Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yana shiga kafafun shi suka fara kyarma dan bandakin akwai tumakin su.

Cikin sauri ya fito yace;"muje"

Ba musu suka tafi Sani yace;"inazamu samu motar dazata fidda mu"

Baffa yayi murmushi yace;"ai a kafa zamu tafi"

Zaro ido Sani yayi yace;"to ai ko a Amalanken mutafi dan akwai nisa"

Baffa yace;"to bari na kira Jabe"

Gida ya koma sai gashi tare da Jabe.

Amalanken suka hau Anuwar banda kallo babu abinda yake, sai tunanin daman akwai mutane masu irin wannan rayuwar??
Kuma suna jin dadin rayuwar.


Dai-dai gidan su Nana Baffa yace;"kaga gidan mahaifinta na nan kauyen"


Kallo Anuwar yabi gidan dashi har suka wuce.

Suna zuwa Batagarawa suka hau motar Katsina.

Suna zuwa Katsina suka shiga tasha babu wanda ya damu da Anuwar tun ya dukar da kai har ya dan saki jiki.


Suna zuwa suka hau mota,motar nada tsawo sosai ga mutane aka amshi kudin motar.

Anuwar yaga yadda za'a tutsa su ya zaro ido yana kallon mutane.

Sani yace;"mutum nawa za'a saka anan?"

Mai motar yace;"Kai Malam wannan wace tambaya ce kasan mutum hudu ake sawa nan inda kuke saura mutum guda kenan"


Sani yace;"a barmana duka sit din baya guda biyu"

Cikin sauri Anuwar ya kalle shi yace;"a haka zamu zauna"


Mamaki Sani yace kudin kejara guda yaso abada nashi shida Baffa kujera daya, amman taya za'ayi su zauna a matse Anuwar??

Haka suka zauna har mota ta cika suka fita.


Lokaci guda Anuwar ya tsohe hancin shi jikin sai zufa ke zuba.

Sani zaiyi magana Anuwar ya daga mashi hannu.


Haka sukaita tafiya shikan shi Sani da yasaba wahalar kauye amman yau jinshi yake a wahalar ce.


Sunyi tafiya mai nisa sosai kana akazo wani gari mai dan girma.


Nan sukaga mutane sun fara sabka a tunanin su nanne Dan-musa su duka hamdala sukayi.

Sai sukaji wani yace;"naji kunce Dan-musa zaku a ajemu nan mu hau mota basai anje Tasha ba"

Su duka suka kalli juna Baffa yace;"eh nan Dutsam-ma ne yanzu zamu hau motar Dan-musar"


Anuwar na fito kayan shi duk sunyi dauda sun ya mutse gashin kamshi ya ya mutse duk ya rame.

Maida numfashi yake kafar shi jini ya taru ya kwanta.


Jikin shi kaikayi yake mashi da kyat yake maida numfashi.

Kallon shi mutunan da zasu tasha yake yace;"amman ku bakine dan Dan-musa aka haifeni ba wanda bansani ba?"

Sani yace;"Eh yau zamu fara zuwa"

Yaron yace;"Haba shiyasa dan har ma aikatan su nasani dayake karatu nake duk weekend saina koma"

Jin jina kai Sani yayi shine Anuwar yana gefe yana maida numfashi har juwa yake gani.

Yaron yace;"mutsaya nan gefen hanya yanzu mota na zuwa har Dan-musa"

Suka tsaya yaron yace;"Shikam dan uwanka na kama da Anuwar dan President din mu amman shi ance bai zama kasar ko jiya saida muka kalli bikin shi a Facebook maganar aketayi ba'a taba bikin da aka kashe ma kudi a Nigeria kamar nashi ba, kai gaskiya kuna kama idan na dauki photon ka na'aza a Facebook sai annemoka"


Kara kallon Anuwar yayi yace;"Kai shine kode mafarki ne"

Kamin Anuwar yace wani abu yaron ya dauki photon shi.

Dai-dai lokacin da wata katuwar matattar mota ta tsaya a gaban su yaran motar yana cewa;

"Dan-musa, Dan-musa"


Anuwar ya kalli Sani cikin mamaki.


Yaron yace;"kunga ga mota nan tazo, muje"


Sani yace;"Yarima..."


Bai idaba yaron yayi saurin kallon su, shima Yarima ya zaro ido Sani kuma ya tushe baki.





MARYAM ANKUDII {QURRAH}
*JARABTAR MU*

*Page65-66*

*Written by-Qurrahโœ๐Ÿป*

https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/

*~โœ๐Ÿฝโœ๐ŸฝGOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATIONโœ๐Ÿฝโœ๐Ÿฝ~*

*~We are bearer's of so golden pen๐Ÿ–Š~*

*~we write assidiously perceive no pain~.*

*~So magical,Our creative golden penโœ,behold our words.~*

*~A product of our pen๐Ÿ–Š,savour our words, for it will cause you no pain.~*

*Zikiri Bayan An Yi Sallama Daga Sallah.*

ุฃูŽุณู’ู€ุชูŽุบู’ููุฑู ุงู„ู„ู‡ (ุซูŽู„ุงุซุงู‹) ุงู„ู„ู‘ู‡ูู…ูŽู‘ ุฃูŽู†ู’ุชูŽ ุงู„ุณูŽู‘ู„ุงู…ูุŒ ูˆูŽู…ูู†ู’ูƒูŽ ุงู„ุณูŽู‘ู„ุงู…ูุŒ ุชูŽุจุงุฑูŽูƒู’ุชูŽ ูŠูŽุง ุฐูŽุง ุงู„ู’ุฌูŽู„ุงูŽู„ู ูˆูŽุงู„ุฅููƒู’ุฑูŽุงู…ู.
Astaghfirul-lah (3) Allahumma antas-salam waminkas-salam, tabarakta ya zal-jalali wal-ikram.

