Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

mutunci,
A hankali ta d'ago kanta ta dubi samarin dake tata iskancinsu 'rasssss .. Taji gabanta ya fad'i ganin wannan saurayin ne daya mata wulakanci ranar nan da sauri tai k'asa da kanta don karya ganta. . haniyar su ta k'ara ji suna tafiya sabida korar karan da lecturer d'in yaci gaba da yimusu.

Bayan ya dawo cikin ajin yaci gaba da k'orafi kan rashin tarbiyar wasu d'aliban Sam basa ganin malaman da ba nasu ba da mutunci,
Haka dai yaci gaba da mitarsa ya hak'ura.

Wajan karfe d'aya sun fito lecture sukai hanyan masallacin mata don yin sallah ita da wata Hafsa wadda tun zuwanta suke zama gu d'aya sabida sunan Aunty Hafsa yasa Nahnah taji ta shiga ranta har suka d'an saba kad'an,
Suna tafe suna d'an hira daga bayanta taji ana fad'in "Ya'n mata ina zuwa cikin wannan ranar"?

Daf taji gabanta ya fad'i don taso ta gane miryan waye "waike wace irin bak'auyi yace ahaka ana kallonki wayaiyiya dake kinyi kwalliya irinta manyan mata amma duk d'abiunki irin na k'auyawa, ai yanzu y'an mata sun daina wannan jan ajin ana kwankwasawa suke bud'ewa, kin san kuwa irin yanda manyan yaran makarantar nan suke yayina duk macan da kika cewa UK tasan ni amma ke tun rannan ana miki magana kina wani basarwa"
Duk maganar da yakeyi ba wadda tasa idonta cikin nasa yana gefan Khadeejah Yanata zubarsa suko tafiyansu suke abinsu har suka isa k'ofan masallacin sukai shigewansu abinsu basu bi ta kansa ba,
Sosa kai yai cike da takaici ya juya ya koma inda abokansa ke jiransa.

Bayan sunyi sallar sun fito Hafsah ta dubi Khadeejah tace"wai a ina kika samo wannan tab'ab'b'an ya ishi mutane da zuba haka."

Tab'e baki tai cike da basarwa tace"oho ni banma sanshi ba kawai shirme ne irin na mazan da basu San abinda ya kawo su makaranta ba."

" To Allah ya kyauta"

Daga nan suka bar zancen suka shiga wata lecture d'in.




Taku ce
Layuza kabir Adam๐Ÿ™‹โ€โ™€
๐Ÿก๐Ÿก๐Ÿก๐Ÿก๐Ÿก๐Ÿก๐Ÿก
๐ŸŒธ๐ŸŒธ๐ŸŒธ๐ŸŒธ๐ŸŒธ๐ŸŒธ๐ŸŒธ
๐ŸŒธ YA'N ARABIC ๐ŸŒธ


NA

LAYUZA KABIR ADAM



DEDICATED TO ALL
ARABIC/ ISLAMIC STUDENTS
๐Ÿ“š๐Ÿ“š๐Ÿ“š๐Ÿ“š๐Ÿ“š๐Ÿ“š๐Ÿ“š๐Ÿ“š




*๐Ÿ’ปZAMANI WRITERS ASSOCIOTION*

๐Ÿ“ .
โ€‹โ€‹Wษ› ษ‘ส€ษ› ษฆษ›ส€ษ› tัณ ษ›ษ—ucษ‘tษ›, Mัณtiัตษ‘tษ› ษ‘ษณษ— ษ›ษณtษ›ส€tษ‘iษณ ัณuส€ ส€ษ›ษ‘ษ—ษ›ส€เธฃโ€‹โ€‹

โ€‹๐Ÿ“š โ€‹โ€‹Zaku iya samun littafan mu a Facebookโ€‹โ€‹ ๐Ÿ‘‡๐Ÿฝ
Fb.me/ZAMANIWRITERSASSCIATION


๐Ÿ“ฉ โ€‹โ€‹Zaku iya aika mana sako ko korafi, Ta email namuโ€‹โ€‹ ๐Ÿ‘‡๐Ÿฝ
Zamaniwriterassociation@gmail.com



