Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yaro"


Cikin sauri ta budi security din dake tsaye bakin kofa tace;"kayi maza ka kira su Mai martaba kiran gaggawa"






MARYAM D'ANKUDII {QURRAH}
[4/4, 8:26 PM] GOLDEN PEN WRITERS ASSOCI: *JARABTAR MU*




*Written by-Qurrah✍🏻*


Page-77-78

https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/

*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*

*~We are bearer's of so golden pen🖊~*

*~we write assidiously perceive no pain~.*

*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*

*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*


*Addu'ar Da Wanda Ya yi Mafarki mara kyau zaiyi.*

أَعُوذُ بِاللهِ مِنَ الشَّيْطَانِ الرَّجِيمِ ثَلاَثٍ مَرَّاتٍ.
a'uzu bi-l-lahi mina shaytani r-rajeem (3)
Wanda ya ga abu mummuna a mafarki, to sai ya yi wadannan abubuwan:-
- Ya yi tofi ta gefen hagunsa sau uku.
- Ya nemi tsarin Allah daga shaidan da kuma sharrin abin da ya gani, sau uku.
- Kada ya gaya wa kowa wannan mafarkin.
- Ya juya daga kwibin da ya kasance yana kwance a kansa.


Idan ya so, ya iya tashi ya yi sallah.

DEDICATED TO.....MY SISTERS😘


Bissimillah Rahmanir Rahim



Page-77-78



---------------Farhanaa tace;"Wai Yaya mu 'ya 'yan aljanu ne?"

Kallon ta yayi cikin azama ya damki hannun ta yace da karfi;"mu gudu"


Aiko cikin sauri Farhana ta bishi da Ammie da Mummy suka tsaya kallon su duk sun rikice cikin sauri Kulsoom ta juya tayi wajen Security din dake bakin get din shigowa part din Ammie.


Suna ganinta a guje sukayo wajen ta cikin sauri haka yaba su Farhana damar fita.

Cikin tsawa tace;"ku kamo yaran da suka fita yanzu-yanzu kada abari subar gidan nan akamo man su"


Suka juya sukabi su Farhana a guje.


Anuwar bayan sun gaisa da Liman yasa aka kawo mashi abinci.

Komawa yayi ya zauna yana jiran ya gama.


Liman ya kalli Sani yace;"bazan ciba saboda nasan Fura na nan na jira yazo mugama abinda zamuyi mu tafi chan"


Sani yace;"Baza ai hakaba nan gidan aka baka masabki Yarima bazai bari ka tafi bakaci komi ba dan haka bari na kira wayar Inna a aiko maka yanzu"


Liman yayi murmushi yace;"to shikenan yazo muyi kaga kamin a kawo man mun gama tunda yace ba'a daukar lokaci"


Sani ya juya yaje inda Anuwar yake zaune ya fada masu yadda sukayi.



Anuwar ya mike ya isa inda Liman yake.


♦♦♦♦♦♦♦♦


Ina zaune aka kira wayar Inna na mika mata.

Bayan ta aje tace;"tashi Nana kiyi maza ki dauko mayafi yau babban bako garemu a gidan Sarki, ki kai mashi fura da kin fita zaki samu abin hawa"


Na mike cikin sauri nace;"to Inna ai a shirye nake"

Saboda yarana yasa nace haka nayi kewar su sosai inaso na dauko su.

Tsaye nayi cikin daki Ina murmushi yau zanga Yarima kenan, wani abu na tuna cikin sauri nayi wajen kayana na dauko zoben nan ina murmushi nace ya dace da wannan babu abinda zan saka mashi dashi amman kyauta koya take tanada amfani, shekara kusan biyar kenan inason nayi mashi kyau murmushi nayi na saka shi a Babban d'an ya tsana saboda idan Inna tagani hanani zatayi.

Inna ta zuba fura na mike tsaye na saka Hijab dina tabani kudin mota na fita.