Ina neman tsarin Allah (sau uku).
Ya Allah! Kai ne Aminci, kuma daga gare Ka Aminci ya ke, alherinKa ya yawaita; ya ma'abocin girma da alheri.

ู„ุงูŽ ุฅู„ูŽู‡ูŽ ุฅู„ุงูŽู‘ ุงู„ู„ูŽู‘ู‡ู ูˆุญู’ุฏูŽู‡ู ู„ุงูŽ ุดูŽุฑููŠูƒูŽ ู„ูŽู‡ูุŒ ู„ูŽู‡ู ุงู„ู’ู…ูู„ู’ูƒู ูˆูŽู„ูŽู‡ู ุงู„ู’ุญูŽู…ู’ุฏูุŒ ูˆูŽู‡ููˆูŽ ุนูŽู„ูŽู‰ ูƒูู„ูู‘ ุดูŽูŠู’ุกู ู‚ูŽุฏููŠุฑูŒุŒ ุงูŽู„ู„ูŽู‘ู‡ูู…ูŽู‘ ู„ุงูŽ ู…ูŽุงู†ูุนูŽ ู„ูู…ูŽุง ุฃูŽุนู’ุทูŽูŠู’ุชูŽุŒ ูˆูŽู„ุงูŽ ู…ูุนู’ุทููŠูŽ ู„ูู…ูŽุง ู…ูŽู†ูŽุนู’ุชูŽุŒ ูˆูŽู„ุงูŽ ูŠูŽู†ู’ููŽุนู ุฐูŽุง ุงู„ู’ุฌูŽุฏูู‘ ู…ูู†ู’ูƒูŽ ุงู„ู’ุฌูŽุฏูู‘ .
La ilaha illal-lahu wahdahu la shareeka lah, lahul-mulku walahul-hamd, wahuwa ala kulli shayin qadeer, allahumma la mani'a lima a'tayta, wala mu'tiya lima mana'ata, wala yanfa'u thal-jaddi minkal-jad.

Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, shi kadai, babu abokin tarayya a gare Shi. Mulki na Sa ne (Shi kadai) kuma yabo na Sa ne (Shi kadai), kuma Shi ne Mai iko kan komai. Ya Allah! Babu mai hana abin da Ka bayar kuma babu mai bayar da abin da Ka hana, kuma wadda ba ta tsirar da mai wadata daga gare Ka.

ู„ุงูŽ ุฅู„ูŽู‡ูŽ ุฅู„ุงูŽู‘ ุงู„ู„ูŽู‘ู‡ู, ูˆูŽุญู’ุฏูŽู‡ู ู„ุงูŽ ุดูŽุฑููŠูƒูŽ ู„ูŽู‡ูุŒ ู„ูŽู‡ู ุงู„ู’ู…ูู„ู’ูƒู ูˆูŽู„ูŽู‡ู ุงู„ู’ุญูŽู…ู’ุฏูุŒ ูˆูŽู‡ููˆูŽ ุนูŽู„ูŽู‰ ูƒูู„ูู‘ ุดูŽูŠู’ุกู ู‚ูŽุฏููŠุฑูŒุŒ ู„ุงูŽ ุญูŽูˆู’ู„ูŽ ูˆูŽู„ุงูŽ ู‚ููˆูŽู‘ุฉูŽ ุฅูู„ุงูŽู‘ ุจูุงู„ู„ู‡ูุŒ ู„ุงูŽ ุฅูู„ูŽู‡ูŽ ุฅูู„ุงูŽู‘ ุงู„ู„ูŽู‘ู‡ูุŒ ูˆูŽู„ุงูŽ ู†ูŽุนู’ุจูุฏู ุฅูู„ุงูŽู‘ ุฅููŠูŽู‘ุงู‡ู, ู„ูŽู‡ู ุงู„ู†ูู‘ุนู’ู…ูŽุฉู ูˆูŽู„ูŽู‡ู ุงู„ููŽุถู’ู„ู ูˆูŽู„ูŽู‡ู ุงู„ุซูŽู‘ู†ูŽุงุกู ุงู„ู’ุญูŽุณูŽู†ูุŒ ู„ุงูŽ ุฅูู„ูŽู‡ูŽ ุฅูู„ุงูŽู‘ ุงู„ู„ูŽู‘ู‡ู ู…ูุฎู’ู„ูุตููŠู†ูŽ ู„ูŽู‡ู ุงู„ุฏูู‘ูŠู†ูŽ ูˆูŽู„ูŽูˆู’ ูƒูŽุฑูู‡ูŽ ุงู„ู’ูƒูŽุงููุฑููˆู†ูŽ.
La ilaha illal-lah, wahdahu la shareeka lah, lahul-mulku walahul-hamd, wahuwa ala kulli shayin kadeer. la hawla wala quwwata illa billah, la ilaha illal-lah, wala na'abudu illa iyyah, lahun-ni'matu walahul-fadl walahuth-thana-ol- hasan, la ilaha illal-lah mukhliseena lahud-deen walaw karihal-kafiroon.

Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah shi kadai, babu abokin tarayya a gare Shi. Mulki na Sa ne (Shi kadai), kuma yabo na Sa ne (Shi kadai), kuma Shi ne Mai iko a kan komai. Kuma babu dabara babu karfi sai da Allah. Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah; kuma ba ma bautawa kowa sai Shi. Ni'ima tasa ce, kuma falala tasa ce, kuma kyakkyawan yabo nasa ne. Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, muna masu tsarkake bauta (daga shirka) a gare Shi, ko da kafirai sun ki.

ุณูุจู’ุญูŽุงู†ูŽ ุงู„ู„ู‡ูุŒ ูˆูŽุงู„ู’ุญูŽู…ู’ุฏู ูู„ู„ู‡ูุŒ ูˆูŽุงู„ู„ู‡ู ุฃูƒู’ุจูŽุฑู’. (ุซู„ุงุซุงู‹ ูˆุซู„ุงุซูŠู†) ู„ุงูŽ ุฅูู„ูŽู‡ูŽ ุฅูู„ุงูŽู‘ ุงู„ู„ู‘ู‡ู ูˆูŽุญู’ุฏูŽู‡ู ู„ุงูŽ ุดูŽุฑููŠูƒูŽ ู„ูŽู‡ูุŒ ู„ูŽู‡ู ุงู„ู’ู…ูู„ู’ูƒู ูˆูŽู„ูŽู‡ู ุงู„ู’ุญูŽู…ู’ุฏูุŒ ูˆูŽู‡ููˆูŽ ุนูŽู„ูŽู‰ ูƒูู„ูู‘ ุดูŽูŠู’ุกู ู‚ูŽุฏููŠุฑูŒ.
Subhanal-lah walhamdu lillah, wallahu akbar (33). La ilaha illal-lahu wahdahu la shareeka lah, lahul-mulku walahul-hamdu, wahuwa 'ala kulli shay'in qadir

Tsarki ya tabbata ga Allah, kuma godiya ta tabbata ga Allah, kuma Allah Shi ne mafi girma. (Sau 33). Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, (Shi kadai), kuma Shi ne Mai iko kan koma.

Ana karanta wadannan surorin (kowace daga ciki har izuwa karshenta) bayan kowace sallah; amma bayan sallar Asuba da Magariba ana karanta su sau uku.

ุจุณู… ุงู„ู„ู‡ ุงู„ุฑุญู…ู† ุงู„ุฑุญูŠู…{ ู‚ูู„ู’ ู‡ููˆูŽ ุงู„ู„ูŽู‘ู‡ู ุฃูŽุญูŽุฏูŒ*ุงู„ู„ูŽู‘ู‡ู ุงู„ุตูŽู‘ู…ูŽุฏู*ู„ูŽู…ู’ ูŠูŽู„ูุฏู’ ูˆูŽู„ูŽู…ู’ ูŠููˆู„ูŽุฏู’ *ูˆูŽู„ูŽู…ู’ ูŠูŽูƒูู† ู„ูŽู‘ู‡ู ูƒููููˆุงู‹ ุฃูŽุญูŽุฏูŒ}

Bismi l-lahi r-rahmani r-rahimi.
Kul huwa l-lahu ahad, Allahu s-samad, Lam yalid wa lam yulad, wa lam yakun lahu kufu'an ahad.
{ู‚ูู„ู’ ุฃูŽุนููˆุฐู ุจูุฑูŽุจูู‘ ุงู„ู’ููŽู„ูŽู‚ู * ู…ูู† ุดูŽุฑูู‘ ู…ูŽุง ุฎูŽู„ูŽู‚ูŽ *ูˆูŽู…ูู† ุดูŽุฑูู‘ ุบูŽุงุณูู‚ู ุฅูุฐูŽุง ูˆูŽู‚ูŽุจูŽ * ูˆูŽู…ูู† ุดูŽุฑูู‘ ุงู„ู†ูŽู‘ููŽู‘ุงุซูŽุงุชู ูููŠ ุงู„ู’ุนูู‚ูŽุฏู * ูˆูŽู…ูู† ุดูŽุฑูู‘ ุญูŽุงุณูุฏู ุฅูุฐูŽุง ุญูŽุณูŽุฏูŽ }
Bismi l-lahi r-rahmani r-rahimi.
Kul a'udhu bi-rabbi-l-falaq, min sharri ma khalaq, wa min sharri ghasikin idha waqab, wa min sharrin n-naffathati fi-l-'uqad, wa min sharri hasidin idha hasad.

