Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

nema yayi parking ya fito da sauri ya shiga parlorn. Samun ta yayi zaune a k'asa da tarin takardu a gaban ta da kuma system tana aiki akai, shigowar Bassam ne yasa ta tsaya da aikin yayin da shi kuma ya fad'a akan sofa, cike da kulawa take kallon sa tace
"Where have you been since morning?" murmushi Bassam yayi yace
"Come on Mammy I'm not a 2 year old boy da zaki fara investigating wurin da nike zuwa" murmushi itama tayi tace
"You are still a kid to me Bassam, tell me ina kaje?" dariya yayi yace
"It seems like kin manta na gaya miki I hit a girl d'azu da safe ko?" ya fad'a had'i da d'aga dukan girar sa questioningly, d'an buga goshin ta Mammy tayi tace
"Oh ya Salam! Na sha'afa wallahi, so, ya jikin ta?"

"Alhamdulillah! Taji sauk'i an discharging nata moreover I handed her to her parents"
"Ma sha Allah! Allah ya k'ara tsarewa baby"
"Ameen ya Allah" ya fad'a had'i da mik'ewa tsaye da sauri Mammy tace
"Abincin fa?"
"Sai nayi wanka first" ya fad'a a tak'aice ya fara tafiya
"All right!" cewar Mammy ta mayar da hankalin ta kan aikin ta shi kuma ya fice daga parlorn.



Shigar sa apartment d'insa ya wuce bathroom kai tsaye yayi wanka had'i da d'auro alwala koda ya fito an fara kiraye-kirayen sallar maghrib, nan take ya tada sallah bayan ya gama ne yayi addu'o'i ya shafa ya jawo wayar sa ya kira Hannah, sun dad'e suna hira sai da ya jiwo kiran sallar ishaa sa'annan yayi sallama da ita ya tashi ya bada farali. Bayan ya gama ya chanza kayan jikin sa zuwa pyjamas da singlet ya fito ya nufi wurin Mammy koda ya shiga parlorn bai same ta ba dining ya nufa ya bud'e food flasks d'in, sakwara ce da miyar egusi wanda taji nama da kifi sai pepper soup a k'yamace haka yake kallon su, sakwarar ya zuba kad'an zai fara ci aroman abincin ya daki hancin sa tsuki yaja ya ajiye ya nufi kitchen ya dafa ruwan zafi had'i da had'a tea ya dawo parlorn ya zauna yana sipping a hankali ya chanza channel da ya tarar zuwa ta ball daidai lokacin ne Mammy ta fara saukowa, sai da tabi ta dining taga abunda yai sa'annan ta k'araso parlorn ta zauna tace
"Ba zaka ci abincin bane?" kamar jiran ta yake dama ya ajiye cup d'in tea yace

"Mammy I told you bana san irin wannan abincin da ake yi"
"All right! Me kake so?"
"Something yummy mana" murmushi tayi tace
"Ok" k'walawa me aikin ta kira tayi cikin lokaci k'ank'ani tazo ta gaya mata ta girkawa Bassam wani abu but not traditional dishes baya so amsa mata tayi tare da mik'ewa da sauri ta nufi kitchen. Sai lokacin ya saki fuskar sa yace

"Yauwa.. Ya labarin yarinyar da kike gayamin an kashe?" dogon numfashi Mammy taja tace
"So far case d'in yana hannun 'yan sanda idan har sun kasa za'ayi filing case d'in a kotu" shuru Bassam yayi na wasu mintuka yace
"Wa zaiyi filing case d'in?"
"Ni mana" cewar Mammy "Iyayen ta sun dank'an komai a hannu na" gaban sa ne ya bala'in rikitowa k'asa sa'annan yace

"Amma Mammy wa ake zargin aikata kisan?" gyara zama Mammy tayi tace
"That's the worst part 'cause yarinyar da ake zargi anan gidan suke rik'e da ita" koro masa labari tayi kamar yadda Abba ya gaya masa tace "Sai da na gaya wa Zainab ta kiyayi irin wa'annan mutanen, poor people are such a mess they are good at destroying lives 'cause na sha ganin case irin wannan amma ta kasa fahimta" shuru Bassam yayi yana kallon Mammy yace
"Yanzu ina yarinyar?"
" 'Yan sanda sunyi nasarar cafke ta da marecen nan d'azu Zainab ta kirani tana sanar dani" zufa ce ta shiga karyo masa ta ko ina, Mammy ta fahimci haka tace
"Bassam lafiya kuwa?"
"Lafiya k'alau" ya amsa mata sa'annan yace "Allah ya kyauta"
"Ameen" cewar Mammy a sanyaye ya mik'e yace mata zai je ya kwanta yana jin bacci sosai, tayi mamaki 'cause suna b'ata dare suna hira amma yau 9:05pm yace zai kwanta sai da safe tai masa sa'annan ya juya ya fita.







