Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

jini zaka biya ni" da sauri Alhaji Bala ya fara tattare fuskar sa hadi da cewa
"Jinin wa kenan?"
"Jinin ka ko na 'yar ka A'ishah wanne zaka bani?" cikin fushi Alhaji Bala yace
"Ba ko daya" wata mahaukaciyar dariya Alhaji Kabara ya ɓarke da gami da cewa
"Ƙarya kake Bala dole sai ka bani jinin ka ko na 'yar ka a matsayin diyyar 'yata da ka kashe" cikin fushi Alhaji Bala ya ƙariso yazo daf da Alhaji Kabara suna fuskantar juna sosai
"Bana kulafucin sulhu dakai Kabara, ka dauki fansa kan yara na da suka kashe 'yar ka ba akan 'yata ba da batada hannu a wannan al'amari idan ba haka ba zan hukunta ka" wata mahaukaciyar dariya Alhaji Kabara ya sake fashewa lokaci daya shima ya murtuƙe fuska kamar wanda aka aikowa mutuwa yace
"Ni 'yata tana da hannu ne a hukumar EFCC da zata yi bincike akan ka? Ayyah Bala da me zaka hukunta ni? Da kudi ko me? Ka shirya kashe su duka don tsiratar da ran 'yar ka don ba zan taɓa samun sukuni ba har sai na dauki fansa" a hankali ya juyo zuwa ga malamin yace "Kai kuma ina so ka zama dan kallo a wannan tafiyar, na barku lafiya" a hankali ya juya ya kama hanyar ficewa daga parlorn.



Shuru suka yi dukansu kowa da abunda yake saƙawa a ransa, a sanyaye Alhaji Bala ya juyo yana kallon malam, shima malamin shi yake kallo sa'annan yayi ajiyar zuciya yace
"Kaji fa abunda yake ikirarin aikatawa Bala, nasan Alhaji Kabara sosai tabbas ba barazana ce yake yi ba, kuyi ƙoƙari kuyi sulhu kadda ku bari wannan gabar ta cigaba" kallon sa kawai Alhaji Bala keyi
"Muyi sulhu fa Mallam? Inace anan yake fadar sulhu daya ne shine na bayar da jini na ko na 'yata a matsayin diyyar tasa 'yar wanda yake daidai da na bada rayuwa ta in bar duniyar da ban gama jin dadin ta ba? Ko kuwa 'yar tawa kacal? Ba zata taɓa saɓuwa ba" shuru suka yi lokaci daya kowane da tunanin da yake yi, iska Alhaji Bala ya furzar daga bakin sa gami da cewa "Kayi iyakar ƙoƙarin ka ka shawo kan abokin ka kada wani abu ya samu 'yata idan ba haka ba sai dai wannan abun ya zama silar tonon asiri garemu" yana gama fadar haka shima ya juya da hanzari ya fice daga parlorn suka bar malamin sororo tsaye a wurin.



Tuƙi Alhaji Bala keyi amma sam hankalin sa baya jikin sa, tunani ne kala-kala ya cunkushe a ƙwaƙwalwar sa. To ya haƙura ya bar duniyar da be gama jin dadin ta ba a matsayin musaya da rayuwar A'ishah ko kuwa ya bayar da 'yar tasa daya tal ne wacce duk wannan fadi tashin akanta yake yi don kawai yaga ya kyautata rayuwar ta? Duk fa wannan arzikin ita kadai yake tarawa to kuma idan ya bayar da ita shi kuma ya mutu kenan aikin sa ya tashi a banza kenan don kuwa wasu ne from nowhere zasu zo su wawashe dukiyar sa bayan ya sayar da lahirar sa don kawai A'ishah taji dadi, girgiza kai ya shiga yi duk uban a.c dake akwai a motar bai hana sa tsiyayar da zufa ba kamar wanda yayi fada da zaki, tunani barkatai yake yi marasa amfani ba tare da samun wata mafita ba da haka har ya iso gida.






*It'z Shawty*💕
[1/7, 7:29 PM] ‪+234 813 551 5123‬: *BARR. BASSAM*
(The Gallant) ❣




By *Shawty*💕

*2017*

0⃣9⃣

Shigowar Alhaji Bala cikin gidan yayi daidai da shigowar Barr. Hindu itama, kusan lokaci daya suka yi parking ko ba'a gaya mata ba tasan wannan shine Alhaji Bala mijin Zainab Bature wanda take bata labari.


