Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tara ne d'auke da sunan "Blvd Kausar" a jiki, juyowa Inspector yayi ya kalle su baki d'aya yace
"Ko kunsan wa take nufi da "Blvd Kausar"?" jiki na rawa Alhaji Bala yace
"Itace yarinyar, itace muka samu akan gawar ta" wani murmushin gefen baki Inspector yayi yace

"Ko kunsan kisan A'ishah za'a iya alak'anta shi da Kausar?"
"Kausar kuma?" suka tsinto maganar Hajiya Zainab cikin disashshiyar murya, juyowa Inspector yayi yace
"K'warai kuwa Hajiya" rinannun idanun ta ta d'ago tana kallon sa tace
"Ban fahimce ka ba" tattara hankalin sa Inspector yayi ya mayar kan Hajiya Zainab yace
"Wayar A'ishah ta nuna Kausar ta kira ta da misalin k'arfe 7:45 na dare ita kuma A'ishah ta kira Kausar da misalin k'arfe 9:15 na dare. Idan kika lura da gawar A'ishah.." ya juyo ya kalli gawar A'ishah sa'annan yace "Zaki tabbatar an dad'e da kisan, kuma fa kinsan A'ishah ba wanda yake tsammanin dawowar ta a cikin daren, shin me Kausar ta gaya mata a wayar da suka yi? Allah ne kad'ai masani wanda kuma yayi daidai da shigowar b'arayi a cikin gidan..." tuni Hajiya Zainab ta bud'e wani babin kuka tana fad'ar
"Kausar kin cuce mu kinci amanar mu" da sauri Inspector ya katse ta yace
"A'a a'a Hajiya! Bamu tabbatar da hakan ba zargi muke yi yanzu ina k'ok'arin nuna miki it's such a big coincidence, zata yiwu kuma Kausar bata da hannu a wannan kisan but zata san wani abu akai she's a witness to the crime" kuka Hajiya Zainab keyi wiwiwi yayin da Goggo Hadiza ta dask'are a wurin kamar ba ta shi kuwa Alhaji Bala har ga Allah yaji dad'i sosai don kuwa tunanin Inspector yayi daidai da abunda yake shirin aikatawa, juyowa Inspector yayi ya kalli Alhaji Bala yace "Yanzu ina kake tunanin zamu samu Kausar?" numfashi Alhaji Bala ya saukar yace
"Nafi zaton ta a gidan iyayen ta"
"Ina ne?" cewar Inspector
"Sabon titi" jinjina kai Inspector yayi yace
"Ina tabbatar muku zamu yi iyakar k'ok'arin mu dan ganin mun bankad'o ko wa yake da hannu a wannan badak'alar, idan kuma har bincike ya tabbata akan Kausar then I pray may God have mercy on her coz the Nigerian Police won't have none" ya juyo kan Alhaji Bala yace "Zaku iya shirya gawar a kaita makwancin ta, Allah ya ji k'an A'ishah" jinjina kai Alhaji Bala yayi had'i da cewa
"Ameen" yayin da 'yan sandan suka sa kai suka fice daga d'akin Alhaji Bala ma ya rufa musu baya aka bar Goggo Hadiza da Hajiya Zainab wacce ta fad'i k'asa kwance sai kuka take tana birgima.







*Shawty*💕
[1/8, 11:06 AM] ‪+234 813 551 5123‬: *BARR. BASSAM*
(The Gallant) ❣



By *Shawty*💕

*PURE MOMENT OF LIFE WRITERS*
(We don't just entertain and educate, we also touch the hearts of the readers.)

Zaku iya samun kowane Novel na PML through these links
#WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
#IG PML WRITERS
#https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
#http://maryamsbello.blogspot.com


*2017*

2⃣3⃣


Kausar wacce tun da ta fita gidan ba abunda take sai gudu haka duk inda ta ratsa mutane da irin wannan gudun mutane zasu yi tunanin ko wani abun ne ke bibiyar ta a baya, haka zasu zura ido amma ba zasu ga kowa ba. Haka tai ta fanfala gudun ita kanta bata san ina ta dosa ba gudun kawai take.


