Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

"He confront me with 10M akan na daina case d'in"
"Whaaaaaattt??" cewar Jabir, jinjina kai Bassam yayi yace
"Yeah remember days back I told you an kira a waya ana cewa na fitar da hannu na a case d'innan ba?" nodding Jabir yayi alamar eh, iska Bassam ya furzar daga bakin sa yace "That call has something to do with him" shiru Jabir yayi baice komai ba a sanyaye Bassam yace "It's a big coincidence, mutumen nan no matter what yasan wani abu game da kisan A'ishah shiyasa yake k'ok'arin b'oye ko menene" jinjina kai Jabir yi shiga yi alamar maganganun Bassam sun shige sa, cikin sanyin murya Jabir yace
"Me ka gaya masa?" d'an d'aga kafad'un sa Bassam yayi yace
"Me fa? I told him bazan daina ba"

"Good" cewar Jabir, jinjina kai Bassam yayi yace
"Yeah kuma d'azu yarinyar ta gayamin duk wanda ya kashe A'ishah a daren ranar da abun ya faru ba A'ishah aka zo kashewa ba akasi aka samu ita aka so a kashe" mamaki ne ya bayyana a fuskar Jabir, a hankali Bassam yace "Kaga another coincidence right?" nan ma jinjina kai Jabir yayi Bassam yace "Get ready gobe zamu sake dawowa nan gidan" da sauri Jabir ya kalle sa yace
"Wanne gidan?"
"Gidan Alhaji Bala mana" shiru Jabir yayi sa'annan yace
"Allah ya kaimu"
"Ameen" Bassam ya amsa da haka har suka kawo gidan su Jabir yayi dropping nasa akan gobe zasu je gidan Alhaji Bala a haka suka rabu.



Gefen Alhaji Bala kuwa fitar Bassam ya d'auko wayar sa ya fara neman Alhaji Kabeer, ringing d'aya a na biyu ya d'aga had'i da cewa
"Hello"
"Kabeer kayi gaskiya" cewar Alhaji Bala
"Me ya faru?" Alhaji Kabeer ya tambaya daga d'aya b'angaren, dogon numfashi Alhaji Bala ya saukar had'i da cewa
"Young barrister nan he's becoming threat to us"
"Ya kuka yi dashi?"
"Yak'i karb'ar kud'in plus jiya naje wurin Hudu Aljani ya tabbatar min Alhaji Kabara bai daina bibiyar mu ba"
"Innalillahi!" cewar Alhaji Kabeer sa'annan ya k'ara da cewa "Na gaya maka ka b'atar da yaron nan Bala"
"Zan cigaba da aika masa da gargad'i idan yayi kunnen uwar shegu ni kuma zan chanza salo" cewar Alhaji Bala
"Bala har yaushe? Bakada wannan lokacin, inace yanzu kake cewa Kabara bai daina bibiyar ka ba ko?"
"Hakane"
"To har wanne gargad'in kuma zaka sake basa? Bala kawai ka kawar dashi ka fuskanci Kabara yafi zame maka babbar barazana a yanzu" jinjina kai Alhaji Bala yayi kamar Alhaji Kabeer d'in yana ganin sa yace
"Haka za'a yi Kabeer, nagode" had'i da katse kiran ya k'urawa bango ido yana tunani.