0โƒฃ0โƒฃ4โƒฃ



Cikin k'warin giwa da nutsuwa Khadeejah ke tafiyar da komai d'inta acikin skul d'in Sam bata shiga cikin shirgin kowa inba Hafsa Usman ba tana naxartar rayuwar kowa ne ta gane inda yasa gaba, tana so ta gane iya kamun kan ko wace mace cikin class d'in nasu ne duk da masha Allah d'aliban Arabic d'alibai ne masu cike da Nutsuwa da kamun kai da matuk'ar wahla kaga d'alibar dake karantar Arabic/ Islamic tana wani abu na rashin d'a'a ko ballagazanci da maza.

Yauma kamar kullum ta shirya tsaf cikin atanfa d'inkin Riga da sket tai d'aurin d'ankwalin fanka ya tashi sosai gwanin birgewa mayafinta na cumar tasa ta d'au jakanta ta fito a parlour ta tarar da Yaya Haroon ta zauna suka gaisa yace"Nahnah ya karatun kina jin dad'insa dai ko?"
Mirmishi tai tace " Yaya wlh Alhamdulillah komai yana tafiya dai-dai."

"Madallah bari in kaiki don yau ba da wuri zan fita ba zamu je wata gaisuwa daga office d'inmu."

Suna tafe suna hira har suka k'araso skul d'in dake ma a new block's zasuyi lecture d'in yasa ya ajiyeta a bakin gate tunda ba nisa zatai ba ya d'auko 1k ya bata godiya tai ta fito.

Cike da nutsuwarta take tafiya harta k'arasa block d'in tasa k'afa ciki tana k'ok'arin zama taji lecturer d'in yace " ุงู†ุช "
A nutse ta juyo ta dubeshi taji ya k'ara fad'in " ู„ู…ุงุฐุง ุชุงูƒุฑุชุŸ"
K'asa tai da kanta don ganin duk idon d'aliban ya dawo kanta ganin batai magana ba yasa yace " ุชุงู„ูŠ ุงู„ุงู‡ู†ุง"
A hankali ta k'araso gaban Allon jikinta harya fara rawa yace" ุงุฎุฑุฌูŠ ." rau rau tai da idonta harya kawo ruwa ta had'a hannayenta waje d'aya alamar ban hak'uri ๐Ÿ‘tace" "ุงููˆุงู† ูŠุง ุนุณุชุงุฐ
Ganin yanda jikinta ke rawa yasa ya kauda kai tare da nuna mata hanya da sauri ta koma ta zauna a gunta tana ajiyan zuciya,

Lecture ya cigaba da yi musu cike da k'warewa irinta malamin daya son harkar education.

Bayan sun fito Hafsahm ta dubeta tana murmushi tace " Khadee haka kike dama da tsoro? daga ance meyasa kika makara sai jikinki ya d'au rawa."
Gyad'a kai tai tace " hhhhmmmm Bazaki gane ba Hafsa ba maganarsa ce ta
tsorata niba idon mazan nan yasa jikina rawa jifa yanda duk suka zuba min idanuwansu"
To meye ai dakewa zakiyi kamar biki gansu ba."
" Ke wlh nifa kinga cikin maza na taso agidanmu amma ni Allah yasa min k'in had'a sabga da wani namiji daba na danginmu ba."
Dariya sosai taba Hafsa don haka sai da tai me isarta sannan tace"To tunda kikazo high institutions ai kinzo gidan maza kuma dole ki alak'a dasu."
Had'e rai tai tace " kai dai Hafsa kema kallon kitse nakewa rogo nai zaton ke d'in me kamewa ce amma meye naji kina fad'a haka?"

Kallonta Hafsa tai sosai kafin tace " Ke nifa ba abinda kike zargi nake nufi ba inaso in nuna miki ne dole ko yaya sai kinyi alak'a da maza akan harkar karatu kamar group discussion, group Assagment da ire ire ransu kinga dole maza da mata ake hadawa."

