Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Mammy bana santa, kawai ina tausayin ta ne" wani fake smile Mammy tayi tace
"Good! Mr. Moral Authority, let me make myself clear idan ma bacci kake yi to ka farka 'cause ko bayan raina ba zaka aura Kausar ba wallahi" cikin d'aurewar kai yace
"Why? Mammy this is not you, wannan fa ba halin ki bane, beside ni ban gaya miki zan aura Kausar ba" mik'ewa tayi tsaye ta kalle sa tayi wane gajeren murmushi tace

"Sanin kanka ne bana san talaka, kuma na d'auka yanzu ma zaka kalli ido na ne ka gayamin sai ka aure ta" sai da ta tabbatar kallon da take masa ya nutsar dashi sa'annan ta juya ta nufi upstairs. Kasa motsawa Bassam yayi ba abunda yake sai tunani, ba'a d'auki lokaci ba sai gashi ta fito ta sako gele da takalmi had'i da d'auko handbag kallon sa tayi tace "Zan fita" jinjina kai yayi a sanyaye ya kasa ce da ita komai yayin da ita kuma tasa kai ta fice.





*Shawty*💕
[1/8, 5:01 PM] ‪+234 813 551 5123‬: *BARR. BASSAM*
(The Gallant) ❣





By *Shawty*💕


*2017*


3⃣3⃣


🎶 *Lemme tell you something about a beautiful girl called Aysher... She's a black amazing girl like she came from Malaysia.. Her voice so sweet like Alicia... Her eyes so white like ruwan sha... She's so cute like a shining star...*🎶 A short lil poem to my sweethearted A'ishah, thanks for all the love and support you have for this novel. *ILYSM💞*

_________________________________________

Kwance yayi wurin uwa mara lafiya ya rasa abunda ke masa dad'i, maganganun Mammy sun matuk'ar tab'a sa, da k'yar ya iya mik'ewa yaje ya had'a tea duk cikin d'imbin kalan breakfast da aka shirya shima da k'yar ya iya shanyewa. Mik'ewa yayi ya suri keys na motar sa ya fice.



Gefen Mammy kuwa tafe take har ta iso unguwar su Kausar kamar yadda Hajiya Zainab ta kwatanta mata, bata san lokacin da ta daki steering motar ba tace
"What a disgust! Dama wannan jejin ne Bassam ke zuwa?" cigaba da tuk'in tai tayi har ta iso k'ofar gidan da take tunanin nan ne gidan da yake unguwar ba wani house number ba komai, wasu yara ta gani a wuri ta tambaye su ko nan ne gidan su Kausar suka ce eh, gyara zaman gelen ta tayi sa'annan ta doshi k'ofar gidan. Buga k'ofar tayi da k'arfi ta kunna kai cikin gidan, Amma ce rik'e da tsintsiya tana shara yayin da Abba ke gefe kan tabarma zaune ya kishingid'a yana rik'e da carbi yana lazimi, kallon su Mammy keyi cike da kyankyami tana yatsina fuska yayin da Amma ta tsaya cak da sharar shima Abba ya tashi zaune. Shiru Mammy tayi bata ce dasu uffan ba sai wani kallon banza da take jifar su dashi, Amma ce ta katse shirun ta d'an yi murmushi tace

"Baiwar Allah sannu da zuwa" a banzace haka Mammy ke kallon su yayin da Amma ta shiga d'aki ta fito da tabarma ta malala ta daga gefe had'i da cewa "K'ariso mana" sai yatsina fuska Mammy keyi tace

