Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

aikin tsayar da jinin da ke fita ta k'irjinsa, ganin hakan ne yasa budurwar itama ta finciko d'ankwalin da ke kanta ta yaga shi gida biyu ta fara d'aure wuraren da harsashen suka shiga a k'afarsa yayin da kowane move nata Jabir na lura dashi ta wutsiyar ido, cikin sanyin murya tace "Jinin nan ba fa zai tsaya ba ya dace mu tafi asibiti kada ya mutu" jinjina kai Jabir yayi ya mik'e tsaye da sauri don kuwa a firgice ma yake he can't think of a better dialogue, kinkimar Bassam yayi da taimakon budurwar suka saka Bassam a motar sa Jabir ya shiga yaja motar yayin da ita kuma budurwar ta rufa masa baya zuwa asibitin. Da farko da suka isa asibitin k'in karb'ar su suka yi a cewar su sai anzo da 'yan sanda, presenting ID cards nasu Jabir yayi yai musu bayani cewar he's been shot kuma baya rasa nasaba da wani case da yake kai plus idan basu karb'e sa ba zuwa neman d'an sanda ka iya jawo mutuwar sa saboda he lose alot of blood, sai a lokacin budurwar tayi magana tace
"Please doctor help him he's dying, idan baku tab'a sa ba komai zai iya faruwa dashi" had'i da ciro ID card nata wanda ke nuna zaman ta Nurse a wani asibitin ta nuna masa ta k'ara da cewa "It's not a big deal halban sa akayi kuma kan ido na nazo wucewa abun ya faru" shiru likitan yayi sa'annan yace
"Abunda kuke so nayi karya doka ce fa" da sauri Jabir ya tari numfashin sa yace
"Bamu ce ba za'a zo da jami'in tsaron ba, what we are after is that you take an action, he lose alot of blood" jinjina kai likitan yayi ya bada umarnin aje a d'auko Bassam, bada dadewa ba sai gashi anzo dashi kan gadon da ake tura marasa lafiya. Bayan doctor ya gama duba sa ya kira Jabir zuwa office nasa, bayan sun zauna ne doctor yace
"Barrister akwai matsala" da sauri Jabir ya kalle sa yace
"Innalillahi! Matsalar mene?"
"Well, several bullet fragments lodged in his chest we need to operate as soon as possible idan ba haka ba zai iya rasa rayuwar sa"
"Innalillahi!" cewar Jabir sa'annan yace "Then what about bullets d'in na k'afar sa?" rausayar da kai likitan yayi yace
"Wannan mai sauki ne compared to na kirjin" mik'ewa Jabir yayi da sauri yace
"Ba damuwa doctor, we are running out of time ayi kawai fatar mu Allah ya basa lafiya" jinjina kai doctor yayi ya mik'e tsaye yayin da Jabir ya juyo ya kalle sa yace "But how sure are you he will survive this?" cike da rashin k'warin gwiwa doctor yace
"50%" jinjina kai Jabir yayi ya juya ya fita likitan ma ya rufo masa baya. Nan take aka fara shirin shiga da Bassam operation wanda duk abunda ake tare da Jabir da kuma wannan budurwar ne sai da aka shiga dashi sa'annan suka dawo suka zauna jugum-jugum, sai a lokacin Jabir ya tuna Bassam ya gaya masa Mammy tayi fushi dashi har ta kore shi daga gidan ta
"But ya kamata ta san abunda yake faruwa" cewar Jabir, da sauri budurwar ta kalle sa tace
"Wacece?" mamaki ya kama Jabir 'cause bai yi tunanin a fili yai maganar ba, a sanyaye yace
"His Mum" jinjina kai budurwar tayi tace
"Hakane ya kamata gaskiya" mik'ewa Jabir yayi ya nufi mota da yake duk wayoyin su suna a motar, d'auko wayar Bassam yayi ya kira Mammy two missed calls bata d'aga ba baiyi mamaki ba ya shiga neman ta da tasa wayar ringing d'aya ta d'aga had'i da cewa
"Jabir..." da sauri ya katse ta had'i da cewa
"Ma'am..." sai kuma ya rasa ta ina ma zai fara, a sanyaye Mammy tace
"Jabir lafiya kuwa? Ina Bassam?" numfashi Jabir ya saukar had'i da cewa
"Ba lafiya" kwance Mammy take amma sai da ta mik'e tsaye cikin rawar murya tace
"Jabir me yake faruwa? Ina Bassam? What happened to him?" cikin rarrashi Jabir yace
"Calm down! You need to be here, Bassam is shot kuma..."
"Whaaaaaattt?" cewar Mammy cikin karaji, muryar ta har tana rawa tace "Kuma ya mutu right? Right? Is that what you called to tell me?"
"No ma'am! Bassam yana nan da ransa yanzu haka an shiga dashi operation you just need to be here" yanzu kam kuka take already tace
"Innalillahi wa innaa ilaihi raji'un! A wanne asibitin ne?" gaya mata Jabir yayi tace "Nagode gani nan zuwa" had'i da katse kiran, kallon budurwar Jabir yayi yace

