Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

chanza ko akwai abinda ke damu na ko akwai wani abu??

Amsar itace sai dai nace mata a'a ban san fuskar shi ba, amman na san kalar jinin shi tunda gashi a jikina.


Kallon jikina nake kamar zanga jinin shi a jiki na.


Haka na yini har asuba ban runtsa ba, tun ina hawaye har na koma yi mishi addu'a.


Damuwar ciwon Yarima yasa ko yara na ban iya kulawa, ina jin su suna kuka haka zan barsu sai dai Inna tayi ta faman lallashi tana min fada, kallon ta kawai nake amman ban san me take cewa ba, zuciyata tana wajen Yarima.

Nikai na saboda damuwa hadda ciwon Kai.


♦♦♦♦♦♦♦♦


Inda Prince yake babu mai ganin shi sai Doctor's babu mai shiga wajen saide ka hango shi kwance da Oxygen a hanci, a kwance yake an rufe mashi jiki fuskar shi kade kake hange, ko motsi bayayi haka ta kasan ce yau har gashi ya kwana biyar a asibitin amman yadda suka kawo shi haka suke hangen shi.




♦♦♦♦♦♦♦♦

Haka nake rayuwa duk wani farin ciki na ya dauke kullun ina cikin bakin ciki.

Na koma shiru-shiru sai sunyi kukan gaske kana nake shayar dasu.


Yau sati guda kenan da haihuwar su, Inna tasa akayi masu aski tunda safe, Jim kadan naga ana shigo da yan kar kun raguna cikin mamaki nake kallon Inna dake nuna inda za'a ajiye su.

Tace; "Ragunan sunan sune aka yanka, ya kamata ki daina sanyin jikin nan ki rage damuwa yanzu kije kiyi wanka".


Nace; "Inna ina aka samu kudi?".

Tace; "Kada ki damu Yarima ya kawo min su masu yawa, ban san yadda zanyi dasu ba, suna wadata mu da abinci da komi yanzu haka cikin turamen daya aikoman ne nasa aka dinka miki guda uku".

Murmushi nayi nace;"Inna banda bakin gode miki sai dai ince Allah ya saka maki da Alkhairi".


Murmushi tayi tace; "yanzu tafi kiyi wanka ki shirya".

Wanka nayo na zauna bisa gado ina kallon atamfofin da Inna ta ajiye min , nace; "ko ina naje komi nawa daga Yarima yake fitowa komi yasa haka?".

Murmushi nayi, duka riga da zanine, kayan sunyi kyau duk da dinkin kalar namu ne na kauyawa ba kalar na gidan Hajiya ba.

Na mike na saka kayan, sunyi dai-dai dani na daura kallabi irin namu na kauyawa.


Abinci Inna ta kawo min tace na kara sha sannan ga wani magani cikin kofi tace nasha na ruwan Nono ne saboda yara biyu ne.

Haka mukayi nida Inna da yamma ta aika aka kira matar Sani da Salisu suka zo.


Sai dare suka gama aikin kana suka gyara gidan Inna ta diban masu mai yawa suka tafi gida.



♦♦♦♦♦♦♦♦


Yau ranar Monday, kwance yake bisa gadon, a hankali ya bude ido ya kalli inda yake.

Bin dakin yayi da kallo ya gane kasar da yake.


A lokacin Dad ne kadai a parloun dakin da aka ajiye shi, lokacin yana magana da Doctors zai wuce gida.

Yana juyowa ya hango Anuwar zaune bisa gadon.


Cikin sauri shida Doctor's din suka yi ciki.


Zaune yake bisa gadon hankalin shi yana akan agogon dakin.

Suna shigo ya kalli Dad, zaiyi magana Dad yayi saurin matsowa kusa dashi.


A hankali yace; "Dad yau yaushe?".


Murmushi yayi ya shafa sumar kanshi yace; "Monday, but why dis question?".


Dukar da kai yayi yace; "Nothing".


Doctor's suka gama aune-aunen su suka tambaye shi yace baijin komi, nan aka rubuta mashi magani, yace Dad zaibi.



Tare suka fito a cikin daren suka nufi gida.

Suna Isa ana bude masu Dad ya kama Anuwar saboda har yanzu kafar shi na mashi ciwo.


Ga jikin shi babu dadi saboda kwanciya daya sha.


Momy da Kulsoom su duka kowa ya tafi part dinshi.