Sanye take cikin baƙar abaya sai dankwalin abayar da ta yane kanta dashi da kuma farin glasses a fuskar ta sai baƙar handbag. Da fara'a ta ƙariso kusa dashi sam bai santa ba don kuwa duk a ƙawayen Zainab bai taɓa ganin ta ba.


Kallon ta kawai yake cikin ransa yace _wannan kuma fa? Ko Kabara ne ya aiko ta?_ tsayawa kawai yayi yana kallon ta har tazo kusa dashi tace
"Barka da dawowa Alhaji"
"Yauwa sannu" ya amsa mata a taƙaice
"Nace idan ba nayi ɓatan kai ba nan ne gidan Alhaji Bala ko?"
"Eh nan ne"
"Nazo ne wurin Hajiya Zainab tana nan kuwa?"
"Eh da yake nima yanzu ne dawowa ta amma ina tsammani ba inda taje"
"Ok"
"Ƙariso mana" yace da ita, murmushi kawai tayi ya shige gaba tana biye dashi har cikin parlorn, da sallama dukan su suka shiga. Hajiya Zainab ce da A'ishah kawai zaune a tangamemen parlorn suna kallo, miƙewa Hajiya Zainab tayi da fara'a ta tarbe su tana cewa
"Ah! Dama Alhaji tare kuke da Barrister?" dummm! Yaji gabansa ya fadi hadi da saurin waigowa ya ƙars kallon Barr. Hindu cikin ransa yace _me kuma ya kawo lawyer a gida na?_ dariyar yake yayi hadi da kauda kansa daga Hindu gami da cewa
"Eh tare muka shigo kuma da dukan alama baƙuwa ce" murmushi Hajiya Zainab tayi hadi da dan rausayar da kai
"Ƙawata ce tun secondary school Allah bai sake hada mu ba sai kwanaki da suka wuce sunan ta Barr. Hindu Alhassan lawyer ce me zaman kanta" _relief_ ya fada a ransa hadi da ƙara kallon Hindu yace
"Allah sarki" da murmushi Hajiya Zainab ta juyo tana kallon Hindu
"Hindu wannan shine miji na Alhaji Bala" murmushi Hindu tayi suka ƙara gaisawa sa'annan ya barsu ya hau upstairs, A'ishah ce ta sauko daga kan sofa ta rusuna tana gaida ta
"Ina wuni?" murmushi sosai Hindu tayi
"Lafiya ƙalau 'yata" juyawa tayi ta kalli Hajiya Zainab
"Itace A'ishah?" nodding kai kawai Hajiya Zainab tay mata tana murmushi alamar eh, itama Hindu murmushin tayi ta juyo ta kalli A'ishah
"Wooow! Masha Allah! Tashi mana" ta dago ta zuwa kam sofa "You're so cute my daughter, ajinki nawa ne?" cike da jin dadi A'ishah ta amsa jin an kira ta cute
"SS3 muna SSCE ma"
"Good sweetheart, Allah ya bada sa'a ko?" da
"Ameen" suka amsa yayi daidai da saukowar Kausar daga upstairs din, kallon ta Hindu tayi then back to Hajiya Zainab tace
"Baƙuwa kika yi ne?" yayi daidai da isowar Kausar cikin parlorn ta rusuna ta gaida ta, fuskar ta ba yabo ba fallasa ta amsa
"Lafiya sannu" murmushi Hajiya Zainab tayi tace
"Kausar jeki ki kawo drinks da ruwa wa Barrister" da
"Toh" ta amsa hadi da miƙewa ta nufi hanyar fita, murmushi Zainab tayi tace
"Kausar da farko me taya ni aiki ce amma yanzu kam 'ya ta ce" gyara zama Hindu tayi tace
"Ban fahimce ki ba" labarin Kausar gaba daya Hajiya Zainab ta kwashe ta bawa Hindu, ajiyar zuciya Hindu tayi gami da cewa
"Gaskiya kibi sannu Zainab, 'yan aikin nan they are not meant to be trusted" dariya Hajiya Zainab tayi tace
"Ba wata matsala in shaa Allah Barrister, tun tana jinjira muke tare da mahaifiyar ta dukansu suna da kirki"
"Ki dai bi a sannu" Hindu ta sake jaddada mata, dariya Hajiya Zainab ta ƙara yi
"Barrister ko kin shinshino wani abun ne nasan aikin ku yana tafiya da predictions" dariya suka yi gaba daya yayi daidai da dawowar Kausar da drinks din ta dire su gaban Hindu hadi da miƙewa cikin sanyin jiki sakamakon wani kallo da Hindu take jifar ta dashi. Chanza hirar Hajiya Zainab tayi tace
"Barrister yaya aiki"
"Alhamdulillah, yanzu haka daga Chamber nake nace bara dai nazo na cika alƙawali" murmushi kwance kan fuskar Hajiya Zainab tace
"Ai kuwa kin kyauta naji dadi sosai, ya Bassam?" murmushi Hindu tayi unlike the other time da lokaci daya hankalin ta ya dugunzuma
"Bassam lafiya, ai shawarar ki tayi fa zaya dawo gida very soon in shaa Allah" murmushi Hajiya Zainab tayi
"Masha Allah! Allah ya dawo dashi lafiya"
"Ameen" Hindu ta amsa haka suka cigaba da hira, bata jima ba tace zata tafi haka suka yi sallama Hajiya Zainab ta rakota har bakin mota akan wata rana idan tana free zata turo A'ishah ta gaida ta a hakan suka yi sallama taja motar ta ta tafi.


