Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

BASSAM*
(The Gallant) ❣




By *Shawty*💕


*2017*

0⃣3⃣

Fitowar sa ke da wuya ya nufi parking lot wanda motoci ne birjik a wurin kamar wurin sayar da motoci, wata latest Ford 2017 ya bud'e ya shiga ya tada yayin da mai gadi ya wangale masa gate had'i da yi masa Allah ya kiyaye.


Tuƙi yake amma sam hankalin sa baya jikin sa sauri kawai yake ya isa. Sabuwar unguwa ce ba yawan mutane, titi ya saki ya nufi wani katafaren gida, daidai bakin gate ya tsaya ya danna horn yayin da mai gadi ya rugo ya bud'e gate d'in, tuni ya fisgi motar ya kutsa kai a cikin gidan.


Shigar sa keda wuya ya nemi wuri yayi parking da hanzari ya bud'e motar ya fito mai gadin sai faman kwasar gaisuwa yake amma ina sam bai ji ba, ƙofar parlorn gidan ya nufa ya tura ya shiga ya bar mai gadin tsaye cike da mamaki don kuwa yasan yau akwai wani abu me girma da yake damun Alhaji Bala.


Tura ƙofar yayi ya shiga, wani dattijo d'an kimanin shekaru saba'in da biyar ne zaune kan wata darduma cikin shiga ta 'yar ciki da wando da hula wanda suka chanza launi daga fari zuwa yalo-yalo alamar datti, gaban sa kuma ƙasa ce aka tara, gefe daya kuma wata 'yar ƙwarya ce ƙarama da wani baƙin ruwa a ciki da kaga mutumen zaka tabbatar malamin tsibbu ne.