"Dare ya fara yi ya kamata kije gida" jinjina kai budurwar tayi tace
"Ina jira ne har mahaifiyar sa tazo" d'an kallon ta Jabir yayi a kaikaice yace
"Ya sunan ki ne?" a sanyaye tace
"Samira" jinjina kai Jabir yayi had'i da yin murmushi yace
"Nice name, sunana Jabir" daga nan kuma ya d'an labarta mata dangantakar sa da Bassam har izuwa yau, cikin mintuna goma sai ga Mammy ta iso asibitin a firgice idan ma ka kalli shirin ta kasan cewa bai samu had'in da ya dace ba, Jabir ne ya taimaka mata ta fito daga cikin motar sai kuka take wane wacce aka tabbatar wa Bassam din ya mutu, rarrashin ta Jabir ya shiga yi yana kwantar mata da hankali amma kamar yana zuga ta ne haka tai ta kuka to the extent bata da strength na kukan anymore, sai a lokacin ta lura da Samira ta tambayi Jabir wacece ita, d'an iyakacin bayanin da ya sani game da ita ne ya koro wa Mammy, murmushi Mammy tayi tai mata godiya had'i da cewa taje gida dare yayi ba musu ta amsa da toh tai musu sallama da cewar in shaa Allah gobe zata dawo taga jikin sa, sosai Mammy taji dadi yanda ta kula da yaron ta ta k'ara yi mata godiya sa'annan ta tafi, juyowa tayi kan Jabir tace
"Jabir kaima ya dace kaje gida tunda gani nazo" girgiza kai Jabir yayi yace
"No, na bugawa Baba na sanar masa abunda yake faruwa ba wani damuwa in shaa Allah" sosai Mammy taji dadi a haka suka zauna jugum-jugum suna jiran tsammani.