"Ba zama ya kawo ni ba kuma koda zaman zanyi ba akan wannan tsummakaran ba" mamaki ya dad'e da lullub'e Abba da Amma cikin d'aurewar kai Amma tace
"Ke kuwa baiwar Allah meke tafe dake?"
"Yanzu kika yi magana" cewar Mammy had'i da k'arasowa kusa dasu tace "Zuwa nayi na gargad'e ku daga ku har 'yar ku..." cikin rawar murya saura kiris Amma ta fashe da kuka tace
"Baiwar Allah me kuma muka yi? Me Kausar tayi?" wani fake smile Mammy tayi tace
"My son is worth everything to me, as I'm sure Kausar is to you. And if I lost him or felt like someone has taken him away from me I will pursue any remedy possible, so saboda haka nazo na rok'e ku da Allah ku fita daga hanyar yaro na" cikin d'aurewar kai Amma ta kalli Abba sa'annan ta maida kallon ta akan Mammy tace
"Baiwar Allah ki fad'a da hausa yanda zamu fahimta" cikin kakkausar murya Mammy tace
"Suna na Barr. Hindu Alhassan niche mahaifiyar Bassam kuma nazo ne na rok'e ku da Allah ku fita hanyar yaro na, Bassam is off limits to you" sai yanzu Amma da Abba suka hango kamannin da ke akwai tsakanin Mammy da Bassam wanda ba ainihin kama bace sai dai a kira shi da shigen jini, cikin kakkausar murya Mammy tace "Zan k'ara jaddada muku ku fita hanyar yaro na, nan gaba idan kuna da buk'atar wani abu get it your damn self, Bassam is not your errand boy" duk da cewar Amma bata jin turanci maganganun Mammy sun tab'a zuciyar ta don kuwa tasan maganganu ne cike da cin fuska da wulakanci, a fusace tace

"Kin kasa hana shi ne shiyasa kika zo rok'ar mu? Ai inace ke mahaifiyar sa ce kinfi mu iko akan shi saboda haka ki koma ki sanar dashi nima ya fita hanyar 'ya ta dan kwa bamu gayyace sa a cikin rayuwar mu ba, Kausar Allah ne gatan.." bata k'arisa ba kuka yaci k'arfin ta yayin da Mammy tayi tsaye sororo tana kallon Amma don kuwa bata tab'a tunanin kalamai irin wannan daga bakin Amma ba, mik'ewa Abba yayi yayi wa Amma alamar tayi shiru da hannu sa'annan ya kalli Mammy yace
"Kiyi hak'uri baiwar Allah in shaa Allah zamu fita hanyar Bassam, kiyi hak'uri" shiru Mammy tayi sa'annan taja tsuki tace
"Aikin banza!" ta kama hanyar fita daga gidan yayin da Amma kuka me ban tausayi ta fashe dashi, lallashin ta Abba ya shiga yi yana bata baki akan tayi hak'uri Allah yana tare da su da haka har ya samu ta daina kukan.



Gefen Bassam kuma bayan ya fito ya hau titi ne wayar sa dake ajiye gefen sa ta fara ringing, dubawa yayi yaga number ce ba suna a hankali ya kai hannun sa ya d'auko wayar had'i da amsa kiran, muryar namiji yaji tace
"Assalamu alaikum" cikin muryar sa me sanyi shima ya amsa da
"Wa alaikumus salam"
"Barrister kana magana da Alhaji Bala mahaifin marigayiya A'ishah" d'an gajeren murmushi Bassam yayi yace
"Ah Allah sarki"
"Barrister ya aiki?" cewar Alhaji Bala, nan ma cikin sanyin murya Bassam ya amsa da
"Alhamdulillah" a tak'aice
"Dama Barrister na kira ne na nemi wata alfarma daga wurin ka"
"Ok inaji, name it" cewar Bassam

"Ko zaka iya ware minti talatin daga cikin ayyukan ka yau kazo ka same ni a gida na akwai maganar da zamu tattauna" shiru Bassam yayi na wasu mintuna sa'annan yace
"K'arfe nawa?"
"K'arfe hud'u zuwa biyar duk sanda kazo cikin lokacin daidai ne" shiru Bassam yayi yana tunani bai ce komai ba yayin da gefen Alhaji Bala a tunanin sa ma wayar ko ta tsinke ne da sauri yace "Hello! Barrister kana ji na?" ajiyar zuciya Bassam yayi yace
"Ina ji Allah ya kaimu lokacin"
"Ameen, nagode sosai Barrister" cewar Alhaji Bala
"Ba damuwa" Bassam ya amsa had'i da katse kiran ya cigaba da driving abinsa ba tare da ya kawo komai a ransa ba.