Miƙewa yayi tsaye ya fara dogarowa da sandar sa yayin da Alhaji Bala ke ƙarasowa cikin parlorn, musabaha suka yi sa'annan ya koma kan dardumar sa ya zauna. Shima Alhaji Bala wuri ya samu ya zauna yana fuskantar malamin. Shiru suka yi gaba daya a ƙalla kusan minti goma, Alhaji Bala ne ya katse shirun gami da cewa
"Me ya faru ne? Ka kira ni kuma kayi shiru" malamin wanda tun da ya zauna kansa a ƙasa sai rubutu yake akan ƙasar da ke gaban sa yana shafewa, sai da aka shafe wasu mintuka biyar sa'annan ya d'ago kansa ya ƙurawa Alhaji Bala ido yace
"Ka ƙagara kaji ko?" gyad'a kai kawai Alhaji Bala yayi sakamakon sanyi ƙalau da jikin sa yayi. Dogon numfashi malamin yaja sa'annan ya cigaba da magana "Tabbas hukumar EFCC zata fara bincike akan dukiyar ka" shiru Alhaji Bala yayi ya tattara dukkan hankalin sa wuri d'aya yana sauraren malamin "Na sha gaya maka Bala wannan dukiyar da kake neman tarawa ta fara zarta tunani ya dace ka saita ta amma kayi kunnen uwar shegu dani, bayan wannan ban hango komai a wannan binciken ba sai tonon asiri da wulaƙanci a gareka wanda zai iya kawo ƙarshen rayukan mu baki d'aya" kallon sa Alhaji Bala keyi cike da firgici da tsintsar tashin hankali jin kalaman da ke fitowa daga bakin malamin don kuwa ya tabbata malamin bai taɓa hasashe ya zama ƙarya ba, shiru suka yi dukansu zuwa wani lokaci Alhaji Bala ya numfasa gami da cewa
"Yanzu menene mafita?"
"Toh! Mafita d'aya ce tak shine zaka kashe bakin su da jinin yarinya matashiya 'yar kimanin shekara ashirin ko sama da haka" wani gwauron numfashi Alhaji Bala ya saukar yace
"Wannan mai sauƙi ne"
"Baya da sauƙi Bala" cewar malamin, da sauri Alhaji Bala ya kalli malamin cike da san jin ƙarin bayani yace
"Kamar ya bayada sauƙi Mallam? Wannan fa abunda muka saba yi ne"
"Wannan karon ina shawartar ka Bala da kada ka sanya yaran ka kaje da kanka wurin farautar wannan yarinyar don gudun samun matsala" cikin d'aurewar kai Alhaji Bala yace
"Kamar ya samun matsala? Wacce irin matsala? Kuma saboda me?" kallon sa kawai malamin keyi yace
"Bani da tabbacin za'a samu matsala amma shawara ce nike baka" shiru suka yi suna kallon juna kowa da kalar tunanin da yake yayin da Alhaji Bala yace
"Toh wacece wannan yarinyar?"
"Koma wacece matuƙar ba zata kasa shekara ashirin ko fiye da hakan ba" dariyar rainin hankali Alhaji Bala yayi had'i da shafa gefen fuskar sa yace
"Meyasa sai ni zanje farautar ta?"
"Kar kayi wasa Bala, ina hango wulaƙanci da tozarta garemu ka nutsu wannan aikin ba kamar sauran ayyukan da muka saba bane idan ma kana tsoro ne to tun wuri ka kawar da wannan tunanin a ranka" wannan karon dariya sosai Alhaji Bala keyi yace
"Tsoro kuma Mallam? Sanin kanka ne na dad'e da yin hannun riga da tsoro, ko ka manta dazukan da na ratsa, maƙabartun da na shiga, nayi zina da gawa, rayukan da na kashe da hannu na da wankan da nayi akan ƙaburbura wanda basu da adadi duk kafin na tara wannan dukiyar ko ka manta ne? Bana tunanin me wannan aikin za'a kira sa da matsoraci" murmushi kawai malamin yayi yace
"To meyasa ba zaka aiwatar da abunda yake tsira a wurin mu baki d'aya ba?"
"Yaushe ake da buƙatar yarinyar?"
"Gobe ne Bala, ɓata lokaci ba al'adar mu bane da zafi-zafi ake dukan ƙarfe"
"Gobe ina da tafiyar gaggawa, zan halarci meeting Abuja"
"Ka fasa" cewar malamin a taƙaice, kallon sa Alhaji Bala keyi cikin rashin fahimta da mamaki yace
"Ya zama dole na halarci wannan taron Mallam"
"Saboda me?" cewar malamin
"Na gaya maka ina neman a tsayar dani takarar Governor a wannan jihar rashin zuwa na wannan taron zai iya jawo min gagarumar matsala a siyasar da nike so in shiga" shiru ya ziyarce su na mintuka sa'annan Mallam yaja dogon numfashi yace
"Toh! Ka kira yaran naka ka sanar dasu don kuwa gobe ake da buƙatar yarinyar"
"An gama" cewar Alhaji Bala, hannun sa yasa cikin aljihun rigar sa ya fiddo waya ya fara danne-danne sa'annan yasa a kunne, ringing d'aya a na biyu aka d'aga
"Alaji da matsala ne?" wata muryar namiji kamar hadari ya taso ne tayi magana
"Kai ji nan d'an iska kaima kasan bana neman ka sai da matsala" wata mahaukaciyar dariya aka kece daga d'aya ɓangaren gami da cewa
"To ya akayi ne Alaji?"
"Yauwa! Yarinya matashiya 'yar kimanin shekara ashirin da biyar ko fiye da haka akeso zaka kawowa Mallam gobe a d'aya gidan sa dake new site"
"An gama Alaji"
"Good, ka kula kada a samu matsala fa"
"Haba Alaji! Baka da matsala ai"
"Yauwa! Idan komai ya daidaita ka kira ni zaka ji kudin ka" wata mahaukaciyar dariya ya sake fashewa had'i da cewa
"An gama Alaji" katse kiran Alhaji Bala yayi ya kalli malamin yace
"T.K baya da matsala zai yi aikin nan yadda akeso, gobe zai kawo maka" jinjina kai kawai malamin yayi baice dashi uffan ba. Miƙewa Alhaji Bala yayi shima malamin ya miƙe suka ƙara musabaha "Kayi iyakar ƙoƙarin ka Mallam" cewar Alhaji Bala, jinjina kai kawai malamin ya sake yi a sanyaye Alhaji Bala yace "Na barka lafiya" ya juya ya nufi hanyar fita parlorn yayin da malamin ya bishi da idanu kawai yana jinjina girman al'amarin a ransa.



_Years passed by_
Shekaru da yawa sun shud'e abubuwa da yawa kuma sun faru ciki kuwa har da samun nasarar Alhaji Bala akan hukumar EFCC da zasu yi bincike akan dukiyar sa.


Hajiya Zainab ma ta haihu ta samu 'ya mace mai suna A'ishah wacce yanzu haka ta girma tana ajin ƙarshe a Secondary School.