_6:00am_
Da misalin karfe shida na safe wanda gari ma bai ida wayewa ba Alhaji Bala ya fito daga cikin gidan sa zuwa farfajiyar gidan, da sauri haka yake tafiya har ya iso parking lot din ya bud'e motar sa ya shiga ya tada yaja ya bar gidan, gudu yake kan titin yau ma kamar wanchan ranar ya kama hanyar fita garin Sokoto ne wanda baya rasa nasaba da zuwa wurin wannan bokan nasa. Gudu kawai yake fanfalawa kan titin sakamakon ba yawan abubuwan hawa har ya iso k'auyen, jin tsayuwar mota yasa bokan fitowa a dudduk'e daga cikin bukkar, cikin sigar fad'a yace
"Bala ni da nace kazo tunda asuba sai yanzu kazo?"
"Ayi hakuri wallahi bacci ne ya sace ni" juyawa bokan yayi ya koma cikin bukkar yace
"Zo da sauri sai da na gaya maka kazo da asuba anfi samun nasara da asuba" bayan sa Alhaji Bala yabi har zuwa cikin bukkar wacce oval shape ce an zagaye ta da jan k'yalle, wani wuri cikin bukkar bokan ya nuna wa Alhaji Bala had'i da umurtar sa ya zauna, ba musu ya zauna shima bokan ya koma nasa wurin zaman ya zauna. Kallon sa bokan yayi ya d'auko wani k'ullin garin magani yana jujjuya shi a hannu yace
"Wannan shine maganin da zan k'ona had'i da kiran sunan ta, zata bayyana sa'annan zan k'ona wani maganin" ya sake juyawa ya d'auko wani k'ullin maganin yace "Idan na k'ona wannan to ta zama baiwar ka kenan sai ka gaya mata bukatar ka da abunda kake so tai maka sai dai.."
"Sai dai me?" cewar Alhaji Bala
"Ba'a siffar mutane zaka ganta ba a fatalwa zaka ganta saboda haka ka kiyaye" jinjina kai Alhaji Bala yayi yayin da bokan ya jawo kasko na farko wanda garwashi ne a ciki ya fara warware k'ullin garin maganin ya fara marmasawa akan garwashin, sai da garin maganin ya k'one tas hayaki ya turnuke bukkar bokan ya rintse idanun sa ya fara wasu sambatun sa na tsafi, bai d'auki minti biyar ba sai ga A'ishah ta bayyana a bangon bukkar cikin fararen kaya iska na hura ta, murmushi bokan yayi yayin da Alhaji Bala ya mik'e zumbur kamar wanda aka tsikara yana k'are mata kallo ya nufi wurin da take tsaye muryar sa na rawa yace
"A'ishah? A'ishah kece da gaske?" tsawa mai firgitarwa bokan ya daka masa had'i da cewa
"Bala dawo ka zauna!" ba musu ya dawo ya zauna a mazaunin sa jikin sa sai b'ari yake yana maimaita kiran sunan A'ishah, kallon sa bokan yayi yace
"Wannan ba 'yar ka bace fatalwar ta ce kuma bata rigaya ta zama baiwar ka ba saboda haka zata iya cuta maka ka kiyaye na gaya maka" jinjina kai Alhaji Bala yayi yayin da bokan ya jaye wanchan kaskon na farko daga gaban sa ya jawo na biyun wanda shima iri d'aya ne da na farkon, wani garin maganin ya sake warwarewa ya fara marmasawa kan garwashin lokaci d'aya yana surutai, nan take fatalwar ta fara wani ihu mai k'araji da amo bukkar wacce sai girgiza ta ake iska kuma kamar ya d'auke ta ya tafi da ita shi kuwa bokan har yanzu bai daina marmasa maganin yana karanto tsafin sa ba, sai da ya shafe fiye da minti biyar yana haka sa'annan ya daina yayi daidai da k'arewar maganin shiru tsit cikin bukkar yayi kamar wani abu bai tab'a faruwa ba, da murmushi kwance a fuskar bokan ya juyo yana kallon Alhaji Bala yace
"An samu nasara Bala, fatalwar A'ishah ta zama mallakin ka saboda haka ka umurce ta da duk bukatar da kake so zatai maka" gyara zama Alhaji Bala yayi cikin sanyin murya yace
"A'ishah" k'ura masa ido tayi bata ko kyaftawa kamar tana sauraren abunda zai fad'a, a sanyaye Alhaji Bala yace "Ina umurtar ki a duk inda Alhaji Kabara ya shiga ki nemo sa ki shiga jikin sa ki sanya shi yayi wa kansa tonon silili akan duk abunda ya aikata daga k'arshe kamar yadda yayi sanadiyyar mutuwar ki kema ki kashe sa" jinjina kai tayi har sau uku sa'annan ta b'ace b'at, wata mahaukaciyar dariya dukan su suka fashe Alhaji Bala yace
"Kabara kai k'aramin d'an iskan matsafi ne".






