Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

suka gangaro wa Mammy suka had'a ido da Jabir a sanyaye Mammy tace
"Me kuke so? Ku fad'a ko nawa kuke so za'a baku" dariya aka sake fashewa da ita sannan akace
"Ba kudi muke so ba shi muke so" sannan mutumen ya k'ara da cewa "Dalili d'aya yasa na d'aga wayar ki saboda ina so na baki sak'o wa wannan abokin aikin nasa" da sauri Mammy ta kalli Jabir shima ita yake kallo sannan aka cigaba da cewa "Ki gaya masa idan yana son rayuwar sa to ya fidda hannun sa a case d'innan, idan kuma yak'i kamar yadda maigidan sa yayi to zamu gauraya dashi, Bassam kuma ku cigaba da rok'a masa rahamar ubangiji don kuwa anan wurin da yake ba alamar rahama" kit aka kashe wayar, sulalewa Mammy tayi k'asa tana wani irin kuka sakamakon kalaman mutumen, yayin da shi kuwa Jabir sak'on da aka fad'i a kanshi ne yasa jikin sa yayi sanyi da sauri ya karb'i wayar Mammy ya sake dialing number Bassam sai dai tuni sun kashe wayar, kuka kawai Mammy keyi ba ji ba gani yayin da itama Samira jikin ta yayi bala'in sanyi haka suka zauna jigum-jigum, cikin muryar kuka Mammy tace
"Shikenan sun raba ni da Bassam!" tasowa Jabir yayi yazo gabanta ya tsuguna yace
"Mammy Bassam fa yana raye" kallon sa Mammy tayi da sauri tace
"Yana raye fa kace Jabir? Cewa yayi fa sai dai mu rok'a masa rahamar ubangiji" girgiza kai Jabir yayi yace
"His last statement was 'ba rahama a wurin da yake' kinga kenan yana raye basu rigaya sun kashe shi ba" shiru sai sheshshekar kukan ta kake jiyowa a hankali Jabir ya mik'e tsaye yace zaije ya kai report police station da gidajen radio da tv, gyad'a kai Mammy tayi yai musu sallama ya fito ya shiga motar sa ya bar gidan.


******


Gefen Alhaji Bala kuwa zaune suke dashi da Alhaji Kabeer a cikin gidan gonar suna ta hira abunsu suna annashuwa, wayar Alhaji Bala ce tayi ringing wanda ya dakatar da hirar ya d'aga had'i da cewa
"T.K kun same shi?"
"Mun same shi Alaji yanzu haka yana hannun mu" cewar T.K
"Good" cewar Alhaji Bala sannan ya k'ara da cewa "Ku tsanan ta matakan tsaro sosai please kada a samu matsala" jinjina kai T.K yayi yace
"Baka da damuwa Alaji" dariya Alhaji Bala yayi yace
"Idan komai ya daidaita kana da kaso mafi tsoka" dariya T.K ya kece da yace
"Nagode Alaji" sannan Alhaji Bala ya katse kiran ya kalli Alhaji Kabeer yayi murmushi yace
"Ba'a tab'a d'aga min hankali ba kamar wannan karon Kabeer, amma yanzu komai ya daidaita" dariya Alhaji Kabeer yayi yace
"Bala mugu ne kai" dariya suka kece da sai raha da annashuwa suke har maghrib tayi suka rabu kowa ya kama gaban sa.