A'ishah me irin ji da kan tsiyar nan ne da taƙama, bata cika nutsuwa ba, nuna isa da bragging mahaifin ta mai kudi ne. Sam karatu baya gaban ta duk kuwa da cewa mahaifin ta yana kashe maƙudan kudi a karatu da jin dad'in ta amma A'ishah kam bata ma san me akeyi ba, idan dai tana gida to aikin ta chart ne, bacci, kallon series ko kuma sauraren beats. Idan kuma bata nan to tabbas ta fita party ne.


Hajiya Zainab tana iyakacin ƙoƙarin ta akan daidaita tarbiyyar A'ishah amma abun ya faskara saboda da hannun Alhaji Bala a gurɓatar tarbiyyar ta coz abunda take so shi ake yi shiyasa wani lokacin take zuba musu ido.


A yayin da Kausar 'yar Hajara me aiki itama ta girma sosai, ganin tasowar Kausar ne yasa Hajara tace zata daina aiki tunda ga Kausar ba abunda ba zata iya taya Hajiya Zainab ba ta fannin aikace-aikace, dama Hajiya Zainab sam ba a matsayin 'yar aiki take kallon Hajara da 'yar ta Kausar ba wannan dalilin yasa ta roƙi arziki abar Kausar a hannun ta saboda ita kam ta yaba da hankali da kuma natsuwar yarinyar, baya ga haka ga A'ishah sun shaƙu sosai da Kausar. Ba tare da nuna damuwa ba Hajara ta amince dan kuwa ba abunda Hajiya Zainab zata nema a wurinsu su kasa yi mata. Haka kuwa akayi Kausar ta dawo gidan Alhaji Bala harta makaranta iri d'aya suke zuwa da A'ishah.


Hajiya Zainab bata fifita A'ishah akan Kausar ba ta kowane fanni, duk abunda zatay wa A'ishah shi zatay wa Kausar kamar ita ta haife su.


Ta ɓangaren yaran ma ba wata matsala haka suke zaune ba wani hayaniya dalili kuwa tun suna ƙanana suke tare. Duk da cewa Kausar ta girmi A'ishah da shekara d'aya wannan ba shi yayi determining girman su ba sai dai halayyar su da suka bambanta don kuwa Kausar complete opposite na A'ishah ce. Tana da kyau sosai don kwa tayi wa A'ishah fintinkau ta kowane gefe, shiru-shiru ce unlike A'ishah wacce masifa ke tsunkulin ta duk da zaman ta da A'ishah ba shi yasa ta koyi hayaniya da halin ta ba, duk fad'in school nasu ƙawar ta daya ce wato Ameerah idan kaga tana raha da dariya to ita da Ameerah ne sam bata alaƙanta kanta da 'ya'yan masu kud'i don fa tasan su talakawa ne dalili ne ya kawo ta gidan su A'ishah kuma tasan wata rana zata barshi don haka ne bata shagala ba ta manta da asalin ta. Ta ɓangaren A'ishah kuwa is a different story saboda gaba d'aya school d'in ba wanda baisan A'ishah Bala ba, uban tara ƙawaye da abokanai ne da ita har da na banza, idan ke ba 'yar me kudi bace to dama ba kwa tare shiyasa wanda suka san asalin Kausar suke mamakin zaman su tare.


Ɓangaren karatun islamiya ma suna yi, Hajiya Zainab da kanta ta samo mai koyar dasu. Sosai Kausar ke maida hankali a karatun cikin lokaci kad'an kuma ta sauka yayin da A'ishah abun ba damunta yayi ba, once za'a ce malamin yazo to zata yi faking rashin lafiya ko bacci kenan har ya tafi.


Jarabawar su ta SSCE sai ƙara matsowa take, Kausar ta duƙufa wurin karatu don taga ta fita kunyar Hajiya Zainab wacce bata taɓa gajiyawa ba wurin yi mata hidima kamar 'yar da ta haifa da kuma mahaifanta wanda kullum fad'an su kenan wa Kausar akan ta tsaya ta maida hankali tayi karatu kar tayi wasa da damar da ta samu domin burin su a kullum shine Kausar ta samu nagartaccen ilimi. Yayin da mutuniyar kam chilling and partying like never before ba abunda ya chanza.