Suna jin shigowar motoci suka san Dad ya dawo, su duka suka fito a parloun saboda dama yau ne akace zai farka koya karfa yayi losing din Memory dinshi koya koma normal shiyasa basuyi bacci ba.


Su duka suna shigowa suka ga Anuwar kusa da Dad, cikin sauri Momy ta Isa wajen tace; "Anuu".

Yace;"yes Mom".

Rumgume shi tayi tana hamdala tare da kallon jikin shi, lallai ya samu sauki.


Cikin sauri ta mike tayi kitchen, Dad yana neman wayar Mai martaba ya fada mashi banda murmushi babu abinda yake, hannun shi cikin na Anuwar.


Lumshe ido Anuwar yayi, tunanin shi ya rabu biyu tunanin yau ne ranar Sunan twins gashi bainan, sannan kuma taya iyayen shi zasu yarda ya kara barin su yaje neman wata yarinya, ba matsalar ma Dad bai yadda da ita mutum ce ba.


Jim an damtsi hannu na da karfi yasa nayi firgigi.

Dad da Momy ne ke kallo sa sai Kursim dake tsaye ta kasa isowa sai hawaye dake bin fuskarta.


Dad yace; "are you okay?".

Cikin sauri nace; "Yes, I am....fine. I am perfectly fine Dad".

Tare da Smile duk dan kada ya saka mashi kokwanto kuma yasan ya mashi laifi sosai.


Yace; "kaji abinda nace?".

Murmushi nayi nace; "I hear you Dad".

Yace haka amman baisan mi Dad yace ba.

Yace; "Dad I hope you're not angry with Sani, kada ka koreshi dole yasa ya bini".


Murmushi yayi yace; "kada ka damu komi ya wuce yanzu ina bukatar lapiar ka".

Murmushi yayi yace; "Thank you Dad".


Momy tace; "Muje yayi wanka yazo yaci abinci, dole gobe gidan nan muyi walima".

Murmushi Anuwar yayi ya mike yana rike kai cikin sauri Dad ya kamashi, yasan baida karfin jiki a jikin shi.

Sosai Anuwar ke ba Dad tausayi yana ganin aljana ta ruda mashi d'ah.


Wajen da Kulsoom take tsaye suka zo zasu gifta sai a lokacin Anuwar ya kalli Kulsoom, shiya manta da ita, cikin zuciyar shi yayi istigifari Allah ya yafe mashi.


Daki Dad ya kai shi shi yayi mashi komi kana ya dawo ya zauna gefen bed, Anuwar na fitowa Dad ya bashi saida ya shirya kana Dad yace sutafi.

Anuwar yace; "Dad ina son na zama ni kadai".

Dad yace; "bai yadda ba ga abinci an shirya masu".

Anuwar bata fuska yayi tare da dukar da kanshi.


Dad ya dawo inda yake tsaye ya zaunar dashi suka zauna tare Dad yace;"mikakeso na baka komi nene zan maka shi kodan na cire ka a cikkin kunci, Anuwar bana so na rasa ka".

Ya ida maganar cikin jimami da kulawa.

Ya kama hannun Dad yace; "alfarma guda ce please Dad kayi min".

Dad ya maida hankalin shi wajen Anuwar dan jin wace alfarma Anuwar keso.

Dad yayi shiru yana jiran mi Anuwar zai ce daya dukar da kanshi??

Dafashi yayi ya dago fuskar Anuwar da hannun shi.


"Subhanallah!! Prince wace damuwa gareka har idanun ka suka koma jawur, ka fada min minene matsalar yanzu zanyi maganin ta, innalillahi".


Lokaci guda natsuwar Dad ta gushe.


A hankali Anuwar ya bude baki.....🤪

MARYAM ANKUDII {QURRAH}
*JARABTAR MU*


*Page-69-70*

*Written by-Qurrah✍🏻*




https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/

*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*

*~We are bearer's of so golden pen🖊~*

*~we write assidiously perceive no pain~.*

*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*

*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*


*Addu'ar Yayin da za a yi Barci:*

Idan mutum ya zo kwanciyar barci sai ya hada tafin hannayensa biyu, ya karanta wadannan surori na Alkur'ani, yana yin tofi cikin hannayen nasa;

(قل هو الله أحد)
(قل أعوذ برب الفلق)
(قل أعوذ برب الناس)
(Qul'huwallahu Ahad)
(Qul'a'uuzu Bi Rabbil Falak).
(Qul'a'uuzu Bi Rabbin Nas).
Sannan ya shafu su iy ainda zai iya na jikinsa; yana farawa da kansa, da fuskarsa da kuma gaban jikins.a ya yi haka har sau uku.



