Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Daddyn Manal??"

Ganin zai fadi yasa Momy tayi wata kara tayi kanshi.


Anuwar na zaune bisa bed dinshi rike da kai.

Jin karar Momy yasa yayi saurin zabura!!

Yayo waje cikin sauri.

Ya iske Momy ta girgiza Daddy su Nifra na kuka.


Cikin tashin hankali ya iso wajen.

Kursim ce tayi saurin kiran Security.

Dan danan aka kira Doctor's sai gasu sun iso.


Suka shiga dashi suka rufe daki.


Momy tace;"Anu meyasa baka jin magana meyasa kake son kashe Daddyn ku, kayi masa biyayya mana, meyasa shin baka son Daddyn naku ya cigaba da rayuwa?".

Shiru yayi idanun shi cike da hawaye saide basu zubo ba.

Tace;"yanzu sai ka zaba, ko rayuwar Daddyn ku ko yarinyar kauye, zabi ya rage naka".

Daga haka tayi hanyar d'akin ta tana kuka.

Nifra tabi bayan ta tana kuka.

Kursim ta taso tazo inda yake.

Itama hawaye take tace;"Haba Prince rayuwar mutun nawa kasa cikin kunci, hadda Daddyn masoyi yarka, kasa mahaifiyar ta kuka, kasa kanwar ta kuka, shin da tana da rai kana tunanin zata yi alfahari da kai? kayi hakuri kayi ma iyayen ka biyayya mana"


Kallon ta yayi yace;"itama fa waccen mutun ce, an shiga hakkin ta tana bukata ta"


Kara matsowa tayi ta rungume shi tace;"Yanzu kodan lafiyar Daddy kayi hakuri da zuwa Katsina kabari hankali ya kwanta nayi maka alkawarin idan muka koma zan taimaka maka wajen gano yarinyar".

Cikin sauri Anuwar shima ya kara rungume ta jin zata taimaka mashi.

So sai Kursim taji dadin rungumar yau itace rana ta farko da Yarima ya rungume ta a jikin shi.


Hakan yasa hawayen ta suka kasa daukewa.

A bangaren Anuwar ya shagalta jinta yayi tamkar mai furar shi,hakan yasa ya kara manneta da jikin shi, yana sakin numfashi.


A haka Momy ta iske su, jin tafiya yasa Kursim ta dan zame jikin ta.

Anuwar kuma sai lokacin ya lura ashe Kursim ce.

Dan ja da baya yayi, Momy na kallan shi.

Ganin kallon da take mashi yasa yabar wajen.


Ya koma dakin shi, ya zauna tare da dafe kai.

Yanzu idan yayi mata haka bai mata adalci ba.


Amman babu yadda zaiyi.

Tunda ya kusan ceta ya rasa meyasa yanzu jin shi yake na daban, yana bukatar ta.

Zan aure ta kenan? Sai kuma yayi murmushi.


Bayan Daddy ya farfado Momy ta fada mashi yadda ta iske su Anuwar yaji dadi sosai yace idan akayi mashi aure zai rage wasu abubuwan.


A parlo Anuwar kusa da Daddy anata fira.

Sai tattalin Daddy yake, idan Daddy yace yana son abu jikin shi har kyarma yake da yayi mashi shi.



*************

Tunda asuba haka Inna tazo ta maka man ruwa tace;" tashi kiyi dakan fura".


Baba dake tsaye bakin kofa yace;"kin kyauta to bari kiji, daga yau ta gama tallar komai ko aiken ta kinbar yi, ai kema kin haifa, sannan babu ruwan ki da ita, ta gama yimaki komai a cikin gidan nan kina da diya tayi maki, idan kuma kika saka ta a bakin auren ki, sai idan ni nasakata, kin ban kunya Rakiya wallahi, banyi tunanin zalin cinki yakai haka ba"


Tace;"lalle kam yarinya kinyi nasara a kaina amman kisani ki guji ranar da zan kamaki da laifi"daga haka ta juya tabar wajen Rai bace.



Baba yace;"kinji abinda nace, wahalar ta isa haka"ya juya yayi masallaci.



**************

Kursim ta samu shiga wajen Daddy da Momy kullun cikin yabon ta suke.


Anuwar kullun yana aikin yin zanen fuskar mai fura.


Kullun sai ya runtse ido yana zanata, yana tuna lokacin da yake shafar fuskar ta.


