Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

fad'in" Abba ka sani fa ka sani a irin haka mamy ta rasu muka rasa ta a gun haihuwa mamy ta rasu ga Khadeejah ma zata mutu wajan haihuwa ".

K'wallar data taru a gefen idon sa ya share da hannun yana jijjiga kai don shima Abba cikin rud'ani yake,haka mamy tai haihuwar sweet taita zubda jini harta rasu,don haka yake jin mutuwar ta ta dawo mai sabuwa A yau duk ya rud'e shima.



Duk abunda ya kamata anyi aiki kawai za'a shiga da ita yanzu.yanda aka turo ta kwance akan keken zuwa d'akin operation d'in ya k'ara saka y'an uwa cikin rud'ani sunata d'aga mata hannu da fatan dacewa.


UK dai kuka yak'i k'arewa kamar k'aramin yaro rik'o hannunsa Abba yai suka shiga masallaci dasu yaya haroon don yin sallar azahar, ko bayan da suka idar ca yai mai ya zauna nan suyita nafilfili do rok'on Allah yasa ayi mata a sa'a.


Likitocin kuwa nata k'ok'arin su wajan ganin komai ya tafi dai dai, sunyi nasarar ciro mata 'ya mace masha Allah nan nurses suka fito da ita don a gyara ta su kuma likitocin na k'orarin mata d'inki.

Su Abba yaya haroon yaya usman da uban gayyar na masallaci tun sallar azahar basu fito ba,don haka koda aka fito da Babyn basa gun su Aunty murjah ne sukai ribibin karb'arta suna godiya ga Allah duk da duk hankalinsu naga son ganin halin da za'a fito da uwar hakan bai hanasu farin ciki da nuna godiyar su ga Allah ba.

Bayan sallar la'asar su Abba suka fito a masallaci suna k'arasowa ana fito da ita daga d'akin zuwa d'akin hutu itada matacciya ba maraba,don haka jiki a sanyaye sukabi bayan su, bayan an d'ora ta bisa gadon likitan dake tsaye ya tsawatar kan banda magana ko motsi me k'arfi a d'akin insha Allah zuwa magriba zata iya farfad'owa.


Nan akai ta kiran y'an uwa da abokan arziki ana sanar dasu haihuwar, kowa dai ya sami sukuni zuwa yanzu amma banda UK fatan shi dai yaga matar sa ta farka.

Sweety na gefe rungume da baby da take nannad'e cikin farin over role da towel sai baccin ta take,zubawa Babyn ido tai tana d'an mirmishi tace "Aunty hafsa kinga Babyn nan kamar su d'aya sak fa da broth komai nata ".


Mirmishi Aunty Hafsah tai tace "gaskiya kam kunwa yarinya ta wayo babu abunda ta d'auko nata duk gidan ku tayo".

Murna fal kan fuskar sweety ta k'ara rungume Babyn a jikin ta tana jin k'aunar ta na ratsata.



******
Duk yanda ake zaton zan farka da wuri ban farfad'o ba sai cikin dare cikin ikon Allah kuma sai na farka cikin hankali na bakina d'auke da salati, Aunty murjah da Aunty Hafsah da suke tare dani suka yo kaina suna fad'in " Khadeejah kin tashi sannu sannu kinji ".

Lumshe idona da yai min nauyi nai ina son tunano abunda ya faru dani amma na kasa tuno komai,don haka nabar idon a lumshe ina son samun nutsuwa, UK dake zaune a parlourn yaji kamar suna ambatan sunana hakan ya tabbatar mai na farka, da sauri ya turo k'ofan ya shigo tare da k'arasowa gaban gadon yana kamo hannun wana yace " Khadeejah, kin farka ko Khadeejah ta".

Ina jinsa amma naki bud'e idona yaita magana nai shiru a haka bacci ya k'ara d'auka na, jin sauke numfashi na ya tabbatar mai na koma baccin.

"Auntyn data farka meta fara cewa?".

Aunty murjah tace " Wlh da salati ta farka kuma ta bud'e idon kuma ta rufe".

Girgiza kai yai yana kallon fuskata data fad'a fayau ta rame tsakankanin lokacin,wani tausayi ne ya kamashi ya dafe kansa dake mai ciwo, Aunty Hafsah tace "Umar kaje ka huta ka samu bacci kona awa biyu".

Mik'ewa yai yana fad'in" To Aunty bari in kwanta kan kujerar parlourn ko zan samu hutu".



