Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yours and here it is_👇🏻


*No sis! Na sanya character na Jay ne for some clarification, had it been ba Jay Bassam ne kawai ke aikin all by himself you wouldn't get to know the story in details since ba zaiyi magana da kanshi shi kadai ba, ba zaiyi sharing abunda yake a ranshi da kowa ba sai dai kurum ya aikata. Secondly, wanda yayi karatu a kasar waje ba zaki hada shi da wanda yayi a Nigeria ba, lol I'm not trying to condemn educational system in Nigeria but everyone knows that's the fact, in one way or the other dole Bassam yafi Jay gogewa a aikin kuma idan kika lura har Mammyn sa yafi kaifin basira anan wacce tun kafin a haife sa take a cikin aikin. Thirdly, idan har Jay zai kawo some strong ideas then the tittle of the novel is not supposed to be BARR. BASSAM❣at all*
Sis with my lil explanation, I hope you are now cleared. It's a good question for sure and I like it this shows you're very reasonable person and please don't hesitate to ask another question if needed. Thanks. 👍🏻🤜

________________________________________



4⃣5⃣


Koda ya iso office din duk a firgice yake, zaunar dashi Jay yayi yaje fridge ya kawo masa ruwa da drinks yace ya sha sai da ya nutsa Jay ya tambaye sa ya akayi, kwashe labarin yayi akan abunda ya faru a gidan Alhaji Bala ya fiddo envelope d'in ya mik'awa Jay, bud'e envelope d'in Jay yayi ya karanta shima sai da jikin sa yayi sanyi yace
"Yanzu ya kenan?" d'an wara hannuwan sa Bassam yayi yace
"So nike na samu Cyber wizard da zai mana tracking number sa da calls da yayi 2 days kafin kisan A'ishah don ya zame mana evidence a kotu" jinjina kai Jay yayi har yanzu sai kallon takardar yake a hankali Bassam yace "Yanzu ya za'ayi mu same shi?" da sauri Jabir yace
"I have a friend da yake da Cyber Cafe lemme contact him though nasan ba zai iya yi mana wannan aikin ba but koda zai iya had'a mu da wanda zai taimake mu" ya k'arasa maganar yana danna wayar sa, d'an resting Bassam yayi kan kujera in relief yace
"Yauwa kira sa please" dialing number mutumen Jay ya shiga yi, ringing biyu a na uku ya d'aga yace
"Jay yane?" murmushi Jay yayi yace
"Daidai ne, please kana Cafe right now?"
"Yeah" dad'i Jabir yaji har cikin ransa yace
"Ok gamu nan zuwa me and a friend, we need your help"
"Ok" cewar mutumen ya k'ara da cewa "Sai kun zo" Jabir ya katse kiran ya mik'e tsaye yace
"Muje Cafe d'in" mik'ewa Bassam yayi shima yace
"But we have to be very cautious, nasan mutanen nan nema na suke ruwa jallo"
"Karka damu, the case is coming to an end in shaa Allah" cewar Jay, suka mik'e tsaye, dakatar da Jabir Bassam yayi yace
"Find somewhere safe in here ka ajiye envelope d'innan please" d'aukar envelope d'in Jabir yayi ya d'aga wani k'aton textbook mai suna Criminal Law ya saka envelope d'in a ciki sannan suka fito office d'in, wani tunanin ne ya sake shigowa k'wak'walwar Bassam ya juyo yace "Wani hanzari ba gudu ba Jay" tsayawa Jabir yayi yace
"Me fa?"
"Ina zamu samu number Alhaji Bala?" cewar Bassam, shiru Jabir yayi yace
"Ka kira Mammy ai matar sa k'awar ta ce right?" girgiza kai Bassam yayi yace
"Haba Jabir! Kaima kasan ba zan tunkari Mammy da wannan zancen ba" shiru suka yi kowannen su yana kalar nasa tunanin a hankali Bassam ya juyo yace "The easiest way shine mu koma gidan Alhaji Bala" zaro ido Jabir yayi yace
"Gidan Alhaji Bala fa kace? Inace yanzu kake cewa neman ka yake helter skelter" dariya Bassam yayi yace
"Use your 6th mana, naje gidan Alhaji ya ganni me gadin sa ya basa labarin abunda ya faru I'm sure Alhaji Bala baya gida yanzu, muje muyi spying me gadin sa kada mu nuna masa number Alhaji Bala muka zo nema, mu nuna masa Alhaji Balan muke nema idan yace baya nan sai muce to ya bamu number sa neman sa muke aka yi mana kwatancen gidan sa gashi kuma bamu same shi a gida ba" shiru Jabir yayi yace
"Anya kuwa kana ganin zata yiwu?"
"Me zai hana?" cewar Bassam "Let's go please" har sun fara tafiya zasu shiga mota Bassam ya sake dakatar da Jabir yace "Kasan me kuwa?" girgiza kai Jabir yayi yayin da Bassam yace "Kai zaka je wurin me gadin 'cause ni d'azu naje zai iya shaida fuskata kuma zargi zai iya shigowa zai iya kiran Alhaji Balan ya gaya masa abunda ake ciki, zan tsaya da motar mu nesa da gidan sai ka taka da k'afa ka isa gidan, do you get it?" jinjina kai Jabir yayi Bassam yace "Good, muje" har sun kawo daf da k'ofar Bassam ya kalli stick d'in dake hannun sa ya yada shi ya fara kokarin bud'e motar da sauri Jabir yace
"Mesa zaka yada stick d'in?" d'an tab'a baki Bassam yayi yace
"Nagaji, I can walk on my own" ya bude motar ya shiga, shi kam Jabir sometimes har mamakin gentility na Bassam yake da haka dai ya bude motar ya shiga Bassam yaja suka bar wurin.


