Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD

katafaren mall, sayayyar kayan abinci ya shiga yi da kayan amfani sai da ya kashe kud'i masu yawa sa'annan ya fito yasa yara suka saka masa a boot ya sallame su yaja motar sa ya nufi gidan su Kausar. Isar sa nan ma yara ya sake nema suka fara d'ibar kayan suna shiga dasu cikin gidan sai da suka kwashe su tsaf sa'annan ya sallame su ya shiga gidan. Koda ya shiga gidan mamaki ne ya hango a fuskokin su, murmushi yayi ya k'arisa kusa dasu ya rusuna ya gaida Abbah had'i da tambayar sa ya mai jiki ya amsa da sauk'i amma wacce ke zaune daga gefe alamar taji sauk'i ba laifi itama suka gaisa ya tambaye ta ya jikin ta amsa masa da sauk'i sosai sai a lokacin Abbah ke tambayar sa wannan kayan fa yace shi ya kawo musu godiya suka shiga yi masa don kuwa ko abunda zasu ci basu dashi Abbah har da kuka, Bassam ji yake wane yayi ihu ya tsani kuka a rayuwar sa lallashin su ya shiga yi akan bakomai ae gida ne. Sai a lokacin Amma ke shaida musu jiya taje gidan Alhaji Bala tana rok'on su su saka baki a saki Kausar da ta dawo ne jiri ya fara kwasar ta sai rashin lafiya, fusata Abbah yayi yace daga yau kada ta k'ara komawa gidan su Allah bai manta dasu ba, shima Bassam ya goyi bayan Abbah yace kada ta k'ara zuwa su bar masa komai a hannun sa godiya suka yi mai d'imbin yawa ya mik'e yace zai je Police Station d'in, Abbah da Amma dukan su they feel safe with Bassam suna jin Allah ya kawo masu Bassam ne a lokacin da suke tsananin buk'atar taimako, rako sa Abbah yayi yana ta faman yi masa godiya har ya shiga motar sa yaja zuwa Police Station d'in.


Isowar sa Police Station d'in yayi daidai da fitowar wani d'an sanda da gudu d'auke da Kausar a hannu unconscious da alama bata san ina kanta yake ba wane ta mutu, zuciyar Bassam ta buga da k'arfi cikin tashin hankali ya cire glasses d'in don ya k'ara tabbatar da abunda ya gani, Kausar d'in dai ce ya gani suke k'ok'arin sakawa mota yayin da DPO ya fito da gudu saura k'iris ya fad'i sai command yake bayarwa da gudu suka ja motar suka bar wurin. Da gudun gaske Bassam ma ya rufa musu baya basu zarce ko ina ba sai asibiti, ba b'ata lokaci aka yi admitting nata a hankali Bassam ya fito ya sami DPO bakin mota sai kai komo yake, ganin Bassam tsaye tall a gaban sa ya zura duka hannun sa biyu cikin aljihun sa yana kallon sa ne yasa gaban sa ya bala'in rikitowa, ba alamar wasa a fuskar Bassam ya k'araso kusa dashi ya basa hannu suka gaisa mutumen duk ya tsinke da ganin Bassam jikin sa sai rawa yake, cikin murya k'asa-k'asa Bassam yace

"Me ya same ta ne?" tsoro ya k'ara kama d'an sandan sai rawa muryar sa keyi tana stammering yace
"Yaran ne suka matsa da tambayar ta aka had'u da tsautsayi ta suma" jinjina kai Bassam yayi sa'annan ya cire glasses dake fuskar sa don d'an sandan ya samu damar hango tsintsar rashin mutuncin dake cikin idanun sa yace
"Officer I'm a glass half-full kind of guy, the second wani abu ya sami yarinyar nan..." yayi wani fake smile "Ku kuka da kanku" ya juya ya bar wurin, jikin d'an sandan sai rawa yake yayin da Bassam ya koma gefe ya fiddo wayar sa ya kira Jabir yace ya samesa a asibitin. Isowar Jabir ne yake gaya masa abunda yake faruwa kuma ya sha alwashin the moment wani abu ya samu Kausar tam there's gonna be an embarrassing shit.


Gefe DPO ya koma ya kira wayar Alhaji Bala ya fara irga masa abunda yake faruwa, kwantar masa da hankali Alhaji Bala ya shiga yi kuma yai masa alk'awalin ba abunda zai same ta kuma ya shaida masa da taji sauk'i kar ya jira komai su maka case d'in kotu sai a lokacin hankalin d'an sandan ya kwanta ya katse kiran.