ุจุณู… ุงู„ู„ู‡ ุงู„ุฑุญู…ู† ุงู„ุฑุญูŠู… {ู‚ูู„ู’ ุฃูŽุนููˆุฐู ุจูุฑูŽุจูู‘ ุงู„ู†ูŽู‘ุงุณู * ู…ูŽู„ููƒู ุงู„ู†ูŽู‘ุงุณู * ุฅูู„ูŽู‡ู ุงู„ู†ูŽู‘ุงุณู *ู…ูู† ุดูŽุฑูู‘ ุงู„ู’ูˆูŽุณู’ูˆูŽุงุณู ุงู„ู’ุฎูŽู†ูŽู‘ุงุณู * ุงู„ูŽู‘ุฐููŠ ูŠููˆูŽุณู’ูˆูุณู ูููŠ ุตูุฏููˆุฑู ุงู„ู†ูŽู‘ุงุณู * ู…ูู†ูŽ ุงู„ู’ุฌูู†ูŽู‘ุฉู ูˆูŽุงู„ู†ูŽู‘ุงุณู}

Bismi l-lahi r-rahmani r-rahimi.
Kul a'udhu bi-rabbi n-nas, maliki n-nas, ilahi n-nas, min sharri-l-waswasi-l-khannas, al-ladhi yuwaswisu fi suduri n-nas, mina-l-jannati wa n-nas.

Bayan kowace sallah sannan a karanta Ayatul Kursiyyu.
{ุงู„ู„ู‘ู‡ู ู„ุงูŽ ุฅูู„ูŽู€ู‡ูŽ ุฅูู„ุงูŽู‘ ู‡ููˆูŽ ุงู„ู’ุญูŽูŠูู‘ ุงู„ู’ู‚ูŽูŠูู‘ูˆู…ู ู„ุงูŽ ุชูŽุฃู’ุฎูุฐูู‡ู ุณูู†ูŽุฉูŒ ูˆูŽู„ุงูŽ ู†ูŽูˆู’ู…ูŒ ู„ูŽู‘ู‡ู ู…ูŽุง ูููŠ ุงู„ุณูŽู‘ู…ูŽุงูˆูŽุงุชู ูˆูŽู…ูŽุง ูููŠ ุงู„ุฃูŽุฑู’ุถู ู…ูŽู† ุฐูŽุง ุงู„ูŽู‘ุฐููŠ ูŠูŽุดู’ููŽุนู ุนูู†ู’ุฏูŽู‡ู ุฅูู„ุงูŽู‘ ุจูุฅูุฐู’ู†ูู‡ู ูŠูŽุนู’ู„ูŽู…ู ู…ูŽุง ุจูŽูŠู’ู†ูŽ ุฃูŽูŠู’ุฏููŠู‡ูู…ู’ ูˆูŽู…ูŽุง ุฎูŽู„ู’ููŽู‡ูู…ู’ ูˆูŽู„ุงูŽ ูŠูุญููŠุทููˆู†ูŽ ุจูุดูŽูŠู’ุกู ู…ูู‘ู†ู’ ุนูู„ู’ู…ูู‡ู ุฅูู„ุงูŽู‘ ุจูู…ูŽุง ุดูŽุงุก ูˆูŽุณูุนูŽ ูƒูุฑู’ุณููŠูู‘ู‡ู ุงู„ุณูŽู‘ู…ูŽุงูˆูŽุงุชู ูˆูŽุงู„ุฃูŽุฑู’ุถูŽ ูˆูŽู„ุงูŽ ูŠูŽุคููˆุฏูู‡ู ุญููู’ุธูู‡ูู…ูŽุง ูˆูŽู‡ููˆูŽ ุงู„ู’ุนูŽู„ููŠูู‘ ุงู„ู’ุนูŽุธููŠู…ู }
Allahu la ilaha illa huwa-l-hayyu-l-qayyum. La ta'khudhuhu sinatun wa la nawm, lahu ma fi s-samawati wa ma fi-l-ard. Man dha l-ladhi yashafa'u 'indahu illa bi-idhnihi. Ya'alamu ma bayna aydihim wa ma khalfahum. Wa la yuhituna bi-shay'in min 'ilmihi illa bi-ma sha'a. was'a kursiyyuhu s-sama-wati wa-l-ard. Wa la ya uduhu hifzuhuma, wa huwal-l-aliyyu-l-azim.

Allah, babu wani abin bautawa da gaskiya sai Shi, Rayayye, Mai tsayuwa da koma. Gyangyadi ba ya kama Shi, wala barci. Abin da yake cikin sammai da abin da yake cikin kasa nasa ne. babu mai yin ceto a wurinsa sai da izininsa. Yana sane da abin da yake gabansu (watau al'amarin duniya) da abin da yake bayansu (na al'amarin lahira). Ba sa sanin wani abu daga iliminsa, sai abin da Ya so. Kursiyyunsa (watau gadonsa) ya yalwaci sammai da kasa, kuma kiyaye su (sammai da kassai) ba ya yi masa nauyi. Shi ne kuma madaukaki, mai girma.

ู„ุงูŽ ุฅูู„ูŽู‡ูŽ ุฅูู„ุงูŽู‘ ุงู„ู„ูŽู‘ู‡ู ูˆูŽุญู’ุฏูŽู‡ู ู„ุงูŽ ุดูŽุฑููŠูƒูŽ ู„ูŽู‡ูุŒ ู„ูŽู‡ู ุงู„ู’ู…ูู„ู’ูƒู ูˆูŽู„ูŽู‡ู ุงู„ู’ุญูŽู…ู’ุฏูุŒ ูŠูุญู’ูŠููŠ ูˆูŽูŠูู…ููŠุชู ูˆูŽู‡ููˆูŽ ุนูŽู„ูŽู‰ ูƒูู„ูู‘ ุดูŽูŠู’ุกู ู‚ูŽุฏููŠุฑูŒ.
La ilaha illal-lahu wahdahu la shareeka lah, lahul-mulku walahul-hamd, yuhyee wayumeet, wahuwa 'ala kulli shayin qadeer

Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, Shi kadai, babu abokin tarayya a gare Shi. Muli nasa ne (Shi kadai), kuma yabo nasa ne (Shi kadai), yana rayarwa, kuma yana kashewa, kuma Shi ne mai iko a kan komai (sau goma bayan sallar Magriba da Sallar Asuba).

