Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ki kwantar da murya, duk da daman ke baki da karfin murya".


Nace;",to shikenan Hajiya zan kiyaye".

Tamkar ranar Sallah haka naga mutane suna farin ciki kusan duk wanda zaka gani yayi kwalliya.

Abin ya ban mamaki kawai saboda auren mutum guda baki daya gari ya sauya.


Tun kafin mu isa get din bayin gidan wato sabon get din da aka bude na hango mutane babu wajen zama duk wajen ya cika sosai.


Hajiya tace;"Mu zagaya tsohon dan nan ya cika, daman munzo nan saboda nasan zaifi saukin mutane chan tun dazun nasan ya chika amman muje mugani".


Nace;"Hajiya nagaji muje mu zauna chan tunda kinche wanchan yafi cika, ko kije zan tafo idan na gama kallon nan"


Hajiya tace;"ina zanbar ki ke kaɗai da wannan ciki haka, baki da kuzari yadda ya kamata kuma idan Yarima zai fito turereniyar ganinshi kesawa a dunga ture wasu saidai duk inda zani naje dake, idan ba haka ba kamin ma ki mike wani ya taushe ki, muje kawai".


Nace;"Hajiya wallahi zan kula da kaina sosai na maki alkawari kuma nima zan biyo ki dana gama insha Allah".


Hajiya dai bata soba hakanan ta tafi ta barni, na riga da nagano nufin ta wannan get din babu manyan mutan da take nufii yawanci duk yara ne da manyan yaku bayi.


Ban damu da abinda suke ba, Hajiya na wucewa na matsa na zauna bisa wata kujera cikin wata runfa ina kallon mutanen dake wajen kowa ne yana sabgar gaban shi, wasu na rawa wasu na kallo kidan da ake kallar na garinmu ne na gargajiya.


Ganin mutanen yasa zuciya ta wasai ni kaina da bani wani abu nike ba amman na rage kewa ne wannan.


Murmushi nike ina kallon su, Inna ta Fado man a rai na girgiza kai, ranar Sallah ana kide-kiden nan a kofar gidan mai gari kowa zaije kallo ban dani, amman yau gani ga kidan.


Hawayen da suka gangaro min nasa hannu na goge lalle nayi kewar Babana yanzu kowa ne hali yake ciki??

Nayi zurfi sosai a cikin tunanin gidan mu tare da kewar su.



♦♦♦♦♦

Tare da Daddy ya fito Daddy na rike da hannun shi ko ina kamshi ke tashi ana ta zuba masu flowers masu kyau da kamshi.


Murmushi yake Dad ma murmushi yake, inda Abie yake zaune suka nufa shima Abie fuskar sa dauke da murmushi.

Yana isa zai duka Abie ya mikar dashi tare da rungume shi.


Jawad ne ya iso da Khalil suma cikin shiga ta alfarma kalar na sarauta.


Abie ya saki Anuwar yayi saurin kama hannun su yace;"ka tafi wajen Dad dinka yara na sun iso ina kukabar Walid?"


Daddy yace;"kafin a gansu Ɗana ake fara gani, taho Anun muje ka hau dokin ka an riga da angama komai mutane na jira kaji My son"

Murmushi yayi ya daga Kai.

Jawad yace;"ga Walida nan zuwa Abie muma muje angama hada namu, wai muzamu ta kema Yaya Anuu baya inji Daddy".


Daddy yayi murmushi yace;"daga taimako idan baku so kuyi zaman ku fita da Anuu dina ai matsayi ne ma".

Abie yace;"ku kyalesu kaji Jawad kuje ku hau amman ba take mashi baya za kuyi ba, shima daga kun taimaka mashi"


Nan de sukayi dariya Anuu yaje ya hau dokin yana murmushi.


Tun daga kwalliyar dawakan su zaka gane wanene Anuwar adon nashi ya fita daban dana saura.


A karamin get zasu fara fita su zagaya sai su iso babban get nan zasu dawo.


Hakan yasa suka nufo get din.



Anuwar banda kallon jama'a babu abinda yake sai su Jawad dake ta daga hannu.




♦♦♦♦♦

Zaune nike ina tunanin su Baba sosai hankali na ya dauku.

Wani irin kuwa da ihu da mutane suka yi yasa na dawo daga duniyar tunani.


