Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

motsa baki ya d'auko ya nufo sa dashi, da sauri d'an sandan ya tare sa yana cewa
"Haba Alhaji! Da kanka? Ae da ka barshi naje na d'auko da kaina" ya mik'a hannu da zummar karb'e trayn daga hannun Alhaji Bala, hana masa trayn Alhaji Bala yayi yace
"Ka barshi kawai Officer aiki na ne akace bak'on ka annabin ka" murmushi d'an sandan yayi ya koma ya zauna yayin da Alhaji Bala ya dire trayn a gaban sa shima ya koma ya zauna, nuni Alhaji Bala yai masa da trayn had'i da cewa
"Bismillah mana Officer" ba musu d'an sandan ya d'auki apple d'aya daga cikin d'imbin kayan marmarin da Alhaji Bala ya jibgo masa a tray ya kai bakin sa ya gutsira ya fara taunawa d'ago kan da zai yi ne yaga Alhaji Bala yana zubda hawaye ajiye apple d'in d'an sandan yayi yana kallon Alhaji Bala wanda sai matsar k'walla yake yace
"Lafiya Alhaji? Me yake faruwa ne?" cikin rawar murya Alhaji Bala yace
"Ina tuna 'ya ta ne Officer" jikin d'an sandan a sanyaye yace
"She's in a better place in shaa Allah, Allah yaji k'an A'ishah Alhaji" share hawaye Alhaji Bala yayi yana kallon tile d'in d'akin yace
"A'ishah itace kad'ai arzikin da Allah ya azurta ni dashi kuma an raba ni da ita ina ji..." sai kuma kuka yaci k'arfinsa, lallashin sa d'an sandan ya shiga yi sa'annan ya samu ya dakatar da kukan yace "Kasan me?" girgiza kai d'an sandan yayi alamar a'a yana sauraren abunda Alhaji Bala zai ce, murmushin yak'e Alhaji Bala yayi yace "Duk dare haka muke zaunawa ni da mahaifiyar ta mu saka hotunan ta a gaba muna kuka" tausayin su sosai ya kama d'an sandan sai girgiza kai yake cike da alhini, cikin rawar murya Alhaji Bala yace "Da taimakon Allah da na malamai aka samu kan mahaifiyar ta saura k'iris mutuwar A'ishah ta zautar da ita" tausayin su ne ya k'ara kama sa jikin sa yayi sanyi k'alau, murya k'asa-k'asa Alhaji Bala yace "Officer taimako zakai mana ko kuma nace alfarma nasan kana akan aikin ka ne kuma kana iyakacin bakin k'ok'arin ka amma ina so kai min wata alfarma d'aya" jinjina kai d'an sandan yayi yace
"Ina jin ka Alhaji"
"Ba wanda yake bani tausayi kamar mahaifiyar A'ishah wato matata kullum sai kuka take tana cewa ba zata tab'a samun sukuni ba idan har bata san ko waye ya kashe A'ishah ba" jinjina kai d'an sandan ya cigaba da yi alamar yana sauraren Alhaji Bala sa'annan Alhaji Bala ya cigaba "Ka dubi girman Allah Officer ku tsananta akan tambayar yarinyar nan koda zata sanar daku wanda yake da hannu a kisan A'ishah, kada kisan A'ishah ya jawo asarar wasu rayukan. Ina tabbatar maka Officer idan har binciken nan ya d'auki lokaci komai zai iya faruwa da mahaifiyar A'ishah ni kuma ba zan iya hak'urin rasa su su biyu ba dan Allah Officer ka taima..." sai kuma wani kukan yaci k'arfin sa, cike da sanyin jiki Officer yace
"Wane irin taimako kake so Alhaji?" da sauri Alhaji Bala yace
"Ina so kawai ku tsananta akan tambayar yarinyar me ta sani game da kisan A'ishah watak'il ya kawo k'arshen bak'in cikin da k'unar zuciyar da matata ke ciki" murmushi d'an sandan yayi yace
"Wannan ai mai sauk'i ne Alhaji"
"A'a Officer ina so ku k'ara akan yadda kuke yi ba wai ina muku katsalandan bane a cikin aiki"
"In dan wannan ne ka kwantar da hankalin ka Alhaji"
"Nagode sosai Officer, Allah ya bar zumunci"
"Ameen" cewar d'an sandan sa'annan Alhaji Bala ya kalli trayn fruits d'in wanda d'an sandan baici komai ba, cikin mamaki Alhaji Bala yace
"Ya haka Officer? Baka ci komai ba" murmushi d'an sandan yayi baice komi ba ya d'auki apple da ya fara ci d'azu ya gutsira ya fara taunawa, mik'ewa Alhaji Bala yayi had'i da cewa "Ina zuwa Officer" ya nufi wata k'ofa, kalle-kalle d'an sandan yake yi a ransa yana cewa wannan fa itace Aljannar duniya ba'a yi minti uku ba Alhaji Bala ya dawo d'auke da wata jaka madaidaiciya a hannun sa yazo gaban d'an sandan ya dire ta sa'annan ya ja da baya ya zauna. Kallon jakar d'an sandan yayi yace
"Wannan jakar kuma fa Alhaji?"
"Bud'e ka gani" cewar Alhaji Bala, bud'e jakar d'an sandan yayi ba komai a ciki sai d'aurin kud'i dubu-dubu cike fal a cikin jakar, kallon Alhaji Bala yayi da sauri zuciyar sa sai bugawa take yace