ุงูŽู„ู„ูŽู‘ู‡ูู…ูŽู‘ ุฅูู†ูู‘ูŠ ุฃูŽุณู’ุฃูŽู„ููƒูŽ ุนูู„ู’ู…ุงู‹ ู†ูŽุงููุนุงู‹ ูˆูŽุฑูุฒู’ู‚ุงู‹ ุทูŽูŠูู‘ุจูŽุงุŒ ูˆูŽุนูŽู…ูŽู„ุงู‹ ู…ูุชูŽู‚ูŽุจูŽู‘ู„ุงู‹.
Allahumma innee as-aluka ilman nafi'an, warizqan tayyiban, wa'amalan mutaqabbalan.
Ya Allah! Ina rokonka ilimi mai amfani, da arziki kyakkyawa (watau na halal), da aiki wanda za a karba. (bayan sallama daga sallar Asuba).

DEDICATED TO.....MY SISTERS๐Ÿ˜˜

Bissimillah Rahmanir Rahim

Page65-66

----------------Muna tashi da safe Inna ita tayi masu wanka ta shiryasu cikin kayan su, ni kuma tace muje ita zataman sai anyi sati tanaman.

Muna fitowa ta zaunar dani tabani dumamen tuwo naci ta mikoman yaran ina shayar dasu.

Lokaci guda naji hankali na ya kwanta dan nasan Inna bazata cutar damu ba daman kirkin ta shine sanadin zuwa na Bauchi.

Ina nan ta gama Fura tayi ayukan ta, idan nace zan tayata ta kama fada bansan ciwon kaina ba da danyen jegon zanyi aiki.

โ™ฆโ™ฆโ™ฆโ™ฆโ™ฆโ™ฆโ™ฆโ™ฆ

Sani cikin sauri yace;"Kai mantawa nake kace abar cemaka Yarima kai baka ga kamar ku ษ—aya ba".

Yaron yayi murmushi yace;"ashe kunsan Yarima Anuwar? koda yake waye baisan shi ba, saboda son da President kema shi kamar shi ya haife shi, ni sai daga baya naji ance ษ—an Uwan shi ya haife shi".

Sani yace;"ko ashe ba dan President din bane? mu yau muka faraji"

Anuwar ya kalli motar da zasu shiga wajen zaman ta duk ya yage, gashi ma matsalar tayi dau da, runtse ido yayi ya tuna bannar da yayi cikin sauri ya shiga suka bi bayan shi.

Kujerar dake kallon wani benci ya zauna, saboda zafi baya.

Suna shiga yaron motar ya rufe, sukaci gaba da tafiya yaron motar yana buga motar yana;"Dan-musa, Dan-musa"

Ko kadan Yarima baison kara amman yau gashi ana buga mota yana ciki.

Kan shine ya dauki ciwo dau rewa kawai yake, suna nan sun bar wani gari suka iske wasu mata na kauye ne tsaye daga gani daga biki suke, suka tsaya yaron mota yace ina zasu suka fadi wani kauye ya bude masu.

Matan suka shigo wasu sai chin kifi suke wasu kuma awara kowa ne da abinda yake, suka cika kujerun baya saura inda Anuwar yake Sani zaiyi magana Anuwar ya daga mashi hannu dole yayi shiru.

Wata mata dake rike da Kaza mai rai a hannu tazo kusa dashi ta zauna kazar ta kamayi kamar zata tashi tana tsuwa.

Sani dake kallo jikin shi sai kyarma yake taya za'ayi ace Yarima ne haka mutunan dake da tsandar abu yau Kaza ce ke hawa hannun shi.

Innalillahi! gaban shi faduwa yake kada wani Abu yasamu Anuwar komi Dad zan iya yi akan hakan.

Ga matar kusa dashi na chin kifi, baigama wannan tunanin ba mota ta tsaya wasu mutane zasu shigo, bencin dake kallon su Anuwar zasu zauna zaro ido Sani yayi.

Yana kallon Anuwar da ya dukar da fuska yasan akwai matsala kenan.

A haka har suka sabke mutanan, sannan suka kara tafiya suka iske wata hanya sai akace to ga marabar Dan-musa kanafa suka dauki hanya.

Suna shiga anayin tafiya kadan dasu sukaga yaron yace zai sabka Baffa yace Suma su sabka.

Suna Sabka Baffa ya fadi sunan inda zasu tafiya kadan sukayi suka isa wani kofar gida, gidan kasa ne amman ba tsoho ba.

Sukayi Sallama Sai gashi ya fito.

Yana kallon su yayi murmushi yace;"Sani kaje inda muke akace nataso sannunku da zuwa"

Sani yace;"Wai daman kai muke nema?"

Suka gaisa da Baffa sannan ya mikama kowa suka gaisa Anuwar ya gane shi lallai kam yasan shi, shine suka hadu kofar gidan su Sani.

Nan Baffa yayi mashi bayani ya kalli Anuwar yace su shiga wani dakin zaure.

Suna shiga da Sani da Baffa suka fito waje.

