Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

My dear I missing you so much please come back tomorrow I need your help, please, please"tayi maganar kamar zatayi kuka.

Dariya Hanan tayi tace;"Umm why don't picking my call??lokacin kuna shan love ko,amman ta da Friends"tsaki Kursim tayi tace;"love ko wahala,bai da lokacin kallo na,sai ma wasu ban zayen masu fura daya ke kallo suna gaban inda muke zaune,harda ma furar yasha,kenan baida time dina saina yan fura"


Dariya Hanan tayi tace;"amman kishin ki yayi yawa harda yan fura kike kishi?? please ki daina irin wannan kishin ai abun kunya ne,haba kada wani yaji mana,yanzu ina Abuja tare da su Mom, maybe next week mudawo zanyi tunani akan Prince,amman wallahi ban taɓa jin mutum mai taurin kanshi ba,kamar dai dutse,zanyi tunani kafin na dawo,insha Allah zamu samu mafita idan yaki ta lalama, wallahi nasan abinda duk kika yi mashi shi saiya aure ki,amman akwai hatsari,sai dai idan nadawo idan bai chanza ba zamu bi ta bayan gida,kada kidamu matar Prince Anuwar"dariya Kursim tayi,sukayi sallama magan ganun Hanan sunyi tasiri a zuciyar ta.


Fita tayi ta nufi part din Umman ta.


*************

A dakina har dare yayi naji karar shigowar Baba,na mike na nufi waje.

Sannu da zuwa Baba,andawo lafiya??

Murmushi yayi yace;"yawwa ina Innar taki,baki shiga dakin ta kuyi fira,zaman kaɗaici baida dadi kinji"daga Kai nayi.

Ledar hannun sa na amsa dai-dai lokacin da Inna tafito,"sallati ta rabka kamar wacce aka yima wani abu,yanzu ita ledar Malam ke kika koma karba kenan na zama kishiyar ki,kema uwar ki zaki taya kishi duk da bata duniyar?"tsawa Baba yayi sannan ya daka mata tsawa yace;"meyasa ke baki da hankali baki san kalar maganar da za kiyima diyar kiba, kullun yarinya cikin wahala,kuma duk da haka ba zaki barta ta huta ba,ki shiga taitayin ki"


Harara ta dallah man ta koma daki.

Ya mikoman wata leda yace"kinga wannan takice wannan kuma ki rike zanyi tafiya kwana biyu zanyi,zanje wajen dan uwana Dan-musa an aiko bashi da lafiya kuma kinsan daga nan zuwa Dan-musa akwai dan nisa shiyasa zanyi kwana biyu,wannan magani ne shi kuma ki jika a ruwa kisha,su kuma kudin kisayi wani abu kici idan bata baki abinci ba"godiya nayi ma Baba sosai, duk da a raina banji dadi ba,dan nasan wahala zata karu,kai yau littinin amman abubuwa sai chakude wa suke,ga auren Shatu na fara lissafa kwana ki,ga Baba zaiyi tafiya.

Daki na koma na hada kudina waje daya na kwanta ina tunanin abinda zai faru bayan tafiyar Baba,dan nasan kwana biyun nan zan fuskan ci matsala.

Lumshe ido nayi nace bari nayi bacci da wuri yanda zan tashi da wurii.


**************
Bayan Kursim ta fito part din Maman ta,part din Anuwar ta nufa kai tsaye ta shiga.

Anyi sa'a yana falo kuma shi kadai ne, Video call yake da Dad ɗin shi,harda Nifra sunyi magana duk tana nan zaune,ta danji dadi yadda yayi wayar,Nifra ke fadin sunyi Missing dinshi, Murmushi kawai yayi,haka suka gama wayar ya kashe,bai kalle taba kuma yaga shigowar ta.

Mikewa yayi har ya juya tace;"Prince baka ganni ba,kuma kasan wajen ka nazo"cikin shagwaba tayi maganar.

Ma ballan rigar ta ta cire, yadda zaiga kwalliyar ta.

