Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

a cheeks yace "I have to go it's time" bata ce dashi komai ba ta janye jikin ta daga nashi, a hankali ya bud'e ƙofar motar ya fito.
Sanye yake da jean trouser da t-shirt a ciki sama kuma ya d'ora sweater ne sakamakon sanyin da ake sai hular sanyi da yasa ya rufe kansa dashi da hand gloves idanun sa ɓoye cikin dark glasses. Bud'e masa boot tayi ya d'auki trolley d'insa ya juyo yai mata waving goodbye ya kutsa kai cikin airport d'in.


Shigar sa airport d'in keda wuya aka kira passengers suka fara shiga. Tafiyar awoyi suka shafe a iska sa'annan suka dira a Abuja, Nigeria. Already dama Mammy tasa an masa booking flight zuwa Sokoto. Nan ma luckily bai dad'e ba aka kira passengers suka fara shiga a haka dai suka tashi zuwa Sokoto, Nigeria. Saukar su keda wuya yayi dialing number drivern da Mammy ta masa sending ba'a dad'e ba sai gashi yazo yai masa sannu da zuwa had'i da d'aukar trolleyn sa yayi masa jagora har zuwa wurin mota ya bud'e masa ya shiga ya mayar ya rufe shi kuma ya koma gefen driver ya shiga ya jasu zuwa Gida.


Tafe suke Bassam ba abunda yake sai kallon gari yana imagining wai shine zai rayu a wannan alƙaryar like what the fuck, murmushi kawai yake duk sanda wannan tunanin yazo masa a ransa yana cewa dole zaiyi convincing Mammy akan zai koma Scotland don kuwa ba zai iya zama a wannan ƙauyen ba da haka har suka iso.


Yayin da gefen Mammy kuwa sosai tasa akayi girke-girke iri daban-daban, tasa aka gyara masa part d'aya a cikin gidan ko ina an gyara tsaf sai sparkling yake just waiting for his arrival.


Zaune take a parlor she is eager sai kallon agogo take after every minute, ƙarar horn taji daga gate wanda yasa ta miƙe tsaye zumbur taje wurin window ta yaye curtains yayi daidai da fitowar Bassam daga mota, tsaye yake ƙyam yana ƙarewa gidan kallo dadi wane ya kashe Mammy, duk da yawan shekarun ta haka ta kama da gudu ta fito daga parlorn. Juyowar da zaiyi ne karaf idanun su suka had'u murna fal akan fuskokin su da sauri ya nufe ta yana dariya yayin da tuni ta bud'e hannayen ta ya fad'a akan ƙirjin ta. Hugging nata yayi very tightly though yafi ta tsawo sosai sai flash back memories na when he was a kid ke masa dancing a ƙwaƙwalwa, sun dad'e a wannan yanayin a hankali ba don tana so ba tayi breaking hug d'in ta ƙura masa ido.


Wani hawayen farin ciki ne ya gangaro mata a fuska, hannun sa yasa yana goge mata had'i da cewa
"It's ok Mammy" murmushi tayi had'i da taɓa cheeks nasa tace
"Tell me"
"What?" ya fad'a yana dariya
"Was it a dream? This is so wonderful to be real" dariya yayi still holding her in his arms
"You are fully awake Mammy, your gracious Bassam is here" kallon sa take yanzu kam daga sama har ƙasa as he stood tall a gaban ta

"It's been a while" tace sai ƙara kallon sa take "Ka ganka kuwa? You've grown taller" dariya suka yi gaba d'aya yace
"Muje ciki Mammy wannan garin naku zafi wallahi"
"Ka cire kanka kenan?"
"Kai tuni" duka ta kai masa suka fashe da dariya just like friends, riƙe take da hannun sa har suka shiga parlorn. Wani ƙamshi ne ya daki hancin sa as he stepped in, gidan exactly tsarin turawa ne sai waige-waige yake kamar baƙauye finally ya fad'a akan sofa gami da cewa
"Relief!"
"Menene?" Mammy ta tambaye sa
"No joking Mammy wannan garin zafi ne dashi like hell, how many degrees ne yau?"
"Idiot! I'm not a geographer" dariya ya fashe sa'annan yace
"Such a beautiful house Mammy" murmushi tayi tace
"Thank you sweetheart"
"So, what's up? How are you doing down here? Naga kinyi kud'i fa" ya fad'a teasingly
"Managing, you?"
"Managing without me ha?" kunnen shi taja sai da yayi ƙara had'i da cewa "I'm sorry! Me kika dafa mun I'm damn hungry?" dariya tayi tace
"Suprise"
"Tam Allah yasa ba tuwo bane" dariya ta sake yi tace
"Still al'adar kan nan ta ƙin tuwo tana nan ba?"
"Ah Mammy a Scotland ina zan ga tuwo ma?"
"Good, zaka koya ai" dariya yayi yace
"All right! Let me take a shower first" ya fad'a had'i da miƙewa tsaye. Ita tayo masa jagora har apartment d'insa, parlor ne madaidaici sai bedroom da toilet, bayan ta nuna masa ne ta bashi privacy ta dawo main parlor ta zauna.