*Shawty*πŸ’•
[1/8, 2:05 PM] β€ͺ+234 813 551 5123‬: *BARR. BASSAM*
(The Gallant) ❣




By *Shawty*πŸ’•

*2017*

2⃣6⃣

_This page is for you Kausar, A'ishah, Meena Sheriff, Ummi and Fauza. Thanks for the supportive role you are playing and a big holla to all *Red Chamber* members, you guys are blessing aswear. From the bottom of my heart, *ILYSM*_πŸ’ž


_Lol jama'a A'ishah almost killed me when she found out that I killed her in the novel since yesterday she's busy yelling at me😁no worries sweetheart I will resurrect you_🀣
________________________________________


Yana shiga bedroom d'insa ya fad'a kan gado yana tunanin an samu matsala kenan. Mammy zata yi handling case d'in which means ita dashi zasu fafata and he knows how extremist she is when it comes to her job. Shuru yayi yana ta tunani sai kuma muryar Kausar ta fara masa ringing a k'wak'walwa irin kukan da take yi lokacin da 'yan sanda zasu tafi da ita, tausayin su ita da iyayen ta ya kama shi mik'ewa yayi jiki ba k'wari ya nufi fridge ya bud'e. Ba komai a fridge d'in sai kwalaben giyar sa jere kamar wurin sayar da ita tsuka yaja ya rufe fridge d'in haushi ya rufe shi. Sam baya san wine na nan baya jin taste d'insu plus Sokoto ba irin garin da ke akwai bar bane ballantana yaje ya nemi foreign wine sai yanzu yasan yayi missing Scotland ba kad'an ba, haka yai ta juyi kan gadon har bacci ya sace shi.



_The next morning_
Ba shi ya tashi ba sai 6:00am mamaki ne ya kama sa yadda yayi bacci haka, mik'ewa yayi ya shiga bathroom yayi wanka ya d'auro alwala yayi sallah ya sake komawa kan gadon nan take kuma wani baccin ya kuma awon gaba dashi. Sai 9:15am ya tashi yayi brush sa'annan straight ya nufi cikin gidan, koda ya shiga Mammy ce ke shirya takardu a cikin wata 'yar briefcase ta shirya tsaf cikin suit da alama fita zata yi, murmushi tayi da taga shigowar Bassam tace
"Yanzu nike cewa zan shiga in ganka kafin in tafi" murmushi shima yayi had'i da zaunawa kan sofa yace
"Morning"
"Morning how was your night?" tace dashi sai kai komo take da alama sauri take, dining yaga ta nufa ta had'a lipton tazo tana sha. Kasa zama tayi a tsaye take shan lipton d'in bata yi four good sips ba ta ajiye cup d'in ta fara tattara kayan ta, Bassam sai ido ya bita dashi yana kallon every move nata, mik'ewa tayi ta rataya jakar system nata ta kwashi wayoyin ta 'yar briefcase d'in kuwa ta rik'e ta a hannu. Murmushi tayi tace