Juyowa yayi ya dawo ya zauna, motsa baki yayi zaiyi magana,cikin doki da jindadi ta maida hankalin wajen shi"Allah na godema yau zai kulani muyi fira kenan"ta fada a zuciyar ta.

Cikin cool voice dinshi yace;"Gobe da wuri ki maidani nasha furar nan"cikin mamaki take kallon shi!!

Murmushi tayi ganin yana kallon ta tayi saurin boye mamakin ta tace"Wow naji dadi da nuna kana son furar nan,amman gaskiya bazan barka ka dunga shan irin wannan furar ba, akwai fura mai kyau da ake saidawa a manyan wurare a Katsina kuma gidan nan ko naman dawisu kake so akwai ballan tana fura,zan sa a dinga kawoma daga sashen Mai martaba"juyar da kai yayi.

Yace;" na fada maki bana shan fura wannan kaɗai nike son sha"yayi maganar cikin dagawar murya,duk da ya daga murya Amman ita kaɗai kejin shi.


Cikin sauri tace;"ohh sorry Prince Allah ya kaimu goben"tashi tayi tace"dare yayi bari na kwanta"cikin sauri tabar wajen,zuciyar ta na mata zafi.

A part din tana zuwa ta kori kowa tace a subar ta ita daya.

Tsakiyar gado taje ta hau tayi ihunta.


A rasa abinda zai zame mata matsala sai masu fura,yaran kauye,kodai furar tsafi ce??

MANAL kadai ya damu da ita a duniya,duk wahalar da take mashi bai gani,saima takaishi wajen masu fura gobe da safe.

Anya ba akwai tsafi ba??
Kodai Aljanu ne??
Shiyasa su duka suke da da kyau harma dai mai furar,yaga wannan ya rude ina ga mai furar??
Kai bazan bari su hadu da mai furar nan ba,dan kila mayune,ya zanyi kenan??

Ga Prince da taurin kai, idan yana son Abu bai chan zawa.

Ya zanyi kenan gobe da Prince??


Qurrah
[1/28, 3:02 PM] GOLDEN PEN WRITERS ASSOCI: *JARABTAR MU*



*Writing by Qurrah*

*~Page 15-16~*


https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/



*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*




*~We are bearer's of so golden pen🖊~*

*~we write assidiously perceive no pain~.*

*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*

*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*

Falalar Tasbihi, Da Godiya Ga Allah, Da Yin La ilaha Illal Lah, da yin Kabbara

Abu Huraira, Allah ya yarda da shi, ya ruwaito cewa; Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya ce; wanda ya ce;
سُبْحَانَ اللهِ الْعَظِيمِ وَبِحَمْدِهِ.
Subhanal-lahil azeem wabihamdih.
(sau dari)
... A rana, za a kankare masa zunubansa ko da sun kasance kamar kumfar teku ne (wajen yawa).

Abu Ayyub Al-Ansari, Allah ya yarda da shi, ya ruwaito daga Manzon Allah, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, cewa ya ce: "Wanda Ya ce;
لاَ إِلهَ إِلاَّ اللهُ وَحْدَهُ لاَ شَرِيكَ لَهُ، لَهُ الْمُلْكُ وَلَهُ الْحَمْدُ، وَهُوَ عَلَى كُلِّ شَيْءٍ قَدِيرٌ. (عشر مرة).
La ilaha illal-lahu wahdahu la shareeka lah, lahul-mulku walahul-hamd, wahuwa 'ala kulli shayin

Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, shi kadai; babu abokin tarayya a gareShi. Mulki ya tabbata gare Shi kuma Shi mai ikone a kan komai.
(sau goma).
To kamar wanda ya 'yanta bayi hudu ne daga cikin 'ya'yan (Annabi) Isma'ila.