*****


A'ishah ce kwance akan 3seater tana chat yayin da Hajiya Zainab ke zaune next to her tana kallo
"Wai nikam ina Kausar ne?" Hajiya Zainab ta tambayi A'ishah
"Tana bedroom"
"Me take yi ne?"
"I dunno maybe bacci take" cewar A'ishah
"Ni na lura she's not herself these days kamar akwai abunda yake damun ta" sai a lokacin A'ishah ta dakatar da chat da take had'i da tashi zaune tace
"Wallahi kuwa Momy, kinga jiya ma da dare she's awake almost 2:00am kuma ba karatu take ba kawai ta saka litafan a gaba ne tana tunani idan na tambaye ta sai tace bakomai"
"Nima na lura da haka" cewar Hajiya Zainab "Me kika fahimta yana damun ta?"

"I dunno" A'ishah ta fad'a had'i da d'an d'aga kafad'arta, shuru Momy tayi na wani lokaci sa'annan tace
"Ku shirya kuje ku gaida Barr. Hindu yafi akan ta zauna a d'aki ita d'aya" sake dakatar da chat d'in A'ishah tayi gami da cewa
"Wannan ƙawar kin nan lawyer?"
"Eh"
"Ok" A'ishah ta fad'a had'i da miƙewa tsaye ta nufi upstairs.





*It'z Shawty*💕
[1/8, 7:26 AM] ‪+234 813 551 5123‬: *BARR. BASSAM*
(The Gallant) ❣



By *Shawty*💕

*PURE MOMENT OF LIFE WRITERS*
(We don't just entertain and educate, we also touch the hearts of the readers.)

*2017*

1⃣4⃣

Tura ƙofar tayi ta shiga d'akin, kwance ta ganta da system a gaban ta a zahiri kamar wacce ke kallo amma ta tsunduma duniyar tunani ne. Hannu A'ishah tasa ta taɓa ta, a razane ta tashi zaune tana kallon ta sa'annan tayi murmushi
"Ya akayi bansan kin shigo ba?"
"Ya za'ayi ki sani fa while kinyi nisa a tunani kamar wata uwar 'ya'ya" murmushi Kausar tayi tace
"Kallo fa nike"
"Ah haba dai? Kin rainan hankali wallahi" dariya Kausar ta bushe da ta koma ta kwanta "Kausar all I'm saying shine mafarki ba gaskiya bane, there's no point da zaki saka kanki a damuwa kawai dan kinyi mafarki"
"Shhh! It's ok pls kallo nike" cewar Kausar
"Me kike kallo ne?"
"The walking dead?"
"Zombies?"
"Yap" dogon tsuki A'ishah taja had'i da cewa
"Ba kya kallon film na arziki sai Zombies, no wonder kike screaming cikin dare" dariya kawai Kausar tayi bata ce da ita uffan ba "Ni ki tashi ki shirya Momy tace zamuje gidan ƙawar tan nan"
"Wacce fa?"
"Wannan lawyer da tazo nan gidan days back mana"
"Yanzu?"
"See idan ba zaki ba kinda tell me bana san tambaya" murmushi Kausar tayi tace
"Dad'i na dake tsiwa"
"Eh naji"
"Kije kiyi wanka first" cewar Kausar, miƙewa A'ishah tayi tace
"Ok" ta nufi bathroom


_15 minutes later_
"Kausar ki tashi fa we are getting late" A'ishah ce ke magana a gaban mirror tana tsara kwalliya yayin da Kausar ke miƙe akan gadon tayi nisa a duniyar tunani bata san ma me A'ishah keyi ba. Juyowa A'ishah tayi ta ganta ta rafka uban tagumi mamaki ne ya cika A'ishah ta d'aga murya tace