Driving yake har ya kawo asibitin yayi parking ya nufi hanyar d'akin da Kausar take ya tura k'ofar had'i da yin sallama, zaune ya ganta ta had'a kai da gwiwa tana kuka tana kiran sunan A'ishah hannun ta d'aya anyi cuffing nasa da k'arfen gadon, k'arasawa yayi yaja d'aya daga cikin plastic chairs dake wurin ya zauna yana kallon ta, d'ago kanta tayi tana kallon Bassam a hankali ta jingina kanta a bangon dake bayan ta ta cigaba da hawaye cikin sheshshekar kuka tana kiran A'ishah, cikin sanyin murya Bassam yace
"I know her death devastated you but weeping bitterly won't bring her back, nothing can. A'ishah is gone and it's terrible but we've got to live on" cikin d'acin rai Kausar tace
"See keep her out of this! This is not about her, this is about me" kallon ta Bassam keyi yanda take fizgo maganar as if wacce ta zautu, cikin kuka ta cigaba da cewa "Please ka taimake ni" gyara zama Bassam yayi da sauri yace
"Eheen.. Me kike so?" share hawayen ta tayi tace
"Nasan nan bada jimawa ba za'a kai maganar kotu, please ka taimake ni ka tsaya a gaban alk'ali ka tabbatar masa niche na kashe A'ishah"
"Subhanallah!" cewar Bassam, da sauri yace "Meyasa?"

" 'Cause I wanted to die my way! Haka nike so in mutu, all I wanted after A'ishah's death was to get out of this horrific nightmare world" a hankali ta fashe da kuka ta d'ago idanun ta tace "Barrister ka taimake ni nagaji da wannan rayuwar, nagaji wallahi. My life is worth nothing ka barsu su kashe ni dama abunda suke so kenan" tsintsar tausayin ta ne ya rufe Bassam yace
"Idan na tsaya a gaban alk'ali bazan gaya masa kawai kece kika kashe A'ishah ba, dole sai na fad'i dalili me zan gaya masa while kin kasa sanar dani komai?" girgiza kai Kausar keyi yayin da hawaye sun dad'e da wanke fuskar ta tace

"Kawai ka gaya masa haka abunda suke so suji kenan" sa'annan ta dakata ta share hawayen ta tayi gajeren murmushi tace "Barrister ba zaka iya kare ni ba, ka taimake ni kawai please..." sai kuma ta rushe da kuka, girgiza kai Bassam yayi yace
"I'm not stupid ba zan iya ba" cikin fushi ta d'ago kai tace

"Tam daga yau ka fita hanya ta! I'm not your little girl, I'm not your wife and I'm sure as hell not your problem" murmushi Bassam yayi yace
"You deserve better, Kausar" kallon sa take yanzu, jinjina kai yayi yace "Sosai! Explain to me why are you taking credit for something you didn't do? 'cause I know ba kece kika kashe A'ishah ba" mamaki ne ya cika Kausar, murmushi Bassam yayi yace "Of course! Ba kece kika kashe A'ishah ba I know when someone is lying" shiru suka yi sa'annan Bassam yace "Ki gayamin abunda kika sani we'll find them and we'll gonna make them pay, Kausar taimakon ki nake so inyi. You've got the hard part, you just leave the rest to me ok?" cikin fushi yanzu ma tayo kansa tace
"Why don't you just go and leave me the hell alone? Barrister kana tunanin nima ba taimakon ka nike ba? Walk away! That's the best help anyone can give you, mutanen nan da kake gani they are next level dangerous"

"So am I" cewar Bassam sai kallon ta yake yace "Don't take the blame for something that is not yours Kausar, ki gayamin waye ya kashe A'ishah ko kuma me kika sani game da kisan A'ishah and I promise you they ain't gonna get away with this" murya k'asa-k'asa Kausar tace
"Here is what I know... Stay out of this!"
"No.." bata barsa ya k'arisa ba ta daka masa tsawa tace

"I told you to stay away!" jinjina kai Bassam yayi ya mik'e tsaye ya nufi hanyar fita, cikin kuka Kausar tace "Abu d'aya na sani game da kisan A'ishah" da k'arfi Bassam ya juyo yana kallon ta yace
"Menene?" share hawayen ta tayi ta fuskanci Bassam sosai tace

"Duk wanda ya kashe A'ishah a wannan daren ba A'ishah yazo kashewa ba akasi aka samu ni akazo kashewa" gaban Bassam ya bala'in fad'uwa yace
"Kamar ya? Tell me in details" girgiza kai kawai Kausar keyi tana kuka hawaye sai gudu suke a kuncin ta kamar lalacaccen fanfo tace
"Wallahi abunda na sani kenan" shiru Bassam yayi bai k'ara takura mata akan sai ya k'ara sanin wani abu ba, murmushi yayi yace
"Thank you" shiru tayi ta kwanta lamo kan gadon tana wani azababben kuka, juyawa Bassam yayi ya bar d'akin yayi daidai da kawowar DPO wurin, gaisawa suka yi anan ne yake shaida wa Bassam yau za'a sallami Kausar kuma za'a mayar da ita cell kuma a yau za'a yi filing case d'in a kotu, jinjina kai Bassam yayi baice komai ba yayin da k'asan zuciyar sa yaji dad'i 'cause ko ba komai Kausar zata fita hannun mugayen 'yan sandan.