Bayan likitan ya bada umarnin ganin ta ne Bassam da Jabir suka shiga d'akin, zuciyar Bassam ce ta buga da k'arfi lokacin da ya ganta kwance kan gado, ja yayi ya tsaya ya kasa k'arisawa cikin d'akin ba komai ya gani ba sai fuskar ta da tayi jajir ta kumbura tai suntum duk da cewa Kausar me dara-daran idanu ce amma yau sun shige flat da fuskar wane basu alamar duka gefen kanta bleeding yake wanda aka sa bandage aka tsayar dashi sauran sassan jikin ta ya gani duk alamar duka ya bayyana don kuwa duk yayi ja, hawayen da yake k'ok'arin b'oyewa ne suka gangaro masa cikin ransa yace haka 'yan sanda suka mayar da this beautiful kid. K'arasowa yayi daf da gadon yana kallon ta cike da tausayi, chan ya tsinto muryar Jabir yana cewa
"Ka kuwa sanar da iyayen ta?" girgiza kai Bassam yayi alamar a'a "Meyasa? 'Yar su ce fa" cewar Jabir, dogon numfashi Bassam yaja yace
"Ba amfanin haka Jabir ba abunda zai haddasa musu illah b'acin rai jiya ma maman ta har BP nata sai da yayi sama kaga idan aka gaya musu kamar an d'aga hankalin su ne" jinjina kai Jabir ya shiga yi sa'annan Bassam yace

"Watch the kid, zanje in dawo yanzu" nan ma jinjina kai Jabir yayi a hankali ya juya ya fice daga d'akin ya nufi parking lot ya shiga motar sa yaja, bai tsaya ko ina ba sai gidan su Kausar yayi faking da cewar yazo ne ya k'ara ganin jikin Amma while ba haka bane yazo ne cikin hikima ya dakatar dasu daga zuwa Police Station d'in kada su fahimci me yake faruwa koda ya bar gidan k'arfe biyu na rana sai a lokacin ya samu kansa ya tuna ko breakfast baiyi ba, karkata akalar motar sa yayi ya nufi gida.




*Readers akwai k'ura fa*😳







*It'z Shawty*πŸ’•
[1/8, 3:41 PM] β€ͺ+234 813 551 5123‬: *BARR. BASSAM*
(The Gallant) ❣




By *Shawty*πŸ’•

*2017*

3⃣1⃣


_Feenah, Ummi Lolo and Abeederh here is your page. I can't help but smile anytime I'm seeing your comments, for every page you guys must comment in your best amazing sense of humor and that makes me tripping. From the bottom of my heart, *ILYSM*_πŸ’ž


__________________________________________

Koda ya isa gida yayi parking bai gan motar Mammy ba wanda ya tabbatar masa bata dawo ba, sashen Mammy ya fara shiga yaci abinci saboda wata mahaukaciyar yunwa da yake ji sa'annan ya nufi sashen sa yayi wanka yayi sallah ya chanza suit dake jikin sa zuwa k'ananan kaya ya suri keys d'in motar sa ya fito ya nufi parking lot yayi daidai da kunnowar motar Mammy cikin gidan, dakatar da shiga motar yayi yaje ya same ta ya bud'e mata k'ofar mota had'i da cewa
"Sannu da zuwa Mammy" ciki-ciki ta amsa masa da
"Yauwa" sa'annan ta fito daga motar, kallon sa ta k'ara yi tace "Har yaushe ka dawo da zaka sake fita?" d'an d'aga kafad'un sa yayi yace
"Yanzun nan"
"Ina kuma zaka je?" k'arya yai mata yace

"Wurin girlfriend nawa" murmushi tayi don a yanzu ba abunda tafi so irin taga Bassam yayi aure, shi kuma ya tabbatar hakane kawai zai gaya mata a zauna lafiya. Cikin fara'a tace
"Ok ka gaida ta" murmushi yayi ya jinjina kai sa'annan ya juya ya shiga motar sa yaja ya bar gidan, sai da yaje ya fara siyan abinci with everything da mara lafiya zai buk'ata sa'annan ya wuce asibitin. Shigar sa d'akin ya samu Jabir zaune gefe kuma d'an sanda ne a tsaye, a hankali ya fara shigowa d'akin yace