"Wannan kud'in fa Alhaji?"
"Naka ne" Alhaji Bala ya fad'a a tak'aice
"Ban gane nawa ba Alhaji kayi min bayani" murmushi Alhaji Bala yayi yace

"Million d'aya ne anan. Kyauta ce Officer, ba cin hanci bane ba kuma na raina albashin ka bane har ga Allah wannan alhairi ne kawai nai maka" idanun d'an sandan suka firfito sai duba kud'in yake muryar sa har rawa take yace
"Alhaji wannan kud'in ai sunyi yawa" murmushi Alhaji Bala ya k'ara yi yace
"Ko kad'an basu yi yawa ba Officer, nidai kawai kayi min alk'awalin zaka taimake ni" da sauri d'an sandan yace
"Ina maka albishir Alhaji b'acin ran da kuke ciki yazo k'arshe don kuwa Kausar sai ta amsa laifin ta ko bata so" murmushin gefen baki Alhaji Bala yayi had'i da mik'ewa tsaye ya mik'awa d'an sandan hannu gami da cewa
"Nagode k'warai Officer Allah ya bar zumunci" da sauri d'an sandan ya mik'e tsaye shima suka gaisa sa'annan yace
"Ni ne da godiya Alhaji" ya juya ya d'auko jakar sa suka fito. Me gadi Alhaji Bala ya kira yace aje a d'auko kayakin da Officer zai kaiwa yara gida, da sauri me gadin ya juya ba'a yi minti biyar ba sai gashi da wasu yara d'auke da kwalaye nik'i-nik'i haka suka zo sukai ta jera kayan a cikin boot d'in motar d'an sandan yayin da shi kam mamaki ne tsintsa ya rufe shi a wurin. Sai da suka gama jera su a boot d'in suka tafi sa'annan Alhaji Bala ya kalli d'an sandan yace

"Wannan kuma a kaiwa yara"
"Alhaji d'awainiyar batai yawa ba?" murmushi kawai Alhaji Bala yayi sa'annan yace "Officer ya fa kamata a chanza motar nan" murmushi d'an sandan yayi yace
"Ai in shaa Allah Alhaji zan chanza"
"Ah Officer ba ina cewa ka chanza mota a cikin kud'in da na baka ba, karka damu gobe da yardar Allah za'a zo gida a kawo maka sabuwar mota" daskarewa d'an sandan yayi a wurin ya rasa da wanne baki zaiyi wa Alhaji Bala godiya yayin da Alhaji Bala kam sai fad'ad'a murmushin sa yake, kallon Alhaji Bala d'an sandan yayi yace
"I'm giving you my words sai Kausar ta karb'a laifin ta" jinjina kai Alhaji Bala yayi ya basa hannu suka k'ara gaisawa suka yi sallama sa'annan d'an sandan ya shiga motar sa yaja ya bar gidan. Sai da ya fita gidan Alhaji Bala ya fiddo wayar sa ya kira Alhaji Kabeer sai da wayar ta kusa katsewa sa'annan ya d'aga, b'arkewa da wata dariyar mugunta Alhaji Bala yayi yace

