Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

san halin da Dad din shi yake, shi ne dalilin da yasa ya zama haka, kila giya ya sha shi ne abinda Sani ke tunani.


Kursim tace mashi ya fita bata son kowa a part din.


Haka ta zauna gefen Anuwar yana bacci har kusan awa guda.


A hankali ya bude idon shi, ganin shi a dakin shi yasa yayi saurin tashi.


Rike kan shi yake, ya kalli Kursim ya kalli dakin yace; "Kulsoom ina Baby take?". Kursim kallon shi take, ganin ya yunkura zai tashi.

Tace; "dare yayi yanzu, kuma wacece Baby?".


Tsaki yayi tare da sauka bisa gadon, kallon kayan jikin shi yake.


Bakin mirror yaje ya tsaya yana kallon kan shi.

Cije leben shi yayi, hakan yasa har yayi jini, tare da wata kuwa, yake cewa; "No!No!!".

Kayan bisa mirror ya zubar tare da saka hannu ya naushi mirror, mirror ya tarwatse, shi kuma hannun shi jini kawai ke fita.


Da kyar Kursim tayi motsi daga inda take duk ta tsorata.


Juyowa yayi yana kallon inda ta daskare yace; "Ina key din motar ki". Cikin tsoro da kyarmar murya tace;


"Prince baka iya mota ba sosai, shi yasa hankali na ya tashi dana zo na iske bakanan babu mota, nayi tunanin airport kayi dan chan nayi, na san kana iya cewa yau zaka je Abuja sai dai na kai ka, amma bazan baka mota ba ina tsoro".

kallon ta yake cikin mamaki.


Me zai je yi Abuja?? Bai gane maganar ta ba.

Yace; "Babu Abujan da zani, kizo ki kaini garin su yarinyar nan, idan bazaki ba ki ara min motar ki, idan kina gudun na bata maki, ita zan lunka maki kudin motar, kiban ita, yanzu zan maki transfer, bana bukatar wata magana".


Wayar shi ya gani bisa bed site yaje ya dauko, bai yi mamakin ganin Miss calls ba.


Message din Nifra yayi mamakin gani yana buda wayar ya shigo.


Tsaki yayi yace kila ma shirmenta ne, sai kuma yayi wani tunani yace bari ya duba.



Ganin message din yasa yayi wurgi da wayar shi yana kallon Kursim, hankali shi a tashe yace; "daman kin san halin da Dad yake kika ki fada min!".

Girgiza kai take tana kuka.

Tace; "wallahi ban sani ba, sai dazun bayan na fita daga gidan nan, na nufin zagayawa cikin unguwa, nan ne Nifra ta kira tace na tura ayi maka booking din jirgi, gobe kaje gida Dad bashi da lafiya kuma sosai, shi ne na kira Hanan ta kaini nayi booking din jirgi, muna dawowa muka iske baka nan, nan hankali na ya tashi nayi tunanin ka sani airport zaka, shi ne muka koma airport nemanka".


Bakin bed din shi ya dawo ya zauna tare da rike kai.

Yanzu ina zashi wajen yarinyar da yayi ma barna??

Ko Kuma wajen Dad da bai san inda yake ba, rai hannun Allah.


Gashi sunan shi Dad ke fadi, shi yake son gani.


Runtse ido yayi yana tunanin aikin da yayi dazun na yima karamar yarinya fade.

Sai kuma ya dunga hango kalar soyayyar da Dady ke nuna mashi, ko wanda ya haife shi bai mishi ita ba.


Yanzu gobe da safe ina zai nufa kenan??



Qurrah
*_JARABTAR MU*_



*_Written by Qurrah_* ✍🏽

Page 29-30


https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/



*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*




*~We are bearer's of so golden pen🖊~*

*~we write assidiously perceive no pain~.*

*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*

*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*


*Addu'ar da ake Wa wanda ya sanya sabuwar tufa*

"تُبْلِي وَيُخْلِفُ اللهُ تَعَالَى"

Tublee wayukhliful-lahu ta'ala

Allah ya sa ka mayar da ita tsumma, kuma Allah madaukaki ya mayar maka da wata (tufar).


"إِلْبِسْ جَدِيداً وَعِشْ حَمِيداً ومُتْ شَهِيداً"

Ilbas jadeedan waAAish hameedan wamut shaheedan.

