Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tunani.

Yana zuwa part din da ya sabka,cikin sauri masu aikin part dinshi suka cire mashi Alkyabba,zasuyi magana ya nuna hanyar fita,suka bar wajen.

Lumshe ido yayi yana tunanin jinshi yake tamkar wata duniya,lalle ba karamar biyayya bace yayima Mai martaba zuwa shi wurin nan.

Shiru yayi yana bukatar kadeci yana bukatar zuwa gefen garii.

Yana son zama gefen gari inda babu haya niyya.

To yanzu wazaima magana kode ya fita shikade??

Wayar shi tayi kara ya duba yaga Ammi, murmushi yayi ya daga kiran.


***************

Ina nan zaune bakin gado karana naji sallamar Baba,jiki na har kyarma yake wajen saurin fita.

Ina fita dai-dai lokacin da Inna da Ma'u suka fito,suka tsaya bakin kofar dakin Inna,ni kuma a nayo wajen Baba.

Tun kamin na iso har hawaye sun wanke man fuskata,dan nasan da wahalar gidan Lado mai jakkai,gwara ta nan gidan,a chan dami zanji da wahalar tukama yaran shi tuwo koda surfe da dakan fura koda masifar matan shi har made Uwar gidan sa yadda naji labarin tana bautar da matan shi.

Hakan yasa dana tuna sai hawaye.

"Subhanallah...!!"Baba ya fadi bakin shi har yana kyarma wajen fadi.

"Mi akayi makine diyata waya tabaki ne kike kuka haka,fadaman ko waye?"

"Aikin banza tattalin shege"inji Inna dake tsaye kofar dakin ta.

Baba wallahi bana son auren nan,kabari nasamu mai sona nima, wallahi ban son Lado,ka taima kaman Baba.

Kallon mamaki Baba yake man kamani yayi ya zaunar bisa turmin dake tsakar gidan "waya fadamaki Lado mai jakkai zaki aura?"

Cikin isa da tinkaho Inna ke takowa har ta iso inda muke tsaye tace;"nice nan nace Lado shima ya aiko da kayan baiko,saboda yayi maka magana baka amince ba,ni kuma a matsayi na na uwarta na amince,ayi rana daya ita da Ma'u "kallon banza ya bita dashi,ya kama hannu na mukayi daki na.


Ya zaunar dani bisa gadon kara na yace; "kiyi hakuri Nanah babu wanda ya isa ya aurar dake ga wanda baki so,indai ina da rai, saidai idan ke kika kawo shi kikace kina so" a jiyar zuciya nayi.

Ya mike ya fita naji hankali na ya kwanta,nayi ajiyar zuciya na kwantar da kaina bisa gadon kara.

Guf naji akayi da dan kyauren da nike rufe daki na.

Zumbur nayi na mike kada kyauren ya fado man cikin zaro idoo....!!!


Tamkar zakanya haka take maida numfashi kamar wanda tayi gudu.

Dafe girji nayi ina kyafta ido!!

Ma'u na bayan ta "ashe duk kashe din dana yi maki baki dauka ba,kenan idon ki har ya bude da zaki tsallake magana ta?? kenan kinsa naji kunya da kaina naje na nemo maki auren Lado,shine zaki watsa man kasa a ido,dan baki zauna cikin cikina ba??to bari kiji wallahi wuya saita sa kin amince da auren Lado,dan sai gidan Lado ya zaman maki Aljannar duniya,dan sai gidan nan ya zaman maki bakin gida,da kafar ki zakije neman Lado"Ma'u tayi tsaki tare da wurgo man harara


Kuka nike tamakar raina zai fita;"Inna ki taimaka man wallahi bazan iya zama gidan Lado ba,zan maki duk abinda kike so,ki taima min Inna "Kafafun ta na rike ina kuka tamkar raina zai fita.

Fizge kafar ta tayi,ta ingiza ni nayi kasa na bige kaina jikin gadon karana.

Wani irin ihu na saki, wayyo Inna na mutu...!! "bata ko waigo ba saima cewa da tayi; "yanzu kika fara ganin azaba Kuma kun kullah alaka da ita kenan" ta fita ta nata bala'i.

Dafe kaina nayi jini na zuba ga kara ya shige man gefen fuskata.

