Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Kausar har yanzu voice nata sai shaking yake, ture system dake gaban ta A'ishah tayi tana kallon Kausar cike da son jin ƙarin bayani tace
"Ban gane ba, watcha talking 'bout?"
"I really don't know A'ishah, I feel dumb" numfashi A'ishah taja tace
"Toh Allah ya kare ki, ki tashi kiyi sallah anyi ishaa tun dazun"
"Ok" tace ta tashi ta nufi bathroom tana shiga ta durƙushe a ƙasa tana kuka, sai da tayi me isarta ta tashi tayi wanka had'i da d'auro alwala ta fito ta tada sallah. Bayan ta gama ta dad'e tana addu'o'i ta shafa yanzu kam tsoron kwanciya take tayi bacci bata san me zata gani ba, novel nata na James Hardley Chase ta d'auko ta fara karantawa ko zai hana ta tunani.


_9:00pm_
Alhaji Bala ne zaune gaban swimming pool dake cikin gidan, wayar sa dake ruri ce ya jawo ya d'aga kiran had'i da sakawa a kunne yace
"Malam..." bai bari ya ƙarisa abunda zai fad'a ba yace
"Bala binciken da nayi ya nuna idan har kana so ka tsira da mutuncin ka to dole sai an kawar da wannan yarinyar" cikin d'aurewar kai Alhaji Bala yace
"Kamar ya kawar da ita?"
"Ina nufin kawar da ita daga doron k'asa" shuru Alhaji Bala yayi na mintuka sa'annan yace
"Saboda me zamu kashe ta Mallam?"
"Kasan me ganin da tayi maka da ƙwaryar jini yake nufi a tsafi?" girgiza kai Alhaji Bala yayi
"Amma me zai hana kayi wani aiki a kanta yanda koda zata yi yunk'urin gayawa wani ba zata iya ba? Kamar dai irin aikin da kayi akan Zainab" girgiza kai shima malamin ya shiga yi had'i da cewa
"Hakan ba zata yiwu ba Bala"
"Saboda me?" numfashi malamin yaja yace
"Wannan yarinyar tana da kariya sosai, kullum a cikin ibada take ba aljanin da zai iya tunkarar ta hallaka ta ne kawai mafita" nodding kai Alhaji Bala yayi yace
"Tam shikenan, ya za'a kashe tan kuma yaushe?"
"Ban gama shirya wannan ba idan na gama zan neme ka"
"Ba damuwa Mallam nagode Allah yaja kwana"
"Ameen" malamin ya amsa ya katse kiran. Jujjuya wayar Alhaji Bala ya shiga yi sam bai ji dad'in kashe Kausar da za'ayi ba yarinyar tana da hankali da natsuwa, ya dad'e zaune a wurinf sa'annan ya mik'e ya koma ciki.





*Shawty*💕
[1/8, 8:09 AM] ‪+234 813 551 5123‬: *BARR. BASSAM*
(The Gallant) ❣



By *Shawty*💕

*PURE MOMENT OF LIFE WRITERS*
(We don't just entertain and educate, we also touch the hearts of the readers.)


*Zaku iya samun kowane Novel na PML through these links*
#WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
#IG PML WRITERS
#https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
#http://maryamsbello.blogspot.com


*2017*

1⃣7⃣

_Happy Birthday and Rest in Peace my dearest sis. 😭You would have been 28 today but it hurt that you are gone, gone and forever. I hope you are in peace, none of us had peace in your final few hours but I hope you have it now. I pray that when next we'll see again is at the gate of Jannatul-Firdaus😭we all miss you Sis. *HBD&RIP*_

___________________________________


_Monday_

Yau ya kama Monday, Bassam ne da Mammy suka fito cikin shiga na suit dukan su da alama dai fita zasu yi. Mammy ce ke jan motar yayin da Bassam ke zaune gefen ta sai hira suke cikin jin dad'i da raha. Haka ta kaisa Chambers da ta bud'e masa da zai fara aiki with all stuffs na aikin tare da wani young barrister mai suna Jabir wanda zai rik'a taimaka masa, though ba dole ne yaga abubuwa kamar Scotland ba amma duk da haka abun ya burge shi ba laifi. Haka ta d'auke sa zuwa nata Chambers d'in nan ma sun dad'e har ya jira ta tayi attending wasu mutane, bayan sun bar nan ta d'auke sa zuwa wurare daban-daban kusan dai yinin ranar basu zauna ba sai da marece suka koma gida.

