Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

years that does the trick. Happy bornday *Neenah*I wish you many happy returns of this day. I hope it's as fantastic as you are. You deserve the best and nothing less sweetheart. This page is highly dedicated to you and *HBD* once more. Back to you my group buddies, I view you oo since morning you were busy eating cake and popping Champagne😁 nima lemme sharp-sharp cover this page and join you. It's *Neenah's* birthday_💃

___________________________________

_Washe gari_
Dalibbai ne zaune a cikin aji suna daukar darasi, A'ishah na hango zaune next to Nailah daga ƙarshen ajin dama they're popularly known at the back (back benchers) sai chatting suke basu ma san me ake ciki ba. Kamar wacce aka tsikara A'ishah ta taɓo Nailah

"Hey babe!" cewar A'ishah, juyowa Nailah tayi tana kallon ta tana kuma sauraren abunda zata ce, gyara zama A'ishah tayi tace "Where's that stupid son of a bitch?"
"Who?" Nailah ta tambaya, ɓata fuska A'ishah tayi gami da cewa
"Don't start with me, wa zan nema apart from that Dipshit?"
"Oh! Sorry Al'ameen?" Nailah ta fada questioningly
"I didn't see him, maybe he's not here" cewar Nailah tana duba dama da hagun ta koda zata gansa, wani deadly smile A'ishah tayi ta miƙe zata bar wurin "Hey! Ina zaki je?" cewar Nailah, ƙara fadada murmushin ta tayi tace
"Watch, don't miss a scene there" ta nufi first seat next to entrance door ta zauna, dariya kawai Nailah tayi hadi da nodding kanta alamar ta fahimta. Yayi daidai da malamin ya kammala darasi yayi bankwana da daliban ya fita.


Fitar sa ke da wuya sai ga Al'ameen ya shigo yana tafe kansa a ƙasa yana danna wayar sa, da sauri A'ishah ta jera ƙafafun ta biyu akan hanyar da zaya bi, sam hankalin sa baya nan tafiyar sa kawai yake kawowar sa wurin ke da wuya A'ishah ta harde ƙafafun sa duka biyu cikin nata dai gashi ƙasa timmm! Dama ƙawayen A'ishah jira kawai suke, ɓarkewa suka yi da dariya at once yayin da Ashraf da Ra'ees suka yo kan abokin su lalace hadi da taimaka masa suka dago shi yayin da A'ishah sai murmushi take. Gaba daya ajin suka zo suka zagaye su, hancin sa da bakin sa duka sun fashe sai jini ke zuba wayar sa kuma screen ya tarwatse. Tsoro da fargaba ya kama su gaba daya har friends na A'ishah tsit suka yi yadda suka ga jini ke fita hanci da bakin Al'ameen. Hannu ya kai ya taɓa bakin sa sai ga jini ya gani a hannun murmushin yake yayi ya juya ya kalli Ashraf da Ra'ees yace
"Can you believe that bitch?" riƙo hannun sa Ra'ees yayi gami da cewa
"She ain't gonna get away with this, let's get you clean up first" murmushin yake yi har yanzu yayin da zuciyar sa sai tafarfasa take, juyawa yayi ya kalli A'ishah wacce tayi crossing ƙafafun ta sai dariyar mugunta take ko kadan she didn't panic, tuni idanun Al'ameen suka kada suka yi ja kukan kura yayi ya nufi A'ishah hadi da chafko wuyan ta sai huci yake kamar wanda yay gudun tsere da zaki yace
"You blood thirsty bitch! This is the biggest mistake you've ever made" tuni idanun A'ishah suka firfito sai wuntsile-wuntsile ta kasa cire hannun Al'ameen daga wuyan ta, duk ƙoƙarin Ra'ees da Ashraf amma sun gagari cire hannun Al'ameen daga wuyan A'ishah. Wani kallo yake mata cike da tsana yacd "I already told you I'm gonna kill you. Not today not tomorrow but I'm gonna KILL YOU" ya jefar da ita sai huci yake, ba A'ishah kadai ba har friends nata, Ashraf da Ra'ees maganar da Al'ameen ya jaddada mata daga ƙarshe ta girgiza su, miƙewa A'ishah tayi da ƙyar ta matso daidai da fuskar sa tana masa wani deadly look tace
"And you'll regret your whole life, asshole!" kalmar asshole da kira sa dashi ya bala'in sosa masa rai ya sake yo kanta, da gudu Ashraf ya tare sa hadi da janye sa tare da sauran squad nasa suka bar class din. Ƙarasowa friends na A'ishah suka yi kowace kusa da ita kowace ta gama tsorata da maganganun Al'ameen

