Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

bar garin don ya tabbatar ba zasu tab'a tserewa tambayoyin mutane da kuma 'yan jarida ba, haka kuwa akayi suka debo duk wani abun da zasu bukata suka fito farfajiyar gidan anan Sadeeq ya sallami me gadi yace ya kama gabansa suka shiga cikin wata tamfatsetsiyar mota suka fito yayi parking ya fito daga motar ya saka manya-manyan padlocks ya rufe gidan sannan ya koma yaja motar tsiyace suka bar garin sai dai muce Allah yasa mufi karfin zukatan mu, ameen.


******


Gefen Bassam kuwa ba shi ya tashi daga bacci ranar ba sai 10:30am, bathroom ya shiga yayi brush yayi wanka ya fito ya shirya cikin bak'in wando da white long sleeve sai dai baiyi zanzaro ba kuma baisa tie ba, fitowa yayi yana dogara stick d'insa ya nufi sashen Mammy, koda ya shiga ya same ta tana breakfast kai tsaye wurin ta ya nufa ya gaida ta, cikin fara'a ta amsa masa ta tambaye sa ya jiki ya amsa mata da sauki, da taimakon Mammyn ya samu ya zauna tai serving nasa suka fara cin abinci ba wanda kece da wani uffan, murmushi Mammy tayi tace
"Bassam we got so lucky when you were shot, I don't know what I'd do if I lost you" murmushi kawai Bassam ya mayar mata suka cigaba da cin abinci. Wayar sa da ya ajiye daga gefe kan dining table din ya dauko ya bude Twitter, wani labari ne yaga Jay yayi re-tweeting yaja hankalin sa ya bud'e ya fara karantawa had'i da kallon video, ba labarin kowa bane sai na Alhaji Kabara murya k'asa-k'asa yace
"Holy shit!" da sauri Mammy ta dakatar da cin abincin da take tace
"Bassam lafiya?" wayar ya mik'a mata had'i da cewa
"Duba kiga" karb'ar wayar tayi ta fara saka medical glasses dinta first sannan ta fara duba labarin, da innalillahi wa inna ilayhi raji'un ta ajiye wayar ta tura ta gaban Bassam tace
"Wannan wace irin zuciya ce?" d'an d'aga kafad'unsa Bassam yayi sai cin abincin sa yake yace
"That's the kind of world we're living these days" cike da alhini Mammy ta saukar da ajiyar zuciya tace
"Allah ya kyauta karshen mu"
"Ameen" cewar Bassam sai cin abincin sa yake yayin da Mammy ta kasa cigaba da cin abincin ma, kamar an mintsile sa ya mik'e zumbur wanda ya manta ma da rauni a jikin sa da sauri Mammy ta rik'o hannun sa tace
"Ina zaka je ne?" murmushi yayi yace
"Apartment nawa" a tak'aice, murmushin itama ta mayar masa tace
"Ok" yayin da shi kuma ya juya ya fice daga parlorn. A farfajiyar gidan ya tsaya ya fara dialing number Jay, ringing d'aya ya d'aga had'i da cewa
"Hey man! Haffa? Ya jikin?"
"Alhamdulillah" cewar Bassam sannan yace "Naga wani news sai circulating yake a social media yau"
"Yeah!" cewar Jay sannan ya k'ara da cewa "Today it's all about Kabara" a hankali Bassam yace
"Baka tunanin baya rasa alaka da case d'in Kausar?" da sauri Jabir yace
"Kai! I don't think"
"Ok" cewar Bassam "But I want to see her though" da sauri Jay yace
"Yaushe? Yau?"
"Yeah! Kana off.. " Jabir bai barsa ya kai aya ba yace
"Haba Bassam! Jiya fa ka dawo daga asibiti you need to rest" saukar da numfashi Bassam yayi yace
"What do you want me to do? Sit down and shut up? Is that it?" shiru Jay yayi a hankali Bassam yace "Karka damu Jay, kana office ne yanzu ko kana gida?"
"Ina office" cewar Jabir
"Ok gani nan zuwa" cewar Bassam had'i da katse kiran ya kira me gadi yace ya d'an goge masa motar sa zai fita, da toh me gadin ya amsa ya juya don cika umarnin Bassam shi kuma Bassam ya nufi cikin gidan. A parlor ya sami Mammy ya d'an sosa kai yace
"Mammy zan fita" kamar jira take dama ta mik'e tsaye tace
"Bassam ina zaka je da raunuka a jikin ka?" a sanyaye yace
"Zanje in ga Jay ne" murmushi Mammy tayi tace
"Be honest and say Kausar" mamaki ne ya kama sa, murmushi Mammy ta sake yi tace "You think you can pull my legs right? Nasan ba zaka daina case dinnan ba kamar yadda ka gayamin" cikin sanyin murya yace
"Mammy.." katse shi tayi tace
"Ae bazan k'ara hana ka ba so, go!" jikin sa ne yayi sanyi ya kalle ta yace
"Mammy look into my eyes again and tell me you don't like me being in the case then I promise you I'm gonna quit it today, right now!" itama jikin ta ne yayi sanyi a hankali ta girgiza kai tace
"Nope sweetheart, but lemme assure you that bana san Kausar saboda ba alkhairi a tare da ita, ta shiga gidan Alhaji Bala ta wargaza musu farin ciki and now since the day she burst into our affairs, our life has become one big kung-fu party" har cikin ransa yaji zafin kalaman Mammy saboda none of them sound like Kausar amma dai ba yadda zaiyi ya jinjina kai yace
"It's okay" ya juya ya fice daga parlorn.