"La'ila ha illahu Kausar! Wannan wacce irin masifa ce ta sameki ne a rana tsaka?" a firgice Kausar ta juyo tana kallon A'ishah
"Haba Eshowliey! Ni kin bani tsoro wallahi"
"Dole kiji tsoro mana, wannan wacce irin fitina ce? Me yake damunki ne?" hawaye suka gangaro daga idanun ta dogon numfashi Kausar taja tace
"Bakomai" shuru suka yi A'ishah ta taso ta zauna kusa da ita tace
"Kausar be fair to yourself, this isn't you. You don't seem to be happy as you used to be, you seem somehow cold" shuru Kausar tayi kamar ba zata amsa ta ba kuma dai ta ƙaƙiro murmushi tace
"Bakomai" haushi A'ishah taji sosai tace

"Fine! Enjoy your secrets sai ki tashi ki shirya ko? Idan kuma zaki zauna ki cigaba da tunanin kina hawaye it's cool with me"
"Har kin shirya ne?" harara A'ishah ta wurga mata tace
"Ke nake jira"
"Oops! Na manta ba'a taɓa beating naki a fita outing ba, be it school"
"Idiot! Naji shoot whatever you like" da dariya Kausar ta shige bathroom yayin da A'ishah sai jinjina mata take akan tayi sauri kadda ta ɓata lokaci.


_10minutes later_
"Kausar nikam fata ne zaki chanza? You know I hate waiting" A'ishah ce ke mata bambami wacce ta gama shiryawa tsaf cikin gown na Atamfa ta matse ta gam daga sama yayin da ƙasan kuma ya bud'e, kallabin an kafa shi wane engine ne ya d'aura fuskar an fente ta dal tayi kyau sosai ba laifi

"Sorry Eshowliey, right away" yayi daidai da murd'a handle na ƙofar bathroom d'in, Kausar ce ta fito daure da towel, tsayawa tayi tana kallon A'ishah tace "Wooow! Madam kinyi kyau fa" wani ƙasaitaccen murmushi A'ishah tayi ba abunda tafi so fiye da ai mata compliment me kyau tace
"Thanks" gaban madubi Kausar ta nufa a gurguje ta fara taje kanta ta d'aure shi wuri d'aya da ribbon sa'annan ta shafa mayukan ta, unlike A'ishah bata iya heavy make-up ba bare tayi, powder kawai ta shafa sai colourless lipstick sai eyelashes da eyebrows da ta gyara. Sosai tayi kyau abunka wa farin mutum, wardrobe ta nufa ta fiddo jalabiya baƙa plain mara kwalliya tasa had'i da yane kanta da himar na jalabiyar shima baƙi ta feshe jikin ta da turaruka ta juyo tace
"Toh we are good to go now" d'ago kai A'ishah tayi with intention tai mata masifa she caught the glimpse of her

