Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

chamber suka d'auki wannan note d'in sannan suka wuce kotun kai tsaye, duba agogon wayar sa Bassam yayi yaga it's almost eleven, da sauri ya kalli Jay yace
"Fast Jay!" k'arawa motar gudu Jay yayi cikin k'ank'anin lokaci suka iso kotun.







*Shawty*💕
[1/8, 7:50 PM] ‪+234 813 551 5123‬: *BARR. BASSAM*
(The Gallant) ❣





By *Shawty*💕


*2017*


4⃣8⃣


Koda suka shiga kotun already alk'ali ya gama sauraren Mammy ya duk'ar da kansa yana rubuce-rubuce ready to pass the judgment Bassam ya shigo, jin an turo k'ofa an shigo ne yaja hankalin jama'ar kotun kallon su ya koma a k'ofar, Bassam ne sanye da wig and gown fuskar sa jina-jina ba abunda yake sai hange-hange ta ina zai ga Mammyn sa don ya tabbata duk wanda zaiyi bak'in cikin b'atan sa to Mammy tana a kan gaba, exclamation da yayi yawa a kotun yake nema ya zama hayaniya ya jawo hankalin alk'ali da Mammy karaf idanun ta suka sauka akan Bassam, zumbur ta mik'e tsaye sai dai ta tuna a kotu take a sanyaye ta koma ta zauna idanun ta suka ciko da hawaye yadda taga fuskar sa duk jini. Gefen alk'alin kuwa dakatar da rubutun yayi don kuwa yasan da magana ganin da yai ma Bassam cikin wig and gown ya tabbatar masa shine lauyan wacce ake zargi wanda ya kasa bayyana a kotun sai yanzu kuma ga fuskar sa duk jini. Gefen uban tafiyar wato kam Alhaji Bala ganin Bassam da yayi yasa ya mik'e zumbur jikin sa ya fara rawa wane mazari, da sauri Alhaji Kabeer ya mayar dashi zaune don gudun kada jama'ar wurin su fahimci wani abu yayin da shima kansa jikin sa yayi sanyi sosai sakamakon ganin Bassam da suka yi a lokacin da basu tab'a tsammani ba. Jikin Alhaji Bala sai rawa yake ya kasa zaunawa da natsuwa sosai wanda har ya bawa Hajiya Zainab tsoro wacce take a gefen hagun sa, murya k'asa-k'asa tace
"Alhaji lafiya kuwa?" kallon ta yayi sai zufa ke keto masa ta ko ina muryar sa har tana rawa yace
"Lafiya k'alau" yayin da sai wani shu'umin kallo Bassam yake jifar sa dashi. Gefen Kausar kuwa ganin Bassam da tayi abu biyu ne ya faru da ita, na farko duk lokacin da zata yi arba da Bassam she'll feel protected like she's standing with an army of men all with weapons irin her mentor is here, na biyu raunukan da ta gani a fuskar sa ya bala'in tayar mata da hankali kenan sun sake attacking nasa sai dai addu'ar ta a lokacin Allah yasa Bassam yazo da shaidu masu k'wari. Gefen Amma da Abba ganin Bassam yasa suka saki hamdala da addu'ar Allah kuma ya kawo k'arshen wannan rikicin. Alk'ali yayi magana lokaci d'aya kotun tayi shiru tsit kamar ba d'an adam a wurin yana sauraren Bassam wanda har yanzu bai k'araso cikin kotun ba, a hankali ya tako har ya iso daidai wurin zaman sa yai wa Mammy murmushi yayin da ita kuwa Mammy hankalin ta yafi tafiya akan raunukan dake jikin sa. Gabatar da kansa yayi gaban alk'alin da neman afuwar kotu sakamakon rashin zuwan sa da wuri sakamakon attacking d'insa da akayi sai dai ya b'oye cewar Alhaji Bala ne, jinjina kai Alk'alin yayi alamar ya gamsu don kuwa fuskar sa ma shaida ce a hankali Bassam ya kalli alk'alin yace
"Nazo da k'wararan shaida ya mai girma mai shari'a" jinjina kai alk'alin yayi yace
"Kotu tana sauraren ka" daidai lokacin ne Alhaji Bala yaga fatalwar A'ishah a jikin bangon kamar anyi pasting d'inta sai dariya take iska na hura ta cikin muryar ta mai sauti da amo tace
"Daddy ka tashi ka fad'i gaskiya kasan ba Kausar ce ta kashe ni ba!" tuni jikin Alhaji Bala sai gaf-gaf-gaf-gaf yake, waige-waige ya shiga yi dama da hagun sa ya fahimci cewar shi kad'ai ne ke ganin fatalwar, nan take ta b'ace bokan ya bayyana yana me k'yalk'yala dariya, cikin tashin hankali mara misaltuwa Alhaji Bala ke kallon sa har yanzu jikin sa bai dakata daga rawar da yake ba, tarwatsewa bokan yayi da wata dariya wacce Alhaji Bala yaji kamar ana girgizar k'asa ne yayin da sauran mutanen dake kotun basu ma san me yake faruwa ba, cikin sautin dariya bokan yace
"Bala lokaci mai tsawo da ya shud'e, nine na gabatar da kai a tsafi, nine bokan da na fara girka ka a tsafi amma lokaci d'aya kayi watsi dani ka manta ni ka manta duk irin taimakon da nay maka lokacin da kake neman arziki ido rufe, ka chanza wasu malaman ka watsar dani sai yanzu da wata buk'atar ta taso kazo ka neme ni dama nasan wannan ranar zata zo. Tabbas na tayar maka da fatalwar A'ishah kuma hakika A'ishah ta kashe Kabara sai dai kaima itace ajalin ka saboda ba'a tab'a yaudara ta na yafe ba, bana yafiya kuma ban san ta ba" zufa ta shiga ketowa Alhaji Bala wanda ba shiri ya cire hular dake kansa ya shiga jijjiga rigar sa, Alhaji Kabeer ne ya lura da halin da yake ciki amma yasan dole ne koma wane irin hali Alhaji Bala ya shiga saboda yau asiri yana gab da tonuwa. Envelope da takardar Bassam ya d'auko ya rik'e a hannu yace
"Ba kowa bane ya kashe A'ishah sai mahaifin ta wato Alhaji Bala! Shine ya kashe A'ishah da hannun sa" kusan gaban kowa sai da ya fad'i a wurin tare da razana sakamakon jin kalaman Bassam in banda Alhaji Kabeer da Alhaji Bala wanda sai faman sharar zufa yake, kallon Alhaji Bala Hajiya Zainab tayi da sauri idanun ta suka firfito dalili kuwa jin abunda Bassam ya fad'a game da mijin ta wanda ta kasa yarda take tunanin kunnuwan ta ne basu ji da kyau ba, gyara zaman ta tayi ta cigaba da sauraren Bassam cikin d'aga murya yace "Wannan takardar itace shaida ta ta farko, na tsince ta ne a gidan Alhaji Bala" tuni hankalin kowa ya koma kan Bassam a hankali ya shiga warware takardar yace
"Ga abunda takardar ke cewa.."