"Na kira sa yazo har ya tafi na gama da matsalar sa" dariya shima Alhaji Kabeer yayi yace
"Na gaya maka mayen kud'i ne zuwa zaiyi, well ya kuka yi dashi?"
"Na basa kud'i sa'annan na koro masa da cewar ina so su tsananta tambayar yarinyar game da mutuwar A'ishah, kasan me nake nufi da haka?"
"A'a" cewar Alhaji Kabeer, murmushin mugunta Alhaji Bala yayi yace
"So nike su kashe ta! Daga nan sai na zare hannu na nace na hak'ura na janye case d'in daga nan kuma na koma kan Kabara"
"Tunanin ka yayi daidai Bala, amma me yasa ba zaka k'yale Kabara ba? I think the equation is balanced ka kashe masa 'ya shima ya kashe taka me kuma yayi saura?" wata 'yar dariya Alhaji Bala yayi yace
"Kabeer kenan! Da alama baka san ko waye Kabara ba ina tabbatar maka idan har ban hallaka shi ba to kuwa shi zai hallaka ni" shuru Alhaji Kabeer yayi sa'annan Alhaji Bala ya cigaba "Ina baka tabbaci Kabeer yadda ya kashe A'ishah haka itama zata kashe shi"
"Wai kuwa kana cikin hankalin ka Bala? Kana da wata A'ishah ne bayan marigayiya A'ishah?" dariya Alhaji Bala ya tarwatse da yace
"Ni kuwa nike cikin hankali na Kabeer, ka zuba ido ka sha mamaki" daidai lokacin ya katse wayar ya k'ura mata ido ya fara tafiya sai murmushi yake ya nufi cikin gidan.







*Shawty*💕
[1/8, 2:27 PM] ‪+234 813 551 5123‬: *BARR. BASSAM*
(The Gallant) ❣




By *Shawty* 💕

*2017*

2⃣9⃣


*"Let whoever think whatever just keep getting better please."*


_This page goes to that special soul that taught me those words 👆🏻 *ILYSM*_💞

____________________________________________


Bayan d'an sandan ya bar gidan Alhaji Bala nasa gidan ya nufa kai tsaye ya ajiye kayan sa'annan ya koma Police Station d'in. Koda yayi parking yaji kamar koke-koke yana fitowa daga cikin Police Station d'in, rufe motar yayi ya nufi ciki koda ya shiga ciki Amma ce zaune daga gefe ta makure tana ta faman kuka yayi daidai da shigowar wani d'an sanda tare da Kausar

"Me yake faruwa ne?" ya tambayi 'yan sandan, wanda ya fito da Kausar ne ya nuna Amma yace
"Sir wannan matar ce tazo tana kuka tace tana so taga 'yar ta shine..." bai barsa ya k'arisa abunda zai fad'a ba ya daka masa tsawa yace
"Shut up! Maza ka koma da ita" kuka Kausar ta fashe dashi ta fara halbe-halbe tana kiran Amma yayin da itama Amma sai kukan take ta mik'e tsaye ta fara magiya, d'an sandan wanda ya shigo tare da Kausar tausayin su ya kama sa sosai ya kasa matsawa ko ina, tsawa babban d'an sandan ya k'ara daka masa yace
"Zaka koma da ita ne ko kuwa?" baya da zab'i haka ya saka Kausar a gaba ya mayar da ita cell d'in, kuka Kausar keyi da gaske tana jijjiga k'ofar cell d'in tana cewa

"Amma kada ki tafi ki barni zasu kashe ni" kuka Amma ta fashe dashi ta sulale k'asa ta rik'e k'afar d'an sandan ta fara yi masa magiya, halbe ta yayi da k'afar ta fad'i ya nuna ta da yatsa yace
"Ki tashi ki fita! Ai kin rigaya kin haifa wa kanki bak'in ciki tunda kika haifi 'yar ta'adda" wani wahaltaccen kuka Amma keyi cike da ban tausayi ga muryar Kausar tana ji amma ba halin ta ganta, kallon ta d'an sandan ya sake yi a banzace yace "Bana so na shiga na fito na ganki anan find your way" yana gama fad'ar haka ya juya ya bar wurin, kuka ta cigaba da yi tana tausayin yanayin da taga Kausar a ciki, d'aya daga cikin 'yan sandan wurin yaji tausayin ta sosai yazo ya kama hannun ta ya tayar da ita tsaye yace
"Kiyi hak'uri ki tafi kar ya dawo ya same ki zai iya yi maki abunda yafi wannan" jinjina kai tayi alamar toh ta share hawayen ta tace
"Nagode" jinjina kai shima d'an sandan yayi sa'annan ta juya ta fita.