"Ba zaka raka Mammy bane?" murmushin shima yayi had'i da mik'ewa ya karb'i jakunkunan hannun ta, tana gaba yana biye da ita suka fito sai sauri take
"Mammy office zaki je ne naga sai sauri kike" haka ta tsinto muryar Bassam daga bayan ta, tsayawa tayi cak ta juyo tace
"Yeah sweetheart, inada aiki ne sosai yau"
"Ok" cewar Bassam da haka har suka iso parking lot, shi ya bud'e mata mota yasa mata jakunkunan ta a ciki sa'annan ya tsaya tall a gaban ta, hannun sa tai grabbing ta masa peck tace
"Take care of yourself ok? You've grown taller bana isa goshin ka" dariya kawai yayi baice komai ba yayin da ta shiga motar ta zauna tace "In daina you are not a 2 year old boy ha?" nan ma dariya yayi tace "Yeah nasan abunda zaka ce kenan" murmushi yayi ya rufe mata motar yace
"Allah ya kiyaye"
"Ameen" ta amsa sa'annan tace "Yau ba zaka fita ba?"
"Yanzun nan da nayi breakfast"
"All right!" ta fad'a taja motar ta a hankali yayin da mai gadi ya bud'e mata gate ta fita. Sai da ta fita sa'annan ya koma ciki yayi breakfast ya koma sashen sa ya sake wani wankan ya shirya cikin suit ya fito yayi kyau sosai lokacin ne ya fara neman wayar Jabir, ringing d'aya a na biyu ya d'aga yace
"Kana ina ne?"
"Office" Jabir ya amsa
"Ok gani nan zuwa" ya katse kiran ya nufi parking lot ya bud'e motar sa ya shiga yaja.



Ba dad'ewa had'uwar su da Jabir yace ya tashi su shiga neman wacce Police Station aka kaita, haka kuwa akayi sai da suka je Police Station biyu duka basu same ta ba sai a na ukun suka same ta, gabatar musu da kansa yayi sa'annan yace shine lauyan ta kuma yana so zai yi magana da ita ba musu aka masa jagora zuwa wani d'an k'aramin d'aki da aka tanada don ganawa da masu laifi ya zauna ba'a dad'e ba sai ga d'an sanda ya shigo tare da ita. Mummunan fad'uwa gaban Bassam yayi da idanun sa suka sauka a kanta bai san lokacin da ya cire glasses d'in fuskar sa ba ya zura mata ido, fuskar ta ya gani tayi jajir ta kumbura alamar duka haka gashin kanta a hargitse ba d'ankwali ga baki d'aya ta fice daga hayyacin ta idan ba yayi mata kallo me kyau jiya ba zai iya rantsewa da Allah ba ita bace, juyar da kansa yayi gefe d'aya yayin da Kausar sai kallon sa take tana mamakin wannan wane irin mutum ne. K'arasowa d'an sandan yayi da ita yaja mata kujera mai kallon wacce Bassam ke kai ta zauna yayi cuffing nata da table sa'annan ya juya ya fita. Sai da Bassam ya tabbatar ya fita sa'annan ya juyo da kansa yana kallon ta, itama kallon sa take cike da mamaki cikin disashshiyar murya wacce ko fita sosai bata yi akan azabar kuka tace

"I will give you a lift, zan kaiki inda zaki je Ok? Daga nan zan kama gaba na. Maganar da ka gayamin kenan jiya da na had'u da kai me kuma ya dawo da kai?" instead ya amsa tambayar da tai masa sai cewa yayi
"Suna na Barr. Muhammad Bassam Muhammad" tunanin ta ne yaje yawo da taji ya fad'i sunan it seems like ta tab'a jin sunan a wani wurin, a razane ta d'ago kai tana kallon sa sai yanzu ta tuna shine suka je gidan su da A'ishah kwana biyu kafin a kashe ta, shine wanda A'ishah ta kamu da sonsa a ranar da ta fara ganin shi kuma shine d'an Barr. Hindu k'awar Momy wato Hajiya Zainab, hawaye ne suka zubo mata a hankali tasa hannu ta share sa'annan tace
"Ba wannan na tambaye ka ba, me ya dawo da kai?"
"I'm here to help"
"Help?" cewar Kausar, jinjina kai yayi yace
"Sosai I'm here to help you" wani gajeren murmushi Kausar tayi tace
"You are wrong. You are dead wrong. Ina shawartar ka da kada ka shigo cikin case d'innan" gyara zama Bassam yayi yace
"Meyasa?" kallon sa yanzu take ido cikin ido tace
"Ina gaya maka ka fita case d'innan, it's not normal ba irin cases da ka saba yi bane they will kill you too" kallon ta yake shima cikin ido yace
"Wa ke nan?"
"Whoever is behind this" ta amsa a tak'aice, gwauron numfashi Bassam yayi yace