Kai kawai ta d'aga bata k'ara magana ba suka nufi cafeteria.

Suna zaune shagon me wainar fulawa suna jira a soya musu Hafsa ta cewa Khadeejah "Deejah ina zuwa bari in kai photo copy can wajan kafin asoya mana."
"Ok to sai kin dawo."

Wayanta ta d'auko tana ta bud'e data don ta duba sok'onnin da aka turo mata tunda ba Wanda zatai hira dashi,
Kasancewar shagon cike yake da mata wasu nacin abinci wasu na hira suna jiran a soya musu,
Wata budurwa ce ta shigo shagon da shadda koriya ajikinta tasa blue d'in hijabi duk ya tattare ya tashi sabida tsufan da yayi ga takalmin soso ruwan hoda fuskar nan tata ko yar powder babu kwata-kwata dai abin ba birgewa waje ta samu ta zauna hannunta d'auke da robar taliya da manja data siyo agaggauce ta cinye tasha ruwanta ta mik'e ta fice,
Tana fita wasu y'an mata suka bushe da dariya d'ayar ta kalli sauran k'awayenta tace "Kai Rahma umar irin wannan d'aukan wanka da kikai ai sai a d'auka meenat event zakije biki"
Wata ma ta amshe " A 'a wlh wannan ba Rahma bace tafi dacewa da Iklima salis."
Bushewa sukai da dariya sunata shak'iyan cinsu wadda aka kira da Rahma ta yatsina fuska tace" kai ai wlh wasu matan suna bada gayu don Allah jibi yanda ta wani zo skul abirkice saikace wadda akaiwa rasuwa, kina high kina zuwa skul da wani shiga irinta mahaukata mitsssss taja tsaki."
Dariya suka k'ara yi Ilkima tace "ai wlh wanna in yar department d'inmu ce ko kulata bazan rink'ayi ba don bata kai ko matsayin in dubeta ba."

Wata dariyan sauran suka saki suna mata tafi wata cikinsu tace" To waiku ina ruwanku da ita maybe ma ba y'ar skul d'innan bace wata k'ilama irin masu masarar nan na bakin gate yunwa ta kamata shine ta shigo ta rage zafi da y'ar taliyarta."
"Ke inji uban wa? to wlh d'aliba ce kina ganinta da Jakarta kawai irin y'an Arabic d'innan ne masu jawa skul d'inmu zagi, bazaki tab'a ganin y'an Arabic da kwalliya ba waisu ustazai."

Karo na farko Khadeejah ta d'ago kanta ta dubesu da maganar da sukeyi najin sun fara zagin department d'inta har zata tanka sai kuma kawai tai shiru,
Wayanta ce ta fara Ring ta d'aga cike da murna da shagwab'a ganin Yaya ja'afar ne yayansu dake aikin soja
" Hello broth"
Daga d'aya bangaran ya amsa
Tace " morning"
"Morning sis"
" how are you"
"Fine broth "

Salon yanda take maganar da shagwab'a yasa duk hankalinsu ya dawo kanta
Nan suka fara kallon kallo da ido suka fara gulmanta dukda dik da English suke maganar duk sunajin me take fad'i sun San bada saurayi take wayanba yayanta ne amma hakan bai hanasu gulmanta ba.
Bayan ta gama ta ajiye wayan tana kallon Hafsa data dawo yanzu fuskanta d'auke da mirmishi tace" Hafsa k'ila yau kafin agama lecture zan gudu gida yayana yace min ya taho daga Lagos zai kawo mana ziyara daga nan ya wuce Garinmu"
Mirmishi Hafsa tai tace" kuma shine zaki gudu gida ai lokacin da zamu tashi har kije ma be zama lalle ya sauka ba, kuma wlh kin San malamin Islamic d'innan da zai mana a k'arshe yace duk Wanda bai attending lecture d'insaba zai sami matsala dashi"

Jim tai kafin tace" To bari injira"

Ta window d'in shagon wata ta lek'o tace " Umm mema sunanku um Y'AN ARABIC."