Gefen Alhaji Bala kuwa zaune suke shi da Alhaji Kabeer ba abunda suke sai rizgar dariya suna pouring drinks a glass cups suna tossing suna sha suna k'yalk'yala dariya like never before wane an musu bushara da gidan aljannah duk kuwa ta dalilin ganin videon Kabara ne da suka yi a social media yana yiwa kansa tonon silili, da ka gansu zaka tabbatar suna cikin farin ciki da annushuwa ne musamman Alhaji Bala, wayar sa ce ta fara ringing amma ba shine ya katse masa dariyar ba, d'auko wayar yayi yaga T.K ne ke kira da sauri ya d'aga T.K yace
"Alhaji yanzu nike samun labari he survived"
"Wa kenan?" cewar Alhaji Bala
"Barristern mana" da sauri cikin fad'a Alhaji Bala yace
"How the hell did that happened?" sai kuma yaja tsuki yace "Ina zuwa I'll get back to you" had'i da katse kiran ya kalli Alhaji Kabeer yace "The son of a bitch has escaped" da sauri Alhaji Kabeer ya kalle sa ya nuna k'asa da farcen tahiya yace
"You mean to tell me Bassam yana raye?" jinjina masa kai Bala yayi alamar eh, wani gwauron numfashi Alhaji Kabeer ya saukar yace "Tsugune bata k'are ba Bala, amma kada kayi yunkurin d'aukar wani mataki idan har harbin da akai masa bai zame masa darasi ya daina case din ba sai mu kuma mu chanza taku" jinjina kai Alhaji Bala ya shiga yi alamar maganganun Kabeer sun shige sa ba abunda yake sai kallon k'asa a hankali yace
"I'm gonna come back for you Bassam, and I'm gonna show you no mercy"







