Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tabbacin gawar A'ishah ne ko kuwa, sulalewa tayi zuwa k'asa

"Innalillahi wa inna ilayhi raji'un" shine kawai abunda yake fitowa daga bakin ta, da k'yar ta samu ta fara jan k'afafun ta da rarrafe har ta isa bakin sofar da gawar A'ishah take a kwance, hannun ta dake kakkarwa tasa ta d'auke pillown da ya rufe fuskar A'ishah don ta tabbatar da zargin ta, zuciyar ta tayi popping da k'arfi taja baya idanun ta suka firfito jikin ta sai kakkarwa yake ba kama hannun yaro. A'ishah ta gani idanun ta a bud'e sun kafe wuri d'aya bakin ta ma a bud'e ga jini ya gangaro a gefen bakin a bushe sai lokacin ta lura sauran wuraren da jinin ya tab'a duk ya bushe alamar an dad'e da kisan. Hawaye ne suka shiga yi mata ambaliya hannu tasa akan wuk'ar da har yanzu take a jikin ta had'i da ciro ta da duk iyakar k'arfin ta, k'urawa wuk'ar ido tayi nan take kuma ta saki wuk'ar ta fad'i k'asa had'i da k'walla k'ara mai tsananin firgitarwa wacce har me gadi da yake a bakin gate sai da ya jiyo ta yayi daidai da shigowar Hajiya Zainab da Alhaji Bala cikin parlorn, wani rikitaccen ihu Hajiya Zainab ta fasa tayi kan gawar A'ishah. Alhaji Bala kuwa mutuwar tsaye yayi a wurin jikin sa sai rawa yake kamar me jin sanyi. Da gudu Hajiya Zainab ta isa kan gawar A'ishah ta fara jijjiga ta tana surutai
"A'ishah! Aishah!! Ki tashi! A'ishah?" kalmomin da take nanatawa kenan tana aikin jijjiga gawar A'ishah, da sauri ta kai kunnen ta akan k'irjin A'ishah, kururuwa mai k'arfi ta fasa ta juya tana kallon Alhaji Bala "Alhaji bata numfashi! Na shiga uku sun kashe min 'ya" sai kuma ta mik'e zumbur amma inaa wani haske taga ya rufe ganin ta a hankali har ya mamaye idanun ta sai gata ta fad'i k'asa rijif, k'ara tsorata Kausar tayi ta kurma ihu ta baza a guje ta fita parlorn, upstairs ta sauka da gudu har tana missing steps tana sauka ta nufi entrance door ta banka ta da duk iyakar k'arfin ta ta fito farfajiyar gidan, bata fasa gudun da take ba har ta iso bakin gate ta samu me gadi zaune yana alwala ganin da yai mata a wannan yanayin da bai tab'a ganin ta a ciki ba yasa ya dakatar da alwalar had'i da mik'ewa tsaye yace
"Kausar lafiya? Me yake faruwa? D'azu na jiyo wani ihu, lafiya kuwa?" lokaci d'aya ya jero mata tambayoyin, har tasa hannu zata bud'e gate d'in kuma sai ta juyo ta kallesa ta sake sa kai ta fice daga gidan "Anya kuwa lafiya yarinyar nan?" ya tambayi kansa, shuru yayi na wani lokaci a sanyaye ya koma ya zauna ya cigaba da alwalar da yake.




Gefen Alhaji Bala kuwa ko motsawa bai yi ba yana tsaye ne kamar gunki cikin rud'ani da tashin hankali mara misaltuwa ga Hajiya Zainab a kwance ta suma amma ya kasa tab'uka komai. Wayar sa dake a aljihun rigar sa ne ta fara ringing haka tayi ringing d'in har ta gama ko k'wak'k'waran motsi bai yi ba. Wani kiran ne ya sake shigowa shima dai har ya tsinke bai d'aga ba, wani kiran ne ya sake shigowa a karo na uku d'aya b'angare na zuciyar sa sai cewa yake ya d'aga sai a lokacin ya motsa jikin sa a sanyaye yasa hannu ya ciro wayar, number ce ba suna kamar kada ya d'aga kuma dai ya d'aga had'i da sanya wayar a kunnen sa, wata mahaukaciyar dariya yaji an fashe da had'i da cewa