"Wooow! Kausar? Masha Allah! I dunno ba kya heavy make-up amma whenever you dressed sai kinyi kyau" dariya Kausar ta fashe da tace
"Funny! Wai dama shine kika wani ƙuran ido? Ai kin fini kyau ma" had'e fuska A'ishah tayi tace
"Didn't I told you ki daina cewa na fiki kyau?" dariya Kausar tayi tace
"Ahh! Yi haƙuri Madam, nevertheless dukan mu munyi kyau ha?"
"Sosai ma" cewar A'ishah, juyawa Kausar tayi ta d'auko flat shoe baƙi tasa had'i da d'aukar wayar ta, yayin da mutuniyar wasu matsiyatan heels pink ta saka ta d'aura wrist watch pink gami da d'aukar pink handbag ta kafa glasses a fuskar ta had'i da cewa
"Muje"
"Tam but I bet those heels sai sun karya ki someday" cewar Kausar
"Ke dai zaki karye wallahi, muguwa kawai" dariya Kausar tayi tace
"Mayafi fa?"
"Mayafi kuma? Dallah muje we're running out of time" mamaki ne ya kama Kausar tace
"Don't tell me a haka zaki fita"
"Just shut up, it ain't the shit you knew" bud'e wayar ta tayi ta fara killing selfies kamar ba wacce ke masifar sunyi latti ba, joining nata Kausar tayi sukayi tayi sai da suka gaji suka sauka downstairs suka sami Momy tana kallo
"Wooow! Masha Allah! Kunyi kyau. A'ishah ina mayafin ki?" dariya Kausar ta fara yi ƙasa-ƙasa dama tasan za'a rina yayin da A'ishah ta turo baki tana gunguni "Koma ki d'auko mayafi kinji ba? Bana san shashanci" yayi daidai da shigowar Alhaji Bala parlorn wani mummunan fad'uwa gaban Kausar yayi tuni ta sadda kanta ƙasa yayin da A'ishah ta ruga da gudu ta fad'a jikin shi ta fara sheshshekar kuka
"Ya kike so ki ɓata kwalyan ki princess? Gashi kinyi kyau" cewar Alhaji Bala, cikin sheshshekar kukan munafunci tace
"Daddy ka gayawa Momy ta barni naje a haka please"
"Momy dan Allah ki barta ta tafi a haka" cewar Alhaji Bala, shuru tayi bata ce komai ba tasan tunda Alhaji Bala yazo to ba sauran magana, murmushi Alhaji Bala yayi yace
"Kuje abunku but mind you kar ayi wasa da mota princess"
"Toh Daddy ba za'ayi ba" ta kalli Momy tace "Momy sake kwatanta min unguwar please" kamar ba zata yi ba kuma dai ta ƙara kwatanta matan "Tam sai mun dawo" cewar A'ishah had'i da jan hannun Kausar yayi daidai da idanun ta suka had'u da na Alhaji Bala wani kallo yai mata har sai da antar cikin ta ta kad'a a sanyaye tabi bayan A'ishah suka fita.





*Shawty*💕
[1/8, 7:30 AM] ‪+234 813 551 5123‬: *BARR. BASSAM*
(The Gallant) ❣



By *Shawty*💕

*PURE MOMENT OF LIFE WRITERS*
(We don't just entertain and educate, we also touch the hearts of the readers.)


*2017*

1⃣5⃣


Jikin ta sai rawa yake wane mazari haka suka shiga mota A'ishah ta ja suka tafi, a hanya sam zuciyar ta ta kasa sukuni ta rasa dalili tun lokacin da suka yi four eyes da Alhaji Bala ta nemi kwanciyar hankali a zuciyar ta ta rasa. Wani tsoro ne ya ziyarce ta kuka ta fashe dashi mara sauti, cikin kad'uwa A'ishah tayi parking motar a bakin titi ta tabbata Kausar ba ƙalau ba don yanzu suka fito gida lafiya lau hannun ta A'ishah ta riƙo tana neman duba fuskar ta wacce ta cusa cikin cinyoyin ta
"Anya kuwa Kausar ba aljanu ne suka shafe ki ba?" d'ago fuskar ta tayi wacce idanun ta suka yi ja had'i da tashin jijiyoyin kanta tana wani irin kuka "Na shiga uku!" cewar A'ishah "Wannan wane bala'i ne ke neman tunkaro mu? Kausar aljanu ne dake?" cikin kuka ta fad'a jikin A'ishah tace
"A'ishah ba aljanu bane"
"To miye?"
"Tsoro nikeji"
"Tsoro kuma?" cewar A'ishah ta fara waige-waige back and front left and right cikin motar tace "Me yake baki tsoro?"
"Nima bansani"
"Sign na shigar aljanu ne jikin mutum, ki dinga addu'a kinji?" nodding tai mata yayin da A'ishah ta shiga share mata hawaye ta d'auko robar faro dake cikin motar ta miƙawa Kausar tace "Ungo wanke fuskar ki" murmushi Kausar tayi ta karɓi robar ta d'an bud'e murfin ƙofar kad'an ta wanke fuskar ta maida ƙofar ta rufe had'i da kallon A'ishah tai mata murmushi tace
"Thanks" murmushi A'ishah itama ta mayar mata tace
"Shut up! What family's for?" ƙara fad'ad'a murmushin ta tayi bata ce komi ba "Muje ne?" cewar A'ishah, jinjina kai tayi gami da cewa
"Yeah muje" a hankali A'ishah ta ja motar wacce dama on slow take suka tafi, cikin raha suke hira har suka iso gidan.