*Shawty*💕
[1/8, 7:15 PM] ‪+234 813 551 5123‬: *BARR. BASSAM*
(The Gallant) ❣




By *Shawty*💕


*2017*

4⃣4⃣


Fitowa Bassam yayi ya nufi parking lot daidai lokacin ne wayar sa ta fara ringing alamar shigowar kira, tsayawa yayi ya d'auko wayar yaga number ce ba suna a sanyaye ya d'aga, muryar mace yaji tayi magana tace
"Hello"
"Hi" ya amsa mata a takaice, cikin sanyin murya yaji tace
"Barrister Samira ce" sai da Bassam yayi dogon tunani sannan ya tuna ta yace
"Oh! Got it, ya kike?" murmushi tayi batayi tunanin zai karb'e ta haka ba tace
"Lafiya kalau ya jikin?"
"Alhamdulillah" ya amsa mata kawai, karya murya tayi tace
"Anjima zan shigo ta unguwar ku zan zo in duba ka idan ba damuwa" shiru Bassam yayi for some time sannan yace
"All right, I'll be expecting you" murmushi tayi tace
"Thanks" suka yi sallama ya kashe wayar da haka ya isa parking lot d'in ya shiga motar sa yaja ya nufi Chamber. Koda ya isa Jay ya samu yana ta faman rubuce-rubuce suka gaisa ya tambaye sa ya jiki ya amsa masa da sauki sosai sannan Bassam ya mik'e tsaye yace
"Barin zo in tafi Prison d'in" kallon sa Jabir yayi yace
"All right! Ko nazo na raka ka ne?" girgiza kai Bassam yayi yace
"No! Ka cigaba da aikin ka kawai I'll keep you updated" jinjina kai Jay yayi yace
"All right! Sai ka dawo" suka yi sallama Bassam ya fito ya nufi motar sa ya shiga yaja ya nufi Prison d'in. Koda ya isa ya gabatar da kansa da wacce yake son gani a matsayin shine lauyan ta, ba b'ata lokaci aka kaisa wani d'aki d'auke da table da kujeru biyu suna fuskantar juna akace ya jira aje azo da ita, ba'a d'auki five minutes ba sai gashi an shigo da ita cuffed still Bassam yana tsaye, bata ma san yana cikin d'akin ba koda mutumen ya shigo da ita ya koma ya rufe d'akin yai tafiyar sa yayin da ita kuma Kausar ta shiga doka kanta a bangon d'akin tana kuka still bata san Bassam yana wurin ba tana cewa
"Gara na kashe kaina na huta!" kamar daga sama taji muryar mutum yana cewa
"Suicide won't serve any purpose, don't keep finding ways to kill yourself we'll solve the problem together" juyo da jajayen idanun ta tayi tana kallon sa tsaye da stick a hannun sa, mamaki ne ya kama ta cikin ranta tace to me ya same shi ko yayi accident ne yaji rauni? Kallon sa tai tayi a hankali ya d'aga hannun sa ya nuna mata d'aya daga cikin kujerun alamar tazo ta zauna, ba musu ta taso tazo taja kujerar ta zauna, shima dogarowa yayi yazo yaja d'aya kujerar da ta rage ya zauna suna fuskantar juna. Cikin sanyin murya Bassam yace
"I know you're having a rough time in here but I promise if you could only tell me something I'm sure we could get rid of this mess" k'anta duk'e a k'asa tace
"Why are you here?" a hankali Bassam yace
"I wouldn't be here if it wasn't important" d'ago da idanun ta tayi tace
"Cewa nayi me ya kawo ka?" gyara zaman sa yayi yace
"I'm here for A'ishah" d'ago kai Kausar tayi da sauri tana kallon sa, jinjina mata kai yayi yace "Yeah! I want justice for her" girgiza kai Kausar tayi cikin d'acin rai muryar ta har tana rawa tace
"But justice isn't gonna bring her back" a hankali ya jawo duka hannayen ta biyu da akayi cuffing nasu da cuffs ya had'a da nasa wuri d'aya yace
"I know I can't bring her back to life but she needs justice" shiru Kausar tayi kanta a k'asa sai hawaye ke d'iga kan table d'in, a sanyaye Bassam yace "A'ishah is gone and it's terrible but we've got to live on, ba don an kashe A'ishah ba kema zaki zab'i mutuwa no! Both of you need justice" har yanzu bata d'ago kai ta kalle sa ba sai hawayen dake zuba a hankali yace "Tell me something you knew Kausar we'll get them but if you don't, then they will certainly get us" nan ma shiru bata d'ago kanta ba bata kuma ce dashi uffan ba, cikin sanyin murya yace "Kinsan me?" sai a lokacin ta d'ago fuskar ta wanda hawaye ya gama wankewa ta girgiza masa kai alamar a'a, murmushi yayi ya saki hannayen ta ya fara b'alle buttons na long sleeve d'insa ya bud'e mata k'irjinsa inda aka harbe sa wanda an manna masa bandage a wurin ta gani, bai ce mata komai ba ya fiddo k'afar sa daga cikin table d'in ya yaye k'afar wandon sa nan ma sai ga wuri biyu rufe da bandage alamar rauni sannan ya mayar da k'afar wandon ya rufe k'afarsa ya mayar da buttons na rigar sa ya rufe ya kalle ta wacce mamaki ne kwance a fuskar ta, murmushi yayi ya sake jawo hannayen ta ya had'a da nasa kamar dai d'azu yace "Plus kin ganni da stick but you don't care to ask me ya same ni ko?" a sanyaye tace
