Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

mata lokacin da ya b'ata, godiya yai mata a tak'aice ita kuma tayi congratulating nasa daidai lokacin ne Amma, Abba da Kausar suka iso wurin, fuuu Mammy ta wuce ta nufi motar ta ta shiga taja ta bar wurin haka Samira ma ya rage Bassam da Jabir sai su Abba anan suka k'ara yiwa Bassam godiya suka ce zasu je su samu keke-napep suje gida, hana su Bassam yayi yace su bari suyi dropping nasu da motar Jay, ba musu suka shiga baya duka su uku Bassam ya shiga gaba Jabir yaja suka bar wurin.










*Shawty*💕
[1/8, 7:59 PM] ‪+234 813 551 5123‬: *BARR. BASSAM*
(The Gallant) ❣






By *Shawty*💕



*2017*



5⃣0⃣


*My 50th, bulkiest, and last page goes to all my fans, wanda na sani da wanda bansani ba, nagode kwarai and thanks for your maximum support. Shawty ta gode walai.*✌🏻


Su Abba suka fara ajiyewa a gida anan suka k'ara yi musu godiya Bassam yace bakomai ai gida ne sannan suka yi sallama Jabir yaja motar suka nufi gidan su Bassam, har cikin gidan Jabir ya shiga da Bassam sannan yace zai koma, ba yanda Bassam baiyi ba akan ya shigo yaci abinci yace a'a, haka dole ya k'yale shi suka yi sallama yaja motar ya tafi. Bassam kuwa gefen sa ya nufa kai tsaye ya cire kayan yayi wanka ya shiga rama sallolin dake kansa 'cause tun lokacin da Alhaji Bala yasa aka tafi dashi baiyi sallah ko d'aya ba, bayan ya gama sallar ya chanza jalabiyar zuwa white three-quarter da white singlet ne yaga wasu pain killers wanda aka masa prescribing tun lokacin da aka harbe sa, d'aukar su yayi tare da wayoyin sa ya nufi sashen Mammy. Koda ya shiga parlorn bata nan straight dining ya nufa sai dai duk abunda aka dafa bai mar ba, kitchen ya nufa ya had'o Ahmad Tea ya dawo parlorn ya zauna ya fara sha, wayar shi ya kunna ya bud'e Twitter ai kuwa nan take yaga pictures d'insa da na Alhaji Bala sai running suke a social media, haka yaga Jay sai tweeting victory da suka samu yake over this asshole traitor, haka ma his grade friends lokacin da yake secondary school Abuja wanda yake da contact dasu sai congratulating nasa suke da fatar masa samun lafiya. Ba abunda yake sai murmushi kamar daga sama ya tsinto muryar Mammy tana cewa
"It's all about you today" murmushi yayi ya d'ago kansa yana kallon ta yayin da ita kuma ta duk'o tai masa peck a goshi had'i da shafa kansa tace "I'm proud of you Bassam" kallon tean Mammy tayi ta d'an b'ata fuska tace "Me haka?" d'an d'aga hannun sa sama yayi don kwa yasan yayi laifi, in a laughter haka yace
"Ahmad tea ne" b'ata fuska Mammy ta k'ara yi tace
"What did I told you about it?" har yanzu dariya yake yace
"It should only be taken after meal" kunnen sa taja tace
"Kunnan k'ashi ba?" 'yar k'ara ya saki da sauri ya rik'e hannun nata yace
"Mammy you're hurting me" sakin kunnan tayi ta zauna kusa dashi tace
"Sort of serves you right" sannan ta kalle sa tace "Let's talk about Samira" d'an dakatar da sipping tean yayi ya kalle ta yace
"Yes, what about her?" in a very serious face Mammy ke kallon sa tace
"She loves you" a diririce ya kalli Mammy yace
"So? Me take so? Me zan mata?" gyara zama Mammy tayi tace
"I want to hear your opinion" d'auke kansa yayi daga kallon ta ya b'ata fuska ya cigaba da sipping tean sa yace
"I'm not interested" murmushi Mammy tayi tace
"Kalle ni nan Bassam" juyowa yayi yana kallon ta tace "Kana san Kausar I know, and don't you dare deny it" jim yayi kad'an na wani lokaci sannan yace
"Ni bana san ta Mammy" murmushi Mammy tayi tace
"Toh wa kake so?" d'an juyar da kansa yayi yace
"Nobody" murmushi Mammy ta k'ara yi tace
"I know what's happening in you Bassam, kana san Kausar and some part of you don't want you to accept that" kallon ta yake a ransa yana jinjina maganganun ta sannan ta cigaba da cewa "But unfortunately bana san Kausar, kuma ba zaka aure ta ba" ajiye cup d'in yayi yace
"Toh ai ni Mammy ban gaya miki zan aura Kausar ba in fact bana san ta" murmushi Mammy tayi tace
"Then? Wa kake so?"
"Nobody" ya sake fad'a kamar d'azu, yanzu kam haushi taji sosai ta balbale sa da masifa tace
"Kar ka nemi rainan hankali mana, kamar ya baka san kowa? Ok fine I chose Samira for you" murmushi yayi yace
"Mammy cewa fa nayi dukansu I'm not interested" harara ta shiga jifar shi dashi daga k'arshe ta mike tsaye tace
"You choose to argue with me all the time right? Chill! Ka kawo wacce kake so I won't interfere again 'cause na lura ban isa ba" tana gama fad'ar haka ta juya ta bar wurin, komawa Bassam yayi kan kujerar ya kwanta had'i da lumshe idanun sa, shi da kansa yasan some part of him yana son Kausar but he don't wanna accept that kamar dai yadda Mammy tace. Na farko dai she's too young, ba zai iya zubar da kansa yace yana son wannan mitsitsiyar yarinyar ba, na biyu kuma ba ajinsa bace wanda ya tabbata yana daga cikin dalilin da yasa Mammy bata santa, shiru yayi a ransa yace bara kawai yaje da Samiran zata fi daidai dashi and at least Mammy tana santa za'a zauna lafiya.