Tana fita ta samu keke-napep ta tsayar da ita ta gaya masa sunan unguwar da zata had'i da fad'awa ciki, tafe suke har suka kawo k'ofar gidan Alhaji Bala ta fito keke-napep d'in ta kwance gefen zanin ta ta fiddo kud'i wanda sune last card nata ta basa ta juya ta nufi cikin gidan. Buga k'ofar take yi da k'arfi sai ga mai gadin ya shararo a guje yazo ya bud'e k'ofar kad'an, koda yaga mahaifiyar Kausar ce yayi saurin wangale mata k'ofar bata jira jin komai daga bakin sa ba ta kutsa kai cikin gidan ta nufi hanyar da zata sada ta da parlorn, shigowa tayi parlorn kamar an cillo ta daga sama ta fad'i gaban Alhaji Bala da Hajiya Zainab tana haki sai kuma ta fashe da kuka, mik'ewa Hajiya Zainab tayi tsaye tana nuna ta da yatsa tace
"Hajara? Wa kuma kuke so ku kashe? Ni ko kuma miji na?" girgiza kai Amma ta shiga yi cikin kuka tace

"Hajiya kuy mana rai, ku dubi girman Allah ku saka baki a saki Kausar wallahi kashe ta zasu yi"
"Ai gara su kashe ta itama ta d'and'ana irin abunda ta d'and'ana wa A'ishah" kallon ta Amma keyi cike da mamaki don kuwa bata tab'a tsammanin fitowar kwatankwacin wannan kalaman daga bakin Hajiya Zainab ba, cikin kuka tace
"Wallahi ba Kausar ce ta kashe A'ishah ba kinfi kowa sanin haka don kwa ba wani halin Kausar wanda baki sani ba" tsawa Hajiya Zainab ta daka mata tace

"Keeee Hajara! I lost my only daughter but I didn't lost my mind! Wannan dad'in bakin naki a baya yayi tasiri akaina don haka tun muna shaida juna ki tashi ki fice min daga gida" kuka Amma keyi wiwiwi yayin da duk abunda ke faruwa akan idon Alhaji Bala amma uffan bai ce ba, rik'e k'afar Hajiya Zainab Amma tayi tana kuka mai tsuma zuciya "Zaki tashi ki fita ko sai na kira anzo an fitar dake?" cewar Hajiya Zainab, shuru Amma tayi sai rusa kuka take har yanzu bata saki k'afar Hajiya Zainab ba, cikin fushi Hajiya Zainab ta haurar da ita gefe d'aya ta juya ta d'auko wayar ta dake kan sofa ta fara danne-danne da sauri Amma ta mik'e tsaye ta share hawayen ta tace
"Ba sai kin kira kowa ba Hajiya zan tafi, sai dai ina rok'on Allah ya gaggauta tona asirin duk wanda yake da hannu a kisan A'ishah" shuru suka yi Alhaji Bala sai kallon ta yake, a hankali ta juya ta fice daga parlorn ta fito farfajiyar gidan har zuwa bakin gate anan me gadin sai magana yake mata amma sam bata jisa ba ta bud'e gate d'in ta fito, tafiya take bata san ina take saka k'afar ta ba gashi bata da ko taro bale ta hau keke-napep dole trekking tai har ta iso gida, koda ta iso maghrib tayi ana ta kiraye-kirayen sallah.




_8:00pm_
Wuraren k'arfe takwas na dare ne Bassam ya fito daga apartment nasa ya nufi parking lot, motar sa ya bud'e ya shiga ya kama hanya zuwa unguwar su Kausar. A bakin k'ofar gidan yayi parking ya fito ya taka zuwa k'ofar gidan ya tura k'yauren gidan had'i da yin sallama, muryar Abbah yaji ta amsa sallamar had'i da yi masa iso, tura k'yauren ya ida yi ya shiga cikin gidan, hango Abbah yayi a tsakiyar gidan zaune ya kunna lantern da alama gidan ba nepa ma, k'arasawa yayi sai a lokacin ya lura da Amma ce kwance yayin da Abbah ke zaune gefen ta yana kuka. Da sauri Bassam ya k'arisa wurin su har yana sassarfa yace

"Abbah lafiya kuwa? Me yake faruwa?" cikin kuka Abbah yace
"Nima bansani ba, na dawo gida daga sallar maghrib ne nazo na same ta a haka" da sauri Bassam yace