(Allah ya sa) ka sanya sabo, kuma ka rayu kana abin yabo, kuma ka mutu kana shahidi (wanda aka kashe a tafarkin Allah).


DEDICATED TO....MY SISTERS😘


Page 29-30



_Bissimillah Rahmanir_ _Rahim_



-----------------A hankali nake bin dakin da kallo,lalle nan ba dakina bane, kuma ba gidan mu bane.

Jin an rike man hannu yasa nayi saurin kai kallo na wajen.


Shatu ce rike da hannu na kanta na bisa gadon da nike kwanec, sauran jikin ta na kasa hannunta cikin nawa,tana bacci ga hawaye nan a fuskar ta duk sun bushe.


Runtse ido nayi na tuna abin da ya faru da dani.

Ban san lokacin dana fizge hannu na cikin nata ba.


Kallon zoben da ya saka man nike,lalle ba mafar ki bane.


Wani irin kuka ne mai cin rai da sauti ya kubu ceman.


Cikin sauri Shatu ta bude ido,ta ganni zaune bisa gado ina kuka.


Kallo na take hawaye na zuban mata,itama daman da alama tasha kuka.


IYA ce ta shigo dakin(mahaifiyar su Shatu)tace;

"Subhanallah! me nike gani haka Shatu?keda ya dace ki bata baki kuma shine kema kuka kike,tun dazun nace kibar wannan kukan haka"


Cikin sauri Shatu ta goge hawayen ta tace;yanzu Iyah miza muyi mata,bata iya tafiya fa dai-dai,kada Inna ta sani,kin san idan ta sani zata fadama mai garin su,ba zasu yadda da ita ba haka zasu ce tana sane,dan haka sai an mata bulala".

Cikin kuka Shatu ke cewa;"Inna dan Allah kiyi wani abu,kada Inna ta sani,kin san bata son ta, kuma daman yanzu ta tsane ta,tabi ko Ina a gari tana cewa wai ta yi ma Ma'u asiri dan kada ta auri Kabiru,kin ga ta samu dama kenan,shi yasa kika ga ina kuka"

Shiru Iyar su Shatu tayi,lalle maganar Shatu gaskiya ne, tomi zata yi kenan?


Zuwa Iya tayi inda nike zaune ta kamani,tace;"muje ga ruwan zafi chan ki shiga,daga nan kiyi tsarki"daga kai nayi.


Sai da ta kama ni na tashi,kana ta kaini bandaki cikin daren nan,haka na shiga ruwan zafi.

Har lumshe ido nike saboda yadda naji dadin su,na danji sauki,ba kamar dazun ba,nayi wankan tsarki na fito.


Ta kamani muka nufi daki, taban kayan Shatu na saka na fara rama sallar da ake bina.


Ina gamawa naga ba kwaryar Inna da ta nono.

Nasan na baro su baran dar mu.

Shatu na kallah ina neman karin bayani.

Tace;"Jabe ya dawo yace bai gan kiba,amman kayan ki na nan,shine Iya tace karya yake muyi sauri muje mu dauko ki baki iya daukar kayan nan ke kade ga hadari,koda muka je babu kowa mukai ta kiran sunan ki, baki nan shine, nace mu dauki kayan mu duba hanya,shine muka iske ki kin suma"


Ganin hawayen Shatu sun ki tsaya wa, yasa na tsaida nawa,Iya ta kawo man tuwo,naci nasha ruwa na zauna, banajin bacci ko kadan saboda dana runtse ido sai intajin tsoro.


*************

Jinin dake zuba daga hannun shi, yasa Kursim mikewa,zata kama hannun ya fizge hannun shi.


Tare da cewa;"No need" cikin tsawa ganin jinin yaƙi tsayawa gashi bai son taimako nata, tayi saurin barin dakin cikin sauri.


Su Sani ta iske bakin kofar dakin sun yi zugu dum su duka,ko wanne yayi ta gumi.


Sani tace ya biyo ta.

Saida suka dan yi nisa kana ta tsaya ta kalle shi tace; "ina son kaje yanzu ka gyara part din Yarima,sannan inason ka shirya mashi kayan shi,gobe karfe takwas zaku tashi".


Kai ya ɗaga tare da cewa;"Angama Gimbiya Kursim"ya juya cikin sauri ita kuma ta koma daki.


Ta iske Hanan tayi zugun da hannu,tana ganin ta tayi saurin mikewa ta iso inda take


Tace;"bai tambayi abinda ya kawo mashi wannan matsanan ciyar sha'awa ba?"yadda taga Hanan duk ta rude yasa tayi mamaki.