*****


_*Dear readers, from page 01 to this page I was just trynna give ya a clue or lemme say a hint about the story just to make things cleared. Sorry for the interruption. Now it starts*_▶


Me gadi ne ya shararo a guje ya wangale gate d'in gidan sakamakon horn da ake dannawa ba kama hannun yaro ko waye yana cikin rashin haƙuri da sauri, a masifance wata mota ƙirar Lexus baƙa sabuwa dal sai sheƙi take ta danno kai cikin harabar gidan. Ba'a yi parking nata a wurin da aka tanada ba don parking motoci a tsakiyar harabar gidan akayi parking nata, tuni mai tuƙa motar ta fito ba kowa bace sai A'ishah cikin school uniform da alama dawowar ta kenan daga school, bata damu da maida murfin motar ta rufe ba sakamakon kukan da take ba ji ba gani wane an mata mutuwa haka ta sharara da gudu ta nufi cikin gidan. Ƙofar d'aya gefen driver ce ta sake budewa ba kowa bace sai Kausar itama cikin uniform wanda ya nuna tare suka dawo kenan, cikin natsuwa ta fito had'i da d'auko musu school bags dinsu wanda garin sauri A'ishah ta manta nata, tuni me gadin ya sake sharowa da gudu ya nufo ta yana washe haƙora gami da yi mata sannu da zuwa ya karɓi school bags d'in, murmushi Kausar tayi har haƙoran ta suka fito ta sakar masa school bags d'in gami da amsa gaisuwar tace
"Yauwa Dauda, Ya aiki?"
"Alhamdulillahi" ya fad'a yana ƙara washe haƙora sa'annan yace "Ya naga mutuniyar tana kuka lafiya kuwa?" gajeren murmushi Kausar tayi tace
"Lafiya ƙalau bata jin dad'i ne" cikin tausayi yace
"Ayyah! Allah ya sawaƙa" da
"Ameen" Kausar ta amsa had'i da yi masa nuni da motar da suka dawo ciki tace
"Kaga Dauda idan ka kai school bags d'in ciki ka mayar da motar a parking lot please" tayi nuni da wurin ajiye motocin sa'annan ta cigaba da cewa "Keys din suna a cikin motar" da
"Toh" me gadin ya amsa ya nufi cikin gidan itama ta rufa masa baya. Alhaji Bala da Hajiya Zainab ne a cikin parlorn sai A'ishah wacce ke jikin Alhaji Bala sai faman rusa kuka take, da sallama Kausar ta shigo parlorn fuskar ta sai murmushi take wanda ya zame mata al'ada cikin girmamawa ta rusuna ta gaida su, cike da fara'a suka amsa yayin da Alhaji Bala ya zarce da tambayar ta