Ya Karanta Ayatul-kursiy:

(اَللهُ لاَ إِلَهَ إِلاَّ هُوَ الْحَيُّ الْقَيُّومُ)
Allahu La'ilaha illahuwal Hayyul Qayyum… (Ilaa A'khiruhaa).
Har zuwa karshenta, wanda ya karanta ta yayin da ya zo kwanciya to ba zai gushe ba yana da wani mai tsaro gare shi daga Allah, kuma shaidan ba zai kusato shi ba har ya wayi gari.


{آمَنَ الرَّسُولُ بِمَا أُنزِلَ إِلَيْهِ مِن رَّبِّهِ وَالْمُؤْمِنُونَ كُلٌّ آمَنَ بِاللّهِ وَمَلآئِكَتِهِ وَكُتُبِهِ وَرُسُلِهِ لاَ نُفَرِّقُ بَيْنَ أَحَدٍ مِّن رُّسُلِهِ وَقَالُواْ سَمِعْنَا وَأَطَعْنَا غُفْرَانَكَ رَبَّنَا وَإِلَيْكَ الْمَصِيرُ * لاَ يُكَلِّفُ اللّهُ نَفْساً إِلاَّ وُسْعَهَا لَهَا مَا كَسَبَتْ وَعَلَيْهَا مَا اكْتَسَبَتْ رَبَّنَا لاَ تُؤَاخِذْنَا إِن نَّسِينَا أَوْ أَخْطَأْنَا رَبَّنَا وَلاَ تَحْمِلْ عَلَيْنَا إِصْراً كَمَا حَمَلْتَهُ عَلَى الَّذِينَ مِن قَبْلِنَا رَبَّنَا وَلاَ تُحَمِّلْنَا مَا لاَ طَاقَةَ لَنَا بِهِ وَاعْفُ عَنَّا وَاغْفِرْ لَنَا وَارْحَمْنَا أَنتَ مَوْلاَنَا فَانصُرْنَا عَلَى الْقَوْمِ الْكَافِرِينَ}
Amanar rasulu bim aunzil ilayhi min rabbihi wa lmu'minuna, kullun amana billahi wa mala'ikatihi wa kutubihi wa rusulihi, la nufarriku bayna ahadin m-min rusulihi, la nufarriku bayna ahadin m-min rusulihi. Wa kalu sami'na wa ata'na, ghufranaka rabbana wa ilayka-l-masir.
La yukallifu l-lahu nafsan illa wus'aha, laha ma kasabata wa 'alayha ma kasabata, rannaba, la tuk'akhizina in nasina aw akhta'ana, rabbana wala tahmil 'alayna isran kama hamaltahu 'ala l-lazina min qabilina rabbana wa la tuhammilna ma la taqata lana bihi. Wa 'fu anna, wa ghfir lana wa rhamna. Anta mawlana fa-nsurna 'ala-l-qawmil-l-kafirin.

Manzon ya yi imani da abin da aka saukar gare shi daga Ubangijinsa, haka ma muminai; kowanne ya yi imani da Allah, da Mala'ikunsa, da litattafansa, da Manzanninsa, (suna cewa) ba ma rarrabewa tsakanin daya daga cikin Manzanninsa. Kuma suka ce mun ji (abin da Ka umarce mu da shi, ji na karba) kuma mun bi. Gafararka muke roko ya Ubangiji, kuma gare Ka makoma take. Allah ba ya dora wa rai (wani abu sai abin da yake da ikon aikata shi; abin da ya aikata (na alheri) yana gare shi, kuma abin da ya aikata (na sharri) yana kansa. (Ku ce) 'Ya Ubangijinmu! Kada ka rike mu idan uka manta ko muka yi kuskure. Ya Ubangijinmu! Kada ka dora mana, abin da za mu iya shi ba. Ka yi afuwa a garemu, Ka yi mana gafara, ka ji kan mu. Kai ne Majibincin al'amuranmu, sai ka taimake mu a kan mutane kafirai".


