Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yaushe ba abunda yake sai karatu sam baya shiga harkar mutane ga zurfin cikin tsiya. Ba abunda Bassam ya nema ya rasa coz tun kafin ya nemi wani abu iyayen sa sun tanadar masa.


Lokacin jarrabawar su yana ƙara kusantowa ba abunda yake sai karatu being the brightest student don kuwa kaf a school d'in ba wanda bai sanshi ba ta gefen ƙoƙari ga d'imbin 'yammata da ke falling masa every day, poor Bassam shi duka basa gaban sa.


Bayan ya gama secondary school ne iyayen sa suka shiga nemo masa admission a Harvard University, dama ba abunda yake kwad'ayi kamar profession na iyayen sa haka kuwa akayi ya samu gurbin karatu a makarantar. Tun tafiyar sa bai sake leƙo Nigeria ba ko hutu suka samu sai dai yayi zaman sa idan iyayen sun samu vacation zasu kai masa ziyara. Haka Bassam ya jajirce yana ta karatu yanzu kam ya zama bature don hausa ma sai jefi-jefi yake yi. Yana a shekarar sa na ƙarshe a karatun sa Allah yayi wa mahaifin sa Justice Muhammad Umar rasuwa abun yayi mummunan girgiza shi that's the first time da yaje Nigeria tun bayan tafiyar sa, duka-duka two weeks kawai yayi ya koma ya cigaba da karatun sa cike da jimami da alhinin mahaifin sa.


Bayan ya kammala University ne he later moved to Scotland anan yayi obtaining M.Sc nashi, tun lokacin mahaifiyar sa taso ya dawo Nigeria ya fara practice amma fur yaƙi a cewar sa ba zai iya rayuwa a Nigeria ba, ba yadda zata yi haka ta haƙura ta zura masa ido sai dai taje ta gansa lokaci-lokaci. Lokacin ne ya zama cikakken bature hausa ma ya fara mantawa duk halayen sa na turawa ne amma ba wannan yasa ya yada addinin sa ba coz yayi joining online Islamic classes haka ma sallolin sa ba wanda yake wuce sa but guy he drink, mashayin barasa ne na gaske wacce ta zama kamar ruwa a wurin sa.


Sai dai sam ba ruwan sa da mata though tun yana Nigeria mata ke tallan masa da kansu saboda kyansa amma sam basa gaban sa sai mace d'aya wacce tun zuwan sa duniya ita kad'ai ta taɓa burge sa har wani abu ya shiga tsakanin su itama sai zuwan sa Scotland ya had'u da ita me suna Hannah.


Haka rayuwa ta cigaba da tafiya wa Bassam da mahaifiyar sa bayan rasuwar mahaifin sa ba abunda yake damun su sai rashin Justice Muhammad Umar.


Itama Barr. Hindu tun rasuwar Justice taga zaman ta a Abuja bayada amfani, dama Justice ya kaita kuma yanzu baya raye wannan dalilin ne yasa ta tattara ta koma mahaifar ta wato Sokoto a katafaren gidan su ta cigaba da practice dinta.