"Kausar me ya samu A'ishah ne? Ta shigo tana kuka mun tambaye ta taƙi tayi magana" cikin sanyin murya Kausar tace
"Wallahi Daddy nima bansani ba tun a mota take kukan na tambaye ta taƙi ma ta saurare ni" d'agowa A'ishah tayi daga jikin Alhaji Bala idanun ta sunyi jajir yayin da Hajiya Zainab ta fara fad'a
"Kinga idan ba zakiyi magana ba kizo ki bar parlorn nan! Ya zaki zo kina rusa mana kuka ba dalili" da sauri Alhaji Bala ya dakatar da ita yace
"A'a Hajiya ya isa haka" ya juyo kan A'ishah "What is it? Tell me" cikin kuka A'ishah ta cire hannun ta wanda tun da ta shigo ba aikin da take sai murza idanun ta dashi, cikin muryar kuka tace
"Daddy ni a chanza min mota" da sauri Hajiya Zainab da Kausar suka kalle ta, cikin fad'a Hajiya Zainab ta daka mata tsawa tace
"Ke! Duka yaushe aka sayi motar ne? Not up to two weeks fa" wani kukan ta sake rushewa dashi ta koma jikin Daddy ta ƙanƙame shi, Kausar kam sai kallon ikon Allah take. Da sauri Alhaji Bala ya fara magana
"Zainab meye haka ne? Ki bar yarinyar nan tayi magana mana, kin san dalilin ta ne?" shiru Hajiya Zainab tayi ya juyo kan A'ishah yace "Me ya samu motar Mama na? Kin buga ta a bango ne?" girgiza kai tayi alamar a'a "To me ya same ta? Tashi kiyi magana" ya d'an riƙo hannun ta, tashi tayi zaune yayin da Hajiya Zainab sai wurga mata harara take tace
"Daddy school mates d'inmu suka fara competing dani, Kausar ai kinsan Al'ameen Dan Ƙasa ba?" jinjina kai Kausar tayi alamar eh sannan A'ishah ta cigaba da cewa "To Daddy shine fa aka sayawa Lexus shima, his friends are even laughing at me mockingly suke cewa how could I let him got so big in the school" sai kuma ta sake fashewa da kuka tace "Daddy ni ka chanza min I can't ride the same ride with him ko kuma na daina zuwa school ba zan yarda friends nawa su raina ni ba" da sauri Hajiya Zainab tace
"Ki daina d'in mana, wallahi Alhaji kai kake d'aurewa yarinyar nan gindi take kawo kowane rainin hankali taga dama, wannan ne dalili?.." da sauri A'ishah ta katse ta tace
"Wallahi Momy ba rainin hankali bane, I'm telling you guys the truth kuma ki tambaya Kausar kiji"
"Zaki rufe min baki ne ko kuwa? Dake nake magana ne?" cikin fushi yanzu Hajiya Zainab take magana, da sauri Alhaji Bala ya sako baki yace
"Ya isa haka Zainab" ya juyo kan A'ishah yace "It's alright Mama. Kinga yanzu zanyi tafiya zanje Abuja I'm here just waiting for your arrival muyi sallama kafin na wuce da yanzun nan sai muje ki d'auko wacce kike so" da sauri A'ishah ta kalle sa tace
"Daddy..." bai barta ta ƙarisa ba ya katse ta had'i da cewa
"Calm down! Akan mota ba za'a daina zuwa school ba, ki cigaba da hawa tawa wannan G4 Sedan d'in before then, idan na dawo sai muje tare ki d'auko wacce kike so ko?" ba kunya ta daka uban tsalle had'i da hugging nasa all at once kamar ba itace ke kuka ba ta manna masa peck a cheeks had'i da cewa
"Yesss! I'm proud of you Daddy" murmushi fal akan fuskar sa yace
"Anything for you Daddy's girl, haka yayi?"
"Yayi Daddy thank you so much"
"Always welcome Mama na" agogon hannun sa ya duba had'i da miƙewa tsaye yace "Barin zo in tafi" miƙewa itama A'ishah tayi tace
"To Daddy Lexus d'in a bawa Kausar ko?"
"An bata" ya fad'a yana murmushi, wani tsallen ta sake yi tace
"Yaaaaay mee! Mun gode Daddy" dariya kawai Kausar keyi itama tayi godiyar, murmushi yayi gami da cewa
"Bakomai Kausar kema ai 'ya ta ce" A'ishah kam murna ba'a cewa komai, Hajiya Zainab kallon su kawai take bata ce uffan ba, kallon su Alhaji Bala yayi yace
"Zan wuce" har suna had'a baki wurin cewa
"Allah ya kiyaye" ita da Kausar dukansu suka rankayo har Hajiya Zainab suka rako sa harabar gidan driver ya d'auke sa zuwa airport.






*Shawty*💕
[1/7, 5:53 PM] ‪+234 813 551 5123‬: *BARR. BASSAM*
(The Gallant) ❣




By *Shawty*💕


*2017*

0⃣4⃣

*Dundee, Scotland.*
Matashi ne d'an kimanin shekara ashirin da shida, dogo ne sosai ba fari bane tas haka kuma ba za'a saka shi a sahun baƙaƙe ba. Kakkaura ne ko ina jikin sa muscles ne. Kyakkyawa ne ajin ƙarshe though bayada hasken fata sosai amma zaka tabbatar akwai hutu da kwanciyar hankali a tattare dashi. Me doguwar fuska ne da dogon hanci had'i da manya-manyan idanu sai dai idanun koda yaushe a lumshe suke kamar mai jin bacci wanda suke ƙara masa kyau matuƙa sai d'an madaidaicin bakin sa wanda ba za'a kira sa da reddish ko pink ba sai dai peach. Gashin kansa da eyebrows d'insa baƙi ne wulik kwance a fatar sa gwanin sha'awa.


Cikin shigar black suit yake wacce ciki long sleeve ce fara da black necktie. Ƙafafunsa sanye suke da black socks a cikin black cover shoes, zaune yake kan couch system ce akan laps nashi yana aiki akai gefe daya kuma wayar sa ce latest IPhone7 jet black hannun sa d'aya riƙe yake da cup da coffee a ciki yana sipping at the same time hankalin sa na akan system d'in da alama abunda yake me matuƙar muhimmanci ne.