Annabi, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya ce; "Idan dayanku ya tashi daga shimfidarsa sannan ya dawo ya kwarya, to ya karkade ta da gefen gyautonsa sau uku, sannan ya yi Bismillahi, domin bai san abin da ya maye gurbinsa ba bayan ya tashi. Idan ya kwanta ya ce;

بِاسْمِكَ رَبِّي وَضَعْتُ جَنْبِي، وَبِكَ أَرْفَعُهُ، فَإِنْ أَمْسَكْتَ نَفْسِي فَارْحَمْهَا، وَإِنْ أَرْسَلْتَهَا فَاحْفَظْهَا بِمَا تَحْفَظُ بِهِ عِبَادَكَ الصَّالِحِينَ.
Bismika rabbee wada'tu janbee wabika arfa'uh, fa-in amsakta nafsee farhamha, wa-in arsaltaha fahfathha bima tahfazu bihi 'ibadakas-saliheen.

Da sunanka ya Ubangijina na kwana, kuma da izininka ne nake tashi. In ka rike raina (da mutuwa), to Ka ji kanta, in Ka sake ta kuwa, ka kiyaye ta da abin da Kake kiyaye bayinka salihai da shi.


اَللَّهُمَّ إِنَّكَ خَلَقْتَ نَفْسِي وَأَنْتَ تَوَفَّاهَا لَكَ مَمَاتُهَا وَمَحْيَاهَا، إِنْ أَحْيَيْتَهَا فَاحْفَظْهَا، وَإِنْ أَمَتَّهَا فَاغْفِرْ لَهَا. اَللَّهُمَّ إِنَّي أَسْأَلُكَ الْعَافِيَةَ.
Allahumma innaka khalaqta nafsee wa-anta tawaffaha, laka mamatuha wamahyaha in ahyaytaha fahfazha, wa-in amattaha faghfir laha. Allahumma innee as-alukal-'afiyah.

Ya Allah! Kai ne Ka halicci raina, kuma Kai ne Kake karbarsa. Gare ka kadai mutuwarsa da rayuwarsa suke. In ka rayar da shi, to ka kiyaye shi; in Ka dauke shi, to Ka gafarta masa. Ya Allah! Ina rokonka aminci daga dukkan mummuna.

Annabi, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya kasance idan ya zo kwanciya sai ya sa hannunsa na dama karkashin kuncinsa. Sannan ya ce;
اَللَّهُمَّ قِنِي عَذَابَكَ يَوْمَ تَبْعَثُ عِبَادَكَ. (ثلاثَ مراتٍ)
Allahumma qinee 'azabaka yawma tab'athu 'ibadak. (3).

Ya Allah! Ka kiyashe ni azabarka a ranar da Kake tayar da bayinKa (bayan mutuwa). (su uku).


بِاسْمِكَ اللَّهُمَّ أَمُوتُ وَأَحْيَا.
Bismika l-lahumma amutu wa ahya.
Da sunanka Ya Allah nake mutuwa kuma nake rayuwa.

سُبْحَانَ اللهِ، ثَلاَثًا وَثَلاَثِينَ
وَالْحَمْدُ ِللهِ، ثَلاَثًا وَثَلاَثِينَ
وَاللهُ أَكْبَرْ. ثَلاَثًا وَثَلاَثِينَ.
Subhana l-lah (33),
Al-hamdu li-l-lah (33),
Allahu akbar (33).

Tsarki ya tabbata ga Allah (Sau 33)
Yabo ya tabbata ga Allah (Sau 33)
Allah ne mafi girma (Sau 33).


اَللَّهُمَّ رَبَّ السَّمَوَاتِ السَّبْعِ وَرَبَّ العَرْشِ الْعَظِيمِ، رَبَّنَا وَرَبَّ كُلِّ شَيْءٍ، فَالِقَ الْحَبِّ وَالنَّوَى، وَمُنَزِّلَ التَّوْرَاةِ وَاْلإِنْجِيلِ،وَالْفُرْقَانَ، أَعُوذُ بِكَ مِنْ شَرِّ كُلِّ شَيْءٍ أَنْتَ آخِذٌ بِنَاصِيَتِهِ. اَللَّهُمَّ أَنْتَ اْلأَوَّلُ فَلَيْسَ قَبْلَكَ شَيْءٌ،وَأَنْتَ اْلآخِرُ فَلَيْسَ بَعْدَكَ شَيْءٌ، وَأَنْتَ الظَّاهِرُ فَلَيْسَ فَوْقَكَ شَيْءٌ،وَأَنْتَ الْبَاطِنُ فَلَيْسَ دُونَكَ شَيْءٌ،اِقْضِ عَنَّا الدَّيْنَ وَأَغْنِنَا مِنَ الْفَقْرِ.
Allahumma rabbas-samawatis-sab'a, warabbal-'arshil-'azeem, rabbana warabba kulli shay', faliqal-habbi wannawa, wamunazzilat-tawra, wal-injeel, walfurqan, a'oothu bika min sharri kulli shayin anta akhithun binasiyatih. Allahumma antal-awwal, falaysa kablaka shay', wa-antal-akhir, falaysa ba'daka shay/, wa-antaz-zahir falaysa fawqaka shay', waantal-batin, falaysa doonaka shay', ikdi 'annad-dayna wa-aghnina minal-faqr.