_Bala sai dai kayi hakuri da abunda ka wayi gari yau dashi, na tabbata ka wayi gari kaga gawar 'yar ka A'ishah wacce ka kashe da hannun ka a bisa umarni na. Hak'ika ba kuskure ne aka samu ba, ba kuskure ne nayi ba ina sane na saka ka kashe 'yar ka da hannun ka. Bala ko zaka iya tuna lokacin da hukumar EFCC zata yi bincike a kanka nasa ka nemo yarinya matashiya 'yar kimanin shekara ashirin ko fiye? Allah yasa kuma zaka iya tuna lokacin da na sanar dakai cewar Kabara aboki na ne. Toh tun lokacin da muka kashe 'yar sa Juwairiyyah yake bibiyar mu ni dakai, kabi umarni na ka kashe 'yar ka A'ishah a rashin sani ni kuma ina kan umarnin Kabara ne. Yayi rantsuwa da ubangijin da ya halicce shi duk ban sanya ka ka kashe 'yar ka ba sai ya kawar dani kaf da zuriya ta a doron k'asa, banida zab'i don kuwa Kabara babban matsafi ne ni na girka sa a tsafi amma har yanzu da nike rubuta maka wannan wasik'ar ina mai tabbata maka Kabara yafi ni k'arfi a tsafi. Na jagorance ka ka kashe 'yar Kabara don rufe bakin hukumar EFCC da zata yi bincike akan dukiyar ka a rashin sani, shi kuma yayi amfani dani wurin kashe taka 'yar bisa d'aukar fansar rayuwar tasa 'yar, dukan ku na yaudare ku sai dai yaudarar ka da nayi tafi wacce nay wa Kabara sai dai hak'uri. Allah yaji k'an A'ishah._