*Shawty*💕
[1/8, 6:10 PM] ‪+234 813 551 5123‬: *BARR. BASSAM*
(The Gallant) ❣






By *Shawty*💕


*2017*

3⃣5⃣



_The next day_
Yau ya kama Sunday sai wuraren 10:00am Bassam ya tashi yayi wanka ya shirya cikin k'ananan kaya ya nufi sashen Mammy, bai same ta a parlorn ba wanda ya basa dama yayi breakfast sa'annan ya fito ya nufi parking lot, wayar sa ce ta fara ringing alamar shigowar kira dubawar da zai yi ne yaga number ba suna, tsuka yaja yayi ignoring kiran don kuwa tun jiya number ke kiran sa da haka har ya iso parking lot d'in ya shiga motar sa had'i da kicking yaja ya bar gidan. Gidan su Jabir ya nufa kai tsaye ya d'auke sa suka nufi gidan Alhaji Bala a hanya sai tattauna case d'in suke da haka har suka iso gidan. Horn Bassam ya danna har sau uku sa'annan me gadin yazo ya wangale masa gate d'in, jan motar yayi ya danna cikin gidan ya samu wuri yayi parking sa'annan suka fito daga motar, me gadin ne ya sake bazowa da gudu suka gaisa a hankali Bassam yace
"Alhajin fa?" da sauri me gadin yace
"Baya nan ya fita"
"Hajiyar fa?" washe baki me gadin yayi yace
"Ah Hajiya tana ciki"
"Good!" cewar Bassam "Shiga kai mana iso" jinjina kai me gadin yayi ya tashi ya shara a guje ya nufi cikin gidan, ba'a d'auki minti biyar ba ya dawo had'i da cewa
"Bismillah ranka ya dad'e" me gadin ne a gaba yayin da Bassam da Jabir suke a baya har suka iso parlorn sa'annan me gadin ya koma bakin aikin sa. Da sallama suka shiga parlorn wanda ba kowa a ciki sai Hajiya Zainab, a sanyaye ta amsa sallamar had'i da cewa
"Sannun ku da zuwa" k'arasowa suka yi suka zauna kan sofa suka gaisa sa'annan Bassam yace
"Sunana Muhamm..." bai k'arisa ba Hajiya Zainab ta katse sa cikin murmushi tace
"Bassam ko?" murmushi Bassam yayi had'i da jinjina kai alamar eh, murmushi Hajiya Zainab tayi itama tace "Naga kamannin da Hindu ai" murmushi Bassam yayi a sanyaye yace
"Ya k'arin hak'uri?" tuni murmushin dake fuskar Hajiya Zainab ya kau cikin sanyin murya tace
"Alhamdulillah"
"Allah ya jikan A'ishah" cewar Bassam, Hajiya Zainab wacce tuni ta fara share kwalla tace
"Ameen" sosai Bassam ya tausaya mata, a hankali yace
"I wish I'm here on a social visit but nazo ne game da case na kisan A'ishah" kallon sa Hajiya Zainab kawai keyi tana jinjina kai a hankali yayin da Bassam ya cigaba "Nine lauya me kare Kausar amma a gefe d'aya ba kare ta kawai nike kamar yadda kuke tunani, nima ina iyakacin k'ok'ari na wurin gano waye ya kashe A'ishah" har yanzu Hajiya Zainab sai gyad'a kai take yayin da Bassam ya gyara zama yace "Hajiya me kika sani game da kisan A'ishah?" tuni Hajiya Zainab ta fashe da kuka mai tsuma zuciya yayin da Bassam da Jabir duka sun tausaya mata, sai da tayi kukan ta gaji sa'annan tace
"Wallahi bansan komai a kisan A'ishah ba kawai mun samu gawar ta da safe an kashe ta"
"Amma waye mutum na farko da kike zargi akan kisan A'ishah?"
"Toh wanda muke zargi da..."
"A'a Hajiya" Bassam yai saurin katse ta had'i da cewa "Ina magana dake ne ke kad'ai, wanda kike zargi, wanda ya fara zuwa miki a rai game da kisan A'ishah" shiru Hajiya Zainab tayi sa'annan taja numfashi tace
"Toh a daren ranar da abun zai faru b'arayi sun shigo nan gidan toh..." da sauri Bassam ya katse ta had'i da cewa
"B'arayi kuma?" ya juya ya kalli Jabir wanda shima Jabir d'in kallon sa yake lokaci d'aya kuma suka maida kallon su kan Hajiya Zainab, jinjina kai Hajiya Zainab tayi tace
"K'warai da gaske a daren ranar b'arayi sun shigo suka yi barazanar hallaka miji na Idan har bai basu kad'i ba ya d'auko mak'udan kud'i ya basu toh..."
"Da misalin k'arfe nawa b'arayin suka shigo kuma kin gansu da idanun ki?" girgiza kai Hajiya Zainab tayi tace
"Bansan ko k'arfe nawa bane amma lokacin da Alhaji yazo yana gayamin misalin k'arfe uku ne na dare"
"Wannan ya nuna ba a wuri d'aya kuka kwana ba ke da Alhajin hakane?" jinjina kai Hajiya Zainab tayi alamar eh tace
"Hakane ba wuri d'aya muka kwana ba" gyara zama Bassam yayi yace
"Meyasa?" shiru Hajiya Zainab tayi a cikin ranta tana ganin Bassam fa yana nema ya wuce gona da iri kamar ba zata amsa wannan tambayar ba kuma dai tai k'arfin hali tace
"Saboda rashin dawowar sa gida da wuri a ranar har bacci ya sace ni a sashe na" jinjina kai Bassam yayi alamar ya gamsu da zancen ta sa'annan yace

"Toh mu koma wanchan zancen, da farko kince b'arayin da suka shigo kike zargi akan kisan A'ishah daga baya kuma fa?"