"Jay" juyowa Jabir yayi had'i da yin murmushi yace
"Yanzu nike cewa zan kira ka Mom wants to see me"
"Ayyah! Sorry" cewar Bassam "I think you gotta go, nima naje gida ne shiyasa" mik'ewa Jabir yayi yace
"Ok Allah ya k'ara sauk'i but har yanzu dai bata motsa ba" jinjina kai Bassam yayi yana kallon Kausar sa'annan suka gaisa Jabir ya tafi. K'arasowa yayi suka gaisa da d'an sandan sa'annan shima ya fita ya koma daga bakin k'ofar d'akin saboda tsaro wanda yayi saura d'akin daga Kausar wacce ke kwance sai Bassam. Kujerar da Jabir ya tashi yaja daf da bakin gadon Kausar ya zauna ya fara kallon ta, ya dad'e yana kallon ta sa'annan ya fiddo wayar sa yana dannawa yana jiran tsammanin tashin ta.


_5:00pm_
Alhaji Bala ne da Alhaji Kabeer zaune akan kujeru cikin makekiyar gidan gonan Alhaji Bala, rausayar da kai Alhaji Bala yayi yace
"D'azu DPO ya kirani yake sanar dani cewar 'yan sanda sunyi wa yarinyar duka har ta suma yanzu haka tana asibiti"
"Ta suma kuma?" cewar Alhaji Kabeer, jinjina kai Alhaji Bala yayi yace
"Haka yake gayamin, ina tunanin na aika T.K asibitin su kashe ta kawai" da sauri Alhaji Kabeer ya kalle sa yace
"Kul Bala! Kada ka kuskura kayi wannan gangancin" kallon sa Alhaji Bala yayi cikin mamaki yace
"Meyasa?"
"Wannan ganganci ne, idan har kasa aka kashe ta to kuwa kallo zai koma sama ne, hankalin mutane zai karkata akan wa ya kashe ta kuma dole suyi tunanin akwai gaskiya a tare da yarinyar har aka bi ta aka kashe" jinjina kai Alhaji Bala ya shiga yi alamar akwai k'amshin gaskiya a maganar Alhaji Kabeer sa'annan yace "Ka bari kawai akai maganar kotu sai kabi alk'alan da lauyoyin duka ka siye su da kud'i shikenan ka gama da case na kisan A'ishah har abada" har yanzu Alhaji Bala sai gyad'a kai yake sa'annan Kabeer yace "Ka kwantar da hankalin ka Bala, kana da kud'i shine babban makamin ka a wannan tafiyar" dogon numfashi Alhaji Bala ya saukar yace
"Akwai wata barazanar da take tunkaro ni Kabeer" gyara zama Alhaji Kabeer yayi yace
"Menene?"
"Akwai wani matashin lauya wanda ya tsaya wa yarinyar kai da fata mai taurin kan tsiya, na saka T.K ya kira sa a waya ya gargad'e sa amma T.K ya shaida min sam yaron baiyi panicking ba kuma kasan me?" girgiza kai Alhaji Kabeer yayi alamar a'a "Mahaifiyar yaron k'awar Zainab ce itama lauya ce kuma ita zata tsaya mana a kotu" shuru Alhaji Kabeer yayi yana kallon k'asa sa'annan yace
"Ka kira sa ka sauke wannan girman kan nasa da Naira kamar yadda kayi da DPO idan kuma yak'i sai ka kawar dashi kawai" kallon sa Alhaji Bala yayi yace

"Kabeer ba zan cigaba da kisan mutane ba, cigaba da kisan su yana nufin tonon asiri a wuri na saboda bazan iya yak'ar su lokaci d'aya ba"
"Ok zaka zura masa ido kenan?" cewar Alhaji Kabeer, shuru Alhaji Bala yayi ya kasa cewa uffan "Bala dole kayi maganin sa fa" jinjina kai Alhaji Bala yayi yace
"Hakane, Kabeer ni fa wannan al'amarin na fara gajiyawa wallahi"
"Kamar ya? Ban fahimce ka ba" cewar Alhaji Kabeer
"Da an rufe wannan matsalar lokacin ne wata zata taso, ka duba fa tun lokacin da hukumar EFCC tace zata yi bincike akan dukiya ta har yanzu ba kwanciyar hankali a tattare dani" murmushi Alhaji Kabeer yayi yace
"Alamar nasara kenan Bala, da yardar Allah nasara a hannun ka take" shuru suka yi na wani lokaci sa'annan suka chanza wata hirar.