Atare Hafsa da Khadeejah suka d'ago suna dubanta tai mirmishi tace"Wlh ban San sunayenku bane muna department d'aya daku daman wucewa zanyi na hango Ku nan."
"Khadeejah tai dariya tace "To ki zaga yo mana Y'AR ARABIC tunda muma bamu San sunanki ba."
Zagayowa tai tazo ta sami gu ta zauna tana fad'in "Wlh sai zagaye nake ni kad'ai wadda muke zama da ita yau bata zoba shiyasa ban San zuwa wajan da ban San kowa duk skul d'in ta isheni fa"
"Kinji duka fa satin mu biyu acikin skul d'in da fara lecture ai sai a hankali za'a saba ke meye sunanki?"

"Saudah Sadeeq suna na"
"Ok ni kuma Hafsa wannan d'in kuma Khadeejah Alk'adi Yusuf."

Tsalam sukaji bakin Iklima cikinsu " Hy friends don Allah wane department kuke?"

Kallon ta Hafsa tai tace"Mu Y'AN ARABIC ne muna department under Islamic."
Da mamaki suke kallonsu don abin ya d'aure musu kai duk cikin su ukun babu wata me k'ask'antacciyar shiga duk Kansu cikin ado suke abinda sha'awa,
A sanyaye Rahma tace tana duban Khadeejah " Amma baiwar Allah dama ke d'in y'ar Arabic ce kina ji munata aibata Y'AN ARABIC biki tanka mana ba."
Cike da b'acin rai Khadeejah tace 'In tanka ince muku meye tunda naga alamar sana'arku ce yi da mutane tunda wannan baiwar Allah ta shigo ta fita kuke zancanta K'arshe ma kuka b'ige da jingina ta da department d'in ARABIC sabida gurb'ataccen tunaninku ya Baku Y'AN ARABIC basa kwalliya, tunda an fad'a muku don mutum yana karantar addini an haramta mai ado wannan rashin kyakykyawan tunanin ne."

Tsit sukai duk kunya ta kamasu gudun kar aga kashinsu yasa d'aya daga cikinsu k'arfin halin fad'in " Ke malama karki fad'a mana magana mana naga zantukanki sina yin gautsi ."

Had'iyan yawu tai taci gaba " ai bamu muka ce Y'AN ARABIC d'in suna zuwa skul da k'azanta ba muma ji mukai ana fad'i don haka karkiga laifinmu."

" To tunda ji kikai ana fad'a daga yau duk Wanda kukaji yana zancan Y'AN ARABIC basa kwalliya to ki k'aryata shi don waccan ma da kuke gulmanta ba department d'inmu take ba, a k'arshe ina me Baku shawara da Ku guji zancan mutum bayan idonsa domin haramunne Allah ya haramta hakan."

Mik'ewa tai tana kallon su Hafsa "Ku tashi mu tafi don saura minti Goma mushiga lecture in mun fito mazo mu amshi Wainar karmu makara."

Har sunje bakin k'ofa ta juyo tana fad'in "y'an uwa sai anjima ."

Bata saurari amsarsu ba ta bar gun.







Taku ce
Layuza kabir Adam๐Ÿ™‹โ€โ™€
๐Ÿก๐Ÿก๐Ÿก๐Ÿก๐Ÿก๐Ÿก๐Ÿก
๐ŸŒธ๐ŸŒธ๐ŸŒธ๐ŸŒธ๐ŸŒธ๐ŸŒธ๐ŸŒธ

*๐ŸŒธYA'N* *ARABIC* ๐ŸŒธ


*NA*
*LAYUZA* *KABIR* *ADAM*



DEDICATED TO ALL
ARABIC/ISLAMIC STUDENTS
๐Ÿ“š๐Ÿ“š๐Ÿ“š๐Ÿ“š๐Ÿ“š๐Ÿ“š๐Ÿ“š


๐Ÿ’ป *ZAMANI WRITERS
ASSOCIOTION*

๐Ÿ“ .
โ€‹โ€‹Wษ› ษ‘ส€ษ› ษฆษ›ส€ษ› tัณ ษ›ษ—ucษ‘tษ›, Mัณtiัตษ‘tษ› ษ‘ษณษ— ษ›ษณtษ›ส€tษ‘iษณ ัณuส€ ส€ษ›ษ‘ษ—ษ›ส€เธฃโ€‹โ€‹