******


Gefen Alhaji Bala kuwa koda ya shigo cikin gidan bayan had'uwar sa da Bassam parking yayi yazo wurin me gadi yace
"Naga wani saurayi ya fita a gidan nan wa yake nema ne?"
"Eh zuwa yayi yace na nemar masa izini wurin Hajiya yana so ya ganta nace toh, koda na shiga na fad'awa Hajiya na fito naga hankalin sa a tashe nace ya shiga tana parlor sai yace min an kira sa a waya amma zuwa anjima zai dawo" jinjina kai Alhaji Bala yayi yace
"Me ka fahimta ya tada hankalin sa?" shiru me gadin yayi yace
"Ina kyautata zaton kila mutuwa aka gaya masa a wayar da yace an kira sa amma dai bansani ba sai dai na gansa rik'e da wata takarda yana karantawa"
"Takarda kuma?" cewar Alhaji Bala, jinjina kai me gadin yayi yace
"Eh Alhaji" nan take zufa ta shiga karyowa Alhaji Bala ya cire hular dake kansa ya fara hurawa kansa iska da ita yana maimaita
"Innalillahi wa innaa ilayhi raji'un" sai a lokacin yake tuna ya d'auko envelope d'in d'azu ya fito da ita ya saka ta a aljihu da niyyar zai fita da ita kenan bata shiga aljihun ba fad'uwa tayi kuma itace Bassam ya gani. Da gudu ya nufi shiga cikin gidan sai kuma ya sake dawowa ya umurci me gadin da ya bude masa gate, da gudu me gadin yaje ya bude masa gate yaja motar da gudu ya bar gidan ya bar me gadin yana mamakin ita kuma wannan wacce irin takarda ce. Yana hawa titi ya kira Alhaji Kabeer yace
"Kabeer wannan tsinannen yaron bansan ya zanyi dashi ba"
"Me akayi ne?" cewar Alhaji Kabeer, cikin rawar murya Alhaji Bala yace
"Yanzun nan ina dawowa gida muka hadu dashi ya fito daga gida na, da na tambayi me gadi yace wai yazo ne wurin Zainab amma kuma yaga wata takarda a hannun sa yana karantawa, hankalin sa a tashe yace an kira sa a waya amma zai sake dawowa kuma wannan takardar itace wacce Mallam ya bayar a bani ranar da aka kashe A'ishah, na fito da ita ne d'azu zanje wurin wannan bokan da nake baka labari har sai da na isa k'auyen na duba ban ganta ba ina d'auka ko a mota na barta na duba motar ban ganta ba ashe fad'uwa tayi bata shiga aljihun ba na dawo gida na duba ashe shegen goran ya riga ni" saukar da numfashi Alhaji Kabeer yayi yace
"Ka kira yaran ka yanzun nan ka gaya musu duk inda Bassam ya shiga su nemo sa su d'aure shi su kaishi su ajiye shi har sai an yanke hukuncin kisa an kuma kashe yarinyar da azabtar wa mai tsanani in kuma ya mutu kafin lokacin then lafiya lau ne" jinjina kai Bala yayi yace
"Haka zanyi" da sauri Kabeer yace
"Ina gidan gonar har yanzu kazo ka same ni" jinjina kai Alhaji Bala yayi yace
"Ok gani nan zuwa" ya katse wayar yana cewa "Tabbas Mallam yayi gaskiya da yace A'ishah ta mutu amma ta bar babban tashin hankali a bayan ta" da haka ya kira wayar T.K ya gaya masa abunda yake so kamar yadda Alhaji Kabeer ya tsara masa, amsawa T.K yayi da angama ya tsinke wayar ya nufi gidan gonar don samun Kabeer.