Ganin ana ta gudu ana matsawa ga 'yan sanda sai turowa baya suke yasa ni tunanin ko me ke faruwa...?

Ban ida tunanin da nike ba naji wani kiɗi tare da wata busa.....


Kiɗin da busar jinsu nayi har tsakiyar kwakwalwata wani irin yana yi na jini ciki.

Kaina na rike dake sarawa.....

Rufe ido nayi ina karanto addu'o'i tare da toshe kunne na saboda yadda busar da kidan ke shiga cikin kunne na.....


Wata irin kara na sakii...!!

Jinayi mutane sun fado kaina an tausheni ihu nike ina kara amman ba Wanda ya damu dani sai takeni ake.



♦♦♦♦♦


Karar da Yarima yaji yasa tsigar jikin shi tashi.


Tare da saurin toshe kunnen shi.


Har yabar wajen kunnen shi a toshe saida aka wuce kana ya saki ajiyar zuciya.


Tunani yake wai meyasa duk inda yaje sai yaji wani abun da zai tuno mashi MANAL wannan irin karar tace.

Haka dai yayta tunanin abubuwan dake faruwa tun da yaje Katsina aka samu matsala, tun daga haduwar shi da yarinyar nan Mai fura komai ya chanza kodai Aljana ce da gaske??

Kuma ai tana da iyaye lalle sai ya bisu yaji komai game da ita, koda bata raye


♦♦♦♦♦


Wani karfafen namiji ya dagoni yana dagoni jini ke zubar min.


Biyu-biyu nike ganin shi saboda yadda na galabaita.


Hajiya ganin baki maza da mata kuma kalar wa'inda take son taga Nana dasu, hakan yasa ta kagara ta iso wajen da take tun kamin Yarima ya iso wurin ya har mutse.

Tsaki kawai take tun dazun ganin lokaci ya kusa Yarima ya kusa isowa Nanah bata zoba yasa tace ma mutanen da take tare dasu bari ta dawo.


Tana zuwa ta hango wani dauke da Nana daya daga cikin masu aikin gidan Sarki dan akwai Uniform a jikin shi mota taga za'a saka ta a guje ta isa wajen.


Aza hannu tayi kai dan a tunaninta ta rasu.

Tace; "wayyo Allah shikenan Nana ta mutu daman hankali na bai kwanta ba da barin ki ke kaɗai a wajen nan"


Waigo wa yayi yana kallon ta yace;"Diyar kice".

Daga kai tayi tana matsar kwallah

Yace;"yi sauri mukaita asibiti shiga mota mutafi".


Cikin sauri ta shiga mota basu zame ko ina ba sai wani hadaden private Hospital mai suna MANAL.


Tace;"Malam banda kudin kawo ta asibitin kudi"


Ya dan waigo yace;"Kada kidamu a MANAL ba'a amsar kudin ku na Yarima ne kyauta ake komai".


Kallon shi tayi cikin mamaki tace;"amman ai a garin nan nike ban tabajin haka ba"

Mutanan kauyen nan na kusa da ita aka bude mawa ta dade ta kusa shekara biyar anan.

Tace;"nasan ta dade dan ina ganinta ko a labarai dan duk Nigeria ance babu asibiti mai kyawunta, amman meyasa yayi ta anan kuma mutanen kauye kaɗai a tunani na 'yan gidan kadai ake dubawa?".


Yace;"Hajiya mun iso bari a fidda yarinyar ayi ta lafiyar jikin ta kana"


Cikin sauri aka amshe ta akayi ciki da ita.


Hajiya ita dai ta kagara taji wannan labarin tasan komai na gidan sunan MANAL ne a jiki, to amman meyasa akayi anan, shin waima wacece wannan MANAL bata mutu ba amman meyasa sunan ta ya kasa bacewa labarin ya rikice mata tasan MANAL 'yar gidan ce kuma asibitin 'yan gidan kaɗai ake dubawa meyasa hadda mutanan kauye?? gidan basu da alaka da wannan kauyen to amman miyasa suke son kauyen??

Gashi ma ana ginin lambu kusa da asibitin kamar kasar waje idan ka shiga ciki.

Ita ta manta da ciwon Nana tunanin ina zata samu cikakken wannan labarin take.


