Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

mata ya d'auke kansa sakamakon wata rama da bak'i da tayi duk ta fita a hayyacin ta bakomai a fuskar sai wannan angelic eyes d'in da suka k'ara firfitowa kamar an hura su sai dogon hancin, Amma kam rushewa tayi da kuka dalilin ganin yanayin da 'yarta take ciki. B'angaren Hajiya Zainab ma jikin ta sai da yayi sanyi da taga Kausar gaba d'aya kamannin ta sun chanza tayi duhu sosai ta rame kamar ba Kausaran da ta sani ba. Ana cikin haka ne Alk'ali ya shigo kowa ya mik'e tsaye kamar yadda doka ta tanada, bayan mai gabatarwa ya gabatar da k'arar ne Mammy ta mik'e tsaye tace
"Ya mai girma mai shari'a suna na Barr. Hindu Alhassan kuma niche lauyar masu k'ara" zaman ta ke da wuya Bassam ma ya mik'e tsaye confidently yace
"Suna na Barr. Muhammad Bassam Muhammad, nine lauya me kare wacce ake zargi" jinjina kai Alk'alin yayi ya basu izinin gabatar da jawabi da shaidun da suke da, mik'ewa Mammy tayi ta fito daga wurin da take zaune zuwa dock da Kausar take a ciki, cire glasses na fuskar ta tayi tace
"Yarinya ya sunan ki?" cikin disashshiyar murya Kausar ta amsa da
"Suna na Kausar Abubakar Sadeeq" lokacin ne Bassam ya karkato kansa baki d'aya izuwa kallon convo dake faruwa tsakanin Mammy da Kausar, jinjina kai Mammy tayi tace
"Miye dangantakar ki da gidan Alhaji Bala?" girgiza kai Kausar tayi tace
"Ba wata dangantaka ta jini tsakanin mu ni 'yar aiki ce a cikin gidan da farko am.. " bata bari ta k'arisa ba tace
"Daga baya kuma fa?"
"Amincin dake tsakanin Momy da mahaifiya ta yasa ta maido ni a gidan"
"Wacece Momy?" a sanyaye Kausar tace
"Mahaifiyar marigayiyar" jinjina kai Mammy tayi sa'annan tace
"A ranar sha hud'u a watan May b'arayi sun shigo gidan Alhaji Bala da dare har suka yi nasarar yin awon gaba da mak'udan kud'ad'e bayan gari ya waye aka samu gawar A'ishah a cikin gidan wanda ke kinsani iyayen ta ma sun sani ranar A'ishah ba'a gidan aka yi tsammani ta kwana ba, mu ajiye wannan gefe bincike ya nuna kece mutum ta k'arshe da kika yi waya da A'ishah kafin a kashe ta. Kausar me kika sani game da kisan A'ishah?" kuka ne ya kufcewa Kausar tace
"Wallahi bansan komai a kisan A'ishah ba" murmushi Mammy tayi tace
"Toh ga yanda abun ya faru.." tuni Kausar ta gyara tsayuwa tana sauraren abinda Mammy zata ce, d'aga murya Mammy tayi sosai a cikin kotun ta yanda kowa zai ji tace "Ta yiwu kin dad'e da mummunan kudurin ki na kashe A'ishah baki samu dama ba sai a ranar kika had'a kai da b'arayi suka shigo suka yi awon gaba da kud'i, baki tsaya a nan ba sai da kika yi nasarar kiran A'ishah a waya kika shirya mata maganganu har ta amince zata dawo gidan a ranar b'arayin da suka shigo suka yi nasarar hallaka ta kika raba bayin Allah nan da 'yar su k'waya d'aya tal, iyayen marigayiyar sun tabbatar wuri d'aya kuke kwana da ita meyasa b'arayin basu tab'a ki ba sai ita? Kausar meyasa kika kashe A'ishah?" kuka Kausar ta fashe dashi tana girgiza kai tace