Kuka nike cikin zuciya ta nace;"zan dauki ko wace azaba akan zaman gidan Lado "na cigaba da kuka ga azabar zafi da kaina keyi,nasa hannu zan cire inda karan ya shiga,wani irin azabar zafi yasa saida nayi kara na cire ina runtse ido.


Har dare yayi ina zaune sai walkiya da akeyi da alamun hadari ne,jim kadan ruwa ya sakko,dan danan sai sanyi gashi kuma Inna ta cire man kyauren dakina gashi babu labule,hakanan na kwanta na dukun kune waje daya.

Zumbur na mike jin ruwa a jikina,dakina ne ke zuba dai-dai wajen gadona.

Kukan tumaki naji zasu shigo dakina na kara rudewa,na rakube gefe guda ina kyar mar sanyi.

Ummeeyyy.......ganin su nayi a cikin daki na.

"Innalillahi..!! wayyo Allah na ku fita kubar man daki "kuka suke suna Ummeeyyy Ummmeeeyyyy,Inna ce a bayan dabbobin.

Nace; "yawwa Inna ki zo ki korasu,su duka sun cika man daki"cikin kuka nike maganar ga dakina na zuba ga sanyi.

Tsaki tayi tace;"su fita suje gidan Uban wa??ai daman kinsan nan dakin sune,nagaji da raɓewar da suke ne,basu san ruwa na bugun su,kinga sai ku raba dakin su a gefen daya daban kema a gefe daya daban,diyar Liman wacce ta girmi auren Lado" harta juya ta fita sai kuma ta dawo "bani hitilata,tunda ba Uban ki yasaya ba,sai ki jira har yasai maki taki" ta gizge hitilar hannu na tayi tsaki tabar wajen.

Kuka tumakin Inna keyi ga babu fitila gashi yau wani irin duhu ake.

Tayaya zan kwana da tumaki daki daya??

Jikina kyarma yake dan tsoro, lokaci guda na nemi zafin ciwon dake goshina na rasa tsabar tashin hankali.


Gab-Gab kakeji cikin dakin sai kuka da suke yi ga fitsari tare da kashi, tamkar babu bil Adama a dakin,saboda yadda na lafe jikin wata kusurwa,gashi dai-dai nan ruwan ke zuba,ban damu ba saboda yafi man zama cikin tumakai kilama su sokeni da kahon su.

Amman duk da haka zuciyata fal da tsoro take,kada suji motsina.

A haka a tsaye nike har aka dauke ruwa nayi hamdala,jikina sai kyarma yake saboda sanyi.

A hankali na tsugunna dan naji tsit,sunbar kuka,nayi zukunne har bacci ya daukeni.


****************


Bayan ya gama waya da Ammi,Abie ya kirashi suka gaisa yace;"babu damuwa ko Yarima?"lumshe ido yayi yasan yana cikin takura baiko kwana ba amman jinshi yake kamar yayi shekara,saida Abie ya kara mai-maita tambayar kana Yarima yace;"Abie inason gobe na fara fita gefen gari,dan na rage kewa"murmushi mai sauti Mai martaba yayi yace;"kada ka damu zan ma surukin naka magana saiku fita da Gimbiya,hakan zaisa shakuwa a tsakanin ku"baiji dadin saka Kursim a ciki ba amman tunda yana son fita babu yadda ya iya.

Sukayi ban kwana ya aje wayar,yayi shirin bacci yayi addu'a ya juya.


Kursim tace;"lafiya kike kallona??kamar yau kika saba ganina?"maida numfashi Hanan tayi tace;"wallahi Princess tausayi kikaban dan na fahimci halin da kike ciki,ina da shawara "kallon Kursim tayi tace"inajin ki,fadaman inji".

Mikewa tsaye tayi ta iske Kursim inda take zaune"mizai hana mu bullo ma Prince ta bayan gida,ina nufin muyi amfani da abinda yake so"kallon ta Kursim keyi tace"Banga ne mikike nufi ba,kamar mi kenan?"

Murmushi Hanan tayi tace;"ina nufin MANAL mana,idan akwai wadda kike mu'amallah dashi a gidan ki tambaye shi wane irin attitude Manal keda?"

Murmushi Kursim tayi tace;"ya akayi Doctor tafi Lawyer dubara??gaskiya komi nawa ya tsaya,idanu na sun rufe"dariya Hanan tayi.