โ€‹๐Ÿ“š โ€‹โ€‹Zaku iya samun littafan mu a Facebookโ€‹โ€‹ ๐Ÿ‘‡๐Ÿฝ
Fb.me/ZAMANIWRITERSASSCIATION


๐Ÿ“ฉ โ€‹โ€‹Zaku iya aika mana sako ko korafi, Ta email namuโ€‹โ€‹ ๐Ÿ‘‡๐Ÿฝ
Zamaniwriterassociation@gmail.com



0โƒฃ0โƒฃ5โƒฃ



Akan hanyarsu ta zuwa lecture d'in kowa bai tankawa d'an uwansa ba, kai tsaye suka shige cikin lecture theater d'in suka maida hankali gun d'aukan darasin.

Tsawon awa guda suka fito Hafsa ta dubi Nahnah tana cewa"mu wuce mu karb'i wainar mu ko ?"

Ba tare data ce komai ba kawai gyad'a kai tail suka wuce ,

Suna zaune zasu fara cin wainar Hafsa ta kalli Nahnah tana d'an murmishi tace " khadeejah daman kin iya fad'a haka ina miki kallon me sanyi da yawa,"

Cikin basarwa tace "fad'an me kuma nayi Hafsah"
"Au har kin manta rikicinku da mutanan nan na d'azu ai naji dad'i da kika gyasa musu magana"

" lalle ke har kinsa wannan abin a gurbin fad'a ai gaskiya kawai na fad'a musu kan kuskuransu"

Hafsah ta bud'e baki da zummar Kara magana ta katseta ta hanyar cewa " mubar wannan batun oya muci abinci donni harna manta ma dasu banda kin tuna"


Cike da zumud'i ta nufi hanyar gida bayan kammala lectures d'insu don tasan yanzu Yayanta ya k'araso tunda daman ya fad's mata bazai wuce awa uku zuwa Hud'u bai sauka ba, don haka da k'arfin gwiya ta shiga gidan ai kuwa muryansa ta fara juyowa suna hira da yaya Haroon da gudu ta k'arasa parlour tana fad'in " Yaya Oyo yo sannu da zuwa marhaban bika "
Dariya yai tare da rik'o hannunta yana fad'in " Nahnah duk wannan sannu da zuwan nawa ne lalle kin cancanci tsara ba me tarin yawa"

Dariya ta k'arayi ta zauna tanaiwa Yaya Haroon barka da gida sannan ta k'ara kallonsa tace "yaya sannu da hanya gaskiya ka tafiyu ya aikin?"

Mirmishi yai yace"um bari kawai y'ar k'anwata sai a hankali ta skul d'in? Um wai yau saiga autar Baffa a high institution abin kamar wasa"
Yaya Haroon ne yai dariya tare da fad'in " kaga Nahnah an zama manya ko "

Yaya nura ya k'ara dariya yana jinjina girman data k'ara,

Aunty Hafsa ce ta fito hannunta d'auke da k'aton faranti da Sauri Nahnah ta tashi ta k'arb'i kayan tana "Sannu Aunty ya gidan ya aiki"
Had'e rai tai cikin sigan wasa tace " bazan amsa ai da biki san da niba kina ta Nura ko"

Caraf yaya Nura ya amshe "a'a Aunty ba ruwana bani na rik'eta ba fa"

Ita dai Bata tanka ba tai cikin d'akin fuskanta d'auke da mirmishi,
Ruwa ta watsa ta d'auro alwala don magriba tayi tazo tai sallah sannan ta fito parlour inda su yaya suke cin abinci ta zauna tare da d'aukan flate itama ta zuba ta fara cin nata.