******


Gefen Kausar kuwa bayan isar su gida wanka tayi ta wanke gashin kanta da kyau 'cause tun ranar da aka kashe A'ishah bai k'ara ganin ruwa ba, Amma ta bata wata jalabiya bak'a tasa sakamakon duk kayanta suna gidan Alhaji Bala, ai kuwa nan mutane 'yan uwa da abokan arziki suka fara tururuwa a gidan suna taya su farin ciki, har wasu daga cikin k'alilan abokan ta na school sunzo that's Ameerah and Maryam, friends na A'ishah ma sunzo Nailah and Kulthum sukai mata gaisuwa suka jajan ta mata abunda ya faru ai kuwa kamar sun tab'o ta haka ta saka su a gaba tai ta kuka suma haka sukai joining nata sukai ta rusa kuka musamman Nailah da Kulthum wanda awoyi kad'an kafin a kashe ta a daren ranar suna tare da ita wurin birthday, haka Nailah ta fiddo wayar ta ta shiga nunawa Kausar pics da suka yi a wurin birthdayn, wani sabon kuka Kausar ta fashe dashi tana duba hotunan wani wurin uwa ta kira ta ta amsa wani pic nasu tai karo dashi a cikin wayar suna a cikin mota zasu je skul da safe A'ishah ta d'auki selfie d'in yayin da Kausar bata ma sani ba kanta yana akan wani textbook, hawaye suka ciko mata ido ta nunawa Nailah pic d'in wacce itama kukan take, a hankali Nailah ta kalli pic d'in then back to Kausar tace
"Shine last dp nata" kuka Kausar ta sake fashewa dashi tayi jifa da wayar ta fad'a kan matattar katifar dake d'akin ta cigaba da rusa kuka.