Daman Hanan na tsoron wani?

Kursim tace "bashi ne a gaban shiba yanzu,yasan halin da Dad din shi yake ciki"

A jiyar zuciya Hanan tayi tare da cewa "thank God".

Kursim tace;"daman duk jarumtar taki kina da tsoro haka?"


Murmushi Hanan tayi tace;"kinfi kowa sanin waye Prince,a kasan su muke,ina tsoron kada wani abu yasamu kujerar Baba na next tenuwa"dafa ka fadar ta Kursim tayi tace;

"Kada ki damu babu abinda zai faru insha Allah,ai yanzu hankalin shi na wajen Dad din nan"


Murmushi Hanan tayi tace"bari na shirya maki kayan ki,dake na shirya tafiyar"zaro ido Kursim tayi.


Hanan tace;"ya kamata ki kasan ce tare dashi, ina tare da ke a koda yaushe, ki nuna kema kin damu a kan ciwon Dad din shi,ance yana Spain ko?"

Daga kai tayi alamar eh.


Murmushi Hanan tayi tace;"yarinya ki farka daga mafarkin da kike,kamar ba mace ba,komi sai an saka kissa a ciki,kina abu kamar ba Lowyer ba"

Dariya Kursim tayi tace;"wallahi duk rudewa nike yi, kuma kinsan idan Dad din nan yace ya aure ni,shikenan matsalar mu ta kare, dan zaiyi ko kaɗan baison bata ma Dad din nan"


Hanan tace;"lalle kiyi amfani da wannan damar wajen sanya soyayyar ki a zuciyar Dad, kiyi amfani da damar ki, zan zo ko daga baya ne".


Haka suka cigaba da shirya kayan Kursim,duk abinda tasan zata bukata ta dauka,har saida dare yayi nisa kana suka kwanta.


Tun asuba suka tashi suka shirya Kursim ta nufi wajen iyayen ta.


Ko kaɗan baiyi bacci ba yana yin sallah ya shirya ya dawo falo.


Har wajen Baban Kursim suka je sukayi mashi ban kwana shidai Prince ba magana.


Kowa yayi mashi uzuri akan rashin lafiyar Dad,da ka ganshi kasan baiyi bacci ba.


Haka suka bar gida,shida Kursim a mota guda.


Suna zuwa airport ba bata lokaci suka bar garin Katsina.


Zuciyar Anuwar da tunani iri-iri.



**************

Bayan munyi sallar asuba,ni dai a zaune nike inbanda hawaye babu abinda nike.

A haka har rana ta fito ina nan zaune.

Saiga Shatu ta shigo da zazzafen tuwo.

Tace;"sabko kici,ga ruwa chan an dafa maki na zafi idan kin gama kije kiyi wanka"kai na daga.


Naje na wanke baki na na dawo,na zauna tare da rintse ido,koya nayi motsi sai naji zafi,daure wa kawai nike dan babu yadda zanyi.


Tuwon nike chi amman jin shi nike tamkar ina cin madachi.

Jin yadda nike jin tuwon yasa na cire hannu na.

Naje na wanke na dawo na kwanta.

Ita ma Shatu tashi tayi ta kai tuwon ta wanko hannun ta ta dawo.


Kusa dani ta zauna, inda nike kwance.


Tace;"kiyi hakuri ki dauka hakan itace Jarabtar ki,kowa fa da irin jarabar da Allah ke mashi,ke kuma haka taki take, insha Allah watarana zai zama labari,amman dan Allah ki saki jikin ki,ki tashi kije ki gasa jikin"


Tashi nayi ina goge hawayen da suka zubo man.


Haka naje nayi wanka na nadawo,na shafa mai na saka kayan Shatu.


Ranar anan na yini ba tare da na koma gida ba,haka suma basu ceman naje gida ba.

Duk abinda Shatu tasan zai faranta man ranar tayi man ita da Iyarta amman da yake zuciya ta babu dadi,sai dai naita binta da kallo.


Ban sanin lokacin da hawaye ke zubo min ba,nan Iya tai ta man nasiha,tare da kwantar man da hankali.



*************

Suna isa tace suka bar kasar sai Spain inda aka kwantar da Dad.


Koda suka isa Anuwar kamar yayi hauka, duk ya rude,gashi ba'a bari a shiga wajen Dad din.