******


Fitowar Alhaji Bala bada dadewa ba daga gidan sa motar su Bassam ta iso, daga nesa ya tsaya kamar yadda suka tsara ya kalli Jay yace
"Karka shiga cikin gidan 'cause naga almost four CCTV cameras wanda lokacin da muka je kwanan baya babu, ka tsaya a bakin k'ofar kayi knocking idan me gadin ya bude ka tsaya daga bakin k'ofar kace Alhaji kake son gani idan yace baya nan sai kace ya taimaka maka da number shi please"
"Idan yana nan fa?" cewar Jabir, shiru Bassam yayi sai kuma dubara ta fad'o masa yace
"Kace ya nema maka iso wurin sa, idan ka ganshi sai kace taimakon kudi kake so" kallon jikin sa Jabir yayi yace
"But kasan banyi kama da masu neman taimako ba" k'agara Bassam yayi yace
"Come on jay! Saboda kana neman taimakon kudi you don't have to look poor, just go and I'm sure Alhaji Bala baya gida" jinjina kai Jabir yayi ya fito motar confidently ya nufi gidan Alhaji Bala, yana isa yayi knocking me gadin ya lek'o hadi da tambayar sa me yake so yace Alhaji yake nema anan yake sanar dashi ai baya nan
"Relief" cewar Jay k'asa-k'asa yanda ko me gadin ba zai iya ji ba ya k'ara da cewa "To ko zaka taimake ni da number sa ya saka ni wani aiki ne kuma yace idan na k'ark'are aikin in same shi a gida kuma gashi nazo baya nan ina so in sanar dashi na gama" bude k'ofar sosai me gadin yayi suna kallon juna a cikin ido shi da Jabir kamar yana zargin wani abu sai kuma ya tuna haka ne fa don kuwa Alhaji ya dawo gida ne bada niyyar sake fita ba zuwan wannan saurayin ne ya sanya shi ya sake fita, hannu yasa aljihu ya d'auko Nokia torch light d'insa ya shiga karantowa Jabir number Alhaji Bala yayin da shi kuma Jabir yana d'auka, bayan ya gama Jabir yai masa godiya yayi kamar ya danna call yasa a kunne suka gaisa da me gadin ya juya ya bar wurin zuwa wurin motar su, tunda Bassam ya hango shi yana murmushi yasan anyi nasara koda ya shiga motar suka bawa juna friendly blow🤜🤛sannan Bassam yaja motar suka bar wurin yace
"We're heading to your friend's Cafe right?"
"Yap" cewar Jay, ya shiga nunawa Bassam hanyar da zai bi suka nufi cafe din.


******


Gefen T.K kuwa tunda Alhaji ya kira sa ya shiga tunanin a ina zai samu Bassam, chamber suka nufa dashi da abokin aikin sa koda suka isa suka ga wurin rufe wanda yake nuna baya nan, da yake akwai wani kiosk a opposite da chamber suka yi parking motar su suka nufi shagon, gaisawa yayi da me shagon ya tambaye sa ko yasan wurin da masu office din chan suka je yace wallahi baisani ba sai wani dake zaune wurin ya shaida musu lallai bada dadewa ba yaga sun fito su biyu sun shiga mota sun fita sai dai baisan ko ina suka je ba, godiya T.K yayi suka fito ya kalli abokin aikin sa yace
"Mu saka motar mu ta lungun in mu jira su na tabbata zasu dawo don lokacin tashi aiki beyi ba" gyad'a kai abokin aikin san yayi suka yi kamar yadda suka tsara suka zauna jiran dawowar su Bassam.