_4:30pm_
Hajiya Zainab da A'ishah ne a cikin parlorn suna kallo, shigowar Alhaji Bala ne ya dakatar da kallon nasu had'i da yi masa sannu da zuwa. Haka suka zauna suka cigaba da kallon sai da aka d'auki kusan mintuna ashirin sa'annan yayi gyaran murya yace

"Ina Kausar ne?"
"Tana sama tana bacci" cewar A'ishah
"Ok" ya fad'a sa'annan yayi jim na wasu lokuta yace "A'ishah zaki je gidan Hadiza kiyi sati d'aya a chan d'azu munyi waya take min complain ba kya zuwar mata" tuni fuskar A'ishah ta chanza yayin da Hajiya Zainab ta zuba mata ido tana kallon ta don kwa tasan Goggo Hadiza da A'ishah basa shiri ko kad'an, turo baki A'ishah tayi ta fara gunguni tana halba k'afafu "Ke!" Alhaji Bala ya daka mata tsawa wacce ba ita kad'ai ba harta Hajiya Zainab sai da abun ya bata tsoro da mamaki cikin ranta tace yau kuma kai da mutuniyar taka, tuni A'ishah ta dakatar da gungunin tana kallon sa with her eyes wide in surprise don kwa Daddy bai tab'a yi mata tsawa irin haka ba, cikin kakkausar murya yace da ita "Kina ji na ai ba?" nodding tai masa kanta a k'asa yace "Good, ki tashi ki shirya"
"Daddy yanzu?" ta sake fad'a cikin mamaki
"K'warai kuwa yanzu"
"Toh Daddy amma da Kausar zamu je ko?" cikin kakkausar murya yace
"Ke kad'ai zaki tafi"
"Daddy amma.."
"Ke!" ya daka mata tsawa har sai da ta zabura ya duk'a daidai fuskar ta yace "Mama na just do as I said" jinjina masa kai kawai tayi yace "Good girl" ya mik'e ya bar wurin, juyowa A'ishah tayi tana kallon Momy wacce kamar ruwa ya ci ta sai kallon su take tace
"Momy kiyi wani abu bana san zuwa gidan Goggo Hadiza you know everything" ajiyar zuciya Momy tayi tace
"Na isa ne na chanza masa ra'ayi? Kawai kije koda 3days kika yi sai ki dawo" tashi tayi ta haura sama da gudu had'i da buga k'ofar d'akin su wane zata b'alla ta fuskar nan ba fara'a, Kausar ta samu mik'e kan gado da Novel a hannun ta tana karatu. Ajjiye Novel d'in tayi tana nazarin fuskar A'ishah tace
"Madam ya akayi ne?" kamar jira take ta fara fad'a tana irgo mata
"Kiji Daddy wai zanje gidan Goggo Hadiza nayi sati d'aya" jim Kausar tayi sa'annan tace
"Toh miye? Kin dad'e baki je ba ai"
"Haba Kausar! Kinfi kowa sanin halin wannan matar fad'an tsiya ne da ita gashi ta cika interfering cikin al'amarin mutum ni kawai Daddy ya fucka ni walai" murmushi Kausar tayi tace
"Kiyi hak'uri ba tare zamu je ba?" don kwa tasan duk irin haka ta taso tare suke zuwa
"That's the worst part ai, yace ni kad'ai zanje ta saka ni a gaba tana kallo wane mayya"
"Haba A'ishah! She's your mother!"