Wayar sa ce ta fara ruri alamar shigowar kira, ko motsawa beyi ba daga abunda yake bale ya juyo ya kalli wayar a haka ta gama ringing tayi shiru. Cigaba da ringing d'in wayar ne alamar shigowar wani kiran ne ya sanya shi dakatar da abunda yake don kuwa ba kadan ringing d'in yake distracting nashi ba. 'Yar tsuka yaja ya juyo had'i da miƙa hannun sa ya jawo wayar, ganin wanda yake kiran ne ya sanya shi ya fara blushing da sauri ya d'aga kiran a sanyaye ya fara magana yace
"Hello Mom" mamaki ne ya cika ni jin accent na turawa ras a bakin sa
"Hi dear" muryar wacce ya kira da Mom ce ta amsa da harshen turanci itama, a sanyaye ya cigaba da magana
"I wanted to call you last night but I've been very busy though..." bata bari ya ƙarisa ba ta katse shi gami da cewa
"I know Bassam, it's alright now whenever you're free give me a call ok?"
"Ok Mamma" ya amsa a sanyaye, da
"Ok" itama ta amsa suka yi sallama had'i da katse kiran, ciro wayar yayi daga kunnen sa ya ajiye ta ya cigaba da abunda yake, sai kuma yayi switching off system d'in ya fara had'a tarkacen gadgets nasa had'i da miƙewa tsaye. Tabbas dogo ne sosai cikakken namiji, duƙawa yayi kan couch da ya tashi yasa hannu ya d'auko sun glasses ya miƙe tsaye ya kafa glasses d'in a fuskar sa, ba kad'an ba yayi kyau a hankali ya juya ya fara tafiya zuwa ƙofar fita. Tafiya yake cike da isa da izza wanda ba zaka iya tantance isar ce da izza ko kuwa yanayin tafiyar sa ne a hakan har ya fice parlorn. He's *Barr. Bassam.*




*WAYE BARR. BASSAM?*
Cikakken sunan sa Muhammad Bassam Muhammad. Sunan mahaifin sa Justice Muhammad Umar, a yayin da sunan mahaifiyar sa Barr. Hindu Alhassan.


Mahaifin sa haifaffen jihar Sokoto ne anan yayi karatun sa na primary da secondary, bayan ya kammala ne ya samu gurbin karatu a Jami'ar Usmanu Danfodiyo University dake a jihar Sokoto a inda ya karanci fannin shari'a wato Law, bayan ya kammala ne yaje makarantar lauyoyi wato Nigerian Law School dake a Abuja. Bayan ya gama ne aka yi musu call to bar anan Abuja, anan Abujar ne kuma ya had'u da Hindu wacce itama 'yar asalin jihar Sokoto ce amma ba anan tayi nata karatun ba a haka soyayya me ƙarfi ta ƙullu tsakanin su har suka dawo gida da alk'awalin zasu yi aure.


Kafin suyi aure ne ya fara practice yayin da ita kuma Hindu sai bayan sun yi aure ta fara practice d'in. A haka suka cigaba da aikin su cike da kwanciyar hankali da soyayya har ya samu cigaba a aikin sa zuwa Supreme Court Abuja, wannan dalilin ne yasa suka tattara suka koma Abuja.


Ya taka matakai kala-kala tun daga lawyer har ya samu justice har Allah ya bashi Chief Justice na ƙasa baki d'aya yayin da ita kuma Hindu tana nan a matsayin ta na lawyer kuma tana practice itama.


Tun lokacin da suka haifi Bassam Allah bai ƙara basu haihuwa ba, yadda boko ya ratsa su hakan yasa ba wani damuwa suka yi ba sai ma ƙara godewa Allah suke yi a kullum samun Bassam a matsayin d'a d'aya tilo.


Bassam ya taso cike da gata da jin dad'i tare da iyayen sa, sun d'auki soyayya da buruka kala-kala sun d'aura akan sa. Haka Allah ya cigaba da raya Bassam har ya ƙare karatun sa na primary bai taɓa neman abu ya rasa ba gata da wadata ne zagaye dashi ta ko ina amma bai hana suka bashi tarbiya ingantacciya ba. Bayan ya gama karatun sa na primary ne ya fara secondary duk anan Abujar haka rayuwa ta cigaba da gudana wa Bassam tare da iyayen sa. Yana girma yana ƙara kyau sai dai miskili ne bayada hayaniya komai a nitse yake yin sa. Kamar yadda iyayen sa suke mafarkin ya kasance haka ta faru dan kuwa koda

Please Login or Register in order to submit comment