Baba ya kalli Anuwar yace;"waye kai da zaka zo neman Nana?? Kuma a ina kasanta? Ko kaine wanda ka bata mata rayuwa?"

Yadda Baba ke maganar Babu wasa ko kadan a fuskar shi.

Anuwar yace;"ina sone kawai naji shin tanada rai kota mutu, zan amsa maka tambayar ka amman saika amsaman tawa, ita ta kawoni nan"

Baba ya kalli Anuwar ya dan tsura mashi ido kamar yasan shi shiru yayi ya dauke kai daga kallon Anuwar yana nazarin maganar shi, da kuma tambayoyi da dama a bakin shi.

Baba yace;"Allah shikade ne yasan Nana nada rai ko bata dashi, saboda a tsakar dare mutanan kauyen mu suka koreta saboda ciki ya bayyana a tare da ita, wannan mutunan daya rakoku Abokina ne da safe dayaji labari yabi bayan ta yana tambayar mutane ko sun ganta amman ba'a samu wanda ya ganta ba, Allah kade yasan wannan al'amari kullun cikin cigiya nake amman shiru, korar da yan kauyen mu sukayi ma Nana yasa na dawo nan saboda ban iya zama a garin, Nana ta hadu da Jarabta iri-iri a rayuwarta amman duk cikin su faden da akayi mata yafi muni yayi mata tabo, wallahi bazan iya yafema duk wanda ya aikata haka ga Nana ba zan iya komi a kansa zan iya daukar mata fansa, ina rokon Allah ya saka mata, Idan tana duniya kuma Allah ya bayyanata idan kuma Allah ya amshi abunshi Allah yasa hakan shiyafi zama mata Alkhairi"

Anuwar da idon shi sukayi jawur yace;"yanzu shikenan ko photon ta babu a saka a gidajen television??"

Murmushi Baba yayi yace;"Duk abinda ke gareni na saida domin neman Nana duk nasa anyi shela amman babu labari"

Shiru Anuwar yayi sai chan kamar ya tuna wani abu yace;"an tambaya duka tashar motochin Katsin?"

Baba yace;"Har littafin da ake rubuta sunan fasinjoji anbani na duba amman babu sunan ta, addu'a ita kade Nana ke bukata"

Anuwar yace;"wacece mahaifiyar ta"

Baba yace;"Bata da Uwa duk duniya wajena kade Nana kejin sanyi sai kawarta Shatu mukenan mukeson Nana a duniya yan kauyen mu da sauran kusa da kauyen mu duk sun tsaneta saboda matar Uba hakan yasa ba'a sayen sana'ar ta har saita fita Binni, Matata itace ta kullah komi saboda kawai ba ita ta haifeta ba tunda na kawota take gana mata azaba har tabar gidan"

Anuwar ya shiga tunani to miyasa tace itace Uwarta a videon nan kode duk rashin kauna ce ko akwai wani abu a kasa??

Nan Baba ya fara bashi labarin Ukubar da Nana tasha a hannun Inna.

Zuciyar Anuwar bugawa take tunda yake a duniya baitaba jin labari kalar na Nana ba baitajin Jarabta irin tataba inama ace tanada rai.

Kama hannun Baba yayi yace;"insha Allah inde tanada rai saina gano maka ita, ko ina ta shiga nine zan ganota, to amman matar ka kuna tare"

Baba ya daga kai, ido Anuwar ya zaro.

Baba yace;"Rakiya itace macen dana fara aure, tanasona sosai haka nima inasonta diyar mai kudi ce a kauyen su, ni kuma almajiri ne dan Mai gari su kesonta tace saini duk da nike almajiri kuma ba'asan dangina ba haka akayi auren mu mahaifin ta yabani gida yaban gona sannan kusan duk wasu lamurran gidana shikeyi, bamu da matsala da ita, saide matsalar ta guda KISHI, kishin ta yayi yawa idan nakai dare a waje zata fara haskani tana kallona wanibi idan zanfita da daddare bina take a baya wai dan kada naje zance hakade nake hakuri da halayen ta, a haka mahaifin ta ya rasu aka basu gado mai yawa, watanni kadan na kwanta ciwo akace Sammune jifa wani malami yayiman lokacin yaran mu sun girma itake zuwa gona itake cidamu tayi wahala sosai dani saboda ko tashi ban iyawa ga wahalar jinya gata neman abinda zamuci, kuma nina hanata taba kudin gadon ta, nanfa tafara nema man magani kullun idan taji malami a wani kauye haka zatayi sabko ashe duk abin nan da kudin gadon ta takeyin shi, saida a haka har nasamu lafiya yan uwanta babu abinda basu ceba haka mahaifiyar ta amman ta daure, hakan yasa nakejin kunyar sakinta ta koma ma danginta shekara Biyar ina kwance tana wahala dani nabarta a gida sannan ga yaran mu yanzu haka bata gani diyarta budurwa ke kula da ita tasamu matsalar ido"

Ajiyar zuciya Anuwar yayi Baba yace;"kaji tambayoyin ka saura nawa ka amsa"

Anuwar na bude baki zaiyi magana yaji jiniya gaban shine ya fadi.

Jin an tsaida motar kofar gidan Malam yasa su duka sukayi shiru.

Jin hayaniyya yasa su duka suka tashi.

Sukayo waje kofar gidan sojoji ne cike da mutane ga yan jaridu.