Abu Huraira, Allah ya yarda da shi, ya ce; Manzon Allah, tsira da amincin Allah su tabbata a gare Shi, ya ce; "Akwai wasu kalmomi biyu masu saukin fada a harshe, masu nauyi a kan mizani (na ayyuka ranar kiyama), masu soyuwa ga (Allah) mai yawan jin kai (su ne).
سُبْحَانَ اللهِ وَبِحَمْدِهِ سُبْحَانَ اللهِ العَظِيمِ.
Subhanal-lahi wabihamdih, wasubhanal-lahil-'azeem.
Tsarki ya tabbata ga Allah, tare da Shi; tsarki ya tabbata ga Allah Mai girma.


Abu Huraira, Allah ya yarda da shi, ya ce; "Manzon Allah, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya ce; Fadin:
سُبْحَانَ اللهِ، والْحَمْدُ للهِ، لَا إِلَهَ إلاَّ اللهُ واللهُ أَكْبَرُ.
Subhanal-lah, walhamdu lillah, la ilaha illal-lah wallahu akbar.

Tsarki ya tabbata ga Allah, kuma yabo ya tabbata ga Allah, kuma babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, kuma Allah ne Mafi girma.
… Shi ya fi soyuwa gare ni daga dukkan abin da rana ta hudo a kansa".


Daga Sa'ad bn Abi Wakkas, Allah ya yarda das hi, yace; mun kasance a wajen Manzon Allah, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, sai ya ce; "Yanzu dayanku yana kasa aikata kyawawan ayyuka dubu a kowace rana? Sai wani mutum cikin wadanda suke zaune tare da shi ya ce; "Ta yaya dayanmu zai aikata kyawawan ayyuka duub? Sai ya ce; "Ya yi tasbihi (ya ce;
سُبْحَانَ اللهِ.
Subhanal-lah.(3)

(Tsarki ya tabbata ga Allah)
... Sau dari, saia rubuta masa kyawawan ayyuka dubu, ko a kankare masa zunubai dubu.

Jabir, Allah ya yarda da shi, ya ce; Annabi, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya ce; "Wanda ya ce;
سُبْحَانَ اللهِ العَظِيمِ وبِحَمْدِهِ.
Subhanal-lahil-'azeemi wabihamdih.

Tsarki ya tabbata ga Allah Mai girma, tare da godiya gare Shi.
... Za a dasa masa bishiyar dabino a cikin aljanna.


Daga Abu Musa al-'ash'ari, Allah ya yarda da shi, ya ce; Manzon Allah, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya ce mini: "Ya Abdullah bn Kais! Ba na shiryar da kai ba zuwa ga wata taska daga cikin taskokin aljanna ba? Sai na ce. Shiryar da ni. Sai ya ce: ka ce:
لاَ حَوٍلَ وَلاَ قُوَّةَ إِلاَّ بِاللهِ.
La hawla wala kuwwata illa billah.

Babu dabara babu karfi sai da Allah.


Daga Samura bn Jundub, Allah ya yarda da shi, ya ce Manzon Allah, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya ce; "Mafi soyuwar zance a wajen Allah shi ne;
سُبْحَانَ اللهِ، والْحَمْدُ للهِ، ولاَ إِلَهَ إِلاَّ اللهُ واللهُ أَكْبَرُ.
Subhanal-lah, walhamdu lillah, wala ilaha illal-lah, wallahu akbar.

Tsarki ya tabbata ga Allah, kuma yabo ya tabbata ga Allah, kuma babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, kuma Allah ne mafi girma.
... Babu komai a gare ka ko da wane daya daga cikinsu ka fara'.



Sa'ad bn Abi Wakkas, Allah ya yarda da shi, ya ce; "Wani balaraben kauye ya zo wajen Manzon Allah, tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi, sai ya ce; koya mini wadansu kalmomi da zan rika fada. Sai ya ce; ka ce;
لاَ إِلَهَ إِلاَّ اللهُ وَحْدَهُ لاَ شَرِيكَ لَهُ، اللهُ أَكْبَرُ كَبِيراَ والْحَمْدُ للهِ كَثِيراً، سُبْحَانَ اللهِ رَبِّ العَالَمِينَ، لاَ حَوْلَ وَلاَ قُوَّةَ إِلاَّ بِاللهِ العَزِيزِ الْحَكِيمِ.
La ilaha illal-lah, wahdahu la shareeka lah, Allahu akbaru kabeera, walhamdu lillahi katheera, subhanal-lahi rabbil-'alameen, la hawla wala kuwwata illa billahil-'azeezil-hakeem.

Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah; babu abokin tarayya a gare Shi. Allah ne mafi girma (Ina girmama Shi) girmamawa. Kuma godiya ta tabbata ga Allah da yawa. Tsarki ya tabbata ga Allah, Ubangijin talikai. Babu dabara babu karfi sai da Allah, Mabuwayi mai hikima.
... Sai mutumin ya ce; "Wadannan na Ubangijina ne, ni kuma nawa fa/ sai yace ka ce;
اللَّهُمَّ اغْفِرْ لِي، وارْحَمْنِي، واهْدِنِي، وارْزُقْنِي.
Allahummagh-fir lee, warhamnee, wahdinee, warzuknee.

Ya Allah! Ka yi mini gafara, K aji kai na, Ka shirye ni, Ka azurta ni.

Tarik Ibn Ashyam al-Ashja'i, Allah ya yarda das hi, y ace; "Idan mutum ya musulunta, sai Annabi, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya koya masa sallah, sannan ya umarce shi ya rika addu'a da wadannan kalmomin.
اللَّهُمَّ اغْفِرْ لِي، وارْحَمْنِي، واهْدِنِي، وارْزُقْنِي.
Allahummagh-fir lee, warhamnee, wahdinee, warzuqnee.

Ya Allah! Ka yi mini gafara, Ka ji kai na, Ka shirye ni, Ka amintar da ni daga bala'i, Ka azurta ni.

Jabir Ibn Abdullah, Allah ya yarda da shi, ya ce Manzon Allah, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya ce; "Mafificiyar addu'a ita ce (fadin):
الْحَمْدُ للهِ.
Alhamdu lillah

Dukkan yabo ya tabbata ga Allah.
…. Kuma mafificin zikiri shi ne (fadin):
لاَ إِلَه إِلاَّ اللهُ.
La ilaha illal-lah.

Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah.


Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya ce; "Ayyuka nagargaru masu wanzuwa su ne (fadin):
سُبْحَانَ اللهِ، والْحَمْدُ للهِ، لاَ إِلَهَ إَلاَّ اللهُ واللهُ أَكْبَرُ وَلاَ حَوْلَ وَلاَ قُوَّةَ إلاَّ باللهِ.
Subhanal-lah, walhamdu lillah, la ilaha illal-lah, wallahu akbar, wala hawla wala kuwwata illa billah.


Tsarki ya tabbata ga Allah, kuma yabo ya tabbata ga Allah, kuma babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, kuma Allah ne Mafi firma, kuma babu dabara babu karfi sai da Allah.

DEDICATED TO.....MY SISTERS😘


Page-15-16


_Bissimillah Rahmanir_ _Rahim_


---------------Bata damu da mutanen dake kallon su ba,saboda an santa gashi kuma anfi ma sanin Prince fiye da ita.

Har kusan faduwa tayi wajen sauri.

Ta iskeshi tsaye,wani mai mashin zai tsaya.

Cikin sauri tayi ma mai mashin nuni da yawuce.


Kama hannun shi tayi yayi saurin juyowa.

Girgiza kai tayi tare da jan hannun shi.

Cire hannun shi yayi daga nata yace; "bana son motar gidan ku,tunda banda iko da ita zanje na sayi wata motar ,tafi ki bani waje bana son ganinki"kayi hakuri mubar nan.

Harara ya dallah mata.

Murmushi tayi tace "kasan ansan fuskar ka yanzu da an ganka bisa mashin yau gidan mu saiya cika da manema labarai,kuma za'ayi ta yaɗawa a social media ina tsoron kada hakan ya ɓata ma siyasar Dady suna kasan dai abu kaɗan ke bata sunan yan siyasa,kayi hakuri na maka laifi amman bazan kara ba" ta ida maganar tare kwalla cike da idanun ta.

Bai mata magana ba ya juya ya nufi motar.