"What happened?" murmushi yayi yace
"They attacked me and shot me thrice" idanu Kausar ta zaro a hankali hawaye suka fara gangaro mata tace
"Ka gani ba? Kaga abunda nike gaya maka ba? This is what I've been telling you I told you to stay away wallahi zasu iya kashe ka" murmushi Bassam yayi yace
"They can only kill me if you don't tell me what you knew, Kausar we're running out of time" rintse hannayen sa tayi gam cikin nata tace
"I won't have you dying for me so, go!" kallon ta Bassam yayi da kyau yace
"Kin shirya mutuwa kenan?" jinjina masa kai tayi alamar eh, murmushi yayi yace
"Well, ni ban shirya ba and so your parents" wani abu taji cikin ranta da ya ambaci iyayen ta, a hankali take kallon sa ya gyad'a mata kai yace "Think about your parents what they've been through, they too want justice to be served, ba zasu so a kashe ki ba akan laifin da baki aikata ba" yanzu kam kuka ta fashe dashi sosai a hankali Bassam yace "Don't imprison your words let them be free, I know you've got a lot to tell me" shiru bata ce masa komai ba sai kukan da take cikin sanyin murya Bassam yace "I know you have good answers for all of this, but if you don't tell me what they are, I can't help you walk out of here, I'm offering you a lifeline Kausar, take it" shiru tayi sai sheshshekar kukan ta kawai kake ji, rintse hannayen ta sosai Bassam yayi yace "Kausar kina so a kashe ni?" da sauri ta girgiza masa kai alamar a'a "Then you are my last hope" a hankali ta d'ago kai tace
"Me kake so ka sani?" gyara zama Bassam yayi yace
"Me kika sani game da kisan A'ishah?" girgiza kai tayi hawaye sai ambaliya suke mata tace
"Na gaya maka bansan komai ba, na tashi kawai da safe ne na samu gawar ta an kashe ta" jinjina kai Bassam yayi alamar ya gamsu yace
"Did you noticed anything out of ordinary, any recent life changes, anything unusual before she's been killed? Ko ta tab'a gaya miki wani abu wanda akwai zargi a ciki kafin a kashe ta?" shiru Kausar tayi na wasu mintuna sannan ta girgiza kai tace
"Babu" nan ma jinjina kai Bassam yayi yace
"Me kika sani game da Alhaji Bala mahaifin A'ishah?" da sauri ta d'ago kai tana kallon Bassam wanda shima ita yake kallo in a very serious face ba alamar wasa a fuskar sa yace "Anything suspicious about him?" girgiza kai tayi tace
"Would you just stop this? They're watching everything, they got eyes and ears all over. And the longer you talk to me, the worse it looks" dariya ta bashi amma dai ya kanne kada ya harzuk'a ta tace ta fasa gaya masa, a hankali yace
"You are safe with me, Kausar ba abunda zasu iya just tell me" shiru tayi ta kasa cewa komai, d'ago fuskar ta Bassam yayi yace "Tell me" a sanyaye tace
"Kwana biyu kafin kisan A'ishah na fito parlorn gidan da tsakar dare sakamakon k'ishirwar da ta addabe ni na sauko don in samu ruwa in sha lokacin ne nagan.." sai kuma ta kasa k'arasawa, lallashin ta da kwantar mata da hankali Bassam ya shiga yi don ya lura kamar tsorace take, a sanyaye tace "Na ganshi rik'e da k'waryar jini kuma da alama yana shan jinin don kuwa hakan ya nuna a gaban rigar sa" zaro ido Bassam yayi yace
"K'waryar jini? Alhaji Balan?" jinjina masa kai Kausar tayi alamar eh, kawar da kansa Bassam yayi daga kallon Kausar zuwa kan table d'in ya k'ura masa ido yana tunani, kamar an mintsile sa yace "Are you sure about this?" nan ma jinjina masa kai tayi alamar eh sannan yace "Sai me kuma?" saukar da numfashi tayi tace
"Tun daga ranar ya cigaba da kallo na da wani dead looks, idan na gaida shi baya amsawa kuma na samu kaina cikin tsoro da tashin hankali, koda yaushe a firgice nike kum.." bai barta ta k'arasa ba ya mik'e tsaye ya zagayo yazo wurin ta ya shiga share mata hawayen da suka zubo mata yace
"Thanks and stop these tears please" jinjina kai tayi alamar toh sannan yace "You're safe kinji? Ba abunda zai same ki" nan ma jinjina kai tayi yai mata sallama ya kama hanyar fita da hanzari.