"Ba abunda ya faru ba kenan"
"Toh me ya faru?" cewar Mammy, share hawayen ta tayi wanda yanzu sun zame mata jiki tace
"Tabbas a daren ranar na kira A'ishah wuraren k'arfe bakwai na marece sakamakon tun tafiyar ta bamu yi waya ba ta shaida min tana lafiya muka dad'e muna waya, wuraren k'arfe tara kuma ta kirani take sanar dani taje birthday na k'awar ta yanzu haka tana wurin kuma da an gama zata dawo gidan saboda ba zata koma gidan Goggo Hadiza ba zatai mata fad'a, ta gayamin zata shigo gidan a sace sai dai kawai a wayi gari a ganta don kuwa ta k'osa da zaman ta a gidan Goggo Hadizan tace kuma kadda na rufe k'ofar d'akin tasan ni da tsoro na amsa mata da toh. Bayan mun gama wayar ne tsoro ya kama ni na kasa samun natsuwa kasancewar parlor ne da bedroom d'akin namu sai na kwanta a bedroom na rufe k'ofar na bar mata parlorn a bud'e koda ta dawo, kuma tabbas A'ishah ta dawo a daren saboda ma akan 3 seater ta kwanta kuma akan ta aka kashe ta" gaba d'aya kotun tayi tsit kowa bayanin Kausar ya tab'a shi a hankali Mammy tace
"An ganki kan gawar A'ishah rik'e da wuk'ar da aka kashe ta kuma tun lokacin kika fita da gudu har zuwa lokacin da jami'an tsaro suka yi nasarar cafke ki, Kausar idan kina da gaskiya me ya saki guduwa?"
"Yadda aka ga gawar A'ishah da safe nima haka na wayi gari na ganta, na kasa tantance abunda idanu na ke hango min ne yasa na isa wurin gawar had'i da ciro wuk'ar daga jikin ta daidai lokacin ne Momy da Daddy suka shigo d'akin, ba kuma guduwa nayi ba tsintsar tashin hankali ne yasa na fita gidan da gudu amma wallahi bani na kashe A'ishah ba" cikin d'aga murya Mammy tace
"Idan ba ke bace to waye?" kamar daga sama suka jiyo muryar Bassam da k'arfi had'i da mik'ewa tsaye yace
"Ina da ja ya mai girma mai shari'a!" gaba d'aya kallon Alk'alin, Mammy da sauran jama'ar da ke cikin kotun ya dawo kan Bassam, yayin da Mammy mamaki ne ya rufe ta murya k'asa-k'asa tace
"Bassam?" d'an juyowa yayi kad'an ya kalle ta sa'annan ya fuskanci Alk'alin yace
"Lauyar me k'ara tasan irin kalaman da zatayi amfani dasu, Kausar k'aramar yarinya ce kadda kalaman ta su tunzura ta ta amsa laifin da ake zargin ta dashi, har yanzu zargi ake akan Kausar" jinjina kai Alk'alin yayi ya kalli Mammy yace
"A kiyaye Barrister" bowing kad'an Mammy tayi tace
"Nagode" ta dawo wurin ta ta zauna a sanyaye.