Cikin sauri tabi bayan shi,ta bude mashi mota ya shiga ya zauna,ta koma itama ta tada mota.


Tafiya suke zuciyar Kursim cike da zafi,haka dama ake So??

Kwallar dake makale ta fara zubo mata,tayi saurin gogewa,ko kallon ta Prince bai yi ba , rashin kallon ta idan tana Abu yana chi mata zuciya.

Suna isa tayi parking din motar,yanzu tana ciki motar takai hannun ta zata bude mashi motar ta ciki,saida ta ɗan hau jikin shi kana hannun ta yakai duk yana zaune.

Kara matsowa tayi jikin shi ta tura kofar.

Tanayin baya ta fada a kirjin shi,lamo tayi zuciyar ta na bugawa da sauri da sauri.

Jin baice mata komai ba yasa,ta saka hannayenta biyu ta rungume shi,tana sakin a jiyar zuciya.


Cikin bacin rai da zafin nama Prince yasa hannu biyu ya fitar da ita daga jikin shi,kamar ba mutum ba haka ya jefar da ita bisa kujerar ta

Kuf...!!!

Kake ji kamar an buga wani abu,kan Kursim ne da Prince ya buga a mota.

Cikin bacin rai yace "ashe ke dama baki da tarbiya??a haka za'a daura mani aure da ke??na tsani macen dake kawo jikin ta a gare ni,bazan iya daukar hakan ba,ina bukatar mace mai tarbiya"

Kuka ta saki mai sauti!!

Toshe kunnen shi yayi yana runtse ido,yana girgiza kai.

Cikin tsawa yake cewa; "ki daina min kuka bana son kukan ki daina!! Ki daina! Ki daina please

Idanunshi a runtse suke,kamar wani mai Aljanu.

Mamaki yasa Kursim yin shiru anya ba akwai Aljanu a jikin shi ba??ita fa akayi ma laifi,tayi zaton zai bata hakuri,maimakon haka sai tsawa.

Duƙar da kanta tayi tana kuka marar sauti.

Shiru motar babu magana saima kuka da take yi marar sauti.

Prince ko a zuciyar babu abinda yake sai nadamar zuwa katsina,ya tsani kukan mace tun daga kukan MANAL da take tana cewa yazo ya tafi da ita,shiyasa a duniya babu abinda ya tsana kamar mace tayi kuka.


Fita yayi daga motar, wajen da suka zauna jiya ya nufa ya zauna.

Sai kuma ya mike yaje wajen katangar Company,ya fuskan ci wajen furar su Nana,hannu a cikin aljihu.


Kursim ta goge jinin dake bin fuskarta,ta fito daga motar ita ma tsaye tayi tarasa abin da zata yi.


*************
Tafiya suke a kafa,har suka iso bakin titi,Shatu tace "sannu da kokari gaskiya kinyi kokari daukar kayan nan"

Murmushi nayi nace"toya zanyi?ai mun kusa isa ko,dan wallahi kamar na fadi"

Shatu tace"mun kusa mana ga wajen chan"muna isa shatu ta sauke kwaryar ta,kana ta kama mani na saike tawa.

Nace "Wash" ido nabi wajen da kallo,chan na hangi wani mutum tsaye bayan mu,amman nisa yasa bani ganin fuskar shi.


Iska ta kaɗa naji wani kamshi ya bugi hancina, lumshe ido nayi,ina jin wani iri a kaina,kamar yana man ciwo,dafe kaina nayi ina addu'a.

Shatu tace"yawwa ga mata da mijin nan chan yauma sun zo, nasan zasu saya kafin ƴan makarantar su fara zuwa "daga kai nayi,ji nayi kaina na juyawa.


**************

Inda yake ta iske shi,bai ji takon zuwan ta ba, hakan yasa yayi saurin waigowa jin mutum a bayan shi.

Tsaye take tana hawaye,ga kufan jini a koshin ta.