"My mother? She ain't my mother wallahi" yayi daidai da shigowar kira a wayar A'ishah da sauri taje ta d'auki wayar ganin wanda yake kiran ne yasa ta fara blushing ta d'aga kiran had'i da cewa "Hey babe haffa?" haka suka yi ta magana sauri-sauri ta ajjiye wayar, kallon ta Kausar tayi tace
"What?"
"Gobe ne birthday na Feenah"
"Oh!" Kausar tace kawai
"Zaki je?" A'ishah ta tambaye ta
"I don't think" cewar Kausar, tab'a baki A'ishah tayi tace
"A haka zaki k'are" murmushi Kausar tayi tace
"Zaki je ne?"
"Hell yeah mune a gaba ai but I dunno koda wannan witch d'in zata barni"
"Oh A'ishah Allah ya shirye ki Goggo Hadizan ne witch?"
"Witch mana" girgiza kai kawai Kausar tayi ta cigaba da karatun ta "Bari inzo in tafi kadda Daddy ya sake fitowa ya hau ni da masifa"
"Au, yanzu zaki tafi?"
"Yeah yanzu yace" daga nan Kausar bata k'ara magana ba A'ishah ta hau had'a kayan ta cikin k'aramin akwati. Bayan ta gama Kausar tace
"Har kin shirya?"
"Yeah"
"Tam sai mun kama a school kenan kinsan gobe akwai tutorial"
"Yeah zanje"
"Tam Allah ya kiyaye"
"Ameen" ta d'auki akwatin ta ta nufi hanyar fita har ta kai bakin k'ofa ta juyo ta kalli Kausar wacce ta mayar da kanta a karatun da take tace "I can't believe I'm gonna say this..." bata k'arasa ba tayi shiru, ajiye littafin Kausar tayi had'i da yin murmushi tace
"What?"
"I'll miss you" ta fad'a tana murmushi, murmushi Kausar itama tayi har hak'oran ta suka fito tace
"I'll miss you more, yau idan nayi ihu cikin dare I gah nobody to calm me down" dariya sosai A'ishah tayi tace
"Better kadda kiyi" dariya Kausar tayi tace
"I won't sweetheart" dariya suka yi gaba d'aya A'ishah taja akwatin ta ta fita. K'asa ta fara sauka bata samu Momy ba ta k'ara komawa saman ta wuce apartment nata ta tura k'ofar ta same ta tana shirya kaya a wardrobe
"Momy zan tafi" tace da ita, juyowa Momy tayi tace
"Tam ki gaida ta saura kuma naji kinyi wani rashin girma" murmushi A'ishah tayi tace
"I won't" murmushi itama tayi tace
"Good ki gaida ta"
"Zata ji" cewar A'ishah had'i da jawo k'ofar ta juya ta sauka k'asa.





*Shawty*💕
[1/8, 8:17 AM] ‪+234 813 551 5123‬: *BARR. BASSAM*
(The Gallant) ❣



By *Shawty*💕

Zaku iya samun kowane Novel na PML through these links
#WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
#IG PML WRITERS
#https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
#http://maryamsbello.blogspot.com


*2017*

1⃣8⃣

_12:00pm_
Kwance yake mik'e a gado ya tsunduma duniyar tunani, daga shigar sa tsafi zuwa yau ya kashe kusan mutane ak'alla goma amma ba wanda kisan sa ya tab'a tsayawa a zuciyar sa kamar na Kausar. Ya rasa gane tausayin yarinyar ne yake ko kuwa tsoro ne yake ji, mik'ewa yayi a hankali ya fita daga d'akin, kai tsaye d'akin su A'ishah ya nufa had'i da tura k'ofar tare da yin sallama, ba kowa a d'an k'aramin parlorn sai Kausar zaune akan 3 seater ta baje litattafan ta tana karatu, d'ago kai tayi had'i da amsa sallamar ganin Alhaji Bala ne yasa ta mik'e zumbur jikin ta ya fara kakkarwa ta fara ja da baya, kallon juna suke kowanen su da kalar tunanin da yake da ka kalli fuskar Kausar zaka tabbatar tana cikin mummunan tashin hankali. Cikin sanyin murya yace
"Karatu kawai ake?"
"Eh" ta fad'a had'i da sulalewa akan gwiwoyin ta hawaye suka zubo mata
"Ki bar karatun haka dare yayi kije ki kwanta" da
"Toh" ta amsa yace
"Sai da safe" bata ce dashi uffan ba har ya fice daga parlorn, wani kuka ta rushe dashi kewar A'ishah ta ziyarce ta don ta tabbata da tana nan da itace mai kwantar mata da hankali. Karatun da bata cigaba ba kenan kamar yadda ya umurce ta ta tashi ta nufi bedroom, kwantawa tayi had'i da tura kanta cikin pillow, addu'o'i duk wanda yazo bakin ta take da haka har bacci ya sace ta bata sani ba.