"Wannan itace d'aukar fansa mafi sosa rai ga wanda aka yiwa" shuru Alhaji Bala yayi yana sauraren wannan abun al'ajabin yace
"Waye?"
"Hahahaha!" yaji an sake bushewa da dariya "Ashe har yanzu kai yaro ne Bala? Dama na gaya maka dole zaka bani jini naka ko na 'yar ka a tunanin ka alk'awalin da na d'auka na manta ne ko kuwa surutun fatar baki ne?" tuni jikin Alhaji Bala ya fara kakkarwa me tsanani cikin sark'ewar murya yace
"A.. Alhaji.. Kabara?" wata dariyar mugunta Alhaji Kabara ya tarwatse da had'i da cewa
"Tabbas tunanin ka bai gaya maka k'arya ba nine, nima haka na tsinci kaina ranar da ka raba ni da Juwairiyyah, ina fatar ka tanadi abunda zaka gayawa jama'a da kuma hukuma game da kisan A'ishah. Na barka lafiya" ya katse wayar, sulalewa wayar tayi daga hannun Alhaji Bala ta fad'i k'asa shima sulalewa yayi yabi wayar had'i da yin zaman dirshan a k'asan, zufa ta shiga keto masa ta ko ina.








*Tighten your belts, the war has just begun.*







*Shawty*💕
[1/8, 8:29 AM] ‪+234 813 551 5123‬: *BARR. BASSAM*
(The Gallant) ❣



By *Shawty*💕

*PURE MOMENT OF LIFE WRITERS*
(We don't just entertain and educate, we also touch the hearts of the readers.)


Zaku iya samun kowane Novel na PML through these links
#WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
#IG PML WRITERS
#https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
#http://maryamsbello.blogspot.com


_Let whoever think whatever just keep getting better please 'cause I don't think inside the box, I don't think outside the box and I don't even know where the goddamn box is_🤷‍♀