******


Bayan Alhaji Bala ya barsu a parlorn kai tsaye bedroom nasa ya wuce, shigar sa keda wuya ya zaro wayar sa daga aljihu ya fara danne-danne sai kuma yasa a kunne, ringing daya a na biyu aka daga
"T.K" Alhaji Bala ya fada da ƙarfi, daga daya ɓangaren zabgegiyar muryar T.K ce ta amsa
"Na'am Alaji"
"Zaka iya tuna lokacin baya da nasa kuka samo yarinya matashiya kuka kaiwa Mallam?"
"Eh na tuna Alaji"
"Yauwa! Wacece wannan yarinyar?"
"Nima ban san ko wacece ba Alaji" nan take Alhaji Bala ya balbale sa da fada
"Don't be silly! Kamar ya kaima baka san ta ba?"
"Wallahi kuwa Alaji ban san ta ba, meke faruwa ne? Ko bata ƙarisa mutuwa bane?" ya fada cikin sigar rainin hankali
"Bana san iskanci kaji ko? By the way, a ina kuka samo ta?"
"A hanyar Sokoto zuwa Gusau ne" cikin fada Alhaji Bala yace
"What took you there? Gashi yanzu kun jawo min tashin hankali"
"Me yake faruwa ne Alaji?" tsuki Alhaji Bala yaja ya katse kiran hadi da yin cilli da wayar kan gado ya dafe kansa dake matsanancin ciwo yayi shuru, ba'a taɓa dugunzuma masa tunani ba kamar wannan karon. Haka yayi ta safa da marwa cikin dakin ba tare da ya samu wata mafita ba. Ya shafe kusan minti talatin a wannan yanayin a hankali yaji an turo ƙofar da sauri ya juyo don ganin ko waye kamar wani mara gaskiya, Hajiya Zainab ce tsaye ta zuba masa ido ko ƙiftawa bata yi a hankali ya kawar da kansa daga kallon ta, takowa tayi ta ƙariso kusa dashi
"Alhaji naji kana ta banbami a waya, lafiya kuwa?" nutsatstsen kallo ya bita dashi sa'annan ya amsa a taƙaice
"Lafiya ƙalau" nan take jikin ta yayi sanyi shuru tayi gum kamar wacce akayi wa sealing baki bata sake cewa komai ba haka shima, gajiya tayi da shirun ta fice daga dakin.


*Kuyi haƙuri da wannan and pray for me, bana jin dadi ne.*





*It'z* *Shawty*💕
[1/7, 7:37 PM] ‪+234 813 551 5123‬: *BARR. BASSAM*
(The Gallant) ❣



By *Shawty*💕

*2017*

1⃣0⃣

*Dundee, Scotland.*
Sanye yake da suit baƙi ciki kuwa long sleeve ce fara yayi zanzaro da red necktie kalar ja da ratsin fari. Tsaye yake gaban dressing mirror yana gyara zaman necktie nasa, a hankali ya miƙa hannu ya dauko turaren sa blue de channel ya feshe jikin sa dashi sai sun glasses da yasa a fuskar sa. Already dama yasa takalmi sosai yayi kyau abunka wa dogon mutum, shi kansa he can't help sai da ya tsaya yana staring at himself a mirror din, da gani dai shirin na fita ne sai dai sam fuskar sa ba fara'a a tamke take. Takawa yayi cikin tafiyar sa ta taƙama yaje wurin bedside drawer ya dauki diary dinsa dake ajiye a kai da wayoyin sa. Juyawar da zai yi ne ya ganta tsaye ƙyam tana kallon sa.