Shi kuma wanda suka zo ganin tana ta zagaye wajen a tunanin shi duk damuwar ciwon diyar tane hakan yasa ya matso yace;

"Hajiya kiyi hakuri zata farfado insha Allah, sunana Sanii anan kauyen nake amman a gidan Sarki nake aiki shiyasa ma na kawo ku nan yadda za'a kula da ita".

Hajiya tayi murmushi tace;"mun gode bawan Allah".


Doctor ne ya fito daga cikin dakin da aka shigar da ita.


Hajiya tace;"lah! Doctor Mubarak daman kana aiki anan".


Yace;"Eh Hajiya"

Ya fada cikin sauri yace;"Hajiya akwai matsala yarinyar nan na bukatar jini sosai idan ba haka ba abinda ke cikin ta da ita kanta akwai matsala za'a iya rasasu"..


Wata Nurse ce ta iso cikin sauri tace;"Doctor akwai matsala babu jininta jininta O- ne".


Cikin sauri ya kalle ta tare da cewa;"Innalillahi...! Yanzu ya za'ayi kenan?"


Sani ya matso yace;"Lafiya Mubarak kayi mana bayani"

Yace;"wallahi jininta wahala yake cikin mutum dari baifi mutum goma ko biyar ke dashi ba, ni wallahi mutum guda nasani dashi".


Cikin sauri Hajiya tace;"waye?? Doctor Mubarak ka taimaka mana gata ga abinda ke cikin ta ka rokan mana shi".


Ajiyar zuciya yayi yace a hankali kamar mai rada;"Yarima Anuu....."

Shiru yayi dan yasan abinda ba zai yiyu bane.

Sani yace;"Kana nufin Yarima Anuwar kenan?"

Daga kai yayi, shima Sanin shiru yayi.


Cikin sauri Hajiya tace;"Dan Allah Sani ka taimaka mana, kaje ka fada mashi halin da muke ciki ka tausaya ma marainiyyar Allah gata ga abinda ke cikin ta".


Mubarak yace;"Sani kataimaka Anuwar aboki nane amman ka fini kusan ci dashi nasan da wahala amman nima zanyi nawa kokarin yarinyar nan twins ne a cikin ta, tunda suka zo last time nayi mata scanning nagani shiyasa nace ma Hajiya bana zubda ciki ban fada maki ba saboda ganin baki murna da cikin, ganin kina bukatar zudda ɗaya ina ga nace biyu ne".


Sani yace;"kana nufin 'yan biyu ne cikin ta".

Daga kai yayi Sani yace;"Bari naje wajen Mai martaba shima da wahala na ganshi Yau saboda baki sun mashi yawa, idan ban ganshi ba zanje wajen Fulani mahaifiyar Anuwar duk da itama ganinta akwai wahala ne a yau".


Mubarak yace;"Sani kayi kokari akwai matsala zan mata wasu alurai kamin lokacin da zaizo zan mashi Message dan nasan bai daukar Call".


Sani ya juya ya fita Hajiya tayi tagumi, lalle yarinyar nan har wahalar yau tana cikin list din kudin da zata biyani.

Doctor Mubarak ya juya ya koma ciki.




♦♦♦♦♦

Baki daya fuskar shi babu annuri a tare da ita.

Haka suka gama zagaya suna isa ya sabka yayi part dinshi cikin sauri.

Su Jawad suka kalli juna miyasa lokaci guda ya chanza shida aka fito ana murmushi tare dashi amman suna dawowa duk ya chanza.


Yana isa part dinshi ya kori kowa yace kada a sake a bude mashi daki kowa ke neman shi har zuwa gobe yana bukatar hutu.


A bisa bed dinshi ya fada rufe kunnuwan shi ya toshe baya son karar da yaji har yanzu yana jinta cikin kanshi.


Rufe kunnuwan shi yayi, jin ana debe mashi ta kalma yasa ya dawo hayyacin shi.

Jawad ne ya cire mashi takalmin kafar shi.

Cikin bacin rai yace;"Miya kawo ka part dina banace bana bukatar kowa ba kowa?? bana son ganin kowamiya kawo ka shigoman part??"


Ciki tsawa! yayi maganar tare da zare ido.