*2017*

2⃣0⃣

Haka ya zauna ya dinga sharb'ar kuka wane k'aramin yaro, kuka yake cike da k'unar zuciya da nadamar abunda ya aikata, ya dad'e a hakan daga k'arshe dai yaga kuka ba zai amfane sa da komai ba ya tashi jiki ba k'wari ya bud'e fridge ya d'auko goran ruwa ya zuba kan Hajiya Zainab. Bud'e ido ta fara yi a hankali har ta bud'e su gaba d'aya, idanun ta suka sauka kan Alhaji Bala juya su tayi zuwa gefen da gawar A'ishah ke kwance ta k'ura wa gawar ido sai ga wasu zafafan hawaye sun zubo mata, haka ta tashi taje wurin kujerar ta zauna had'i da d'ora kan gawar A'ishah akan cinyoyin ta ta cigaba da rusa kuka. Kuka suke ita da Alhaji Bala ba me lallashin wani suna a wannan yanayin ne suka ji kamar ana sallama a k'asa, Alhaji Bala ne yayi k'arfin hali ya fito daga d'akin, Goggo Hadiza ce ya hango k'asa sai faman rafka sallama take, a hankali ya fara saukowa daga upstairs d'in idanun shi sunyi jajir alamar yayi kuka. Cikin firgici Goggo Hadiza ta tare sa tana cewa
"Yaya lafiya?" sai a lokacin ya k'arisa shigowa cikin parlorn had'i da cewa
"Ba lafiya Hadiza"
"Me yake faruwa? Ina A'ishah?" d'ago idanun sa yayi cikin ido yace
"An kashe A'ishah" haka taji al'amarin yazo mata kamar almara
"Kamar ya an kashe A'ishah Yaya?"
"Muma bamu sani ba. Jiya da dare b'arayi sun shigo nan gidan da bindigogi suka yi barazanar hallaka ni idan ban basu kud'i ba na d'auko kud'i masu yawa na basu, bayan tafiyar su na fito naje d'akin Zainab don ganin lafiyar ta da yake ba a d'aki d'aya muka kwana ba na tarar ita bata ma san me yake faruwa ba, nayi yunk'urin zuwa naga A'ishah saboda firgici ya mantar dani a wurin ki ta kwana, Zainab ta tuna min ai A'ishah a gidan ki ta kwana sai Kausar kawai. Haka muka fito waje don ganin ina mai gadi yaje da har b'arayi suka shigo anan muka tarar dashi yana bacci bayan na tada shi ina sanar dashi abunda ya faru ne yake gayamin bai dad'e da kwanciya ba, haka muka dawo cikin sanyin jiki da gari ya fara haske ne muka je d'akin su A'ishah don ganin yaya Kausar ita kuma anan muka tarar da gawar A'ishah an kashe ta muka sa.... " bai k'arisa ba kuka yaci k'arfin sa, salati Goggo Hadiza ta shiga rafkawa tana kuka tana tafa hannu tace
"Ni kuma mun kwanta lafiya k'alau da ita sai neman ta nayi da asuba ban ganta ba, haka nai ta neman ta rariya-rariya a cikin gidan ba A'ishah ba dalilin ta har na fito tsakar gidan na tarar da motar ta alamar bada mota ta fita ba cikin daren na shiga kiran wayoyin ka duka basa zuwa na Zainab kuwa tana ringing ba'a d'agawa shine na yanke shawarar zuwa naga ko nan tazo ashe A'ishah ajali ne.... " cikin kuka Alhaji Bala yace
"Ni abunda yafi d'aure min kai shine na rasa dalilin dawowar A'ishah cikin daren"
"Ajali ne Yaya.. Yanzu ina Kausar?" shiru Alhaji Bala yayi sai kuma yace
"Bamu san ina taje ba, tunda muka ganta tare da gawar A'ishah lokacin ne ta fita a guje bamu san ina taje ba" shiru Goggo Hadiza tayi sa'annan Alhaji Bala yace "Ki hau sama Zainab tana ciki zanje in dawo" da sauri Goggo Hadiza tace
"Ina kuma zaka je Yaya?"
"Ba nesa zan je ba yanzu zan dawo" jinjina kai tayi alamar toh shi kuma ya kama hanyar fita parlorn, kallon sa Goggo Hadiza keyi har ya fice parlorn sa'annan ta juya jiki a sanyaye ta hau sama.



Fitar sa parlorn ne ya fiddo wayar sa ya fara neman layukan Mallam wanda dukan su kashe, da sauri ya k'arisa parking lot yayi daidai da isowar mai gadi wurin kallon fuskar Alhaji Bala yayi wanda yayi matuk'ar basa tsoro yace
"Alhaji lafiya kuwa?" lafiyayyen kallo Alhaji Bala ya bisa dashi sa'annan yace
"Jeka ka bud'en gate" da gudu me gadin ya kama ya nufi gate d'in had'i da wangale sa, da gudu Alhaji Bala ya fisgi motar saura k'iris ya hau kan me gadin sai da yazo daf dashi yace "Keep a close eye kada ka bar kowa ya shigo gidan nan" kuka me gadin ya fashe dashi yace
"Dan Allah Alhaji ku sanar dani abunda yake faruwa mana" kallon sa Alhaji Bala yayi cikin ido na tsawon mintuka sa'annan yace
"Ba lafiya, an kashe A'ishah" mutuwar tsaye me gadin yayi a wurin ya wangale baki da hanci yayin da Alhaji Bala yaja motar a guje ya barsa tsaye sororo a wurin.