Kowa ka gani a wurin baki hangame haka yake sauraren Bassam har ya kai aya, ba mutanen wurin ba kad'ai harta alk'alin sai da yayi mamakin duk girma da haibar da Alhaji Bala ke dashi a cikin al'umma ashe aika-aikar da yake aikatawa kenan, yayin da ita kuwa Hajiya Zainab daskarewa tayi a wurin ta kasa motsa koda yatsan ta ne ta k'urawa gefe d'aya ido ko kiftawa bata yi. Shi kuwa Alhaji Bala kwasawa yayi da gudu ya nufi hanyar fita kotun nan take 'yan sandan dake cikin kotun suka chafko sa suka mayar dashi, takawa Bassam yayi ya gabatar da takardar gaban alk'ali yayi bowing sannan ya dawo wurin da yake tsaye, yayin da shi kuwa Alhaji Bala k'ara ganin fatalwar A'ishah yayi a bangon kamar dai d'azu sai dai yanzu tana a cikin kayan da aka kashe ta da wuk'ar a cikin ta sai dariya take b'anb'alawa nan take Alhaji Bala yaji ya had'iye wani abu mai tsananin kauri da girma ta wuyan sa zuwa cikin sa, fashewa fatalwar ta sake yi da wata dariyar a lokaci d'aya kuma bokan ya bayyana suka had'e sukai ta masa dariya lokaci d'aya kuma suka b'ace b'at, juyowa Bassam yayi ya kalli Alhaji Bala yayi murmushin mugunta ya juya ya fuskanci alk'ali yace
"Shaida ta ta biyu itace, bayan na tsinci wannan takardar a gidan Alhaji Bala na saka akayi tracking number sa wannan shine sakamakon binciken d'auke da muryar Alhaji Bala da malamin sa.. " a hankali ya fiddo wayar sa ya kunna voice note na farko wanda Cyber Wizard d'in ya turo masa kamar haka:-