Ganin zanen fuskar MANAL na fitowa yasa saida ya yaga papers din da yake drawing din.


A haka har sukayi sati biyu a Spain.


Momy da Daddy kullun cikin waya suke yi dasu Abie da Ammi yadda za'a tsara bikin idan sun dawo.


Momy ita tayi order komai na laifen Anuwar.


Anuwar ko kullun cikin zane yake, amman yakasa sai fuskar MANAL da yake zanawa.


Saida yayi murmushi ya ce;"Ina sonki Manal nakasa son kowa ce mace sai ke, ita ma wannan ashe ba sonta nike ba, kawai dai ina tausayin tane tunda na kasa zana fuskar ta sai taki"


Nifra dake tsaye tana kallon shi ta juya cikin sauri

Ta tsaya a kurido tana kuka.

Ta yaya Anuwar zai amshi wata mace a matsayin mata.

Ita kam ba zata iya fada mashi sakon Momy ba.

Shiru tayi tana tunani

Kodai taje ta fada mashi Amman tana tsoro.


*************


Haka muke zaune ba ruwa na da Inna sai gaisuwa itama bata amsawa.

Lafiya kalau muke zama da Ma'u har muyi fira.

Inna ko kullun kara tsanata take, kullun addu'ar ta Allah ya kawo abinda zai sa nabar mata gida, duk silata ce komai ya faru, na raba ta da mijin ta gashi kullun Ma'u bata da magana sai Lado.

Sunyi neman abinda zai karya asirin amman shiru.


Anyi auren Shatu amman banje ba saboda Baba ya hanani fita, wai kada a cutar dani ganin abinda ya samu Ma'u nima kada aban nacii.

Amman yace shida kan shi zai kaini naje dakin ta, duk randa ya samu lokaci.


Kwance nike bisa gado ina sun sunar rigar atamfata ranar da abin ya sameni, Ina matukar son kamshin kayan, har wanke su akayi amman kullun kamar ana samasu turaren, naji cikina kamar ana mani motsi.

Daman kwana biyu ina jin motsi.


Gashi kwana biyu kullun cikin kwanciya nike kasala taman yawa.

Nace komai ke damu na??

Kwana biyu kullun cikin kasala bari Baba yazo na fada mashi ya samo man magani.


*************

Nifra dake tsaye tana hawaye sai ga Momy.

Tayi saurin goge hawayen.


Momy tace;'mike damun kine?kin fadama Anu yazo yaga kayan sunyi?"


Nifra ta goge hawayen ta tace;"Momy kina ganin Yaya Anuwar zai amshi wata mace a matsayin mata?? Momy ina ga kamar ba'a yi mashi dai-dai ba ya kamata ayi shawara dashi"wani kallo Momy tayi mata yasa tayi shiru.

Momy tace;"daman naga yadda kike ma ma Kulsom tamkar kishiryar ki, na lura baki sonta ko kema son Anuwar din kike? Idan son shi kike ki fito ki fadi yafi wannan magan ganun naki".

Cikin kuka tace;"Momy har abada babu aure tsakani na dashi, kana kin manta 'yar uwata fa ya aura kuma ita yake so, Allah ya kyau ta naso mijin 'yar uwata, ina jin kunyar ta koda bata duniyar amman ina jin kunyar ta"


Tsaki Momy tayi tace"idan bazaki iya Fadi mashi ba bani waje ni naje na fada mashi ke kuma kita kuka,ko ince ki chigaba da taya 'yar uwar taki kishi, tunda ita bata duniya kinga sai ki taya ta".

Daga haka tabar Nifra tsaye tayi hanyar dakin Anuwar.

Nifra tayi murmushi takaici ta yi sannan tace naga yanda wannan Al'amarin zai kasan ce, lalle naso naga yadda Yaya Anuwar zaiyi.



Qurrah
[2/13, 8:46 PM] GOLDEN PEN WRITERS ASSOCI: *_JARABTAR MU*_



*_Written by Qurrah_* ✍🏽

*Page 33-34*


https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/



*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*




*~We are bearer's of so golden pen🖊~*

*~we write assidiously perceive no pain~.*

*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*

*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*


*Addu’a Yayin Cire Tufafi.*

بِسْمِ اللهِ.bismi l-lahi
Da sunan Allah.