_6:00pm_
Har k'arfe shida na marece Bassam na zaune a asibitin tare da Kausar, motsi yaga k'afar ta nayi wanda yasa ya d'ago kai yana kallon ta, ta juya nan ta juya nan ta shiga yi bisa gadon a hankali kuma ta bar juye-juye ta fara motsa idanun ta da suka yi nauyi tana so ta bud'e su sai dai haske yai mata yawa, da k'yar dai ta samu ta bud'e idanun tana kallon d'akin sa'annan idanun ta suka sauka a kan Bassam, murmushi yai mata sai kuma ta fara k'ok'arin tashi amma ba dama sakamakon matsanancin ciwo da jikin ta keyi, komawa tayi kwance ta fashe da kuka wanda ya bawa Bassam tausayi, matsowa yayi kusa da gadon yace
"Sannu" kallon sa tayi ta mik'a masa hannu alamar ya tada ita zaune, pillow yasa a bayan ta ya d'auke ta cak ya jingina ta a pillow yace "Yayi haka?" jinjina masa kai tayi sa'annan ta had'a kai da gwiwa ta fashe da kuka, tausayin ta ya masifar kama Bassam a hankali ya rik'o hannun ta d'aya ya had'a da nasa duka biyu a sanyaye yace

"Stay strong it solves every problem, I know bad things have a tendency to happen to good people but you'll get through this in shaa Allah" juyo da idanun ta tayi ta kalle sa fuskar ta ga baki d'aya hawaye ya wanke ta, jinjina mata kai Bassam yayi had'i da yin murmushi yace "In shaa Allah I give you my words" kallon sa take a sanyaye tace
"Thank you" murmushi yayi yaji dad'i da tai masa magana atleast ta fara yarda dashi kenan, kallon ta yayi yace
"Zaki iya cin abinci?" da sauri tai masa nodding alamar eh, abincin ya d'auko with intention ya bata a baki tace ya bata da hannun ta zata iya ci, ba musu ya mik'a mata. Abun ya basa tausayi da mamaki yadda yaga take cin abincin wane wacce bata tab'a ci ba, sai da ta kusa cinye abincin sa'annan ta mik'a masa sauran tace ta k'oshi, ruwa ya d'auko zai bata nan ma tace zata iya ya bata tasha da kanta sa'annan ya d'auko magungunan da aka siyo, ai kwa nan fir tace ita bata san ta sha magani ba, bud'e idanu Bassam yayi wide in suprise ta sake kallon sa cikin ido tace ba zata sha ba, ajiye maganin yayi yace
"Well, barin je in kira doctor ta yiwu allura kika fi so" had'i da juyawa kamar zai bar d'akin, ihu ta fasa ta zame daga kan pillow ta fashe da kuka, da sauri Bassam ya dawo yai kanta had'i da cewa "Easy! Menene?" chan k'asa-k'asa tai masa whispering
"Zan sha maganin" murmushi yayi ya gyara mata zaman ya d'auko maganin, da d'aya-d'aya ya dinga bata har ta shanye duka sa'annan ya rabu da ita. Wayar sa ya d'auko ya fara dannawa koda ya k'ara d'ago kansa yaga har bacci yayi awon gaba da ita, kwantar da ita yayi sa'annan ya juya ya fita d'akin ya sanar da d'an sandan ya duba ta zai je ya dawo. Koda ya fito ana shirin sallar maghrib sai da yayi sallah sa'annan ya nufi gida.





*It'z Shawty*πŸ’•
[1/8, 4:56 PM] β€ͺ+234 813 551 5123‬: *BARR. BASSAM*
(The Gallant) ❣




By *Shawty*πŸ’•


*2017*

3⃣2⃣


_Nancy, Serayah, Nens and Leslie (future Americans sensation🀣) I dey hello. This chappy is for y'all a cigaba da slaying_✌🏻😁


_*#TEAMBASSAM*❣ just know that words ain't enough to describe how happy I am for your warm wishes and prayers. I've received all your messages and they don't go unnoticed, if only I could fly to your various places and hug you up but I believe this is a good way to say thank you and God bless you_