Ranar haka ya yini baici komi ba,haka ita ma Kursim dake gefen shi, komai bata ci ba

Saida Daddare kana Momyn Nifra tace,su wuce su tafi,sai zuwa gobe za'abari a ganshi.


Anuwar yace nan zai kwana, Kursim ma tace nan zata kwana.


Momy tace a'a su dai wuce gida ita mace ce, haka ta hakura ta bar Anuwar suka wuce gidan su Nifra dake nan.


Tana zuwa tayi wanka taci abinci,tana zauna ta kira wayar Anuwar bai dauka ba.

Daga karshe ma kashe wayar yayi.

Zaunawa tayi tare da tagumi,tana tunanin anya Anuwar zai sota??


Tsaye yake a cikin parlo yana kallon Dadyn shi da ke kwance yana barci.


Dawowa yayi ya zauna cikin daya daga cikin kujerun parlo,idan kaga wurin baka cewa asibiti ne,parlo ne wanda aka shirya kamar ba asibiti ba ya tsaru sosai.


Daga parlon kana kallon wanda ke jinya ta gilas,amman an kulle,babu mai shiga sai Doctors ko kuma sai idan su sukayi maka izini.


Lumshe ido yayi yana tuna abinda ya faru jiya.


Yana bukatar ya koma Nigeria kodan yaje wajen yarinyar, ya sanya mata laifi Amman babu yadda zaiyi kaddara ce.


Yana bukatar yarinyar zai ne mota ,itace mace ta biyu da yaji wani abu akan ta,bayan Manal sai ita.

Zata iya maye gurbin Manal??


A haka har dare yayi nisa,yana zaune.

Chan cikin dare ya mike domin ya ga Dad koya farka.


Yana zuwa ya ganshi idon shi bude,yana kallon wajen parlon shi.


Cikin sauri yayi kofar shi,ya ganta rufe.

Cikin tsawa yake kiran Security.


Jin tsawa yasa duk suka rude,cikin kyarmar jiki suka iso wajen.


Kofa ya nuna masu,cikin sauri suka bude.


Yana zuwa rungume Dad din shi yayi yana murmushi tare da sakin ajiyar zuciya.

Ya ɗago yana kallon Dad din nashi na da yake hawayen farin ciki.


A hankali yace;"I missing you so much my Son"tare da manna mashi kiss a
goshi, yana shafa sumar kanshi.

Murmushi kawai Anuwar yake yana son Dad dinsa duk abinda zaima Abie shima zai iya yima shi.


Koda ku Momy suka zo asibiti da safe.

Zaune suka iske Dad da Anuwar bisa gado, suna fira su duka sunyi wanka sun ci abinci kamar ba marar lafiya.


Matsowa Kursim tayi ta gaida Dad, ya amsa cikin sakin fuska da jin dadi, Anuwar kuma ko kallon ta baiyi ba saima latsar waya da yake.


Ta gaida da shi, kai kawai ya daga mata.


Haka a bangaren Momy sai jan Kursim take a jiki, Nifra ce ma dai da bata shiga lamuran ta ba,dan Nifra jinta take kamar itace President din, daman Fawad na makaranta banda shi aka zo, baiko san Dad bai lafiya ba.


Fira suke sosai amman Anuwar bai saka masu baki.


Tashi yayi zai bar wajen Dad ya rike shi, kallon Dad yayi da alamar tambaya??


Da ido Dad ya nuna mashi waje ya zauna.

Koma wa yayi ya zauna, amman jin shi yake tamkar bisa ƙaya yake zaune , yana son ya kebe yayi tunani miya kamata yayi akan yarinyar nan.



*************

Yau koda na tashi na kasa, jiki na naji sauki sosai, haka nayi ta zama duk da koda yau she muna tare da Shatu.


Shatu na kokari wajen gusar man da damuwa.


Haka itama Iyarta duk abinda suka san ina so saida aka aika Jabe ya siyo man.


Muna zaune nida Shatu,tana ban labarin yadda suke bikin su, hakan yasa na saki jiki amman kasan zuciya ta na man zafi, saide wani labarin dole ka dara.


Jabe ya shigo yace;"Adda wai kinji anata cigiyar 'yar gidan Malam, wai ta bace"mamaki nike daman Inna zata iya nema na??


A haka har dare yayi na kwanta, sai bacci saboda jiya sama-sama nayi bacci.