_"Hello" cewar Alhaji Bala, gyaran murya malamin yayi yace_
_"Bala binciken da nayi ya nuna idan har muna so mu tsira da mutuncin mu to dole sai ka kashe wannan yarinyar"_
_"Kana nufin sai na kashe Kausar?" cewar Alhaji Bala_
_"K'warai Bala"_
_"Ta yaya kake tunanin zamu kashe ta ba tare da hukuma ta sako hannun ta cikin al'amarin kisan ba?"_
_"Zaka kashe ta kuma hukuma zata sako hannun ta sai dai idan ka kiyaye abunda zan gaya maka to ba abunda zaya faru" da sauri Alhaji Bala yace_
_"Wai kana nufin nine zan kashe ta da hannu na?"_
_"K'warai kuwa" numfashi Alhaji Bala ya saukar yace_
_"Toh ina sauraren ka"_
_"A wuri d'aya 'yar ka A'ishah ke kwana da yarinyar?" cewar Malamin, da sauri Alhaji Bala yace_
_"K'warai kuwa a d'aki d'aya suke kwana"_
_"Abunda nike so da kai shine ka tura A'ishah zuwa gidan 'yan uwan ka da zummar kwana biyu ko uku wannan shi zai bamu damar mu aiwatar da nufin mu ba tare da wata matsala ba"_
_"Na'am ina sauraren ka" cewar Alhaji Bala_
_"Idan ta tafi, da misalin k'arfe biyu ko kuma dai ko wanne lokaci ne a tsakiyar daren ranar ka d'auki wuk'a ka nufi d'akin da yarinyar ke kwana amma ka tabbatar ka saka handkerchief ko wani k'yalle a handle d'in wuk'ar koda hukuma zata sako hannun ta a bincike yatsun hannun ka ba zai nuna ba, idan ka kashe ta sai ka tada hankalin kowa a gidan cewar b'arayi sun shigo sunyi barazanar hallaka ka idan har baka basu kud'i ba kai kuma ka d'auko kud'in ka basu... " da sauri Alhaji Bala ya katse shi gami da cewa_
_"Miye fa'idar yin hakan?"_
_"Na farko koda hukuma zata sako hannun ta a binciken a k'alla akwai wanda zargi zai hau kansa shine b'arayin, kaga hankalin su zai fi karkata akan cewar b'arayin da suka shigo gidan a wannan daren sune suka kashe ta, na biyu yarinyar tana tsare mutuncin ta, zaka iya yin hasashen cewa ta yiwu b'arayin sun so suyi mata fyad'e ne da bata basu had'in kai ba suka kashe ta" ajiyar zuciya Alhaji Bala yayi yace_
_"Toh mai gadi fa? Ka fa san dole a tambaye sa yana ina har b'arayi suka shigo"_
_"Ka bar al'amarin mai gadi a hannu na, zan saka shi nannauyan bacci a daren ba zai san abunda zai faru ba" shiru Alhaji Bala yayi yana sauraren Malamin sannan ya cigaba da cewa "Idan gari ya waye aka tashi da gawar yarinyar, kada kayi k'asa a gwiwa ka kira jami'an tsaro suzo kai musu bayanin cewa b'arayi ne suka shigo jiya da dare suka yi barazanar hallaka ka idan har baka basu kud'i ba kai kuma d'auko mak'udan kud'ad'e ka basu, koda kuma kuka wayi gari kuka sami gawar yarinyar an kashe ta. Ka basu dukkan goyon bayan da suke buk'ata a binciken don gudun wani zargi ya shigo ciki, ka jajirce ka nuna kamar 'yar ka ce aka kashe, na tabbata 'yan sanda zasu yi bincike ba tare da sun gano komai ba saboda wad'annan b'arayin ba su k'irk'irar su aka yi, daga k'arshe ka kira iyayen yarinyar da 'yan sanda kace kai dai ka hak'ura da wannan binciken, kud'in ka da suka d'auka ka yafe iyayen yarinyar kuwa kayi alk'awalin basu diyyar 'yar su saboda a gidan ka ne wannan tsautsayin ya cika da ita idan sun karb'a diyyar ruwan su idan ma basu karb'a ba ya rage nasu, 'yan sandan kuwa ka kawo kud'i mai yawa ka basu ina mai baka tabbaci daga ranar wannan case d'in ya mutu saboda kamar yadda ka gayamin iyayen yarinyar talakawa ne ba zasu iya cigaba da bawa 'yan sanda kud'i ba don tsananta binciken" numfashi Alhaji Bala ya saukar yace._
_"Da kake cewa zan kashe ta da wuk'a, kasan fa b'arayin wannan zamanin da bindiga suke amfani" dariya malamin yayi yace_
_"Idan ka lura b'arayin sun shigo a wata b'oyayyiyar siffa ne basu zo da niyyar kashe kowa ba kurum kud'i ne ya kawo su, sai dai a hasashen da zaka yi zaka ce kana kyautata zaton yarinyar tunzira su tayi tak'i ta basu had'in kai shiyasa suka kashe ta. Idan har kayi amfani da bindiga wurin kashe ta to dole ne matar ka taji k'arar harbin, kuma shima mai gadin zai iya jiyo k'arar harbin kaga kenan ba batun saka mai gadin bacci"_
_"Idan muka yi amfani da silencer fa?" cewar Alhaji Bala, da sauri Malamin yace_
_"Bala kawai ka barshi a wuk'ar ni nasan abunda nike"_
_"Toh shikenan, nagode" cewar Alhaji Bala_
_"Bakomai Bala, sai kayi taka tsan-tsan sosai fa"_
_"Bakomai kada ka damu" cewar Alhaji Bala_