*Shawty*💕
[1/8, 6:59 PM] ‪+234 813 551 5123‬: *BARR. BASSAM*
(The Gallant) ❣





By *Shawty* 💕

*2017*

4⃣0⃣

_The next day_
_4:00pm_
Bassam ne kwance shantam akan gadon asibiti kafar sa inda bullets din suka shiga a daddaure da bandage yayin da kirjin sa ma an lafta masa bandage, gefe daya kuma Mammy ce zaune a gaban gadon da Bassam ke kwance ta rafka tagumi, lokaci zuwa lokaci hawaye su gangaro mata ta share wani lokacin kuma sai tayi kukan sosai take samun sauki tana imagining idan Bassam bai tashi ba shikenan, a hankali Bassam ya fara bud'e idanun sa wanda Mammy bata ma lura ba saboda tayi nisa cikin tunani, a hankali a hankali har ya bude idanun gaba daya suka sauka kan Mammy, Mammy bata yi aune ba sai ji tayi ya kira sunan ta
"Mammy" zabura tayi ta juyo tana kallon sa lokaci daya kuma murmushi ya subuce mata, cikin sanyin murya tace
"Bassam?" sai kuma ta d'aga kai sama tace "Alhamdulillah ya Allah" ta maida kallon ta akanshi tace "Sannu Bassam" d'aga mata kai kawai yayi alamar amsawa a hankali ta riko hannun sa d'aya ta hada da nata yayi daidai da shigowar Jabir da Samira cikin dakin, gaisawa suka yi da Mammy Samira ta karaso kusa da Mammy ta dire babban food basket cike da coolers na abinci, murmushi Mammy tayi tace
"Hada dawainiya haka?" murmushi Samira tayi ta dukar da kanta tana wasa da wayar ta, murmushin itama Mammy tayi tace "Mun gode sosai Allah ya saka da alhairi"
"Ameen" ta amsa sannan tace "Ya mai jiki?" nan ma murmushi Mammy tayi ta kalli Bassam tace
"Alhamdulillah jiki da sauki yanzun nan ya farka" hada ido suka yi da Bassam ta sakar masa murmushi sannan ta maida kallon ta akan Mammy tace
"Allah ya kara sauki"
"Ameen" Mammy ta amsa sannan ta kalli Bassam wanda kansa ya bala'in daurewa don kuwa shi ko a dangi baisan wannan ba, in a serious face Mammy take kallon sa tace
"Bassam ka gani ba? Kaga abunda sukai maka ba? Bassam.." kara matse hannun ta Bassam yayi yace
"It's all right Mammy" hade fuska tayi tace
"It's not all right Bassam, there's no goodness in this girl" a sanyaye Bassam yace
"There's goodness in Kausar" har ga Allah Samira taji haushi yadda taji yayi complimenting wata though bata san ko wacece kuma bata san labarin su ba, a sanyaye Bassam yace "Mammy ya zaki yi tunanin Kausar ce tasa aka harbe ni wacce presently tana jail kuma..." katse shi Mammy tayi tace
"But she can plot it"
"She's just 19 fa, how do you expect a 19 year old can plot all these shit?" murtuke fuska Mammy tayi tace
"Bassam ba fa zaka iya gyara Kausar a ido na ba saboda haka just tell me that you quit the case, bana so na rasa ka Bassam wallahi zasu iya kashe ka" sai kuma idanun ta suka yi raurau, jinjina kai Bassam yayi yace
"I quit" ko kadan Mammy bata yi tsammanin jin haka daga bakin Bassam ba cikin sauki cike da farin ciki tace
"Are you serious sweetheart?" gyada mata kai yayi alamar eh yana murmushi, dukawa tayi tai kissing forehead nasa tace
"Thank you sweetheart, Allah ya baka lafiya"
"Ameen" suka amsa gaba daya sannan Mammy ta mike tsaye ta kalli Jabir tace
"Jabir please help him yaci abinci zanje naga wani client nawa yana jira na a office"
"Ok" Jabir ya amsa sannan ta juyo ta kalli Bassam ta shafa kansa tace
"I'll be back soon sweetheart, take care of yourself ok?" jinjina kai Bassam yayi alamar toh yana murmushi, a gurguje Mammy tai musu sallama ta fice daga dakin. K'arasowa Jabir yayi ya zauna gefen gadon ita kuma Samira ta zauna a wurin da Mammy ta tashi, kallon ta Bassam yake yi daga sama har kasa sannan ya juyo ya kalli Jabir irin wannan kuma fa, murmushi Jabir yayi yace
"She's Samira, jiya da aka harbe ka itace ta taimake ni muka kawo ka asibiti, guy I'm telling you Jiya ba itace ta bar asibitin nan ba sai after 10pm" sai a lokacin Bassam ya dan rage kallon Banzan da yake mata ya jinjina kai yace