Ban farka ba kuma sai bayan sallar asuba wannan Karon ma da salatin na farka amma kuma yanzu ina gane komai da tunano komai da Irin wuyar dana sha duk lokaci guda suka dawo min a k'wak'walwa, runtse idona nai Ina girgiza kai, da sannu suke ta jeramin a lokacin kuma UK daya kira likita suka shigo tare . k'ara duddubani yai yana min tambayoyi don

tabbatar ina cikin hankali na "Khadeejah ina Babyn da aka ciro miki?".

Shafa cikin nai idona a rufe na tuna ashe fa anmin aiki an ciro baby da sauri nace " Ina Babyn nawa don Allah Ku bani inga mena Haifa?".

Mirmishi likitan yai yanaiwa Aunty Hafsah alama data mik'o Babyn, saita min Babyn yai a fuskata yace " ga baby girl d'in ki me kama da Abban ta "

Zuba mata ido nai na tsawon lokaci sannan na lumshe idona a raina nake tasbihi ga ubangiji na gode mai bisa wannan Babban ni'ima da yai min.

Ganin na lumshe idona yasa likitan mik'a musu yarinyar yana fad'in "Alhamdulillah ta dawo hankalin ta,zuwa ko wane lokaci in tai tusa kotai gyatsa sai Ku bata ruwan tea tasha".

Dafo kafad'ar UK yai yana dariya yace" My friend kuka ya k'are ga madam ta dawo normal ".

Shima UK dariyan yai yana d'an shafa kansa.



***********
Bayan sallar asuba wajan k'arfe shida naji shigowan UK cikin d'akin yanaiwa su Aunty sallama zaije gida yai wanka,Aunty tace " Daddy ka samu in kaje kai wankan kaci abinci ka kwanta ka huta ko zuwa azahar ne saika dawo ".

Amsawa yai da to ya k'araso bakin gadon ya lek'a fuskata yana fadin" wannan allurar tanada k'arfi sosai baccin bai bar kantaba har yanzu".

Aunty murjah ce ta amsa mai da "Eh ai sai a hankali zata sake ta, kuma baccin ma shi yafi mata kaga zata k'ara samun nutsuwa sosai ".

Gyad'a kai cikin gamsuwa sannan ya k'arasa gadon da Babyn ke kwance yana kallon ta fuskar sa d'auke da mirmishi ya d'an shafa gefan kumatun ta, ya juya ya fice.

Bayan fitar sa inajin su Aunty nata hiran irin firgicin daya shiga lokacin da nake labour da yanda yake ta kuka yana fad'in karna mutu na barshi, jin maganganun su ya k'ara sani cikin mamaki dukda ina cikin halin ciwo amma nima na tabbatar da tashin hankalin daya shiga don yanda ya kafe a labour room d'in nan yanata rirrikeni da tofa min addu'o'i har sautin kukan da yake nake jiyowa cikin kunne na,to wai daman UK bai daina sona ba kome,nikam na fidda raima da k'aunar shi gareni nai tunanin ko ina haihuwa ma ya sakeni amma sai naga wata kulawa yake ban ta musamman, tun asubar jiya har zuwa yau,kai anya kuwa babu wata k'ullalliya daya shirya min don haka bazan tab'a yarda da shiba,kuma zanyi taka tsantsan da yarinya ta don yanda ya nuna bai son haihuwar nan babu wani abu dazai canja mai ra'ayi.




_To_ _UK_ _bari_ _mu_ _jira_ _muga_ _me_ _kake_ _k'ullawa_ _kamar_ _yanda_ _Khadeejah_ _ta_ _fad'a_ πŸ‘€πŸ‘€πŸ‘€




*Taku* *ce*
*Y'ar* *mutan* *ja'oji* πŸ™‹
🍑🍑🍑🍑🍑🍑
🌸🌸🌸🌸🌸🌸
*'YAN* *ARABIC*
🌸🌸🌸🌸🌸🌸
🍑🍑🍑🍑🍑🍑

*NA*
*LAYUZA* *KABIR* *ADAM*

_DEDICATED_ _TO_ _ALL_
_ARABIC_ / _ISLAMIC_ _STUDENTS_
πŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“š


πŸ‘©πŸ»β€πŸ’»πŸ‘¨πŸ»β€πŸ’»
*ZAMANI* *WRITERS* *ASSOCIATION*
πŸ“
_We_ _are_ _here_ _to_ _educate_ , _motivate_ ,and _entertain_ _our_ _Readers_




*Allah kaimin maganin damuta ka kawo min mafita cikin* *lamarina ,Allah ka shiga tsakanin mu da mak'iyan mu* πŸ™πŸ™πŸ™



0⃣5⃣1⃣


Allah ya taimake ni wajan k'arfe goma iska ta fita a cikina don haka suka ban ruwan tea nasha nan na d'an ji k'arfin jikina, kafin me kuwa asibitin cike yake da jama'ar mu, y'an katsina ma da akai musu waya tun jiya wasu sun d'auko hanya yau,tunda akace musu aiki akamin duk hankali su yak'i kwanciya.