*******



_8:00pm_
Alhaji Bala ne da Hajiya Zainab zaune a cikin parlor suna hira, zata iya cewa tun ranar da aka kashe A'ishah basu sake samun lokaci suka zauna suka yi hira mai tsawo ba kamar yau. Gefen Alhaji Bala kuwa tun bayan kisan A'ishah bai tab'a samun kwanciyar hankali ba kamar yau. Wayar ta Hajiya Zainab ta d'auko ta bude Whatsapp dinta, anan taci karo cikin group nasu na Ex-students na secondary school dinsu Mammy tayi posting sanarwar b'atan Bassam attached with his pictures almost ten, cike da mamaki Hajiya Zainab tace
"Innalillahi wa innaa ilayhi raji'un" kallon ta Alhaji Bala yayi yace
"Lafiya kuwa?" cikin tsintsar mamaki tace
"D'an Barr. Hindu Bassam ya b'ata wai" zaro ido munafukin yayi shima irin cikin mamakin nan yace
"Kada ki kawo min wasa Zainab, kada ki gayamin yaron Barr. Hindu ne ba'a gani ba" da sauri Hajiya Zainab tayi viewing pic din Bassam ta mika masa wayar tace
"Duba ka gani"
"Innalillahi!" cewar Alhaji Bala sannan ya kara da cewa "To garin yaya haka ta faru?"
"Ina zan sani nima yanzu nike ganin post din nata ai" cewar Hajiya Zainab, da sauri tayi dialing number Mammy sai da ta kusa tsinkewa sannan ta d'auka muryar ta ciki-ciki alamar tayi kuka har ta gaji tace
"Zainab" cikin alhini Hajiya Zainab tace
"Hindu labarin da na gani gaskiya ne?" hawaye ne suka zubowa Mammy tace
"Gaskiya ne Zainab, Bassam ya b'ata"
"Innalillahi wa innaa ilayhi raji'un" cewar Hajiya Zainab sannan tace "Tun yaushe? Garin yaya?" hawayen da suka zubo mata ta share tace
"Kinsan na gaya miki anyi attacking nasa an harbe shi ko?" da sauri Hajiya Zainab tace
"Eh hakane"
"Toh har an sallame shi daga asibiti yau ya shirya ya fita office tun fitar shi har yau bai dawo ba sai dazu abokin aikin sa ke sanar dani ai yaga motar sa a hanya sai dai baya ciki" sai dai tayi kokarin boye mata wasu ne suka kama Bassam, salati Hajiya Zainab ta shiga rafkawa yayin da Mammy ta fashe da kuka, a nan ne Hajiya Zainab ke shaida mata ai yanzu suna tare da Alhaji ne suke ganin labarin shima yana ta mamaki, a hankali ta juyo ta kalli Alhaji Bala ta mika masa wayar don ya jajanta mata al'amarin, amsar wayar Alhaji Bala yayi hadi da cewa
"Assalamu alaikum"
"Wa alaikumus salam" cewar Mammy muryar ta k'asa-k'asa, nan dai ya shiga jajanta mata da rarrashin ta tare da yi mata alk'awalin in shaa Allah za'a tsananta bincike kuma Bassam zai bayyana da izinin Allah, sosai Mammy kalaman Alhaji Bala suka dan kwantar mata da hankali tai masa godiya sannan suka yi sallama ya katse wayar ya mika wa Hajiya Zainab yace
"Kai abun tausayi sai kuka take" ajiyar zuciya Hajiya Zainab tayi tace
"Dole tayi kuka ai, itama shi kadai ne da ita" girgiza kai Alhaji Bala yayi cike da tausayi yace
"Allah sarki! Allah ya bayyana shi" da
"Ameen" Hajiya Zainab ta amsa Alhaji Bala ya mike tsaye ya haura ya nufi upstairs, yana shiga bedroom dinsa ya kece da wata mahaukaciyar dariya.











*Shawty*💕
[1/8, 7:47 PM] ‪+234 813 551 5123‬: *BARR. BASSAM*
(The Gallant) ❣





By *Shawty*💕


*2017*


4⃣7⃣


*_"People come in search of knowledge, but knowledge doesn't seek people."_* words of wisdom 👌🏻