Jim Kursim tayi kamar tana tuna wani abu tsalle tayi tace;"yes I remember muntaba fira da Sister dinshi Ahalam tace Manal nada funny attitude ita kade ke sakashi dariya,sai Ammi da Abie iyayen shi"zaro ido Hanan tayi cikin mamaki!!!

Jin jina kai tayi tace;"kenan Princess zata koyi bada dariya kenan??"murmushi Kursim tayi tace;"yanzu da muna shiri da Nifra da saina tambaye ta game da Sister dinta".

Bata fuska Hanan tayi tace"wallahi banson yarinyar nan, saboda kasaitar ta da jin kanta,gata karamar yarinya,amman sai iskanci,kinga wani biki danaje na Dikko,yaron wani ambassador,ashe coursin dinta ne,wallahi tana shigowa Hall din saida aka mike nide naki tashi,ganin yadda hankalin kowa ya koma kanta yasa nabar wajen,kinga yadda diyan Governor's keson shiga kamar itace President din,shiyasa banson ta,bata ko magana saide daga hannu"dariya Kursim tayi tace;"shiyasa mina bamu shiri,kuma yadda akace sanda uwayen kema Manal ko rabin shi basuyi ma Nifra,saboda gata kamar a cinyeta shiyasa sukayi garkuwa da ita,gashi kakan ta wanda ya haifi Maman ta Major ne,ko chan Family din su Maman ta kamar su hadiye ta danso,kinga son da sukema Manal ne ya koma kan Nifra,gata ta ko ina shiyasa dole tayi wulakan ci"tsoki Hanan tayi tace"kila kuma banzar dan taga tanada kyau"

dariya Kursim tayi tareda mikewa tace"ance duk kyanta Manal tafita"

Cikin mamaki da zaro idoo Hanan tace;"Aljana ce ita Manal din??dan gaskiya duk da banshiri da Nifra amman nasan tanada kyau"

Dariya Kursim keyi tace"wallahi naga photu nan su"girgiza kai Hanan tayi tace;"dole Prince ya rude shiyasa duk wahalar make up din da akayi maki bai yababa,amman akwai dabaru da yawa da duk munin mace tayi amfani dasu Namiji sai ya rude balle kema mai kyau ce".

Agogo Kursim ta kallah tace"wai daman haka dare yayi munata fira??mu kwanta hakanan firar Yarima saita kaimu gobe ba'a gama ba"tare suka kwanta kowa ce da kalar tunanin ta a zuciyar ta.


****************
Ummeeyyy-Ummeeyyy kukan tumaki yasa nayi firgigi na bude ido anata kiran asuba.

Subhanallah!!

Na mike cikin sauri jin kaina na ciwo,gani nayi kamar lokacin dana kwanta bacci.

Banda warin kashin su tare da zarnin fitsarin su babu abinda dakin keyi,banson wari ko kadan a rayuwa ta,ni dai kamshi shine abinda nike,na toshe hancina.

Na mike tsaye jin motsi yasa suma suka mike.

Nazo zanfita sun tare kofa,duk suka rude sai kuka suke,nima yau cikin zuciya tsoron su nike,duk da tunda na budo ido a duniya nagan su,amman yau saboda sun zama abokan rayuwata babu sabon kwana waje daya yasa na rude.

Da kyar nasamu na tsallaka har na bige da bango nafadi yaraf!!

Su kuma duk sun rude, suma suka fito nayi saurin janye jikina kada su fadaman.

Kafa ta ta bugu zafi nike ji sosai,jina cikin lema yasa nayi saurin mikewa.

Zanena duk ya jike da laka,saboda ruwan jiya,ina murnar kayana sun bushe sai kuma murna ta koma ciki to dame zanje tallah Yau,su kadai suka rageman riga da zanii,masu lafiya.

Cikin sauri na koma dakin lokacin sungama fita,na toshe hancina saboda warii.

Haske ya dan fara na hango buhuna na kaya,ina zuwa na kamashi nayi saurin saki ganin kashin tumakai ne da fitsarin su.

"Innalillahi..!! Sama suka kwana kenan yanzu yazan yi??"

Dauko buhun nayi na fito bakin rijiya na zazzage kayan.