Da sauri ya fito ya shiga motar sa yaja ya bar prison d'in, sai da ya hau titi sosai ya d'auko wayar sa ya kira Jabir yace
"Jay you know what?"
"Nope" cewar Jabir, da sauri Bassam yace
"Yarinyar ta bani wani information" da sauri Jabir yace
"What did she said?"
"She told me two days before the incident taga Alhaji Bala rik'e da k'waryar jini yana sha"
"Whaaaat?" cewar Jay da k'arfi, da sauri Bassam ya amsa masa da
"Yeah! You know what?"
"Nope" cewar Jabir, cikin sanyin murya Bassam yace
"A cikin videon Alhaji Kabara da akayi releasing a social media, idan ka lura yana rik'e da wani container wanda ya tabbatar jinin 'ya'yan sa ne a ciki kuma da alama ya sha jinin plus yace yaje yak'ar wani ne wanda ya fishi k'arfi a tsafi ya aiko masa da fatalwa sai dai bai fadi sunan ko waye ba. It's a big co-incidence Jay, shi yake nuna da alama aika-aikar da Kabara ke aikatawa zata zo d'aya da ta Alhaji Bala kuma ni ina kyautata zaton Alhaji Bala ne Alhaji Kabara ke magana akai cikin videon" shiru Jabir yayi yana nazarin maganar Bassam wacce kusan akan hanya take, muryar Bassam ya tsinto yana cewa "Yanzu ina zan samu Alhaji Kabaran?" cikin sanyin murya Jay yace
"Na samu labarin ya mik'a kansa ga 'yan sanda a wani division da baya da nisa da unguwar da yake zaune"
"Ya sunan unguwar?" cewar Bassam, gaya masa sunan unguwar Jay yayi sukai sallama yace zai dinga sanar masa da abunda ake ciki ya katse wayar, da tambaya har ya iso unguwar su Alhaji Kabara akai masa kwatancen Police Station d'in ya karkata motar sa ya nufi chan. Koda ya iso harabar wurin yayi parking yayi daidai da fitowar da 'yan sandan suka yi da gawar Alhaji Kabara a mace, wani d'an sanda Bassam ya tara ya tambaye sa ko wannan station d'in Alhaji Kabara ya kawo kansa ya amsa masa da eh ai shine ma aka fito da gawar sa yayi mutuwar wulakanci, zaro ido Bassam yayi yace
"Kana nufin Kabara ya mutu?"
"K'warai kuwa" cewar d'an sandan, duka Bassam ya kai wa motar sa had'i da cewa
"Holy shit!" ya dad'e tsaye a wurin yana zagaye sannan ya d'auko wayar sa ya kira Jabir yace
"Jay, we lost him"
"Ban fahimce ka ba" cewar Jabir, cikin rashin k'warin gwiwa Bassam yace
"We lost Kabara"
"Whaaaat?" cewar Jabir da k'arfi
"Yeah! Ya mutu wallahi yanzun nan aka fito da gawar sa, bansan me zanyi next ba Jay, shine kawai mutumen da zai warware wannan matsalar and he's dead" shiru Jabir yayi sannan yace
"Yanzu ya kenan?" wata dubara ta fad'o wa Bassam a rai yace
"Zan je gidan Alhaji Bala right now"
"Me zaka yi?"
"I'm gonna ask his wife some questions"
"All right" cewar Jabir sukai sallama Bassam ya katse kiran ya juya ya shiga motar sa yaja ya nufi gidan Alhaji Bala. Isowar sa k'ofar gidan yai ta danna horn sai ga mai gadi yazo ya bude yaja motar ya shiga cikin gidan yayi parking ya fito, gaisawa suka yi da mai gadin yace ya shiga ya nemar masa izini wurin Hajiya yana so zaiyi magana da ita, ba musu me gadin ya amsa ya juya ya nufi cikin gidan yayi daidai da Bassam ya hango wata envelope yashe daga gefe a wurin, takawa yayi ya isa wurin envelope d'in ya duk'a ya d'auko ya bud'e yaga takarda a ciki da wani written note, karance rubutun yayi tsaf hankalin sa a tashe ya d'ago kai yayi daidai da kawowar me gadin wurin yace ya k'arasa tana parlor, tuni zufa sai karyowa Bassam take ta ko ina ya girgiza kai yace