******


_5:00pm_
Wuraren k'arfe biyar na marece haka Bassam ne zaune a harabar gidan ba abunda yake sai kallon tsuntsaye sai shawagi suke, k'arar bud'e gate d'in gidan yaji da sauri ya juya don ganin ko waye ai kuwa sai ga motar Jabir ta danno kai cikin gidan, murmushi Bassam yayi had'i da mik'ewa yaje ya taryo shi suka nufi apartment nasa, sai da ya zauna Bassam ya d'auko cups da drink ya zuba masu a hankali ya kalli Jabir yace
"Jay there's problem, serious problem" kallon sa Jay yayi yace
"Problem kuma?"
"Yeah" cewar Bassam "It's about Samira" gyara zama Jabir yayi yace
"Me ya faru?"
"Ta gama sayan Mammy mana wai ma ta zab'ar min Samiran" shiru Jabir yayi sannan Bassam ya cigaba da cewa "Man I'm thinking of going back to Scotland kawai" kallon sa Jabir keyi yace
"Why? Kaima kasan Mammy ba zata bari ba" furzar da iska yayi sannan yace
"It's all like hell here Jay" kallon sa Jay keyi yana nazarin fuskar sa yace
"Kausar" mamaki ya kama Bassam yace
"Kausar kuma?" k'ara fad'ad'a murmushin sa Jabir yayi yace
"Kana san Kausar and you don't want to admit that" girgiza kai Bassam yayi though yasan hakane amma dai yayi k'arfin hali yace
"Bana santa Jay, the only girl I ever wanted is Hannah" kallon sa Jay yayi cikin ido yace
"That was then but right now you're lying" haka dai sukai ta arguing, Bassam ya dage akan baya san Kausar while Jay ya kafe akan yana santa, tsuki Jay yaja yace "Shut up and pour me a drink please" murmushi Bassam yayi da haka suka cigaba da hira sai around 6 Jay yace zai tafi dama yazo ya gansa ne kawai da haka suka fito ya shiga wurin Mammy suka gaisa tayi congratulating nasa sosai sannan yai mata sallama ya fito Bassam ya raka shi har wurin mota suka yi sallama akan maybe zai shigo Chamber gobe, tuni Jabir ya katse shi yace ya bari har ya huta ya k'ara samun lafiya tukuna, godiya Bassam yai masa da haka suka rabu. Komawa yayi sashen sa ya chanza kayan jikin sa zuwa k'ananan kaya ya fesa turare ya suri wayoyin sa da keys na motar sa had'i da kafa glasses a fuskar sa ya fito ya nufi parking lot ya shiga motar yaja ya bar gidan, koda ya hau titi shi kansa baisan ina zaije ba bai kuma sha mamaki ba sai da yaga ya kama hanyar gidan su Kausar, mamakin kansa ya shiga yi kamar ya juyo ya dawo kuma dai ya cigaba da driving har ya iso k'ofar gidan yai parking. Ya dad'e cikin motar zaune sannan ya fito ya nufi k'ofar gidan ya tura k'yauren ya shiga, Amma ce kawai ya samu a tsakar gidan tana aiki yayin da Kausar tana cikin d'aki tare dasu Nailah, ganin Bassam yasa Amma sakin murmushi tai masa sannu da zuwa ta d'auko tabarma ta malala masa ya zauna anan ne take cewa su da suke so suje har gida suyi godiya kuma sai gashi ya riga su zuwa, murmushi kawai Bassam yayi ya tambaye ta Abba tace ai ya fita amma yana gab da dawowa jinjina kai Bassam yayi next wanda yaso ya tambaya Kausar ce sai dai ya kasa, haka suka cigaba da hira da Amma ana haka ne sai ga su Nailah sun fito daga d'akin su hud'u, kallon Bassam suka shiga yi kowaccen su yai mata kwarjini kuma duk sun shaida sa shine young lawyer da hotunan sa suke circulating on progress a matsayin wanda ya jajirce yayi probing mummunan aikin da Alhaji Bala ke aikatawa, basu tantance kyan sa ba sai yanzu da suka ganshi one on one a haka dai suka rusuna suka gaida shi sukai wa Amma sallama zasu tafi, godiya Amma tai musu da fatan Allah ya kiyaye yayi daidai da fitowar Kausar daga d'akin cikin abayar bak'a da wani long veil bak'i ta d'ora shi akanta ta rufe sauran jikin ta dashi, ganin Bassam yasa tayi murmushi ta gaida shi ya amsa a tak'aice ta sanar da Amma zata raka su Nailah k'ofar gida, amsawa Amma tayi da toh tabi bayan su Nailah suka bar gidan ya kuma yi daidai da dawowar Abba, tuni Bassam ya mik'e tsaye yai masa sannu da zuwa suka gaisa anan ne shima Abban ya maimaita masa abunda Amma tace, murmushi kawai Bassam yayi ana haka sai ga Kausar ta dawo daga raka k'awayen ta, kallo d'aya Bassam yai mata ya d'auke kansa a hankali tazo ta shige d'akin tayi kwanciyar ta. Hira suka cigaba da yi Bassam yace ya maganar makarantar Kausar Abba yace ba sauran maganar makaranta 'cause su basu da kudin da zasu cigaba da biya mata wannan makarantar. Sai kusan Maghreb Bassam yai sallama dasu ya tafi, straight gidan su Jay ya nufa bayan sunyi sallah ya d'auke sa suka je mall, kaya ya shiga d'ibar wa Kausar da kayakin amfani uwa mai had'a lefe bayan ya kwashi me isar sa suka fito ya biya suka sake komawa gidan su Jabir, anan ya bar masa kayan yace please ya taimaka masa ya kaiwa Kausar, ba musu Jabir ya amsa suka yi sallama ya tafi gida. A takaice dai Bassam sai da ya chanza rayuwar Kausar da iyayen ta suka dawo ba abunda suka nema suka rasa. Hajiya Zainab ma taji sauk'i kuma tazo har gida ta rok'i gafarar Kausar da iyayen ta suka ce bakomai ai.