**************

Juya wayar dake hannun shi yake, kowa yana sha'anin shi a parlon, da Momy da Kursim da Nifra, Dady na zaune suna ta bashi labari.


Kadan-kadan yayi tsaki tare da runtse ido.


Daddy na kallon duk abinda yake.


Ta shi yayi ya koma dakin shi ya rufoshi da karfi.


Bakin bed din shi ya zauna yana buga kan shi.


A hankali Daddy ya bude kofar yayi tsaye yana kallon Anuwar.


Matsowa yayi ya zauna kusa dashi.


Ya rike hannun shi guda, kallon shi Anuwar yayi.


Dady yace;"nasan kana cikin matsala minene fada man"



A hankali yace;"ina son zuwa Katsina gobe"kallon shi Dady ya ke cikin mamaki.


Yace;"miza kayi ne a Katsina bayan gamu nan tare da Kursim"gir giza kai yake yace;

"Please Dad kabar ni na tafi mana "yayi saurin rike hannayen Dad.

Kallon shi Dad yake yana nazarin wani Abu.

Miyasa yake son zuwa katsina??


Kuma daga ance bai zuwa duk yabi ya rude lalle akwai dalili.


Daddy yace;" sai ka fada man gaskiya me zaka je kayi?"


Shiru yayi ya kasa magana.


Dady yace idan ba zaka fadi ba shikenan babu inda zaka Ina bukatar ka kusa dani.


Shiru yayi yana tunanin kode ya fadi ma Daddy abin da ke faruwa.

Bazai iya daure wa ba idan baiga yarinyar nan ba.


To yanzu menene mafita??


Qurrah
[2/13, 8:46 PM] GOLDEN PEN WRITERS ASSOCI: *_JARABTAR MU*_



*_Written by Qurrah_* ✍🏽

Page-31-32


https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/



*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*




*~We are bearer's of so golden pen🖊~*

*~we write assidiously perceive no pain~.*

*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*

*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*


*Addu'ar da ake Wa wanda ya sanya sabuwar tufa*

"تُبْلِي وَيُخْلِفُ اللهُ تَعَالَى"

Tublee wayukhliful-lahu ta'ala

Allah ya sa ka mayar da ita tsumma, kuma Allah madaukaki ya mayar maka da wata (tufar).


"إِلْبِسْ جَدِيداً وَعِشْ حَمِيداً ومُتْ شَهِيداً"

Ilbas jadeedan waAAish hameedan wamut shaheedan.

(Allah ya sa) ka sanya sabo, kuma ka rayu kana abin yabo, kuma ka mutu kana shahidi (wanda aka kashe a tafarkin Allah).


DEDICATED TO....MY SISTERS😘


Page-31-32

_Bissimillahir Rahmanir_ _Rahim_



-----------------Shirun da yayi yasa Daddy yace;"Anu dina idan ba ka fada man damuwar ka ba zan iya zargin wani abu, sai inyi zargin kamar ban kai matsayin da zaka fada man damuwar kaba"

Cikin sauri Anuwar yayi saurin rike hannayen Dad din shi, tare da gir giza kai.


Murmushi Dad yayi tare da kara rike hannun shi yace;"Anu dina fada man ina jin ka, kada kaji komai zan fahimce ka"


Shiru yayi sannan ya juyar da fuskar shi, daga kallon Dad yace"wata karamar yarinya nayi ma fade..."sai yayi shiru.


Shiru Dad yayi yana kallon shi, yarasa me zaice, bai taba tunanin haka daga Yarima ba.

Yasan Yarima yana da tausayi a tunanin shi taimako zai maida shi Katsina.


A jiyar zuciya Daddy yayi kana yace;"fada man ya akayi hakan ya faru??dan nasan halin ka ba zaka iya aikata wani abu marar kyau ba saida dalili"


Shiru Anuwar yayi, murza hannun shi Dad yayi.

Kana yace"wallahi Daddy I don't know how to explain, kawai na tsinci kaina cikin wata irin sha'awa...."sai kuma ya kara juyar da fuskar shi, tare da yin shiru.


Gyaran murya Daddy yace"okay, no need to explain, my Son I understand".

Shiru ya biyo baya kana Daddy yace"ya sunan ta? kuma a wane unguwa take a Katsina??
Ya kuma kaman ninta suke??"