__________________________________________

Isowar sa gida har duhu ya fara sauka, parking yayi ya nufi sashen Mammy kai tsaye shigar sa parlorn zumbur Mammy ta mik'e tsaye jikin ta har rawa yake alamar shi kawai take jira tace

"Ina kaje?" kallon ta yake cike da mamaki yadda ya hango tsintsar masifa a idon ta, a sanyaye yace
"Mamm.." bata barsa ya k'arisa ba ta sake daka masa tsawa
"I said ina kaje and don't you dare lie to me" wani murmushi tayi cike da takaici tace "From that blood-thirsty murderer right?" shiru yayi jikin sa gaba ki d'aya yayi sanyi, kamar saukar aradu haka ya sake tsinto muryar ta a masifance tace "Right?" jinjina mata kai yayi a hankali alamar eh, wani murmushin takaici ta sake yi cikin fad'a tace "Bassam what have you gotten yourself into? A ina kake so ka saka kanka ne? Ka san ko wacece ita? Kasan miye manufar ta? Do you know what she is up to? Look sweetheart, you are walking into some weird-ass shit" a sanyaye Bassam yace
"Mammy I just wanna help"
"I wanna help too, and I want you to do the same but not that way not with them"
"Mammy I think we need to re-think this, we need to right enemy, we need to be absolutely certain who did this before we strike" murtuke fuska tayi yanzu tam tace
"Bassam who's Hindu Alhassan to you?" tsoron yanayin da ya ganta ciki ya kama sa ya kasa magana, tsawa ta daka masa tace "I said who's Hindu Alhassan to you? Ko baka jin turanci ne?" idanun sa suka kad'a suka yi jajir cikin sanyin murya yace
"She's my mother"
"Fine! Let me put an end to this argument today, right here! Idan har na isa da kai ina umurtar ka ka fidda hannun ka a case d'innan, see not just this case har wanchan banzayen mutanen, I heard har provision kake musu right?" kallon ta yake cike da mamaki, murmushi tayi tace "Of course! Kana mamaki ya akayi na sani ko? Call me selfish Bassam, but I'd rather want to see you take care of yourself than doing something that can't be done. The more you continue to fight against this, a fight you can't possibly win" kallon ta kawai yake he can't believe what is happening like is this even happening? Ta ya zata hana masa aikin sa, chan ya tsinto muryar ta tana cewa "I'm sorry sweetheart, we are living in a different world than we were yesterday. Mutane basu da amana Bassam, zaka iya jajircewa ka taimaki mutum at last ya cuce ka just like abunda Kausar tay wa Zainab da mijin ta, bana san irin haka ya same ka. You can't just keep charging into this, the girl might need something from you and rushing in blindly could be it"

"Mammy I don't care what happen to me, come what may!" mamaki ne ya kama ta bata san lokacin da ta wanke sa tas da mari ba tace
"Bassam are you nuts? Ni kake gayawa haka? Bari in shaida maka what I had to do is to protect you ba zan barka kana engaging kanka da wannan yarinyar ba, wannan witch d'in? Ah haba" idanun sa suka k'ara kad'awa suka yi wani masifar ja, murya k'asa-k'asa yace
"Mammy stop calling her names! The best way to proceed is to treat her as a witness not a suspect. I just want to make sure that your emotions are not clouding the fact that this was clearly a set-up. No disrespect and I'm sorry to say... I won't stop and I'll make sure I bring justice into this" mamaki ne ya rufe Mammy zufa ta shiga zubo mata duk uban a.c dake akwai d'akin, cikin sark'ewar murya tace
"Bassam you choose those poor people of all people over me? Your mother?" girgiza kai yayi had'i da rik'o shoulders nata, ture sa tayi da sauri tace "Have a nice ride to them sweetheart, kaje wurin iyayen Kausar" tana gama fad'ar haka ta juya ta haura sama, bayan ta yabi da sauri amma inaa bai same ta ba tana shiga bedroom d'in ta mayar da k'ofa ta rufe, haka yai ta tsayuwa ya rasa abunda zaiyi daga k'arshe dai ya nufi sashen sa.