_____________________________________

Bassam ne kwance kan siminti a d'ad'd'aure hannu da k'afa cikin wani d'an k'aramin d'aki mai duhu sai 'yar window 'yar k'arama wacce ta nan ne kawai haske da iska ke shigowa. A hankali ya fara bude idanun sa daga doguwar suman da yayi sakamakon dukan da sukai masa na fitar hankali, fuskar sa, bakin sa da kansa duk sun farfasa su sai jini ke fita yayin da raunin shi na k'irji inda suka harbe sa duk ya sha duka, raunin k'afar sa ma duk sun sa k'afa sun tattaka shi, rigar shi white long sleeve duk ta b'aci da jini a tak'aice duk wanda yasan Bassam idan ya gansa cikin halin da yake yanzu ba zai iya shaida shi ba. K'afafu hud'u ya gani wanda ya tabbatar masa da mutane ne tsaye a wurin, kokarin tashi zaune yayi T.K yasa k'afa daidai raunin sa na k'irji ya halba sa, k'ara mai tsananin azaba ya fasa ya koma kwance idanun sa rufe gam ya cije leb'en sa sakamakon wani masifar ciwo da yake ji a wurin, da sauri Alhaji Bala ya dakatar da T.K yace ya barshi haka ya isa, kallon Bassam sukai tayi wanda sai numfashi yake saukarwa a hankali d'aya bayan d'aya da ka ganshi kasan yana jin jiki. Kokarin tashi Bassam yayi a karo na biyu yayin da shi kuwa Alhaji Bala ganin haka yasa ya rage tsawon sa ya tsuguna kan k'afafun sa yana kallon shi yana murmushi, sai da ya tayar da kansa zaune ya bude idanun sa a hankali suka sauka kan fuskar Alhaji Bala wanda sai wani fake smile yake lokaci d'aya ya d'an b'ata fuska yace
"Sad to see you in such a state Barrister, your stubbornness leads you to all this mess" kallon sa Bassam keyi sannan Alhaji Bala yace "I confronted you with ten million Naira saboda kawai ka daina case dinnan amma kayi banza dani, na lallab'e ka na rarrashe ka amma duk a banza, Barrister is any cost too low for your survival?" kallon sa kawai Bassam keyi a hankali yayi wani gajeren murmushi sai dai bai ce komai ba, murmushi shima Alhaji Bala yayi yace "Unfortunately, I'm the kind of man that doesn't let anything stand on my way, when a snake is in your kitchen you don't invite it to a dinner, you cut off its head" dariya yanzu Bassam yayi yace
"Locking me up here is not smart, you know what?" kallon sa Alhaji Bala keyi yana jiran abunda zaice, a hankali Bassam yace "I promise I'll do what is needed to be done so, screw you!" murmushin takaici Alhaji Bala yayi don kuwa su T.K sun bashi labari tun randa aka kawo Bassam ba abunda yake sai gasa musu maganganu marasa dadi, a hankali Alhaji Bala ke kallon sa yace
"Are you always rude for people that are trying to help you?" murmushi Bassam yayi ya girgiza kai yace
"I'm not rude, I just say what others don't have the guts to say" a hankali ya saukar da numfashi hadi da lumshe idanun sa sakamakon zogin da k'irjin sa ke masa yace "You wanna stop me? Kill me then" dariya Alhaji Bala yayi yace
"Ba yanzu zan kashe ka ba sai ranar da aka yankewa Kausar hukuncin kisa kuma aka kashe ta, a ranar zan zo maka da wannan labarin then you'll know you definitely failed" murmushi Bassam yayi yace
"You are the one who failed 'cause you never fought someone to protect someone else" murtuke fuska Alhaji Bala yayi don kalaman Bassam sun fara tunzira shi yace
"Watch your words Barrister" kallon sa Bassam yayi cikin ido ba alamar tsoro tattare dashi yace
"Do your fucking worst blood-thirsty murderer!" da sauri T.K yayo kansa Alhaji Bala ya dakatar dashi, haushi T.K yaji yace
"Alaji ya zaka bar wannan d'an yarinyar yana fad'an abubuwan da yaga dama?"
"Barshi" cewar Alhaji Bala yana murmushi ya mike tsaye ya k'ara kallon Bassam da kyau yace
"You are as good as dead" sannan ya juyo ya kalli T.K yace "Ku bashi ruwa da abinci I don't wanna kill a plump corpse at last" dariya T.K ya fashe da ya jinjina kai ya fita d'akin, in two minutes sai gashi ya dawo d'auke da take away da ruwan gora yazo ya dire su gaban Bassam, ya tsuguna ya fara kwance masa hannayen sa, bayan ya gama ne ya mike tsaye Bassam ya kalli hannayen sa wanda har sun fara swelling saboda d'auri, murmushi kawai yayi ya d'auki robar ruwan ya kafa a bakin sa sai da ya shanye tas sannan ya rufe robar ya jefa ta a k'aton tumbin Alhaji Bala ya koma ya jingina da bango ya lumshe idanun sa hankalin sa kwance, da sauri T.K ya kalli Alhaji Bala cikin tsabar mamaki yayin da Alhaji Bala sai murmushi yake saboda wani lokacin rashin tsoron Bassam yana burge sa, cikin fushi T.K yace
"Alaji ka barni na yayyaga wannan gayen mana" girgiza kai Alhaji Bala yayi har yanzu sai murmushi yake yace
"Barshi" sannan ya juya ya fita, tsayawa T.K yayi ya d'aure hannayen Bassam sannan yabi bayan Alhaji Bala hadi da rufe d'akin saboda tsaro. Shiru Bassam yayi yana tunanin Mammyn sa baisan a wanne hali take ba, yasan by now tayi kuka har ta gaji haka ya gangaro zuwa kan Jay yasan sunyi neman shi har sun gaji, wani tausayin Mammyn sa ne yazo masa hawaye suka zubo masa amma har yanzu yana nan yana counting ranar da za'a sake sitting shari'ar.