Shiru yayi tare da dukar da kan shi kasa;"ban san komai game da ita ba, saide nasan tana saida fura, kuma bansan fuskar taba,saide nasan tanada Funny attitude"

Kallon shi Daddy keyi cikin mamaki.

Yace;"to taya za'a gane ta Anu, ko dai Aljana ta aure ka?? ko kuma sammun da aka man ya fara shafar ka?"


Anuwar girgiza kai yake yace"please Daddy ba aljana bace, tun da naje Katsina abincin ta nike ci, furar ta ko zogalan ta, please Daddy zan nemo ta a kauyan Katsina take, kuma ban son kowa ya bini, saboda kauyen su na tsoron mutane"


"Subhanallah! Anu kana cikin hankalin ka?? Kaman ce kokai waye?? taya za'ayi nabar ka kaje cikin kauyen da suke tsoron mutane tsabar kauyan ci, ina! ba zai yiyu ba lalle aljana ce wannan yarinyar"


Cikin sauri Daddy ya saki hannun shi, yayi saurin tashi yabar dakin, ya fita ranshi a bace.


Yana fitowa yadda Momy ta gan shi yasa tayi saurin tashi tace;

"Lapiya Daddyn Manal??mike damun Anu, wani abu yasa meshi ne??"


Cikin hawaye yace;"makiyya sun taso ni gaba wallahi aljana aka turama ma Anuwar, so suke su halaka man shi wai yanzu duk halin da yake ciki wai akan wata mai fura ce,mun raba shi da Manal da kyar yanzu kuma ya rasa inda zai fada wai sai akan mai fura, ke kin san idan ba Aljana bace ba, to babu yadda za'ayi Anuwar ya koma haka saboda ita ba"


"What..! Mai fura fa kace?"daga kai yayi.

Jan hannun shi tayi ta zaunar dashi bisa kujera.

Kursim hawaye kawai take, meyasa wannan mai furar zata shigo masu rayuwa??


************

Ina zaune ni da Shatu munata ta tsar nono tana ban labari ina dariya.


Saiga Jabe a guje, haki yake ya kasa magana.

Shatu tace;"Jabe lafiya?"

Yace;"ga Baffa nan tare da Baban ta"ya nuna ni.

Ban san lokacin da na mike ba.

Nace;"Da gaske"

Yace;"wallahi ko"

Kama hannu na tayi muka wanke hannun mu tace;"ki natsu nasan zai fahimce ki,kuma ko Baffa bai san abinda ya faru ba dagani sai Iya dan haka kiyi shiru, kinga kin samu lafiya"

Kai na daga amman duk da haka ina jin tsoro gani nike kamar zai gane.

Runtse ido nayi ina tuna lokacin da nike bisa kirjin shi.

Nayi saurin bude ido na lokaci guda hawaye suka fara zubar man.

Sai ga Iya tace"muzo ga Baba na yazo"Shatu ce ta ce to,nikam kamar an daskarar dani wajen

Kama hannu na Shatu tayi muka bar wajen.

Na saka hijab din Shatu muka fito nan inda suke zaune.


Yana bisa tabarma, muna tafiya kaina a kasa jiki na sai kyarma yake, kara gyara tafiya ta nike dan kada ya gane.

Muna zuwa nida Shatu muka zukunna muka gaida shi, Shatu tabar wajen.

Ya kalleni yace;"sannu Nana Allah ya yi maki albarka, makwabcina ya fada man duk irin dukan da akayi maki, kuma Baffan su Shatu ya fada man ashe yaran shi suka tsinto ki cikin daji kin Suma, kiyi hakuri kinji Allah zai maki sakayya"hadda hawayen shi.


Nima hawaye nike,yanzu yakenan idan Baba ya gane abinda ya faru dani wane hali zai shiga??

Na goge hawaye na,da suke bin fuskata.

Baba ya mikama Baffan su Shatu hannu yace;"Nagode Malam Garba Allah ya saka da Alkhairi, naji dadi da ta fada hannu na gari".

Yace;"kada kadamu Mallam ai Nanah diyata ce, Allah ya kara karemu"

Yace;"Ameen"

Ya mike nima na mike nace;"zan dauko kwarya ta"na juya na koma ciki.

Shatu na labe jikin dannin su.

Tayi saurin rungume ni tace;"Allah mun gode maka, yanzu muje ki dauki kwaryar ki"dariya nayi nace;

"Muje na cire maki kayan ki, tunda an wanke nawa"

Bata fuska tayi tace;"wallahi banso kije nabar maki, zan ma kara maki wasu, tunda aure zanyi, kuma tun nan ki cire wannan abin na hannun ki, ki boye daga gani yanada daraja"

Cikin sauri na kalli hannu na, nayi ajiyar zuciya.