A nan ne voice note d'in ya k'are, tuni kotu ta kacame da hayaniya da ashar da mutane ke ta d'urawa Alhaji Bala, yayin da Hajiya Zainab yanke jiki tayi ta fad'i somammiya a wurin aka d'auke ta aka fita da ita, shi kuwa Alhaji Bala sake tsinkowa yayi da gudu zai bar kotun 'yan sanda suka sake chafke sa. Mammy, Amma, Abba jikin su yayi sanyi sosai yayin da Kausar kam ba abunda take sai rizgar kuka. Alk'alin ma shiru yayi yana jinjina wannan al'amarin a ransa yayin da Bassam sai magana yake cikin hayaniyar mutanen yana k'ok'arin gabatar da voice note na gaba amma sam hayaniya ta hana a ji shi.





*Ina fatar masu karatu sun fahimci bayanin*👆🏻








*It'z Shawty*💕
[1/8, 7:54 PM] ‪+234 813 551 5123‬: *BARR. BASSAM*
(The Gallant) ❣





By *Shawty*💕



*2017*


4⃣9⃣



Alk'alin saukar da numfashi yayi yai magana nan take kotun tayi tsit, mik'ewa Alhaji Bala yayi ya d'aga hannu alamar yana da magana, bashi dama alk'alin yayi ya fito jiki sanyaye daga wurin zaman sa ya nufi wurin Bassam, kallon juna suke ido cikin ido wanda su kad'ai ne suka san ma'anar kallon a hankali Bassam yayi murmushi murya k'asa-k'asa yace
"Some birds are not meant to be caged" har yanzu sai kallon juna suke a hankali Alhaji Bala ya taka ya isa d'ayan dock d'in wanda yake fuskantar wacce Kausar ke ciki ya tsaya, kallon sa kowa keyi har Bassam ana jiran abunda zai ce, gyaran murya yayi yace
"Ba k'arya a cikin dukkan shaidun da lauya mai kare wacce ake zargi ya gabatar, tabbas nine na kashe 'ya ta A'ishah!" sautin muryoyin mutane ne ya gauraye kotun da innaalillahi wa innaa ilayhi raji'un, Kausar kam kuka ta fashe dashi yayin da Bassam sai kallon ta yake a ransa yana cewa kukan me kuma take, cigaba da magana Alhaji Bala yayi yace "Tabbas na kashe 'yar Alhaji Kabara munyi amfani da jinin ta mun rufe bakin hukumar EFCC da zasu yi bincike akan dukiya ta, daga baya kuma Malami na da Alhaji Kabara suka had'a kai suka yaudare ni suka saka ni na kashe 'ya ta wanda nayi k'ok'arin d'aura laifin akan Kausar..." ya d'aga hannu ya nuna Kausar sannan ya cigaba da cewa "Na tayar da fatalwar A'ishah na tura ta ta shiga jikin Alhaji Kabara ta saka shi yayi yawo a gari yana yiwa kansa tonon silili daga k'arshe kuma na umurce ta da ta kashe shi" mutane sai al'ajabi suke ashe dama labarin da ya watsu a gari na Alhaji Kabara duk Alhaji Bala ne, cigaba da magana yayi yace "Nayi alk'awarin hallaka duk wanda yayi k'ok'arin saka hannun sa a wannan case, shiyasa nasa aka yi attacking wannan bawan Allah.." ya sake d'aga hannu ya nuna Bassam, tuni Mammy ta zabura tana kallon Alhaji Bala wanda shima ita yake kallo nan take hawaye ya zubo mata ba abunda ta tuna sai ranar da tayi waya dashi yake kwantar mata da hankali tare da d'aukar mata alk'awarin zaya yi iyakacin k'ok'arin shi wurin nemo Bassam ashe dama shi ya d'auke shi, wani kuka marar sauti ta fashe dashi ta d'ora kanta akan desk dake gabanta tana da