Gudu yake a titin k'wak'walwar sa ta cunkushe da tunani barkatai haka motar ta fara tangal-tangal wane mashayi ne ke driving da k'yar ya iso bakin gate d'in gidan malam ya danna horn, da sauri me gadin yazo ya bud'e gate d'in yayin da Alhaji Bala ya fisgi motar ya kutsa kai cikin gidan yaja ya tsaya ya fara k'ok'arin fitowa daga motar yayin da me gadin ya k'ariso had'i da cewa
"Sannu da zuwa Alhaji" fitowa yayi daga cikin motar bai tsaya ta kansa ba ya nufi cikin gidan, bin sa me gadin yayi a baya had'i da cewa "Alhaji baya nan fa" juyowa Alhaji Bala yayi da k'arfi had'i da nuna k'asa da yatsan sa yace
"Kana nufin Mallam baya cikin gidan nan?"
"Baya nan Alhaji" cikin tashin hankali Alhaji Bala yace
"Ina yaje?"
"Ban sani ba amma ya bani wannan yace idan kazo na baka" ya zura hannu cikin aljihu ya ciro envelope ya mik'a masa, da sauri Alhaji Bala ya fisge envelope d'in ya farka ta had'i da fiddo wata takarda daga ciki, da sauri ya bud'e takardar wacce ke k'unshe da rubutu mai d'an tsayi ya fara karantawa. Da sauri-sauri yake karantawa a lokaci d'aya kuma zufa ke tsatstsafowa daga kowane sassan jikin sa, zamewa yayi kan gwiwoyin sa ya durk'ushe a wurin yana wani azababben kuka wanda ko lokacin da yayi ido hud'u da gawar A'ishah bai yi irin sa ba.





C *It'z Shawty*💕
[1/8, 8:53 AM] ‪+234 813 551 5123‬: *BARR. BASSAM*
(The Gallant) ❣



By *Shawty*💕


*PURE MOMENT OF LIFE WRITERS*
(We don't just entertain and educate, we also touch the hearts of the readers.)


Zaku iya samun kowane Novel na PML through these links
#WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
#IG PML WRITERS
#https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
#http://maryamsbello.blogspot.com


*2017*

2⃣1⃣


_*Shawty* is only angry when *Shawty* is hungry. 😁So, if you have a problem with *Shawty* you should get over it yourself 'cause *Shawty* don't give a damn_✌🏻


___________________________________

Kuka yake cike da bak'in ciki da k'uncin zuciya me gadin kwa sai faman tambayar sa yake yi amma ko jin sa baya yi, mik'ewa yayi ya shiga motar yaja a guje ya fita daga gidan.