Nace;"nagode Shatu, da Baba ya ganshi dana bani"na cire ta saka manshi cikin dan abin sarkar ta da mijin ta ya siyo mata daga birni,kana ta saka cikin bakar leda ta sakaman cikin kayan da taban.


Ina jin dadi sosai yadda Shatu ke nuna man soyayya ban san lokacin da hawaye suka zubo man ba.

Nace;"nagode sosai Shatu"bata fuska tayi
tace;"kada ki damu ba komai wallahi da ina da dan uwa babba wallahi daya aure ki kodan ki huta amman mu cigaba da fadama Allah zai mana magani"


Hawaye nike ban san dame zan gode ma Shatu ba.

Iya ta shigo tace;"Kubar kukan haka, addu'a ya kamata kuyu kuma yanzu Baban ta na jiran ta, sannan Nanah duk lokacin da kike bukatar taimako kizo wajena koda lokacin Shatu tayi aure kinji?"

Kai na daga saboda ban iya magana.


Na dauki kwarya ta da ƙullin kayan da Shatu taban muka fito.

Baba ya amshi kayan yace;"sun maki yawa, muje"nabi bayan shi na tafi ina dagama Shatu hannu dake tsaye tana hawaye.

Har muka bace muna dagama juna hannu.

Tafiya kadan ta kaimu kauyen mu.

A hanya banda bani hakuri ba abinda Baba keyi sai ban hakuri, ni dai sai dai nace ba komai.


Muna shiga gida da sallama.

Inna ta fito ta tsaya bakin kofar dakin ta.

Tunda na shigo take kallo na, hakan yasa jikina kyarma ina addu'ar Allah yasa kada ta fahimci komai a tare dani.


Ma'u ta fito daga daki tazo ta amshi kayan hannun Baba tace;"Baba sannu da zuwa"

Yace;"yawwa Ma'u"

Tace;"Nanah kin dawo, muje na share maki dakin ki"zata amshi kayana Inna tace;

"Wallahi kul kika amshe su, idan kuma kika amshe su sai na bata maki rai, don tabar maki Lado kike wannan biyayyar to dama kin daina, har abada ba zaki auri Lado ba"tura baki Ma'u tayi tace;

"Amman Inana ai 'yar uwata ce dan zan taimake ta, wani abu ne"


Ta amshi kayan hannun nata suka nufi daki.

Muna zuwa ta ajeman kayan tace;"akwai biredin da Lado ya kawoman jiya kinaci, dan jiya burni yaje"na girgiza kai.

Nace;"naci abinci gidan su Shatu"ta zaunar dani bisa gadon karana.

Ta rike hannu na tace;"wai mikike ma Lado, komai sai yace kalar naki yake so, yaki sona Nanah kuma ni shi nike so banko san ganin Kabiru, shi kuma Lado sai ya kama min wulakan ci, jiya ma biredin ke ya kawo mawa yayi tunanin kin dawo, hadda lemon kwalba".

Na rike mata hannu nace;"kada ki damu 'yar uwata Lado zai soki kinji"tayi murmushi tace;"nagode".


Ta mike ta fita nabita da kallon tausayi, nida ita ban san wacece abin tausayi ba, mu duka muna cikin jarabawa Allah ka yaye Mana imanin mu .


Haka na yini ni kaɗai cikin daki sallah kaɗai ke fidda ni waje.


***********

Momy tace;"Kulsoom fada mana mike faruwa, da gaske Aljana ta auri Anu"

Nan ta fada masu komai.

Su duka suka hau yin sallallami.

Momy tace;"Lalle maganar ka gaskiya ce, baicin komai sai nata sannan kuma dole kullum a kai shi wajen ta, hadda cewa tana mashi kalar tafiyar Manal, lalle zasu yi amfani da Manal dan yaudarar shi, ya kamata Mai martaba yasan halin da ake ciki"shiru Daddy yayi.


Ya rasa abinyi duk ya rikice jin yadda labarin yake.

Lallai Aljana ce ke son yaudarar shi.


Riƙe zuciyar shi ya farayi tare da runtse ido.

Cikin sauri Momy tace;" lafiya

Please Login or Register in order to submit comment