******


Gefen Mammy kuwa labarin dai d'aya ne, kullum bata da aiki sai ta zuba hotunan Bassam a gaba tana kuka addu'ar ta Allah ya bayyana mata koda gawar Bassam ne, chamber ma ta daina zuwa ba inda take zuwa koda yaushe tana gida tana faman kuka yayin da kullum sai Samira tazo ta taya ta zama har maman ta da sisters nata sai da ta kawo suka jajantawa Mammy b'atan Bassam wanda ba k'aramin dad'i yake yiwa Mammy ba, kullum gidanta cikin tururuwar mutane yake 'yan uwa da abokan arziki suna zuwar mata da addu'ar Allah ya bayyana Bassam. Gefen Jabir kuwa sosai Mammy ta tsawata masa akan ya fita case dinnan musamman akan gargad'in da mutanen sukai masa, dama Jay matsoraci ne ba musu ya yarda shima ya daina fita chambers baki daya kullum yana gida yana juyayin Bassam kullum fatan su Allah ya bayyanar musu dashi safe and sound.


Gefen su Amma da Abba kuwa yanda aka watsa b'atan Bassam a kafofin yad'a labarai ne yasa suka samu labari tun daga ranar suka duk'ufa da addu'a da sallolin dare da bayar da saukar alk'ur'ani da rok'on Allah ya kub'utar da Kausar ya kuma bayyana Bassam. Shi kuwa Alhaji Bala duniya ta zame masa sabuwa dal, baya da wata damuwa threat d'insa guda biyu duka ya magance su, ba Alhaji Kabara Bassam kuwa yana a tsare sai jindad'in sa yake yana annashuwar sa.