UK kuwa tunda ya wuce gida zuciyar sa ke cike da nauyi da kuma farin cikin daya rasa wane iri ne, zai shiga gate suka had'u da Abban bayan ya fito a mota sun gaisa yake k'ara mai barka da tambayar me jiki,amsawa yai cike da mirmishi akan fuskar sa, ganin da Abba yai idonsa jajir ya tabbatar akwai tarin bacci akansa,don haka yace yaje ya kwanta ya d'an sami hutu, gyad'a kai yai ya wuce ciki.


Yana shiga parlourn ya taddashi tsaf masu su lami sun gyareshe tas duk inda ya b'aci, daga nan sama ya haye zuwa d'akin sa ya watsa ruwa bayan ya fito kuma ya fuskanci tarin yunwar daya tara,don haka ya wuce kitchen ruwan tea kawai ya had'a da bread yasha a tsatstsaye sabida wani zazzafan bacci daya kama idanuwan sa, yana gamawa kuwa ya kwanta nan parlour ya kunna a.c .



*********
A can asibiti kuwa y'an barka sunk'i Yankewa wannan ya shigo wannan ya fita kama daga kan mutanan mu zuwa mutanan gidan su UK, kowa yazo sai yai maganar tsananin kamar da Babyn nan keyi da Baban ta, babu wani abu data d'auko nawa banda girman ido,inajin sweety da Aunty ummu sulaim nata mana tsiya wai yanda yayan family d'in mu ke kama damu haka suma babyn su ke kama da family d'in ta,tunda tayo Abban ta don ita sweety ma dagewa tai kai da k'afa bada UK take kama ba da ita take kama,Abban su na zuwa ta kalleshi cikin yanayin shagwab'ar ta tana fad'in "Abba don Allah Baby dawa take kama in ba niba".

Dariya yai yace " Tabbas kuwa baby da maman ta sweety take kama kobo da kobo".
Kowa dariya ya farayi, Abba kuwa zubawa Babyn ido yai fuskar sa d'auke da mirmishi aran sa yake fad'in "Alhamdulillah Allah abin godiya,muna godiya gareka da wannan babbar kyauta da kai mana,Allah ka rayata ka albarkace ta tsawon rayuwar ta".

Ya dad'e asibitin saida su yaya sukazo sannan suka fita tare da zasu tafi, yacewa Aunty murjah itama ta shirya taje gida daga nan akwai sak'o duk ta had'o tazo dasu.


Bayan sallar Azahar Aunty murja taje gida,d'akin ya rage daga ni sai sweety da Aunty Amrah sai k'awata Hafsah, don su Aunty Hafsah kuma da y'an gidan su da Aunty ummu sulaim suna can parlour, Babyn dake hannun Hafsa ta fara kuka,inaji na lumshe idona kamar ina bacci, sweety tace " Aunty na Baby na na kuka a tashi a bata nono kika wani rufe ido".

Dariya su hafsa sukai ni kuwa nai kamar ma banji ba, sunata tsiyar su nai musu shiru, ga Babyn taki barin kukan sweety ta d'auko ruwan zamzam take bata,inajin yanda take lasan ruwan tan tan,sabida ansa dabino a ciki, wani irin sukuni da nishad'i nakeji a zuciyata,tabbas zuciyata daga jiya zuwa yau babu inda babu farin ciki a ciki, har tsoro nakeji yanda k'aunar y'ata take a cikin zuciyata tun kafin tazo duniya don haka nake rok'on Allah ya tallafa min wajan tarbiyar abunda zan haifa ,kar tsananin so da k'auna yasa na gaza wajan tarbiya, yanzu haka ji nake kamar in bud'e ido inganta rungume a k'irjina amma ba dama don tunda na dawo hankali na su Aunty ke cewa in sata a jikina amma tsananin kunya da kawaici bazai barni ba,dukda ina buk'atar hakan, jin kukan da Babyn ta k'ara tsanyawa yasa na d'an bud'e idon anan Aunty Amrah tace "Nahna karfa ki tsaya wani jin kunya ki d'au hakkin yarinyar nan,wlh nono take buk'ata gashi nan sai lasan harshe take .