"Toh bayan gari ya waye ne Alhaji ya sanar da 'yan sanda abunda yake faruwa a nan ne d'an sandan yake hasashen za'a iya danganta kisan da Kausar saboda mun same ta akan gawar A'ishah rik'e da wuk'ar da aka kashe ta, kuma da aka duba wayar A'ishan an ga tayi waya da Kausar har sau biyu wanda kuma a daren ranar A'ishah bata kwana a gidan ba"
"Bata kwana a gidan ba? A ina ta kwana?" kuka Hajiya Zainab ta fashe dashi a karo na biyu tace
"Tsautsayi ya dawo da A'ishah a daren ranar don kuwa taje gidan k'anwar Alhaji da zancen zata kwana biyu a wurin ta sai kawai muka samu gawar ta anan gidan da safe"
"Toh me ya dawo da ita?" cewar Bassam, cikin kuka Hajiya Zainab tace
"Abunda ya d'aurewa kowa kai kenan don kuwa ba wanda ya sani sai Kausar zata yiwu tasan wani abu game da dawowar ta gida a wannan daren"
"Kenan wannan shaidun su suka karkata tunanin ki daga cewar b'arayi ne suka kashe A'ishah zuwa Kausar hakane?" gyad'a kai Hajiya Zainab tayi alamar eh sa'annan Bassam yace "Amma a iyakar sanin ki da Kausar, kina tunanin zata iya kashe mutum?" girgiza kai Hajiya Zainab tayi tace
"Ko kad'an sai dai mutum zai iya chanza halin sa a koda yaushe" murmushi Bassam yayi yace
"Hakane, amma iyayen Kausar sun tabbatar tun Kausar tana 'yar k'ank'anuwa kike tare da ita na tabbata ba wani hali na Kausar wanda baki sani ba"

"Hakane amma kamar yadda na gaya maka mutum zai iya chanza halin sa a koda yaushe" jinjina kai Bassam yayi yace
"Nagode sosai Hajiya kuma ina tabbatar miki jinin A'ishah ba zai tafi a banza ba duk wanda yake da hannu a kisan A'ishah gaskiya zatai halin ta" jinjina kai Hajiya Zainab tayi tace
"Hakane" mik'ewa Bassam da Jabir suka yi lokaci d'aya Bassam yace
"Mun gode Hajiya idan da bukatar mu dawo zamu dawo"
"Bakomai Bassam" cewar Hajiya Zainab had'i da cewa "Ka gaida Mammyn ka" murmushi yayi yace
"Zata ji" sa'annan yace "Ko zaki iya gayamin address na gidan k'anwar Alhajin wacce Kausar ta kwana a gidan ta?" gaya masa address d'in Hajiya Zainab tayi suka yi godiya suka fice daga parlorn.


A bakin gate suka samu mai gadi a hankali Bassam da Jabir suka taka suka isa wurin shi Bassam ya gabatar masa da kansa, tuni me gadin ya sha jinin jikin sa ya jawo kujerar da yake zaune ya tura gaban Bassam had'i da cewa
"Bismillah ranka ya dad'e" murmushi Bassam yayi ya girgiza kai yace
"Ba sai na zauna ba tambayoyi zan maka"
"Toh toh ina jinka ranka ya dad'e" cewar me gadin, had'e fuska Bassam yayi yace
"Hajiya ta tabbatar muna daren da za'a kashe A'ishah b'arayi sun shigo gidan nan kana ina haka ta faru baka yi k'ok'arin dakatar dasu ba a matsayin ka na me gadi?" tsoro ya kama me gadin yace
"Wallahi ranka ya dad'e bacci ya sace ni lokacin" jinjina kai Bassam yayi yace
"Kuma a daren ranar A'ishah anan gidan ta kwana wanda kowa yasan ta bar gidan nan taje gidan k'anwar mahaifin ta kana ina A'ishah ta shigo baka ganta ba?"
"Wallahi ranka ya dad'e bansan shigowar ta ba" waige-waige Bassam ya shiga yi yace
"Toh ko akwai wata hanyar da zata iya shigowa ne bayan wannan?"
"Babu ranka ya dad'e wannan ce kad'ai hanyar shigowa nan gidan" nodding Bassam yayi yace
"Kuma baka san lokacin da ta shigo ba right? Wanda alhakin kula da shiga da ficen kowa na nan gidan yana kanka" tsoro sosai ya kama me gadin yace
"Wallahi ranka ya dad'e ina gaya maka iyakar abunda nasani ne bansan lokacin da ta shigo ba"
"Ba damuwa" cewar Bassam sa'annan ya k'ara da cewa "A iyakar sanin ka da Kausar kana tunanin zata iya kisan kai?" da sauri me gadin yace
"Ko kad'an idan ma marigayiyar ce akace tayi kisan kai zan iya yarda amma Kausar ba zata iya kashe kowa ba ina tabbatar maka da haka yarinya ce mai hankali da nutsuwa" jinjina kai Bassam yayi yace
"Mun gode" suka yi sallama suka juya suka nufi wurin motar su.