Ya Allah! Ya Ubangijin sammai bakwai, Ubangijin Al'arshi mai girma, Ubangijinmu kuma Ubangijin komai, mai tsaga kwayar tsiri da kwallon dabino, mai suakar da Attauna da Injila, da Alfurkani! Ina neman tsarinka daga sharrin komai wanda kai ne mai rike da makwarkwadarsa. Ya Allah! Kai ne na farko, babu wani abu kafinka, kai ne na karshe, babu wani abu bayanka, kai ne bayyananne, babu wani abu da yake sama da kai, kai ne boyayye, babu wani abu da yake boyewa gare ka. Ka biya mana basussuka, kuma ka wadatar da mu daga talauci.


اَلْحَمْدُ ِللهِ الَّذِي أَطْعَمَنَا وَسَقَانَا، وَكَفَانَا، وَآوَانَا، فَكَمْ مِمَّنْ لاَ كَافِيَ لَهُ وَلاَ مُؤْوِي .
Alhamdu lillahil-lathee at'amana wasaqana, wakafana, wa-awana, fakam mimman la kafiya lahu wala mu'wee.

Yabo ya tabbata ga Allah, wanda ya ciyar da mu, ya shayar da mu, ya isar mana, ya ba mu makwanci. Da yawa wanda ba shi da ma'ishi, wala mai ba shi makwanci.


اَللَّهُمَّ عَالِمَ الْغَيْبِ وَالشَّهَادَةِ فَاطِرَ السَّمَاوَاتِ وَاْلأَرْضِ رَبَّ كُلِّ شَيْءٍ وَمَلِيكَهُ، أَشْهَدُ أَنْ لاَ إِلَهَ إِلاَّ أَنْتَ، أَعُوذُ بِكَ مِنْ شَرِّ نَفْسِي، وَمِنْ شَرِّ الشَّيْطَانِ وَشِرْكِهِ، وَأَنْ أَقْتَرِفَ عَلَى نَفْسِي سُوءاً أَوْ أَجُرَّهُ إِلَى مُسْلِم.
Allahumma 'alimal-ghaybi washshahadah, fatiras-samawati wal-ard, rabba kulli shayin wamaleekah, ashhadu an la ilaha illa ant, a'oozu bika min sharri nafsee wamin sharrish-shaytani washirkih, wa-an aktarifa 'ala nafsee soo-an aw ajurrahu ila muslim.

Ya Allah! Masanin abin da ke fake da na sarari! Mai kagen halittar sammai da kassai! Ubangijin komai, kuma mamallakinsa! Ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai kai. Ina neman tsarinka daga sharrin raina, da kuma sharrin shaidan da shirkarsa, da in tsuwurwurtawa kaina wani abu mummuna, ko in jawo shi ga wani Musulumi.

Ya karanta suratu As-sajdah (Alim lam mim, tanzilul) da suratul mulk (tabaraka).


اَللَّهُمَّ أَسْلَمْتُ نَفْسِي إِلَيْكَ، وَفَوَّضْتُ أَمْرِي إِلَيْكَ، وَوَجَّهْتُ وَجْهِي إِلَيْكَ، وَأَلْجَاْتُ ظَهْرِي إِلَيْكَ، رَغْبَةً وَرَهْبَةً إِلَيْكَ، لاَ مَلْجَأَ وَلاَ مَنْجَا مِنْكَ إِلاَّ إِلَيْكَ، آمَنْتُ بِكِتَابِكَ الَّذِي أَنْزَلْتَ وَبِنَبِيِّكَ الَّذِي أَرْسَلْتَ.
Allahumma aslamtu nafsee ilayk, wafawwadtu amree ilayk, wawajjahtu wajhee ilayk, wa-alja'tu zahree ilayk, raghbatan warahbatan ilayk, la maljaa wala manja minka illa ilayk, amantu bikitabikal-lathee anzalt, wabinabiyyikal-lathee arsalt.