"I'm afraid ba barazana ce yake yi ba babe, the only language this guy understand is violence" cewar Nailah full of fear, harara A'ishah ta watsa mata tace
"So, you believe him? This drunkard?"
"No babe na gani ne, I saw it in his eyes"
"Lol.. Wah did you saw?" cewar A'ishah cikin rainin hankali haka
"Hatred.." wani kallo A'ishah ta katse ta dashi "Of course hatred" cewar Nailah "This guy you're seeing zai iya aikata whatever is on his mind" tsuki A'ishah taja tace
"Not with me wallahi"
"Careful babe bayada mutunci" tuni A'ishah tayo kanta da masifa
"Wai nikam yaushe kika fara tsoran sa ne? Al'ameen of all people? This asshole?"
"No babe, I'm just afraid he may do something fishy"
"Mysww" A'ishah taja tsuki ta koma ta zauna hadi da crossing ƙafafun ta.


*Dundee, Scotland.*
Zaune yake a bakin beach mutane ne birjik a wurin kowa yana hidimar gaban sa. Sanye yake da beachwear yana kallon yadda ruwa yake kai komo daga sea din zuwa bakin beach with so many thoughts in his mind. Ƙarar wayar sa ne ya dawo dashi daga duniyar tunanin da ya lula a sanyaye yasa hannu ya jawo wayar gami da picking yasa a kunne
"Hi Mom I.." bata bar sa ya ƙarisa fadar abunda zai ce ba ta katse sa cike da tsiwa
"Shut up you silly" tsananin mamaki ne ya lulluɓe sa coz he can say he have never heard his Mom in such a bad mood ba sai yau "Yauwa! Who's Hindu Alhassan to you?" sounding serious ta jefe sa da tambayar, mamaki da kaduwa suka hade masa wuri daya, tsawa ta sake daka masa "Ka gayamin!" kamar saukar aradu haka yake jin maganganun ta a kunnuwan sa, a sanyaye yace
"She's all I've got, she mean the world to me" a sanyaye yake maganar unassured of what's wrong, itama daga daya ɓangaren ya bata tausayi don kwa bata san yadda maganar zata zo masa ba
"Good, ka saurare ni. When are you planning to come back home?" kasa gane abunda take nufi yayi
"Mom.." cikin fushi ta katse sa ta balbale sa da masifa
"Do you think I can support your life styles? This is your last of a thousand chances Bassam, don't waste it" kamar a mafarki haka yake jin ta duk uban sanyin da akeyi haka ya tsinci kansa yana hada gumi kamar wanda ya hadiye kunama, shuru yayi ya kasa cewa komai "Hello? Bassam?" tace dashi
"Yeah" ya amsa mata sounding defeated
"Yayi kyau" tace "Come back home or never, choice is yours and it makes no difference to me in either way" dif ta katse call din, cike da firgici ya ciro wayar daga kunnen sa ya kuma sake mayarwa
"Hello? Mom?" shuru yaji alamar ta katse kiran da gaske, shuru yayi ya rasa me ke shirin faruwa ne haka. Dubara ta fado masa da sauri ya sake dialing number amma har ta gama ringing bata daga ba, sai da yay mata missed calls uku a jere ba wanda ta daga at last ma ta kashe wayar gaba daya. Dafe kansa yayi idanun sa sun chanza kala lokaci daya "Mom are you damn serious?" a fili yay ma kansa tambayar wacce ya kasa samun amsar ta, iska ya furzar daga bakin sa hadi da girgiza kansa in disbelief "No! She must be joking" ya fada a fili hadi da miƙewa tsaye ya fara safa da marwa a bakin ruwan bayan wani lokaci kuma ya tsaya cik hannun sa na dama ya dunƙule ya kaiwa dayan naushi gami da fadan "This is bullshit!" da ƙarfi. Ba dan ya gama shan iskar ba sai dan rashin walwala dake tattare dashi yasa ya tattara ya koma gida.