Bisa ga rashin k'wararan shaidu daga b'angarorin guda biyu Alk'alin ya d'aga sauraren shari'ar zuwa nan da sati uku don basu damar yin bincike kuma a dawo masa da gamsassun bayanai ya bada umurnin a cigaba da tsare Kausar a gidan kaso.

Koda suka fito Bassam da Jabir suka nufi mota kai tsaye suka fasa, yayin da Mammy da Hajiya Zainab sai da suka tsaya suka tattauna sa'annan suka rabu, straight Mammy gida ta nufa a zaton ta zata samu Bassam sai dai Bassam da Jabir Chamber suka nufa don suna da cases da yawa, sai around 4 Bassam ya bar Jabir yace masa za shi gida ya gaji sosai a haka suka rabu Bassam ya nufi gida.







*Shawty*💕
[1/8, 6:53 PM] ‪+234 813 551 5123‬: *BARR. BASSAM*
(The Gallant) ❣




By *Shawty*💕

*2017*

3⃣7⃣

Koda ya iso gida bai nufi sashen Mammy ba nasa part d'in ya wuce kai tsaye. Wanka yayi ya canza kayan jikin sa zuwa jalabiya fara mai hannu iya gwiwar hannu sa'annan ya fito ya nufi wurin Mammy, koda ya shiga parlorn bata nan abinci kawai yaje ya had'o ya dawo kan sofa ya zauna ya fara ci sakamakon wata matsananciyar yunwa dake addabar sa, kamar daga sama haka ya ganta ta shigo parlorn ta tsaya akan sa fuskar ta cikin b'acin rai, ajiye plate d'in abincin yayi yana kallon ta saboda ya bala'in tsorata a yadda ya ganta, cikin fad'a muryar ta har tana rawa tace
"Is that what your father had in mind with you when he was raising you? Bassam I regret this day I mean today! Ina fad'a kana fad'a? You even shout at me?" murmushin takaici Bassam yayi yace
"Mammy we are just doing our jobs ain't we? Kinfi kowa sani haka yanayin aikin mu yake, beside I'm trying to go beyond what my father taught me" tuni idanun ta suka kad'a suka yi jajir hawaye ya ciko idon, a hankali Bassam ya taka ya isa gaban ta yace "Had it been Paa is alive today, he'd be proud of me Mammy 'cause his dreams had come true, ko kin manta when he told us he can't wait to see me in front of him as a lawyer in a court? Then what about you and me? Can you imagine how happy would he be?" girgiza kai tayi duk da tasan gaskiya Bassam ke fad'a amma b'acin rai ya hana taga gaskiyar, cikin kakkausar murya tace
"He will never be proud of you yaga kana arguing dani, na lura I'm as good as stupid to you ban isa da kai ba saboda haka pack all your belongings and get the hell outta my house" daskarewa Bassam yayi a wurin ya kasa motsi tsawa ta daka masa tace "Ka fita nace!" cikin sarkewar murya Bassam yace
"Mam..mmy..?" yanzu kam dukan su hawaye suke cikin kuka Bassam yace "Mammy kora na kike?" cikin kuka tace
"Bassam ka fitar min a gida and never come back! Ever!" sai kuma ta fad'i sanin cewar tana da hawan jini hankalin sa yayi mummunan tashi yayi k'ok'arin taimaka mata ta tashi amma ta fizge jikin ta tace "Baka ji ne Bassam? Ka fita nace!" jinjina kai yayi hawaye na bin kumatun sa yace
"It's alright Mammy zan tafi" a hankali ya fara ja da baya sai kuma ya tsaya cak yace "Ya ayyuhal ladheena aamanu koonoo qawwameena bil qisdi shuhada'a lillahi wa lau ala anfusikum awil walideena wal aqrabeena in yakun ganiyyan au faqeera... Ke kika gayamin haka sanda Paa ya rasu that wannan shine wasiyyar da ya bar mana ni da ke, now you want me to dishonor his will for your selfish reasons?" jikin Mammy tuni yayi sanyi kalau, a hankali ya share hawayen sa yace "Da baki takurani na dawo Nigeria ba da duka haka bata faru ba plus da ban san ko wacece Kausar ba but you forced me, now that I knew her kuma nasan akan gaskiya nike you wanna stop me?" girgiza kai yayi yana k'ara kallon parlorn yace "I will go and I will always call this place a home" da sauri ya juya ya bar parlorn yana share hawaye yayin da Mammy jikin ta yayi likis ta kwanta a wurin ta rushe da kuka. Fitar Bassam ya nufi part nasa ya suri keys d'insa ya fito ya nufi parking lot, har ya shiga motar sa kuma ya fito yaje ya samu mai gadi yace ya dinga duba Mammy akai-akai zai d'an yi tafiya ne for the meantime amsa masa mai gadin yayi da toh sa'annan ya juya ya shiga motar sa ya bar gidan. Koda ya hau titi rasa ina zai nufa yayi, kiran Jabir yayi ya shaida masa har yanzu yana Chamber yace toh ya jira sa yana zuwa.



Gefen Alhaji Bala kuwa bayan sun koma gida kasa samun natsuwa yayi sakamakon abubuwan da Kausar ta fad'a a kotu, waya ya d'aga ya kira Alhaji Kabeer yace
"Kabeer anya kuwa abun nan zai yiwu?"
"Bala idan har baka shafe wannan Barristern ba ina baka tabbaci ba Kabara zai ga k'arshen ka ba wannan young lawyern ne" jinjina kai Alhaji Bala yayi yace
"K'warai kuwa I don't trust him, he thinks too much men like him are dangerous"
"K'warai da gaske he listen, think and observe but there's no need to fear him" cikin sanyin murya Alhaji Bala yace
"Bana tsoran sa but I watch him very carefully"
"You don't have to watch him, kashe shi zaka yi ko kuwa ya tona maka asiri yasa a kashe ka" jinjina kai Alhaji Bala yayi yace
"Amma nace ko nayi threatening nasa da mahaifiyar sa, that idan bai fita case d'in ba za'a kashe ta?" girgiza kai Alhaji Kabeer yayi kamar Balan na ganin sa yace
"No threaten him with his life" jinjina kai Alhaji Bala yayi yace
"Nagode Kabeer" had'i da katse kiran.