Ya Allah! Na sallama raina gare ka, na maid a al'amarina gare ka. Na fuskantar da nufina gare ka, na dogara da kai (a cikin dukkan al'amurana) saboda kwadayin abin da keg are ka, da tsoron ka. Babu mafaka, babu matsira daga gare ka sai zuwa gare ka. Na yi imani da littafinka da ka saukar da kuma Annabinka da ka aiko.


DEDICATED TO.....MY SISTERS😘


Bissimillah Rahmanir Rahim


Page-69-70


---------------Maida hankalin shi yayi baki ɗaya wajen Anuwar daya kasa magana sai yayi kamar zaiyi sai yayi shiru.

Dad ya kama hannun shi duka biyun yace;"kada kaji tsoro ko shakku"


Murmushi Anuwar yayi yace;"Ina son na koma Nigeria idan su Abie suka zo, ina bukatar zaman Nigeria a yanzu, please Dad kada kace a'a"


Miƙewa tsaye Daddy yayi baice komi ba yabar ɗakin, saboda banyi tunanin haka daga Anuwar.


Anuwar yabi shi da kallo har ya fice.
Ganin yanayin Dad yasa Mommy saurin matsawa tace;"lafiya ko jikin ne nashi da saura"

Girgiza kai Dad yayi yace;"Aljanar nan ta cucemu saboda ita ya kusa rasa ranshi amman har yanzu itace a ranshi, wannan wane irin sone?? Wannan ba so bane dan idan so ne ai yaso MANAL kafin ita, to son yayi yawa lallai wannan yarinyar mayya ce"


Mummy tace;"Yanzu ace har Videon dana bashi ya kallah bai mashi ba, tunda Anuwar ya hadu da ita natsuwar shi ta kauce, gobe idan su Mai Martaba sun iso ya kamata kuyi wani abu"


Anuwar dake tsaye basu ji zuwan shiba yace;"Mummy kema kina goyan bayan Dad Mummy yarinyar nan na bukatar taimako, saboda daman mutanen garin su sun tsane ta, yarinyar bata san soyayyar kowa ba saita mahaifin ta kuma wannan ba ita ta haifeta ba"


Dad yace;"Kinga abinda nake fada maki, duk idan kika ga bakauye yaƙi abu to akwai dalili babba, lallai mayya ce in ko ba hakaba tana da wani mugun hali marar kyau idan ba haka ba babu yadda za'ayi su gujeta, ita abun guduce ga kowa hadda kai ba Alkhairi bace a rayuwar ka"


Anuwar yace;"Dad da ciki na a jikin tafa, taya za'ayi nabar jinina a wulakance, wallahi Dad zan bada rayuwata fansa a jinina bazan iya jurewa ba kodan ajiyar danayi mata"


Zaro idoo Dad yayi lokaci guda kwallah suka taru a idon shi.

Innalillahi yake ambata duk ya rude Jin maganar Ciki itama Mummy mutuwar tsaye tayi haka Kulsoom.

Cikin sauri yayi maza yabar wajen yayi sama da sauri.

Mummy tabi bayan shi, itama cikin sauri.


Kulsoom dake tsaye tana hawaye ta matsa kusa dashi.


Kallon ta yayi ya kauda fuska.

Cikin sauri ta rungume shi tana ajiyar zuciya.

Sun dade a haka kana ta sake shi.

Kallon shi tayi kwata-kwata hankalin shi bai wajen ta, kama hannun shi tayi suka ida sabkowa a parloun.

Zaunar dashi tayi tace;"kana bukatar abinci tunda kazo bakaci komi ba kasan akwai matsala"

Kallon ta yayi tare da daukar Apple din gaban su da Mummy ta aje.

Mikewa tayi jim kaɗan sai gata da abincin.

Ta aje ta duƙa ta zuba ta Miƙa mashi.

Ture plat din yayi yace;"I am okay with the apple for now, I will eat later"

Mikewa yayi ya nufi hanyar bedroom dinshi.

Yana zuwa ya zauna gefen bed ya rike kanshi dake sarawa.


Turo kofar akayi Kulsoom ce da kayan bacci a jikinta riƙe da Cup a hannu.


Zuwa tayi ta zauna kusa dashi hannun shi ta kama ta daga rigarta ta aza bisa cikin ta.

Saurin kallon ta yayi murmushi tayi tace;"Baby yace yayi missing din Dad dinshi, yace yayi fushi"

Ta ida maganar kamar zatayi kuka.