******


Kwance yake kan makeken gado ya ƙurawa ceiling ido kallo daya zaka yi masa ka tabbatar baya cikin walwala. Boxer ne da singlet ne kawai a jikin sa dukam su farare, hairy skin nasa yayi kyau sai sheƙi yake yi gashin kwance luff ga muscles da packs sun fito wanda ya ƙara fidda halittar sa ta mazantaka, such a young and builded man.


Wayar sa ce dake gefen sa ya dauko ya sake dialing number Mom for the fifth time but she ain't picking, shuru yayi ya rasa abunda zaiyi he can't take it. Wata dubara ta fado masa ya fara composing message mata

_I'm sorry Mom, I'm really sorry. This is not you, atleast you should hear me out. If only you picked up my call you would've heard how sorry I am_

Da sauri ya tura mata, tana kwance ta rasa abunda yake damun ta, she loves him and she knew how hard it is ya dawo Nigeria but there's no other alternative rather than dawowar sa gida. She know it won't be easy for him but he have to withstand it. Shigowar message taji a wayar ta da sauri ta duba to her surprise Bassam as she thought, breaking kawai tayi da murmushi then she feel guilty about what she did amma ta ƙudira a ranta ba zata daga wayar sa ba har sai an kwana biyu.


Back to Bassam, jin shuru-shuru ba reply daga Mom ya tabbatar masa lallai tayi fushi ne ba kadan ba, haƙura yayi da kiran ta yayi shuru da haka har bacci yayi awon gaba dashi.



_Hey! The party isn't rocking, grab your partner and feel the beats_💃





*Shawty*💕
[1/7, 6:58 PM] ‪+234 813 551 5123‬: *BARR. BASSAM*
(The Gallant) ❣




By *Shawty*💕


*2017*

0⃣7⃣

_And this page goes to *Ayatullah*,a friend with so much benefits. Thanks for the supportive role you are playing, *Shawty* and ya *Gallant* Barrister loves you_😍

____________________________________

Ƙarasowa ciki yayi kamar kazar da ƙwai ya fashewa a ciki, tafiya yake har ƙafafun sa suna hardewa da alama a gajiye yake haka har ya shige parlorn. Straight bedroom ya nufa yana shiga yayi cilli da diary dinsa akan gado shima ya fada kan gadon all exhausted.


Ya kusa shafe mintuna goma kwance kan gadon flat bai ko motsa ba da ƙyar ya miƙe ya fara tafiya wurin wardrobe. Kayakin jikin sa ya fara ragewa sai da yayi saura daga shi sai boxer woow! He's damn hot.


A hankali ya taka zuwa bathroom, ya ɓata almost 20mnts sa'annan ya fito daure da towel a ƙugun sa sai wani ƙarami da ya dora akan wuyan sa, sai da ya gama tsane ruwan jikin sa sa'annan ya koma wurin wardrobe ya dauko wata sleeveless singlet da shorts army color ya saka.


Juyawa yayi ya koma wurin darduman sallah hadi da tada sallar. Cike da natsuwa yake sallar har ya gama, ya dade yana addu'o'i sa'annan ya miƙe ya nufi hanyar fita bedroom din.