*Shawty*💕
[1/8, 5:47 PM] ‪+234 813 551 5123‬: *BARR. BASSAM*
(The Gallant) ❣





By *Shawty*💕


*2017*

3⃣4⃣


*Alhamdulillah! I'm now off the hook, thanks for your countless prayers.*


___________________________________________

Motar sa ya nufa kai tsaye ya shiga yaja, ya hau titi ne wani tunani yazo masa akan yaje yaga iyayen Kausar, juya akalar motar yayi ya nufi unguwar. A bakin k'ofar gidan yayi parking ya fito ya nufi gidan, tura k'ofar yayi ya shiga had'i da yin sallama, Abba ne zaune a tsakar gidan yana cin abinci, amsa masa sallamar yayi cike da sakin fuska yayin da Bassam ya k'arisa shigowa cikin gidan ya tsuguna ya gaida Abba, cikin fara'a Abba ya amsa masa ya k'arisa warware tabarmar da yake kai had'i da cewa

"Zauna mana" cikin jin nauyi Bassam ya zauna daga gefe suka k'ara gaisawa wanda yayi daidai da fitowar Amma daga d'aki, rusunawa Bassam yayi daga zaunen ya gaida ita, fuskar ta ba yabo ba fallasa ta amsa masa ta samu wuri itama ta zauna. Shiru ya biyo baya yayin da Abba ya rasa ta ina zai fara, wanke hannun sa Abba yayi yayi gyaran murya yace
"Bassam ya aiki?"
"Alhamdulillah" cewar Bassam sai kuma shiru ya biyo baya, jikin sa ne ya gaya masa ba lafiya don kuwa duk sakin fuskar da Amma ke masa yau ta kau, cikin sanyin murya yace "Abba lafiya kuwa? Ko akwai matsala ne?" d'ago kai Abba yayi yace
"Bassam mahaifiyar ka tazo nan gidan d'azu" gaban Bassam ya bala'in fad'uwa, cikin d'aurewar kai yace
"Mammy?" d'aga kai Abba yayi yace
"Tabbas!" Innalillahi wa innaa ilaihi raji'un abunda Bassam yace a ransa kenan, cikin sanyin murya Bassam yace
"Me ya faru Abba?" cike da rashin k'warin gwiwa Abba yace

"Toh tazo ta fad'i maganganu marasa dad'i tana cewa tabbas mu fita a hanyar ka" dafe kai Bassam yayi yayin da Abba ya cigaba da cewa "Kayi hak'uri Bassam, nasan kana da zuciyar alkhairi amma iyaye ba abun wasa bane musamman uwa saboda haka kayi hak'uri kayi yanda take so" shiru Bassam yayi baice uffan ba a gefe d'aya kuma zuciyar sa sai tafarfasa take "Mun gode sosai da abubuwan da kai mana Allah yayi albarka" cewar Abba, idanun sa ne suka kad'a suka yi ja wane garwashi ya mik'e yasa takalmin sa ya juya ya nufi hanyar fita, chan ya tsinto muryar Abba yace "Bassam" tsayawa Bassam yayi cak had'i da juyowa yana kallon Abba "Zo nan" cewar Abba, jiki sanyaye Bassam ya dawo yazo gaban Abba ya tsuguna, dafa kafad'ar sa Abba yayi yace "Kayi hak'uri Bassam, kamar yadda na gaya maka iyaye ba abun wasa bane kayi hak'uri kadda naji kaje mata da wannan zancen kayi mata yadda take so kaji ko?" jinjina kai Bassam yayi alamar toh sai lokacin Abba ya d'auke hannun sa daga kafad'arsa yace "Jeka Allah yai maka albarka, mun gode sosai" mik'ewa Bassam yayi kamar wanda k'wai ya fashewa a ciki ya nufi hanyar fita daga gidan, fad'awa mota yayi a sukwane ya nufi gida.