_The next day_
Da misalin k'arfe biyu na rana Kausar ce kwance akan sofa cikin main parlor ta rasa abunda ke mata dad'i sai juyi take, na farko ga kewar A'ishah na biyu kuma bugun zuciyar ta na yau yafi na kullum tana ji a ranta wani abu mummuna zai faru tana cikin wannan yanayin ne Hajiya Zainab ta shigo parlorn wacce bata san ma ta shigo ba har tazo daidai wurin sofar bata sani ba, dukan sofar Hajiya Zainab tayi da k'arfi had'i da kiran sunan ta, a firgice ta tashi zaune ganin Hajiya Zainab a kanta ne yasa ta k'ak'iro murmushi
"Kausar lafiyar ki kuwa?" Hajiya Zainab ta tambaye ta cike da kulawa
"Lafiya ƙalau"
"Anya kuwa? Na shigo ina ta magana amma sam baki ji ba" murmushi kawai tayi bata ce komai ba sai kuma hawaye suka fara zarya a kumatun ta "Haba ni nasan akwai abunda yake damun ki" cewar Hajiya Zainab, nan ma shuru bata ce mata uffan ba "Mey ke damunki Kausar?" kuka ta fashe dashi gwanin tausayi ta fad'a jikin Hajiya Zainab cikin rawar murya tace
"Ina ji a jiki na wani abu mara kyau zai faru" shafa bayan ta Hajiya Zainab ta shiga yi ta fara kwantar mata da hankali
"Tunani ne kawai Kausar ba abunda zai faru in shaa Allah kinji?" har yanzu kukan take bata daina ba tace
"Momy Amma"
"Amma kuma?" gyad'a kai tayi alamar eh "Me ya sami Amman? Ko bata lafiya ne?" girgiza kai tayi alamar a'a tace
"Bakomai ina so inje in ganta kawai"
"Ok yanzu?" nan ma gyad'a kai kawai tayi alamar eh "Ok zaki iya driving ne ko kwa driver yazo ya kaiki?" cewar Hajiya Zainab, girgiza kai tayi tace
"A'a zan iya"
"Toh shikenan ki gaida ta"
"Zata ji" ta amsa had'i da mik'ewa tsaye ta nufi upstairs, hijab bak'i tasa har k'asa had'i da d'auko wayar ta tayi kyau sosai cikin hijab din though da ka kalli idanun ta zaka tabbatar tayi kuka, saukowa tayi k'asa ta sami Momy tai mata Allah ya kiyaye sa'annan ta fita.


Tuk'i take tana Allah-Allah taga ta isa, tana isa tayi parking da sauri ta bud'e motar ta fito ta isa bakin k'ofar gidan had'i da tura k'yauren k'ofar gidan ta shiga, hango Amma tayi a tsakiyar gidan a bakin murhu tana hura wuta, ajiyar zuciya tayi me nauyi a sanyaye ta k'arisa cikin gidan. Ita kam Amma sai aikin ta take batasan shigowar ta ba, hugging Amman tayi ta baya da sauri ta juyo don ganin ko waye ganin Kausar ne yasa ta saki murmushi ta ajiye aikin da take gami da juyowa suna fuskantar juna tace
"Kausar yanzu ake tafe?"
"Wallahi kuwa ina ta tunanin ki ne"
"Ayyah" ta fad'a tana shafa kanta tace "Ya na ganki ke d'aya? Ina A'ishah?"
"Taje gidan Goggo Hadiza"
"Ayyah! Ya kuma naga idanun ki kamar kinyi kuka?" ta fad'a tana nazarin fuskar ta, murmushi tayi tace
"Bakomai" tana wasa da wayar ta "Aiki ne kike haka Amma?" cewar Kausar tana nema a daina wanchan maganar
"Kin ganni zan d'aura girki ne"
"Bara na taya ki" cewar Kausar, da
"Toh" Amma ta amsa, ta cire hijab suka fara aikin cike da jin dadi da barkwanci. Hira suke abunsu gwanin sha'awa kamar ba ita bace ke kuka d'azu ba, bayan sun gama girkin ne suka ci suka zauna suna hira ne Kausar take irga mata yanayin da take ciki, kwantar mata da hankali Amma ta shiga yi da k'ara jaddada mata ta tsare addu'o'i da haka sukai ta hira har Abbah ya dawo shima ya jona hirar. Sai daf da maghrib tace zata tafi Amma ta rako ta har k'ofar gida tana k'ara gargadin ta akan ta yawaita addu'a, amsawa tayi da toh suka yi sallama da cewar ta gaishe da Hajiya Zainab da haka suka rabu.