Straight kitchen ya nufa sakamakon wata yunwa dake azabtar dashi, coffee ya hada ya dauko coffeecake ya juya ya koma bedroom. Ajiye su yayi kan bedside drawer shima ya zauna hadi da juyawa ya dauko tab dinsa ya fara danne-danne a ciki. Coffeecake yake ci hadi da sipping coffee din a hankali, tunawa yayi Mom is usually free at this time, skyping nata yayi hoping she'd respond kadda ta share sa like she's being doing all this days, haka kuwa akayi to his surprise suka fara magana
"Mammy of life" ya fada hadi da winking eye mata, dariya tayi itama ta amsa da
"Baby of life" dariya suka yi gaba daya, a hankali ya kama kunnuwan sa duka biyu da hannayen sa hadi da dan ɓata fuska in a childish manner
"I'm sorry Mammy, I'm really sorry. I shouldn't have behaved stubborn that day beside kinsan..." bata bari ya ƙarisa ba ta katse sa tana dariya, Bassam will never behave matured when he's with her, dariya ya bata sosai tace
"Shhh! It's ok honey, karka damu ha?" murmushi sosai yayi yace
"Thank you" murmushi itama ta mayar masa gami da cewa
"Always welcome, me kake ci ne haka?" ta tambaye sa, kallon coffeecake din yayi then back to her
"Coffeecake.. Sorta. I'm damn hungry" hade fuska Mom tayi tace
"Didn't I told you ka daina zama da yunwa?" murmushi yayi he love yadda Mom ke ji dashi yace
"I'm sorry, yanzu na dawo I've been busy all day ban samu na zauna ba"
"Ba excuse bane make time for yourself right?" dariya ta basa yadda warning nasa just like 1year kid
"Right" yace "Wanna join me?" girgiza kai kawai tayi tana murmushi
"Naaa! I'm full. You know I'm not into coffeecakes, be it a patty" shi kam cin abunsa kawai yake yace
"I know but it's yummy" daga kafadunta tayi in I don't care manner as she's busy combing her hair, dariya yayi yace
"Mammy me kike ci ne? You are always looking younger than your age, I couldn't understand" sai grinning yake, dariya tayi hadi da dakatar da combing din ta dan ƙura masa ido
"You too sweetheart. I can see that Scotland have softenef you up, you're just sparkling" dariya sosai yayi har coffeecake din ya kusa kama sa yace
"Combing kike ne?" ya tambaye ta
"Yes dear, want to help Mammy?" murmushi yayi hadi da shafa gefen fuskar sa
"Yeah I missed you so much Mammy" murmushi itama tayi tace
"Same here Darling, I missed you more" dariya suke yi sosai kamar ba sune suka yi rigima days back ba da ka gansu zaka tabbatar they are having a good time "Wait honey..." tace dashi "What about what we talked last?" ta tambaye sa ba alamar wasa in a serious way
"What?" ya tambaye ta shima, bude idanun ta tayi wide in surprise
"Your fight mana, have you got the visa?" nan take mood nasa ya chanza kamar ba shine yake dariya yanzu ba
"Holy shit!" ya fada ƙasa-ƙasa in between his teeth hadi da kauda kansa daga kallon ta, tayi noticing yadda yanayin sa ya chanza all of a sudden murmushi tayi tace
"Why the sudden change, Bassam? It seems like you ain't happy to live with me ever again, nevertheless, I'm quitting. I won't talk about this anymore. Chill" ta fada idanun ta suka ciko da hawaye, idan har akwai abunda ya tsana shine fushin Mammyn sa she's all he have da sauri ya fara lallashin ta
"No Mom, don't start it please. You didn't understand what I'm up to, pratice da nike yi anan fa?"
"I've planned everything here and I'm sure you'll like it" zura mata ido kawai yayi sun kada sunyi ja lokaci daya "Bassam?" ta kira sa kamar zata yi kuka, kallon ta kawai yake baice da ita uffan ba "Come back home please, you're all I've got. I need you here" shuru yayi har yanzu ya kasa ce da ita komai "Can I count on you?" ta fada yanzu kam har hawayen da take ɓoyewa sun fara zubowa kan fuskar ta, da sauri yace
"It's alright Mom, I'll be back"
"When?"
"Soon" still not looking at her
"When exactly?" ta fada dan kwa ta saba jin wannan soon din
"In a week" ya fada sounding defeated, dariya sosai tayi wani dadi ne ya ziyarce ta
"Thank you so much dear" kai kawai yay nodding mata, a haka suka cigaba da hirar wacce ta koma boring dan kwa Bassam ya daina responding mata sai ita kadai ke surutu, cike da jin dadi suka yi sallama akan in the next week zaya dira Nigeria. Jifa yayi da tab din kan gado dama tuni ya dakatar da shan coffee da yake ya fada ta baya kan gadon cikin rashin ƙwarin gwiwa.