*Nasan zaku ga this page is too tiny, sorry k'arashen page 36 ne nayi in a separate page but let's just call it 37 please to avoid confusion. Nagode da addu'o'in ku gareni, I'm getting better.*






*Shawty*💕
[1/8, 6:55 PM] ‪+234 813 551 5123‬: *BARR. BASSAM*
(The Gallant) ❣





By *Shawty*💕


*2017*

3⃣8⃣


*My groups TEAMBASSAM*❣ *and* *BARR. BASSAM'S FANS*❣ *soyayyar ku ta daban ce, together we shall wreck the ball in shaa Allah. ILYSM*💞


_________________________________________

B'angaren Bassam kuwa gudu kawai yake kan titin "Bassam ka fitar min a gida and never come back! Ever!" shi kawai ke masa dancing a brain he can't help saukar hawaye kawai yaji a fuskar sa, gudu yake fanfalawa kan titin wanda Allah kawai ya kaishi Chamber lafiya. Da sauri ya fito bai damu da rufe motar ba ya nufi cikin office d'in ya samu Jabir zaune yana rubutu, Jabir yana ganin sa yasan ba lafiya saboda ga baki d'aya kamannin sa sun chanza fuskar sa tayi ja haka ma idanun sa, straight wurin fridge ya nufa ya d'auko goran ruwa ya kafa a bakin sa sai da ya sha iya cikin sa sa'annan ya juyo yana kallon Jabir yayin da shima Jabir d'in shi yake kallo yana nazarin fuskar sa yace
"Barrister lafiya kuwa?"
"Ba lafiya Jay, it's getting worse" ajiye pen dake hannun sa Jabir yayi ya fuskanci Bassam sosai yace
"What? Me yake faruwa?"
"Mammy ta kore ni daga gidan ta" ya amsa masa a tak'aice, mik'ewa Jabir yai tsaye yace
"Whaaaaaattt? Me kay mata haka?"
"Me fa? Akan case d'innan ne" cewar Bassam, komawa Jabir yayi kan kujerar ya zauna had'i da cewa
"Shit! Yanzu me abun yi? I think kawai ka daina case d'innan Barrister" murmushi Bassam yayi ya gyara tsayuwar sa yace
"Saboda me?"
"Saboda Mammy mana" murmushi Bassam yayi yace
"Kada ka damu I knew her, sometimes she can't control the way she get angry na d'an wani lokaci ne zata sauka" d'aga gira Jay yayi yace
"Are you sure? Kadda kaje kayi abunda zaka dawo kana regretting fa" murmushi Bassam yayi ya zauna kan d'aya daga cikin kujerun yace
"Ba regrets in shaa Allah" d'an rausayar da kai Jay yayi yace
"Toh Allah yasa! Yanzu ya kenan gidan zaka koma ko yaya?" girgiza kai Bassam yayi yace
"No! Hotel"
"Hotel?" cewar Jay "Why not kazo muje gidan mu?" nan ma girgiza kai Bassam yayi had'i da yin murmushi yace
"No! Karka damu zanje Hotel d'in" gyad'a kai Jabir yayi yace
"Alright then" mik'ewa Bassam yayi ya nufi hanyar fita da sauri Jabir ya dakatar dashi yace "Ina zaka je?" juyowa yayi yace
"Zan je ATM daga chan kuma zan wuce Mall I need to buy some stuffs" jinjina kai Jabir yayi yace
"Ok" suka yi sallama Bassam ya fita ya shiga motar sa. Tun da ya fita ya hau titi ya fara tafiya ya hango wata mota k'irar Mercedes da dark glasses a bayan sa ta front mirror, lokacin da ya isa ATM d'in yayi parking ya fito ne yaga motar ta wuce, bai kawo komai a ransa ba ya isa ATM d'in ya ciro kud'i ya dawo ya shiga motar sa ya nufi mall. Bayan ya hau titi sosai ne ya sake hango wannan motar a bayan sa ya lura kuma the moment ya k'ara speed na motan sa itama zata k'ara gudu kuma da ya rage itama zata rage wanda ya tabbatar masa ko waye binsa yake, tuk'in sa kawai yake har ya iso mall d'in ya shiga yana cikin tafiya ne bai yi aune ba yaji yayi karo da wani abu, da sauri ya tada kansa don ganin mey yai karo dashi wani saurayi ya gani bak'i murdadde sanye da singlet fara da jean da wata sark'a a wuyan sa kansa yayi irin askin nan da ake aske rabi a bar rabi, fuskar sa murtuke bakin sa bak'ik'irin da alama baya rasa shan weed ko wani abu da chewing stick a bakin sa da kayi masa kallo d'aya zaka tabbata irin thugs d'innan ne, kallon juna suke tsakanin sa da Bassam amma ko ya motsa, a hankali Bassam yace
"Excuse me dude" har yanzu mutumin bai motsa ba sai kallon Bassam yake, cikin husky voice nasa yace
"Sorry dude we just bumped into each other" magana yake amma ba alamar janyewa daga blocking Bassam da yayi kuma it seems hak'uri yake bayarwa amma ba alamar nadama tattare dashi, murmushi Bassam yayi ya gyara tsayuwar sa ya zura hannayen sa biyu cikin aljihu yace
"In a city of more than one million people we just happen to bump into each other? Are you having me followed?" d'an murmushi yayi yace
"Kasan kwanan zancen kenan but you haven't returned my calls Barrister"
"I haven't returned anybody's call" cewar Bassam "What do you want?" murmushi mutumen yayi yace
"I want to talk to you" kallon sa Bassam keyi irin ina sauraren kan nan, k'arasowa mutumin yayi daf da fuskar Bassam yace "I couldn't help but take it personally, I'm here to ask you to be careful Barrister" dariyar rainin hankali Bassam yayi yace
"Be careful why?"
"Whatever it is you stumbled onto, it's big" cewar mutumin, dariyar Bassam ya cigaba da yi yace
"I didn't stumbled onto anything, I took this case on purpose" cikin mamaki mutumin yace
"What purpose?"
"Well, my purpose is to take whoever is behind this down" dariya sosai mutumin yayi yace
"Listen, I don't know you well enough so, I'm gonna say this.. Walk away and please do it now!" murmushi Bassam yayi har hak'oran sa masu kyau suka fito yace