Ina fita nayi bakin titi duk sainaji daban saboda ban fita ko kadan.


Ina bakin titi rike da sabuwar kwaryar Inna a hannu na saiga mai adai-daita sahu yazo.


Yana zuwa na fadi inda zani muka tafi.

Kara kallon garin nike duk ya chanza rabona da shiga Bauchi tun da nabar ta.


♦♦♦♦♦♦♦♦


Farhan yaja Farhana suka boye bayan wata mota dake gefen wani daki, suna kallon yadda Security din wajen kebin dogon titin gidan da kallo babu yara sai lekawa suke wurare .

Farhana sai zufa take tace;"Yaya dan Allah kayi hakuri nasaka wahala wallahi haka nace mata muga diyar hannunta ta araman na taba shine tace wai Allah ya kyau ta taba yarinyar kazama kamar ni diyarta, shine nace niba kazama bace shine ta turani na fadi, wallahi ba laifina bane"


Jin motsin mutum yasa sukayi shiru suka kara labewa.


Anuwar na zaune yana fada mashi yadda fuskar ta take.

Saboda shape din fuskar su guda da MANAL hakan yasa yake zanen shi cikin kwanciyar hankali.


Yadda shape din girarta take ta kusa hadewa saboda cika da tayi da idanunta girman su dai-dai dana MANAL sun dan ciko su basuyi yawa ba su basuyi kadan ba sai dogon hancin ta.

Sani na tsaye yana kallon ikon Allah.


Anuwar na gama zanawa ya dauki photon yana kallo rude ba dai-dai yayi zanen ba kusan kamar su guda da Manal dan Manal dinshi na yarinya wannan na babba.


Sani yace;"amman wannan kamar Nanar Inna maman yan biyu"

Cikin sauri Anuwar ya kalle shi.


Jin shiru Security bai dawo ba yasa su Mummy suka fito dai-dai lokacin da Abie da Daddy suka iso nan su Mummy suka basu labari kuma yara sun bace.


Daddy yace;"ayi sauri a bincike ko ina na gidan a binciko su" dan danan aka fara neman yara Daddy yace yaron mayyar yarinyar nan ne.


Suna zukunne kusa da motar da aka dauko su Sani daga airport gefen dakin dasu Anuwar suke ciki.


Hannun farnana daya fito daya daga cikin security din ya taka.

Wata kara ta saki wadda saida Farhan ya rude yayi zumbur yayi bisa titin gidan saboda rudewa.


Security din dake tsaye suka bishi yayi hanyar babban get din gidan.


Dai-dai lokacin da Nana ta shigo get din ai yana hangota yayi wajen ta yana ihu, itama hangen shi tayi ana binshi.

Mamaki take lafiya ko laifi yayi cikin sauri tayi wajen.


Yana zuwa inda take yayi bayan ta ya boye yana kiran sunan Farhana.


Cikin tashin hankali tace;"ka fadaman miyasamu Farhana laifi tayi?"


Daga kai yayi ya jikin shi sai kyarma yake.


Security din take tsaye gabana suka zagaya suka fizgo Farhan dake bayana wani irin ihu yake nabi na rude lokaci guda na fara Kuka ina binsu ina cewa kuban d'ana da alama basujin abinda nike cewa.




Hanko Farhana nayi tana ihu a hannun wani nayi wajen a guje kamar ma haukaciya ina isa ta ganni ta fara ihu tana cewa;"Ummie zasu kashe mu Ummie wai sun ce mu yaran Aljanune Ummie kada su tafi dani"



Rudewa nayi na hango Farhan sunyi nisa.


Wani irin Ihu nayi nayo wajen Farhana dake mikoman hannu.


Anuwar dake tsaye karar TV yasa basajin komi chan yaji irin ihun daya tabaji.


Liman yayi shiru Sani yace;"kamar muryar Nana"


Cikin sauri suka fito dai-dai lokacin da nasaki kwaryar hannu nayi wajen Security ina kuka Ina son ban bare Farhana a hannun shi.