Tuk'i yake cikin kwanciyar hankali music na flowing a motar yana kad'a kai yana bin wak'ar bai ankara ba sai hango ta yayi zata tsallaka titi duk iyakar k'ok'arin sa sai da yayi don ganin ya taka birki amma abun yaci tura saboda from nowhere haka ya ganta kamar daga sama
"Who's this bloody fool?" ya fad'a a fili kuuuu! K'arar taka birkin amma inaa sai da ya gabje ta sai ga Kausar k'asa. Bassam wanda ke tuk'a motar dukan stiring yayi da k'arfi yace "Holy shit!" had'i da tsayawa cik. Da yake safiya ce mutane basu fara bazuwa kan titi sai wa'anda ba za'a rasa ba suka taso da gudu suka zo kanta had'i da zagaye ta, da sauri Bassam ya bud'e murfin motar ya fito ba komai a jikin sa sai pyjamas da wata 'yar k'aramar t-shirt sai halve shoes. Cikin tafiyar sa ta k'asaita ya kawo wurin, haka mutane sukai ta darewa ana bashi hanya har yazo daf da inda take kwance unconscious tsugunawa yayi kan k'afafun sa yana kallon fuskar ta yayin da gefen kanta ya d'an fara bleeding, da sauri ya mik'e had'i da cewa mutanen dake wurin
"Ina zamu samu clinic nan kusa?" mamaki ne ya kama wasu daga cikin su don basu ma yi zaton yana jin hausa ba sai dai kuma hausar gata nan dai gwaranci-gwaranci haka kamar dai bai k'ware ba, wani d'an saurayi da ba zai wuce shekara ashirin ba yace ya sani Bassam ya rok'e sa akan yazo ya nuna masa wurin, jiki na rawa d'an saurayin yace ba matsala a haka Bassam ya duk'a ya d'auko ta cak irin bride-like d'innan yayi ma saurayin nuni da ya bud'e masa bayan motar da sauri ya bud'e masa ya kwantar da ita a back seat ya rufe ya sake yiwa saurayin nuni da ya shiga su tafi da sauri dukansu suka bud'e motar suka shiga Bassam yaja yayin da saurayin ke nuna masa hanya har suka iso wata private clinic.


Isar su ne fur suka k'i karb'ar ta a cewar su dole sai an zo da d'an sanda ba yanda Bassam bai yi ba ganin yadda bleeding d'in nata ke k'aruwa haka ba yadda ya iya suka sake shiga motar shi da d'an saurayin suka nufi Police Station ya gabatar musu da kansa yai musu bayanin abunda yake faruwa, ba b'ata lokaci aka had'o sa da 'yan sanda guda biyu suka sake komawa clinic d'in anan take a kai admitting nata. Sai da ya sallami 'yan sandan da yaron sa'annan ya koma d'akin da aka kwantar da ita, ba kowa a ciki sai likitan da ke tsaye a kanta, k'arasowa Bassam yayi cikin d'akin had'i da tambayar yaya jikin ta damuwa k'arara a fuskar sa, murmushi likitan yayi ya tabbatar masa ba wani internal injury sai bleeding da tayi shima sun tsayar dashi don kuwa ga bandage nan a gefen goshin ta had'i da drip da jini da aka saka mata ya tabbatar masa zata d'an jima tana bacci don kuwa tana buk'atar hakan, godiya Bassam yayi yayin da likitan ya juya ya fita shi kuma yaja kujera da take fuskantar ta ya zauna.


Sai a lokacin ne yake k'are mata kallo cikin ransa yace
"Very young and innocent" shuru yayi yana ta kallon ta yayin da fuskar ta shar kamar ba abunda yake damun ta sai bacci take.



_9:00am_
Har wannan lokacin zaune yake a gaban ta amma yanzu kansa na a wayar sa yana danne-danne shigowar kira a wayar sa ne ya dakatar dashi daga abunda yake ganin Mammy ce ke kiran sai a lokacin kuma ya tuna duk abunnan dake faruwa bai sanar da ita ba da sauri ya d'aga kiran, daga d'aya b'angaren Mammy ta fara tambayar sa
"Bassam kana ina ne?"
"I'm just out for a ride sai kuma aka samu matsala"
"What? Me ya faru?" cewar Mammy cikin tsoro
"No mom ba wani big deal bane I just hit a girl yanzu haka muna asibiti"
"Inna lillahi! Shine kuma ba zaka sanar dani ba?"