Jikin Jawad sai kyarma yake baitaba ganin Anuwar cikin wannan yanayin ba yanzu fa suka fita yana murmushi kuma tare sukayi zagaya babu wanda ya bata mashi saima so da kauna da ake nuna mashi..

Bai ida tunanin shi ba yaji ya daka mashi tsawa! yace;"Fita! fita! fita nace".


Cikin sauri ya mike yayi wajen Anuwar yaje ya kulle ko Ina ya dawo ya fada bisa gado yana toshe kunne.


Cikin sauri yayi toilet sakar ma kanshi yayi ruwa yana maida numfashi.



Koda Sani ya iso yayi iyakar kokarin shi Amman Mai martaba bai ganuwa gashi Daddy yana tare dashi manyan matakan tsaro aka saka a part din Mai martaba sojoji ne gasunan tsaye kamar wajen yaki saboda Dad yana ciki ga manyan mutane na kasa Nigeria dana kasashen ketare.


Part din Ammie ya nufa tareshi akayi ba'a barin maza zuwa wajen, gashi duk an chanza masu tsaron gidan duk ba wadan da yasaba dasu bane ballen tana ace sunsan matsayin shi wadannan ko Hausa basuji.


Part din Momy 'yan matane su Nifra ne a ciki Momy na part din Ammie.

Nan ma matakan tsaro ya iske inyamurai basujin yaren shi.

Da'ace zaiga Walida da da sauki zama yayi kusa da part din ko Walida zata fito.


Har dare ya fara ba Walida.

Ya mike yayi masallaci yayi salloli ya dawo part din Anuwar kamar nan shugan kasar yake yafi ko ina matakan tsaro.


Haka yayita yawo babu kowa cikin yaran gidan sai mutane ko ina anata raye-raye da kide-kide bayin gidan duk gasunan saboda an chanza ma'aikata.


Zuwa yayi bakin kofar part din Yarima ya zauna nan bacci ya dauke shi.


Saida ya dauki lokaci kana ya fito kaya ya chanza ya dawo bakin window ya tsaya kokadan baijin bacci.


Saida dare yayi sosai kana ya kwanta.



♦♦♦♦♦


Hajiya dake zaune Doctor Mubarak ya fito yace;"Hajiya ga daki nan ki shiga ki kwanta kamin gobe da safe nayi mashi Message bai dubaba na kirashi bai dauka ba amman nasan Sani zaiyi iyakar kokarin shi dan yanada mutumci, Kuma Yarima yanada tausayi idan har yaji abinda ke faruwa tozaizo nan insha Allah".

Tace;"to shikenan nagode Mubarak"

Saida Hajiya ta leka dakin da Nana take kwance ta hango ta ko motsi batayi, kana ta shiga dakin daya nuna mata, saboda Sani kawai yasa take wahalar nan da tuni tayi gida babu mai kara ganinta tanason jin labarin nan saboda tasan labarin MANAL amman batason wannan ba, batason miya suke son gefen ruwan nan ba ko minene dalili??


A jiyar zuciya tayi tare da tsoki yarinyar nan tasa tayi asarar costumers.


Haka ta kwanta bisa gado mai kyau ta juya sai bacci.



♦♦♦♦♦

Bai runtsa ba har akayi asuba.

Yaune safiyar daurin aure kuma karfe Tara Daddy yace zasu airport koma yayi ya kwanta saboda bai sami bacci.


♦♦♦♦♦

Doctor Mubarak ne ya tada Hajiya.

Ganin yanayin sa yasa ta murmuje ido yace;"Hajiya kiyi wani abu mana yarinyar nan zata iya rasa ranta duk nayi magana asibitocin garin nan babu shi idan kinsan akwai mai kalar jinin ni zan saya nasan kina hudda na mutane da yawa".


Hajiya tace;"Mubarak Koda ina hudda da mutane tambayar su zanyi kalar jinin su basan mai Shiba koni bansan kalar jinina ba balle na wasu"


Yace;"Bari naje gidan da kaina Allah yasa bai wuce daurin aure ba"


Mubarak ya fita cikin sauri yabar Hajiya zaune.

Tana murguda baki anya yarinyar nan Alkhairi ce a gareta??

Anya ba korarta zatayi ba idan ta warke zata iya daurewa tayi wahala cikin watannin da suka rage Anya tana iyawa??