Sai da suka hau titi sosai Jabir yace
"Kaji wata sabuwa kuma, anya kuwa ba b'arayin ne suka kashe ta ba?" girgiza kai Bassam yayi yace
"Ni fa bana tunanin b'arayi sun shiga gidan a ranar"
"What?" cewar Jabir
"Yeah" Bassam ya amsa masa, cikin d'aurewar kai Jabir yace
"Me kake nufi?"
"Haba Jay! Use your 6th mana! According to what she reveals idan har da gaske b'arayi sun shigo toh kud'i ne ya kawo su kuma ya basu. Secondly, ita bata gansu ba mai gadi bai gansu ba shi ya k'ara tabbatar da cewar basu zo da niyyar tab'a kowa ba kud'i ne ya kawo su kuma an basu but amazingly sun shiga d'akin yaran har suka kashe A'ishah suka bar Kausar meyasa zasu kashe d'aya su bar d'aya? Idan har da niyyar kisa suka zo I suggest me gadi ne mutum na farko da zasu fara kashewa but mind you ina maka magana ne akan idan har da gaske b'arayin sun shigo gidan kenan " shiru Jabir yayi a sanyaye Bassam yace "Abun akwai d'aure kai but I want to see wannan k'anwar mahaifin tan right now" nodding Jay yayi ya dinga nuna masa hanya da yake Bassam ba sanin gari yayi ba da taimakon address da Hajiya Zainab ta basu da haka har suka iso gidan Goggo Hadiza, nan ma me gadi suka sa yai musu iso sa'annan suka shiga suka same ta zaune a cikin parlorn tana kallo. Bayan sun gaisa ne Bassam ya gabatar mata da kansa sa'annan yace
"Hajiya mun zo ne game da kisan A'ishah" gyara zama Goggo Hadiza tayi tace
"Toh"
"A matsayin ki na Goggon A'ishah kuma wacce ta saka A'ishah k'arshe a ido ranar, me kika sani game da kisan A'ishah ko kuma meyasa A'ishah ta bar gidan ki a ranar da dare ta koma gidan su?" shiru Goggo Hadiza tayi na wani lokaci sa'annan tace
"Nima bansani ba saboda mun kwanta lafiya k'alau da A'ishah sai neman ta nayi da asuba ban ganta ba kuma na sami motar ta wanda ya tabbatar da cewa da k'afafun ta ta bar gidan" jinjina kai Bassam yayi yace
"Nagode, amma wacce irin shaida zaki bada akan Kausar idan aka baki dama? Kina tunanin Kausar zata iya kisan kai kuwa?" girgiza kai Goggo Hadiza tayi da sauri tace
"Ko kusa, Kausar yarinya ce mai ladabi da tarbiya sai dai..." da sauri Bassam ya katse ta yace
"Sai dai me?"
"Yan sanda sunfi karkata hankalin su akan itace ta kashe A'ishah" murmushi Bassam yayi yace
"Har yanzu zargi suke ba'a tabbatar ba" juyar da kai Goggo Hadiza tayi ta share hawayen da suka zubo mata cikin jimami tace
"Allah yayi gaggawar tona asirin duk wanda yake da hannu a kisan A'ishah"
"Ameen" Bassam da Jay suka amsa suka yi godiya had'i da yin sallama suka fito suka sami me gadin, kamar yadda ta faru tsakanin sa da me gadin gidan Alhaji Bala haka ma ta faru tsakanin sa da me gadin gidan Goggo Hadiza don kuwa shima ya tabbatar musu da baisan lokacin da A'ishah ta bar gidan ba, nan ma godiya suka yi suka shiga mota Bassam yaja suka bar gidan. A hankali Jabir yace
"Wai kwa yarinyar nan ko aljana ce? Ta ya za'a ce ba wanda yaga shigar ta da fitar ta" murmushi Bassam yayi yace
"Mutum ce akwai dai wani abu a k'asa yanzu ba wanda zai iya warware wannan kullin sai Kausar kuma na lura kamar tana jin tsoron fad'ar wani abu a kan abunda ta sani"

"I think muje mu ganta" cewar Jabir, girgiza kai Bassam yayi yace
"Zamu je amma ba yanzu ba" da haka dai sukai ta hira har suka iso gidan su Jay yai dropping nasa shi kuma ya nufi gida.