"I'm sorry" ya fad'a a sanyaye
"It's ok" cewar Mammy "I will be on my way right now wacce asibiti ce?" da sauri Bassam yace
"No mom ba sai kinzo nima yanzu zan dawo gida ne nayi wanka"

"Ya zaka barta all by herself ita kad'ai?" cewar Mammy cikin sigar fad'a haka
"Tana bacci ne kuma akwai enough Nurses da zasu kula da ita"
"It's all right" cewar Mammy had'i da katse kiran, mik'ewa yayi tsaye sai da ya k'ara kallon ta sa'annan ya juya ya fita ya sanar da Nurses d'in zai je ya dawo har suna had'a baki wurin amsa masa da toh don kuwa ba kad'an ba yai musu k'warjini, da sauri ya fito ya nufi parking lot ya shiga motar sa yaja zuwa gida.


Isar sa gida ne ya samu Mammy a dining tana breakfast kujera shima yaja ya zauna ta fara tambayar sa ya me jikin yake sanar da ita da sauk'i sosai, daidai lokacin ne wayar ta ta fara ringing ganin wanda ke kiran ne yasa ta fara murmushi had'i da d'aukar kiran, kuka ne ta jiyo cikin wayar da sauri tace
"Hajiya Zainab lafiya kuwa?"
"Ba lafiya Barrister an kashe A'ishah!" ta fad'a cikin kuka yayi daidai da Bassam ya mik'e zai bar parlorn, zumbur Mammy ta mik'e tsaye ta fara maimaita kalmar shahada yayin da Bassam ya tsaya cak had'i da juyowa yana kallon Mammy wacce tayi tsaye sororo rik'e da waya ta kasa tab'uka komai, tambayar ta yayi lafiya amma sam bata ji shi ba sai da ya tako yazo gaban ta had'i da d'an girgiza ta, da sauri ta kalle sa ya k'ara tambayar ta lafiya ajiyar zuciya tayi ta tuna masa da 'yan matan da suka zo gidan the other day har suka gaisa da d'aya daga cikin su toh itace aka kashe jiya da dare, sam Bassam bai tuna komai ba akan Kausar ce d'ayar kuma itace ya buge da mota, jajantawa Mammy yayi don yaga gaba ki d'aya hankalin ta ya dugunzuma sa'annan ya juya ya bar parlorn, ta dad'e a tsaye a wurin sa'annan itama ta nufi bedroom tayi wanka had'i da shiryawa cikin bak'ar jalabiya kamar kullum ta fito parlorn yayi daidai da shigowar Bassam shima cikin k'ananan kaya yayi kyau sosai nan take gaya masa zata je office ne daga chan kuma zata wuce gidan mutuwar idan ta gama da sauri zata zo taga yarinyar a asibiti, tare suka fito kowa ya shiga motar sa yaja ya kama hanyar sa.



*Wasu daga cikin groups da nike ciki zaku ji ni shiru but here are my digits 07069602381 duk wacce ke neman cigaban labarin ta neme ni PC. Nagode.*



*Shawty*💕
[1/8, 11:17 AM] ‪+234 813 551 5123‬: *BARR. BASSAM*
(The Gallant) ❣



By *Shawty*💕

*PURE MOMENT OF LIFE WRITERS*
(We don't just entertain and educate, we also touch the hearts of the readers.)


Zaku iya samun kowane Novel na PML through these links
#WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
#IG PML WRITERS
#https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
#http://maryamsbello.blogspot.com


*2017*

2⃣4⃣

_4:30pm_
Da misalin k'arfe hud'u da rabi na yamma Bassam ne da Jabir wanda yanzu ya zama tamkar aboki wa Bassam zaune suke kan kujeru gaban gadon da Kausar ke kwance har yanzu bata farka ba gashi basu san yadda za'ayi su sami iyayen ta abunda kawai ya rage musu shine su jira har lokacin da ta tashi.