*Sokoto, Nigeria.*
Yau ya kama Sunday Hajiya Zainab ce take saukowa downstairs cikin shiga ta alfarma da gani shirin na fita ne, saukowa take at the same time tana ƙwalla kiran A'ishah, Kausar ce ta fito da sauri tana amsa kiran tace
"Momy tana bacci ne" tsayawa Momy tayi chak tace
"Bacci?" had'i da duba agogon hannun ta tace "Baccin safen ne almost 1:30pm?" sosa kai Kausar ta shiga yi tana neman ƙaryar da zata yi ta kare A'ishah daga fadan Momy
"A'a Momy ta tashi komawa dai tayi" taɓa baki Momy tayi tace
"Kwa ji dashi, ni zan fita sai na dawo"
"Toh Momy a dawo lafiya" cewar Kausar
"Allah yasa" ta amsa, tare suka sauko Kausar ta rako ta har zuwa farfajiyar gidan ta shiga mota yayin da me gadi ya bud'e gate taja motar ta fita. Sai da Kausar taga fitar ta gidan sa'annan ta juya ta koma ciki straight bedroom nasu ta nufa. Yadda ta bar A'ishah haka tazo ta same ta tana baccin ta, gadon ta hau ta d'auki pillow ta fara dukan ta dashi tace
"Tse-tse fly wake up! Tashi baccin ya isa haka" wani gurnani A'ishah tayi cikin muryar bacci tace
"Leave me alone! Zaki fara ba?"
"Ki tashi it's almost 2:00pm fa" cewar Kausar
"So? Meye damuwar ki?" ta fada had'i da juya mata baya. Shiru Kausar tayi tana tunanin me zata yi ta tada ta, wurin tafin ƙafar ta ta koma ta fara yi mata susa ba shiri A'ishah ta tashi sai haure-haure take yayin da Kausar sai ƙyalƙyala dariya take da gudu ta sauka kan gadon
"Kausar!" A'ishah ta kira sunan ta almost frustrated sai kuma taja tsuka tace "Ke dai banza ce, yanzu da kika tayar dani me zan miki?" d'aga kafadunta Kausar tayi in I don't care manner tace
"Nothing! I just can't watch you sleep when I gah nobady to talk to. Momy ta fita ke kuma kina bacci? Haba kema kinsan ba zata saɓu ba" ta ƙarisa maganar tana munching sweets a bakin ta
"Ina Momy taje?" A'ishah ta tambaye ta
"Uhumm.. I dunno ta dai gayamin zata je unguwa" tsuka A'ishah taja ta sake komawa ta kwanta alamar har yanzu bata daina jin haushin Kausar ba kuma har yanzu da sauran baccin a idon ta, da gudu Kausar tayi kanta bisa gadon tana fadin "Don't start it! Wallahi ba zaki yi baccin nan ba" ba arziki A'ishah ta tashi zaune suka yi ta punching juna baccin da A'ishah bata yi ba kenan.