Tuk'i yake amma sam hankalin sa baya jikin sa wayar sa ya d'auko yayi danne-danne sai kuma yasa a kunne, ringing biyu a na uku aka d'aga cikin rawar murya yace
"Alhaji Kabeer kana gida?"
"Eh" aka amsa daga d'aya b'angaren
"Ok gani nan zuwa"
"Lafiya kuwa Alhaj..." kit Alhaji Bala ya katse kiran ya ajiye wayar ya cigaba da tuk'in sa cikin matsanancin gudu har ya iso bakin gate na wani tangamemen gida. Horn ya dinga dannawa kamar ba gobe ba shiri me gadin wannan gida ya tsinko a guje ya bud'e masa gate d'in a sukwane yaja motar nan ma saura k'iris ya hau kan me gadin ya kutsa kai cikin gidan yayi daidai da fitowar wani mutum gajere bak'i k'irin cikin jalabiya ta maza ya k'ariso wurin motar Alhaji Bala ya taimaka masa ya fito daga motar ya fara jero masa tambayoyi
"Alhaji Bala lafiya? Me yake faruwa ne da sassafe haka? Ya naga ka fita daga hayyacin ka?" kamar wanda ya gama gasar tsere sai numfashi yake mayarwa yace
"Ba lafiya Kabeer, an kashe A'ishah, asiri na yana gab da tonuwa"
"Ban fahimce ka ba su waye suka kashe A'ishah?" hannu ya zura aljihu ya fito da wannan takardar da me gadin gidan Mallam ya basa ya mik'awa Alhaji Kabeer ya shiga koro masa labarin abunda ke faruwa daga farko har k'arshe, Alhaji Kabeer wanda ya gama karance takardar tsaf sai kallon Alhaji Bala yake yana jinjina girman wannan tashin hankali yayi gyaran murya ya dafa kafad'ar Alhaji Bala yace
"Keep calm"
"Shine matsalar" Alhaji Bala ya fad'a had'i da ture hannun Alhaji Kabeer daga wuyan sa "I'm all out of calm, ka gayamin meye mafita" shuru suka yi dukan su na tsawon mintuka sa'annan Alhaji Kabeer yace
"Kayi diverting hankali da tunanin mutane daga ainihin musabbabin mutuwar A'ishah zuwa wani b'angare daban, a hankali sai ka biyo baya kana tufke warwarar da Alhaji Kabara yai maka" cikin rawar jiki Alhaji Bala yace
"Kamar ya kenan? Ban fahimce ka ba"
"Shiyasa nace ka ajiye hankalin ka a gu d'aya wannan abu ne na taka tsan-tsan" fara tattara hankalin sa da nutsuwar sa yayi zuwa ga Alhaji Kabeer yace
"Ina ji"
"Yauwa.. Abunda zaka yi shine ka juya akalar kisan A'ishah zuwa kan wannan yarinyar da kake bani labari ma'ana ka nuna wa jami'an tsaro ita ce prime suspect a wurin ka" cikin d'aurewar kai Alhaji Bala yace
"Ban fahimce ka ba" murmushi Alhaji Kabeer yayi yace
"Ka fahimce ni Bala, ko zaka fito ka gayawa duniya cewar Alhaji Kabara shine yayi jagora a mutuwar A'ishah a dalilin d'aukar fansar kisan tasa 'yar da kayi?" girgiza kai Alhaji Bala ya shiga yi yace
"Ko kad'an ba zan fara wannan rashin hankalin ba"
"Toh ka gani? Abunda nake so ka fahimta kenan, juya akalar kisan A'ishah zuwa kan wannan yarinyar shi kad'ai ne mafita idan kuma kana da wata mafitar gayamin inji" iska Alhaji Bala ya furzar daga bakin sa yace
"Amma ta yaya zan juya akalar kisan a kan ta bayan na sani sarai ba itace tayi kisan ba? Plus bani da k'wak'wk'waran shaidar da zan gabatar wa jami'an tsaro wanda zasu yi daidai da nuna ita ce tayi kisan" kallon sa Alhaji Kabeer yayi cikin ido yace
"Kana da shaidu Bala"
"Ehenn ina jin ka"
"Kana da kud'i iyayen ta talakawa ne. Kana da girma da haiba a cikin mutane iyayen ta mak'ask'anta ne wannan kad'ai ya isa ya zame maka shaida" shuru Alhaji Bala yayi yana nazarin maganar. Dafa kafad'ar sa Alhaji Kabeer yayi yace "Baya ga haka kun same ta akan gawar A'ishah rik'e da wuk'ar da aka kashe ta wannan ma ya isa shaida, bayan shigowar ku d'akin ta fita gidan a guje wanda ku kanku baku san ina taje ba, me ya sanya ta guduwa idan har tana da gaskiya? Kaga wannan ma shaida ce. Meyasa b'arayin basu yi yunk'urin tab'a kowa a gidan ba sai ita? Shima abun dubawa ne" shuru ne ya biyo baya kowanen su ya tsunduma duniyar tunani sa'annan Alhaji Kabeer ya cigaba "Ina tabbatar maka wannan ita ce kad'ai mafita a yanzu" wani gwauron numfashi Alhaji Bala ya saukar yace
"Amma na rasa dalilin dawowar A'ishah cikin daren"
"Wannan ba abun damuwa bane, mutum d'aya ne yasan dalilin dawowar ta a wannan lokacin"
"Waye?" Alhaji Bala yace da sauri
"Aishah!" Alhaji Kabeer ya fad'a yana murmushi yace "Itace kad'ai tasan dalilin dawowar ta a lokacin kuma ta mutu so, me yayi saura?" shuru Alhaji Bala yayi ba abunda yake sai nazarin maganganun Alhaji Kabeer "Ka kira 'yan sandan ka sanar dasu abunda yake faruwa kuma kayi amfani da kud'i ka rufe musu baki a lokaci d'aya ina mai tabbatar maka ba abunda zai faru" hannu Alhaji Bala ya zura aljihu ya fiddo wayar sa ya fara danne-danne, da sauri Alhaji Kabeer ya dakatar dashi yace "Me zaka yi?"
"Zan kira 'yan sandan ne" murmushi Alhaji Kabeer yayi yace
"Ka nutsu Bala kada mutuwar A'ishah ta nemi zauta ka, ba zaka kira 'yan sandan a nan ba idan suka riga ka isa gidan fa? Wani zargin zai iya shigowa ka bari sai ka isa gida tukunna" jinjina kai Alhaji Bala yayi had'i da juyawa zai shiga motar, rik'o hannun sa Alhaji Kabeer yayi yace "Allah ya ji k'an A'ishah" a sanyaye Alhaji Bala ya amsa da
"Ameen" sai kuma hawaye suka zubo masa, bubbuga kafad'ar sa Alhaji Kabeer yayi yace
"Kayi hak'uri Bala, idan akayi nasara shikenan" da sauri Alhaji Bala ya juyo yace