A hankali ta furta "duk rashin sone ya kawo haka??meyasa baka tausayi na??ban ɓata maka rai ba, shin baka ganin tausayina ko sona a idon ka, sai ma tsana da nike gani,ko da yaushe idan na matso kusa dakai,saika nuna man baka da lokaci na,nayi hakuri akan haka,meyasa baka tausayi na,koda baka soni ba,ina son ka saki jiki dani ko da yaushe na kasan ce a kusa dakai, ka daina hantara.

Ta kare maganar cikin kuka.

Baice komai ba,saima juya wa da yayi, ya cigaba da kallon wajen yan fura.

Tace"kana bukatar fura??na siyo maka"daga kai yayi.

Ta juya ta fita,yana kallon wajen,da ta tafi saita waigo ta daga mashi hannu,a haka har ta isa.

Yau ma baki na saki ina kallon ta.

Sallama tayi,Shatu ta amsa tare da gaidata,bata amsa ba tace "asaman fura,yau a chan zan dama,da kaina kuma ina so ku aje man wata,kamar guda shidda idan zan tafi zan zo na amsa "cikin jin dadi Shatu ta amsa.

Tace "Hajiya ga zugale yayi dadi "kallon zogalan tayi tace "idan yana bukata zan zo na amsa" mika mata kayan damu Shatu tayi.

Ta juya muka bita da kallo.

Da murmushi ta nufi inda Prince yake.

Mota ta bude ta fiddo ruwa.

Inda suke zama ta zo ta zauna.

Ta fara tunanin yama zata yi.

A hankali ta rufe ido ta bude kamar ta tuna wani abu.

Ta fara dama furar ta gama.

Ta rufe kwaryar da fai-fai,ta iso inda yake tsaye tace "na gama kai nike jira" juyo wa yayi tayi gaba,shi kuma yana binta a baya,suka zauna bisa kujerun wajen.

Ta bude ta saka mashi ludde a ciki.

Ta mika mashi ya amsa,tare da murmushi a fuskar shi.

Kallo ta bishi dashi na mamaki!

Ya fara shan furar,yana kallon yar kwaryar kamar mai karanta wani abu a jikin ta haka yake binta da kallo.


Ta kasa dauke ido akan shi,yana dagowa suka hada ido.

Kallon ta yake yanzu saboda yadda ya ga hawaye yanzu ma a fuskar ta.

A hankali yace "baki da lafiya ne?"girga kai tayi alamar a'a,kauda ido yayi daga kallon ta.

Ya dan sha furar kana ya rufe.

Tace "zakaci zogala??su ne ke saida wa na amso maka"girgiza kai yayi alamar a'a.

Tace "yanzu kasan minike so dakai?kaga na maka abinda kake so please nima kayi man,ina son muje na koya maka Driving"

Kallon shi take taji mai zai ce,tasan bazai jeba, ,amman babu yadda zata yi tayi ma Hanan alkawari zata ce, amman tasan ba zai yadda ba.

Shiru na wasu lokuta yayi,sannan kuma ya dan motsa bakin shi, kamar wanda zaiyi magana.

Ta maida hankali wajen shi.

Yace"muje,ammn fa idan akwai wahala bazan koya ba,kuma menene amfanin iya driving din?"ta langwabar da kai tayi kamar wacce zata yi kuka.

tace "nidai ina so"

Miƙewa yayi ta dauki kayan su Shatu tace "Bari na dawo" daga kai yayi.

Cike da murna ta isa wajen su.

Ta mika masu kudi,ta amshi wadda tace a aje mata,sannan ta sayi zogala.

Yau dari biyar ta basu,suka mika mata chanji,nayi baya ita kyamar ma kudin take,tace subar su,a wannan lokacin da kagan ta kasan tana tare da farin ciki a tare da ita.

Ta juya ta iskeshi yana latsar waya.

Tace "muje nadawo" mota ya nufa ya tsaya ta bude mashi ya shiga ya zauna,ta rufe ta tada motar,suka bar wajen.


***************
Wani irin ciwo kai ne nike yi kwakwalwata na zafi,hakan yasa ni duƙar da kaina cikin cinyoyi na,ko anzo sayen fura Shatu ke saidawa.