*Ku tayani addu'a, zazzabi ke damuna*😫





*It'z Shawty*💕
[1/8, 6:50 PM] ‪+234 813 551 5123‬: *BARR. BASSAM*
(The Gallant) ❣




By *Shawty*💕


*2017*

3⃣6⃣


_*This page goes to Meena Sheriff & Co whom pay me a visit yesterday, thank you so much. I really appreciate it and it means a lot.*_❤


__________________________________________


Alhaji Bala ne ke sharara gudu a cikin motar sa ya kama hanyar fita Sokoto, sai da ya fita gaba d'aya daga garin ya kama daji sosai sa'annan ya saki titi ya kama wata hanya wacce ba kwalta ya doshi wani k'aramin k'auye wanda zai kai kusan kimanin 3-4kilometers, haka yai ta tafiya ya fad'a nan ya tashi nan har ya kai k'auyen, wata hanyar ya sake d'auka ya nausa cikin dokar daji chan kuma ya hango wata bukka a gaban sa wacce ita kad'ai ce alamar gida a wurin, murmushi yayi ya tunkari bukkar har ya iso yayi parking ya fito daga motar yana k'arewa wurin kallo. Kama hanya yayi izuwa wurin bukkar ya shiga, wani d'an tsoho ne zaune bakomai a jikinsa sai walki kansa da wasu tsoraye sunyi fik'i-fik'i idanun sa jajir yayin da fatar jikin sa bak'a ce k'irin, a tak'aice dai siffar wannan mutumin abin tsoro ce kuma kallo d'aya zakai masa ka tabbatar boka ne. Ganin Alhaji Bala ne yasa ya saki baki wangalau wanda mafi yawan hak'oran sa sun zube yana kallon Alhaji Bala, cikin mamaki yace
"Wa zan gani haka kamar Bala?" murmushi Alhaji Bala yayi yace
"Ba kama bace nine" cikin tsintsar mamaki bokan yace
"Dama Bala kana raye?" nan ma murmushi Alhaji Bala yayi ya samu wuri ya zauna yace
"Ina nan" jinjina kai bokan yayi yace
"Gaskiya ne ba kwa neman mu sai da buk'ata idan anci moriyar ganga sai a yada koran"
dariya Alhaji Bala ya kwashe da had'i da cewa
"K'warai kuwa yanzu haka buk'ata ce ke tafe dani nasan ba wanda zan iya tunkara da ita sai kai" murmushi tsohon yayi yace
"Na sani, meke tafe da kai?" labarin badak'alar dake tsakanin sa da Alhaji Kabara ya shiga irga wa bokan har kawo yau, jinjina kai bokan yayi yace
"Yanzu me kake so?" gyara zama Alhaji Bala yayi ya lank'washe k'afa yace
"Ina so ka tayar min da gawar A'ishah a matsayin fatalwa" cikin d'aurewar kai bokan yace
"Ban fahimce ka ba Bala"
"Ina nufin ka tayar da 'ya ta A'ishah a matsayin fatalwa kuma baiwa a wuri na ina so zan aike ta"
"Wurin wa zaka aike ta?" kallon bokan Alhaji Bala yayi da kyau yace