"Ba shikenan ba Kabeer"
"Me kuma yayi saura?" Alhaji Kabeer ya tambaya cike da mamaki
"Kana nufin shikenan Kabara yaci bulus kenan?" wani murmushin mugunta Alhaji Bala yayi yace "Ya kashe A'ishah kuma A'ishah ce zata yi ajalin sa shima" cikin tsintsar mamaki Alhaji Kabeer yace
"Wacce A'ishar kuma? Me zaka yi?" har yanzu murmushin Alhaji Bala keyi yace
"Kar ka damu ba yanzu ba sai na kammala da wannan case d'in" wani gwauron numfashi Alhaji Kabeer ya saukar yace
"Toh Allah ya bada sa'a try to look as normal as you can, don't make anyone suspicious" jinjina kai Alhaji Bala yayi ya shiga motar sa yaja yayin da me gadi ya bud'e masa gate d'in yaja ya fice daga gidan.

Tafe yake yana matsar kwalla yana tuna lokacin ganin sa na k'arshe da A'ishah lokacin da yake gaya mata ta shirya taje gidan Hadiza, wani kuka ya fashe dashi da haka har ya iso gida. Bakin gate ya tsaya ya fara danna horn yayin da me gadin yazo ya lek'o ganin motar Alhaji Bala ne ya sanya sa wangale gate d'in yayin da Alhaji Bala yaja motar ya shiga cikin gidan, shigar sa yaja ya tsaya had'i da yafuto me gadin da hannu da sauri yazo ya d'an rusuna
"Ina fatar ba wanda ya shigo" cewar Alhaji Bala
"Ba kowa Alhaji"
"Good" Alhaji Bala ya fad'a yaja motar yayi parking d'inta a parking lot sa'annan ya fito ya nufi cikin gidan.






*Shawty*💕
[1/8, 9:25 AM] ‪+234 813 551 5123‬: *BARR. BASSAM*
(The Gallant) ❣





By *Shawty*💕

*PURE MOMENT OF LIFE WRITERS*
(We don't just entertain and educate, we also touch the hearts of the readers.)


*2017*

2⃣2⃣

Shigar sa parlorn bai samu kowa ba wanda ya tabbatar masa suna a sama tare da gawar A'ishah, straight saman ya nufa ya tura k'ofa ya shiga, Hajiya Zainab ce tare da Goggo Hadiza sun saka gawar A'ishah a gaba ba abunda suke sai rusa kuka a sanyaye ya shiga d'akin yayi gyaran murya lokaci d'aya suka d'ago rinannun idanun su musamman ma Hajiya Zainab suka kalli Alhaji Bala, cikin sanyin murya yace