Murmushi yayi tare da matsowa kusa da ita suna jin numfashin juna.

Duƙar da kai yayi daidai cikin ta tare da manna kiss wajen cibiyarta.


Cup din hannunta ta mika mashi Jin maganar Baby yasa ya manta da fushin Dad ya amsa yasha madarar Cup din.


Saidai ya mika mata cup, aje Cup din tayi ta hau gadon da yake ta kwanta.

Wayar shi ya dauka yayi ma Sanii Message pictures dinshi na Camera yake so, su Abie su tafo dasu.

Koda safiya ta waye tun kamin Kulsoom ta mike Anuwar har ya fita a lambu.

Tana fitowa taga ma aikatan gidan nata shirye-shirye.

Suka gaisa da Mummy da Daddy.


Wajen karfe goma na sai gasu Abie da sauran yan gida.

Nan aka murnar tashin Anuwar, amman shi yaki sakin jiki sai murmushin dole yake, saboda Koda ya gaida Dad bai ansaba.


Abie ya lura Dad ko irin kulawar nan baya ba Anuwar ba kamar daba, idan ana tare yana yawan fadin kaci abinci baicin abinci Sai Anuwar yaci Amman yau shiru ko magana baiyi ba duk da yasan Anuwar yayi mashi laifi dan abinda yai zai iya taba siyar shi.

Bayan sun kebe da Dad da Abie da Ammie da Mummy.

Nan Dad ya bayyana abinda ya faru amman ya boye masu maganar ciki saboda basusan Anuwar yayi ma wata fadeba.


Su duka sallallami sukeyi suna mamakin wannan wace irin Jarabta ce haka??

Dad yace;"Dole yanzu mu koma yi masa addu'a saboda itace mafita"

Nan de suka ja janta ma juna.

A ban garen Kulsoom kawarta Hanan ta kira ta fadi mata abinda ke faruwa.

Hanan tace;"duk wahalar da mukasha da kudin da muka saki hadda yan garifa muka ba, amman duk a banza lallai maganar Dad gaskiya ce aljana ce matar nan in ban haka taya za'ayi ace Anuwar da ya fito Babban gida kuma Baban shi shugaba sannan yace yanason shege, kaunar da yake ma shegen ko ke da keda cikin sunnah Wanda aka samu a aure bai nunama waba kinsan akwai wata a kasa Sai kin dage"

Kulsoom tace;"toni mizan yi cikin nannefa naga yakeson ya amsoman soyayya ki taimaka man"


Hanan tace;"zan taimaka maki, amman akwai matsala saboda Malamin Mom ne zan kaiki wajen shi, nima sirri ne tsakani na da Mom bansan tanada Malami saida inson Ammar kana, Amma fa aikin shi kamar yankan wuka yake"


Kulsoom tace;"nide inde zai fidda hatsabibiyar yarinyar nan a zuciyar Prince banda matsala inaso tabar man mijina haka inaso nayi rayuwar aure kamar yadda kowace mace kiyi, wallahi inde akwaita a rayuwar Anuwar toni ba komi bace face yar zaman gida"

Hanan tace;"to Malamin a maiduguri yake, kinga akwai kudin jirgi sannan zan kawo maki abinda ya bada, kinga zanzo Spain kenan"


Kulsoom tace;"wallahi zan baki ko nawa ne Dad dinshi na yawan yiman kyau banda matsalar kudi nide a fidda ta a zuciyar shi"


Maganar da sukayi da Hanan yasa hankali Kulsoom kwanta.


Su Abie sai kara bata hakuri suke akan halin ko in kula da yake mata tana cewa ai babu komi.


Nan suka kwana biyu suka koma.

Yau Friday Anuwar ya kasa zama tunani yake taya zaibar kasar dan bazai iya wata guda a cikin ta ballai shekaru a ciki.

Wai ya gama zuwa Nigeria saide ko wace kasa yakeson zuwa zaije banda Nigeria lallai wannan hukunci bazai iya jurewa ba.


Kiran wani ma aikaci yayi ya bashi Camera dinshi aka tafi da ita.

Jim kadan aka dawo da wani katon photo.

Anuwar ne da twins ranar da zaije Katsina.

Kallon photon yake yana murmushi.