Na dauko bahon wanki kofar dakin Inna.

Nazo na jawo ruwa na zuba banji karar tafiya ba sai dai naga Inna tsaye gabana cikin tsoro nace;"Inna Ina kwana!!

Umm Daman "tsawa ta dakaman tace"kada ki kwashe ruwan rijiyar nan,kuma ki maidaman baho Ubana ya saiman ba Malam ba,kada ki sake tabaman kaya,kije korama kiyi wankin ki sarkin yan tsabta" hawaye suka zo man.

Na kwashe kayana zan bar wajen tace"narasa inda yarinyar nan ta gajii kafiya da taurin rai"bance komi ba"tace ki ratse kibi tabaya,kada kibi ta gaban massalacin da Malam ke bada karatu,idan kika bari ya ganki,saina yimaki wata azabar kuma kidawo kiyi aikin fura dan yau da wuri nike bukatar kifita tallah,dan nagaji da ganinki"nayi saurin fita.

Babu kowa saboda sanyi ruwan jiya,har nagama wanki a korama babu wanda yazo,na dauki kayana nayi gida.

Ina zuwa Baba baidawo ba na wuce nayi sallah,na gyara dakin,kana nafara aiki.


*************

Kalolin abinci ne agaban shi,amman bai kalli ko guda saima tashi da yayi ya bar wajen,bakin window ya tsaya kamar kullun hannu cikin aljihu,ina bukatar fita ya ambata a fili.


Cikin Farin ciki da shigo dakin ta tada Hanan dake rankon bacci.

Bude ido tayi tace"miya faru Princess zaki tadani,bayan kinsan jiya bamuyi bacci da wuri ba"murmushi ta saki tace"fita zamuyi gefen gari da Prince"zaro ido Hanan tayi ta murtsike ido tace"wow thank God ga opportunity kinsamu bari na fada maki abinda zakisa Prince ya rude"kusa da ita taje tayi mata rada a kunne,su duka sukayi dariya Kursim tace"kai kawata dama kece Lawyer kin san dubaru da yawa shawarar ki ta amsu bari na tashi na shirya yau bani bukatar kowa ya shiryani nizan yi da kaina"ta mike ta nufi toilet.


Shima Prince ya shirya ya fito ana masa kirari har ya iso wajen motocin da zasu fita.

Kursim ce tafe tana kamshi cikin shiga ta Alfarma tayi kyau nagani na fada,cikin purple din riga ta material ita Order tayi daga Dubai,duk kayanta order ne tayi wadan da zata saka har Yarima ya koma.


Babu magana ta mika hannu ta amshi Key din mota,ta kashe mashi ido tareda murmushi tayi nuni da ya shiga.

Ba musu ya shiga ya zauan.

Princess ta shiga Driver sit ta zauna.

Cikin mamaki yake kallon ta daman tana driving??

Tunda yake bai taba driving ba,gashi ita mace zatayi to mi hakan ke nufi dagashi sai ita kenan zasu fita??

Akwai wani abu a kasa kenan ko miye oho??


*************

Na gama aikin fura nayi wanka na saka kayana da suka bushe.


Nace"Inna na tafi"bako ta kalleni ba saima waka da takema Ma'u,wai sarauniyya kuma Gimbiya matar Kabiru dan Mai garii.

Na fita nabi ta bayan garii saiga su Shatu.

Na hau muka gaisa tace"waike kullun cikin rauni kike"nayi Murmushi tace"yau zamu shiga birni jabe zai kaimu"zaro idoo nayi nace"Birni Kuma??"ta daga kai.

Hakanan naji banson shiga birni,saidai ko dan kaunar da Shatu keman zanje.

Yau zanga mutanen Birni😅😅

Qurrah
[1/28, 3:02 PM] GOLDEN PEN WRITERS ASSOCI: *JARABTAR MU*



*Writing by-Qurrah*


Page-5-6

https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/



*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*




*~We are bearer's of so golden pen🖊~*

*~we write assidiously perceive no pain~.*

*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*

*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*

*~Addu'ar Wanda Ya ji Tsoron Faruwar Wani Abu Mummuna saboda Kambun Baka~*


Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya ce; "Idan dayanku ya ga wani abu da ya kayatar da shi ga dan uwansa, ko ga kansa, ko ga dukiyarsa, to ya roki Allah ya sanya albarka gare shi; domin kambun baka gaskiya ne.