"Thanks" a takaice, murmushi Samira tayi bata ce komai ba yayin da Bassam ya mayar da kallon sa kan Jabir yace
"Kwana na nawa a nan?" dan juyar da kai Jabir yayi yace
"Jiya ne kwanan ka daya"
"What did the doctor said?" ya kara tambayar Jabir
"They removed all the bullet fragment and he said there is no permanent damage" cewar Jabir, jinjina kai Bassam yayi a hankali yace
"Alhamdulillah" a hankali ya fara kokarin tashi zaune sai dai wani azabar ciwo da yaji daga aikin da akai masa a kirjin sa wata k'ara ya saki ya koma kwance ya cije lebe, da sauri Jabir yai kansa had'i da cewa
"Easy man" sake kokarin tashi zaune yayi da dubara da kuma taimakon Jabir ya tashi zaunen Jabir ya yasa masa pillow a baya ya jingina akai sannan yace
"Jay ina son ganin doctor"
"Me zaka gaya masa?" cewar Jabir, a sanyaye yana lumshe ido yace
"I need to leave" cikin mamaki Jabir yace
"Kana cikin hankalin ka kuwa? Da wannan bandages din zaka bar asibiti? Beside na tabbata ko tsayuwa ma ba zaka iya ba sosai kake nema ka bar asibiti wait.. Idan ma ka bar asibitin ka koma gida me zakayi inace a nan ka gayawa Mammy ka daina case din, I think the other cases I can handle them" murmushi Bassam yayi yace
"It's not safe here Jay mutanen zasu iya biyo ni a nan, plus na gayawa Mammy hakane don kawai hankalin ta ya kwanta mu zauna lafiya"
"It's not safe out there too, kana tunanin barin asibitin da wuri shi zai sanya su daina bibiyar ka?" girgiza kai Bassam yayi yace
"Nope but at least ba'a wuri daya nike zaune ba zai musu wuya suyi tracing nawa plus I will be cautious but nan kaga komai zai iya faruwa" girgiza kai Jabir ma yayi yace
"Bassam ya dace ka daina case dinnan"
"Ita fa yarinyar? Su kashe ta kenan?" cewar Bassam
"A'a ba haka nike nufi ba"
"Then?" cewar Bassam
"Allah ba zai basu iko ba, ba zasu samu damar yin hakan ba Allah zai kubutar da ita, Bassam idan har suka iya harban ka haka, me kake tunani zasu iya yi maka next?" riko hannun sa Bassam yayi yana kallon sa yace
"Jay, why did you study law?" a hankali Jabir ke kallon sa yace
"To serve justice of course"
"So I did" cewar Bassam sannan ya kara da cewa "So my dad wants me to be" kallon sa kawai Jabir keyi ya cigaba "And so does Mammy, but ita mace ce tana da rauni she can't take to see me get hurt shiyasa take nema ta hana ni but I want to do it my way, I wanted to follow my dad's footsteps" shiru suka yi Jay yana auna maganganun Bassam a hankali Bassam ya sake riko hannun sa yace "It's not their job to stop, it's our job to stop them. If we quit they will win, and that girl's family they will never know happiness saboda za'a kashe 'yar su ne akan laifin da bata aikata ba, just think about it Jay" jinjina kai Jabir yayi alamar maganganun Bassam sun shige sa a hankali Bassam yace "It shall be worth it in the end if not, then I'm ready to die for that girl Jay" shiru ne ya biyo baya yayin da duk hirar da suke akan kunnen Samira a ranta tana cewa wannan yarinyar wacece kuma mi ta aikata ne haka gefe daya kuma haushin ta take ji duk da cewa bata san ta ba amma ta lura Bassam ya damu da ita ba kadan ba, a hankali Bassam ya kalli Jabir yace
"Make me some tea please" karaf Samira ta dauko flask da cup ta shiga hada masa tea din yayin da shi kuwa Bassam mamaki ne ya kama sa don kwa Jabir yace ya hada masa tea, bayan ta gama ne tazo da cup din kusa dashi tana kara stirring with intention tayi feeding nasa, amshe cup din Bassam yayi yace "No, thanks" a hankali ya fara sipping tea din, komawa tayi sai satar kallon sa take tana kallon irin hallittar sa packs ne da muscles ta ko ina plus ga gashi kwance luf akan kirjinsa da kafafun sa a ranta tana cewa he's really hot, shi kam Bassam bai ma san abunda take ciki ba sai shan tean sa yake a hankali yana masa tunanin.