Cikin tsawa Anuwar yayi ma Securityn magana ya saki Farhana bata tsaya kallon suwaye ba.


Ta kama hannun Farhana tabi hanyar da aka dauki Farhan a guje.



Dai-dai lokacin da ta hangi mutane tsaye an aje Farhan a gaban su.


Chan ta nufa a guje rike da Farhana.


Tana zuwa ta iske an saka Farhan a gaba kowa na kallo.


Tana isa wajen taji an kwala mata kira tayi saurin juyawa saboda muryar da taji.


Tana waigowa taga Yaya Sani da Baban ta da wani matashi daya kura mata ido.


Kuka take sosai kamar ranta zai fita ta isa inda suke.


Bakin ta na kyarma tace;"Ba...ba"


Yace;"Na'am Na...na"



Wani irin ihu tayi wadda hakan yasa duk mutanen dake wajen hankali su ya dawo kanta.


A gefen Anuwar take hakan yasa tayi baya-baya zata fadi ta fada a bisa kirjin shi



Rumgume ta yayi ya zugunna kasa tana bisa jikin shi, Daddy da Abie dasu Mummy da Ammie dasu Kulsoom sukayo wajen.


Kulsoom ta kalli mace a bisa jikin Anuwar yana girgiza ta.



Farhana da Farhan sukayo kanta suna cewa;"Ummie kitashi kada su tafi damu zasu cutar damu, Ummie sunce mu yaran Yarima bane Ummie kitashi mu koma wajen Inna tunda bamu da Baba, mun hakura Ummie bazamu kara neman Baban mu ba"

Jin kalaman su yasa zuciyar shi tsinkewa cikin azama ya d'ago mata hannu domin yaji tana da rai, hakan yaba duk wanda ke wajen damar kallon zoben dake d'an yatsan ta Babba.




MARYAM D'ANKUDII{QURRAH}
*JARABTAR MU*




*Written by-Qurrah✍🏻*

Page-79-80


https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/

*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*

*~We are bearer's of so golden pen🖊~*

*~we write assidiously perceive no pain~.*

*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*

*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*


*Addu'ar Da Wanda Ya yi Mafarki mara kyau zaiyi.*

أَعُوذُ بِاللهِ مِنَ الشَّيْطَانِ الرَّجِيمِ ثَلاَثٍ مَرَّاتٍ.
a'uzu bi-l-lahi mina shaytani r-rajeem (3)
Wanda ya ga abu mummuna a mafarki, to sai ya yi wadannan abubuwan:-
- Ya yi tofi ta gefen hagunsa sau uku.
- Ya nemi tsarin Allah daga shaidan da kuma sharrin abin da ya gani, sau uku.
- Kada ya gaya wa kowa wannan mafarkin.
- Ya juya daga kwibin da ya kasance yana kwance a kansa.


Idan ya so, ya iya tashi ya yi sallah.

DEDICATED TO.....MY SISTERS😘


Bissimillah Rahmanir Rahim



Page-79-80



---------------Jikin shi har kyarma yake yayi saurin sakin hannun ta.

Abie ne ya matso inda suke ya ɗaga d'an ya tsanta yaga lallai zoben tambarin masarautar sune wanda yaba Anuwar, kallon Anuwar yake cikin mamaki lokacin Anuwar ya dukar da kanshi a kirjinta domin yaji numfashin ta.

Mike yayi da ita a hannu ya kalli Dad yace;"Dad ka taimakaman ka kira Doctor kada ta mutu idan ta mutu nima mutuwa zanyi Abie kutai makaman MANAL dina ce"


Jin ya ambaci MANAL yasa su duka sukayi tunanin lallai ya zauce.


Cikin sauri Mummy ta kamashi sukayi hanyar part din ta.


Suna tafiya saura suka biyo su baya.


A bedroom aka shigar da ita aka kwantar.