"If I don't then what?"
"You're going to regret it later" dariya Bassam yayi yace
"Is this about protecting me or protecting you?" confidently mutumin yace
"Protecting you Barrister, I don't wanna see you loose everything you've worked hard for" dariya Bassam yayi yayi tapping shoulders d'in mutumin yace
"Dude, there are people who run from the fire and there are people who run into it so, save yourself some time and stop worrying about me 'cause I don't care about myself, I've made up my mind and I won't change it for any murtherfucker" mamaki sosai ya cika mutumin saboda yadda Bassam ke zaro maganar ba alamar tsoro ko razana tare dashi confidently yake magana abunsa ko kad'an bai yi panicking ba, murtuke fuska mutumin yayi yace
"Bassam or not, there are alot of us and one of you" d'an raising shoulders d'insa Bassam yayi questioningly yace
"Is that a challenge? I'll do whatever it takes to preserve justice and save the poor kid" jinjina kai mutumin keyi yana kallon Barrister don ya bala'in basa mamaki yace
"Nice try" ya juya yai tafiyar sa, kallo Bassam ya bisa dashi har ya b'ace daga ganin sa sa'annan ya shiga mall d'in ya fara neman abunda ya kawo shi, bayan ya gama ya biya kudin ya fito ya shiga motar sa ya ja ya tafi.


Gefen wannan thug d'in kuwa yana shiga motar sa ya kira Alhaji Bala had'i da cewa
"Alaji wannan guy d'in kasan yadda zaka yi dashi da gaske yake yi"
"Whatever cave, cavern or hole he is, I want you to find Barr. Bassam and shoot him" cewar Alhaji Bala, jinjina kai thug d'in yayi yace
"Kana nufin mu halbe sa kenan?" lullube sa Alhaji Bala yayi da masifa yana cewa

"Don't be silly! Kamar ya ku halbe sa? I'm giving you shoot to kill order"
"Toh ae hausa sosai zaka yi Alhaji, da kace mu halbe sa ina d'auka ko a k'afa haka" cewar thug d'in cike da rainin hankali, tsuki Alhaji Bala yaja yace
"Mtsww shoot him to death stupid kawai" had'i da katse kiran.