nasanin d'aukar case d'in Alhaji Bala, cikin sanyin murya Alhaji Bala ya cigaba da cewa "Nasa aka harbe sa daga baya kuma nasa aka sace shi sunkutukum sai dai nayi kuskure don kuwa kadara ta riga fata, malam ya sha gayamana idan har muka bari wannan gabar ta cigaba to kuwa zamu hallaka ne" tuni kotun ta sake hargitsewa da hayaniya yayin da Alhaji Bala ya cigaba da cewa "Tun lokacin da na shiga tsafi har zuwa yau a k'alla na kashe rayukan mutane kusan ashirin ko fiye da haka" tuni samarin dake wurin suka fara d'aga murya suna cewa a basu Alhaji Bala suyi masa kisan gilla, buga gavel alk'alin yayi nan take kotun tayi tsit shi kuma ya cigaba da rubuce-rubucen shi yayin da Alhaji Bala sai zubda hawaye yake, Mammy ma sai kuka take yayin da Bassam ya fitinu da kukan Mammy Allah-Allah yake alk'alin yayi passing judgment d'in yaje yayi calming Mammy, d'ago kai alk'alin yayi yace
"Bayan gabatar da shaidu daga b'angaren lauya mai kare wacce ake zargi da kuma karb'a laifukan da mai laifin yayi cikin sauk'i, kotu ta yankewa Alhaji Bala hukuncin kisa ta hanyar rataya kuma ta wanke Kausar Abubakar daga laifin da ake zargin ta dashi" murmushi Bassam ya saki wanda har hak'oran sa suka fito ya juyo da sauri yana neman fuskar Kausar suyi four eyes unfortunately fuskar ta a k'asa sai kuka take. Abba ma hamdala da godewa ubangiji ya shiga yi yana dariya yayin da mutanen dake zagaye dasu sai barka ake musu a inda Amma kam kukan farin ciki ta shiga yi. Gefen Alhaji Kabeer kuwa tuni cikin sa ya d'uri ruwa yana gudun kadda a tab'o file d'insa, tuni kotun ta sake breaking da hayaniyar mutane suka shiga cewa hukuncin yayi daidai yayin da wasu suka ce kamata yayi ai masa mummunan kisan gilla idan aka rataye shi ai ma an masa da sauk'i, buga gavel d'in alk'alin yayi alamar an zartar da hukunci had'i da mik'ewa tsaye, nan take mutane ma suka shiga mik'ewa cikin su kuwa harda Bassam ba abunda yake sai murmushi, nan mutane suka shiga congratulating nasa yana amsawa, mik'ewa Mammy tayi ta tattara takardun dake gaban ta ta cire wig d'in ta rik'e a hannu ta nufi hanyar fita kotun fuskar ta ta jik'e sharaf da hawaye yayin da aka yi gaba da Alhaji Bala. Tuni aka nemi Alhaji Kabeer aka rasa ya cika wandon sa da iska, k'arasowa Amma da Abba suka yi cike da fara'a suka taya Bassam murnar nasarar da ya samu da kuma gode masa, murmushi yayi kawai ya juya ya kalli Kausar wacce har yanzu take tsaye a cikin dock d'in, sai a lokacin ta d'ago fuskar ta idanun ta sunyi luhu-luhu saboda kuka, kallon d'an sandan dake gefe tayi tana tsoron fitowa daga dock d'in don gani take kamar zasu sake chafke ta ne, murmushi yayi ya nuna mata hanya da hannun sa irin now you are free kallon Bassam tayi sai murmushi yake, rugowa tayi da gudu in a high speed ta fad'a k'irjin Bassam ta fashe da wani irin kuka, hannun sa d'aya yasa yana shafa bayan ta yayin da d'ayan yake rik'e da wig d'insa bai nufi bata hakuri ba 'cause yasan it's normal to have a cold feet irin wannan lokacin, kukan Amma da Abba suma suka fashe dashi Abba yaja hannun Amma suka bar kotun leaving Bassam and Kausar alone, ba abunda take yanzu sai ajiyar zuciya, don kanta ta fiddo kanta daga k'irjin shi amma bata bari suka yi ido hud'u ba, murmushi yayi yai mata peck a goshi ya goge mata hawayen fuskar ta yace