Waya Mummy tayi tazo ta dafa Anuwar da yake rumgume da ita kamar zai maidata cikin jikin shi.


Dafashi tayi amman bai dagoba sai kara kan kameta yake.


A haka har Doctor ya shigo dakin.


Mummy fita tayi dan tasan Anuwar bazai fita ba.

Tana fitowa ta iske su Mai martaba a parloun ta tare da yara tunda ta fito take kallon yaran da idanunta da sukayi jawur saboda kuka, sun rike Sani da kagan su kasan sun tsorata.


Kallon yarinyar tayi ta kalli photon Manal dake parloun, ta maida kallon ta ga yaron komi nashi kalar na Prince kamar yayi kaki, zuwa tayi ta zauna tayi shiru kamar yadda kowa yayi shiru a parloun.


Farhana dake hawaye ta kalli Sani tace;"Kawu su bamu Ummien mu mutafi gida, wallahi bazamu kara dawowa ba mun yafe zamu zauna bamu da Baban"


Mummy da hawaye suka cika mata ido tace;"minene sunan maman ki"

Farhana tace;"Nanah"

Mummy tace;"Baban kifa"


Farhana tace;"Yarima"

Su duka parloun suka maido hankalin su wajen ta.

Nifra ce ta shigo parloun kamar an jefota.


Farhana ta kura mata ido tace;"Yaya kalli mai kama da Ummien mu su bamu tamu wannan ce tasu"


Sukabi hannunta da kallo inda take nunawa Nifra dake tsaye tana raba ido.


Mummy tace;"Sani su waye dangin yaran nan"


Sani cikin girmama ya nuna Baba yace;"a gidan mu take zaune tsawon shekara shidda saboda dangin ta sun koreta saboda cikin yaran nan, itace wadda Yarima ke nema shiyasa naje na taho da Baban ta to bansan ita bace saida aka aikota ta kawo mashi fura ta ganshi su kuma yaran sune wadan da Yarima ya taba ba Maman su jini wasu yan biyu da aka taba haihuwa a MANAL hospital yace shine zai zaman masu uba to shine da ya tafi bai kara dawowa ba sai yanzu shine idan suka tambayi waye Uban su saina ce masu Yarima shine suka rike abun kullun suna maganar shi yanzu da yazo shine na kawo su sugan shi kwanan su biyu a tare dashi cikin gidan nan"


Duka dakin suka hau kallon yaran, Mummy cikin tashin hankali tace;"sune nan kenan Sani?"

Ta nuna wani katon photo na Yarima da Yara a hannun shi dake a parloun ta.

Yace;"eh sune ranar da aka haifesu ne nan"

Mummy ta kalli Dad tace;"Inagafa itace yarinyar da Yarima yayima fade a Katsina"

Cikin tashi hankali su Abie suka kalleta Ummie dake kusa da ita ta rike mata hannu cikin tashin hankali tace;"yaushe Yarima ya taba ma mace fade?? Yarima dako kallo mace baiyi kai Hajiya kila de kin manta kode Jawad kike nufi?"


Mummy ta kalli Dad tace;"ya kamata su sani tunda abin yazo a haka, ya kamata kada abar yaran nan subar gidan sai anyi tabbacin yaran waye, nifa abin ya fara rudani inaga yaran Yarima ne"


Nan Mummy ta fadi yadda akayi shi yasa yake neman ta.


Su duka banda Sallallami babu abinda suke

Mai martaba ya kalli Baba yace;"kaine Uban yarinyar?"


Yace;"Eh sanadiyar zuwan ta tallah wani yayi mata fade bamusani saide aka tashi tana da ciki a lokacin baninan wannan shine sanadiyar barinta gida"


Abie yace;"ta fadamaku sunan wanda yayi mata fade ko tasan shi?"