DEDICATED TO....MY SISTERS😘






-------------Babu ɓata lokaci jirginsu ya tashi sai katsina suna isa suka iske taro anzo tar barsu.

Babu wanda Yarima ya kallah saka makon faduwar gaba da ta riskeshi yana isowa garin yaji wani iri ya kasa gane ma kanshi zufa kawai yake.

Na bayan shine ke cewa Yarima na bada gaisuwa ga duk wanda kenan.

Har ya shiga mota suka bi hanyar gidan sarki.


********************

Yau koda na tashi na jini lafiya kalau ga karfi da nike ji a jikina.

Yauma kamar kullun har na gama wanke-wanke.

Aikin fura na fara ina daka Ma'u na zaune tana kwalliya sai ga kawayen ta.

Da girman kujerar ki matar Kabiru a gida sai dai a kirɓa a baki kisha haka a gidan Miji sai dai a kirɓa a baki ki sha.

Duk garin Dansabau babu macen da bata yin daka sai ke Ma'u diyar Liman matar Kabiru.

Wani daɗi ya ziyarci Ma'u a zuciyar ta tace " mace sai dai tayi man kirɓi nasha naba wa'inda nike so amman idan yarinya tayi biyayya kila na tausaya mata nasa ta cikin masu take man baya garin namu ne "shewa sukayi tare da guda.

Matar mai gari da girman kujerar ki "tace shiyasa nike son ku yanzu kuzo muje Tashar Ado mu kaso kudin tallar da waccen banzar ta samo jiya "daman abinda suke so kenan suka miƙe suna mata kirari kamar wata matar sarki.

Tace "yan bakin ciki sai dai su mutu ta Allah ba tasu ba "suka kara shewa suka fita.

Ina ma Ma'u zata gane bana mata bakin ciki da auren Kabiru.

Nasan bazan samu kamar Kabiru ba amman ban taba jin kyashi ko hassada akan auren nasu ba,saboda nayi imani da Allah ke bada wa ,kuma ban isa na hana abinda Allah ya kaddara ba,tome zai sani bakin ciki kuma akan 'yar uwata.

Haka na gama aiki na gaji wajen sha biyu nayi wanka na dunƙule furar ,na leka dakin Inna,nace Inna na gama sai naga babu kowa.

Nayi zaman jiran Inna jim kaɗan sai gata,tace yawwa tunda kin gama ina so in baki sabtu idan kinje.

"Kisawo ma Ma'u turaren nan dan aune na Muttala ukku" nace to "kema ki dauki Muttala guda kisai wani abu" cikin jin dadi nace nagode Inna.

Kallo take taga Ina farin ciki tace "ban yadda dake ba mikoman kwaryar nan na ƙirga furata dan naga yau nishad’i kike zaki yi min cuta ko kin samu dama ki zalun ceni "na miƙa mata tace "Allah yasa 'yar biyar ta bace kiga kalar bugun da zaki sha a gidan nan sai yafi na jiya kuma da kafa nace kije kada kihau wata mota "nace to Inna.

Koda na fita bakin gari naga Amalanken su Shatu ina isa naga Shatu ciki da kwaryar nonon ta"tace tun dazun muke jiran ki jiya Jabe yace baki da lafiya "nace ai naji sauki na hau muka tafi muna fira.

Yau zuciyata wasai nike jinta jinike kamar an man wata kyauta farin ciki nike ji a raina na rasa dalili.

Muna zuwa muka zauna a inda muke zaunawa koda yamma ta yi munsaida.

A cikin tashar Batagarawa muka shiga nida Shatu tayo sayayyar kayan su na fulani,ni kuma na siyoma Ma'u turaren aure.

"Shatu tace ba zaki sayi kamshi ba nasan kina son kamshi"

Nace Baba na ya siyoman jiya.

Muka dawo muka dauki kwaryoyin mu.

Jabe yazo ya dauke mu da Amalanken shi.

Awara muka sawo munaci muna fira.

Idan ina tare da Shatu har mantawa nike da matsala ta.

Muna zuwa Kauyan mu na dire nace sai gobe Shatu na gode.

Shatu tace gobe ki fito da wuri na daga kai.