*It'z Shawty*💕
[1/8, 8:25 AM] ‪+234 813 551 5123‬: *BARR. BASSAM*
(The Gallant) ❣




By *Shawty*💕


Zaku iya samun kowane Novel na PML through these links
#WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
#IG PML WRITERS
#https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
#http://maryamsbello.blogspot.com


*2017*

1⃣9⃣


_9:00pm_
Kausar ce zaune akan 3seater a parlorn su ta baje litattafan karatun ta as always, unlike other days yau kam bacci ne sosai a idanun ta amma ta nace da karatun. Gyangyad'i ta fara a zaune wanda ya sanya ta dole ta bar karatun, bata damu da tattara litattafan ba haka ta barsu a hargitse ta tashi ta nufi bedroom. Shigar ta bedroom d'in ne aka d'auke wuta d'if duhu ya mamaye ko ina wani tsoro ne ya fara ziyartar ta da sauri ta nufi wurin curtain d'in d'akin ta d'aga don ganin me yake faruwa wutar gidan ta d'auke wanda zai iya baka damar ganin ko mey yake faruwa a farfajiyar gidan wanda kuma yayi daidai da dannowar hasken motar Alhaji Bala cikin gidan, dummm! gaban ta yayi mummunan fad'uwa da sauri ta saki curtain d'in haka ta fara lalube har ta samu ta isa bakin k'ofar d'akin ta murza key ta dawo da gudu ta haye kan gadon ta duk'unk'une a cikin blanket jikin ta ya fara rawa daidai lokacin ne wutar gidan ta dawo tare da shigowar kiran A'ishah a wayar ta....



Gefen Alhaji Bala kuwa bayan yayi parking straight ya nufi cikin gidan da sauri bai ko tsaya amsa gaisuwar ma'aikatan gidan ba, shigar sa parlorn bai sami kowa ba straight bedroom d'insa ya wuce had'i da murza key yayi kwanciyar sa.


Gefen Hajiya Zainab kuwa jin shiru-shiru Alhaji bai dawo ba yasa tayi kwanciyar ta itama, dama ba sabon abu bane a wurin ta wasu lokutan ma baya kwana a gida sai da safe yake dawowa idan ta tambaye sa sai yace yana d'aya daga cikin companyn sa ne dare yayi kawai yayi decidinh ya kwana a chan. Wani lokacin yana a gidan amma sai ta neme sa ta rasa kamar wani aljani, bata nufi kiran sa a waya ba kawai tayi kwanciyar ta bata wani damu ba.