♦♦♦♦♦


Jin ana tadashi yasa ya bude ido.

Ganin Dad yasa yayi saurin bude ido.

Dad yace;"ka kyauta Anu saura one hour jirgin mu ya tashi amman ace kai bacci kakeyi kowa ya fita a tunanin mu kana nan kagama shiryawa to mungode yauma kabamu kunya ka tuzar tamu a idon jama'a zargin da yan garin ke maka ya tabbata kenan mungode kaji Anuwar"


Daga haka ya fita rai bace yabar dakin tashi yayi ya shiga toilet Jawad ya hada mashi ruwan wanka.

Koda ya fito an ajemashi kaya yana sakawa Jawad ya shigo ya saka mashi takalmi ya mika mashi hula hannunshi ya kama ya saka mashi agogo.


Duk abinda ake Anuwar sai bata rai yake duk abinda yake saboda ganin ran Dad ya baci yasa yake sauri.

Baifi fourty minutes ba ya fito tare da Jawad.


Yana fitowa aka rufa mashi baya.


Kai tsaye wajen motoci yayi, yana zuwa zai shiga mota yaji muryar Sani yana kiran shi cikin dagawar Murya kuma Anuwar yau yace ba Yarima ba.


Juyawa yayi yaga Security sun hanashi matsowa sun rikeshi.

Abin mamaki ya bashi daga masu hannu yayi Sani ya iso a guje ya dukarsa.

Kafafun shi ya kama yace;"Anuwar ka taimaka kayi ceton ran mutane da yawa, Kai kade ne zaka iya ceton ran yarinyar nan da abinda ke cikin ta"


Kallon Sani yake bai gane miyake nufiba, da yayi ceton rai shida ba Doctor ba minene nashi a ciki?? Idan kudi yakeso ai kwai Hospital kuma yasani.


Dai-dai lokacin da Doctor Mubarak ya iso.

Ya kalli Anuwar nan yake mashi bayani abinda ke faruwa.

Shiru Anuwar yayi bazai iya barin ayi asarar rai ta dalilin shi ba amman kuma Dad da Abie da sauran mutane fa??

Kallon agogon hannunshi yayi ya zaro ido....



Qurrah
*_JARABTAR MU*_







*_Written by-Qurrah✍🏼*_



*Page-51-52*


*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*

https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/


*~We are bearer's of so golden pen🖊~*

*~we write assidiously perceive no pain~.*

*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*

*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*

*Zikiri Yayin Shiga Gida.*


بِسْـمِ اللهِ وَلَجْنَـا، وَبِسْـمِ اللهِ خَـرَجْنَـا، وَعَلَـى رَبِّنَـا تَوَكَّلْـنَا .

Bismil-lahi walajna, wabismil-lahi kharajna, wa'ala rabbina tawakkalna.

Da sunan Allah muka shiga, kuma da sunansa muka fita kuma ga Allah kadai, Ubangijinmu, muka dogara.



DEDICATED TO.....MY SISTERS😘


Page-51-52

_Bissimillah Rahmanir_ _Rahim_



----------------Cikin sauri yayi yun kurin shiga mota.


Doctor Mubarak yace;"Prince yarinyar nan karamar yarinya ce kuma twins ne a jikin ta marainiyya ce sannan kasan O- wahalar samu ne dashi, idan bakai ba wallahi ban san wani dashi ba sai matar ka data rasu, nasan da tana da rai na tabbata yadda take da tausayi kuma take son taimako tun tana yarinya da yanzu ta bayar, nasan halinku iri daya ne amman meyasa zaka chanza daga halin data mutu tabar ka dashi".


Kallon shi Anuwar yake ga Security tsaye ga time na tafiya.

Mubarak yace;"time din idan akayi sauri zai isa".


Ɗa ga mashu hannu yayi sannan yayi nuni daya shiga mota.

Prince ya shiga mota aka rufe Mubarak zai shiga Security suka nuna mashi motar bayan Prince.


Ya koma suka shiga shida Sani suka wuce.


Cikin mintuna kaɗan suka isa asibitin koda suka isa babu Hajiya.


Basu damu ba cikin sauri suka isa Lab aka gama abinda za'ayi aka ɗibi jinin Prince, koda aka gama saura ten minutes jirgi ya tashi cikin sauri Prince ya juya yabar asibitin.