Ba kowa bace sai Hannah, his only bae. Sanye take da wata half gown baƙa iya gwiwa me dan ƙaramin hannu ta dame ta gam sai high heels. Tsayawa yayi yana kallon ta har yanzu fuskar sa tana nan a tamke, lokaci daya ya kawar da kansa ya cigaba da tafiya zuwa entrance door din wurin da take tsaye. Ganin ya kusa isowa ne yasa ta tare hanyar ta yadda ba zai iya wucewa ba, kallon sa itama take har ya kawo bakin ƙofar fuskar nan a murtuke yace
"Excuse me" bata motsa ba haka bata ce dashi uffan ba sai wani sabon salon kallon da take masa "Excuse me" ya ƙara ce da ita, a hankali tasa hannun ta duka biyu ta dan tura sa baya ta fara matsowa kusa dashi har suna jin numfashin juna
"Moh what is it?" ta tambaye sa, shima baice da ita uffan sai kallon da yake bin ta dashi uwa kurma. Ƙara matsowa tayi kamar zata shige jikin sa tace "You seem worried these couple of days. I asked you yesterday you just looked at me angrily and waved me away, I left you alone because I don't wanna make you angrier but Moh.." tace dashi very softly "I must know what's wrong" girgiza mata kai kawai yayi hadi da cewa
"I'm not feeling very well" girgiza kan itama tayi
"It's a lie Moh, you are clever I knew that. If you were unwell, you would've gone to a doctor, your body isn't sick but your mind is. I'm your only bae and I must know what's wrong" ajiyar zuciya yayi gami da jawo hannun ta suka zauna bakin gadon ya fara irga mata abunda yake faruwa tsakanin da da Mom at last ya ƙura mata ido don yaji me zata ce. Shuru suka yi dukansu na wani lokaci sa'annan tace
"We'll be going together" murmushi yayi har haƙoran sa suka fito hadi da taɓa cheeks nata
"We can't Hannah" cike da mamaki take kallon sa tace
"Why?" shima kallon ta yake yi ya riƙo kafadun ta hadi da cewa
"Look up here Hannah" dago idanun ta tayi tana kallon sa yace "This is way too complicated for you to understand, but I'm sure things will work fine. When I get there I'll try to convince.." bata barsa ya ƙarisa ba ta katse sa
"Wait.. What if they didn't?" murmushi yayi hadi da bata friendly punch
"Don't worry they'll come just as I planned" murmushi tayi ta fada ƙirjin sa ta kankame sa
"I love you Moh" hannun sa daya yasa yana shafa bayan ta
"I love you more Hannah" sun dauki almost 10mnts a wannan yanayin sa'annan ya ciro ta daga ƙirjin sa yana kallon agogon hannun sa yace "It's getting late, I gotta go"
"All right" ta fada hadi da miƙewa tsaye ta riƙo hannun sa, diary nasa ya dauko suka fice daga dakin.