DEDICATED TO....MY SISTERS😘

Page 33-34


_Bissimillah Rahmanir_ _Rahim_



-----------------A hankali Momy ta tura kofar ta shiga.

Hankalin shi yana wajen wayar shi, murmushi yake tare da manna ma wayar kiss.

Gyaran muryar da Momy tayi ne ya dan jiyo yana kallon ta.

Murmushi ta sakar mashi tare da shigowa ta zauna bisa daya daga kujerun dake a bedroom din shi.

Ta sowa yayi yazo ya zauna kujerar dake kallon ta.

Yace;"Momy kun fidda ranar da za'a koma Nigeri ne?"

Girgiza kai tayi tace;"Babu rana amman cikin satin nan insha Allah, daman wata magana ce zamuyi, nasan zaka fahimce ni, hukunci Daddyn ku ya yanke akan ka, ba dan komai yasa yayi hakan ba saidan yana ganin ya isa da kai"


Shiru Anuwar yayi yana nazarin maganganun ta.


Kara maida hankalin shi yayi yace;"Momy inaji, kada kidamu fadi koma menene".


Murmushi tayi tace;"Nagode Anu daman mun yanke hukunci a matsayin mu na iyayen ka, idan mun koma da sati biyu za'ayi bikin ku kaida Kulsoom, komai su mai martaba sun riga da sunyi kafin mu iso, sunyi magana da iyayen ta sun baka, damar kayan lefe ne aka kawo shine nace muje kagani sunyi, idan basuyi ba zaka iya karowa, koma a chanza baki daya idan basuyi ba".


Tunda ta fara maganar yake kallon ta, tana gamawa ya juyar da kanshi wani gefe.


Tasowa tayi ta kama hannayen shi tace;"Haba Anu nasan kana da tausayi, musamman ma akan mace to miyasa baka tausayama Kulsoom itama fa mace ce, ka duba kaga duk irin wahalar da tasha, miyasa baka tausayin ta? wallahi Anu Kulsoom ita kaɗai ce wadda zata iya zama da kai saboda tana matukar sonka".


Kara damke hannun shi tayi tace;"yanzu ni 'yar sako ce, Daddyn ku na jiran ka, Amman ina rokon ka alfarma kada kace a'a kodan lafiyar shi, please Anu wannan itace alfarma ta ta farko dana rokeka, a matsayina na Uwar ka kuma tsohuwar sirikar ka"ta ida maganar da hawaye.


Tamkar dutse haka Anuwar ya koma ko motsi ya kasa.

Haka kuma fuskar shi bata nuna wani alamun yadda ko akasin haka ba.


Momy ta saki hannun shi ta mike tana goge hawayen ta tayi waje.


Mikewa yayi tsaye yaje bakin window ya tsaya hannu cikin aljihu.


Kallon lanbun dake waje yake, tsallen da take lokacin da ta nufosu rige da kara a hannunta, murmushi yayi yana kallon yadda take tsalle.



***************

Ina jin shigowar Baba nayi saurin fitowa.

Lokacin Inna ta fito tana tsaye a bakin kofar dakin ta.

Wata harara data sakar man hakan yasa na tsaya daga inda nike.


Baba ya jingine keken shi a bango.

Yace;"Nana barka da gida ya gajiya"nayi saurin karasawa.

Nace;"Baba sannu da zuwa, andawo lafiya"ya mikoman wata leda.

Tun kafin tazo hannuna miyau dina ya tsinke.

Na amsa nayi godiya na juya cikin sauri na isa daki.


Soyayyan kifi ne a ciki, cikin sauri nike chin kifin dan danan na chinye.


Na fito na wanke hannu na, na zauna ina zama naji zuciyata na tashi.


Lokaci guda naji cikina ya murɗa.

Zuciya ta sai tashi take, jin amai yazo man lokaci guda yasa nayi saurin mikewa nayi waje a guje.


Ba kowa hakan yasa nayi bandaki.

Ina zuwa sai amai duk abinda naci saida na juye shi.


Nayi mamaki sosai yadda akayi hakan ta faru saboda jikina ba zafi ko kaɗan.

Gashi inacin kifi sosai to amman ya akayi hakan ta faru??

Na wanke bakina na fito dai-dai lokacin da Inna ta shigo rike da kwaryar nika a hannunta.


Ta kalleni tun daga sama har kasa.


Tace;"idan tayi wari munji"nide bance komai ba, naje na aje butar nayi dakina na kwanta.