"It's all right" jinjina kai tayi a hankali ya rik'o hannun ta yana gaba tana biye suka fito zuwa harabar kotun. A nan suka samu dandazon mutane don kuwa wasu tun ana cikin kotun suka fara recording abunda yake faruwa suna watsawa a social media anan fa labari ya fara watsuwa not to talk of lokacin da akace an yankewa hamshak'in mai arzikin nan wato Alhaji Bala hukuncin kisa nan take 'yan jarida suka kamo hanyar zuwa kotun don samun labarai, fitowar Bassam da Kausar suka yo chaaa akansa, ya tsaya ya amsa wasu daga cikin tambayoyin da suka shiga jero masa a matsayin sa na lauyan da yayi nasara saura kuma ya ture su yaja hannun Kausar suka bar wurin, hango Jay yayi tsaye ya zura duka hannuwan sa cikin aljihu dama shi bai shiga kotun ba a waje ya tsaya, yana hango Bassam ya nufo shi da sauri yana dariya had'i da ware hannuwan sa duka biyu, sakin hannun Kausar yayi ya nufi Jay suka yi hugging juna in a manly manner sannan Jay yayi breaking hug d'in ya kalli Bassam sai murmushi yake ya mik'a masa hannu yace
"Congratulations Barrister! This is a great day for all of us" murmushi Bassam yayi ya mik'a masa hannu in return suka gaisa sosai yace
"Thank you so much Jay! We did it!" murmushi dukan su suka yi suka sake hugging juna, breaking hug d'in Bassam yayi yace "Mammy fa?" juyawa Jabir yayi ya nuna masa wani wuri gefe da hannu, hango ta Bassam yayi zaune bisa dutsi k'ark'ashin wata itaciya sai kuka take, da sauri Bassam ya ture Jabir ya nufi wurin ta har yana so ya had'a da gudu sai dai k'afar sa dake masa ciwo, tsugunawa Bassam yayi ya rik'o hannayen ta duka biyu yace "Mammy?" da sauri ta d'ago kai ta kalle shi sai kuma ta rushe da kuka, cikin kuka tace
"I'm very stupid out there Bassam, everything he said to me was a lie and I believed him" share hawayen ta Bassam ya shiga yi yace
"No Mammy you are very brave out there, and that's because he's piece of garbage and you are human" ture hannun sa tayi tace
"Bassam mutane zasu d'auka ni abokiyar cin mushen shi ce shiyasa na tsaya masa a kotu" girgiza kai Bassam yayi yace
"No! He outsmart everyone, ba wanda zaiyi tunanin haka beside you are just doing your job" shiru tayi sannan tace
"Bassam you already knew everything about him shine kak'i sanar dani ko?" murmushi Bassam yayi yace
"You refused to listen to me" shiru tayi don kuwa tasan hakane. Rarrashin ta Bassam ya shiga yi har ya samu ta taso suka nufi wurin ajiye motoci, anan suka hadu da Samira Mammy ta shiga bashi labarin hidimar da tai

Please Login or Register in order to submit comment