"Ok taimake ta ta tashi muje asibiti" girgiza kai Abbah ya shiga yi cikin kuka yace
"A'a Bassam ba sai munje asibiti ba ina kyautata zaton hawan jinin ta ne ya tashi" zura masa ido Bassam yayi yana mamaki yace
"Abbah ana ciwo ba magani ne?" mik'ewa Abbah yayi had'i da cewa
"Barin d'auko maka takardar maganin da aka rubuta mata" ba yadda Bassam ya iya haka ya tsaya yana kallon sa ya shiga d'akin ya fito, ba'a dad'e ba ya fito rik'e da takarda ya mik'awa Bassam, duba takardar Bassam yayi had'i da jinjina kai yace
"Ina zuwa" yana gama fad'ar haka ya juya da sauri ya bar gidan, motar sa ya shiga da tambaya har akai masa kwatancen wani babban pharmacy a chan yaje ya siyo dukka magungunan da aka rubuta ya dawo, koda ya shigo gidan ya tarar dasu a gun da ya barsu, k'arasawa yayi ya dank'awa Abbah maganin yai masa bayani kamar yadda pharmacist d'in yai masa. Har Abbah ya b'allo maganin zai bata Bassam ya dakatar dashi yace

"Wait taci abinci kuwa?" hawaye ne suka shiga bin kuncin Abbah ya girgiza masa kai a hankali, mik'ewa Bassam ya sake yi ya dakatar da Abbah daga bayar da maganin yace ya jira sa yanzu zai je ya dawo, sake fitowa yayi ya shiga motar sa da tambaya yanzu ma har ya samu wata eatery don kuwa bai san kan gari ba kuma ba tare da Jabir suke ba, take away yai musu mai rai da lafiya ya koma ya kaiwa Abbah yai masa Allah ya sawak'a da alk'awalin in shaa Allah gobe zai dawo yaga jikin ta. Abbah akan jin dad'i kasa godiya yayi sai kuka ya fashe dashi juyowa kawai Bassam yayi ya bar gidan dan kwa ya tsani kuka.



Sai _9:15pm_ ya iso gida, shigowar sa ya nufi main parlor anan ya tarar da Mammy zaune k'asa da system a gaban ta da alama aiki take yi, zaunawa yayi next to her yace
"Mammy" banza tayi dashi uwa bata san yana wurin ba, shima share ta yayi ya fiddo wayar sa ya fara danne-danne sai da ta shirya magana dashi ta dakatar da aikin ta juyo ta kalle sa tace

"Mr. Moral Authority, an gayamin an ga motar ka a gidan matsiyatan mutanen nan me ya kaika?" mamaki ne ya kama sa a ransa yana cewa wato kam Mammy spying nasa tasa ake yi, murmushi yayi kawai confidently yace
"Naje na samu wasu informations ne unfortunately na tarar mahaifiyar ta ba lafiya" gyara zama tayi ta cire glasses na fuskar ta tace
"Bassam nikam me yake damun ka ne?"
"Nothing" ya amsa mata har yanzu hankalin sa na akan wayar sa, cikin fushi tace
"Wato kam ban isa na gaya maka magana kaji ba ko?" ajiye wayar sa yayi ya fuskance ta yace
"Mammy wannan ba halin ki bane, it's not like you to show such a lack of sympathy mutanen nan suna buk'atar taimako, you should've atleast heard how her mother cried"
"Bassam you have to see how big this case is! Abun nan fa plotting nasa akayi that there was a plan to make sure A'ishah ce kawai aka kashe" girgiza kai Bassam yayi yace

"Hypothetically speaking akwai wani b'oyayyen al'amari a game da case d'in and I'm adamant sure ba Kausar ce ta kashe A'ishah ba"
"If not her then who did?" murmushi Bassam yayi yace
"I don't know yet, but I believe we will find out"
"Kalli nan Bassam" cewar Mammy, juyo da kansa yayi yana kallon ta tace "Knowing and proving are two different things and this girl is ten times dangerous, har yanzu baka da wata shaida da zai yi proving nata innocent. Idan kana dealing da case you only defend what you can prove" murmushi kawai yayi yace

"Mom I don't think that is necessary, our working styles are different plus duka wannan evidences da kike da shi ba haka abun yake ba nema kawai ake ayi distracting hankalin ku" mamaki ne ya kama ta wai Bassam ne yake gaya mata bata iya aikin ta abunda take ciki tun kafin a haife sa, cikin kakkausar murya tace

"Bassam I'm warning you for the second time, ka fita hanyar su and so my case" kallon ta yayi baice uffan ba sa'annan tace "Do exactly what I said or you suffer the consequences na fika sanin aikin nan" murmushi yayi ya mik'e tsaye yace
"Mammy ba abunda zai same ni in shaa Allah" sa'annan ya juya ya fita parlorn, mamaki ne k'arara a fuskar Mammy cikin ranta tana cewa wannan wane abun kunya ne tana case yaron ta yana opposing nata kasa cigaba da aikin tayi daga k'arshe ma ta tattara kayan ta ta nufi bedroom.