*Two months later*
In those days Kausar ta saba da Bassam sosai shima haka, kusan kullum sai yaje gidan su sun sha hira sosai a waya ma haka, zan iya cewa itama ta falla ba kad'an ba sai dai bata da labarin shirye-shiryen auran sa da Samira is in progress haka ma su Abba don idan ba Jabir ba ba wanda Bassam ya sanar wa maganar auren. Tafe suke a mota kowannen su cikin suit sai dai Bassam ya bambanta 'cause ya saka glasses a fuskar sa, tafiya kawai suke amma ba wata hira da suke saboda da kaga Bassam kasan yana cikin damuwa, basu zarce ko ina ba sai wani makeken printing press Bassam yayi parking juyowa yayi ya kalli Jay yace
"Jeka ka karb'o please" bud'e mota Jay yayi ya nufi wurin, ba'a d'auki ten minutes ba sai gashi ya dawo da wata leda a hannu ya bud'e motar ya shiga ya shiga nuna wa Bassam invitation cards d'in da sukai masifar kyau, d'an tab'a baki Bassam yayi ya d'an dafe kansa da kusan kullum a cikin kwanakin ciwo yake masa, cike da damuwa Jabir ya kalle sa yace
"Man you're not doing fair to yourself, idan baka san auran ya kamata ka dakatar da abun ba wai ka saka kanka damuwa ba" kallon sa Bassam yayi sannan yai murmushin takaici yace
"I need to make heaven Jay, tun lokacin da na gama secondary school na bar Nigeria ba yanda Mammy bata yi ba kan na dawo bayan na gama karatu na nak'i, bayan kuma na dawo na fara case na Kausar, you all knew how that case turned out to a war between us but at last akayi nasara kuma ta hak'ura now Samira, it's too much I can't say no to her" shiru suka yi Jay bai ce komai ba Bassam yaja motar basu tsaya ko ina ba sai gidan su Samira, kiranta Bassam yayi a waya yace yana k'ofar gidan tace ya shigo yace sauri suke ta fito dai ba'a d'auki five minutes ba sai gashi ta fito, bud'e motar Bassam yayi ya fito ya taka ya isa gabanta ya tsaya ya zura duka hannayen sa cikin aljihu yana kallon ta ta cikin glasses yace
"Kinje gidan su Kausar kin gaya mata in any uncertain condition to stay away from your husband right? Well I'm not yet your husband, and just because I planned to marry you doesn't make me a shitty person, Kausar has nothing and absolutely nothing to do with this so keep her out" mamaki ya kama Samira yadda Bassam ke neman wulak'anta ta akan wannan aljanar yarinyar, gyara tsayuwar sa yayi yace "And I heard kince idan bata rabu dani ba zaki d'auki mataki right?" shiru tayi ta sunkuyar da kanta k'asa, cire glasses na fuskar sa yayi yace "Let me make myself clear, the second you hurt that girl I'm gonna hurt you worst you get that?" shiru tayi jikin ta yayi sanyi sai ga Jabir ya fito rik'e da ledar invitation cards d'in zai fara