Ƙarar ƙofa ne ya dawo dashi daga duniyar tunanin da yaje alamar shigowar mutum, Hannah ce tsaye cikin shiga ta mini skirt da high da wata armless top sai high-heeled shoes. Dama ita blondie ce gashin kanta irin yellowish brown color dinnan ne ya zuba har a kafadunta, ƙarasowa tayi har kusa da shi ta zauna, bece da ita uffan ba sai ma kawar da kansa da yayi to one sided wall, hannun sa da nata ta hada wuri daya tana murzawa a hankali sai kuma ta saki hannun ta bishi kan gadon. Fuskar ta ta kawo daidai da tasa har suna jin numfashi da heart beat na junan su, a hankali ta fara motsa bakin ta wanda ya sha red lipstick kamar wacce bata son magana tace
"Moh what is it?"
"Nothing" he shrugged his arms gently
"Then why the frowned face? This is not you"
"Nothing" yace "I just..." kamar mayunwaciya haka tayi shutting nasa with a hot kiss, tun yana ƙoƙarin ture ta har ya sallama ya bada gari ya fara responding mata, kissing suke kamar zasu hadiye junan su sunyi kusan 15mnts a wannan yanayin bayan nishin su ba abunda kake jiyowa. Shorts nasa ta fara pulling a hankali, tuni ya gano inda ta nufa hannu yasa ya ture ta gefe daya hadi da cewa "Stop it!" da ƙarfi gami da tashi zaune, itama tashi tayi zaunen ta sake dawowa kusa dashi, bakin ta tasa akan lipa nasa ta fara tsotsa amma wannan karon bata yi nasara ba, ƙara daka mata tsawa yayi hadi da finciko ta daga jikin sa "Stop it Hannah" yace da ƙarfi wane zai dake ta, ta taorata sosai yadda ta hango tsintsar masifa a idanun sa miƙewa yayi ya fice ya barta a dakin. Parlor ya nufa wurin mini fridge ya bude ya dauko kwalbar liqour dinsa ya dawo kan Sofa gently ya zauna hadi da bude kwalbar ya kafa ta a bakin sa, sai da ya sha fiye da rabi sa'annan ya dire kwalbar ya jingina jikin Sofan ya rintse idanun sa.





*Shawty*💕
[1/7, 7:20 PM] ‪+234 813 551 5123‬: *BARR. BASSAM*
(The Gallant) ❣




By *Shawty*💕

*2017*

0⃣8⃣

*Sokoto, Nigeria.*
Alhaji Bala ne zaune a gaban malamin sa wanda ya shafe kusan mintuna talatin zaune a wurin malamin baice dashi uffan ba sai rubuce-rubucen tsafin sa yake yi a ƙasa yana shafewa yana wani yare wanda shi kadai yasan ma'anar sa.