******


_*On the very day*_
_9:00am_
Bassam ne zaune a d'ad'd'aure hannu da k'afa kamar koda yaushe ba abunda yake tunani sai Kausar yasan if he didn't show up in the court today, there's possibility a yanke mata hukuncin kisa, ba abunda yake sai rok'on Allah ya kawo masa hanyar da zai fita daga d'akin, yana nan zaune ne yaji surutun mutane biyu hadi da tab'a k'ofar alamar za'a shigo, gyara zama Bassam yayi sai gashi sun shigo, ba wasu bane sai su T.K dashi da abokin aikin nasa sunzo kawo masa breakfast, bayan T.K ya ajiye masa breakfast din ne ya fara kwance masa hannuwa don ya samu yaci abincin yayin da Bassam ba abunda yake sai kallon abokin aikin T.K don kuwa yana lura dashi yana da tausayi kuma duk azabtarwar da ake masa bai tab'a saka hannu ya dake shi ba hasalima sai dai yasa kai ya fice daga d'akin kawai. Bayan ya gama kwance masa hannun ne Bassam ya d'auki cup din yayi sipping daya ya ajiye still yana kallon abokin aikin T.K, juyowa abokin aikin yayi ya kalli T.K yace
"Baabaa ka d'an kwance guy nan a k'afafu ya d'an huta mana" kallon sa T.K yayi yace
"Ba za'a kwancen ba"
"Hab.." bai barsa ya k'arasa ba ya daka masa tsawa yace
"Nace ba za'a kwancen ba!" arguing suka shiga yi wanda yayi turning ya zama fad'an gaske sosai, kokawa suka shiga yi har abokin aikin ya samu ya tandara T.K a k'asa ya fiddo wata 'yar k'aramar wuk'a daga k'ugun shi ya nuna T.K da ita sai huci yake yace
"I won't hesitate to kill you man!" samun sa'ar shi T.K yayi ya buge hannun sa wanda yake rik'e da wuk'ar yayin da wuk'ar bata tsaya ko ina ba sai wurin Bassam, d'an gocewa wuk'ar Bassam yayi don gudun kada ta yanke sa ba abunda yake sai kallon show din su T.K, wuntsilar dashi T.K yayi ya fiddo bindiga daga k'ugun sa sai huci yake ya nuna shi da ita yace
"If you tested my patience again, then I've got enough bullets in this gun for you and him" ya juyo ya nuna Bassam da bindigar shima, tuni abokin aikin jikin sa ya shiga b'ari don ya tabbata ba k'aramin aikin T.K bane ya halbe sa da bindigar, surrender yayi ya d'aga hannuwan sa duka biyu, T.K bai ankara ba sai ji yayi ya buge hannun sa da bindigar nan take ya bude k'ofar ya fita a guje, da sauri T.K ya suri bindigar sa ya bi bayan shi da gudu suka bar k'ofar bude, Bassam na ganin haka ya d'auki wuk'ar ya yanka igiyoyin da aka d'aure shi a k'afa dasu ya mik'e tsaye sai dai ya manta k'afafun nasa akwai raunuka, fad'uwa yayi k'asa amma dai yayi dauriya ya sake mik'ewa tsaye, wani k'arfe ya gani wanda T.K yake dukan sa dashi mostly, hannu yasa ya d'auki k'arfen yaja k'afafun sa ya tura k'ofar ya koma daga bayan ta ya lab'e ya rik'e k'arfen da kyau daidai kuma lokacin ne ya jiyo k'arar gun shot har sau biyu da ihun abokin aikin T.K alamar ya kashe shi kenan, rintse idanun sa Bassam yayi ya gyara tsayuwar sa at that moment he's ready to kill, echo na sawun dawowar T.K yaji daga nesa har ya kawo k'ofar d'akin ya turo k'ofar, yana shigowa Bassam yai masa kyakkyawan duka da k'arfen a k'afafun sa wanda ba shiri ya saki bindigar had'i da k'walla k'ara ya rik'e k'afafun sa, da sauri Bassam ya d'auki bindigar ya nuna shi da ita, abu na farko da Bassam ya fara tambayar sa shine
"Where's my phone?" surrender T.K yayi ya d'aga hannayen sa duka biyu sama yace tana d'aya d'akin "Let's go!" cewar Bassam had'i da nuna masa hanya, ba musu T.K ya mik'e tsaye yana gaba Bassam na biye dashi har d'akin ya d'auko wayar da tarkacen I.D cards da ATM cards nashi ya mik'a wa Bassam, sai da Bassam ya kunna wayar ya tabbatar komi lafiya k'alau sannan ya saka ta aljihu ya nuna masa hanya alamar ya shige su tafi, lura dashi Bassam yayi like he's trying to act smart cikin kakkausar murya Bassam yace
"Don't try anything funny man, I have no regrets to blow up your brain, zan fasa kanka da bullet ne I don't fucking care!" jikin T.K tuni yayi sanyi da haka har suka fito waje, dube-dube Bassam ya shiga yi ya hango gawar abokin aikin sa a wurin da kuma motar da su T.K suke yawo da ita, nan ma cikin kakkausar murya Bassam yace "Pass me the keys" ba musu yasa hannu cikin aljihu ya fiddo key d'in motar ya jefa wa Bassam ta baya, duk'awa Bassam yayi ya d'auki keys d'in duk yana taka tsan-tsan sannan yace "Right, muje ka bud'en gate" nan ma ba musu T.K ya shige gaba Bassam yana baya har suka isa bakin gate d'in yasa hannu ya fiddo keys na gate d'in yayi unlocking nasu, tsawa Bassam ya daka masa yace "Open them wide!" ba musu ya wangale gate d'in sannan suka dawo daidai wurin motar, d'an ja baya Bassam yayi like almost five steps haka sannan yace "Turn" juyowa T.K yayi da niyyar ya buge Bassam ya karb'e bindigar sai dai yaga Bassam yayi nisa dashi, murmushi Bassam yayi without a second thought ya sakar masa bullets ta-ta-ta-ta har guda hudu a k'afafu, k'ara T.K ya k'walla ya fad'i k'asa yana ihu yana gurnani had'i da cewa