"Kenan kin san wanda ya kashe A'ishah" girgiza kai tayi yayin da idanun ta suka chanza launi daga fari zuwa ja cikin wata irin murya da bazan iya fassara ta ba tace
"Of course na sani"
"Waye?" cewar Bassam da sauri, kallon sa take ko k'iftawa bata yi tace
"Ni na kashe A'ishah!" razana Bassam yayi dan kwa bai tab'a tunanin jin haka daga bakin ta ba, cikin mamaki yace
"Excuse me" ya fad'a yana kallon ta ba alamar tsoro ko fargaba tare da ita, confidently tace
"Yeah I killed her"
"Excuse me" cewar Bassam "I either misheard you or you misspoke" confidently ta sake cewa
"No, you heard me correctly Barrister, ni na kashe A'ishah!" mik'ewa tsaye Bassam yayi had'i da kafa glasses a fuskar sa ya d'auki diary d'insa ya kalle ta da kyau yace
"Thanks idan da buk'atar in dawo zan dawo" kallo ta bishi dashi yayin da hawaye suka shiga yi mata ambaliya kamar an bud'e fanfo fita yayi daga d'akin yaje wurin 'yan sandan yai musu sallama ya fito yayi daidai da kawowar motar Mammy bakin Police Station d'in, gaban sa ne ya d'an fad'i kawai ya dake cikin tafiyar sa ta izza ya nufi motar sa kamar ma bai ganta ba ya shiga ya tada dama Jabir yana ciki ja kawai yayi suka bar wurin. Yayin da Mammy kuwa mutuwar tsaye tayi cikin motar ta kasa fitowa ta tsaya tana kallon sa har ya bar wurin
"Bassam?" ta fad'a a fili k'irjin ta na dukan uku-uku, bata da k'arfin da zata yi aikin da ya kawo ta jan motar ta tayi a sanyaye ta bar wurin itama.




*Masu yimin complain basa samun post nawa da wuri da masu cewa na turo musu a PC kuma suka ga ban turo musu ba duka I'm sorry, I'm very busy these days amma ga shawara wa'anda basa samun post nawa da wuri da wa'anda suke cewa na turo musu ta PC ina disappointing nasu zan bud'e group idan nayi posting a ciki kowa zai gani yafi akan in tura wa kowa individually ga number na ga mai so sai ya min magana in saka shi 07069602381. Thanks. ILYSM*πŸ’ž




*Shawty*πŸ’•
[1/8, 2:10 PM] β€ͺ+234 813 551 5123‬: *BARR. BASSAM*
(The Gallant) ❣




By *Shawty*πŸ’•


*2017*

2⃣7⃣

Straight office ta nufa sai dai ta kasa tab'uka komai ta rasa wane dalili ne yakai Bassam Police Station da Kausar take, kasa hak'ura tayi ta d'auko wayar ta ta fara neman wayar sa, missed calls uku tai masa a jere ba wanda ya d'aga mamaki ne ya cika ta kada fa zargin da take yi ya zama gaskiya, ba don ta gama ayyukan da zata yi ba ranar kawai ta shiga tattara abubuwan da tasan zata nema ta fito ta shiga motar ta, gida ta nufa kai tsaye sai Allah-Allah take ta samu Bassam a gida da haka har ta iso gidan.