Isar sa gidan ya fara danna horn kamar ba gobe, da gudu me gadin ya fito ya wangale masa gate d'in ya danna cikin gidan, parking yayi da sauri ya nufi cikin gidan. Shigar sa parlorn ya sami Mammy zaune da system akan laps nata, d'ago kai tayi ta kalle sa ta d'anyi murmushi ta mayar da kanta akan system d'in
"Mammy" haka Bassam ya kira sunan ta his voice almost trembling saboda tsabar b'acin rai, d'ago kai Mammy tayi tace
"Yes sweetheart"
"Mammy mesa zaki min haka? Why for God sake?" ajiye system d'in tayi ta juyo ta fuskance sa tace
"Saboda naje nayi warning those worthless people zaka zo ka tsaya min aka kana neman duka na? Of course I warned them zaka iya zuwa ka doke ni" jikin sa ne yayi sanyi a hankali yace
"Amma Mammy kinsan what you did isn't fair ba?"
"Yeah saboda iyayen ka ne ba" ta amsa masa a tak'aice, yanzu kam he is speechless, shiru yayi yayin da idanun sa suka k'ara ja cikin kakkausar murya Mammy tace "Bassam mesa kake nema ka fifita iyayen Kausar a kaina?" a sanyaye yace
"Ba haka bane Mammy"
"Fine! Idan ba haka bane I want you to stay away from them" girgiza kansa ya shiga yi a hankali ya furta
"I can't and I won't" cikin sigar fushi da masifa Mammy ta fara mik'ewa tsaye yayin da Bassam ya juya ya fice daga parlorn ya bar Mammy tsaye a wurin.


Sashen sa ya nufa sai a lokacin ya ankara lokacin sallar azahar yayi alwala ya d'aura ya saka jalabiya fara irin ta maza ya nufi masallaci, bayan ya dawo bai nufi ta kan Mammy ba straight part d'insa ya nufa ya chanza jalabiyar zuwa shorts ya k'ara sanyin a.c ya kwanta kan luntsimemen gadon sa. Tunanin Kausar ne yazo masa yanzu haka idan an sallame ta asibitin tana in some kind of trash place, tausayin ta ne ya ziyarce sa a ransa yace she is too to experience such dilemma haka dai yai ta tunani har bacci yai awon gaba dashi.

Ba shine ya tashi ba sai past 4 da k'yar ya iya mik'ewa ya nufi bathroom ya watsa ruwa had'i da d'aura alwala yazo yayi sallah, yana zaune ne ya kasa tashi wayar sa ta fara ringing da k'yar ya d'aga had'i da cewa
"Hello?"
"Barrister Alhaji Bala ne ya maganar had'uwar mu ne?" yaji an amsa daga d'aya b'angaren, sai a lokacin ya tuna sunyi da Alhaji Bala zasu had'u da sauri yace

"Sorry I'm on my way" bai jira abunda zai fad'a ba ya katse kiran ya mik'e tsaye ya shirya cikin suit bak'i had'i da kafa glasses nasa na al'ada, fitowa yayi cikin tafiyar sa ta k'asaita ya nufi parking lot yayi daidai da fitowar Mammy farfajiyar gidan, ganin Bassam da tayi cikin shiga alamar fita zaiyi ta razana
"Wai me yake damun Bassam?" ta fad'a a fili yayin da shi kuwa Bassam har ya shiga mota me gadi ya bud'e masa gate d'in yaja ya fice, haka tai tsaye har ya fice daga gidan sa'annan ta koma ciki.


Gefen Bassam kuwa haka yai ta sharara gudu bai tsaya ko ina ba sai a gidan su Jabir, kiran sa yayi a waya yace ya fito yana waje, ba b'ata lokaci sai gashi ya fito suka gaisa Bassam yace
"Hurry up! Shiga ka chanza kazo mu tafi"
"Where?" cewar Jabir questioningly, kallon sa Bassam yayi yace
"Gidan Alhaji Bala" gyara tsayuwa Jabir yayi yace
"Ban gane ba, me zamuyi a gidan sa?" labarin kiran da Alhaji Bala yai masa ya bashi yace "Yi sauri please" jinjina kai Jabir yayi ya juya ya koma gidan, ba'a jima ba sai gashi ya fito cikin shiga ta k'ananan kaya ya bud'e gaban motar ya shiga Bassam yaja suka nufi gidan Alhaji Bala.