Sani yace;"Allah ya taimake ka akwai matsala wai sojoji kai suke nema wai anga photunan ka a Facebook cikin motar haya a cikin shigar shigar talauci"

Zaro ido Anuwar yayi tareda cewa;"Subhanallah! ya akayi hakan ta faru? Dad da Abie sun sani?"

Kamin Sani yayi magana daya daga cikin sojojin ya iso.

Sani yace;"mutafi akwai matsala ga waya nan hannun shi zakuyi magana da Dad dinka"

Anuwar ya amshi wayar hannun sojan.

Muryar Dad yaji a rude yace;"Anuwar mun gode da tozartamu da kayi a idon duniya, idan mun isa dakai kabisu su ajeka Katsina, muna godiya da sakayyar da kayi mamu, idan ka kara one minute a garin nan saide kanemi wasu iyayen amman bamu ba"

Daga haka ya kashe wata Idon shi sunyi Jawur ya rasa mike mashi dadi a duniyar dami zaiji ne??

Sani ya kama hannun shi;"yace muje"

Anuwar ya kalli Baffa da Malam da suke al'jabi yace;"Nagode maku sosai, Sani zai kawo maku sako kuma zandawo mu ida maganar mu zakaji amsar ka Malam nagode"

Ya kalli Baffa yace;"ka gaidaman da Shatu kace mata Nagode da kaunar da tayima Nana"

Ya juya yabar su cikin mamaki to minene alakar shi da Nana?

Yana fito aka fara mashi questions.

Nan fa Sani yaba yan jarida labarin Anuwar yanason taimako ne yanaso yasan ya mutane ke rayuwa a cikin taulauci yanason ya taimaka ma wata yarinya da yayi sayen fura wajen ta, nan yabasu labarin abinda ya faru.

Kowa mamaki yake wajen

Anuwar na cikin wata mota anyi gaba dashi fuskar nan tashi tayi jawur shikade yasan yadda yakeji jiyake zuciyar shi tamkar ta fito ya huta.

Koda suka isa Katsina Dad ya iso.

Yadda yaga Anuwar a tv ashe a fili yafi abin tausayi hawaye ne suka zuboma Dad ya juya cikin sauri yayi hanyar shiga mota ya shiga, ganin haka Anuwar shima cikin sauri yabi bayan shi, koda ya isa har an kulle mota.

Ya koma ya shiga motar baya.

Rike kai yayi yau shine Dad ke rufema mota.

Basu tsaya ko inaba sai airport suna fitowa nan ma a cike take da manema labarai.

Babu bata lokaci jirgin su ya tashi har yanzu Daddy bai cemashi komi amman idanun shi jawur.

Suna isa Bauchii da kyat aka saka Anuwar mota saboda taron jama'a da yan jarida kowane suyake Anuwar yayi magana.

Kai tsaye gida suka nufa, suna shiga gidan kowa yana waje banda Abie.

Hannun shi Daddy ya kama yayi part din Abie yan Uwan shi banda kuka Babu abinda suke.

Suna isa Abie yana tsaye tsakiyar parlo.

Kallon Anuwar yayi shima ranshi bace.

Ya iso inda suke tsaye shida Dad.

Dad yabar Anuwar tsaye yaje ya zauna bisa kujera ya rike kanshi dake sarawa.

Karar marin da yaji yasa dagowa cikin sauri Abie ne ke marin Anuwar.

Cikin sauri ya mike yana cewa;"miyasa zakayi haka?? Anuwar bai cikin hankalin shi wallahi iskane aka hadashi dasu suke sakashi komi baida laifi Makiya nane sukeso su halakar man dashi kamar yadda suka halakar da MANAL dina"

Hannu biyu Abie ya saka ya ingiza Anuwar daman babu karfi a jikin Anuwar aiko ya tafi yayi kasa.

Kanshi ya bugi wata flower da aka aje wajen.

Daddy yace;"Miyasa baza ka yadda da zance naba, Anuwar baida laifi ko kadan yanzu idan wani abu yasame shi fa, ka duba kaga halin da yake ciki baka tausa mashi ba sai duka"

Cikin sauri yayi inda Anuwar yake kwance ya dago shi.

Koda ya dagoshi jini ke zuba a fuskar shi, Anuwar ya bude ido gani yayi Dad dinshi ya koma biyu tun yana ganin Dad dinshi har ya daina.

Jijjiga shi Dad yakeyi yana cewa;"Anuu!! Anuu!! katashi mana"

Kanga kashi yayi wajen numfashin shi yaji baya numfashi.

Kama hannun shi ya daga yasaki yaga ya fadi.

Zame Anuwar yayi daga jikin shi ya kwantar dashi bisa center carpet din dakin , ya mike tsaye yana hawaye yana dagowa yaga Ammie da Momy da sauran kishiyo yin Ammie a tsaye suna hawaye.

Yayi saurin goge hawayen shi, ya kara dukawa ya kullema Anuwar idanun shi.

Abie ya kalli Dad cikin tashin hankali.

Dad ya girgiza kai yana kara goge hawayen da suka zubo mashi.

Ammie ta matso kusa tace;"Shima sun kashe shi ko? ku fadamana yanada rai ko ya mutu"

Kasa kallon ta Dad yayi, karar tafiya sukaji suna juyawa sukaga Kulsoom.