_4:30pm_
Sai k'arfe hud'u da rabi na marece Bassam ya dawo gida, straight apartment nasa ya nufa yayi wanka ya chanza kayan jikin sa zuwa shorts, kwantawa yayi kan gado yana tunanin yadda zasu k'ark'are da Mammy ya tabbatar ta gansa a Police Station d'in shiyasa ta kira sa har kusan three missed calls. Da k'yar ya tashi ya fito ya nufi cikin gidan, a parlor ya same ta tana kallo hankalin ta sosai ya tafi a kallon, shigowar mutum ne yasa ta juyo don ganin ko waye ganin Bassam ne yasa ta d'auke kanta ta cigaba da kallon da take, k'arasowa Bassam yayi cikin parlorn ya zauna kusa da ita. Har yanzu idanun ta na akan tv but honestly jira kawai take taji ta ina zai fara, cikin sanyin murya yace
"Mammy" shuru tayi kamar bata ji shi ba, cikin sanyin murya ya k'ara cewa "Mom?" sai a lokacin ta juyo fuskar ta a murtuk'e tace
"What took you there?"
"Where?" ya fad'a as if baisan abunda ke faruwa ba, kallon sa take yi kawai tace
"Where I saw you" shuru yayi kamar yana nazarin wani abu yace
"Mammy bansan me kike fad'a ba, a ina kika ganni?" masifa ta fara yi tayo kansa wane zata cinye sa tace
"Don't bullshit me Bassam, kar ka nemi raina min hankali, I said me ya kai ka Police Station d'azu da safe" murmushi yayi yace
"Oh! Sorry! Wajen Kausar naje"
"Whaaaaaattt!!" cewar Mammy cikin k'araji tace "You gotta be kidding me" d'an d'aga kafad'un sa yayi yace
"I'm serious Mammy"
"Ka san kuwa case d'inta ne nike akai?"
"Na sani" cewar Bassam hankalin sa na akan tv sam bai bawa conversation d'in muhimmanci ba, cikin fushi tace
"Bassam kar mu fara haka da kai, kinda stay out of my case" murmushi yayi yace
"It's mine also, abunki nawa ne ae" mamaki ne tsintsa ya rufe Mammy tace
"Bassam are you kidding me?" sai yanzu ya juyo yana kallon ta yace
"Mammy we are all doing our job, ain't we?"
"Bassam kasan kuwa abunda ta aikata? Kisan kai fa!"
"No! Ba ita ta kashe A'ishah ba!"
"If not her, then who did?" d'aga kafad'un sa yayi yace
"I don't know but I believe we will find out" cikin fushi Mammy tace
"Well, idan ma kana k'ok'arin kare ta ne this girl is guilty shaidu sun nuna da hannun ta dumu-dumu a wannan badak'alar"
"Wannan ba shaida bane Mammy, duk wad'annan abubuwan da kuke kawowa ba zai tab'a proving Kausar ita ce ta kashe A'ishah ba"
"Well, miye naka shaidar akan ba itace ta kashe ta ba?"
"I don't have any but I believe we will find out plus her parents confirmed that Kausar ba zata iya kashe kowa ba talkless of A'ishah da suka shak'u sosai" dariya Mammy tayi sosai tace
"You believe that's true? Dama zasu kasa goyon bayan 'yar su ne? Bassam you barely know what poor people are capable of doing" shuru yayi bai ce da ita komai ba, cikin kakkausar murya fuskar ta ba alamar wasa tace "And let me say this very simply stay the hell outta my case" kallon juna suke yi fuskar Mammy ba alamar wasa mik'ewa tayi tsaye ta bar parlorn.



Gefen Kausar kuwa zaune take a cikin cell ta had'a kai da gwiwa ba abunda take sai kuka, kuka take yi wanda a yanzu ya zama kamar abinci a wurin ta. Ta rame tayi bak'i kamar ba ita ba kullum cikin azabtar da ita ake abinci ma sau d'aya ake bata a rana sai kuma gobe duk da haka kad'an kawai take ci don kadda yunwa tai mata illah. Tana a wannan yanayin ne taji kamar ana tab'a k'ofar cell d'in da sauri ta d'ago kai don ganin ko waye, wani mutum ne k'ato bak'i mummuna sanye cikin kayan 'yan sanda da alama shine babban a wannan division d'in wato DPO tare da wasu k'ananan 'yan sanda guda biyu wanda suke take masa baya, bud'e cell d'in suka yi yayin da babban d'an sandan ya shigo sauran kuma suka tsaya daga bakin k'ofa, tsugunawa mutumen yayi kusa da ita yace
"I'm gonna ask you some questions and you're gonna answer them. The sooner you do, the sooner we will be done" jinjina kai Kausar tayi alamar taji, murmushi yayi har hak'oran sa suka fito wanda ya k'ara masa muni yace "Good! Da farko Kausar meyasa ba zaki yiwa kanki adalci ba ki hutar damu kuma ki hutar da kanki?" kallon sa take don ita bata ma gane me yake nufi ba, murya k'asa-k'asa yace "Meyasa kike da taurin kai? Meyasa ba zaki karb'a laifin kiba?" girgiza kai tayi in disbelief hawaye suka fara gudu a kumatun ta, cikin muryar kuka tace