Mirmishi nai nace " Hafsa tallafa min na tashi".

Kamani tai na tashi na jingina jikin gadon a hankaki bayan na kara filo,saida na daidaita zamana sannan sweety ta d'oro min ita kan cinyata, tallafota nai jikin k'irjina na zuba mata ido ina kallon yanda taketa lasan baki tana harba hannu ga idanuwan ta bud'e tar masha Allah, ganin na tsaya kallon ta ban shirin bata nonon yasa Aunty Amrah matsowa kusa dani tace "bafa kallon ta zaki tsaya yiba zuge zif ki bata tasha".

d'an marairaicewa nai nace " wlh nifa zafi nake tsoro".

Dariya sukasa gaba d'aya na d'ago ina kallon su tare da turo baki nace"ke sweety zoki d'auke ta bazan bayar ba".

Itama matsowa tai gaban gadon tana danne sauran dariyar tace "yi hak'uri Aunty na d'an bata kad'an kinji babu zafi ko Aunty Amrah". Ta k'arashe maganar da kallon ta.

Ganin yanda suke ta ban baki yasa na zuge zif d'in rigata a hankali cike da fargaba da kunyar karon farko da zan fara bud'e rigata haka gaban jama'a, a sannu nasa mata a bakinta ai kuwa ta cafke da sauri ta fara tsotsa,can na runtse idona na cije baki inajin zafin yanda take tsotsa.

Aunty Amrah ce ta kawo bakin ta kunne na tana min rad'a" ke raguwa ce Allah, Katon gardi ma yasha balle y'ar Babyn nan".

da sauri na kauda kai gefe ina fad'in "um um nidai baya sha ".

Dariya tasa tana gyaramin kan Babyn sosai a jikina,ta juya ta d'auki Baffa dake kuka.
A dai dai nan aka turo k'ofar d'akin duk hankalin mu ya koma ga k'ofar, sanye yake da k'ananun kaya farare tas takalmin k'afar sa ma fari tas yayi kyau shar dashi, jingina yai jikin k'ofar fuskar shi d'auke da mirmishi, kallo d'aya nai mai na maida kaina, gaisheshi suka farayi ya amsa fuskar shi d'auke da mirmishi, suna mai barka sai washe baki yake yana amsa musu,da d'ai d'ai suka fita sweety na tsokanar shi " broth kama daina yarda da masu cewa kamarku d'aya da Baby na,don dazu da Abba yazo yace bada kowa take kamaba illa dani".

Dariya yai yace "To sweety ai in tai kama dake to nima zata iya kama dani ko"?.
Gyad'a kai tana dariya tace'kumafa haka ne broth".

Mik'a mai hannu tai suka tafa sannan itama ta fita.

A hankali ya k'araso bakin gadon da muke yazo tsaya a kaina yana zuba min idanuwan sa,wani kallon k'urulla yake min wanda ni kuma wata kunya da ban san dalilin taba ta rufeni,ga wani takaicin sa kuma a sashin zuciyata,don na d'au aniyar koya sauko ya hak'ura ni kuma saina gasa mai aya a hannu,

Jinai ya sako hannunsa yana shafa kan Babyn sannan a hankali ya furta"Congratulation my khady, Alhamdulillah jiki ya fara kyau,ga Babyn ma cikin k'oshin lfy ,amm ki rink'a lura sosai kinga c .s akai miki sai kin kula don mu samu ya had'e da wuri ".

Shiru namai kamar banjin sa, bai gajiba ya d'ora da fad'in
" sannu kinji Khadeejah kinsha wahala matuk'a kin d'aga min hankali, gani nake kamar ranki zai fita yanda numfashi ke fita a lokacin nan,wlh na tsorata matuk'a, yanzu Khadeejah duk a haka mata ke haihuwa su tara yaya amma wasu sai ki gansu ma da yaya goma har sama da haka, hhhmmmm sannu kinji".


Still ban d'ago balle in amsa,sai k'ok'arin rufe rigata dana fara don naga ta koma bacci,hannun nasa zan zuge zif d'in amma sabida a rank'wafe nake hannun bai kaiba,matsowa yai sosai ya zuge min zif d'in sannan ya zauna kan kujeran dake gaban gadon tare da d'aukan Babyn, zamewa nai na kwanta tare da lumshe idona.