******


Gefen su Bassam kuwa bayan sun isa Cafe din Bassam ya tsakurawa mutumen kadan daga cikin labarin ya shaida musu gaskiya baya irin wannan aikin amma yasan wanda zai hada su dashi, nan take Bassam yace ya hada su dashi din kawai yai ma Jabir kwatancen Cafe din mutumen suka yi godiya suka nufi chan. Koda suka je suka gaisa da mutumen ya kawo musu kujeru suka gaisa Bassam yace
"Dude we want your help"
"Name it" cewar mutumen, jinjina kai Bassam yayi yace
"Wata number nike so kai mana tracking" da sauri mutumen ya girgiza kai yace
"I'm sorry I can't" dafa kafad'arsa Bassam yayi ya ciro masa I.D card d'insa ya nuna masa, sannan ya umurci Jabir shima ya nuna masa nashi shima ya nuna masa sannan Bassam yace "We don't look like criminals dude, did we?" girgiza kai mutumen yayi alamar a'a sannan Bassam yace "Zaka iya kiran abokin ka wanda ya had'a mu dakai he's a friend to Jay he can explain better" shiru mutumen yayi sannan Bassam ya cigaba da cewa "Taimako zaka yi wani case ne muke, rayuwar wata yarinya is in big dilemma and if we don't play dirty we wouldn't stand a chance to win this case" har yanzu mutumen sai kallon Bassam yake da alama kam basuyi kama da criminals ba ko kadan amma dai yace bari ya d'an yi testing nasu yace
"What if it leaks out that I'm the one who did it?"
"Then hold me responsible" cewar Bassam sannan ya fiddo wallet d'insa ya fiddo d'aya daga cikin ATM cards d'insa ya mik'awa mutumen yace "You can withdraw any amount akwai 10M a ciki, idan kuma basu isa ba ka gayamin right now pin 6099" ba mutumen ba harta Jay sai da yayi mamakin Bassam, ya sha gaya masa ba don kudi yake case din Kausar ba amma bai tab'a yarda ba sai yau a hankali Bassam ya d'auki wayar mutumen ya saka number shi a ciki yace "To be loyal here are my digits, if it leaks out, the police can track me too" mutumen bai k'ara yarda da Bassam ba sai lokacin sannan Bassam yace "Idan ka taimake mu nan bada dadewa ba zaka ji social media breaks down da labarin aikin ka" shiru mutumen yayi sannan yace
"Ka bani labarin case d'in" girgiza kai Bassam yayi yace
"I'm sorry to say I can't 'cause it's matter of security, but if everything works out zaka sani" jinjina kai mutumen yayi yace
"Me kake so?" number Alhaji Bala Bassam ya basa da date guda biyu two days kafin kisan A'ishah yace
"Number nan nike so kayi tracking da calls da akayi a wad'annan dates din" jinjina kai mutumen yayi sannan Bassam yace "Kayi saving voice calls d'in duka please then sai kayi min forwarding d'insu through Whatsapp da wanchan number da na baka" gyad'a kai mutumen yayi alamar ya fahimta sannan Bassam yace "Can I count on you? And how long will it take you?"
"Ina wani aiki right now amma da na gama zanyi wannan and once I'm done I'll give you a call" cewar mutumen, jinjina kai Bassam yayi sukai masa godiya suka fito suka shiga motar su. Sai da suka hau titi sosai Jay yace
"Dude kana san Kausar da yawa fa" juyo da kansa Bassam yayi ya kalli Jabir wanda sai kallon sa yake yana blushing, dariya kawai Bassam yayi don yasha gayawa Jay he just wanna help her and ya kasa yadda dashi yace
"Ni ina zaka je ne? Gida ko Chamber?"
"No ka mayar dani Chamber ban gama aiki na ba kai kuma sai ka koma gida ka huta ka sha yawo yau" murmushi Bassam yayi ya nufi chamber don ya sauke Jabir, koda suka iso Bassam ya kalle sa yace
"I'll keep you posted idan mutumen ya kira ni" gyad'a kai Jabir yayi yace
"Ok Allah yasa a dace" suka yi sallama Jabir ya fito ya nufi office shi kuma Bassam ya juya ya nufi hanyar gida. Duk abunda ya faru akan idon su T.K Bassam yana juyawa suka shiga motar su suka rufa masa baya basu bari ya fahimci binshi suke ba har sai da ya kama hanyar gida da yake wurin shiru-shiru ne ba yawan mutane, nan take suka k'ara wa motar su gudu har suka zo daidai da Bassam sukai overtaking dinsa suka taka birki a gaban sa, gaban Bassam bai tab'a faduwa ba tunda ya fara case d'innan sai yau, fitowa suka yi su biyu dukan su da mask a fuskokin su d'aya yana rik'e da bindiga d'ayan kuma yana rik'e da wani dogon k'arfe yayin da Bassam har yanzu yana cikin motar sa sai kallon su yake, bude motar yayi ya fito ya tsaya yana kallon su yayin da su kuma sai k'arasowa suke bai yi aune ba kawai yaji saukar dukan k'arfe akan sa daga baya, sulalewa Bassam yayi ya fadi kasa wurin unconscious gefen kansa ya fara fitar da jini ashe su uku ne d'ayan tun kafin suyi overtaking Bassam suka ajiye sa. D'aure shi suka yi hannu da k'afa suka d'auke shi suka saka shi a boot d'in motar su sai dai basu rufe gam ba saboda gudun numfashi sannan suka duba motar sa suka d'auko wayoyinsa sannan suka koma suka shiga motar su suka fasa suka bar motar Bassam a wurin.