Jabir ne yayi noticing yatsan ta na dama ya fara motsi da sauri ya tab'o Bassam ya fara nuna masa, tsayawa suka yi cak suna kallon ta a hankali idanun ta suka fara motsi kamar zasu bud'e sai kuma suka tsaya daga motsin, wani razanannen ihu ta fasa had'i da tashi zaune tana kiran A'ishah, sakamakon jikin ta ba k'wari yasa ta koma kan gadon jagwab ta kwanta ta cigaba da ihun kiran sunan A'ishah still idanun ta a rufe gam ga hawaye sun gangaro daga idanun. Bassam da Jabir wanda tun lokacin da ta fasa ihun suka mik'e tsaye sai kallon ta suke cike da mamaki, a hankali Bassam ya k'ara jawo kujerar ya zauna gab da gadon ya had'a hannun sa da nata d'ayan kuma ya d'ora shi akan goshin ta fuskar sa d'auke da murmushi yace
"Hey" a hankali ta fara bud'e idanun ta har suka bud'e gaba d'aya suka sauka akan Bassam, murmushi yai mata a hankali ta juya idanun ta zuwa Jabir wanda yake a tsaye tana k'arewa d'akin kallo sai kuma ta lumshe idanun ta abunda ya faru tun tashin ta da safe har zuwa lokacin da aka buge ta da mota ne ya fara dancing mata a brain, dafe kanta tayi da taji ya sara kamar zai fashe ta fashe da kuka tana kiran sunan A'ishah, tausayi ta bawa Bassam ya k'ara dafa kanta yace "Sannu ko?" sa'annan ya juyo ya kalli Jabir yace "Kira Doctor please" sa'annan ya juyo kanta cike da kulawa yace "How are you feeling now?" bata ce dashi uffan ba sai kukan da take ta rizga daidai lokacin ne Jabir ya shigo tare da likitan. Duba ta yayi sa'annan yace zata iya cin abinci had'i da cire mata jinin da ake sa mata sa'annan ya fice, da sauri Bassam ya jawo ledar abincin da suka siyo suka zo ya fara bud'ewa wuf ta tashi zaune duk da cewar jikin ta ba k'wari ta fincike drip d'in dake hannun ta ta fara k'ok'arin mik'ewa tsaye da sauri Bassam ya rik'o hannayen ta yana yayi k'ok'arin maida ta zaune yace "Hey! Ina zaki je ne?" fisge hannayen ta tayi ta daka masa tsawa kamar ba mara lafiya ba tace
"Get your goddamn filthy hands off me" sororo Bassam da Jabir suka tsaya suna kallon ta yayin da ta cigaba da k'ok'arin mik'ewa, cikin yardar Allah kuwa ta samu ta mik'e sai dai jirin da take gani kamar zata fad'i ta dafe kan ta fara tafiya a hankali ta nufi hanyar fita, da sauri Bassam ya sha gaban ta yace
"Hey! Ina.." bata bari ya k'arisa ta sake daka masa tsawa tace
"The second ka k'ara tara na zaka sha mamaki" shuru Bassam yayi yayin da sai harara take zabga masa chan suka tsinto muryar Jabir yana cewa
"Let her please baka san ko wacece ba" juyowa dukan su suka yi suna kallon sa Kausar tai masa wani gajeren murmushi tace
"Better" tasa kai ta fita, tafiya take har tana had'awa da gudu tana layi kamar 'yar maye tana rik'e da kanta bata had'u da kowa ba har ta kawo bakin gate d'in asibitin ta fice, da sauri Bassam da Jabir suka fito amma ko alamar ta basu gani ba da gudu-gudu Bassam ya isa parking lot ya shiga motar ya tsaya wa Jabir ya iso ya bud'e motar ya shiga yaja suka nufi gate d'in suka fito, bakin gate d'in suka ganta durk'ushe da sauri Bassam ya samu wuri yayi parking ya fito da sauri ya nufi wurin ta da sauri shima Jabir ya bud'e motar ya fito ya biyo bayan sa yana kiran sunan sa
"Bassam! Wait!" cak Bassam ya tsaya ya juyo yana kallon Jabir, k'arasowa Jabir yayi kusa dashi yace "I think kawai mu tafi Bassam you have no idea who she is you can't trust anyone these days" murmushi kawai Bassam yayi yasa kai ya nufi wurin da Kausar take durk'ushe, jin alamar akwai wani tsaye a kanta ne yasa ta d'ago jajayen idanun ta tana kallon sa zumbur ta mik'e tsaye ta fara masa masifa
"Wanne irin mutum ne kai? Are you woefully deaf?" murmushi Bassam yayi yace
"No, my hearing is just fine"
"Good, ka tafi" ta fad'a tana nuna masa hanya, murmushi ya k'ara yi yace
"Listen to me kid, you are barely on your feet ba kya da strength da zaki iya tafiya plus I just wanna help" shuru tayi ta zuba masa jajayen idanun ta tana kallon sa cikin sanyin murya yace "I will give you a lift zan kaiki inda zaki je Ok? Daga nan zan kama gaba na" cikin disashshiyar murya tace
"No, my feet work just fine" murmushi yayi da yaga yanzu ba cikin tsiwa tayi maganar ba, lallashin ta ya shiga yi har ya samu ta yarda zata bisu. Da kansa ya bud'e mata bayan motar ta shiga ta zauna ya rufe da sauri ya juya ya koma gefen driver ya shiga shima Jabir ya shiga yaja suka tafi.