*Sokoto, Nigeria.*
_9:00pm_
A'ishah ce kwance akan gado tana danne-danne a wayar ta yayin da Kausar take zaune akan gadon tana duba wasu textbooks, juyowa tayi ta kalli A'ishah hadi da cewa
"In tambaye ki mana"
"Go on" A'ishah tace ba tare da ta kalle ta ba
"Mey tsakanin ki da Al'ameen Dan Ƙasa?" dakatar da chatting da take tayi ta kalli Kausar
"Nothing! Ya akayi ne?"
"Bakomai, dazu he met me at class yake gayamin nayi warning naki coz he's gonna deal with you" dariya A'ishah tayi har da buga ƙafar ta a gadon
"Son of a bitch! Baya da hankali fa, the other day har cewa yayi zai iya shaƙe ni to death" ta ƙare maganar tana dariya
"Meyasa ne ba kya ji Eshow? Ya zaki je kina fada da namiji at the first place?" mamaki ne tsintsa ya cika A'ishah
"Ah! He started it Kausar, look I'm not the one at fault fa"
"All I'm saying ki kiyaye sa kinsan abunda ya faru tsakanin sa da Nailah dai"
"Ni Nailah ce?" ta fada questioningly
"Fine" cewar Kausar "Ku cigaba it's cool with me"
"Better" cewar A'ishah
"Careful Eshow, next time kika ƙara fada zan gayawa Daddy" dariya A'ishah ta bushe da hadi da cewa
"Toh mama na I won't" murmushi Kausar tayi tace
"Kuma.." bata bari ta ƙarisa ba tace
"It's all right please, voting muke online kina damu na fa"
"Voting kuma?"cewar Kausar
"Yeah baki da labari ne?"
"Voting mey?"
"Class of 2017 best ass mana between me and Desi girl I got 32 votes ita kuma just 12" wani banzan tsuki Kausar taja tace
"Rashin aiki bala'i ne"
"Mun ji" taɓa baki Kausar tayi ta cigaba da going through her books "Abeg ni idan kin gama jarababben bokon kiyi switching off wutan alhuda hudan banza" dariya Kausar tayi tace
"Calm down! Har dakin zan bar miki a parlor zanyi karatu"
"Better" cewar A'ishah hadi da juya mata baya, girgiza kai kawai Kausar tayi ta miƙe tsaye ta tattara litattafan ta ta nufi hanyar fita gami da kashe wa A'ishah wutan tace
"Allah yasa ayi beating naki"
"Ba ameen ba wallahi, idiot!" dariya Kausar ta bushe ta fice daga dakin.





*It'z Shawty* 💕
[1/7, 8:20 PM] ‪+234 813 551 5123‬: *BARR. BASSAM*
(The Gallant) ❣




By *Shawty*


*2017*

1⃣1⃣


*PURE MOMENT OF LIFE WRITERS*
(We don't just entertain and educate, we also touch the hearts of the readers.)



_This page is in dedication to all PML writers. It wasn't started with you, but it's a privilege to meet y'all. Thanks *Faty Axland* it's a honor I never thought of_😘

________________________________

_2:00am_
Misalin ƙarfe biyu na dare ne ta kammala karatun da take, miƙewa tayi tsaye bacci ne sosai a idanun ta ta nufi bedroom nasu, yadda ta bar A'ishah kan gado haka tazo ta same ta, bathroom ta shiga tayo wanka hadi da dauro alwala tazo ta tayar da sallah. Nafila tayi raka'a biyu ta dade tana addu'o'i sa'annan ta shafa.


A sanyaye ta miƙe tsaye ta cire hijab dake jikin ta taje gun wardrobe ta chanza kayan jikin ta zuwa na bacci, zuwa tayi ta kwanta kan gadon gefen A'ishah hadi da jan comforter. Har ta kwanta kuma taji tana jin ƙishirwa sosai, kai tsaye ta sauko daga kan gadon ta koma parlorn nasu a inda tayi karatun, ƙaramin fridge din dake parlorn ta nufa ta bude da niyyar ta samu ruwa ta sha amma me? Wayam fridge din ba ruwa sai drinks ne kawai kuma sosai tana da buƙatar ruwa kafin ta kwanta kenan dole sai ta sauka downstairs a main parlor kafin ta samu ruwa gashi tsoron tsiya ne da ita kamar farar kura.


Haka tayi ta shawarwari daga ƙarshe dai taga ba zata iya kwanciya bata sha ruwa ba ta yanke shawarar kawai ta sauka ta nemo ruwan. Haka kuwa aka yi ta doshi hanyar fita parlorn, as she stepped out gaban ta yayi mummunan faduwa kamar ta fasa ta juyo ta dawo kuma dai taji ba zata iya haƙurin ƙishirwar ba.


Saukowa take daga upstairs din a hankali cikin sanda kamar wata ɓarauniya gashi duhu ne ya mamaye ko ina a parlorn ko tafin hannun ka ba zaka iya gani ba, a daddafe ta ida saukowa cike da tsoro da yake tasan kan parlorn bata sha wuya ba wurin gano switch din, da sauri ta kunna haske ya mamaye ko ina a parlorn.


Alhaji Bala ne ta gani zaune akan 3 seater dake gaban ta ya bada baya, hasken da ya gauraye parlorn ne yasa shi waigowa da ƙarfi cikin tsananin tashin hankali

"Kausar?" ya fada his eyes wide in shock, abunda ya iya fitowa bakin sa kenan firgicin da yake ciki ya ƙaru. Kallon ta ya cigaba da yi baki hangame cikin tsintsar mamakin ganin ta a wannan lokaci.