Baba yace;"banson komi game da haka ba saide munyi magana ta kawarta tace cikin dare abin ya faru bataga fuskar shi saide zobe da yabata, inaga zoben ne a hannunta"



Abie da Ummie suka dauki sallallami, dai-dai lokacin da Doctor ya fito.



Suka maida kallon su.

Dad yayi saurin mikewa yace;"ina Anuwar ya lafiyar shi? Yana lafiya?"

Doctor Ashraf yace;"eh saide yarinyar itama ta tashi daman lafiyar ta kalau firgitar da tayi ne yasa numfashin ta daukewa ta suma, amman yanzu Alhamdulillah zaku iya ganinta"



Cikin sauri su Farhana dake jikin Sani kwance sunyi lamo kamar suna bacci suka mike


Farhan yace;"Kawu muje mu dauki Ummie kada ta kara faduwa"


Sai lokacin su Abie suka kara kare mashi kallo yadda yake maganar da kuma siffar jikin shi take.



Nanah na bude ido ta jita cikin jikin namiji kuma irin kamshin da bazai iya gushe mata ba, bata yadda itace ba kara runtse ido tayi tana cewa a fili;


"Ya Allah ka taimaka man kada ya kara cutar da rayuwata shine ya kara dawowa ya Allah kasa bashi bane Yarima ba ya Allah ka taimaka man zai kara mani wani cikin"


A hankali ta bude ido ta kalli girjin shi, cikin sauri tayi saurin mikewa daga jingine da take da jikin shi.



Zata fizge daga jikin shi yayi saurin rikota ta kara fadowa bisa Kirjin shi, kan kameta yayi ya matse ta gam yana sakin numfashi.



Sun dauki lokaci a haka su duka zuciyo yinsu bugawa suke kamar zasu fito Nana ta kasa kwace wa sai hawaye dake bin kumatun ta shikenan tata ta kare.


Tuna abinda yayi mata yasa cikin zafin nama ta tura shi.


Baya yayi ya jingina da gado kallon juna suke su duka idanun su sunyi jawur.


A hankali ya furta;"MANAL"


Kallon shi take ta kasa dauke idon ta akanshi kanta ke wani irin juyawa wani irin ciwo da zafi kanta ke mata.


A hankali take maida numfashi, jitayi numfashin zai dauke zatayi baya yayi saurin rikota ya kara rumgume ta.


Shiru tayi ta kwanta a bisa kirjin shi wani irin ciwo kanta keyi mata kamar zai cire data runtse ido saita hango wasu mutane na dawo mata, amman ta kasa tuna komi.


Jin ana shafa bayan yasa ta tuna mike faruwa cikin sauri ta mike tace;"Baba na, na shiga ukku ni Nanah"


Tashi tayi daga jikin shi kallon juna suke tace;"kaine Wanda ka rabani da Babana ka rabani da mutunci na kasa jama'an kauyen mu suka tsaneni ka shiga tsanina da Baba ka nisan tani da iyaye na na haifar maka yara da bakasan kamannin suba, taya zan yafe maka"


Kuka take sosai ya kasa dauke idon shi akanta, saboy gaban shi na faduwa jikin shi duk ya mutu.

Tace;"kai waye? Ya Allah kasa bashi bane Yarima dan Yarima na insha Allah bazai zama macuci ba irin ka, ka fadaman kai waye ina Baba na?"



Turo kofa akayi suka shigo tayi saurin juyawa.


Kallon su take tana lumshe ido kamar tasan su.


Mummy tace;"MANAL...?"