_8:00pm_
Bassam ne da Jabir cikin mota suna tafiya bayan sun kammala aikin chamber Bassam zaiyi dropping d'insa a gida, tafe suke suna hira abunsu basu ankara ba sai ganin wata mota suka yi ta tunkaro su had'i da kunna wuta full light wanda ya hana basu damar hango wanda yake tuk'in tazo ta tsaya gabansu d'aya daga cikin masu tuk'a motar ya fito fuskar sa rufe da mask, ba shiri Bassam ya taka birki suka tsaya gashi titin ba yawan mutane cikin tsoro Jabir yace
"Wannan fa? Su waye?"
"Bansani ba lemme check" cewar Bassam ya fara k'ok'arin bud'e murfin k'ofar motar ba alamar tsoro ko fargaba tare dashi, chafko hannun sa Jabir yayi ya gama tsorata yace
"Ina zaka je?" juyowa Bassam yayi had'i da yin murmushi yace
"Calm down Jay, ba kai suke nema ba ni suke nema zanje naji da wacce suke tafe" haka suka yi ta arguing Jay yana cewa ba zai fita ba shi kuma yana cewa sai ya fita har dai yayi galaba ya bud'e motar ya fito, kallon-kallo suka tsaya yi da mutumin cikin d'aga murya mutumin yace
"Nice try Barrister" kafin Bassam ya bud'i baki yace wani abu kawai yaji saukar bullet a gefen k'irjin sa he can't help yadda abun yazo masa unexpected ya dafe gefen k'irjin had'i da duk'awa ya dafa motar bai yi aune ba ya sake jin saukar wasu tagwayen bullets d'in a k'afar sa ta hagu, wata k'ara mai firgitarwa ya saki ya fad'i k'asa a wurin cikin jini sai da shooter d'in yaga ya kai k'asa sa'annan ya juya ya shiga motar suka bar wurin lalace, cikin tsananin firgita wacce ba za'a iya misalta shi ba Jabir ya fito daga motar yayi kan Bassam da gudu yayi daidai da kawowar wata mota fara k'irar Elantra a wurin, matashiyar budurwa ce 'yar kimanin shekara ashirin da hudu ta bud'e motar da sauri ta nufo su.










*Shawty*💕
[1/8, 6:57 PM] ‪+234 813 551 5123‬: *BARR. BASSAM*
(The Gallant) ❣





By Shawty 💕

2017

3⃣9⃣


Mik'ewa Jabir yayi zumbur yana kallon budurwar yayin da ita kuma irin kallon da Jabir ke mata yasa ta dakata daga k'arasowar da take suna kallon juna, a hankali Jabir ke kallon ta daga sama har k'asa yace
"Wacece ke?" shiru tayi bata ce masa komai ba sai kallon sa take, takaici sosai Jabir yaji musamman idan ya kalli Bassam yaga yadda yake zubar da jini ita kuma tazo tana nema ta b'ata masa lokaci, tsawa ya daka mata yace "I said wacece ke? Are you one of them?" tsoron tsawar da Jabir ya daka mata ya kama ta da sauri ta girgiza kai tace
"A'a"
"Then? Meke tafe dake?" cewar Jabir, juyawa tayi ta kalli motar ta tace
"Nazo ne zan wuce na hango abunda yake faruwa kuma ina tunanin hango mota na da suka yi ne ya sanya su guduwa amma wallahi ni ba tare dasu nike ba" shiru Jabir yayi don kuwa har yanzu ya kasa yarda da ita, kallon Bassam budurwar tayi da sauri ta mayar da kallon ta akan Jabir tace "He's dying, bawan Allah nan yana buk'atar taimako" sai a lokacin hankalin Jabir ya dawo jikin sa ya kalli Bassam ya gansa in a pool of blood, rigar jikin sa ya shiga tub'ewa da sauri ya durk'usa ya fara

Please Login or Register in order to submit comment