******


Tuƙi take cikin natsuwa da kwanciyar hankali har ta iso bakin gate d'in gidan, horn ta danna wanda yasa me gadin ya fito da sauri ya bud'e gate d'in, a hankali taja motar ta kutsa cikin farfajiyar gidan ta nemi wuri tayi parking. Tamfatsetsen gida ne na ji da fad'a babban mansion wanda zai iya gogawa da nata gidan, fitowa tayi tana waige-waige yayin da me gadin ya rufe gate d'in ya nufo ta
"Sannu da zuwa Hajiya" ya fad'a yana dariya, waigowa tayi gami da yin gajeren murmushi
"Yauwa! Hindu fa tana ciki?"
"Eh eh Hajiya tana ciki"
"Ok" ta fad'a ta juya ta nufi cikin gidan yayin da shi kuma ya koma bakin aikin sa. A hankali ta shiga parlorn ba kowa sai tangamemiyar tv'n bango dake manne sai aiki take, sallama tayi har sau biyu a na ukun ne wata mace ta fito da sauri had'i da yi mata maraba
"Sannu da zuwa Hajiya"
"Yauwa, ina me gidan ne?"
"Tana ciki barin kira ta" da
"Toh" ta amsa ta juya ta zauna kan wata luntsumemiyar Sofa dake bayan ta, du ba za'ayi minti biyar ba sai gashi ta fara saukowa daga upstairs, Hajiya Zainab ce ta d'ago kai suka had'a ido, chak matar ta tsaya had'i da cire farin glasses dake kan fuskar ta had'i da d'an mutsika idanun ta cike da mamaki tace
"Ahhh! Wa zan gani haka kamar Zainab Bature?"
"Barrister ana ciki ana aikin rubuce-rubucen Chamber ne?" cewar Hajiya Zainab d'in, dariya suka kwashe dukan su, ƙarisowa tayi ta zauna kusa da Hajiya Zainab har yanzu tana mamaki
"Kinsan Allah? Na d'auka fa ba zaki zo ba kin kawai fad'a ne"
"Sai kuma gani ba" cewar Hajiya Zainab
"Wonders!" Barr. Hindu tayi exclaiming suka tuntsire da dariya lokaci d'aya tace "Bari a kawo miki ruwa ko?" cewar Hindu, murmushi Hajiya Zainab tayi tace
"Toh shikenan" Larai me aikin ta ta ƙwalla wa kira sai gashi ta shigo parlorn da sauri had'i da rusunawa
"Jeki ki had'o ruwa da drinks ki kawo" da
"Toh Hajiya" ta amsa ta miƙe da sauri ta nufi hanyar fita, Hajiya Zainab ta maida kallon ta kan Barr. Hindu tayi murmushi tace
"What a nice house Barrister!" murmushi Barr. Hindu ta mayar mata had'i da cewa
"Thank you"
"It's been a while Barrister... Yauwa ina yaron ki da kika bani labari?" cewar Hajiya Zainab, dogon numfashi Hindu taja kafin ta amsa mata tace
"Kin manta ne? Ai na gaya miki baya gari yana Scotland"
"Ohh! Na manta wallahi, so, yaya aikin?" shiru Hindu tayi ta kasa ce da ita uffan sai hawaye ya ciko idanun ta "Lafiya Hindu? Me ke faruwa ne?" cewar Hajiya Zainab, d'an hawayen da ya zubo mata ta goge tace
"Abunda ke yawan damu na ne kika tuna min Zainab" gyara zama Hajiya Zainab tayi tace
"Me yake damun ki ne haka?" ajiyar zuciya Hindu tayi tace
"Ai na gaya miki Bassam baya gari yaje Scotland ba?" gyad'a mata kai kawai Hajiya Zainab tayi alamar eh sannan Hindu tace "Toh Bassam yaje ƙasar waje ne tun lokacin da ya gama secondary school har yau maganar da ake kenan, zuwan sa d'aya Nigeria tun bayan rasuwar mahaifin sa tun lokacin bai ƙara zuwa ba. Abun yana damu na sosai, beside, 'yan uwa na da na mahaifin sa duk tsegumi na suke a cewar su na hana shi yasan dangin sa bai san kowa ba wasu ma da ya sani duk sun mutu most of all kewa ta dame ni na gaji ina zaune a wata duniyar yaro na yana a wata" girgiza kai Hajiya Zainab keyi cikin alhini tace
"Ke kuwa Hindu ya akayi kika bari haka ta faru? Icce tun yana d'anye ake lanƙwasa shi"
"Hakane Zainab"
"Gaskiya Hindu kina cikin damuwa, amma me zai hana ki saka shi a gaba akan dole sai ya dawo?"
"Anya kuwa?" cewar Hindu "Kwata-kwata fa baya san zancen dawowar"
"Manta da wannan, ai zaki nuna masa ɓacin ranki ne matuƙa na tabbata it will make an impact on him" cikin rashin ƙwarin gwiwa, Hindu tace
"Toh zan jaraba"
"Try it" cewar Hajiya Zainab "Nima kinga al'amarin Alhaji yana matuƙar bani tsoro"
"Me yake faruwa ne?"
"Yawan dukiyar sa mana, abun yana matuƙar d'aure min kai ya fara zarta hankali fa
"It's normal, d'an kasuwa ne ya dad'e yana kasuwanci yadda kika bani labari so, kinga yasan yadda zai sarrafa komai I think sai dai ki godewa Allah kan ni'imar da yay muku" dogon numfashi Hajiya Zainab taja sannan Hindu ta cigaba da cewa "Shi fa ba yaro bane Zainab bare ya dinga facaka da kud'i" shiru Hajiya Zainab tayi don ta lura sam Hindu bata fahimci me take nufi ba. Wata hirar suka sake ta yaushe gamo a haka har la'asar tayi tace zata tafi, rakota Barr. Hindu tayi har bakin mota suka yi sallama da alkawalin itama bada dad'ewa ba zata kawo mata ziyara.



*Barr. Hindu da Hajiya Zainab ƙawaye ne tun secondary school, rabuwar su ta samo asali ne tun lokacin da suka gama secondary school basu sake ji daga juna ba sai bayan dawowar Barr. Hindu Sokoto suka hadu, anan suka shaida juna har Hajiya Zainab tayi wa Hindu alƙawalin zata kawo mata ziyara wata rana.*





*Shawty*💕
[1/7, 6:40 PM] ‪+234 813 551 5123‬: *BARR. BASSAM*
(The Gallant) ❣




By *Shawty*💕


*2017*

0⃣5⃣

_The next day_
Tun da asuba A'ishah ta tashi bacci abunda yayi matuƙar bawa Kausar mamaki coz A'ishah bata taɓa tashi sallar asuba ba koda zata nufi tashin ta ba zata tashi ba daga ƙarshe ma suyi fada wanda tasan wannan tashin da wuri baya rasa nasaba da zata hau sabuwar mota ne.