Ina rakube gefe guda.


Nana!Nana!tashi ga mutanen nan zasu wuce,tashi ki gani, kafin su daga gilashin motar,idan suka daga ba'a ganin su.

Fizgewa nayi nace"Shatu kyale ni banda lafiya,wani abu ke yawo cikin kaina,wasu mutane nike gani idan na rufe ido"shiru Shatu tayi tace"ai sun ma wuce"

Tunani Shatu keyi anya ba tana da Aljanu ba,wasu abubuwan idan tana yi kamar ba ita kaɗai ba,ko kayan nan da ta dauko,mugun nauyi amman tun daga maraba har nan ta kawo su.

Kallon tausayi ta bita dashi tace"ki dinga addu'a,Allah ya sawaka yasa musai da da wuri mu koma gida"


************

A titin Sardauna estate suka bi suka mike daya ke mota bata gittawa ta wajen sosai.

Tace"kaga yadda nike kuma kaga abinda zaka taka,idan kana so tayi tafiya"daga kai yayi yana kallon ta.

Haka ta koma kamar wata malamar shi.

Fitowa tayi ta bude mashi,tace"yanzu kai zaka jamu"fitowa yayi ya koma inda ta fito ya zauna,ya kunna motar,ya fara tafiya a hankali.

Kallon shi take tana dariya tana yawwa Prince,sosai suka yi tafiya har suka kai wajen Fatima shema estate.


Kana ya juyo suka dawo tabi shi da kallo tana dariya, parking yayi gefen hanya yace.

Ya lumshe ido alamar ya gaji.

Kallon shi take,idon shi a lumshe,ga dogayen girar idon shi kamar an saka mashi da ma daidai cin bakin shi,daya motsa.

Idon shi ya bude,ta lumshe ido tana ganin fuskar shi.

Kallon ta Anuwar yayi,sai kuma ya kauda kai.

Har a zuciyar yau tausayi ta bashi, saboda yadda ya fidda mata jini,kuma yasan tana kokari,saidai ko kaɗan kamar babu zuciya a tare dashi har yanzu bai jin sonta a zuciyar shi.

Cikin zuciyar yace"Anya kuwa ina kara soyayya?"titi yake kallo kamar shi zaya bashi amsar tambaya.

Tace"yanzu mutafi gida ko?"kai ya daga.

Ta koma wajen zaman ta yadawo nashi,ta tada mota suka bar wajen.


**************

Munyi chiniki sosai saboda yau akwai rana,duk nan yan makaranta suka zauna,suna sha.

Saida muka saida muka tashi muka nufi hanyar zuwa garin mu,bayan mun biya nasaima Ma'u yadilan dinta.

Yau daya ke munsaida da wuri saida muka jira Jabe, kana sai gashi.

********
A gajiye ya isa saboda driving din da yayi,babu ko ban kwana yayi part dinshi.


Cikin azama suka hada mashi ruwan wanka bayan ya gama,ya iske abinci iri-iri ya zauna ya chi.

Kana ya mike ya fita cikin lambu.

A bangaren Kursim ta zuwa ta iske sakon idan ta dawo Umman ta nason ganinta.

Wuce tayi daki ta kwanta,tana tunanin abinda ya faru,mikewa tayi,wanka tayo tazo ta zauna.

Tana kallon raunin a mirror.

Wayar ta ta dauka ta kira Hanan.

Hanan ta dauka tana cewa"Amarya ta ango ya gida"tsaki Kursim tayi tun daga nan tasan akwai matsala.

Tace"yadai ko shawara ta bata yi aiki ba?"nan fa Hanan ta bata labarin komai.

Tsaki Hanan tayi tace"wai halan shine autan maza,taya da gatan ki da kyan ki da duk surar da Allah yayi maki,amman na miji zai tsaya yana wahalar da ke,gaskiya ki chanza"shiru Kursim tayi.

Jin shirun yasa Hanan cewa"baza ki iya ba kenan tunda gashi autan maza?zan shigo gobe da morning,amman sai idan Momy ta bari sai na taho "daga haka ta kashe waya.