_Already Ummi is crying right now 'cause saurayin ta ya shiga trap din Alhaji Bala sai dai Allah ya kyauta walla_😁





*_Almost forgotten, this page is for you my sweethearted girlfriend, Happy birthday Salma and Allah Ya raya ki. Age with grace. On this date, a queen was born_* ❤❤❤❤❤❤❤❤❤







*It'z Shawty*💕
[1/8, 7:21 PM] ‪+234 813 551 5123‬: *BARR. BASSAM*
(The Gallant) ❣





By *Shawty*💕


*2017*


4⃣6⃣


_4:30pm_
Wuraren k'arfe hud'u da rabi na marece Mammy ce zaune cikin tangamemen parlorn ta tana kallo, tayi nisa sosai a kallon da take ta tsinto muryar mace tana sallama, juyowa tayi tare da amsa sallamar idanun ta suka sauka kan Samira, murmushi Mammy tayi tace
"Ah! Samira kece a gidan namu" murmushi Samira tayi kanta a k'asa tace
"Eh Mammy"
"K'araso mana" cewar Mammy, k'arasowa tayi ta zauna suka gaisa sosai ta tambayi Mammy ya jikin Bassam tace mata da sauki har ya fita aiki ma, d'an mamaki ya kama Samira a ranta tana cewa lallai Bassam namiji ne, haka sukai ta hira Mammy tasa aka kawo mata abinci da abun sha daban-daban amma ta kasa tab'a komai saboda kunya, daidai lokacin ne ta mike tsaye tace zata tafi, kallon agogo Mammy tayi taga almost _5:20pm_ kuma gashi har yanzu Bassam bai dawo ba wanda a k'a'ida _4:00pm_ yake dawowa k'ololuwa _5:00pm_ dakatar da Samira tayi tace
"Barin d'auko wayata in kira shi bai dace kizo duban mara lafiya ki koma baki ganshi ba" murmushi kawai Samira tayi ta koma ta zauna yayin da Mammy ta mik'e ta nufi upstairs don d'auko wayar ta, ba'a d'auki minti biyu ba sai gashi ta sauko rike da waya tana dannawa, a tsakar d'akin taja ta tsaya ta fara neman wayar Bassam, sai da ta kira sa 3 missed calls ba wanda aka d'aga nan take jikin ta ya bata ba lafiya tazo ta zauna kan d'aya daga cikin sofas d'in da damuwa k'arara a fuskar ta, kallon ta Samira tayi tace
"Mammy lafiya kuwa?" girgiza kai Mammy tayi tace
"Bana tunanin lafiya Samira, na kira shi 3 missed calls bai d'aga ba jiki na ya bani ba lafiya" shiru Samira tayi yayin da hawaye ya d'an ciko idanun Mammy, wayar ta itama Samira ta d'auko ta shiga kiran Bassam, itama sai da ta kira sa har sau uku a jere amma ba wanda aka d'aga, hawayen da Mammy ke kokarin b'oyewa ne ya zubo mata a hankali tasa hannu ta share sai kuma wata dubara ta fad'o mata ta fara neman wayar Jabir, ringing d'aya a na biyu ya d'aga muryar Mammy na rawa bata tsaya amsa gaisuwar sa ba tace
"Jabir kana tare da Bassam ne?" gaban Jabir yayi mummunar fad'uwa ya mik'e tsaye ya d'an tattara confidence nashi ya saita muryar shi don kada Mammy ta fahimta yace
"A'a bama tare tun d'azu muka rabu da cewar zai je gida" kuka Mammy yanzu kam ta fashe dashi tana maimaita kalmar shahada, lallashin ta Jabir ya shiga yi yace "Baya gida ne?" cikin kuka Mammy tace