Bayan sun gama sallar ne A'ishah ta koma tayi kwanciyar ta tana danne-danne a waya da haka har wani baccin ya sake awon gaba da ita. Kausar kuma sai gyara zama tayi ta cigaba da adhkar, bata tashi ba daga wurin sai da gari yayi haske tas sa'annan ta shiga bathroom tayi wanka tazo gaban dressing mirror ta fara taje gashin kanta me uban yawan gaske ta daure shi wuri daya. Mayukan ta kawai ta shafa sai powder sa'annan taje wurin wardrbobe ta fiddo ironed school uniform nata.


_7:00am_
Ba A'ishah ta tashi daga baccin ba sai ƙarfe bakwai, Kausar a lokacin har ta gama shirya kanta tana a dan madaidaicin parlorn su tana kallo. Miƙewa A'ishah tayi da hanzari ta shiga bathroom tayo wanka tazo gaban dressing mirror ta fara shafe-shafe as always, ta ɓata about 30mnts sa'annan ta shirya cikin school uniform itama hadi da dauko school bag nata ta nufi parlorn. Cikin sauri ta shigo parlorn ta fara fitinar Kausar akan ta tashi su tafi
"Wake-up Kausar! Tashi ki shirya we're getting late" dariya Kausar tayi ta kalle ta tace
"Tab! Wani abun sai sabuwar mota" harara A'ishah ta ɓalla mata hadi da dakatar da saka takalmin da take
"Kinga wallahi zan tafi idan ba zaki yi sauri ba" dariya Kausar tayi ta miƙe tsaye ta nufi bedroom tana cewa
"Wani abun sai G4 Sedan. Wait..." ta juyo tana kallon A'ishah tace "When last ma da kika tashi sallan asuba?"
"Mtsww.. For fuck's sake zaki tafi ki shirya ne ko yaya? Ke ba zaki fahimta ba walai" dariya kawai keyi har ta shige bedroom din yayin da A'ishah ta cika fam sai masifa take "Idan kin gama ni ki same ni downstairs"


Dama Kausar a shirye take duka bata yi 5mnts ba itama ta sauko downstairs, A'ishah da Momy ne kawai ta samu akan dining suna breakfast, rusunawa tayi kamar koda yaushe ta gaida Momy
"Ina kwana Momy?" da fara'a Momy ta amsa
"Lafiya ƙalau Kausar, kin tashi lafiya?"
"Lafiya ƙalau" ta fada hadi da miƙewa tsaye taja daya daga cikin kujerun ta zauna. Abinci suke ci ba mai ce da wani uffan zuwa wani lokaci A'ishah ta katse shirun
"Oya Kausar! Kiyi sauri barin je in gayawa Dauda ya fitar da motar" jinjina kai kawai Kausar tayi alamar taji yayin da Momy sai kallon ta take har ta fita parlorn. Ba'a dade ba sai gashi ta dawo hadi da daukar school bag nata
"Let's go!" tace da Kausar in hurry
"Ke dallah ki barta ta gama breakfast mana" cewar Momy, cikin shagwaɓa A'ishah tace
"Momy zamuyi latti fa"
"Sai yau kika san da lattin? Inace other days anan ake fama dake ki tashi" turo baki tayi tana gunguni yayin da Momy ta cigaba da cin abincin ta. Tsam Kausar ta tashi hadi da daukar school bag, A'ishah tana ganin haka tasa kai ta nufi hanyar fita parlorn, bin ta da ido kawai Momy tayi har ta fita girgiza kai kawai tayi wa Kausar Allah ya kiyaye sa'annan itama Kausar ta rufa mata baya. Koda ta fito farfajiyar gidan A'ishah ce sai killing selfies take a jikin motar, murmushi Kausar keyi har ta kawo daidai wurin motar tace
"Sarkin ƙorafi muje kadda ayi lattin" harara ta aikawa Kausar tace
"After kin gama shanya ni ba? Nima sai na gama abunda nike" ta fada har tana murguda baki, Kausar tasan idan ta biye ta zasu na dinga arguing kenan kuma ba za'a tafin ba, wuce ta kawai tayi ta bude ƙofar gaba ta shiga ta zauna. Itama shigowa tayi motar ta rufe hadi da kicking tuni me gadi ya wangale mata gate a hankali taja motar ta fice.