"Wurin Kabara"
"Me zatai masa?"
"Kashe shi nike so tayi"
"Miye fa'idar yin haka?" cewar bokan
"Shine d'aukar fansa mafi bak'in ciki da zanyi wa Kabara kafin nan ina so ta shiga jikin sa tasa yayi yawo rariya-rariya yana yiwa kansa tonon silili daga k'arshe ta kashe sa a lokacin zata koma tayi kwanciyar ta" har yanzu sai kallon sa bokan keyi yace
"Har yanzu baka gayamin fa'idar yin hakan ba"
"Idan har banyi gaggawar kawar da Kabara ba, to yana gab da kawar dani" jinjina kai bokan yayi yace
"Kazo da magana mai girma Bala" murmushi Alhaji Bala yayi yace
"Nasan zaka iya ne shiyasa nazo gare ka" numfashi bokan yaja yayi shiru sa'annan yace
"A tsawon rayuwa ta cikin tsafi yau shekaru fiye da sittin sau d'aya na tab'a tada matacce a matsayin fatalwa Bala" murmushi Alhaji Bala yayi yace
"Yanzun ma zaka iya" girgiza kai bokan yayi yace
"Ba iyawar ba akwai matsala a cikin sha'anin fatalwa"
"Matsalar me?"
"Ba zata iya zama baiwar ka ba har abada kuma ina tsoron wannan shu'umin abokin gabar ka kadda ya halbo jirgin mu" girgiza kai Alhaji Bala yayi yace
"Idan har zan umarce ta ta kashe shi ai ta zama baiwa ta ta har abada, kuma da ta kashe shi ai itama zata bi bayan sa ne ba zan barta ba"
"Idan ya gano abunda muke shirin aikatawa fa?"
"Ba zai gano komai ba zaka rufe aikin ka da k'arfin tsafin ka" dariya mutumen ya b'arke da had'i da cewa
"Bala mugu ne kai, a wurin mugunta sai dai a barka wani lokacin ina mamakin hangen nesan ka" wani k'asaitaccen murmushi Alhaji Bala yayi sa'annan bokan yace "Sai dai wannan aikin yana da matuk'ar wahala Bala, kafin in tanadi magungunan da zan tayar da ita za'a d'auki lokaci"
"Ba damuwa" cewar Alhaji Bala "Kai dai kawai ayi komai cikin gaggawa" jinjina kai bokan yayi ya fara karanto kalmomin tsafin sa wanda shi kad'ai yasan ma'anar su, da Alhaji Bala yaga abun nasa bana k'arewa bane ya mik'e tsaye ya ajiye masa d'aurin kud'ad'e had'i da cewa "Zuwa nan da kwana biyu zan sake zagayowa" jinjina kai kawai bokan yayi alamar yaji yayin da Alhaji Bala ya fito daga cikin bukkar gidan ya nufi wurin motar sa ya shiga yaja ya kama hanyar komawa.




_2 weeks later_

*In a court*
Minti ashirin kafin a fara sauraren k'arar Hajiya Zainab, Mammy, Alhaji Bala, Alhaji Kabeer, Goggo Hadiza, Amma da Abba da duk wani d'an uwa da abokan arziki sun hallara a harabar kotun sai Bassam kawai wanda baya wurin, ba shine ya samu isowa ba sai ana minti biyar da za'a fara sauraren k'arar wanda gaban Mammy yayi mummunar fad'uwa da ta hango motar sa wani haushi da takaici ya ziyarce ta tayi nadamar kasancewar Bassam lauya a yau. Gefen Bassam kuwa bud'e motar suka yi shi da Jabir suka fito cikin shiga ta suit dukansu suke wanda Bassam ta zame masa al'ada kamar koda yaushe sune kayan da yake sakawa, bayan motar sa ya bud'e ya d'auko Wig and Gown d'insa a lokacin suka yi four eyes da Mammy wani kallo take masa wanda zai iya cewa bai tab'a ganin tsintsar b'acin rai ba a fuskar ta kamar yau, yana kallon ta yaga ta shiga danna wayar ta sai kuma ta saka a kunne still ta k'ura masa ido, wayar sa ce ta hau ringing yana dubawa yaga Mammy b'aro-b'aro akan screen d'in wayar sa d'ago kai yayi yana kallon ta itama shi take kallo yayin da jikin sa yayi sanyi k'alau yana kallon call d'in har ya tsinke yak'i d'agawa a hankali ya girgiza mata kai had'i da furta
"I'm sorry Mammy" yanda ya furta maganar ko wanda yake kusa dashi ba zai Iya jiyowa ba talkless of Mammy da akwai distance a tsakanin su, juyawa yayi ya fuskanci wani b'angaren ya daina kallon ta ma.


_5 minutes later_
*Courtroom*
Alk'ali ne zaune a wurin sa da aka tanada yayin da Mammy, Bassam da Jabir suke a nasu mazaunin sai Kausar wacce aka fito da ita da handcuffs a hannayen ta aka kaita wurin da masu laifi suke tsayawa a kotu(dock). Kallo d'aya Bassam yai

Please Login or Register in order to submit comment