da sauk'i ".

" Masha Allah, Aunty mu wuce gida ko?".


Gyad'a kai Aunty murjah tai tana fad'in"Ai masha Allah jikin nata,in mun je sai tai wanka da ruwa me d'umi zata k'ara jin k'arfi".

Aunty Hafsah tace gida zata wuce tunda dai jikin nawa Alhamdulillah zuwa gobe zata k'ara dawowa ta duba ni, don haka sai da muka biya ya sauketa a gida sannan muka wuce .


Wani haushi naji ya turnik'eni yanda naga fara'a sosai kan fuskar UK, wato ni ina jin jiki amma ko a jikin sa ko sau d'aya banga alamun damuwa da tausayi na kan fuskar shi ba,sai wata dariya yake ma, gate d'in Su sweety muka tsaya Aunty ta sauka sannan muka shiga namu,yana tsayawa na bud'e murfin zan fita da sauri ya dakatar dani ta hanyar rik'oni cikin fishi na fizge nai wucewata,da mamaki ya tsaya kallona sannan ya rufe motar da sauri ya biyo ni.

A falon k'asa muka had'e ya rik'oni jikin sa sosai yana fad'in "Meya faru ne My Happiness?".

Turo baki nai nace " Don Allah cikani inje in huta na gaji".

Bai k'ara magana ba ya d'aukeni cak mukai sama,bai dire ni ba sai cikin d'aki, bakin gado na kwanta shi kuma ya shige toilet ya had'a min ruwan wanka me zafi,lokacin daya fito har bacci ya fara fizgata don alluran bata cika ni ba,kaya ya fara cire min inata tuttureshi da turo baki,shi dai sai dariyar sa yake annuri na k'ara fad'ad'a kan fuskar sa,abunda kW k'ara kular dani ina tunanin ya daina damuwa da ciwo na.

Sosai ya gasa min jikina ya min wanka, sannan yace in d'aura alwala don rama sallar azahar.

Da kansa ya samo doguwar riga cikin closet d'ina ya samin sannan ya shimfida min prayer mat nai salla.

Kafin na idar ya sauka k'asa wajan su Lami ya amsomin faten patato da su kayi min.

Haka ya sani a gaba yana bani a baki,ba dan naji dad'in saba da bazan ciba sai turo baki nake,abunda ke k'ara sashi dariya, sai da na cinye tass sannan ya b'allo min magungunan ina tirjewa haka ya sani jikin sa da lallashi na samu na sha.


Sai bayan da ya dawo sallar la'asar sannan ya zo ya zauna kusa dani cike da annuri ya rik'o hannayena yana magana k'asa k'asa "Sweety wai na ga kina ta had'e rai ne ko jikin ne?".

kauda kaina nai ina k'ara turo bakin.

Sani yai sosai cikin jikin sa yana min magana masu dad'i da tambaya dalilin fishin da nake, cikin shagwaba nace" ba kai ne ba".

"Ayya ni kuma my Happiness me nayi?".

" Kaine kana ganin banda lafiya amma ka ke ta wani farin ciki sam ma baka damu da halin da nake ciki ba".

Wata irin Runguma yayi min cike da tsananin shauk'i murya can k'asa yace "Nahna Khadeejah! Allah ya amsa addu'ar mu kukan mu ya k'are, Doctor ya tabbatar min kina d'auke da ciki na wata biyu yanzu".

Da sauri nai baya daga jikin sa ina kallon sa kallon son tabbatarwa,d'age min gira hak'oran sa duk bayyane cike da dariyar farin ciki yake k'ara tabbatar min,wani farin ciki wanda ban san iya girmansa ba ya ziyarceni na rasa in da zansa raina,kawai sai na sa hannayena na rufe fuskata ina sakin wani mirmishi me cike da kunya.


Cikin dariya ya jawoni jikin sa,yana fad'in" ba maganar kunya fa Baby,bud'e idonki mu cashe mu godewa Allah ".

Hawaye na zuba kan fuskata nace " Taso muyi sallah mu godewa Allah ".

Salla mukai raka'a biyu mun dad'e muna addu'o'i da nuna godiyar mu ga Allah tare da fatan Allah ya saikeni lfy.


Account d'ina na duba naga uban kud'in da ke ciki nan da nan naiwa Yayan mu Babba dake Sakkwato Transfer na kud'i dake yana aiki da gidan marayu nace don Allah ya cire a siyawa marayu abunci sadaka.

Can yamma Sai ga Sweety tana takawa da k'yar ta shigo tare da sakin gud'a, dariya nasa ina tashi daga kwancan da nake nace " Maman biyu sannu fa,kink'i daina fita ko? Kina son nakuda

Please Login or Register in order to submit comment