A hankali suke tafiya yau unlike jiya da suka dawo a tsiyace, waƙar Miley Cyrus_Malibu ne ke flowing a hankali, Kausar sai kallon side road take yayin da A'ishah zuciyar ta fal da farin ciki yau zata rama rashin girman da Al'ameen Dan Ƙasa yay mata. Lokacin da traffic ya tsayar dasu ne a junction ta lura da motar sa na zuwa a bayan su da sauri ta taɓo Kausar tace
"Look! There he comes" ta nuna mata a front mirror na motar, dan waigawa kadan Kausar tayi then back to A'ishah tace
"Waye?"
"Dan Ƙasa mana matsiyaci!"
"Mtsww" Kausar taja tsuka "You guys should stop this game.. Wai miye amfanin wannan competition din?"
"Ko kuma shi ya daina ba" cewar A'ishah hadi da kallon Kausar "He started it, ko kin manta ni na fara zuwa da mota a duk school din in the next week shima yazo da tasa? Na fara hawa Elantra in two weeks shima yazo da tasa, naje da Lexus shima yaje da tasa now G4 Sedan" sai kuma ta fashe da dariya hadi da kafa glasses a fuskar ta "I want to see whether his Dad can afford it" yayi daidai da chanzawar traffic light din zuwa green, fizgar motar tayi ƙarfi suka wuce saura kadan ta hada hadari yayin da mutanen wurin sai dura mata ashar suke. Kallon ta kawai Kausar tayi taja bakin ta tayi shiru har suka iso bakin gate din makarantar. Motar Al'ameen ce a gaba tasu tana a bays, koda suka shigo kallo ya koma sama tsegumi da gulma suka miƙe, tafe suke har suka isa parking lot na dalibai, shi ya fara parking then A'ishah. Fitowa tayi ta dan jingina a jikin motar tana karkada keysdin motar, Kausar ce ta fito daga motar tace
"Kizo mu wuce class"
"Kije zanzo" cewar A'ishah "I'm here sai matsiyacin nan ya fito" taɓa baki kawai Kausar tayi ta juya ta nufi class yayi daidai da isowar squad na A'ishah a wurin da kuma fitowar Al'ameen da friends nasa daga motar. Ihu friends na A'ishah suke tun daga nesa suna fasa mata kai
"Shegge Babe kina wuta!" cewar Nailah best friend nata tana ƙara duba motar yayin da Al'ameen da friends nasa suka tsaya sororo sai kallon su suke
"Nice ride Babe, motar tayi ne wallahi" cewar Kulthum, blushing kawai mutuniyar keyi daidai lokacin Al'ameen da friends nasa suka juya zasu bar wurin
"Hey!" A'ishah ta kira sa, juyowa suka yi gaba daya suna kallon ta ita da friends nata sai giggling suke, kamar kada su tsaya sai kuma suka tsayan, takowa tayi tazo har gaban sa sa'annan ta juya ta kalli motar then back to him tace "Baka gani bane?" ta fada tana masa kallon rainin hankali
"Na gani" yace da ita shima cikin rainin hankali "Nice ride" ya sake fada sa'annan ya juya zai wuce, da sauri A'ishah ta taɓo kafadar sa tsayawa yayi chak hadi da juyowa
"Ina zaka je ne? We're not get done. Just like we did with Lexus na baka 3 days kacal ina so na ganka da G4 Sedan" juyowa tayi tana kallon friends nata tace "Nailah and Co ku fara yi mana count down daga yanzu idan kuma ya kasa then he definitely fail the game" dariya suka fashe baki daya sa'annan ta juyo in a serious face tana kallon sa tace "And get ready within those days zan iya chanza wannan" tayi nuni da motar "And you have to pay for it" tayi masa winking one eye "You know it's a game" dariya suka tarwatse ita da friends nata, juyawar da zata yi sai ga wani abokin Al'ameen wato Ashraf dama neman sa take ruwa a jallo don yana cikin wanda suka yi mata dariya the other day. Kallon sa tayi tsaf sa'annan ta cire glasses na fuskar ta tace "Welcome Ashraf" ta miƙa masa hannu alamar gaisuwa, ba yadda zai yi dole ya miƙa mata hannu in return suka gaisa tace "Dama kai nake jira your friend is mistaken he's messing with the wrong bitch, tell him to get the hell outta my trouble"
"Watcha talking 'bout?" yace da ita yana wani yamutsa fuska ta lura sam be lura da motar ta ba, taɓo kafadar sa tayi hadi da cewa
"Dude kalli nan" juyowar da zai yi ne idanun sa suka sauka akan motar da sauri cikin mamaki ya kalle ta
"Whaaaaaattt? G4 Sedan?"
"Yes!" tace dashi tana ƙoƙarin mayar da glasses din a fuskar ta tace "You can't touch us you get that? We fucking bulletproof" sai da ta tabbatar kallon da take masa ya nutsar dashi sa'annan ta juya back to her friends wanda sai ihu suke suna hailing nata, cike da jin dadin ta rama abunda akayi mata suka bar wurin to their classes suka bar Al'ameen, Ashraf da sauran friends nasa speechless a wurin.