A daya ɓangaren mutuwar tsaye Kausar tayi ganin yanayin da taga Alhaji Bala a ciki. Cikin shigar jajayen kaya ta gansa ta gansa riƙe da ƙwaryar jini a hannun sa bakin sa duk jini ne ya zubo har akan rigar sa, kasa janye idanun ta tayi akansa kowace gaɓa ta jikin ta sai rawa take kamar wacce aka mannawa shocking, hannayen ta biyu tasa gami da toshe bakin ta
"Innalillahi wa innaa ilayhi raji'un" shine kawai take nanatawa ƙasa-ƙasa, ganin ya miƙe tsaye ya fara kusanto ta ne yasa ta fara tafiya da baya bugun zuciyar ta na ƙaruwa, wani ƙarfi ne ya shigo ta lokaci daya ta juya a guje ta koma upstairs, da ƙarfi ta banka ƙofar parlorn ta fada har sai da ta fadi ƙasa miƙewa ta sake yi a guje ta banka ƙofar bedroom dinsu shima ta fada hadi da mayar da ƙofar ta rufe. Sulalewa tayi a ƙasa cikin matsananciyar bugawar zuciya ba abunda ke replaying a idanun ta sai yanayin da taga Alhaji Bala a ciki riƙe da ƙwaryar jini. Tuni ta nemi ƙishirwar da take ji ta rasa tsintsar tashin hankali, fashewa tayi da kuka ƙasa-ƙasa cikin muryar ta me sanyi, haka tayi ta kukan ba me lallashin ta har ta gaji tayi shuru dan kanta.


A'ishah kam sai baccin ta take peacefully bata ma san me yake faruwa ba, da ƙyar ta miƙe har tana ganin jiri a daddafe ta isa kan gadon ta kwanta hadi da jan comforter, duk a.c dake akwai dakin bai hana zufa ta keto mata ba har yanzu jikin ta bai daina ɓari ba sai ajiyar zuciya take akai-akai ta dade a haka har bacci ɓarawo yayi awon gaba da ita.


Gefen Alhaji Bala shima mutuwar tsaye yayi a wurin yana kallon ta har ta shige, shuru yayi ya fara safa da marwa a tsakiyar parlorn yana tunanin Kausar ce mutum na farko da ya fara sanin asirin tsafin sa
"I'll tackle it" ya fada in between his tooth hadi da yin gajeren murmushi, kinkimar ƙwaryar jinin tsafin sa yayi ya haura upstairs din ya nufi apartment dinsa.


_4:30am_
Bacci take tana juye-juye fuskar ta a yamutse wane zata yi kuka, haure-haure kawai take da ƙafafun ta tana wani irin nishi, ƙara me tsanani ta ƙwalla hadi da tashi a firgice tana mayar da numfashi, A'ishah ce ta farka a firgice sakamakon ihun da Kausar tayi cikin muryar bacci tace

"Kausar? Me yake faruwa?" shuru bata amsa ba sai maida numfashi take, zumbur A'ishah ta tashi zaune hadi da kunna dim light dake gefen gadon ta fara nufa to tace
"Kausar menene?" ja da baya Kausar ta fara yi ta ƙara ƙwalla wani ihun, a rikice A'ishah ta miƙe da sauri taje ta kunna wutar dakin haske ya mamaye ko ina, ganin ta tayi a durƙushe kan gwiyoyin ta jikin ta sai rawa yake ta dafe kanta matsowa kusa da ita A'ishah take hadi da kiran ta a hankali "Kausar?" dago kanta tayi a firgice ta miƙe tsaye tace
"Kadda ku kashe ni" idanun ta a rufe take maganar yayi daidai da isowar A'ishah daf da ita ta riƙo hannuwan ta duka biyu tace
"Kausar ba wanda zai kashe ki, open your eyes niche" shuru bata amsa ba sai rawar da jikin ta keyi "Open your eyes ba kowa a nan kinji?" bude idanun ta tayi a hankali ta kalli A'ishah tace
"A'ishah?" cikin muryar tsoro da kuka, murmushi A'ishah ta sakar mata hadi da cewa
"Yes it's me" fashewa tayi da wani wahaltaccen kuka ta fada jikin A'ishah tana

Please Login or Register in order to submit comment