Alhaji Bala ne yayi gyaran murya a karo na biyu yace
"Mallam ka kira ni amma har yanzu baka sanar dani komai ba" shuru ne ya biyo baya yayin da malamin yaji abunda Alhaji Bala ya fada sarai amma hakan bai sanya shi ya daina abunda yake ba. Yanzu kam ido kawai Alhaji Bala ya zuba masa sai da aka kusa shafe wasu mintuna goma sa'annan malamin yayi ajiyar zuciya hadi da dago kansa ya kalli Alhaji Bala
"Bala ka kashe maciji amma baka sare kan ba" kallon sa kawai Alhaji Bala keyi cike da rashin fahimtar abunda yake fada
"Kamar yaya fa? Wanne macijin kake magana?"
"Zaka iya tuna lokacin da hukumar EFCC zata yi bincike akan dukiyar ka har muka sa ka kawo mana yarinya matashiya muka yi maka aiki?"
"Ƙwarai na tuna" Alhaji Bala ya amsa
"Toh fa jinin wannan yarinyar bai tafi a banza ba" dariyar rainin hankali Alhaji Bala ya tarwatse yana kallon malamin yace
" 'Yar wanne shegen ce? Wa kake tsoro? Me kuma aka baka wanda ni ban baka ba?" kada kai malamin ya shiga yi
"Bana tsoron kowa kuma ba'a bani komai ba sai hango makomar mu da nayi idan har muka yi wasa"
"Baka ƙarisa amsa min tambayoyi na ba, 'yar uban waye?" cewar Alhaji Bala
"Ƙarfin ku daya da mahaifin ta don kuwa shima babban matsafi ne, ya mallaki zobe kamar kai. Yadda ka bada mahaifar matarka akan ba zaka sake haihuwa ba haka shima ya bayar da ƙwan halittar sa akan ba zai sake haihuwa ba. Yadda ba zaka sake wani auren ba koda kuwa matar ka ta mutu, haka shima ya salwantar da rayuwar matar sa don kawai ya tara arziki. Yadda duk duniyar nan A'ishah ce kawai 'yar ka, haka shima Juwairiyyah ce kadai 'yar sa kuma itace ka kashe. Yadda ka sayar da lahirar ka don kawai kayi kudi, haka shima ya sayar da tasa lahirar don kawai yayi suna. Yayi alƙawalin daukar fansa kan duk mai hannu a kisan 'yar sa kuma tun lokacin yake bibiyar mu" wannan karon dariyar mugunta Alhaji Bala keyi yace
"Toh me zai iya yi? Inace ta mutu kuma ba zata dawo ba" Alhaji Bala ya tambaya
"Tabbas Juwairiyyah ta mutu, amma ta bar babban tashin hankali a bayan ta" cike da rashin fahimta Alhaji Bala ke kallon malamin
"Yaya tashin hankali Mallam?"
"Ƙwarai akwai tashin hankali da zai tunkaro mu idan har kuka yi sake da wannan al'amari" cewar malamin "Abunda nike so dakai yanzu shine, nan bada dadewa ba zaya zo na kira sa a waya abokina ne kuyi ƙoƙari kuyi sulhu a tsakanin ku idan ba haka ba zata kwaɓe ne kawai Bala dukan mu zamu hallaka"
"Kace ya sunan sa ma?"
"Kabara! Alhaji Kabara" jinjina kai kawai Alhaji Bala yayi lokaci daya suka yi shuru kowa da kalar tunanin da yake a ransa. Motsin shigowar mutum ne ya ankarar dasu lokaci daya dukan su suka miƙe tsaye. Babban mutum ne zabgege fari tas sanye yake cikin shiga ta kamala wato 'yar ciki da babbar riga da hula dukansu farare. A hankali yake takowa cikin parlorn a cikin yanayin da ba zaka misalta shi ba, kallon su yake daya bayan daya har ya iso daf dasu a sanyaye Alhaji Bala ya miƙa masa hannu hadi da cewa
"Alhaji Kabara ko?" jinjina kai kawai Alhaji Kabara yayi ya miƙo masa hannu shima yana mai yi masa wani shu'umin kallo
"Hakane kuma da dukan alama kaine Alhaji Bala wanda ya kashe min 'ya" saukar da kansa ƙasa Alhaji Bala yayi a sanyaye gami da cewa
"Kuskure aka samu bada sani na bane" dariyar rainin hankali Alhaji Kabara ya bushe hadi da cewa
"Nima bada sani na ba zan dauki fansa" da sauri malamin ya tari numfashin Alhaji Kabara yana cewa
"Baka riga ka dauki fansar ba Kabara, zaku iya yin sulhu" da sauri Alhaji Kabara ya juyo yana kallon malamin
"Mi kake cewa Mallam? Nayi sulhu da wanda ya kashe min 'ya? Ba zata taɓa sa saɓuwa ba" a sanyaye malam yace
"Toh zaya biya ka diyya" murmushi fal akan fuskar Alhaji Kabara ya juyo yana kallon Alhaji Bala yace
"Wai haka ne zaka biya ni diyya Bala?" cike da jin dadi Alhaji Bala ya amsa da
"Ƙwarai kuwa" jin an ambaci diyya, dariya Alhaji Kabara ya bushe da hadi da cewa
"Da me zaka biya ni diyya Bala? Nasan dai bada kudi ba don kuwa banyi maka kama da talaka ba"
"Me kake so?" Alhaji Bala ya tambaya
"Da

Please Login or Register in order to submit comment