"No! An kira ni a waya it's urgent but zuwa anjima zan sake dawowa ka koma ka bata hakuri please" mamaki ne ya kama mutumen don yasan lafiya kalau ya bar Bassam ya shiga cikin gidan amma ya dawo ya tarar dashi hankali a tashe amma sai yafi kyautata zaton ko mutuwa aka gaya masa a wayar da yace an kira sa, jinjina kai me gadin yayi yayin da Bassam ya shiga motar sa ya tada me gadin ya ruga ya bud'e masa gate ya fita gidan yayi daidai da kawowar motar Alhaji Bala ma'ana dai ya dawo gida, kowannen su daga cikin motar sai jifar d'an uwan sa yake da wani irin kallo sun shafe kusan minti biyu sannan Bassam yaja motar sa da k'arfi ya wuce. Sai da ya hau titi sosai ya kira Jabir cikin muryar tashin hankali yace
"Jay na samu wata envelope da written note a ciki a gidan Alhaji Bala it explains everything about this case but unfortunately mun had'e dashi lokacin da nike fitowa daga gidan kuma me gadin gidan ya ganni da envelope d'in I'm sure he's gonna tell him" da sauri Jabir yace
"But note d'in yana hannun ka?"
"Yeah" Bassam ya amsa masa duk a firgice yake
"Me note d'in yake cewa?" cewar Jabir, cikin tashin hankali Bassam yace
"There's no time for explanation Jay, my life is in danger anytime from now they can attack me but do you know any Cybercriminal, Cyberbully, Cybercop or any computer wizard? Wanda yake very good at internet the son of a bitch is gonna pay" mamaki ya kama Jay yace
"Me kuma ya kawo Cybercriminal a cikin wannan case?" da sauri Bassam yace
"Idan ka sani ka gayamin a inda zan same shi kawai I'm running out of time, my life is in danger" da sauri Jay yace
"Keep calm dude! Kazo chamber right now" tsawa ya dakawa Jay yace
"Don't bullshit me jay! Don't you get it? I told you my life is in danger!"
"Ba abunda zai faru In Shaa Allah Bassam, kawai kazo" cewar Jay in a calming voice, hankali a tashe Bassam ke gudu kan titin ya nufi chamber d'in kamar yadda Jabir yace.




*Readers hope baku manta da envelope da Mallam ya bawa me gadin sa ba yace idan Alhaji Bala yazo ya bashi a ranar da aka kashe A'ishah*






*Shawty*💕
[1/8, 7:18 PM] ‪+234 813 551 5123‬: *BARR. BASSAM*
(The Gallant) ❣





By *Shawty*💕


*2017*



_Assalamu alaikum. A sister talked to me about *JABIR(JAY)* in the novel, she said that he's a lawyer too why doesn't he come up with ideas since it's almost like they are doing a teamwork but it's just Bassam? I would like to post your question and my response here in case if there is anyone with the same thoughts as

Please Login or Register in order to submit comment