Tafe suke tana nuna masa hanya har suka iso unguwar, unguwar k'ananan mutane ce ba irin manyan gine-gine har aka zo daidai kwanar gidan su gaban ta ne yayi mummunan fad'uwa da ta hango motar 'yan sanda a bakin k'ofar gidan su jikin ta ne ya shiga kyarma tana karanto inna lillahi wa inna ilayhi raji'un, Bassam wanda sai kallon ta yake cikin front mirror na motar yaga tun lokacin da suka shigo kwanar hankalin ta ya tashi chan ya tsinto muryar ta tana cewa
"Ya isa haka" taka birki yayi tun kafin motar ta k'arisa tsayawa Kausar ta fito, hango Amman ta da Abban ta tayi tsaye tare da 'yan sandan sai magiya suke musu suna kuka rugawa tayi da gudu taje ta k'ank'ame Amma tana wani irin kuka, d'aya daga cikin 'yan sandan wanda ke rik'e da hoto a hannun sa ya kalli hoton then back to Kausar nan take ya bawa d'aya daga cikin 'yan sandan umarni yayi cuffing hannuwan Kausar. Wani azababben kuka Kausar ta fashe dashi tana ihun ba ita ta kashe ta ba amma inaa ko sauraren ta basu yi ba suka saka mata ankwa a hannu suka saka ta a motar suka tafi.



Kuka take wane ranta zai fita tana kiran Amma da Abbah amma inaa haka suka ja motar suka yi gaba da ita. Amma wacce ta fad'i a wurin sai kuka take gwanin ban tausayi yayin da Abbah ke tsaye a wurin yana kai komo sai hawaye ke ambaliya a fuskar sa. Bassam da Jabir tsaye suke k'yam duk abunda ya faru akan idon su jiki a sanyaye Bassam ya juya ya kalli Jabir yace

"I think something fishy is happening right there" bai jira abunda Jabir zai ce ba ya taka ya nufi wurin su.



*Wasu daga cikin groups da nike ciki zasu ji ni shiru here are my digits 07069602381 duk wacce ke san cigaban labarin ta neme ni PC. Nagode.*



*It'z Shawty*💕
[1/8, 1:54 PM] ‪+234 813 551 5123‬: *BARR. BASSAM*
(The Gallant) ❣




By *Shawty*💕

*2017*

2⃣5⃣

K'arisawa Bassam yayi wurin su had'i da yin sallama, Abba ne kawai ya ji sa yayin da Amma sai kuka take wane ranta zai fita, hannu Abba ya mik'awa Bassam suka gaisa sai kuma Bassam ya rasa ta ina zai fara. K'ara gyara tsayuwar sa yayi ya zura hannun sa d'aya cikin aljihu d'ayan kuma yana rik'e da shantaleliyar wayar sa, cike da tausayi ya kalli Abba wanda har yanzu sai sharar hawaye yake yace
"Me yake faruwa ne?" kallon sa Abba yayi tsaf sa'annan yace
"Samari waye kai kuma daga ina?" rufe bakin sa keda wuya Bassam yace
"Suna na Barr. Muhammad Bassam Muhammad" kallon sa Abba yake yana mamaki yace
"Samari me yake tafe da kai?" koro masa labari Bassam yayi tun lokacin da ya buge Kausar da mota har zuwa lokacin da suke tsaye a wurin sa'annan yace
"Meyasa 'yan sanda suka tafi da ita? Me ta aikata?" hawaye suka ciko idon Abba ya jawo hannun Bassam had'i da cewa
"Mu shiga daga ciki" ba musu Bassam ya bi sa tare da Amma da Jabir cikin gidan, tun da ya shiga cikin gidan tausayin su ya kama sa yana tunanin wacce kalar rayuwa ce suke yi a cikin wannan kufai. D'aki Amma ta shiga ta d'auko tabarma ta malala a k'ofar d'aki, Abba ya juyo ya kalli Bassam da Jabir yace "Bismillah" ba musu suka zauna kan tabarmar sa'annan shima Abba ya zauna yayin da Amma ta d'auko kujera 'yar tsuguno ta zauna daga gefe. Gyaran murya Abba yayi ya fara basu labarin rayuwar su tun farko wani wurin ya tsaya yayi kuka sosai wani wurin kuma ya zubda hawaye har zuwa had'uwar su da Hajiya Zainab da irin taimakon da tai musu da komawar Kausar gidan har zuwa jiya da tazo take sanar dasu tana ji a jikin ta wani abu mara kyau zai faru. Tun da ya fara basu labarin Bassam ke tausaya musu sosai dama shi mutum ne mai matuk'ar tausayi gefen Jabir ma abunda ya faru dashi kenan. Shuru suka yi dukan su sa'annan Abba yace "D'azu muna zaune muka ji tsayuwar mota a k'ofar gida sai ga 'yan sanda, da farko bamu tsorata ba saboda bamu kawo komai a ranmu ba. Suka fara da tambayar Kausar muka ce bata nan ba b'ata lokaci babba daga cikin 'yan sandan ya bada umarnin a shiga ko ina a bincika haka suka shiga suka bincike gidan kaf basu ganta ba, a lokacin ne yake sanar damu ana zargin Kausar da kisan A'ishah 'yar gidan Alhaji Bala, mun tsorata da jin maganar ba kad'an ba sa'annan ya shaida mana idan har bamu fito da Kausar ba suka dawo to ba makawa dani zasu tafi har sai sun same ta" daidai lokacin ne ya fashe da kuka abun tausayi, tun lokacin da ya fara bada labarin Bassam ya gano kisan A'ishah ne mahaifiyar ta ta kira Mammy take sanar da ita sai lokacin ya tuna inda yasan Kausar wato ranar da suka je gidan su. Shuru yayi sa'annan shi da Jabir suka shiga rarrashin su da basu baki akan su yi hak'uri cikin hikima Bassam yace