Dad yace;"Hajiya kada ki rude mana kamar Anuu akwai kamanni fa, wasu idan kika gansu sai kice yan biyu ne amman basu da wani alaka ya kamata ki saita natsuwar ki abi komi a hankali"


Kallon shi tayi tace;"Ina cikin hankali na, nifa uwace taya za ai na dau cikin ta na haifeta sannan nakasa gane diyata wallahi wannan itace kuma yaranta yaran Anuwar ne itace wadda Anuwa yayi ma fade lallai Anuwar Yau na kara yadda babu wata Aljana data shafeka lallai tun shekarun baya kaga MANAL ba aljana bace"



Abie yace;"kuyi shiru hakanan mubi komi a hankali bazamu bari subar gidan nan ba har sai an gano gaskiya"



Farhana ce ta kwace daga hannun Sani tayi wajen Mamanta tana isa ta rumgume ta, Farhan ya iso yana murmushi Farhana ta dago ta kalli Anuwar tace;


"Baba kaga Ummien mu ko, dan Allah kace masu su kyale mu mu zauna dakai muna sonka sosai kada su rabumu su Indo suyita mana gori bamu da Baba, Baba munji dadi da muka ganku a tare Baba kaman alkawari bazamu kara rabuwa ba Ummie zata dawo nan"


Rumgume su yayi baki daya yace;"bazamu kara rabuwa ba har abada MANAL tawa ce"


Cikin saurin nayi saurin fita da jikina cikin nashi.


Kaina a kasa saboda akwai mutane a dakin amman ya rumgume mu.


Sabkowa nayi daga bisa gadon.

Cikin sauri Anuwar ya mike ya rungumoni ta baya.

Saura kadan numfashi na ya dauke saboda yadda naji anrungumeni a gaban su Baba.


Kasa motsi nayi na kasa daga kai na kalli mutanan cikin dakin.


Juyowa yayi dani ya kara rumgume ni yana sakin ajiyar zuciya.


Yace;"Bana iya rabuwa dake nayi kewar ki, bazan iya rayuwa mai dadiba idan babuke ni nasan kece kika dawo man"


Jikina kyarma yake nakasa motsi a gaban kowa yau Namiji ya rungume ni, hadda mahaifina da yaran dana haifa runtse ido nayi.


Anuwar ajiyar zuciya yake jiyake kamar ya maidata ciki idanun shi sun makan ce ya manta da wasu iyayen su da yaran dake zaune kara rungume ta yayi sosai yace;

"Kiyiman alkawarin bazaki kara rabuwa dani ba zamu kasan ce a tare"


Cikin daga murya Dad yace;"bazaku kasan ce a tare ba har abada, kuma kasaki yarinyar mutane so haukane akan ka aka fara mutuwa? soyayyar Manal tana niyyar maidaka mahaukaci miyasa bazaka dan ganaba ka dauki kaddara a gaban iyayen ka ka rungumi mace kasake ta nace"


Mummy tace;"wallahi wannan diyar kace"

Dad ya kalleta rai bace yace;"daman da saninki yake komi kenan? Kece kika goya mashi baya kenan"

Mummy zatayi magana ya daga hannu yace;"idan har Manal ce miyasa ta kasa ganeki a matsayin ki na mahaifiyar ta, Anuwar yafi kowa kusan ci da ita miyasa bata ganeshi ba ai yakamata ko maganar shi taji ta dawo hankalinta inma losing memory tayi miyasa tun tuni bata tuna kowa ba, har alakar kusanci ta shiga tsakanin su bata tuna komiba, yanzu gamu a gaban ta tana mana kallon bata sanmuba a haka zata zama diyar mu"


Mummy ta taso tazo inda muke tsaye hannu na cikin na Yarima tace;

"Kifadaman wacece ta haifeki waye mahaifin ki, suwaye dangin ki na ainahi?"


Hannuna na kyarma na nuna Baba ina hawaye.


Kallo dakin nayi banga su Farhana ba, na kalli Anuwar ina mashi kallon tuhuma.


Yaya Sani ne ya shigo ganin ina waige-waige cikin dakin yasa yace;"suna kasa wajen Inna"


Ajiyar zuciya nayi, Mummy ta isa gaban Baba ta kalle shi ido cikin ido tace;


"Daga ganinka ko a fuska kai mutunan kirkine nasan bazaka mana karya ba saboda akwai gobe kiyama zamu koma ga Allah inaso ka fadaman gaskiya Nanah diyar kace?"