Gefen Bassam kuwa shigar sa d'akin keda wuya wayar sa ta fara ringing number ce ba suna, kamar kada ya d'aga kuma dai ya d'agan, wata bud'ad'd'iyar murya me amo ce yaji ta fara magana tana cewa

"Barrister Muhammad Bassam ina fatar na fad'a daidai" jinjina kai yayi kamar mutumen yana ganin sa yace
"Hakane"
"Na bugo ne na gargad'e ka da Allah ka fidda hannun ka daga case na kisan A'ishah"
"Waye?" Bassam ya fad'a cikin zargi
"Sanin ko waye ba zai amfane ka da komai ba amma idan kayi abunda na gaya maka to ka tsira" murmushi Bassam yayi ya zauna bakin gado sa'annan yace
"If you think you can stop me I think you re-evaluate your methods! I have sharp elbows when I'm fighting for something I believe in" dariya mutumen ya fashe da sa'annan Bassam ya cigaba "Ba zan daina ba untill I brought justice into this" dariya mutumen ya sake b'arkewa da sa'annan yace
"Yayi kyau! Other arrangements will be made" had'i da katse wayar, jefar da wayar Bassam yayi ko kad'an baiyi panicking da maganar mutumen ba ya shiga bathroom yayi wanka yazo ya kwanta.






*It'z Shawty*💕
[1/8, 3:20 PM] ‪+234 813 551 5123‬: *BARR. BASSAM*
(The Gallant) ❣




By *Shawty*💕

*2017*

3⃣0⃣

_Slowly and steady wins the race. Page 30 here we come._

__________________________________________


_The next day_
Tun da safe Bassam ya tashi yayi wanka ya shirya tsaf cikin suit sai dai yau bai saka coat d'in ba zanzaro kawai yayi da long sleeve fara sai red necktie sai nace yau yafi ko yaushe kyau. Fitowa yayi daga apartment nasa sai a lokacin yasa sun glasses a fuskar sa ya fara tafiya with so much arrogance which sounded natural to him. Kai tsaye gefen Mammy ya shiga bai same ta parlor ba, da d'an gudu ya haura sama zuwa bedroom nata, tura k'ofar yayi had'i da yin sallama, bata amsa sallamar ba bata kuma juyo ta kalle sa ba sai wayar ta take yi. Zama yayi gefen gadon ya fiddo wayar sa yana jiran ta ta k'are wayar, ta b'ata kusan minti goma tana wayar finally ta kashe ta cigaba da duba takardun dake gaban ta bata da alamar kula sa. Murmushi yayi yace
"Morning" ko kallon sa bata yi ba ta cigaba da abunda take, abun ya bala'in sosa masa rai a sanyaye yace "Mammy muna fad'a ne?" nan ma banza tai masa, shuru ya ziyarce su sa'annan Bassam ya mik'e yaje daf da ita ya rank'wafa yayi mata peck a goshi just like yadda take masa tun yana k'arami a sanyaye ya juya ya fice daga bedroom d'in. Har ga Allah abunda Bassam yayi ya bala'in tsaya mata a rai a ranta tana cewa wannan wace irin masifa ce ke neman tunkaro su, da sauri ta sauko daga kan gadon har tana tuntub'e ta sauko downstairs with intention ta tsayar dashi suyi magana amma bata same shi ba, da gudu ta fito farfajiyar gidan yayi daidai da fitar motar Bassam daga gidan. Tsayawa tayi sororo ta tabbata gidan wa'annan matsiyatan zaya je
"Me yake damun Bassam ne?" ta fad'a a fili, rasa amsar tambayar ta tayi taja jiki a sanyaye ta koma ciki.


Gefen Bassam kuwa ATM ya wuce kai tsaye ya fiddo kud'i masu yawan gaske daga nan kuma ya zarce sai wani

Please Login or Register in order to submit comment