"Kuna tunanin Kausar zata iya kisan kai?"
"Wallahi Kausar ba zata iya kashe kowa ba balle A'ishah wacce suka shak'u da ita" haka suka tsinci muryar Amma cikin kuka tana fad'a "Sharri ne kawai dan anga bata da gata" sai kuma tasa fuskar ta cikin hijab ta cigaba da rusa kuka. Kallon Bassam Abba yayi yace
"Kausar ba zata iya kashe kowa ba ina tabbatar maka da haka" shiru Bassam yayi yana jinjina maganganun su yace
"Ku kwantar da hankalin ku in shaa Allah ba abunda zai sami Kausar zanyi iyakar k'ok'ari na wajen kub'utar da ita" har cikin ransu sunji dad'in maganar Bassam, cike da jindadi Amma tace
"Mun gode mun gode sosai Allah ya saka maka da alkhairi ya kuma shige maka gaba" da

"Ameen" suka amsa baki d'aya sa'annan Abba ya k'ara kallon Bassam sosa yace
"Amma dai yaro kai ba bahaushe bane ba ko?" sakamakon yadda yaji hausar tasa a diririce haka da alama turanci ya rigaya ya karya harshen sa, murmushi sosai Bassam yayi yace
"Sosai kuwa ni bahaushe ne Abba" har ga Allah Abba yaji dad'in yadda Bassam ya kira sa da "Abba" shi kuma Bassam ya kira sa da Abban ne kamar yadda yaji Kausar ta kira sa dashi kafin a tafi da ita. Kallon sa Abba yai tayi sa'annan yace

"Amma kafi kama da turawa" nan kam dariya ya basu shi Jabir sai a lokacin Jabir ya sako bakin sa ya fara basa labarin Bassam ya dad'e ne a k'asar waje shine sanadiyar gurb'acewar hausar sa gyad'a kai Abba yayi yace
"Haba! Biri yayi kama da mutum ne!" dariya suka yi gaba d'aya sa'annan suka mik'e tsaye shi da Jabir, Bassam ya k'ara basu tabbacin zai yi iyakar k'ok'arin sa godiya suka shiga yi masa me tarin yawa sa'annan suka nufi hanyar fita, har k'ofar gida Amma da Abba suka rako su yai masu alk'awarin zai sake dawowa bada dad'ewa ba, k'ara gode masa suka yi sa'annan suka juya suka tafi.




Tun da suka shiga motar ba abunda suke labari sai halin da Amma da Abba suke ciki da haka har suka iso unguwar su Jabir yayi dropping nasa akan gobe zai zo ya d'auke sa suje su nemi Police Station da aka kai Kausar sakamakon yanzu maghrib ake nema, da haka suka rabu da Jabir Bassam yaja motar sa ya nufi gida.


Shigar sa gidan ya hango motar da Mammy ta fita da ita alamar ta dawo kenan, wuri ya

Please Login or Register in order to submit comment