Har dare ina kwance babu abinda ke ban sha'awa balle inci


Haka na kwanta jiki na babu kwari, ina son inje wajen karatu amman ban iyawa, kuma ni ban masan mizan cema Baba yana damuna ba, saboda yanzu ban jin dadin komai.


Haka na kwanta tare da addu'ar bacci a bakina rigata na bisa hanci na ina sun sunawa har bacci ya daukeni.


**********

Gajiyar da yayi da tsayuwar yasa ya dawo ya zauna.


Wayar shice ta fara kara yasa hannu ya dauka.

Muryar Ammi ce a dayan ban garen.

Kara gyara zama yayi yasa Bluetooth a kunnen shi.

Yace;"Ammi kin mantani kinbar kirana ko?"

Murmushi tayi wanda saida yaji sautin shi tace;"Ban manta da kai ba Ɗana, hidimar Ƙanwata akeyi Rahama kasan tana nan gida munsha bikin sunan Manal".


Yace;"Ohh haka ne aba Maman Manal hakuri ina nan zuwa,mun kusa dawowa, ashafa man kan Manal dina, ace mata Uncle dinta na nan zuwa ganin ta".


Dariya tayi tace;"abunda diyar taku bata da kyau, diyata Manal ta fita kyau"

Shima murmushi yayi yace;"lalle Ammi babbar diyar tamu kike cema bata da kyau, duk garar da muka yi maku?"

Dariya itama tayi sun dan dade suna fira kana tace;"Daman akan maganar auren kane na kira ka"


Jin haka yasa wutar Anuwar ta dauke.

Ammi tace;"Yanzu Daddyn ku suka gama waya da Mai martaba yace saboda an maka magana fushi kake da kowa, baka fita chin abinci ba sannan kai ke bashi magani amman yau baka zo ba har time ya wuce".

Shiru yayi yana sauraren ta tace;"Haba Yarima kada kamanta kalar kaunar da yake maka mana, saboda kaunar da yake maka yasa ya dauki 'yar shi 'yar shekara tara ya aura maka, duk saboda kaunar da yake maka, saboda farin cikin ka, wahalar da yayi dakai mahaifin ka baiyi dakai ba, sannan yanzu ka kasa mashi biyayya akan zai kara inganta rayuwar ka, taimakon ka zaiyi fa, kayi tunani bai kamata kayi mashi haka, kyau ace ka nuna mashi yafi karfin komai a wajen ka, kayi hakuri nasan ba'a shiga rayuwar ka kullun abinda kake so kake yi saide a matsayina na mahaifiyar ka naga ya dace na baka shawara wannan shawara ce ba umarniba"

Daga haka ta kashe waya.


Shiru yayi yana tunani, duba time yayi ganin lokacin shan maganin Dad ya wuce yasa yayi saurin tashi ya fita.

Parlo ya fito babu kowa ciki, kasa ya nufa.

A hankali yake sabko wa daga matakalan benan.

Daga Daddy sai Momy ne a parlon kasan.

Kaya ne a gaban Momy tana dagawa Daddy na zaune bisa kujera.


Bai iya kirga jikun kunan dake gaban Momy gasunan zube a kasa.


Daddy ya dago yana kallon shi.

Ganin inda Daddy ke kallo yasa itama Momy tabi wajen da kallo.


Murmushi Daddy ya sakar mashi shima haka ya maida mashi.


Baiyi magana ba ya zauna kusa da Daddy.


Kallon Daddy yake yana kallon maganin dake kusa dashi.

Daddy ya gane abinda yake nufi yayi murmushi yace;"bazan sha magani ba sai Anu dina yazo yaban, Momyn ka ce ta dauko zata ban nace ban sha, saboda ba ita ke ban ba, zangani idan Anu yana san lafiyar Daddyn shi"


Murmushi yayi tare da tashi ya dauko ruwa ya mika ma Daddy maganin ya mika mashi ruwa.


Har saida ya shanye kana Daddy yace;"kana fushi dani har yanzu, saboda zan maka aure shine kake fushi dani, wallahi Anu hankalina ya tashi ganin yadda ka kasa control din kan ka har saida ka kusanci km karamar yarinya yanzu a lokacin da kana da mata ita zaka jemawa, kayi hakuri bazan fasa auren nan ba, ina gudun kada asake samun irin wannan matsalar, kasan ada ban ba maganar karfi ba har rokan maka Mai martaba nike ya kara maka lokaci amman ganin abunda ya faru nima ina goyan bayan shi"


Shiru Anuwar yayi ya rasa mizai cema Daddy.