Tunda yasa Babyn a jikin sa ya zuba mata ido yana k'ara tabbatar da tsantsan kamar dake tsakanin su,banda kwayar idonta baby abunda yake jikinta ba irin nasa ba, d'aga ta yai yasa ta a k'irjin sa yana wani lumshe ido,wata tsantsan k'aunar ta yakeji yana saukar mai a cikin k'irjin sa, hannayen sa yasa ya k'ara rungume ta a jikin sa,idanuwan sa a lumshe, tsawon mintina goma sha biyar yana a haka duk wata gab'a ta jikin sa tai sanyi,wai daman wannan halittar ce a cikin Khadeejah amma har yake ikirarin baya so,daman haka d'a yake da dad'in kalla da dad'in d'auka, yanzu wannan Babyn tasa ce mallakin sa,hhhhhmmm Lalle yaso ya tafka wauta a rayuwa, yanzu wannan tsananin son nata da yaji yana ratsa zuciyar sa da gangar jikin sa duka haka iyaye sukeji akan yayan su,masha Allah, hak'ik'a Allah abun godiya ne".

K'ara sauko da ita daga k'irjin sa yai yasa ta akan cinyar sa,ya kama yatsun hannunta yana kalla sannan ya cire safar k'ofar ta ya duba yatsun k'afar ma, jijjiga kai yai yana fad'in "tsarki ya tabbata ga ubangiji halitta".



Nikam tunda na rufe idona ina dan tunani daga haka bacci ya d'auke ni, ban k'ara sanin me yake ba.


Zaman awa guda cif yai a d'akin shi d'aya yana kuncewa da sak'awa,bak'in da akai yasa ya tashi ya fita,ni kuwa banma san me akeba, sai bayan na tashi sweety ke cemin ai ya dad'e bai fito a d'akin ba ta shigo taga na barshi shi d'aya zaune ni inata bacci,mirmishi kawai na mata na kauda zancan.




**************
Kwanakin mu hud'u yau a asibin masha Allah jikin nawa yanata yin kyau,don yanzu da kaina zan tashi in zazzagaya a haraban asibitin kuma koda yaushe in za'amin dressing wajan suna fad'in banida k'anjiki don yana had'ewa yanda nakeso.
Koda yaushe safe da dare UK na asibitin nan wata zafaffiyar k'auna ke nunawa Babyn nan,gaban kowa bai jin kunya ko hannun wa take in yazo zaiwa sweety inkiya ta karb'a mai ita, kuma inya amsheta haka zaita rungume ta yana mata kiss har hira zakaji yana tayi da ita kamar tana jinsa,wani sa'in ma fita yake da ita harabar asibitin sab'e a kafad'ar sa yana zagaye da ita. Y'an uwana da sukazo daga sakkwato kullum suna zuwa su yini ana da dare yaya in yazo ya wuce dasu gida don Aunty Hafsah da sweety ne suke kwana dani, tsakanina da UK ba sauyi in yazo zaita jana da surutu da hira yana nuna min wata kulawa ta musamman amma in ba' a gaban mutane bane kallo bai isheni ba,in na saurareshi to bamu kad'ai bane a cikin d'akin da mutane amma donni dashi duk maganar da zaiyi kurma nake komawa, abun na damun sa matuk'a ya ban hak'uri yamin magiya ya rarrasheni amma a banza,koda yaushe ca yake yayi nadama in yafe mai,amma ko zuciyata tai sanyi naji kamar in bar komai in share sai inji na kasa inna tuno maganganun da yake fad'a min duk sai inji wani takaici na taso min.


************
Randa mukai kwana biyar aka sallamemu, muka dawo gida Goggona da zata zauna dani har nayi arba'in aka ware mata d'aki guda a k'asa don haka nima na dawo k'asan gaba d'aya da zama.

Shirye shiryen suna aka fara dukda Abba yaso a d'aga sunan zuwa satin sama zuwa lokacin na k'asa yin k'wari sosai,amma su Aunty murjah sukace k'ara ayi kawai, in huta gaba d'aya.

Ana gobe suna Me k'unshi da kitso sukazo gida yimin me kitso nayi me k'unshi nayi nan danan suka gama min nai shar dani,gidan ya cika damk'am da jama'a don duk mutanan mu na sakkwato sunzo hakama b'angaran UK y'an uwan su na katsina da yawa sunzo amma su suna gidan su su sweety dukda katanga d'aya muke don haka ba sukuni duk gidajan.