*Shawty* ce💕
[1/8, 7:00 PM] ‪+234 813 551 5123‬: *BARR. BASSAM*
(The Gallant) ❣




By *Shawty*💕

*2017*

4⃣1⃣

_*A'ishah, Kausar, Neenah, Ayatullah and Ummi.* Thanks for all the love and support, muna nan tare in shaa Allah #OneLove_❤💛💙


_The next day_
Bassam ne zaune kan gadon asibiti da tab dinsa a hannu, gefe daya kuma Mammy ce da Jabir sai hira suke cikin nishadi da barkwanci da alama kuma Bassam yana samun sauki. Shigowar likita ne yasa suka dakatar da hirar suka gaisa ya karaso kusa da gadon da Bassam yake kai yace
"Barrister, how are you feeling?" wani kasaitaccen murmushi Bassam yayi ya d'an bud'e hannayen sa yace
"Well, like I've been shot" dariya suka yi gaba daya likitan yace
"Atleast your sense of humor is still intact" nan ma dariya suka yi sannan Bassam yace
"Doctor I hope kazo kayi discharging dina ne" kallon sa Mammy tayi da sauri tace
"Discharge? Ban gane ba what are you talking 'bout?" d'an b'ata fuska Bassam yayi yace
"Mammy I need to go home"
"A hakan? Are you nuts?" murmushi Bassam yayi yace
"I'm okay Mammy I just need to go home it's matter of security 'cause they can attack me here too plus we got a lot to do at office, once I'm here, Jay won't be able to handle all those stuffs.." likitan bai barsa ya karasa ba yace
"Sure Barrister, I know you have a job to do, but I wouldn't be doing mine if I didn't advise you against leaving the hospital so soon after surgery" murmushi Bassam yayi yace
"Doctor, I understand completely, but I really do have to get back to work, thought yesterday you were the one who said we have a busy-job right?" jinjina kai likitan yayi yace
"True, but I also cautioned against undue stress, so, I'm discovering.." Bassam bai barsa ya karasa ba yace
"Look Doctor, I promise you I will do everything I can to take it easy" jinjina kai doctorn yayi don kuwa yasan Bassam ba yaro bane ya juyo ya kalli Mammy wacce ba abunda take sai zabgawa Bassam harara, murmushi doctorn yayi yace
"I'm sorry ma'am but Bassam isn't a kid I'm sure zai kula da kanshi" bata ce masa komai ba a hankali ya juyo ya kalli Bassam yace "Don't work too hard please" gyada kai Bassam yayi yace
"Copy that"
"Also you need a stick 'cause you are shot on the left side of your chest and also the shots on your leg is on the left hand side so, don't be too hard on that side please" jinjina kai Bassam yayi yace
"Okay" takarda likitan ya fiddo ya kara rubuta masa magunguna yayi handing takardar wa Mammy yace zasu iya tafiya gida tare da fatar Allah ya kara sauki, godiya Mammy tai masa sannan yace su jira a kawo masa sandar da zai dinga dogarawa da ita a hankali ya juya ya fice daga dakin yayi daidai da shigowar Samira cikin dakin, har kasa ta duka ta gaida Mammy cike da sakin fuska Mammy ta amsa ta tambaye ta ya mai jiki ta amsa mata da sauki har ma an sallame su, kallon Bassam tayi tai masa ya jiki kallon ta yayi a shiririce haka sannwya amsa mata da sauki sannan Mammy tace
"So, Bassam you just make a decision without my consent right? Koda baiyi min ba I should just go to hell right?" dariya Bassam yayi ya fara kokarin mikewa tsaye da taimakon Jabir ya samu ya mike had'i da

Please Login or Register in order to submit comment