tsokanar Samira, dakatar dashi Bassam yayi ya mik'a masa hannu yace ya bashi ledar, ba musu Jabir ya mik'a masa ya juyo ya kalle ta had'i da mik'a mata ledar yace "Here" hannu biyu tasa ta karb'i ledar sannan yace "Ki fad'a kud'in da zai isheki nai miki transfer yanzu 'cause idan na bar nan wurin ba dole ne ki sake gani na ba and you don't have to send those clueless friends of yours to start chasing on me akan kud'i" hawaye ne suka zubo mata sannan yace "And please next time you want something ki kira ni ki gayamin not Mammy 'cause nine mai bada kud'in" hawaye suka shiga zarya a kumatun ta, tab'a baki Bassam yayi yace "Ke muke jira, kiyi magana" kuka ta fashe dashi a hankali Bassam ya juyo ya kalli Jabir ya d'an d'aga kafad'a in I don't care yace "Jay I think we are good to go na lura bata son kud'in" yana gama fad'ar haka ya juya ya nufi mota, da sauri ta d'ago kai tace
"Bassam" tsayawa yayi cak ta k'araso gaban sa tace "Akan Kausar ka zab'i ka wulak'anta ni?" jinjina kai yayi alamar eh yace
"Yeah who are we without principles? That's my decision and my decision is fucking better than yours" sannan ya kalli Jabir wanda shima mamaki ya kama sa bai tab'a tunanin Bassam yana da irin wannan halin ba sai yau, mayar da glasses d'in sa yayi a fuska yace "Muje" ya bud'e motar ya shiga Jabir ma ya shiga yaja suka bar wurin, sai da suka hau hanya Jabir yace
"Baka kyauta ba wallahi" juyowa Jabir yayi ya kalle sa yace
"Kasan abunda tayi kuwa? Gidan su Kausar taje d'azu fa tare da k'awayen ta they almost beat her, ni bansan abunda yake faruwa ba I called her she picked up tana ta kuka ashe tana tare da friend nata sai friend d'in ta karb'e wayar take gayamin abunda yake faruwa" tuni shima Jabir ya dawo daga goyon bayan ta da yaje da haka sukai ta hira har yayi dropping d'insa a gida shi kuma ya wuce gida. Koda ya isa gida sashen sa ya nufa kai tsaye yayi wanka yasa pajamas kawai ya d'auko kwalaben giyar sa ya saka a gaba ya fara kwankwad'a, Mammy ce ta turo k'ofar ta shigo ganin sa da tayi haka yasa ta k'araso jiki sanyaye ta zauna kusa dashi, invitation cards nata ya d'auko da na d'aurin aure wanda tace zata kaiwa dangin ta da na baban sa ya mik'a mata, cikin kulawa ta kalle sa tace
"Bassam ba zaka daina shan wannan ba ko?" kallon ta yayi sannan ya kauda kansa yace
"Mammy you have no idea what my life right now is like, no goddamn idea! I like shots! I take shots every day! Sometimes it's good to lose control" shiru tayi tana kallon sa ya bata tausayi ba kad'an ba tasan yana son Kausar amma ta rasa mesa yak'i ya yarda da haka, girgiza kai kawai tayi ta tashi ta bar d'akin.