Dad ya yafito shima murmushi yayi yace;"Wai daman kanada photon nan, Kai amman yarona kayi kyau sosai, Nima inaso na saka a room dina na Nigeria har Mai martaba sai nasa anmawa shima babba kamar naka mukeso saboda kayi kyau da yaran"

Murmushi Anuwar yayi yaba ma'aikacin da ya aika da yayo ma su Daddy shi kanshi yasan baitaba photon da yayi kyau wannan ban


Kallon yaran yake yana murmushi da kaga photun kasan yana cikin farin ciki.


Daddy yace;"Allah ya nuna mana naka"

Yace;"Ameen"


Kulsoom da Mummy ma sai santin yaran suke dake cikin kaya masu kyau photon yayi farin jini Mummy da Kulsoom ma naso Kulsoom tayi haka dan samun shiga.


Suna zaune da yamma saiga Hanan ta iso.

Nan Mummy ke fada miyasa Bata sanar dasuba da ammata shiri.


Hanan tace bakomi suka wuce part din Kulsoom.

Nan suka zauna Kulsoom ta kara fadama Hanan halin da ake ciki ba.

Hanan tace;"yanzu ba Abie ya hana shi zuwa Nigeria ba, wannan dama ce sosai"

Ta mika mata wani abu a cikin abu a leda tace wannan a abinci ko a ruwa, ta mika mata wani turare mai kamshi normal turare ne baka cewa akwai magani.


Tace;"duk yaci wannan insha Allah saikin karaman kudi, wannan turaren kuma idan yaji kamshin shi zaiji koda yaushe baison zama da kowa saike, zakiyi mamaki"

Cikin jin dadi Kulsoom tace;"wallahi banda abinda zance sai godiya"

Hanan tace;"kada kidamu yaushe su Daddy zasu koma?"


Kulsoom tace;"cikin week din Nan"


Murmushi Hanan tayi tace;"a sha love lafiya, amman fa wani hanzari ba gudu kinsan shi irin wannan aikin yana karewa saide lokaci zuwa lokaci zamun dunga wai-wayen Malam"

Kulsoom tace;"kada kidamu kinsan kudi ba matsala ta bane zan yi komi banson matsala a rrayuwata nayi iya hakuri na"


Murmushi Hanan tayi ranar atare suka yini.


Hanan ta kalli katon photon Anuwar tare da yara biyu a hannu tace;"Wow My Friend ina Prince yasmu yara kamar nashi sun mashi kyau sosai"

Kulsoom ta tabe baki tace;"kinsan shi da shegen sun yara, Amman wadannan na daban ne wai har Maman su yaba jini ko a MANAL hospital suka hadu ohow ni kishin son yaran yasa van tsaya Jin labari"

Hanan tayi murmushi tace;"maganar kishi ta kare kinyi kishin Mai fura kin dawo kina na yara mubar maganar"



Kwanan Hanan biyu tabar gidan Suma yau su Dad zasu koma, har airport sukayi masu rakiya suka dawo.


Kulsoom ta hada ma Anuwar maganin Hanan a cikin abinci ta saka turaren ta doso parlaour inda yake zaune yana waya dasu Abie yana jin kamshin turaren cikin sauri ya dago Kai.


♦♦♦♦♦♦♦♦

Haka muka cigabada rayuwa nida Inna kullun cikin tunanin lafiyar Yarima nake.


Inna na kokari wajen yaran sosai shiyasa nima kullun cikn son kyautata mata nake.


Data tambaye ni iyayena Nan nayi kukan karya nace iyayena sun rasu wajen matar uba nake Kuma ta koreni ban boye mata cewa yarana basuda uba ba na fada mata fade akayima shine matar uba ta korene Kuma bansan. Dangina ba.



Jin labari na yasa take tausayina.

Koda Sani ya iske yake cewa kamar yasanni.

Kamar ya taba daukar wata yarinya ya kaita asibiti har aka saka mata jinin Yarima Amman so guda ya taba ganin ta lokacin bikin yarima ya daukota antaketa.

Nan nabashi labarin hadda taimakon da Dr Mubarak yayiman yayi mamaki sosai dayaji niba yar uwar Dr ce da kuma zaluntar da Hajiya tayiman yace zaisa a daure naita bashi hakuri saboda banson tone tone.


Ina tayata Inna aikin fura dama nace mata ni bakauya ce ganin yadda nayi daka da Fura ta yadda dani sosai, Na kware wajen sarrafa fura lallai ta yadda daga kauye na fito.

Sunan da Yarima ya saka masu dashi nake kiran su saboda hakan nasani farin ciki idan na tuna sunan daga wajen shi

Please Login or Register in order to submit comment