"Bai zo gida ba har yanzu mun kira sa 6 missed calls ba wanda ya d'aga, kun dade da rabuwa ne?" jinjina kai Jabir yayi yace
"Almost 2 hours ago" kuka Mammy keyi ba kama hannun yaro, cikin kwantar da murya yace "It's all right Mammy, gani nan zuwa" ya kashe wayar ya mik'e tsaye ya shiga saka system d'insa da sauran kayakin sa cikin jaka ya suri wayar sa ya fito cikin sauri ya rufe office d'in ya shiga tasa motar yaja ya bar wurin. Yana cikin tafiya ya kusa isowa wurin da abun ya faru ya hango motar Bassam, k'arawa motar sa gudu yayi ya isa wurin yayi parking ya fito ya nufi wurin motar, a bude ya ganta ya shiga waige-waige dama da hagun sa amma wurin shiru tsit sai kukan tsuntsaye kake ji, duba motar Jabir ya shiga yi bai ga alamar jini ko wani abu ba kuma ga keys d'in motar nan a jikin motar, juyowa yayi yana duba harabar wurin, nan ya samu jini kad'an, shiga motar yayi had'i da yin kicking yaja ta ya mayar da ita gefen hanya ya fito ya rufe yayi locking nata ya koma ya shiga motar sa ya nufi gidan Mammy. Koda ya shigo gidan da sauri yayi parking ya fito har yana had'awa da gudu ya shiga parlorn, koda ya shiga parlorn samun Samira yayi tare da Mammy tana ta faman lallashin ta da bata baki, suna ganin Jabir suka zabura Mammy ta mik'e tsaye wane Jabir ne zai kawo mata Bassam, cikin muryar kuka Mammy tace
"Jabir...?" sai kuma ta fashe da kuka, sosai ta bawa Jabir tausayi jikin sa yayi sanyi sosai ya k'araso daidai da ita ya riko kafadun ta ya jawo ta ya sanya ta cikin k'irjin sa ya shiga tapping bayan ta yana lallashin ta, sun d'auki minti kusan hud'u a haka sannan ya ciro ta daga k'irjin nasa yaja hannun ta ya zaunar da ita akan sofa, d'auko wayar sa yayi shima ya shiga neman wayar Bassam amma shiru, cikin kuka Mammy tace "Na sha gayawa Bassam ya fita hanyar yarinyar nan ba alkhairi tare da ita amma ya nace, this is what I've been telling him all this while, the moment you helped someone they will stab you in the back" shiru suka yi in banda kukan Mammy ba abunda kake ji yayin da shi kuwa Jabir yasan tabbas Alhaji Bala ne amma yana tsoron gayawa Mammy gaskiyar al'amarin, share hawayen ta Mammy tayi ta sake d'auko wayar ta ta shiga neman wayar Bassam to her very surprise taji alamar anyi picking, mik'ewa tsaye tayi zumbur yayin da Samira da Jabir ma suka mik'e da sauri, loudspeaker tasa don Jabir ya iya jiyo abunda za'a ce, gyara muryar ta tayi tace "Hello" shiru ba'a amsa ba kuma ta tabbatar call d'in ba katsewa yayi ba a hankali tace "Bassam?" dariya wacce tazo musu kamar saukar aradu suka ji an fashe da akace
"Bassam sai dai ki haifa wani" hawaye

Please Login or Register in order to submit comment