Horn d'aya Bassam ya danna sai ga me gadin ya bud'e gate d'in, jan motar yayi ya kutsa cikin harabar gidan ya samu guri yayi parking dukansu suka fito. Waige-waige suka shiga yi sai suka hango wani mutum cikin shiga ta 'yar ciki da babbar riga da hula dukansu farare yana tunkaro su wanda ya tabbatar musu da shine Alhaji Bala, isowa yayi ya mik'a musu hannu suka gaisa sa'annan Alhaji Bala yace
"Welcome to my kingdom Barrister" cikin barkwanci haka, dukansu dariya suka yi yayin da Bassam kuwa wani gajeren murmushi kawai yayi, kallon Jabir Alhaji Bala yayi then back to Bassam yace "Wannan fa?" murmushi Bassam yayi yace
"A friend" jinjina kai Alhaji Bala yayi yace
"I'm sorry amma kai kad'ai nake son gani" Bassam bai ji dad'in maganar ba amma dai ya kanne ya d'an buga kafad'ar Jabir yace
"Jira mu a mota, we won't take long" murmushi Jabir yayi yayin da Bassam da Alhaji Bala suka nufi wani sashe cikin gidan, iso Alhaji Bala yai masa ya zauna akan sofa yai crossing legs sa'annan shima Alhaji Bala ya zauna suka k'ara gaisawa yayinda Bassam ya kagara bai ji dalilin kiran sa ba, murmushi Alhaji Bala yayi yace
"Barrister wata alfarma nake nema a wurin ka"
"Alfarma kuma?" cewar Bassam sounding weird, jinjina kai Alhaji Bala yayi yace
"K'warai da gaske"
"Eheen.. Wacce irin alfarma ce?"
"Case na kisan A'ishah nike so ka fidda hannun ka a ciki" haka zancen yazo ma Bassam a diririce, cikin rashin fahimta yace
"Ban fahimce ka ba Alhaji" murmushi Alhaji Bala yayi yace
"Kamar yadda kaji ina so ka fidda hannun ka daga kisan A'ishah" murmushi Bassam yayi yace
"Saboda me? I think Mammy ya dace ka gayawa haka 'cause da ita kuke aiki" girgiza kai Alhaji Bala yayi yace
"Barrister yarinyar da kake k'ok'arin karewa ita ta kashe 'ya ta kana tunanin zan zuba ido na k'yale ta?" girgiza kai Bassam yayi yace
"Ba kariya kawai nike bata ba"
"Toh me kake yi?" cire glasses dake idon sa Bassam yayi ya kalli Alhaji Bala da kyau yace
"Nima ina taya ku binciken waye ya kashe A'ishah 'cause wacce kuke zargi ba ita bace" gaban Alhaji Bala ya bala'in fad'uwa amma ya danne ya jawo briefcase dake kusa dashi ya bud'e wanda kud'i ne cike a ciki ya tura gaban Bassam, kallon briefcase d'in Bassam yayi yace
"Wannan fa?" dogon numfashi Alhaji Bala yaja yace
"Kud'i ne 5M ba siyan ka zanyi ba ba kuma cin hanci bane"
"Toh miye?" cewar Bassam
"Kyauta ce" dariya Bassam yayi yace
"5M ba zasu iya sayan aiki na ba Alhaji" gyara zama Alhaji Bala yayi yace
"Ok will you settle for 10M?" dariya Bassam yayi ya rufe briefcase d'in ya tura gaban Alhaji Bala had'i da mik'ewa tsaye ya kafa glasses a fuskar sa yace
"I think I will only settle for the truth whether I liked it or not, ka bar kud'in ka Alhaji duk wanda yake da hannu a kisan A'ishah sooner or later gaskiya zatayi halin ta" shiru Alhaji Bala yayi ya kasa wani kwakkaran motsi, kallon sa Bassam yayi yace "With all due respect, thanks Allah kuma yaji kan A'ishah" a hankali ya juya ya fice daga parlorn. Tafe yake cikin tak'amar sa har ya kawo wurin da suka yi parking ya bud'e ya shiga yaja motar suka fice daga gidan.


Sai da suka hau titi sosai sa'annan Bassam ya cire glasses na fuskar sa ya kalli Jabir yace
"Jay ban yarda da guy nan ba"
"Waye?" cewar Jabir
"Wannan Alhajin mana" gyara zama Jabir yayi yace
"What about him? Ya kuka yi dashi?"
"Ban yarda dashi ba he's got something to hide"
"Me ya faru?" cewar Jabir


Please Login or Register in order to submit comment