Bud'e motar suka yi dukansu suka fito suna ƙarewa gidan kallo, danƙareren mansion ne naji da fad'a a haka suka kutsa kai cikin gidan, ita kad'ai ce a cikin parlorn da tarin takardu a gaban ta, da sallama suka yi at once suka shiga da fara'a ta tarbe su yayin da dukansu suka rusuna suka gaida ta

"Lafiya ƙalau" ta amsa musu cike da fara'a "Ya gida ya maman ku?"
"Tana lafiya, tace ma mu gaida ki" cewar A'ishah, murmushi Mammy tayi sosai had'i da cewa
"Ina amsawa" shuru suka yi gaba daya Mammy ta d'aga murya tayi kiran me aikin ta in just a minutes tazo ta umurce ta da taje ta kawowa baƙi abun motsa baki da hanzari ta miƙe don cika umurnin uwargidan ta, anan ne take Mammy ke sanar dasu dawowar Bassam akan idan sunje gida su gayawa Hajiya Zainab suka amsa da toh. A haka sukai ta hira wanda mafi yawan hirar da A'ishah ne, Kausar dama ba gwanar surutu bace ba abunda take sai game da wayar ta shigowar Bassam ne ya katse hirar A'ishah da Mammy...


Sanye yake da white singlet da white pyjamas, tafiya yake cike da ƙasaita yana danne-danne a wayar sa yayin da d'aya hannun sa riƙe yake da mold wanda lipton ne a ciki. Har ya shigo parlorn bai d'ago kansa daga wayar ba, shigowar sa ce ta katse hirar Mammy da A'ishah, murmushi Mammy tayi gami da cewa
"Kin ganshi ma" galala haka A'ishah ta saki baki da hanci tana kallon Bassam a ranta tace _he's damn hot_ yayin da shi sam baisan suna a parlorn ba yayin da ita kuma Kausar sam hankalin ta baya tare dasu game d'inta kawai take bugawa cikin kwanciyar hankali. Sai a lokacin ya d'ago lumsassun idanun sa manya-manya wanda ko yaushe cikin glasses suke banda yau yana kallon su, baice dasu uffan ba ya zauna akan sofa next to wacce A'ishah da Kausar suke a kai, a sanyaye murya ƙasa-ƙasa A'ishah tace
"Ina wuni" ko kallon ta baiyi ba sai danne-dannen sa yake a waya disdainfully, jin A'ishah ta gaida wani ne ya sanya Kausar d'ago kanta don ganin waye, kallon sa kawai tayi ta maida kanta a game d'inta wanda sam Bassam d'in baisan tayi ba yayin da A'ishah kam kunya ce ta lulluɓe ta, murmushi Mammy tayi tace
"Bassam?"
"Yes" ya fad'a had'i da d'ago kansa yana kallon Mammy
"Baka ji ba ana gaida ka?" kallon A'ishah yayi had'i da cewa
"Oh!" ya ajiye cup na lipton d'insa a ƙasa had'i da miƙa mata hannu yace "Sorry Muhammad Bassam Muhammad" duk rashin kunya na A'ishah haka ta tsaya sororo tana staring wa palm nasa ta kasa cewa komai, da ƙyar ta miƙa masa hannu in return suka gaisa tace
"A'ishah Bala" wani gajeren murmushi yayi yace
"Pleased to meet you" sai a lokacin ya saki hannun ta gami da mayar da kansa a wayar, duk abunda ya faru akan idon Kausar taɓa baki tayi had'i da cigaba da game da take, a sanyaye A'ishah ta d'auki handbag nata tace
"Zamu tafi Mammy"
"Da sauri haka?" cewar Mammy, murmushi kawai A'ishah tayi she is totally weak tun lokacin da suka yi shaking hands da Bassam "All right ina zuwa" Mammy ta fad'a da sauri ta hau upstairs ta barsu anan yayin da mutumen har lokacin hankalin sa na akan wayar sa ba'a dad'e ba sai ga Mammy ta sauko riƙe da leda cike da turaruka da mayuka ta miƙawa A'ishah, hannu biyu A'ishah tasa ta amsa suka yi godiya ta rakosu har bakin mota suka shiga taja sai a lokacin ta juya ta koma parlor.