Bayan sallar isha'i duka suna zaune a parlour sinata hira yaya Nura ya jawo trolley back d'insa yana fad'in Nahnah bari in baki tsara banki irin ta y'an matan jami'a,

Cikin zumud'i ta matso gabansa tana cewa "yauwa my broth na gode sosai fa"

Dariya yai "ke tun kafin abaki har kin fara godiya "

Ita dai a zumid'ance take kallon jakan taga me zai d'auko,

Zuge jakan yai ya fara ciro wasu dogayan riguna y'an ubansu guda biyar sannan takalma k'afa uku da jakunkunan su sai wasu jakun kunan irin wanda d'alibi yake buk'ata masu kyau ya tura mata gabanta yana fad'in
"To gashi amma Allah yasa rigunanma suyi miki dai-dai don naga kin k'ara tsayi"

Tsananin Murna bayyane kan fuskarta take d'aga kayan tana fad'in "masha Allah broth amma ka burgeni na gode Allah ya k'ara muku bud'i da wadata ya yalwata arzik'inku"

Da mirmishi kan fuskarsu suke amsawa da Ameen don a kullum burinsu bai wuce ganin farin cikin autar tasu ba ko don amanar da Baffansu ya bar musu.

Da sassafe yaya Nura yai shirin d'aukar hanyar sakkoto bayan ya cika wa Nahnah jakanta da kud'i yace don tana buk'atar kud'i a irin wannan lokacin.


A haka Nahnah taci gaba da tafiyar da karatun ta cike da nutsuwa sai abu guda da yake cin ranta yake dagula mata lissafi shine UK ya matsantawa rayuwanta da yawa duk inda ta shiga sai ya bita kuma daya ganta ba maganar arzikin da zai furta mata sai masu ciwo arai.

Yau ma kamar kullum ta shigo cikin skul d'in sanye da doguwar riga yellow an mata aiki sa stones red color masu d'aukan ido don haka tai amfani da red d'in mayafi wajen yin rolling d'in kanta k'afanta sanye da takalmi red da jaka red, kallo d'aya zakai mata ka Tabbatar da ainihin kyan da tayi masha Allah.

Tafiya take cike da nutsuwa da kamun kai irin na d'aliban da addini ya ratsa su.

hon d'in motan dake bayanta ne ya isheta don haka ta juya don ganin waye yake son rikita mata kwanya haka,
Caraf idonta ya fad'a cikin na UK yana mata wannan banzan kallon nashi me cike da izza da jin kai, a hankali tai k'asa da idonta tare da Kau da kai gefe tana jin wani b'acin rai aranta.

Tsawon tafiyar da tai daga bakin gate d'in zuwa inda zatai lecture UK bai fasa bin bayanta ba tare da sakar mata hon d'in motar Wanda hakan yai sanadiyar jan hankalin dukkan wanda ke bin hanyar kanta.

Sanin halinsa da d'aukacin d'aliban sukai yasa hakan bai zama bak'on abu agunsu ba, sun sanshi d'alibi ne mai d'aukar magana da maida mace ba abakin komai ba,kai tsaye sun san tsokananta yake yana son watsa ta.

Jiki babu k'wari ta k'arasa hole d'in tana shiga ta zauna zuciyanta na bugawa don b'acin rai, ko sallama batai wa d'aliban dake zaune gefanta ba wanda wannan ba d'abi arta bace kai bama d'abiar duk wani d'alibin Arabic bane.

Tun shigowarta suka fahimci akwai damuwa tare da ita amma ba Wanda ya tanka mata kasancewar Malam ya fara darasi.


Babu abinda ta tsinta cikin lecture d'in har malamin ya fita, ahankali taji Hafsah ta dafa kafad'anta tana fad'in
"Khadeejah ya akayi ne na ganki so silent?"

Sharrrr hawaye ya fara bin kumatunta don dama kad'an take jira tai kuka,

"Subhanallah Khadeejah meke faruwa haka ko baki da lfy ne?"