Baba ya kalli mutanen yace;"dogon labari ne a tsaye bai dace ba"


Dad yace;"kinsan bazan yadda da wannan dramar da kuka shirya keda Anuwar ba, idan har MANAL ce muna da tabbacin mutuwar ta ko ana mutuwa a dawo ne?"


Mummy ta kalleshi tana hawaye tace;"Ba'a mutuwa a dawo, amman kasan Alhaji NURA SAIKAYI babban matsafi ne idan mutuwar Manal bata gamshe shiba bai yadda da itaba zai iya abinda zai mantar da ita dangin ta, kada ka manta lokacin da ya mutu tsafin yasa babu wanda yaje wajen gawar sa saboda tsoron da yakeba mutane ta yadda Allah ya maida halittar sa, kaima a lokacin Allah ne ya baka mulkin shiyasa kayi shi, Allah ne ya nuna mashi shike badawa, zai iya komi dan ya rabaka da diyar da kafiso a duniya maybe yaga mulki dole sai kayi shi, hakan yasa yayi maka haka dan ya dasa maka bakin ciki"



Shiru Dad yayi maganar ta tayi tasiri a zukatan wadan da kenan.

Abie yace;"Tabbas hakane zai iya mantar da ita koda tanason tunawa ta kasa, amman yanzu abin yafi mu saurari bayanin wannan bawan Allah sannan muje wajen Babban yaron shi Alhaji NURA zamuji komi dan tun kamin ya mutu suka rabu, hakan yasa Alhaji NURA saida ya lalata mashi dukiya ya koma baida komi Koda wannan ya ishemu ishara sannan a auna jinin yarinyar danaka dana Anuwar dana yaranta wannan shine yanzu muje zuwa Salllah idan aka gama sai a zauna ayi magana hankali kwance yanzu zansa ta taho da yaron Alhaji NURA kamin mugama Sallah yanzu azo a dibi jinin ku"


Dad ya aminta da maganar Mai martaba suka juya har zasu fita Mai martaba ya juyo ya kalli Anuwar daya rike hannun Nanah kamar za'a kwace mashi.

Yayi murmushi yace;"Kai baka Sallar, kuma matar ka ta fita tana kuka ya kamata kaje wajenta, tunda taji kanada wasu yaran kaga ka mata laifi"

Mummy ta kallesu tace;"aiko a kaunar da Anuwar kema Maifurar shi kasan akwai alamun tambaya, Ammie kalli yadda sukayi kyau"


Ammie murmushi tayi tace;"Nifa yaran nan inde ba yaran Aljanu bane to yaran Anuwara ne babu tantama tuni na yadda, yaro karami amman ace yanada zuciya da izzah sannan komi nasu iri daya ai abun dubawa ne lamarin"


Ammie ta kalle shi tace;"muje kayi sallah a cikin jam'i"


Rumgume ni yayi ta baya ya kwantar da kanshi bisa kafadata yace;"Ammie bazan iya rabuwa da ita ba, a tare zamuyi"

Mummy tayi dariya Ammie tace;"idan akayi bincike ba Manal bace saikayi istigifari akan shige mata da kakeyi ko kunyar yaran ka bakaji a gaban su ka rumgume Maman su hadda lumshe ido, duk randa ka kara haka a gaban mu saina saba maka kai har yau bakajin kunyar mu"


Mummy tace;"kagan ka Anuu yawan shige mata yasa a wanchan karon Mai martaba yace baza'a barku kutafi ba babu aure ta fara girma shine yanzu ma a gaban shi kayi halin naka, koda yake na manta kace idan kana tare da Manal baka iya control din kanka"



Ta ida maganar tana dariya suka fita suna murmushi.


Maida kallon shi yayi gareta jan hannunta yayi ya zaunar da ita gefen gado ya kura mata kallo duk saita ta kura saboda babu Hajib a jikinta.