"Bansan komai ba akan kisan A'ishah" murmushi d'an sandan ya k'ara yi yace
"Ni nasani kuma ga yadda abun ya faru..." zabura tayi da k'arfi wanda yasa ya dakatar da maganar da yake yi tana kallon sa cikin mamaki, murmushi yayi yace "Kina mamaki ne? Kin had'a kai da armed robbers suka shiga gidan Alhaji Bala suka yi robbery suka kwashe masa mak'udan kud'ad'e, baki barsa a haka ba sai da kika yi nasarar kashe masa 'ya wacce kowa ya tabbatar daren da abun zai faru bata gidan kika kira ta a waya kika yi nasarar brain washing nata ta dawo gidan cikin daren ba tare da kowa ya sani ba kika aikata mummunan k'udurin ki" kuka mai ciwo Kausar ta fashe dashi kuka mai tsuma rai numfashin ta har sama da k'asa yake yi cikin muryar kuka wacce ko fita sosai bata yi tace
"Ba ni na kashe A'ishah ba" murmushi d'an sandan yayi yace
"Zata yiwu ba ke kika kashe ta da hannun ki ba amma definitely akwai umurnin ki a kisan marigayiya A'ishah" kuka take tana girgiza kai yanzu ko maganar ta kasa murmushi kawai d'an sandan keyi yace "You are smart girl now right? Kin b'oye munanan halayen ki a inuwar bak'ak'en halayen ki ko? You did something no one believes it's possible kina tunanin kin zaki iya b'ata hankalin kowa ko? Kinyi kuskure Kausar, ba zaki iya b'ata hankalin 'yan sanda ba kuma ina miki albishir nan bada jimawa ba hukuncin kisa zai hau kanki" mik'ewa yayi tsam suka fita had'i da rufe cell d'in suka barta, kwantawa tayi a k'asa tana rusa kuka gwanin tausayi.


Fitar sa keda wuya wayar sa ta fara ringing, dubawa yayi yaga number ce ba suna d'aga kiran yayi yasa a kunne gami da cewa

"Hello"
"Ranka ya dad'e Officer kana magana da Alhaji Bala" washe baki d'an sandan ya shiga yi yace
"Ah Alhaji kaine ka kira ni da kanka?"
"Bakomai Officer ni ke nema saboda haka dole nine zan bi" dariya d'an sandan yayi cike da jin dadi sa'annan Alhaji Bala yace "Officer ina neman alfarma ka ware minti talatin daga cikin aikin ka kazo gida na ka same ni zamuyi magana" da sauri d'an sandan yace
"Ah Alhaji don wannan kawai? Karka damu gani nan zuwa"
"Nagode Officer" cewar Alhaji Bala had'i da katse kiran. Ba b'ata lokaci d'an sandan ya chanza hanya daga zuwa office dinsa zuwa hanyar fita station d'in, straight wurin motar sa ya nufa ya shiga ya tada ya bar wurin.






*Shawty*πŸ’•
[1/8, 2:17 PM] β€ͺ+234 813 551 5123‬: *BARR. BASSAM*
(The Gallant) ❣




By *Shawty*πŸ’•


*2017*

2⃣8⃣

Isar sa gidan ne ya danna horn, ba dad'ewa mai gadi yazo ya bud'e masa gate. Alhaji Bala wanda dama tunda suka yi wayar yake tsaye a farfajiyar gidan yana jiran isowar sa, murmushi yayi da yaga shigowar motar sa ya taka ya nufi wurin da yayi parking. Fitowa d'an sandan yayi suka gaisa da Alhaji Bala sosai cikin girmamawa sa'annan Alhaji Bala ya kalli motar da d'an sandan yazo da ita Kompressor ce blue ta d'an sha wuya da ka ganta then ya juyo yana kallon sa yace

"Officer ya kamata a chanza wannan motar" murmushi d'an sandan yayi yana sosa bayan kansa da keys na motar sa yace
"Ae Alhaji abubuwan ne sai a hankali" murmushi Alhaji Bala yayi yace
"Gaskiya ne, toh mu shiga daga ciki" ba musu d'an sandan yabi bayan Alhaji Bala har zuwa sashen bak'i ya bud'e suka shiga, nan ma wata duniyar ce ta daban uwa ba'a mutuwa zaunawa d'an sandan yayi sai kalle-kalle yake yayin da Alhaji Bala bai zauna ba straight fridge ya wuce ya had'o masa fruits da kayakin

Please Login or Register in order to submit comment