Kuka sosai take kamar wadda akaiwa mutuwa, abinda ya tayar da hankalin Hafsah matuk'a ta shiga rik'e hannunta tana jijjigata, abinda yaja duka hankalin matan dake ajin suka shiga Tambayar lafiya meya faru.

Ganin mutane sun cika kanta yasa tai k'ok'arin tsaida kukanta ta share hawayen,
Nasiha suka rink'a mata akan kome ke damunta ta barwa Allah ta daina kuka haka, gyad'a Kai kawai tai ba tare da ta furta komai ba.

Kusan 5 minutes suna zaune gun ita da Hafsah ta sauke ajiyan zuciya tare da furta" Hafsah me na tsarewa wannan mutumin yake takura rayuwata me namishi?"

Kallon ta Hafsah tai cikin rashin fahimta tace "Waye ne Khadeejah?"

"Mutumin nan daya takura min a skul d'innan,_ yau tun daga bakin gate yake bina da horn har bakin hole d'in nan, Hafsah biki ga yanda mutane ke kallona ba kamar nayi lefi. . ."

Ta k'arashe maganar tana matse k'wallan da ya k'ara taruwa a idonta.

Shiru na d'an lokaci ya shiga tsakaninsu daga bisani Hafsah tace " kiyi hak'uri Khadeejah ki cire wannan mutumin aranki, duk abinda zai miki karki sa damuwansa cikin zuciyarki,irinsu suna da yawa marasa mutunci kinga maybe ma shi yanzu ya manta ya miki hakan ke ya barki da damuwa."

"Hafsah biki San yanda na tsani kallo ba, duk yanda muke da mutum ban so ya fiye kallo na amma yau mutumin nan yaja min tarin idanuwan jama'a akaina kamar nayi lefi."

Ruk'o hannunta Hafsah tai tana fad'in " Tashi mu tafi kiyi hak'uri ki bar batun nan kinji."




**********************
Kwanaki da yawa sun shud'e yayin da karatun su Nahnah yai nisa sun fara shirin fara exam na first semester N.C.E one, ta maida hankalinta sosai kan karatun ta don ita bamai wasa bace kan harkar karatun ta.


Damuwanta d'aya ne UK a kullum k'ara matsawa rayuwarta yake ba sassauci duk wani motsin Hafsah akan idonsa yake, abin haushin kuma ba wai fa yana sonta bane a'a kawai kullum burinsa ya ganta ya musgunawa rayuwarta da bak'ak'en kalamai wai yana fad'in tunda ya nuna da farko yana ra'ayinta ta watsa mai k'asa a ido ta watsashi to shima sai ya rama da babban wulak'anci agareta.

Yau zasu fara da exam d'in Education 111 Wanda za'a shiga k'arfe goma.

Tun k'arfe Tara saura kwata tazo skul d'in kai tsaye (ุงู„ู…ูƒุชุจุฉ) library ta wuce don taci gaba da duba hand out nata.

30 minutes ta samu cikin ู…ูƒุชุจุฉ d'in ta fito zuwa inda zasuyi exam d'in don ta sami waje me kyau,

Ta kusa daf da lecture Theater d'in taji ana bin bayanta kamar za'a taka mata takalmi da sauri ta tsaya cak ba tare data wai waya ba don jikinta ya bata ko waye, ilai kuwa muryanshi ya daki dodon kunnanta " ke villager girl yau kuma saurin me kikeyi haka, ho har college d"in ta fara bugarki naga an daina yangar da yauk'in"

Tsit bata bashi amsa ba yaci gaba " ke ko muguwar gidahuma ce a haka dai gashi jiki ya karb'i gayu amma cikin kan sai duhun jahilci taf, sai anyi batu kuce wai Ku y'an ARABIC ustazai, me ake da macan Arabic medium babu komai a tare da ita sai duhun kai da rashin wayewa, duk gayu da iya kwalliya irin na macan Arabic inka latsata ba wayewa, banza tsami kawai ware ki bawa mutane waje."


A kasalance ta d'aga k'afarta ta tafi zuciyanta kamar zata fito idonta duk ya kawo ruwa.



Please Login or Register in order to submit comment