Kayan barkar da Abba yai mana nida Babyn masha Allah, haka UK da yamma ya shigo da nashi akwatinan da yai mana set guda abun sai son barka,kowa Allah sa albarka yake gwanin birgewa.

Da dare ina zaune tsakiyan y'an uwana munata hira yayin da wasu kecan b'angaran masu aiki sunata aikin hidiman suna, wayata dake gefe ce tai ringing na kai kallona ga screen d'in wayan Hubbey na gani na yawo akai,yinai kamar bazan d'auka ba sai kuma dai na d'auka bance kala ba saida yai sallama na amsa yace "Khadeejah ina son ganin Baby na a kawo min ita yanzu".


Zanyi magana naji harya datse kiran, Tabbas nasan umarni ya bani kuma sab'a umarnin sa dai dai yake da sab'awa ubangiji na, kallon Fatima y'ar Auntyn mu nai da Babyn ke hannun ta nace " kinga wai Abban ta yace akaita ko zaki mik'a mai ita sama".

Da sauri Aunty tace "A'a ita da tazo yau tasan kan gidan kune da zata mik'ata,tashi a ki kaita da kanki mana".

Marairaicewa nai da fad'in" Aunty nifa bazan iya hawa upstairs da ita ba".

"To tashi ta rakaki da ita".

Mik'ewa nai na gyara d'aurin zanina sannan nai gaba fatima ta biyo bayana da babyn.
A hankali nake taka steps d'in ina hutawa don ban son abunda zanyi in sami matsala a d'inki na, muna zuwa step d'in k'arshe fatima ta tsaya tana mik'omin ita,d'an mirmishi nai na karb'eta na wuce zuwa d'akin nasa da sallama na tura k'ofan na tsaya,

" shigo mana ". ya fad'a da siririyar murya, a sannu na shiga tsakiyan d'akin na tsaya, yana zaune bakin gado ya zubamin ido, ni kuwa na kauda kai gafe ciki ciki nace " gata ".

Tasowa yai a hankali ya k'araso gaba na tare dasa hannunshi ya karb'e ta,ganin da yai na juya ina shirin fita yasa ya rik'oni,da sauri na kalleshi shima idon sa tsaf cikin nawa, kauda kaina gefe nai ina fad'in" meya faru kuma".

"Ki tsaya ina son muyi magana ne".

" amma ai ca kai kawai in kawoma ita".

"Eh na sani, amma don Allah kiban d'an lokaci muyi magana".

Bazan iya bijirewa umarnin saba don haka na juyo na tsaya kaina a gefe, kamo hannu na yai zuwa bakin gadon muka zauna,ganin yanda ya matseni sosai yasa na d'an matsa ,mirmishi kawai yai idon sa akan Babyn yana wasa da hannunta, ita kuwa idonta tsaf kansa,ta gefan ido nake kallon sa,yanda yake mata wasa yana kissing d'in ta.

Kusan mintina uku,sannan ya d'ago kansa gareni yana zama serious yace " Khadeejah! Shin yanzu Khadeejah bazaki iya afuwa gareni ba,bazaki sassauta min ba Khadeejah, nayi nadama nayi nadamar furuci na, ban san haka haihuwa keda dad'i ba Khadeejah saida Babyn nan tazo duniya duk bayan second's k'aunar ta k'ara tsanan ta take a zuciyata, don Allah kimin afuwa kinji ".

K'asa nai da kaina kawai don ban son mai rashin kunya domin nasan hukuncin hakan wajan ubangiji na,zafin zuciya bazai sani in fad'awa halaka,haka kuma ban shirya saukowa ba don haka shiru shine mafi alkairi daga magana.

Rik'o hannuna yai sosai cikin nasa yana k'ara matsowa jikina yace " k'unshin nan yai kyau sosai,da ina nan akayi zan bawa me k'unshin kyauta ta musamman. . . shafawa hannuwan yai tayi yana yaba k'unshin.
" shike nan tunda baza kiyi magana ba, daman kan batun sunan da za'a sawa Baby ne,shin kinada sunan da kike so a samata ?".

Girgiza kai nai kawai,yace "babu?".

Nace " Eh ".

" To daman tunda aka haifeta araina naso saka mata sunan mama na wato Ruk'ayya,hakan yayi miki".

Gyad'a kai nai ina fad'in "Eh yayi,Allah ya raya min ita ".

Cikin mamakin furucina ya kalleni nad'an sakwanni sannan yace " Allah ya raya miki

Please Login or Register in order to submit comment