******

_8:00pm_
Gefen Kausar kuwa taci kuka har ta godewa Allah, ita ba zuwan Samira da k'awayen ta gidan su yafi k'ona mata rai ba kamar Bassam zaiyi aure amma bata da labari, ko dama yasan tana san shi ne shiyasa ya nemi ya yarfa ta, kuka take yi ba ji ba gani kan cinyoyin Ameerah wacce sai shafa kanta take tana aikin bata hak'uri tace
"Bassam is a good man, he's just wrong this time kuma kece kike ganin baya sanki but he loves you I'm sorry he couldn't tell you that himself" wani kuka mai ban tausayi ta fashe dashi cikin sanyin murya Ameerah ta cigaba da cewa "Just because he's getting married that's not the end of it, there's hope. Had it been baya sanki he wouldn't risk his life to save you" kukan dai take tayi nan Amma ta shigo d'akin ta shiga yiwa Kausar fad'a akan duk abunda Bassam yai mata bata gode bane sai dan zaiyi aure zata zauna ta saka su a gaba tana kuka, haushi Amma taji ta fita d'akin a fusace ta barsu. Cigaba da lallashin ta Ameerah tayi a hankali wayar ta ta shiga ringing alamar shigowar kira, koda Ameerah taga Bassam ne kawai picking tayi ta mik'a mata yace ta fito yana waje, ba musu ta amsa da toh ta ajiye wayar ta gyara kwanciyar ta
"Au, ba zaki fita bane?" cewar Ameerah, kallon ta Kausar tayi da jajayen idanun ta tace
"Ba zanje ba ai gidan ba bak'on shi bane ya shigo idan da gaske yana san gani na" d'an wara ido Ameerah tayi tace
"Ok" ta mik'e ta fita taje ta cinno mata Amma akan Bassam yazo tace ba zata fita ba, ai kuwa tana jin haka ta zumbula hijab d'inta har k'asa ta fito, kicib'is suka yi da Amma bakin k'ofa zata shigo d'akin, wani kallo ta watsa mata da sauri ta wuce ta ta kama hanyar fita waje. Zaune yake cikin mota cikin shigar k'ananan kaya sai music ke flowing a hankali ga sanyin da motar ta d'auka, a sanyaye ta bud'e motar ta shiga k'amshin turaren sa da sanyin motar suka had'e wuri d'aya suka jefa ta cikin wani yanayi, a hankali ya kalle ta though akwai d'an duhu amma zaka gane tayi kuka plus muryar ta ma ta chanza, a sanyaye yace
"I'm sorry" cikin sanyin murya tace
"For what?"
"All of it, bansan Samira zata zo ba I would've stopped her" shiru tayi bata ce masa komai ba a sanyaye yace "Kukan me kika yi? Akan Samira ne ko kuwa me getting married?" hawaye suka ciko idon ta ta girgiza masa kai alamar a'a a ranta tana cewa wato kam yasan ma d'aya daga cikin wannan shi yasa ta kuka, murmushi yayi yace "Kausar there's problem, serious problem" mayar da hawayen tayi tace
"There's no problem" cikin wata irin murya taji yace
"Say your mind and that will be the end of your restlessness" kallon sa tayi cikin ido ta had'o duka confidence nata wuri d'aya tace
"I don't love you!" gabansa yayi mummunan fad'uwa yadda yaji maganar unexpected amma dai ya danne yace
"You're lying" kallon sa ta k'ara yi tace
"I'm not lying" tuni yanayin sa ya chanza idanun sa ma suka fara chanzawa yace
"You aren't?" gyad'a masa kai tayi alamar eh sannan ya gyara zaman sa suna kallon juna sosai yace "Look into my eyes and tell me that we weren't made for each other" maganar haka tazo mata a bazata jikin ta yayi sanyi sosai tace
"We weren't" kallon ta ya cigaba da yi yace
"Tell me that when I leave you, you don't turn to look at me" tuni hawaye suka sake ciko mata ido cikin murya raga-raga haka kamar zata fashe da kuka tace
"I don't" tuni shima idanun sa suka chanza launi zuwa ja hankalin sa yai masifar tashi, grabbing hannuwan ta yayi yace
"Tell me that nothing happen to you when I touch you" tuni hawayen da take b'oyewa suka zubo mata tace
"Nothing" matse hannayen ta yayi sosai cikin nashi yace
"Tell me that you don't want to come into my arms right now" yanzu kam kuka take sosai cikin muryar kuka tace
"I don't" ji yayi kamar yayi kururuwa yadda take shunning nasa duk da yasan ba gaskiya bane, cikin wata murya ta daban yace
"Look into my eyes just once and tell me that you don't love me" sai kuka take jikin ta yana rawa amma this time ta kasa kallon sa, voice nata sai trembling yake tace
"I don't" ta k'ara fashewa da kuka ta fad'a k'irjinsa, shima he can't help sai da hawaye ya cika masa ido ya shiga shafa

Please Login or Register in order to submit comment