Driving kawai A'ishah keyi amma jikin ta sam ba ƙwari, parking motar tayi suka tsaya gefen titi chak
"Lafiya?" cewar Kausar
"I can't drive" A'ishah ta amsa a taƙaice
"What? Baki lafiya ne?"
"Mtsww.. Banza! Ba wannan ba"
"Then..?" cewar Kausar
"Kausar that guy is really hot tunda muka yi shaking hands ya gama weaken jiki na"
"Mtsww.. You must be crazy! After what he have just done to you"
"Ke kika san wannan" cewar A'ishah "To me I guess I don't love untill now" mamaki ne ya kama Kausar tace
"He just shunned you fa, what if it was in public?"
"So?" cewar A'ishah "Ke fa kika san wannan baki ji abunda naji bane I'll do whatever it takes to win over him komai izzar sa" hararar A'ishah tayi tace
"Yanzu ya za'ayi? Zaki iya driving d'in ne ko kuwa?"
"Ba zan iya ba wallahi, zo ki ja" cewar A'ishah had'i da bud'e murfin ƙofar suka yi exchanging seats Kausar taja had'i da juyowa ta kalli A'ishah wacce ta jingina a seat ta lumshe idanun ta tace
"Alhamdulillah! Kema ga taki masifar nan on the way" dariya A'ishah ta fashe yayin da itama Kausar dariyar take tace "A'ishah please muje mu gaida Amma it's been a while"
"Ok muje" cewar A'ishah "It's not yet maghrib ai" ta fad'a tana duba agogon hannun ta, a hankali Kausar ta juya akalar motar suka nufi gidan su. Sun sha hira da Amma da Abba har maghrib tayi suka yi sallah suka ci abinci sa'annan suka juyo zuwa gida.


Isowar su ne yasa gaban Kausar mummunan fad'uwa, tsintar kanta tayi cikin yanayi na ƙunci wanda batasan dalili ba kamar kada su dawo gidan. A sanyaye ta bud'e motar ta fita bata jira A'ishah ba ta nufi cikin gidan, bata samu kowa a parlorn ba straight ta wuce bedroom d'insu, shigar ta ne kawai ta fad'a kan gadon ruf da ciki wasu hawaye da batasan ko na meye ba suka gangaro mata a haka A'ishah ta shigo d'akin ta same ta, da sauri ta goge hawayen kada A'ishah ta gani ta tashi ta shiga bathroom gami da wanke fuskarta ta fito, kwantawa tayi nan take bacci yayi awon gaba da ita.





*It'z Shawty*💕
[1/8, 7:37 AM] ‪+234 813 551 5123‬: *BARR. BASSAM*
(The Gallant) ❣



By *Shawty*💕

*PURE MOMENT OF LIFE WRITERS*
(We don't just entertain and educate, we also touch the hearts of the readers.)

*2017*

1⃣6⃣


~Ta kasa tsaye ta kasa zaune sai waige-waige take. Babban fili ne tsananin girma da haske ta kasa tantance gabas da yamma kudu da arewa duk iyakar ganin ta wannan filin ne me uban haske, tana cikin wannan yanayin ne ta hango wani abu a dunƙule baƙi ƙirin yana nufato ta da gudun tsiya, tsayawa tayi tana kallon abun har ya ƙariso wurin ta sai a lokacin ta gane wasu munanan tsutsotsi ne manya-manya marar kyan gani haka suka zo a guje suka fallatsar mata a fuska. Hannu tasa had'i da kare fuskar ta amma duk da haka sai da jinin wad'annan munanan tsutsotsin ya fallatsar mata a hannu, wata mahaukaciyar dariya me sauti da amo taji an fashe from nowhere, ji tayi wurin na girgiza da ita wane ana girgizar ƙasa ne duk inda hankalin ta yayi dubu sai da ya tashi haka ta fad'i sumammiya a wurin.~


"Innalillahi wa inna ilayhi raji'un" da wannan kalmar ta tashi daga bakin ta, zufa ce ke tsiyaya ta ko ina daga jikin ta sai numfashi take mayarwa. A'ishah wacce ke zaune da system a gaban ta tana kallo sai kallon ta take tana nazari, juyowa Kausar tayi tana kallon A'ishah har yanzu a razane take
"Ai wallahi idan ba zaki daina kallon Zombies ba kin cigaba da ganin su a mafarkin ki kenan" cewar A'ishah
"A'ishah it's not about Zombies, this is more dangerous, more evil" cewar

Please Login or Register in order to submit comment