Zuciyar sa sai tafarfasa take wane zata ɓallo ƙirjin sa ta fito idanun sa suka kada suka yi jajir tsabar ɓacin rai yayin da sauran friends nasa sai jinjina girman rashin kunyar da A'ishah tayi musu suke. Gefe Ashraf yaja sa yace

"Calm down man" fizge hannun sa yayi daga riƙon da Ashraf yayi masa hadi da cewa
"How? Tell me how"
"Just breath man ba zamu barta ba ai"
"You know what Ashraf?" cewar Al'ameen yana kallon Ashraf in a serious face
"Wallahi she can't get away with this, I'm gonna beat the hell out of her" ya fada hadi da juyawa da sauri yabi bayan A'ishah da friends nata, tuni Ashraf da sauran friends nasu suka rufa masa baya. Bai same su ba sai suna daf zasu shiga class, cikin fushi ya finciko ta
"You bloody bitch! Don't get it twisted kina ganin kinzo da wancan gongonin har kina bragging, wai ma I wanna know tun lokacin da muka fara game dinnan kin taɓa beating nawa ne?" dariya A'ishah tayi tace
"I don't but baka taɓa burge ni ba coz you've never come up with your own styles sai dai ka kwaikwaye ni" sai matsowa take kusa dashi har ta kawo daf da fuskar sa tace in whisper "Son of a bitch!" tas! kake ji ya wanke ta da lafiyayyen mari wanda sai da taga stars a idanun ta, tuni wurin ya rude da shewa daga abokan Al'ameen sai zuga sa suke, matsowa yayi kusa da ita yace "I told you never get it twisted, ba mari ba zan iya shaƙe ki har ki mutu and next time you should watch your words" hawaye sai kwararowa suke daga idanun A'ishah yayin da best friend nata Nailah ke riƙe da ita, cikin fushi Nailah tace
"Don't think you can get away with this wallahi" murmushi Al'ameen yayi ya tako yazo gaban ta hadi da dago haɓar bakin ta yace
"You know what I'm capable of ke zaki bata labari last haduwar mu dake" jikin Nailah sai rawa yake don tasan Al'ameen sheggen mara mutunci ne of the highest rank zai iya yarfa ta a wurin sa'annan yayi wani gajeren murmushi suka juya da friends nasa suka wuce
"Do your fucking worst! Bastard! Bloody fool!" haka Nailah tay ta jifan sa da baƙaƙen kalmomi yayin da ko waigowa basu yi ba suka wuce. Dawowa tayi ta shiga lallashin A'ishah hadi da cewa
"It's alright kinji?" nodding kawai A'ishah tayi hadi da yin murmushi tace
"He's gonna pay for it" murmushi itama Nailah tayi don kuwa tasan ko waye friend nata and what she's capable of suka wuce class.


Labari fa ya watsu a cikin school A'ishah Bala the real Slay Queen ta faso gari with G4 Sedan 2017, ko ina a cikin school din sai labarin ake yayin da Kausar bata san me yake faruwa ba. Haka after closing hour suka yi ta slaying ita da friends nata.





*Shawty*💕
[1/7, 6:47 PM] ‪+234 813 551 5123‬: *BARR. BASSAM*
(The Gallant) ❣



By *Shawty*💕

*2017*

0⃣6⃣

_Being in friendship doesn't make me happy it's being a friend of you, years after

Please Login or Register in order to submit comment