Daddy yace;"kaga kayan da Momy tayi order sunyi ko a kara wasu?"

Kai ya daga Daddy yace;kaga yanzu next week zamu koma ko akwai abinda kakeso?"girgiza kai yayi.


Daddy yace;"saura naka laifen Momyn ku bata iya zaben kayan maza ba, shiyasa zan sa Usman yayi maka"yana maganar yana dariya.

Murmushi Anuwar yayi tare da mikewa yace;"Daddy zan fita"kallon shi Daddy keyi cikin mamaki yasan bai zuwa ko ina, kuma baida friends, towai miyasa Anuwar keson zuwa Spain, kuma bai taɓa jin ya ambaci sunan wani dasunan abokin Shiba.

A Nigerian Turkish yayi Primary, secondary dinshi yayita a Dubai babu wanda yasani a Spain, amman yana yawan zuwa.


Ganin Daddy na tunani yasa yace;"Daddy please kabarni zan kula da kaina".

Dariya Momy tayi tace;"lallai a Spain zaku yi Honeymoon dinku, duk kasa shen da muke zuwa baka fita sai munzo Spain lalle dole a yabama Spain"


Dariya Daddy yayi yace;"nima hakan ya sani dogon nazari"

Shima Anuwar murmushi yayi yace;"wai Dad kamanta pack din nan da ka taba sawa aka kaimu ranar Birthday din Manal na five years, to ai chanzani yau shekarar ta sha bakwai kenan, ina son naje".


Murmushi Dad yayi yace;"sai ka dawo"ita kuma Momy bata kara magana saima shiru tayi tana kallon Anuwar.


Dad yace;"Amman ai yanzu dare yayi baka bari sai gobe".


Bata fuska yayi yace;"Dad kamanta karfe Daya na dare aka haifeta da minti tara, Momy please kice yabarni na tafi zanje Hospital din da aka haifeta, daga chan na wuce pack ba gida zan kwana ba"

Murmushi Momy tayi saboda idan tayi magana hawayen dake makale a idon ta zasu zubo.

Ganin haka yasa Daddy yace;"ka kula saika dawo"ya juya zai fita kenan yayi kicibis da Kursim dake tsaye tana hawaye a bakin kofa.


Kallon ta yake yana mata kallon tuhuma yace;"mikikeyi a tsaye bakin kofa, yanzu idan maganar sirri muke fa".

Ta goge hawayen ta tace;"nazo shigowa naji kana maganar Birthday din Manal shine na tsaya ka gama, dan Allah zan raka ka ina. son na kasan ce dakai a wannan daren kodan muhimmancin shi a wajen ka"



Saboda yadda yake jin yau zuciyar fes yasa ya daga mata kai.


Cikin sauri tace;"one minute please"tare da hada hannayen ta biyu.

Daga Kai yayi cikin sauri tayi ciki shi Kuma yayi waje.

Yana tsaye sai gata sanye da wando da riga, sai ta aza Dubai Abaya(after dress)a sama Amman bata saka maballen taba, tayi rolling din gyalen rigar ta saka wata jakka a bayanta tayi kyau sosai dan surar jikin ta ta bayyana.


Tun kafin ta iso kam shinta ya iso inda yake.


Tana isowa ta sakar mashi murmushi tace;"da wane motor zamu fita?".


Baiyi magana ba ya nufi wata 'yar karamar mota fara.


Cikin sauri ta nufi wajen Driver ta amso makullinta.


Ta bude mashi ya shiga ta kulle.


Motar a bude take saman ta, duk budewar idon Kursim bata taba ganin kalar motar ba.

Ta burgeta sosai hakan yasa take driving din cikin nishadi.


Shike nuna mata inda zasu har suka isa.

Ga mamakin ta a asibitin tunda suka shiga har suka isa office din wani Doctor duk wanda suka hadu dashi inde ma'aikaci ne to yasan Anuwar, sai sungaisa.


Suna shiga taga Doctor din ya taso cikin fara'a ya rungimi Anuwar.

Bayan sun gaisane yake ce mashi matar shice wannan mai kyaun.


Jin an ambace ta maikyau a gaban Anuwar yasa tayi murmushi mai kayatar wa.