Ina bude ido naga jini na shiga a jikina lumshe ido nayi ina tunanin jinin waye ake sakaman? nan na tuna irin yadda busar gidan Sarki da kidan gidan suka fara tashi, ashe sune suka ruɗani to komai yasa naji wannan yana yin da naji akan Busar ohow??


Wata ma a'ikaciyar gidan asibitin ce tace;"Sannu ya karfin jikin ki?"

A hankali na motsa baki nace;"da sauki"

Mikewa tayi ta fita, kallon jinin dake shiga jikina nike yau itace rana ta farko da aka sakaman jini to jinin wanene wannan ke gunada a jikina??.


Bude kofar aka yi na kai dubana ga kofar likita ne ya shigo cikin sauri ya iso inda nike ganin nasan likitan ya sani zaro ido tare da taɓa cikina koya zubar man da ciki ne??.

Shine likitan da Hajiya tace azubar man da ciki yace bai zudda ciki, to ko dubara yayi man?? Tunda wannan ba kalar waccen asibitin bace.


Ganin yadda nike kallon shi ga hannuna a bisa cikana ina shafawa yace;

"Cikin ki yana nan lafiya kalau kinji, daga yanzu anan zaki ringa zuwa awo kinjii?"


Na daga kai cikin jin kunya nace;"nagode sosai".


Hajiya ce ta bude kofar ta shigo tana rike da kuloli na abinci cikin wani kwando.

Sannu da zuwa yace tare da mikewa.

Tace;"yawwa likita bokan turai, sannu da kokari wajen ceto rayuwar ta".

Yace;"ai babu komai Hajiya ga magunguna nan asibitin kyauta take komai".


Tace; "Ah! Lalle mungode Allah yabar zumunci"

Yace;"Ameen"


Nan ya nuna ma Hajiya magungunanta ya juya yabar mu.


Hajiya tace;"Ya jikin naki".

Nace;"da sauki Hajiya sannu da kokari nagode sosai Allah ya saka da Alkhairi"


Hajiya tace;"ai Yarima ne abin godiya shida ya ceto ranki, jininshi ne aka saka maki nayi mamaki daya bada jinin nan, saboda shi jinin mulki ne da sarauta lalle kina da sa'a a rayuwa ace jinin Yarima a jikin ki, ban taba tunanin haka zai yiyu ba gaskiya dan koshi ya bada iyayen shi zasu hana amman ke kinyi sa'a sosai"


Na kalli jinin da ke tafi jikina naga saura kaɗan ya ida shigewa jikina nayi murmushi nace;"lalle kam Hajiya Doctor Mubarak yayi kokari kuma kema saidai na biki da addu'ar Allah yayi maki sakayya ta Alkhairi".


Hajiya tace;"Umm"

Daga haka bata kara magana ba.




♦♦♦♦♦


Suna isa airport su Daddy har sun shiga ana shirin rufe jirgi kana Yarima ya iso.


Yana zuwa ya shiga kusa da kujerar Daddy ya zauna duk da cikin jirgin duk Family din sune Maza yan daurin aure.


Ganin audiga a hannunshi yasa Dad yace;"Subhanallah Anuu me ya sameka ne?"

Yayi saurin riko hannun ya cire addugar jini ya fito ya goge.


Baice ma Dad komai ba, hakan yasa Dad ya saki hannunshi.


Shiru a tsakanin su bamai magana sai yan uwa da keta fira suna janshi wai makararren Ango shidai yayi murmushi kawai.


Suna isa Katsina tun daga airport mutane ne har suka isa fada garin cike yake sosai.


Suna isa aka kaisu masabki Daddy ya kira daya daga cikin Security yana tambayar shi mike faruwa ne, nan take ya fadama Daddy.


Shiru Daddy yayi yana kallon Anuu, Abie sai sabgar gaban shi yake baki sun mashi yawa baida time din Anuwar din ma.

Daddy yaja hannun Anuwar wani daki suka shiga ya kulle dakin yace;"Anuwar ka faɗa man gaskiya Aljanar nan data aure ka ta kara biyo ka ko?? Itace kaje kaba jini ko saboda duk duniya ita kaɗai ke saka ƙin bin umarnin mu itace ke saka baka ganin kowa a yanzu sai ita, ka fada man itace ta biyo ka Bauchi ko?".