Ina shiga gida da sallama.

Da farin ciki a tare da dani hakanan yau da farin ciki natashi.


Kaya nagani a tsakiyar gidan mu "Innah ke guda tana cewa yuriri diyata mai goshi" ga kayan nan kwalayen biskit da alawa da cingam,sai wasu a ware yan kadan Kuma ba biskit da cingam su a kasa suke na Ma'u kuma bisa tabarma.

Da murnata nace Inna wa aka kawoma kaya ne haka na Ma'u ne? "tace eh wannan na mai kashin arziki ne, sai ta nuna yan kaɗan ɗin wannan kuma na mai kashin tsiya ke da Ma'u "zaro ido nayi nace Inna aini banda saurayi" Lado mai jakkai ne ya kawo maki "innalillahi!!

Inna jaki fa gareshi kuma matan shi ukku Inna abarni na zaba kamar yadda Ma'u ta zaɓa "iyye daman mijin Ma'u kika sama ido kenan kalar shi kike so to bari kiji ke da gidan sarauta ko kudi sai dai gani sai hange har abada,da wane asalin naki za'a so ki? da shegan takar taki? dan kin samu Lado mai jakkai yace yana so "kuka na aza dan Allah ki taimaka man,wallahi ba irin mijin Ma'u nace nike jira ba kinga shi tsoho ne kuma ga mata ga yara,gashi ko abinci ba'ayi gidan shi wannan jakin shi kadai gareshi.

"Makwabta kushigo kuji bakin ciki fili shegiya na zabar miji to bari kiji idan ubanki yazo kikace baki son Lado wallahi sai na maki bakar azabar da baki taɓa jin kalar labarinta ba "kuka nike sosai na tashi na nufi daki.

********************

A Masarautar katsina ko Ina bushe bushe ake da kide kide.

A fada suka zauna Sarki ya fito suka gaisa da Yarima cikin girmamawa.

Aka kaisu masauki, abinci babu kalar da ba'a aje masu ba.

Wurin da aka kaishe ya kayatu.

Harda lambu a cikin wurin,wanka yayi ya fito lambun wurin ya mashi kyau sosai.

Zuciyar shi fes babu damuwa a tare da shi harya manta abinda ya kawoshi.


Yana wurin zaune har zuwa la'asar ya tashi yayi wanka yayi sallah.

A cikin gidan sarki kuma Gimbiya Kursim ce da kawar ta Hanan diyar Governor din garin itama daka ganka kasan wayayya ce kuma da alamun kudi na aiki a jikin ta.


Mai makeup suka dauka daga Abuja tana ma Kursim heavy Make-up ake mata tamkar wata Amarya.

Wow my dear kingan ki tamkar wacce zata je gasar kyau na duniya.

Red din rigane a jikinta wacce tayi order din shi a Dubai rigar tayi kyau kuma wacce tasa rigar itama mai kyau ce, sai abun ya zama na biyu ga kyan riga ga kyan mai riga.

Kursim nada kyau sosai wanda ba kowa ne namiji bane zai ganta ya dauke kai ba ,tana wayewa sosai kasancewar baki daya rayuwar ta a turai tayi ta .

Mai Makeup ta gama ta fita.

Wallahi wannan guy din ko dutse ne shi da baya motsi yau idan ya ganki sai yayi motsi.

Ance wata guda zaiyi?? murmushi tayi tace wallahi one week yayi yawa guy din nan sai ya haukace.

Da fata tayi tace "My dear As soon as that is done the Prince is bound to fall in love with you".


Umm murmushi Kursim tayi, tace my friend Yarima ba kalar sauran maza bane yana da wahalar sha'ani.

Duk yawan fadin Yarima da kika ji ina yi to soyayyar bangare daya ce.

"What do you mean? I don't understand your proverbs Soyayyar bangare daya".

Murmushi Kursim tayi tace ina nufin ni kaɗai ke son shi shiyasa iyayen sa suka turoshi dan mu shaku yanzu ne za'a fara soyayyar bawai an turo shi dan mu kara son junan muba.

Zaroo ido Hannan tayi tace "Wallahi kursim I can't do that akan na miji" ke dai bakisan so ba .

"Towai ya taɓa yin soyayya ko yanzu zai fara?"