Tayi saurin amsawa da eh, kana suka gaisa.


Bata kara shiga mamaki ba saida taji Anuwar yace;"ya fitar da abinda za'a ba da ga yaran da za'a haifa Yau"

Murmushi Doctor din yayi yace;"ai tun kafin kazo munyi komai kamar yadda aka saba"bata gane maganar ba hakan yasa take son karin bayani.



Anuwar ya mike zai zagaya asibitin, wata Nurse ce ta shigo ganin Anuwar yasa ta saki murmushi, suka gaisa tana cewa shekarar ta dawo kenan tunda mungan ka shima dariya yake.


Ta juyo tana kallo na cikin mamaki tace matar shice tace eh.


Da Anuwar da Doctor din suka fita daga ita sai wannan baturiyar Nurse din


Nace mata meyasa naji Doctor yace za'ayi kamar yadda aka saba me Anuwar keyi a irin wannan ranar tace;

"A wannan asibitin aka haifi MANAL, tunda ta mutu duk ranar zagayo war haihuwar ta, Prince na bada kyauta mai tsoka ga duk yarinya ko yaran da aka haifa irin ranar, shine yau yazo, muna da masu ciki duk wadda ta haihu tana da kyauta mai tsoka, ko bai nan za'a aje sunan wanda ta haihu a ranar duk shekara haka yake".


Wata irin raunanniyar ajiyar zuciya Kursim tayi.


Nurse ta dauki file din da tazo dauka tayi ma Kursim ban kwana ta fita.


Tana kallon series fim na kasashe kala-kala amman bata taɓa ganin irin wannan soyayyar ba.

Anya idan ta biye ma son zuciyar ta ba zata wahala ba??

Tana tsakar tunani sai gasu sun dawo suka yi ban kwana.


Suka bar wajen basu yi tafiya mai nisa ba suka isa wani haɗaɗɗen pack.


Wajen mai ice cream suka nufa.


Shima cikin fara'a ya tarbi Anuwar yana cewa sannu da zuwa Prince.

Shima abin mamaki maganar MANAL yake.

Miko mashi wani ice cream yayi.

Bata fuska Anuwar yayi.

Murmushi mai ice cream yayi yace;"wannan yana da dadi Madam za'a ba , ga ice cream din dana san kana ba yaran nan kalar wanda MANAL kesha, dan nasan yau zaka zo shiyasa gashinan da yawa aka ajema, kuma koba ka zoba yau saina bada shi ga yara"


Dariya Anuwar yayi ya mikama Kursim ƙin amsa tayi.


Kallon ta yayi murmushi ta saki tace;"nima kallar wanda MANAL ke sha zan sha".


Murmushi yayi da yake da turanci tayi maganar yasa mai ice cream baiji abinda TACE ba, yayi murmushi ya miko mata.


Ta amsa ta juya tana goge hawayen dake zubo mata.

Wani waje ta samu ta zauna.


Tafi minti talatin tana tunani.

Koda ta juya ta hangi Prince shi da yara suna dariya yana rungumar su yana mika masu Ice cream.


Dariya tayi ta mike, ta nufi inda suke photuna take mashi shida yaran.


Haka har kusan awa guda suna abu daya.

Tana mashi photuna tana mashi video da wayar ta.


Cikin nishadi yake har karfe Daya.


Bata yi mamaki ba saida taga yaje wajen mai ice cream ya amso abin sallah.


Ya fara sallah a wajen tana zaune har asuba yana abu guda.


Tun tana hawaye har ta fara tausayin shi har bacci ya fara daukar ta daga zaune, sai wajen asuba ta bude ido tace wannan wace irin Jarabta ce haka.


Saida akayi asuba kana suka nufi hanyar gida.


Suna zuwa ta wuce daki saboda a gajiye take ga bacci ta naji.


Dakin shi ya shiga yayi wanka ya fara karatun Al-qura'ani cikin murya mai sanyi.


A haka har rana tayi kana ya fito.


Koda ya fito ya iske anata kallon Videon da Kursim tayi mashi.

Yana isowa Daddy yace;"Nayi maka laifi nasha magani, dan nasan kana bukatar hutu nama yi tunanin bacci kake".


Nifra tace;"Morning Yaya Anu"da kai ya amsa.