"Motherfucker!" da k'arfi, murmushi Bassam yayi ya k'araso kusa dashi gami da nuna kansa bindigar yana k'ok'arin sakar masa wani bullet yace
"The Motherfucker is unkillable!" da sauri T.K ya shiga rok'ar Bassam don yaga alamar da gaske halbin sa zai kuma yi da bindigar yace
"Dan girman Allah kayi hakuri, right now I mean you no harm ka shiga motar ka tafi kawai I promise you'll leave unharmed" k'ara murtuke fuska Bassam yayi ya k'ara nuna sa bindigar ready to shoot, kuka mai ban tausayi T.K ya fashe dashi ya shiga yiwa Bassam magiya, saukar da bindigar k'asa Bassam yayi sai ajiyar zuciya yake yace
"I don't kill with a gun, he who kills with a gun has forgotten the face of his father! I kill with my lips" (Already readers kunsan mahaifin Bassam he was a judge and judges they don't execute, but they give execution orders. Abunda Bassam yake nufi kenan meaning he'll kill them in the court.) kallon sa T.K yake cikin mamaki don kuwa bai tab'a tsammanin Bassam zaiyi sparing rayuwar sa ba, a hankali ya juya da baya da baya har ya isa wurin motar ya shiga yaja a 360 in a blink of an eye T.K ya neme sa wurin ya rasa, sai da Bassam ya fita ya jefar da bindigar a cikin daji ya cigaba da gudu kawai all the way daji ne yake gani gaba da bayan sa, haka ya rik'e motar cikin matsanancin gudu ba ji ba gani a hankali ya fara hango wani k'auye, k'arawa motar gudu yayi har ya iso k'auyen wanda mutane ne ke wurin suna saye da sayarwar su. Parking Bassam yayi ya fito daga motar, ganin da mutane sukai masa jina-jina ne yasa suka yo kansa da gudu had'i da tambayar sa lafiya, a hankali Bassam yace
"Nan ina ne dan Allah?" d'aya daga cikin mutanen ya shaida masa wani local government ne cikin Sokoto, jinjina kai Bassam yayi yaga wani mai sayar da fetur a bakin hanya yace
"Ko zaku iya taimako na?" har suna had'a baki mutanen suka ce
"Taimakon me kake so bawan Allah?"
"Mai nike so ku zuba min a mota wanda zai kaini Sokoto amma ba kudi a tare dani" mamaki ya kama mutanen wani daga cikin su yace
"Kaga yanda kake kuwa? A haka zaka hau hanya jina-jina?" gyad'a kai Bassam yayi yace
"Dole ne ta kama ku taimake ni dan Allah" wani daga cikin mutanen yace a zuba masa man da zai isa ya isar dashi Sokoto shi zai biya kud'in, nan take aka zuba masa Bassam yayi godiya ya shiga motar ya sake fisgar ta cikin matsanancin gudu ya bar mutanen k'auyen cikin al'ajabi. Tafe yake yana tambaya har Allah ya iso dashi garin Sokoto, nan ma tambayar hanyar da zata sada shi da unguwar su Jabir yayi aka nuna masa, cikin ikon Allah kuwa ya gane har k'ofar gidan yayi parking ya fito yana jan k'afar sa sai layi yake kamar mashayi yayi knocking gate d'in gidan, nan take mai gadin yazo ya bud'e ganin Bassam ne ya cika shi da mamaki baki hangame yace
"Bassam kaine kuwa?" jinjina kai Bassam yayi alamar eh yace
"Jabir fa? Yana ciki?" da sauri me gadin ya rik'o shi don yaga yana alamar fad'uwa suka shigo gidan sai ga Jay ya fito daga shi sai singlet da shorts, ganin Bassam a halin da ya ganshi ne yasa ya banzamo da gudu yayo kanshi, rik'e shi da kyau Bassam yayi yace
"Jabir jeka ka kawon wig and gown d'inka" zaro ido Jay yayi yace
"What? You came in here pretty bloody kake tunanin zan barka ka fita wani wurin ai sai dai muje asibiti" wani kallo Bassam ya jefe shi dashi yace
"And do you think you can stop me? I'm afraid they are looking for me shiyasa banje gida ba I would've not come to you" cike da damuwa Jay yace
"Bassam a haka zaka je kotu?" jinjina kai Bassam yayi yace
"I have no choice time is against us right now, jeka ka kawon please kuma kazo da keys na chamber zanje na d'auki wannan written note d'in" juyawa Jabir yayi ya koma cikin gida, samun wuri Bassam yayi a k'asa ya zauna daidai lokacin ya fiddo wayar sa ya bud'e Whatsapp ai kuwa sai ga messages na voice notes attached with a message daga cyber wizard d'in, murmushi Bassam yayi yai downloading d'insu gaba d'aya yayi daidai da fitowar Jay cikin shigar suit da wig and gown a hannu, suka rankayo suka fito at first Bassam so yayi yai driving Jay ya hana shi suka shiga motar Jabir suka bar wacce Bassam yazo da ita Jay yaja motar suka bar gidan. Sai da suka fara zuwa

Please Login or Register in order to submit comment