Ta iso itama fuskarta hawaye be kwance.

Ganin Yarima kwance tsakar daki ido rufe yasa ta kalli Momy dake gefen ta tana hawaye.

Tace;"Momy miyasamu Prince miyakeyi a kasa, Momy ku kalli jikin shi ya kumbura kafar shi jini ya taru Momy kuyi wani abu"

Matsawa tayi kusa da Ammie dake kallon Mai martaba da Dad tace;"Ammie ku fadaman mike faruwa dan Allah"

Cikin sauri Dad ya dauko waya yayi waje yana hawaye.

Ammie ta durgusa inda Anuwar yake kwance baya motsi ko kadan rike hannun shi tayi tana kuka tana cewa;"Anuwar ka bude ido nice Ammien ka, Anuwar kada katafi kabar ni"

Tun tanayi a hankali har ta kaiga tana rungumar Anuwar tana sabbatu

Momy ta iso ta durgusa kusa da ita, itama hawaye take Kulsoom ma.

Cikin sauri saiga Dad ya shigo daukar Anuwar yayi, yayi waje aka saka shi mota.

Shida Abie suka shiga, sukabar gidan a guje.

Momy da Ammie da mutanan gidan sukabi bayan su.

Suna isa anshiga da Anuwar Doctors sunyi kanshi.

A bakin kofar dakin da Anuwar yake suka iske su Abie.

Cikin lokaci kadan hospital din ta cika da Family dinsu.

Suna tsaye kowane yana kaiwa da komowa babu mai magana suna jiran Doctors su fito.

Suna nan tsaye kusan two hours saiga Doctor Ashraf ya fito.

Yana fitowa yaga asibitin a cike.

Tsaye yayi ya kasa motsi, su duka suka zagaye shi suna jiran jin amsar shi.

Dad ya kalle shi cikin bacin rai yace;"kafada mana yana da rai??"

Shiru Doctor Ashraf yayi ganin yadda suke kallon shi.

Dad ya kama mashi kafada da hannu biyu yace;"kalleni kafadaman wane hali yaro na yake, idan baka iya magana ka baceman da gani, kayi magana"

Kawai sai sukaga jikin Doctor Ashraf na rawa.

Su duka hankali a tashe suka zuba mashi ido ganin yadda sai Kyarma.

Cikin in-inah ya fara magana yace;"Ummm.............
"

MARYAM ANKUDII {QURRAH}
*JARABTAR MU*




*Written by-Qurrahโœ๐Ÿป*




https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/

*~โœ๐Ÿฝโœ๐ŸฝGOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATIONโœ๐Ÿฝโœ๐Ÿฝ~*

*~We are bearer's of so golden pen๐Ÿ–Š~*

*~we write assidiously perceive no pain~.*

*~So magical,Our creative golden penโœ,behold our words.~*

*~A product of our pen๐Ÿ–Š,savour our words, for it will cause you no pain.~*




DEDICATED TO.....MY SISTERS๐Ÿ˜˜


Bissimillah Rahmanir Rahim



Page-67-68



--------------Muna zaune da Inna muka ji karar motoci Inna tace; "anya lafiya garin? Ko Shugaban kasa ya shigo garin ne? ko kuma Gwamna".


Tana kulle baki muka ji sallama.

Inna ta fita naji tana cewa; "Subhanallah! Sani mike faruwa dakai??".

Cikin kuka naji muryar namiji yana cewa; "Inna Yarima!! Inna Yarima...!".

Cikin sauri tace; "miya samu Yariman??".

Yace; "Har yanzu ba'asan yanada rai ba ko babu, Inna idan Yarima ya mutu nima kila sai sun kashe ni, saboda tare dani muka yi tafiyar".

Inna tace; "Innalillahi! ya Allah ka tada kafadun Yarima".


Ni kaina jikina duk ya mutu, gashi gabana faduwa yake lokaci guda naji duk wani kuzari dake gareni ya gushe.

Zama nayi nayi tagumi hawaye ne suka zubo min, na rasa hawayen menene.



โ™ฆโ™ฆโ™ฆโ™ฆโ™ฆโ™ฆโ™ฆโ™ฆ


Su duka wajen yayi tsit an zubama Doctor Ashraf ido.

Yace; "umm.....daman yanada rai...".

Bai ida maganar shi su duka suka dauki Hamdala, murmushi ya bayyana a fuskar Dad.

Zuwa yayi ya rumgumi Abie yana hawaye yace; "Banson na rasa Anuwar, kayiman izini nabar kasar dashi yanzu, yana bukatar kulawa ta musamman".

Abie ya dago shi yace; "Anuwar D'anka ne yana bisa ikon ka, banson irin wannan maganar".


Cikin wannan time din Dad yasa aka hada komi na tafiya, daga shi sai Momy sai Kulsoom suka tafi.

Cikin daren sukabar kasar, Spain suka nufa inda suke ganin likitan su.


Koda suka isa airport din Spain ana jiran su.

Haka aka saka Anuwar mota ba tare da sanin shi ba.



โ™ฆโ™ฆโ™ฆโ™ฆโ™ฆโ™ฆโ™ฆโ™ฆ

Har dare jikina babu dadi na kasa cin abinci sai zufa da nike yi, duk jikina yayi sanyi.

Ranar kasa bacci nayi Inna sai fada take min, lafiya na

Please Login or Register in order to submit comment