Mikewa tayi ta saka kaya taje tabada zogalan da suka zo dashi tace a saka mashi kayan hadi.

Cikin zuciyar ta tace"tunda abinta kade kake so,nasan zaka so zogalan"

Ta juya tayi part din Mom din zuciyar ta cike da tunanin abinda zata fadi mata game da raunin ta.


Kwance yake bisa wata doguwar kujera ya lumshe ido.

Kamshin jikin kwaryar nan yaji yana bala'in so??

Yanzu ya za'ayi yasamu kwaryar?? saboda kamshin dake jiki.

To kode kamshin Kursim ne itada ta dama??

Kirgiza kai yayi,yasan kamshin da Kursim ke amfani dashi.

Wai miyasa yake son komi na mai wannan furar??

Ya kamata na ganta kamin na wuce.

Gashi yamma tayi bare naje garin su.

Zan iya ya fada a fili.

Mikewa yayi ya nufi kofar fita.



***************

Muna isa Shatu na miko man kudin da muka samu chanjin matar binni,nace"a'a Shatu barsu,wajen ki,yau haka Inna tace kudin tane"dariya Shatu tayi tace nasan abinda zan sai maki dasu kuma nasan zakiyi murna.


Mukayi sallama nashiga gida,ba kowa tsakar gidan na ciwo kai tsaye dakin Inna.

Tana zaune tana kirga kudi,nayi sallama ta amsa cikin fara'a.

Baki na saki ina kallon ta!

Yaushe rabon da Inna tayiman murmushi kila tunda nike da ita bata taba ba,sai yau.

Tace"shigo mana auta ta"nan ma mamaki ya kusa sani faduwa.

Nashiga tace"zauna ga wajenan"na zauna gefen gadon karfen ta.

Tace"kiya maza kamin akira sallar magriba kiyi wanka,ga Lado nan zuwa da anyi sallah kinji yar autata"mutuwar zaune nayi.

Idona suka ciko da kwallah.

"To wallahi bari kiji ko kitashi kishirya ko kici na jaki ba magana nike maki ba"!!


Na mike na fita zuciya cike da kunci sai ga Ma'u ta shigo"ina yadilan dita?"nanu mata dakin Inna.

Ta wuce da wakokin ta hankalin ta kwance.

Daki na zauna ina tunanin shin intashi inyi wanka??koko nayi zamana koma de na gudu gidan su Shatu??

Kai idan Inna ta ganoni saina tau sayama kaina??

Tashi nayi ina tunanin taya zan amshi Lado??


Qurrah
[1/28, 10:11 PM] Maryam Marubuciya: *JARABTAR MU*



*Written by Qurrah*

*~Page-17-18~*

https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/



*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*




*~We are bearer's of so golden pen🖊~*

*~we write assidiously perceive no pain~.*

*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*

*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*


Yadda Annabi, Tsira Da Amincin Allah Su Tabbata A gareshi, Yake Kirga Tasbihinsa.

Daga Abdullahi bn Amr, Allah ya yarda da shi, yace; Na ga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, yana kirga tasbihi da (yatsun) hannun damansa.


DEDICATED TO...MY SISTERS😘

Page-17-18


_Bisssimillahir Rahmanir_ _Rahim_


--------------Walkiyar da akayi ne yasa nace daman akwai hadari a garin?

Haba shiyasa yau akayi zafi,mu kuma muka samu chini ki,ashe hadari ne.

Kafin na ida tunanin saidai naji sab kowar ruwa!!

Alhamdullah!! Yau na tsira da zuwan Lado,duk na chinshi ai bazai fito cikin ruwa ba,iska na kadawa lokaci guda naji zuciyata tamkar an wanketa.

Wani sabon littafi ne da Baba ya siyoman na dauka,nafara karan tawa sosai littafin ya dauki hankali na.

Tun farkon fejin littafin,mai littafin ya fadi tayaya zaki zabi mijin aure,ya kawo

Please Login or Register in order to submit comment