Kursim ta gaishe shi Daddy yace;"photunan jiya muke kallo sunyi kyau sosai, kaima Allah ya baka yara da wuri, yadda kake son yara Allah ya kawosu nan da wasu watanni"

Ita dai Kursim kunya taji amman shi Anuwar yace;"Amin Dad ina son yara sosai ina son yara masu yawa kayi man addu'a Allah yaban Baby nan kusa"dariya suka yi

Momy tace"to Allah ya bada mai Albarka Allah ya nunaman yaron ka Anuwar"dariya Nifra tayi tace;

"Idan kana so kaji maganar Yaya Anuwar to kayi masa maganar yara, dan haka Auntie Kulsoom saiki shirya"tana maganar tana dariya.


Kursim ta dukar da kanta kasa"Momy ta da fata tace kyaleta Kulsoom"nan suka yi Breakfast harda Anuwar yau itace rana ta farko daya shiga cikin su.


Haka suka cigaba da rayuwa a Spain kullun cikin tunanin mai furar shi yake.


Gashi ya kasa zana fuskar ta.


Haka sukaci sati guda yau watan su guda kenan Dad ya samu lafiya ya gama shan magun gunan shi.


Suka nufo Nigeria baki daya kowanen su da irin abunda yake sakawa a zuciyar shi.


Kursim murnar take lokacin auren ta yayi.

Shi kuma Anuwar murna yake zaiga mai furar shi.

Su Momy kuma yadda za'a kayata bikin wanda ba'a taɓa yin shi a Nigeria ba suke magana.


Haka jirgin su ya iso Nigeria


*************
Haka muke rayuwa a gidan bani wata wahala amman babu ruwana da Inna sai gaisuwa

Ina zaune saiga Ma'u ta shigo da langa a hannu.

Dumame ne ta aje a gabana, nace nagode tace to ta juya.

Ina saka hannu cikin abincin naji zuciyata na tashi nayi saurin toshe hancina ban son kamshin miyar.



Yaune ranar da nike saran jinin al'ada yazo man shiru sai na kara kwana biyu nan ma shiru babu alamun shi


Ina jin motsi a cikina amman ban kawo komai a raina ba,gashi ba komai nike ciba


Nakara kwana biyu Amman shiru babu al'ada karatun fikihu ya dawo man.


Zaunawa nayi bakin gado na ina nazarin alamomin masu ciki.

Gaba na ya fadi gashi sai wani haske nike, kullun Inna cikin kallona take daga sama har kasa tana cewa idan tayi wari munji.


Mikenan take nufi?? innalillahi!! Abinda zai bani tabbacin ina da ciki shine rashin ganin al'ada ta.


Wani irin faduwar gaba tare da wasu zafafan hawaye suka zuboman.


Me zai faru ne dani?? Wannan wace irin jarabtar rayuwa ce nagama da wahalar duka da zagi da zangwama na Inna da mutane yanzu kuma wani tabo zai shafeni?


Kenan yanzu ne zan fara ganin wahalar rayuwa ada chan sulmin tabu ne.


Dafe kirji nayi nace;"yanzu idan Inna ta sani zata kaini gidan Mai gari kenan?daman jiran laifi na take"


Mikewa nayi tsaye yanzu me zan yi kenan inje na tambayi inda aka kai Shatu idan akwai abinda zan sha ya zube.


Wata zuciyar tace a'a nace to idan ba haka ba idan Inna tasan da wannan cikin ya kenan??


*Qurrah word counter 3014*

*_JARABTAR MU*_



*_Written by Qurrah_* ✍🏽

*Word Counter 2473*

*Page-35-36*

https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/



*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*




*~We are bearer's of so golden pen🖊~*

*~we write assidiously perceive no pain~.*

*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*

*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*



*Addu'ar Shiga Bandaki.*

(بِسْمِ اللهِ)اللّهُـمَّ إِنِّـي أَعُـوذُ بِـكَ مِـنَ الْخُـبْثِ وَالْخَبائِثِ.

(Bismil-lah) allahumma innee a'u'zu bika minal-khubthi wal-khaba-ith



DEDICATED TO....MY SISTERS😘


Page-35-36


_Bissimillah Rahmanir_ _Rahim_


----------------Cikin takon Isa da kasaita yake sabkowa daga bisa matakalar jirgin da ya kawosu.


Ta ko ina daukar su ake da Camera, airport din cike take da manema labarai da

Please Login or Register in order to submit comment