"Kukan ya isa haka" kallon sa Hajiya Zainab ta k'ara yi cikin disashshiyar murya tace
"Alhaji ya maganar kawar da ita?"
"Ba maganar kawar da ita Zainab har sai 'yan sanda sun zo" shiru Hajiya Zainab tayi bata ce komai ba tana ta aikin kallon gawar A'ishah tana matsar kwalla sa'annan yace "Ko kinfi so rayuwar A'ishah ta tafi a banza ba tare da an hukunta wanda ya kashe ta ba?" girgiza kai tayi tasa hannu ta toshe bakin ta wanda wani kukan ne ke neman kufce mata, hannu ya zura aljihu ya d'auko wayar sa ya shiga neman layin comissioner of police anan yake shaida masa abunda yake faruwa, ya tausaya masa sosai had'i da jajanta masa ya kuma yi masa alk'awarin cikin mintuna kad'an jami'an tsaro zasu iso gidan, godiya Alhaji Bala yai masa sa'annan ya katse kiran.


A dole ya sako Hajiya Zainab da Hadiza a gaba suka sauko downstairs suka yi zaune jigum-jigum anan ne ya d'auki waya ya fara sanar da mutane abunda yake faruwa, ba kad'an ba mutuwar A'ishah ke girgiza duk wanda labarin ta ya riske shi suna a wannan yanayin ne suka jiyo siren wailing na motar 'yan sanda, da sauri ya mik'e ya fita parlorn zuwa farfajiyar gidan. A k'ofar gida suka yi parking suka shigo su uku, biyu maza d'aya mace k'arasowa suka yi har wurin da Alhaji Bala ke tsaye suka yi musabaha sa'annan wanda yake tunanin shine babban su yace

"Suna na Inspector Ibrahim Wada" had'i da fiddo I.D card ya nuna masa sa'annan ya juya kad'an ya kalli sauran yace "Tare da abokan aiki na guda biyu" jinjina kai Alhaji Bala yai baice uffan ba sa'annan Inspector ya cigaba "Ba sai an gaya min ba na tabbatar kaine Alhaji Bala wanda ka kira kayi report game da kisan 'yar ka wacce kuma baku san dalili ba kun kawai tashi da safe ne kuka tarar da gawar ta" jinjina kai Alhaji Bala yayi yace
"K'warai haka ne"
"Bismillah mu shiga ciki" cewar Inspector, jagora Alhaji Bala yai musu yana gaba suna biye dashi har cikin parlorn gidan anan suka tarar da Hajiya Zainab da Goggo Hadiza zaune suna ta rusa kuka, shigowar 'yan sandan ne yasa suka tsakaita kukan sukai musu jaje akan abunda ya faru cike da alhini sa'annan yace ai masa jagora zuwa wurin gawar, nan ma Alhaji Bala ne a gaba yayin da sauran 'yan sandan da Hajiya Zainab da Goggo suka rufa masa baya har zuwa cikin d'akin.


Cirko-cirko suka tsaya suna k'arewa gawar kallo anan ne Alhaji Bala ya fara koro masa labarin da ya sani daga farko har k'arshe tun da ya fara Inspector ke ta gyad'a kai har ya kai aya sa'annan yaja numfashi me nauyi yace

"Ina wannan yarinyar da kake magana?"
"Bamu sani ba muma tun da muka same ta kan gawar a lokacin ne ta fita a guje bamu san ina taje ba" gyad'a kai Inspector yayi ya bawa yaran sa umarnin d'aukan hotunan gawar sa'annan yasa suka d'auki wuk'ar da akayi kisan had'i rufe ta da handkerchief a daidai lokacin ne Inspector ya hango wayoyin A'ishah guda biyu a k'ark'ashin ta, takawa yayi had'i da jawo wayoyin IPhone7 jet black ce sai d'ayar Samsung Galaxy J7, k'okarin bud'e IPhone d'in yayi amma ba dama don tayi securing nata da password komawa yayi kan Samsung d'in luckily ita ba password, straight wurin call log ya nufa wanda ya nuna k'arshen kiran da tayi k'arfe

Please Login or Register in order to submit comment