Yace;"yanzu Manal baki gane Yaya Anuu din kiba?"


Na dukar dakai nace;"nide banson kuba kasa karman hannu kuma kabar rikeni babu kyau kumani tafiya zanyi saboda babu kyau keban cewa tsakanin Namiji da Mace"


Murmushi yayi ya maso saide najini cikin kirjin shi.

Gabana faduwa yake na tuna lokacin da yasakani a kirjin shi, dago hannuna yayi yana kallon zoben yace;"daman kina saka shi?"


Dagowa nayi na kalleshi nace;"Ban taba sakashi ba sai yau, kyauta nazo nayi dashi shiyasa na saka shi kuma bana bukatar ka sake tabaman jiki"


Kallona yaie ya maimaita...kyauta.

Yace;"wazaki ba kyautar shi"


Na kalleshi gabana na faduwa saboda yana man kwarjini nakasa mashi rashin mutum cin dana tanada ga duk wanda ya bataman rayuwa amman shi na kasa mashi na dukar da kaina nace;

"Saboda Yarima yasa nazo gidan nan inason na ganshi shizan ba, ka fadaman wanene Yarima na asali wanda ya taba ban jini wanda ya ceto rayuwata"


Murmushi yayi yace;"miyasa baki yadda danine Yarima ba"

Kai tsaye nace;"saboda duk d'an Sarki Yarima ne"

Murmushi yayi yace;"muje muyi alwala lokacin Sallah na kurewa kuma mu ake jira Matar Yarima dan gana son Yarima a idanun nan naki"

Mikewa nayi ina kallon kozanga Hijab dina.

Nunaman bandaki yayi yace;"ga toilet nan"

Na shiga ina kallon wajen Babu buta hakan yasa nayi tsaye shigowa yayi nayi saurin juyawa nunaman yadda zanyi amfani dashi yayi.


Nayo alwala ina fitowa an ajeman Hijab da abun Sallah.

Zuwa nayi nasaka duk yana tsaye yana kallona.


Natada Sallah ina gamawa naga shima yana sallah yana gamawa na mike na linke abin sallar na mika mashi ya amsa.

Kama man hannu yayi yazo bakin madubi dani ya aza kanshi bisa kafadata yana ganin hawaye na zuba yasa yayi saurin daga kanshi ya juyoni.


Nace;"miyasa zaka kara cutar dani a karo na biyu, niba matar ba amman tunda muka hadu kaki barina"


Shiru yayi yana goge mata hawaye.

Kama hannunta yayi batace mashi komi ba suka fito dakin.


A hankali suke taka takalen benen dakin suna sabkowa jama'an dake parloun suna kallon su

Cikin sauri Mummy ta mike ta kamo hannun Nana.

A bisa kujera ta zaunar da ita ta zauna itama.

Aza kan Nana tayi bisa jikinta.

Mai martaba yayi sallama yace za'a diban jinin su kana yaron Alhaji NURA ya fara magana sai Baba.


Bana son allura hakan yasa da za'a sakaman abun dibar jini na runtse ido cikin sauri Yarima ya dawo kusa dani.

Shida Mummy sai faman sannu sukeman Mummy ta rumgume ni tana sannu Anuwar kuma yana rike da hannu na yana sannu.


Doctor yafita da jinin mu, Mai martaba yayi gyaran murya yace;

"Muna jiran ka"

Ya kalli yaron Alhaji NURA

Yaran Alhaji NURA ya gyara zama zai fara magana.....kowa ya maida hankishi ga yaron Alhaji NURA danjin ya labarin yake.


MARYAM D'ANKUDII {QURRAH}
*JARABTAR MU*

Page-83-84


*Written by-Qurrah✍🏻*




https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/

*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*

*~We are bearer's of so golden pen🖊~*

*~we write assidiously perceive no pain~.*

*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*

*~A product of our

Please Login or Register in order to submit comment