_3:00am_
Alhaji Bala ne ya sharo da gudu daga apartment d'insa zuwa na Hajiya Zainab cikin tsintsar tashin hankali da firgici ya fara bubbuga k'ofar yana kiran sunan ta
"Zainab! Zainab!! Ki bud'e" cikin bacci Hajiya Zainab taji kamar ana kiran sunan ta, a hankali ta fara bud'e ido, k'arar bugun k'ofar da jijjiga ta bai daina ba wane za'a b'alla ta sai kuma taji muryar Alhaji Bala "Zainab ki bud'e k'ofar" tashi zaune tayi da sauri had'i da cewa
"Waye?" ta tambaya don k'ara tabbatarwa
"Nine Zainab ki bud'e"
"Alhaji lafiya kuwa?"
"Ba lafiya Zainab ki bud'e" mik'ewa tayi zumbur ta nufi k'ofar da gudu har tana tuntub'e, tana bud'ewa taga Alhaji Bala tsaye cikin tashin hankali ya fara magana "Ina fatar dai basu tab'a ki ba"
"Su waye Alhaji?"
"B'arayi!" dafe k'irji Hajiya Zainab tayi idanun ta suka firfito
"B'arayi?" jikin sa har rawa yake da gudu ya sauka downstairs bai tsaya ta kanta ba, da gudu itama Hajiya Zainab ta rufa masa baya da k'yar ta samu ta sha gaban sa cikin rawar murya tace "Ina kuma zaka je da wannan uban daren Alhaji?"
"Zan bisu na karb'o kud'i na ne" yanzu kam Hajiya Zainab ta tabbata ba a cikin hayyacin sa yake ba, hannun ta tasa da sauri ta rufe masa baki tace
"Alhaji idan basu fita ba suka jiyo ka fa? Ba inda zaka je ka barsu da kud'in mu godewa Allah ma ba wanda suka tab'a" shiru yayi sai kuma ya juya da sauri ya nufi upstairs, nan ma da sauri ta sake shan gaban sa tace "Ina kuma zaka je?"
"A'ishah da Kausar! Zan je in ga lafiyar su suma" murmushi Hajiya Zainab tayi taja hannun sa suka zauna akan kujera
"Ka manta ne A'ishah a gidan Hadiza ta kwana? Ai Kausar ce kawai, itama na tabbata ba abunda sukai mata"
"A'a Zainab muje dai muga lafiyar ta"
"A'a kaga tana bacci yanzu kar mu tada hankalin ta a banza mu bari har gari yayi haske" shuru yayi bai k'ara magana ba chan kuma yaja dogon numfashi yace
"Amma me gadi yana aikin me har ya bari suka shigo?" Hajiya Zainab wacce ta rafka uban tagumi ta d'ago kai had'i da cewa
"Gaskiya kam" mik'ewa yayi zumbur kamar wanda aka tsikara gami da cewa
"Kada fa yayi yunk'urin hana su shigowa ne suka aikata masa wani abun" jin haka yasa Hajiya Zainab ta mik'e zumbur itama "Kar fa wani abu ya samu bawan Allah ta dalili na Zainab" da sauri ya nufi k'ofar fita waje, binshi Hajiya Zainab tayi a baya har suka fito farfajiyar gidan, ko ina haske ne k'al kamar rana tafiya suke suna waige-waige da ka gansu kasan a tsorace suke har suka iso bakin k'ofar d'akin me gadin, Alhaji Bala ne ya tura k'ofar had'i da kunna kai ciki, kwance yake yana bacci abun shi cikin fushi Alhaji Bala ya kalli Hajiya Zainab yace
"Ba mamaki kin ga bacci ma yake" shuru Hajiya Zainab tayi, juyawa Alhaji Bala yayi ya k'arasa cikin d'akin ya fara tashin sa, a firgice ya tashi ganin Alhaji Bala tsaye a kansa jikin sa ne ya basa cewar ba lafiya yace
"Lafiya Alhaji?" wani mugun kallo Alhaji Bala ya bisa dashi had'i da cewa
"Shashasha! Dama aikin da kake kenan?"
"Wallahi Alhaji ban dad'e da kwanciya ba" har yanzu Alhaji Bala bai daina jifar sa da mugun kallo ba cikin fad'a yace
"Ban ga amfanin d'aukar ka a matsayin me gadi ba tunda har zaka kwanta kayi bacci san ranka, to b'arayi sun shigo sunyi awon gaba da kud'ad'e na masu yawa" hannu me gadin yasa akai cikin tashin hankali yana maimaita kalmar shahada "Bari in shaida maka kana gab da barin aikin nan shashasha kawai!" kuka me gadin ya fara yana magiya had'i da bawa Alhaji hak'uri ko kallon sa bai yi ba ya juyo yasa Hajiya Zainab a gaba suka koma ciki, akan hanyar ne take basa hak'uri akan me gadi
"Alhaji kayi hak'uri wannan abun k'adara ne koda idon sa biyu tunda Allah ya k'adara sai b'arayin nan sun shigo to fa ba makawa, mu godewa Allah shima basu tab'a sa ba"
"Ai tunda ba kud'in ki aka d'auka ba kowane wa'azi zaki yi, jira ma bacci na kawo sa yayi ko aiki?"
"K'adara ne Alhaji kayi hak'uri" da haka har suka iso parlorn tana basa hak'uri, zaunawa suka yi kan 3seater kowannen su da kalar tunanin da yake.



_6:00am_
Har k'arfe biyar na safe suna zaune a parlorn basu rintsa ba kowannen su sai tunani yake ba mai ce da wani uffan, cike da sanyin jiki Hajiya Zainab tace

"Alhaji ya kamata muje muga Kausar" gaban sa ne ya fad'i jin ta ambaci Kausar, cikin sanyin murya yace
"Muje" tafe suke Hajiya Zainab a gaba yana biye da ita har suka kawo k'ofar parlorn.



Kausar ce a kwance kan gado, ta farka daga baccin amma idanun ta sai lumshewa suke alamar bata gaji da baccin ba. Tashi zaune tayi ba don tana so ba ta zuro k'afafun ta daga kan gadon zuwa k'asa, ganin wayar ta ajiye akan bedside drawer ya tuna mata da wani abu, zumbur ta ida mik'ewa tsaye ta nufi k'ofar parlorn su straight. Koda ta fito ba haske sosai a parlorn wurin switch ta nufa ta kunna haske ya gauraye parlorn, tana juyowa idanun ta suka sauka kan mummunan tashin hankalin da bata tab'a gani ba a rayuwar ta. A'ishah ce kwance akan sofa cikin jini ga wuk'a a cikin ta, jini ne duk ya fallatsa a wurin. Mutuwar tsaye Kausar tayi a wurin baki hangame, kasa motsa koda yatsan hannun ta tayi cikin mummunan tashin hankali har yanzu idanun ta na akan abunda bata da

Please Login or Register in order to submit comment