Soyayyar ce tasa baya shiga cikin jama'a tsawon shekaru tara "kamar ya inji Hanan cikin Surprise", mace guda yake so tunda yake a rayuwar sa tunda aka haifeta yake sonta shi ya zama Nanny shike mata komai, har ta kai shekara tara ranar data cika shekara tara ranar aka daura masu aure da ita, kuma ranar aka sace ta lokacin babanta yana Governor akan hanyar su ta zuwa airport,wa'inda suka sace ta sukace suna bukatar ya janje takarar shi ta Governor lokacin yayi four years zai kara wasu,yace sai sun maido mashi ɗiyar shi kana ya janye,sunyi maganar da daddare koda aka tashi da safe a bakin get din Government House aka iske wani kaset aka kai ma Baban ta koda aka kunna,sun daure mata hannu tana kuka tana fadin Yaya Anuu kazo katai dani,kawai suka caka mata wuka,nan take ta mutu suka dauketa suka kaita cikin wani gulbi suka yarda ruwa ya tafi da ita ko gawar basu kawo masu ba.

Harda hauka saida Prince yayi ya dade baya kasar yana asibi,bayan ya warke sai ya fara shan giya ta zama ruwan sa wallahi Hanan idan kika ga yadda mahaifin shi ya koma sai kin tausaya ma Family,tunda wannan lokacin rayuwar sa ta chanza,da kyar mahaifin shi ya rabashi da shan giya bayan ya kaishi Saudia wajen Friend dinshi.

Akwai lokacin da ina karatu,akace Prince yazo London lokacin ana Birthday din shi,naje nakai mashi Gift bai kalli Gift din ba bareni ya kalleni.


Babu time yanzu yana jirana ina so naje naga da wace kalar fuska yazo man .

"Please My Friend ina da questions da yawa akan rayuwar Prince ki bari mu ida labarin, "sorry Hannan nasan Mom din ba zata hanaki kwana anan ba kibari na dawo na ida maki labarin Prince.

Ta mike zata fita "Hanan tace ya sunan yarinyar?"


MANAL daga haka ta juya ta fita.

Zuciyar ta cike da tunanin wane kalar tarba Prince zai mata??


Qurrah
[1/28, 3:02 PM] GOLDEN PEN WRITERS ASSOCI: *JARABTAR MU*


*Writing by-Qurrah✍🏽*




https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/



*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*




*~We are bearer's of so golden pen🖊~*

*~we write assidiously perceive no pain~.*

*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*

*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*



Page-9-10


DEDICATED TO......MY SISTERS😘



_Bissimillah Rahmanir_ _Rahim_


----------------Kallon ta yake yadda take Driving cikin kwarewa da murmushi dauke a fuskar ta.

Kallon shi tayi tana murmushi tace, "ya dai Prince, ko kana bukatar wani abu bayan fitar?". Girgiza kai yayi.

Murmushi tayi na jin dadi da alama kwalliyar yau ce tayi masa, ta san ita mai kyau ce, ta yarda da kyaun ta, ta san ko bai so ta dan komi ba zai so ta dan kyaunta.

Motsa baki yayi alamar zai yi magana, ta dan rage tafiya tana kallon shi, cikin Cool voice dinshi yace, "daman kina iya driving gaskiya bazan iya ba akwai wahala, kinyi kokari". Cikin mamaki take kallon shi.

Tunda ta taso da gata gaba da baya, amman bata dauki driving abu mai wahala ba, amman shi mamaki yake yake, wannan wane irin gata ne, ai abun yayi yawa.


Har suka isa cikin wani estate dake gefen garii.

A cikin gidajen estate ta shigar da motar, har tayi parking bai ce komi ba.

Gidan ya tsaru sosai, kallon gidan Yarima yake yana zaune cikin mota.

Fitowa tayi daga motar tayi gaba, har ta dan kusa kai wajen kofar parlon ta waigo bata ga Prince ba.

Baya ta koma yana zaune cikin motar yadda ta barshi.

"Kenan ita ma motar baya iya budewa itama wahala ce? wannan wane irin Mulki ne da izzah??".


Murmushi tayi ta bude mashi motar.

A hankali ya sauko da kafar shi kasa, ya fito yana kara shan kamshi.


Kallon gidan ya gama yi yace; "babu

Please Login or Register in order to submit comment