Wanka yayi sa'annan yai sallah, straight fridge ya wuce ya d'auko kwalaben Vodka da Liquor d'insa yazo ya dire su akan bedside drawer, sake fita yayi ya d'auko cup yazo ya fara kwankwad'ar giyar sa kamar ba gobe sai da ya shanye kwalba d'aya sa'annan ya kwanta ya runtse idanun sa, wani zafi yake ji k'irjin sa na masa ga wani ciwon kai duk suka had'e masa a guri d'aya. Gefen Mammy kuwa abun damunta yai tayi bata san lokacin da ta sauko ta nufi part d'in Bassam ba, da sallama ta shiga had'i da tura k'ofar bata same shi a parlor ba kai tsaye ta nufi bedroom. Hango shi tayi bakomai a jikin sa sai shorts kwance yayi ruf da ciki, k'arasawa tayi wurin gadon wanda gaban ta yayi mummunan fad'uwa da ta hango kwalaben giya akan bedside drawer, hannu tasa ta d'auko su tana dubawa a fusace ta ajiye su ta fara jijjiga shi tana kiran sunan sa, inaa sam baiji ta ba haka taji hawaye na zuba akan kuncin ta, kasa hak'ura tayi ta zauna gefen gadon ta rushe da kuka sai da tayi me isar ta sa'annan ta mik'e zumbur kamar wacce aka tsikara ta nufi sashen ta. Bedroom d'inta ta nufa da sauri tana shiga ta suri wayar ta ta fara neman wayar Hajiya Zainab, ringing biyu ta d'aga had'i da cewa
"Hello Hindu" muryar Mammy har tana rawa tace
"Please Zainab wacce unguwa iyayen Kausar suke zaune?"
"Me yake faruwa ne? Ya naji muryar ki ba a yadda na saba jin ta ba?" Mammy wacce sai kai komo take tana zufa tace
"Bassam ne! He's turning into something else Zainab, baya jin magana ta, na kasa fahimtar abunda yake damunsa duk akan wa'annan matsiyatan mutanen" cikin d'aurewar kai Hajiya Zainab tace

"Kamar ya? Yi min bayani sosai mana" cikin rawar murya Mammy tace
"Ina tufka yana warwara mana, shi zai tsaya wa yarinyar a kotu nikam Zainab wannan wanne irin abun kunya ne?" salati Hajiya Zainab ta shiga rafkawa tace
"Bassam d'in?"
"Shi fa! Nima kaina I'm as shocked as you, kawai ki gayamin unguwar da iyayen ta suke gobe zanje in gargad'e su su fita a hanyar yaro na" dogon numfashi Hajiya Zainab ta saukar tace
"Gaskiya kam" ta fara yi mata kwatancen gidan su Kausar, godiya Mammy tayi ta katse kiran, a tak'aice dai wannan daren bata samu tayi baccin arziki ba Allah-Allah take gari ya waye.



_The next day_
Tun da sassafe tayi wanka ta shirya tsaf cikin wani lace blue da ratsin fari, zaune take cikin katafaren parlorn tayi crossing legs tana jiran shigowar Bassam. B'angaren Bassam kuwa sai da ya shirya tsaf cikin k'ananan kaya sa'annan ya nufi b'angaren Mammy, shigowar sa ne ya hango ta zaune tayi crossing legs fuskar ta ba rahama sai kallon tv take. Ta jiyo sallamar sa amma saboda haushin sa da take ji ta kasa amsa sallamar. K'arasowa yayi ya zauna kusa da ita yace
"Morning" juyowa tayi fuskar nan a tamke tana kallon idanun sa tace
"You're slipping, wai me yake damun ka ne? A wace rayuwa kake neman jefa kanka?" a sanyaye yace
"I'm fine" murmushin yake tayi tace
"You're fine? Like when I found you passed out on your bed last night?" yanzu ma cikin sanyin murya yace
"Na sha wani muscle reliever ne" fad'a ta fara yi wane zata cinye sa d'anye tace
"Vodka? Liquor? Sune muscle reliever? Tell me what else have you been taking" shiru yayi yanzu bece da ita uffan ba, d'ago fuskar sa tayi tace "Bassam kalle ni nan" d'ago kansa yayi yana kallon ta, murya k'asa-k'asa tace "Kana san Kausar ko?" haka tambayar tazo masa banbarakwai, murmushi Mammy take tana jinjina kai tace "Of course! Kana san Kausar I know" tunani ya shiga yi shi dai a iyakar sanin sa ba son Kausar yake ba kawai yana tausayin rayuwar da suke ciki, a sanyaye yace
"No
DOWNLOAD
DOWNLOAD

Please Login or Register in order to submit comment