Yadda Daddy yayi maganar kasan yana cikin damuwa sosai.


Anuwar ya dukar da kai yace;"Nidai Dad jiya da muka fito zagayen fada naji kalar kararta ina nufin kalar kukan ta, kuma ita wadda naba jini 'yar uwar Sani ce tana da mijinta hadda ciki gareta na twins sannan jininta O ne, kasan dagani sai MANAL ke da shi duk nan kusa shine nagani da ayi asarar rai gwara na taimaka mata nima sai Allah ya taimaka man wata rana".


Shiru Daddy yayi yana nazarin magan ganunshi.


Anuwar yace;"wallahi Dad tun jiya nake cikin kunci, amman tunda na bata jinin nan na jini cikin farin ciki zuciyata tayi sanyi sosai kaga ikon Allah ko, wallahi daban bata jinin nan ba da yanzu ina cikin kunci".


Kama hannayen Dad yayi yace;"kamar ta manzon Allah yace "ku gusar da bakin ciki da damuwa dayin Sadaka, kaga jinin nan ba kudi na amsa ba sadaka ce nayi dan Allah Please Dad Understand me"


Murmushi Dad yayi yace;"naji dadin kalaman ka na baya lalle Allah yana tare da kai kana da zuciya mai kyau, yanzu muje time din zaman ka ango yazo muje a daura"


Murmushi Anuwar yayi suka fito tare da Daddy banda bushe-bushe da kide-kide Babu abinda ke tashi a gidan sai kirari da akema Ango.


A fadar Katsina aka daura auren Anuwar AbdulAziz Imam da Kulsoom Muhammad Imran, jama'an da suka hallacci daurin auren ba'a magana na birni dana kauye.



Ana gama daurin aure su Dad da Anuwar suka juyo zuwa Bauchi.


Koda suka iso kai tsaye Anuwar ya wuce part dinshi saboda ya gaji sosai.



Ya kasa gane tunda ya bada jininnan yake cikin farin cikin da ya da ɗe baiyi shiba lalle ceton rai na daban ne, Babu abinda yakai aikin Alkhairi dadi.



A haka ya yini har dare shi kaɗai sai lokacin yaga message din Momy Amarya tana part din Ammie ya bude nashi.


Sani ya kira ya hada mashi ruwa yayi wanka kana ya kalli Sani daya aje mashi abinci yace;"ka rufe wayar ka kabar gidan nan sannan ka rufeman part dina, dan ma kada a ganka ace ka bude bana bukatar kowa a yanzu ina bukatar kadaici".


Cikin grimama Sani ya amsa da to yayi yadda yace.


Abincin da aka zuba mashi ya faraci yana fara'a ya dade baici abinci kamar Yau ba.


Momy sai kiran shi take yaki dagawa.

Zai kashe wayar kiran Dad ya shigo

Cikin sauri ya dauka;"ka bude part dinka a shigo da amarya"

Yace;"Dad kafa san ina cikin farin ciki, shine hadda kai za'a saka baki dan a takura ni a kai ta wani part din kona kusa dani a ajeta".


Dad yace cikin bacin rai;"tunda kaba Aljanar ka jini ba, tun dazun na tambayi Sani yace shi taimako yayi bai san ta ba, ta riga data shiga jikin ka shiyasa ita ke saka ka wannan farin cikin to Allah ya fita, ka tashi ka bude tun kamin na iso, yanzu wajen Mai martaba nayi asan mafita tunda saboda ita ka kema Kulsoom wulakanci gwara adau mataki".


Daga haka ya kashe waya.

Tashi yayi yaje ya bude kofa ya dawo ya haye sama ya kulle ko ina tun daga palour har zuwa bedrooms din shi na sama".


Yauma kamar kullum zama yayi ya fara zana mai fura rike da sandarta a hannu tana tsalle, bai san kallar fuskar ta ba hakan yasa yayi mata kalar fuskar MANAL tunda kalar tafiyar su guda.


Yana jin motsi a kasa amman bai motsa ba ya cigaba da abinda yake.




♦♦♦♦♦

Bayan jinin ya kare aka sallame mu muka koma gida.



Yauma aka kawoman abinci kala-kala

Please Login or Register in order to submit comment